Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba .
sai kawai tafi daukar abin amatsayin mafarki ne irin wanda tasaba .
ko shigowar Deeni batajiba har sanda ya karaso gabanta .
bata sani ba.
zama yayi a Gefen gadon tare da rungumeta a faffadan kirjinsa.
yana kaiwa wunyata sumba. Ita kuwa nablah jin an rungumeta yasata dawowa Daga duniyar tunani data lula tare da sauke A jiyar zuciya da karfi ta tsura masa shanyayyun idanunta tana narke fuska .

Shima rikitattun idanunshi ya tsura mata yana kallon 'cikin kwayar idanunta masu narkar da zuciyarsa da gangar jikinshi .
ahankali yake fidda wani numfashin sama sama tamkar wanda yayi gudun tsare .
wani irin feelings yake ji yana tasomasa marar misaltuwa a duk lokacin da yake tare da ita.


sake lafewa tayi sosai a jikinsa tana sake sauke ajiyar zuciya tana shakar daddad'an kamshinsa.
sun d'auki tsawon lokaci a haka kowannensu da abinda zuciyarsa take saka masa ahankali ya d'agota daga jikinsa ya kafeta da rikitattun idanunsa, itama shi take kallo da shanyayyun idanunta.

fuskarsa ya had'e da tata yayinda sukejin numfashin juna cikin maganarsa Me kamada rad'a yace "tunanin me kikeyi ne haka?"

Muryarta a raunane tace babu komai fa tare da kauda fuskarta Daga gareshi.
yace "koma meye yakamata ki rage wlh bason tunaninnan da kike yi , kar yazo yashafi lafiyar babyna"
yafad'a yana kashe mata ido tareda shafo cikin nata cikin wani irin shauki yakarasa fadar hk.
Bakinshi yakai daidai tsaitin kunnenta yace ki shirya anjima dake zan wuce asibiti aduba min lafiyarku,ke bby nah
shagwab'e fuska tayi sosai tana turo masa Dan karamin tsukaken bakinta kana tace "uhm uhm gaskiya ni banason xuwa hospital .
Km ko bashi bama ni gani nake tamkar za'aa gane cikin dake jikina.
Sai daya tsotsi lips dinta sannan " yace "wayema zai ganki a mota ta fa zaki shiga"
tace "nidai a'a" shiiiiii yace "banason jin komai Daga bakinki .Yar rainin hankali kawai Amman
ranar nan dayake gidanku zakije bakiji kunyar fita da 'cikin ba, bananan ma kika yi tafiyarki ... sannan kina jin tsoron xuwa hospital sbd kada wani yaganki da ciki ,kika iya shigowa motar wani jaki tundaga geto area din ku har zuwa nan ,bakiji komai ba sai yanzu ne zaki kawo wa mutane salo.
, dan haka banason musu ko wani iyayi ki shirya kawai kafin na gama breakfast marar kunyar karya kawai .
Ya Mike tsaye yana kokari barin dakin .
To dole ne sai naje hospital din ince 'cikin nawa ne .
km lafiyata za'a duba . Ya Dan dawo dabaya da baya ya juyo yana kallonta .
yess Haka ne fa ,Amman km dole kije yarinya kiga doctor .yana gama fadar hkn ya fice gabadaya.
"

Ahankali yake taka step har yakarasa saukowa zuwa dining area din fuskasa cike da tsansar annuri da zati so fresh dashi ya zauna akan kujerar dinning wanda oready yake a shirye. ummi da zeenat ne zaune suna zaman jiran fitowarsa .
,abinci zeenat ta hada masa da coffee dinsa Na gado yasoma ci yana jin wani irin sanyi har 'cikin zuciyarsa 'cikin sanyi jiki yasoma cin abinci sbd Yadda yaga umminsa tana kallonsa.
Sosai idanun ummi ke yawo a tsantsar jikinshi ,km da zarar sun hada ido da ummi sai yaga tana masa wani irin kallo kmr Na tunhuma kmr Na tambaya wanda shi kwata kwata Bai ganewa manufar hkn ba.
kasancewar shi ba me son mgn bane Yasa yashare ummi kawai Bai ce mata komai ba .
bai km Bai tambayeta dalili ba Amman shi aranshi yana jin kmr an dauke masa wani dutse ne sbd yana jin kanshi so freshi da farinciki byn yakammala da cin abincinsa yake sanarwa ummi zance zuwansa asibiti da nablah zai wuce .
domin yana son ya kaita a duba masa lfyrta.
tun kafin ummi tayi mgn zeenat tace Kai gsky kam my hrt yakamata wlh danni nima Na dade da yin tunani akan hk .
Km tun jiya kayi mgn ai da tare zamu .
Me zai hana yanzu ma kibisu kuje taren ai zaifi tunda kinga ke mace .
Bakamar ba .

Girgiza kanta kawai tayi bari suje kawai ummi wani lokaci maje .
koma Na kaita da kaina ..


Bayan sun isa asbiti aka dubata da lafiyar bby akace za'a yi mata scanning.
fur Nablah taki yarda tasoma kuka dole haka Deeni.
Yana ji yana Gani ya hakura dan ya fuskanci rikici takeji dashi .
Daga hospital din Kai tsaye office dinsa ya wuce da .

Suna shiga ta Mike kan kushin dinsa me kama da bed tayi Kwanciya .
shi km ya kulle office din yasoma abinda yakawoshi ..

Ahankali bacci ya dauketa baita ta tashi ba sai gurin la'asar.
kallonsa tayi kmr zatayi kuka tace deeni kana tsoron Allah kuwa ?
Kalli yadda lokaci bautar Allah Ya wuceni baka tashe ba wai Kai wani irin mutu ne please ?

Murmushi yayi tare da girgiza mata kanshi alamun shima Bai sani ba .
harara ta cilla masa Daga inda take cike da takaicin halinsa.
Sannan mike ahankali zuwa toile din dake office din..


'Bayan ta idar da salolinta tayi addu'a ta shafa ta nike prayer mat din dayabata tayi salla dashi ta matsa ta daura masa saman table dinsa ta koma ta zauna fuskarta a hade Dan jin haushinsa .

Xoki dauki abinci kici yace daita .

Azumi nake tabashi amsa adakile alhalin km babu wani azumin datakeyi .

Bai km mata magana ba Yacigaba da rubuce rubucesa har zuwa karfe shida saura tana zaune shr shi km yanata aikinsa kmr Bai san da mutun ba duk har 'cikin zuciyarsa yaji bbu dadin rashin cin abincin dabatayi ba ..

Ahankali yaga ta Mike tsaye ta nufi kofar fita .

Taji sautin muryarsa 'cikin sanyi wani abu kike son akawo miki ?
yace daita batare daya dago Daga abinda yake ba .
shanyayyun idanunta ta tsura masa wanda Yasa shi dagowa ahankali idanunsu suka sarke 'cikin juna ita tafara janye nata tayi kasa da kanta tana murza hannuwata 'cikin juna .

Sosai tabashi tausayi Dan ya hango gajiya da wunya attare daita .
Bataji motsinsa ba sai hucin numfashinsa taji daf daita a dan razane taja baya ya cilla mata wata uwar harara ,kauda Kai tayi tana mamakin yadda shi kwata kwata abun harara Bai yi masa wuya .

Mutafi ko kin gaji ?

Batare da ta amsa masa ba tasoma tafiya .
shi km yana biye daita abaya.
har suka shiga lift suna fitowa ta barshi tayi gaba ta abinta .
Tsaye ya sameta ajikin motarsa murmushi gefen baki yasakar mata sanda yakaraso Inda take.
Ta yamutsa fuskarta tare da turo masa Dan karamin tsukaken bakinta.
dariya ya kyalkyale dashi sosai yana nunata da key .

Bakinta ta bude Dan mamakin abinda yasakashi dariya har hk .


Nas.. aliyu Muhammad khaliyal ashe rai kanga rai ?
wata matashiyar budurwar ce fara Sol amman daganin ba tmby kasan ankara da cream din bleaching ke cewa deeni hk .
yayinda take karasowa gurinsu bbu ko dar ta rungume deeni ajikinta cike da dokin ganinsa tare da bashi sumba a kirjinsa .

Wayyohhhyyy zuciyar nablah tayi wani irin matsanancin harbawa da karfi , sannan takoma ta dinga bugawa da sauri da sauri .
sai data saki kara a can kasan makoshinta wanda ita kadai taji sautin abinta .
Banda dokawa bbu abinda ZUCIYAR nablah keyi Dan ganin wannan tashin hankali ganin matar nan taki raba jikinta danashi.
Taji wani irin tutukin haushi ya tsaya mata akirji .
Yasa a fusace ta janyo matar tayi cilli daita gefe tare da dauketa da wasu mahaukan mari . muryarta a sarke tace ke wacce irin jaka ce ki dinga kula da jikin mazan mutane .
Dan gabadaya zaki iya fadawa tarkon sharia ..tana nunata da yatsanta . sororo deeni yayi yana aika mata da kallon mamaki ..
Uhmmmm su nablah kennan .
ta juya ahankali ta jingina da jikin motar .

Hannayeshi zube duka 'cikin aljihun wandonsa yabita da kallo fuskasa dauke da wani irin matsanancin murmushi farinciki .

Nas aliyu wacce wannan wawiyar yarinyar har ta iya taba lafiyar jikina agabanka kana kallo ?
Wani irin mugun kallo ya sauke mata wanda Yasa tayi saurin ja da baya bashiri tafiya yasoma yi Dan isa idan take da hanzari Tasha gabansa yanzu Nas aliyu kana kallo aka wulakantani Amman ka kasa daukar mataki alhalin rabonmu da ganin juna over 12 year kennan Ina ta nemanka sai yau Allah yabani sa'a gashi nazo taka Nas Dan Kai Amman da alamun ko murna haduwarmu da juna bakayi ba.
haba Dan Allah duk me yakawo hk ?

A kufuke ya Daga mata hannu kibarni naji da riginar da kika cazamin akan wanda nake ciki jidda Dan wulakanci ma ki rasa irin tarbar dazaki min sai ta runguma 'cikin bayyanar jama'a .
Ai Ni wlh nablah tayi min daidai data dauke min ke da mari shasha kawai yasoma kokarin bude motarsa .kamoshi tayi cike da fitsari nablah dake tsaye still tana facing dinsu ta runtse idanunta gam.
karar saukar wasu irin mahaukatan maruka taji deeni ya sauke mata masu kyau d lfy . Ta sake runtse idanunta.
Banson shirme da shiriritanki Na iskanci leave me alone ..ya fada a fusace tun abaya banyi irin hk dake ba sai yanzu ne danake da lafiyayayun mata har guda biyu .....Ya nuna mata yatsunsa biyu
take gabanta ya fadi tagane wacce yarinyar data mareta yanzu matarsa ce .. wani irin kallon rainin hankali nablah da bude idanunta ke masa jin ya ambaci mata biyu ..


Yana gama fadar hkn ya bude motarsa yace ke.....shiga muje.
Nablah tayi masa banza taki motsawa ballanantana tashiga kmr yadda yabata umarni.
Bai wani tsaya westing time ba sai ji tayi an dauke ahankali byn ya bude mota side din baya ya sakata ya rufe shima yashiga.
Direbansa ya tada motar .

'Bayan motarsa ta bi da kallo cike da mamaki da takaicin tallabe da fuskanta .
Wato sai har yanzu shi yana tamkar yadda tasanshi bai canzawa . atunani ganin yadda ya fito Daga cikin companies dinsa yana murmushi .
Ya canza Daga wance Nas aliyu din data sani zuwa wani daban.
tana kallonsa har sanda securities dinsa suka saka motarsa a tsakiya suna kokari barin haravar ma'aikatan sannan ta nufi motarta a guje ta fige motar tazo ta wuce shi .
Tabe bakinsa yayi yayinda azuciyarsa yace fitinanniyar banza kawai bbu abinda ta iya sai shashanci .
ban saurareki ba acan baya sai yanxu .
shasha mara aji kawai mtsssssss ya furta a bayyane ..

Har suka Kai gida bbu wanda Yayi dan'uwansa mgn Daga nablah har deeni .
sai da motar ta tsaya ne nablah ta yunkura tana shirin fitowa taji .
an janyota an maidota ahankali tare da juyo daita suna fuskantar junansu .
cikin kwayar idanunta yake kallo yana hango tsagwaron sonshi da kishinsa tattare da tashin hankali iri iri a 'cikin su .
Muryarsa a kausashe yace as from today Karki kara yi min wannan stupid thing din da kikayi yau .
Wato marin wata akaina .Dan Banga abinda ya dameki dani ba ,da km rungumar datayi min .
Ko kina sona dazaki haushi ?
Tayi shr tare da tsurawa 'cikin idanushi nata kwayar idanun.
Dan iskanci har dayi abu kmr wata matata ko zeenat datake matata bazata yi min abinda kikayi ba.
Muryarta cike da rauni tace ..Amman ta ya'ya Dan tana Yar isaka zata rungumeka a.... shiiiiii gara ma nata akan Na wasu take tagane hannuka me sanda yayi mata idanunta suka cicciko zatayi kuka ..
muryarsa a sanyaye yacigaba da mgn km wlh kinci darajar 'cikin jikinki ne if not ni kadai bansan abinda zan miki ba .wawiya kawai idan ance kina son mutun kice a'a .

dama kince kina sona ko na dan taimaka Na aureki ko Dan dararjar kyautar bby da kika min .

taja tsarki tare da bude kofar motar da karfi ta fice ta barshi nan zaune . murmushi yayi kawai yana shafa sumar kanshi ahankali ahankali yarinyar kin makaro fa domin Na dinga kunna wutar kauna kennan acikin zuciyarki .

Wata irin kulawa da tarairaya ta musamman Deeni yake bawa Nablah ita kuwa saidai ta Bishi da shanyayyun idanunta akan duk abinda zai mata domin kwata kwata batajin hidamarsa gareta yana birgeta.


Sannu ahankali rayuwa tayi ta tafiyar masu har zuwa lokaci da watan haihuwar nablah tayi 'cikin ya fito sosai yayi tsini har abun ya Daga hankalin deeni da ummi yayinda gabadaya tunda watanta haiguwarta ya tsaya take 'cikin fargaba da tunani kusa zeenat da deeni har ma da ummi suke bata kulawa da nuna mata tsansar soyayya ..wanda kusan yanzu deeni da zeenat kullun suna dakin nablah suna kwantar mata da hankali akan ta kwantar da hankalinta zata haihuwa lfy.
wani lokaci ma har kwana suke a dakin su saka deeni a tsakiyarsu .wanda ita nablah sai dai taja gefe can tayi kwanciyarta tabarsu tana mamakin yadda zeenat gabadaya ta sauya mata yanzu ba kmr da ba .


Yau kmr koda kullun deeni yashigo dakin ya iske tsaye a gaban mirrow tana duban yadda cikinta yayi girma sosai ahankali yakaraso Inda take tsaye yana dubanta tsunganawa yayi agabanta tare da manna kunnenshi kan cikinta a tare suka kalli junansu sakamakon motsin bby suka ji .Ya dage mata gira yana nuna mata 'cikin da yatsansa lumshe shanyayyun idanunta tayi tana Daga kafafunta da kyar Dan son zuwa kan gado ya Mike tsaye jikinshi a sanyaye ya cimmata tare da riko hannuta 'cikin nashi ya zaunar daita akan gadon km har lokacin hannu nablah Na rike 'cikin nashi yana aikin murzawa .
ya tsura mata ido ahankali yana kallonta gabadaya ta sauya takoma wata kalar tausayi Ya saki hannunta .
ya kamo kafafunta ahankali ya maida bisa gado yashiga mammatsa mata sbd wani irin kumburi da sukayi .sosai take jin dadin yadda yake massaging din kafafunta ta Dan yatsuna fuska tana sake lumshe shanyayyun idanunta sorry please.. kiyi hakuri inshallahu lfy zaki haifi abinda ke cikinki dukkanin mu Muna miki addu'ar kema kina ?
Me kike cewa tayi masa banza tamkar bada ita yake ba .jin motsin turo kofa Yasa ya saki ya zame hannunshi Daga abinda yake mata
zeenat ce tashigo tana sheki da daukar hankali ta zauna a gefenshi tana yiwa nablah sannu .
Dan ita kanta yanzu takan tausayawa yarinyar da 'cikin jikinta . Murmushi tayi suka shiga hirar 'cikin jikin nablah .
ita dai nablah shr tayi bata ce dasu komai ba sai dai tana sauraransu ..wlh Allah nake naga yarinyar ta haihuwa kodan sbd mama ta abuja .
Deeni yana jinta yayi mata shr tacigaba kana ji ko my hrt idan yarinyar idan ta haifi mace fateeha za'a saka mata idan km namiji ne sunan fateehu za'a Sa .
ya juya inda take zaune tana yauki ya watsa mata wata uwar harara sbd yagane dalilinta . Nacewa hk Amman ya kanne Yace sbd me zan saka wannan sunan duk da akwai shi 'cikin alqur'ani me girma?
.Ni sunan first love dina zan saka idan macece idan km nmj ne sunan abbana zan saka .
Ta Dan yatsuna fuska tana duban 'cikin jikin nablah kana tace gsky Bai kamata kasawa wannan 'cikin sunan iyayenmu ba.
naga bby din ba daga tsatso me kyau suka fito ba ..tsaki yaja yana mata kallon tababbiya yayi kwanta can kusa da nablah tare da juya mata baya .
Kwanciya tayi itama abayansa ita dai nablah nata idanune kawai domin kusan tafi su matsuwa ta rabu da 'cikin jikinta .
km ko bbu komai tana jin dadi yadda suke bata kulawa sosai .fiyye da da .

Wata safiyar tafiya gaugawa takama deeni zuwa abuja kwana biyu zai yi ya dawo Bai so tafiyar ba Amman takama sai shi dine zai je da zai tafi tamkar ya wuce da nablah hk yaji ,sai ummi ta nuna bacin ranta sannan ya wuce ..


'cikin bacci nablah taji tamkar an tsunguleta ahankali km ta dinga jin wani irin zazzabi ciwo mara iyaka abayanta da mararrta .
ta bude idanunta wanda da kyar tamkar jira ciwon yake ta farka yace bismilla . Ta sauko Daga kan gado ahankali bata son tayi motsin mai karfi sbd ummi da zeenat su farka .
Dan yanzu tare suke kwana tashiga bayi sbd ji datayi kmr tana jin 'bayan gida

' hk ta dinga shiga toilet yakai Sau goma tana tsugunawa Amman shr yaki fitowa ta dawo ta kwanta tana jin ciwon yana ratsata ta sake jin cikinta ya cure guri tare da wata irin murdawa ta km tashi da kyar takoma toilet Daga ba sai ciwo ya tsananta ba .
Ta sake fitowa ta kifa kanta da gado ta jujjuyawa da cicciza lips hannunta daya dafe da mararta 'cikin ummi ta farka da sauri tace nablah yaya ?
Muryarta da kyar tace ummi marata zan mutu ,ummi ta duro da mugun sauri tare da tashin zeenat itama a rude ta Mike tana duban nablah dake murkususu ciwo ummi ta dafa tare da cewa kiyi addu'a nablah inshallahu bazaki mutu ba abu fa kmr wasa ciwon nakuda yakama nablah yi take cicciza lips dinta tana buga kasa tana kiran mutuwa zanyi ummi ki taimakeni wlh mutuwa zanyi ......





MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗



AYSHA A BAGUDO



Dedicated to
HAUWA A USMAN
JIDDARH



Kainuwa association



Page 98



Ki daina furta kalmar mutuwa nan nablah addu'a kawai shine mafuta .
zeenat wacce gabadaya tagama rudewa sbd ganin halin da nablah take ciki tasoma zariya a dakin tana Kai kawo da furta kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun.
A rude ummi tace kamamin ita zeenat mukaita dakin kasa .


Zeenat dake tsintitin acikin dakin takaraso da sauri .
Takai hannuta jikin nablah ita da ummi zasu kamata.
nablah tayi saurin girgiza kanta tana dukan Tear's da tafin hannunta .
kibari akai ki dakin kasa nablah zai fi sauki akan nan din.

uhmmmm ummi uhmmmm takasa cewa komai sai uhmmmm da murkususu ciwo .
take wani irin gumi me zafi shiga tsaftsafo mata takoina jikinta.
Jikinta ke wani irin kirma Dan azabar radadin ciwo.
ta dinga cizan lip's dinta da karfi tsabar tashin hankali .
kuka take da idanunta tana kokarin kamo hannu ummi 'aiko Allah yabata sa'a ta damke hannun ummi 'cikin nata da karfi tsiya .
nishi take hankali sbd numfashinta dake sizing yana dawo .
zeenat dibo min ruwa a cup kikawo nayi mata addu'a.

hk zeenat ta fita jikinta Na rawa biyu biyu ta dinga taka step taje takawo ummi ruwa acikin cup .

ummi takarba tayi mata addu'a tabawa nablah tasha Amman still ciwon Bai ragu ba .
Sai abunda ya Karu Na naxaba wani irin murdawa cikin nata yayi da karfi aiko ta saki wata irin razananniyar kara wanda Yasa zeenat fashewa da wani irin matsanancin kuka jikinta yacigaba da rawa .
Tana kuka tace ummi Dan girma Allah mukai yarinyar nan asibiti karfa Yar mutane ta mace mana mushiga uku Daga taimako ..

bazata mutu ba inshallahu .

Duk wani taimakon da ummi tasan anayiwa me nakuda tayiwa nablah shi Amman Sam bbu wata alamun zuwan bby wanda hkn ya nuna ummi cewa doguwar nakuda gareta.
Daman km dayawa anasamun hk wani zaga alokacin rainon ciki basashan wahala sai gurin haihuwa wasu km tun gurin daukar 'cikin suke shan wahala har zuwa haihuwa wasu ma kwata kwata basu San da wannan matsalar ba zasuyi renon ciki lafiya Haka ma haihuwar 'cikin sauki zasuyi ta .

kuka nablah keyi tana kiran mutuwa zatayi itama zeenat kuka take tana cewa ummi kinga abinda nake gudu da jin tsoro ko........
ummi kalli yadda yarinyar mutane ke shan wahala kalli yadda numfashinta keyi ni dai wlh tsoro nake ji wani abu yasameta 'cikin wani irin kuka zeenat takarashe zancenta da wallahi ummi bazan iya haihuwa ba ban zan iya ba wallahi Na hakura da haihuwar gabadaya .

'Cikin fushi ummi ta buga mata tsawa Dan Allah kiyiwa mutane shr duk kinbi kin cikawa mutane kunne ba'a haihuwa ke uwarki ta haifeki.
zakizo ki ishi mutane da surutan banza da wofi shasha kawai 'aiko kowace da yadda haihuwa take zuwa mata kamamin ita ni mukaita kasa .. .

Haka suka kama nablah zuwa dakin kasa ummi ta kwantar daita tunda tun dazu a tsugunne take a sama har garin Allah yawaye ciwo yaki ci yaki cinyewa banda murkususu ciwo bbu abinda nablah keyi da ikin kiran sunan mamata da mutuwa zatayi .
Wani daren yashigo nablah Na kan abu daya , tayi firifiri daita tayi mugun fita haiyacinta iya jigatuwa tayi shi har tasoma gajiya tana janyo numfashi da kyar tana fitawar da kyar km still ummi da zeenat Na tsaye akanta Amman haihuwa shr.
Gashi km sosai nablah ke jin wata irin azababen azaba har tasoma fezgar gashin kanta ....
ta daina gane suwaye akanta ta dawo bbu karfin komai ajikinta bakinta ya bushe sannan Yayi fari fat.. idanunta suka bushe .
hawayen dake idanunta suka kafe suka bar xuba bakinta ne kawai ke motsin ahankali tana karanto duk wata addu'ar tada iya ji taje da zata iya data fizge 'cikin jikinta ta huta da radadin azabar ciwon datake ji ...

Daren ranar bbu shiri ummi ta da zeenat suka cucibi nablah tamkar wata Yar bby suka sakata abayan mota batare da sanin kowa ummi ta zauna baya tare da nablah zeenat ta shiga gaban mota ta tayiwa motar key sai wani asibiti kudi me zaman kanshi da shegen kyau.

suna xuwa hospital doctor yana dubata yace haihuwa ce Amman km da saura Dan yanzu ma tasoma nakudar domin har lokacin jikin nablah Bai bude.
ba jin Haka Yasa zeenat sadaukarwa da mutuwa zatayi duk wannan azabar data kwana tana Sha .
Ace km yanzu taka fara nukuda ita kam tunda take arayuwarta bata taba ganin irin ciwon nan ba.
shi Yasa tasawa ranta ta nablah takare ..


Tun daren jiya jikin mahaifiyar nablah yake a tashe takasa runtsawa sakamakon gabanta daketa aikin faduwa tamkar ana buga mata guduma wanda batasan dalilin faruwar Hakan ba Dan Haka ta Mike jikinta a sanyaye Daga kwanciyar datayi tazo ta dauki buta tayi alwala tashiga jero nafiloli da addu'oi neman tsari .


Shi can bangaren deeni tun daren jiya jikinshi yabashi gidanshi bbu lafiya sbd mafarkin barkatai daya kwanayi km duk akan nablah ne Dan Haka tun da asuba yashiga neman layin zeenat dana ummi Amman shr bbu wanda ya dauka acikinsu ,Bai hakura ba Yacigaba da neman layin Daga karshe ma daya Kira yaji wayar akashe .
nan fa hankalin shi yayi mugun dagawa yakasa yin komai sannan Kuma rasa jin dadin zuciyarsa kawai yaga gara ya dawo gida .batare da bata lokaci ba yabada Umarni siyan Tiket kawai yana shirya jikinshi yana neman layin ummi dana zeenat Amman har lokaci shr swchoff ake ce masa . Wani tashin hankali ma sai jirginsu ya sauka a Lagos gabansa ya tsananta faduwa zuciyarsa Na tsinkewa Allah Allah yake yaganshi agida kawai ..


Yana shigowa 'cikin gidan da zeenat yasoma cin

1 Comments On AUREN SIRRI
avatar
adam-ado

9 months ago

Reply

Very interested book

Please Login or Register in order to submit comment