Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da sallah yayi yan addu'oinsa yake wuce wa gida .
fk ya dube sa da kyau yana nazarinsa kafin daga baya yace lfy kuwa naganka haka ? Gabadaya fk yagama tsurewa da ganin yanayinsa sai da ya sake maimaita tambayarsa sannan DEENi yace ina fa lfy jiya ummi kwana Tayi ba lfy har tana barmin wasiya burinta da muradinta yanzu bai wuce nayi aure ba.
fk yayi shr yana jin DEENi har sanda yagama bayaninsa sannan yace baita kadai ba har big dady ma burinsa kennan dan ko jiya sai daya min maganar nida kai Amman tunda kai ummi ta damu ta tsananta gara kayi kawai kurabu lfy .
DEENi yace ai bakasan inda zan nemi matar ba nifa gabadaya en,mata family din nan basu min ba sannan kuma sun min kankanta da aure ,fk yace A'a bawani kankanta" mace na kankanta da aure ne ? kaine dai kawai kake ganin haka ,ni yanzu na yanke shawarar zan tsaida shemah kawai tunda na dade ina sonta nida zakaji shawarata ma da zeenat ka aura DEENi ya mishi wani irin kallon bakada hankali sannan yaja tsaki yace haba dai zeenat , fk yacigaba yarinyar akwai hankali wlh ,ba kmr wancan banzar ubannata ba, dayake duk sun tsani halinsa.
kaga kawai sai a hada bikinka da nawa kawai kaga zeenat batada matsalar, km ko bakomai ummi zata ji dadin Sosai da wannan hadin.
DEENi yace Amma ban taba jin koda alamar digon sonta ba, kuma ni gaskiya ina ganin tamin yarinta dayawa duk fa shekarunta sha tara zuwa sha ashirin ne fa. nafison mutual girl wace ta mallaki hankalin kanta tasan yadda zata kula dani akan bed ,amman wannan Yar bbyn maimakon ta kula dani ,ni ne zan koma renonta.
fk ya dubesa a kaikaice yace lallai yaran zamanin da kasani Amman banda na yanzu, sai su maka abinda manyan matan baza su iya ba, kana rai nata ne kawai , sai kaga mararta ta daukeka tsab, DEENi yaja tsarki kai ban son iskanci shawara nake so, ba wani shirme ka can na bazan ba .
fk ya kada kafada yace well tunda kaga bata maka ba kana iya duba wasu acikin gari .
DEENi ya kalleshi yana watsamasa harara "kaifa dan iskane dan kaga nazo maka da maganata shine zaka rainawa kanka hankali " sai kuma yayi kasa kasa da murya yace kasan Allah ni fa ko a waje ba wai ina kallon mata bane, fk yace to katsaya akan zeenat din kawai, duk inda ake neman macce mai natsuwa yarinyar nan takai ,DEENi ya sake jan tsaki yace ai inda takaicin yake kennan sai kuma nakirata ince ina sonta ...ya fada yana tabe baki "hade jin takaici da haushin shawarar da fk yakawo masa " fk yace inda bazaka iya ba kabi ta sama , ma'ana kasamu big dady da maganar kawai, kasanar dashi kana sonta nasan zai ji dadi Sosai .
DEENi ya sake watsamasa wata harara yace dan Allah malam ka dameni , ina ganin fa kmr kafara samun tabin hankali , wa yace dakai ina sonta "zan dai yi aure badan ina so ba ,ya juya yabar fk nan tsaye yana binsa da kallon mamaki sannan kuma yace ai kaine babban mahaukacin dan iskan kawai , sai iskanci fall ciki ,shi bai ga laifinsa da yace bazata ya saukarsa a bed sai nawa sai kuma ya kwashe da dariya .



MMN SUDAIS CE

πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
AUREN SIRRI
πŸ’–πŸ’–πŸ’–
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—



AYSHA A BAGUDO


Page 7-8


Har DEENi yazo gida tunanin yake akan shawarar da fk ya bashi" anya kuwa zai iya amince da auren zeenat ?
Lokacin da yashigo yayi daidai da zeenat ta tabare magani tana mikawa ummi ,ta amsa ta apa zeenat ta Mika mata ruwa ,yayinda shi km yake tsaye jingine da jikin kofa rungume da hannuwansa duka a kirjinsa yana kallonsu, take zuciyarsa ta dinga ingizashi akan lallai bbu wace ta dace ya aura sama da zeenat bisa ga hujarsa tacewa ,bazai taba samun matsala daita gurin kula da mahaifinsa saboda irin soyayyar dake tsakaninsu "
yasan ko yana nan ko baya nan zata kula daita, umminsa zata zamo a karkashin kukawarta tunda zeenat bata da wata uwar da wuce ummi tunaninsa ya katse lokacin da ummi takira sunansa' tace son karaso mana yayi frigigit ya dawo natsuwarsa ahankali yashiga takowa har inda ummi take ,ya zauna zeenat ta gaidashi ta mike zata fice daga dakin bai amsa mata gaisuwar data masa sai dai yabi bayanta da kallo" ummi ta kalleshi ta kauda kanta, yace first lov yajikin naki ummi ta danyi murmushi hade daura hannuta kan sumar kansa tace naji sauki sosai , ahankali sauke ajiyar zuciya ko bai ce komai ummi ta fahimci yaji dadin yadda yaganta ,yana nan zaune , Sam yakasa yiwa ummi zance yana ya auren zeenat din ,daga karshe ma tunani yayi kawai gara yasamu ya mahamud da zance dan gaskiya kunya yake ji yayiwa ummi maganar da kansa .

Da yammacin ranar byn ya dawo daga office yaje har gida yasamu ya mahamud da maganar ya ji dadi kwarai da gaske, har yarasa inda zai sa DEENi dan farinciki dan shima da kansa ya matsu yaga DEENi ya ajiye iyali kmr kowani magidanci , yace Shikenan sai kasamu yarinyar da zance, ku daidaita kanku DEENi yace A'a ina ganin basai na sameta ba in dai first lov ta amince ai Shikenan .
yaya mahamud yace ummi bazata taki ba Amman dai kasan kaidar auren gidanmu kennan bbu dole a ciki "muddin kuka daidaita kanku na iyayenmu may sauki ne idan Kuma ita ummi ta amince ita yarinyar tace bata sonka fa? DEENi yaji haushi da takaici sunkamasa alokaci guda yace ai nima ba wai ina sonta bane kawai dai zan aureta ne.
Yaya mahamud yace shirme bazan kennan kai yanzu idan anzo meeting cewa zakayi basonta kake yi ba ,zadai ka aureta ne ?DEENi yayi murmushin gefen baki har dimple dinsa ya lotsa sannan yace cewa kurum zanyi ina son zan aure zeenat ne ' Yaya mahamud yace to Allah ya mana zabi na alkhari kabari zanje gurin ummi tukun duk yadda mukayi daita zakaji DEENi yace Shikenan ya mike fice ,a office ma koda yaje aikinsa kawai yasa gaba .
dan shi gabadaya ya manta da wani zance aure can .


Mahamud yasamu ummi cike da karfin gwiwa" ganinsa ba wanda zai kai ummi murna tunda daman burinta kennan naganin auren DEENi, Amman ga mamakinsa yana gama labarta mata abinda yakawo shi, sai yaga ummi tayi kicin kicni da ranta tamkar bata taba sanin wani abu farinciki ba "sai da gaban Yaya mahamud ya fadi dan ganin yadda ummi tayi da fuska tamkar yazo mata da zance mugun abu " tace kai ne kaga sun dace kaba shi shawara ya nemi aurenta ko Kuma shi da kansa ya sameka da zance ?
Da sauri yaya mahamud yace A'a shine dai yazo min da zance ummi ta sake daure fuska, sannan tace ka koma ka fada masa ban amince ba ,kace masa akwai sauran mata a gidan nan yana da damar zabar duk wacce tayi masa, idan ma ya canza ra,ayinsa nakin auren family' to yaje waje ya nemi matarsa can itama Allah zai bata nata mijin, Amman Sam ni ban yarda da wannan hadin ba " tayi shiru na wani lokacin kana zubawa Mahmud idanunta tana kallon yanayin daya shiga ,ahankali ta numfasa sannan tace kana iya wucewa idan kana da abinyi ka manta da wannan shirme na DEENi .
Yaya mahamud yayi kasa da kansa Sosai cikin muryasa can kasa kasa da alamun km rarrashi yace dan Allah ummi ki amince da auren nan bazan iya tunkarar DEENi da maganar ba.
duk da bansa dalilinki nakin amincewa ba" ummi ta dan saki fuskanta ba kmr dazu ba tana mugun son mahamud tamkar dan da ta haifa acikinta tana jinsa har cikin zuciyarta .

tace bawai ina kin hadin bane duk duniya idan akwai wanda zai so auren DEENi da zeenat a bayana yake ,na farko dai kaima kasan halin DEENi da dan bazar zuciya , ga saurin fushi ga maseefar miskilanci tsiya ga jin kai sannan da bakinsa yasha gayamin cewar shi bazai taba yin auren family ba sannan shi mai digiri yake so ya aura ,shine km yanzu zai zowa mutane da wani salo.
ni da tawa iya secondary kadai ta tsaya" ai kai da jin zancensa ma kasan akwai wani makirci daya shirya "dan nace yayi aure ai bance lallai sai ya aure tawa yarinyar ba , Muhamud yace ummi ki duba lamarin abun tunda shi da kansa ya furta cewa ita ta masa ba za'a samu wata matsala ba ,.
ummi tace Sam bata yarda da wannan tsarin ba " ita dai yaje gaba ya nema hakurin duniya nan bbu wanda yaya Muhamud bai bawa ummi ba amman taki amincewa ,duk ta inda ya bullo mata sai itama tabiyo masa ta wata hanyar, har ran yaya mahamud yasoma baci ,yaji haushin abinda ummi tayi dan haka ya hakura ya fice ransa abace .


DEENi zaune a office dinsa ya dukufa wajen tura sakwanni a yanar gizo ,hankalinsa kwance yake bin komai daki daki , yaji daya daga cikin wayoyinsa ,daya ta dauki karar sauti mai dadi ,ya dauke idanunsa daga kallon system din yasa hannu ya dauki wayar yana dubawa ganin sunan dake yawo akan screen din ne" yasa yayi sauri dagawa yakara a kunnenshi hade da yin sallama" kana ina muryar Yaya mahamud yaji ta daki dodon kunnenshi cikin sanyi murya DEENi yace ina office yace ok idan katashi kabiyo inason ganinka sannan ya kashe wayar .

DEENi zaune a gaban Yaya mahamud kansa sunkuye a kasa yayinda idanunshi ke kallon zarazaran yatsun kafafunsa yana sauraron sakonshi da ummi tabayar a sanar dashi.
a gurin Yaya mahamud sam bai tsammaci jin haka daga umminsa ba ,ga mamakin Yaya mahamud sai yaji deeni yace Shikenan babu komai Allah yasa haka shine mafi alkhari .
ya mahamud yace ka hakura kennan? Nashi ganin bazai damu dan ummi ta hanashi auren zeenat , dan haka Yace eh "tunda daman ba wai yana sonta bane" nan dai suka bar zance aure suka shiga wata hirar daban a inda Yaya mahamud ya tashi yaje ya kwaso wasu takardu da file files ya zubesu nan a gaban DEENi yace yasa masa hannu ciki " kai tsaye DEENi ya zaro wani hadadden Biro daga gaban aljihun rigarsa yasoma cike gurraren da akeso yayi sign, dan gabadaya dukiyar DEENi , sulaiman da Muhamud ne akai su suke kula daita kuma komai na tafiya daidai " domin dukkannisu abu guda ne a gurin ummi dan ma idan ba'agaya maka ba…
zaka dauka duk ummi ce ta haife su .

Sai da DEENi yagama sign din ,sannan yaya mahamud hada da mishi bayanin companies din da suke son budewa a kasar American, sun turo musu da sako akan suna da bukatar mutun daya daga cikin masu company din " yazo interview dan haka shi ya wakilta sulaiman yaje , DEENi yayi murmushin yace Shikenan bbu komai duk yadda kukayi ,daidai ne Allah ya taimaka .


To byn DEENi yakoma gida ya dingawa ummi wani irin kallon, wanda shi kansa yakasa gane dalilin yin haka, yana son yi mata magana Amman yayi shr ,yayinda zuciyarsa ke kwabarsa akan ya share kawai ai baita kadai bace mace a duniya" daman ai dan ita yake son ya aure zeenat din ,da yaje waje ya aure wata wacce bai san halinta na boye ba ai gara zeenat din Amman tunda bata so shima ya hakura .


Da misalin karfe goma na dare DEENi sanye da rigar wanka dan fitawarsa kennan daga bathroom ,ya tsaya gaban dress mirrow yana karewa jikinsa hade da zare rigar wanka dake jikinsa" ya saura daga shi sai boxer , yabi koina a jikinsa da turaren Hamilton 27, sai daya kammala da komai na al'adarsa da yasaba yi kafin ya kwanta sannan ya hau kan royal bed din ya lumshe rikitattun idanunshi, alamun yana son yayi bacci' sai dai baccin yaki zuwa kawai ya tsinci kansa da tunanin zeenat.ya rinka jinta ajikinsa , yadda yake jinta a halin yanzu bai tsammaci abin har ya zai haka ba ,,
Sosai ya tsinci kansa cikin damuwa ko baya son yarinyar hakika ya tsananta da son aurenta yayi shr yana tambayar kansa abinda ummi take nufi da kin amincewa datayi,shi ya guji big dady da maganar a tunaninsa sai umminsa tafi kowa murna da jin dadi 'ya dauki tsawon lokacin kwance kafin bacci barawo yayi gaba dashi .

Byn kwanaki , DEENi yakasa hakuri da maganar zeenat din kmr yadda yaso shima ta share da zance kawai ya manta dasu "
Amman yakasa, ya samu ummi da kansa a wata safiya dayazo gaisheta byn yayi shirinsa na zuwa aiki cikin kakinsa dake kara masa kyau tamkar dan shi kadai akayi" sai kamshin yake zubawa ta koina "gashin kan nan nasa kwance luf luf luf dasu , duk da bacika yawa sukayi ba ,saboda yanayin aiki "Amman dayake Allah yayi mishi suma takoina ajikinsa ko yayi askin ma baya wani dadewa" gashin zai sake fitowa" sosai yayi kyau matuka ,ita kanta ummi satar kallonsa take har ya tagota ya sakar mata murmushi tace son kayi kyau sosai fa, uniform din nan nakara maka kyau ,ya dage mata girarsa daya yace Allah first lov yace ai daman can nj may kyau ne sannan duk maccen datayi dacen samuna , ta gama samun duniyarta sai dai ta nemi lahirarta kawai " ummi tayi dariya sosai ya kamo hannun umminsa cikin nasa muryasa a shagwabe hade da dan karyar da wuyansa, yace first lov da kanki ma kin yaba dani "tace uhmm yabon gwani yazama dole "yace to meyasa bazaki bani auren zeenat ba ?
Ta lissafomasa dalilinta kmr yadda ta sanarwa Muhammad ta Kuma sake jaddada masa yaje gaba ya nemi mata Amman banda diyarta ranshi ya baci Amman ya share take Yar fara'a dake fuskarsa ta dauke " sai dai bai nuna ba , cikin sanyi murya yace to Shikenan ummi na hakura" Amman bazan taba zuwa koina neman aure ba" saboda banida nagartar daza'a soni Kuma bani aure" ummi tace ba fa haka nake nufi ba yace haka ne mana first lov" ina da munanan halayen da ban cancanci abani mata aure ba. ummi tayi murmushi tace nifa bance haka ba yace haba first lov kince mana gashin nan kema da kanki kin hanani taki Yar , to waye zai amince yabani yana kaiwa nan ya cire hannun umminsa cikin nasa ya mike cikin sanyi jiki tamkar bai damu ba ,.
gabadaya jikin ummi yayi tsanyi ita bawai auren ne bata so ba halinsa take gudu ta yaya zata yarda ta aura masa marainiyar Allah yazo yana cutar mata da yarinya .

Abin mamaki duk a tunanin DEENi na bazai shiga damuwa ba akan kin amincewar ummi ,
sai gashi dumu dumu cikin tashin hankali kullun sai yayiwa umminsa naci da magiya akan tabashi auren zeenat ,ita kuwa ummi duk lokacin dataga ya dauko mata zance sai share hade da bata fuska .



Please kumin uziri , may be zaku dan jini shiri sakamakon matsalar rashin wuta naso narinka muku type akai akai batare da westing time ba Amman kuyi hakuri ana kyawun tare🀝🏻🀝🏻



MMN SUDAIS CE
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
AUREN SIRRI
πŸ’–πŸ’–πŸ’–
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—



AYSHA A BAGUDO



Page 9-10


Zeenat kwance a bedroom din ummi hannuta rike da wani English novel face to face tayi zurfi cikin karatun novel din saboda yadda take enjoy din novel din ya .

Yaya DEENI ne yashigo gaishe da ummi kafin yafita aiki ,byn sun gaisa ne ummi tace har ka shirya fita kennan ? Yace mata eh sannan yaja ya tsaya yayi shr ya zubawa ummi idanunshi .
ummi ta dubeshi tace da magana ne ? Tunda tarigada tasan muddin yayi shr irin haka to da magana a bakinsa.

koda yake tasan dai zance nasa bai wuce maganar zeenat bane " Kuma daman tana son zeenat din tajima kunneta idan ta amince ruwanta "
dan haka ummi kalleshi da kyau tana nazarinsa ta numfasa sannan tace masa kayi shr alhalin nasan da magana abakinka .
, muryasa a shagwabe yace first lov kan dai maganar zeenat ne ,dan Allah first lov, ba yabon kai ba "ina da qualities din da za'a bani auren kowace irin mata nake so" Kuma ko Yar gidan waye ,.
Yar taki ma daba wani kyau ne daita ba" dan ma zan taimaka mata "ya fadi haka fuskarsa a hade ,.

ummi tace duk da haka day bazan bada diyata ba kaje waje ka gwada sa'a r ka" wai ma in tambayeka DEENi yamaida hankalinsa sosai ga umminsa" tace kai da kake ta damun kanka da zance nan kullum. kasamu ita yarinya da maganar ,kun daidaita kanku ne ?
DEENI yace uhmm kece dai zaki sanar mata, ummi ta nuna kanta da dan yatsanta, nice ma zan tayaka yakin nemar maka soyayyarta" lallai ma bason auren nata kakeyi ba" kashare zance kawai tunda baka shiriya neman aure ba. yace to ni first lov in na fada sai naga tamkar Raina ne zatayi, ummi tace kunji girman kan ba a hassale ummi tace dan Allah kayi hakuri kabar zance nan. haba duk kabi katadda hankalinka da nawa. yarda ne dai bazanyi .
dan haka kayi hakuri kabar zancen nan kwata kwata dan ba yarda zanyi ba .

DEENI daya gaji dayiwa ummi magiya ya hakura ya ficewarsa ,yana jin takaici kansa, tunda daga lokacin da zeenat taji DEENi ya ambaci sunanta ta mike zubur zaune daga kwanciyar datayi, hankalinta a tashe jikinta har rawa yake tsabar rudewa" ita zeenat din yaya DEENi yake nufi ko wata daban.
ahankali ta furta in ko ita yake nufi dakuwa ta more a rayuwarta, dan gaskiya yaya DEENi ba irin namijin da mace zatace bataso bane , ahankali ta sake furta A'a dan Allah ummi kada kimin bakinciki mana.

tana jin fitarsa ta fito da sauri daga dakin tana kallon ummi dake zaune tana jan carbi, zatonta ko ummi zata mata maganar ne. Amman sai taga sabanin haka .
dan kuwa ummi ko kallon inda zeena take tsaye batayi ba.
dan tarigada tasan taji komai" to Kuma bayanin me zata tsaya yi mata. Ta dai yi shr ne taga yadda zata dauki lamarin .
Can kuma, ummi ta dago tana duban zeenat din tana nazarinta" yayinda zeenat din itama ummi take kallo" har zuwa lokacin ummi batace komai ba .
sai ma kau da kanta gefe datayi , ganin ummi bada niyyar ce mata komai ,yasa zeenat kira sunan ummi" ta juyo tana duban zeenat din da kyau".
ahankali cikin sanyi murya tace ummi wai wata zeenat din yaya DEENi keso ?
Ummi ta dan tabe baki sannan tace dan Allah rabu dashi wai ke yake nufi "da sauri zeenat tasa hannuwanta duka ta dafe kirjinta dasu tana zaro idanu waje "tace da gaske ni yake so ?
ummi tace zan miki karya ne" zeenat ta marairaice murya tace shine Kuma ummi zakice masa baki yarda ba.

ummi tace to may kike nufi ,kina son kice min kina son DEENi kennan ? Zeenat Tayi shr dan bata da amsar bawa ummi dan gabadaya ilahirin jikinta bbu inda bai dauki rawa ba.
ummi ta sake yin magana daman kina son DEENi ne naga duk kin tada hankalinki haka ?zeenat tace nifa bance ina son shi ba Amman ke meyasa zakice A'a Kuma ma mayye dalilin dayasa kika ki amincewa ,ummi tace ok tutseni zakiyi" kan naki yarda ko yaya , zeenat tace ba haka bane" ummi tace tsaya ma kiji abinda yasa naki yarda, DEENi "da" nane' ni haife shi da cikina sannan ke ma kinsa halinsa sarai da shege miskilanci da saurin jin haushi mutun ,abu kankani ke hassalashi ga tarin girman kan tsiya, zeenat ta tsugunna nan gaban ummi hade kamo hannuwan ummi duka cikin nata muryarta sanyaye tace haba ummi dan day kawai saboda wannan halin nasa ne "zai sa kike amincewa , in dai dan haka ne' ni na amince da aurensa kinji .
ummi tace duk kinbi kin koma kalar tausayi wai ma meyye birgeki da DEENi ne naga duk jikinki ya dauki rawa haka ?.
Zeenat tace ai gaskiya yaya ba irin mutunmin da za'a tsaya cewa ba,aso bane ni dai na amince ,ummi tace ko kin amince, ni nace A'a ban yarda ba ,.

Zeenat ta mike cikin fushi tayi bedroom din ummi .
da kallo ummi tabi bayanta dashi ummi taji matukar mamakin ganin reaction dinta musamman da tasan zeenat din ,bata fiyye nuna fushinta akan abu ba .

Koda tashiga dakin ma waje tasamu ta zauna abunta tayi tagumi batayi aune ba, kawai taji hawaye na silalowa mata.
ita kanta tasha mamakin ganin hawayen na zuba a idanunta "ta tambayi kanta to daman can tana son DEENI ko yaya? domin abun itama yayi maseefar daure mata kai ".
kuka takeyi " iya karfinta hade da ganin laifin ummi din ,to meyyesa ummi zatace batason aurenta da ya'ya DEENi byn ita tasha kisma haka a ranta .
taci kukanta sosai har sai da taji alamun kanta ya fara mata ciwo ta runtse idanunta sannan ta kwanta "nan a gefen bed din ummi tacigaba rera kukanta kasa kasa .

Yinin ranar tayi shi ne cikin daki hade da tunanin DEENi da kitsima kalar rayuwar da zatayi a gidan DEENi.
Da zarar taga ummi kuwa take hade fuskarta saboda jin haushin abinda tayi " .
kusan zuwa Maryam uku gidan "Amman zeenat taki saukowa kasa" dan gabadaya takasa samun sukuni gabadaya haushin kowa take ji.
,ita kuwa ummi sai binta take da idanu dan ma kasa magana tayi , gashi ranar Sam DEENi ma kin dawowa yayi da wuri sai wajen shabiyu , .


haka ma washegari tun asubar fari yabar gida ya dai shigo ya gaida umminsa a tsaitsaye.

,byn ummi ta idar da sallah ne kafin ta soma lazimi , yayinda zeenat ke kwance akan bed , idanunta a runtse tamkar may bacci Amman Kuma ba baccin take ba .
ummi takira sunanta kusan sau uku Amman tayi mata shr alhalin tana jinta.
ummi ta sake kiran sunanta tace zeenat nasan kina jina Kuma idanunki biyu Amman kika min banza , hade da ganin laifina .
bakomai yasa kika ga naki yarda da maganarki da DEENi ba" nasan halin DEENi ciki da bai bashida dadin sha'ani kwata kwata gashi da bakar zuciya tsiya azo ayi auren nan yazo yana gana miki azaba, .

ni.. nasan abinda nake gudar miki Amman inda kinkiji ke kika sani , kije Allah yabada sa'a .
Amman ki sani idan akwai wanda zai ji dadin aurenki da DEENi a bayana yake, Amman duk da hakan bazai hanani fadar gaskiya ba idan tazo.
Kuma shawarata gareki ki

1 Comments On AUREN SIRRI
avatar
adam-ado

9 months ago

Reply

Very interested book

Please Login or Register in order to submit comment