Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Na wani irin bugawa km tana son sanarwa yayarta zance cikin jikinta Amman bakinta Yayi mata nauyi takasa cewa mata komai.

Uhm Ina jinki nablah ki sanar min da abinda ke damunki ko zan iya taimaka miki idan km har abun yafi karfina sai mu sanarwa da aunty Salma. still shr nablah tayi taki cewa komai duk yadda nuratu taso nablah ta sanar mata da damuwarta Amman taki. Dan hk nuratu ta hakura tace shawarata takarshe da zan baki kada ki kuskura ki gudu kije koina ki zauna duk rintsi km komai Yayi tsananin sauki Na zuwa da izinin Allah .sannan
Ta Mike ta fice Daga dakin ..

byn fitar nuratu nablah ta sake afkawa 'cikin duniyar tunani iri iri a game da rayuwarta shekarata, ta 'cikin Sha takwas kennan Amman tension din dake idanunta Yayi mata yawa. zuciyarta banda zafi bbu abinda take mata ,tana murna tazo gida gashi tazo ta tadda wani sabon tashin hankali dayafi na 'cikin jikinta.
Wai babanta ya daura mata aure da mutumin da ko shi kansa Bai San kowaye ba .abu kmr a film..
Yadda nablah batasamu runtsawa ba hk ce takasance da deeni shima.
Dan kwata kwata ko kwanciya kasawa Yayi atsaye yake yana ta faman aikin zariyar a dakinsa .
Da tunanin abinda zai biyo baya domin ake uku yayiwa Kule direban ummi zuwa unguwar su nablah ya daukota Amman taki biyo shi wai ba yanzu zata dawo ba har yakira ummi 'cikin tashin hankali fisrt love kin Gani ko.
kinga abinda yasa kikaji naki yarda da zuwan yarinyar nan ko... yanzu meyye solution ?

nifa zanje kai tsaye komai ma zai faru sai dai....naji Amman kabari zuwa gobe mugani ummi ta katse shi ta hanyar ce masa hk.
Ni San yarinyar nan bazata iya zaman gidansu. Da 'cikin jikinta ba .
Jin ummi kawai yake Amman gabadaya hankalinsa a mutukar tashe yake.
zariya yake sosai hannuwansa duka rungume da kirjinshi ...yana Allah Allah gari yawaye.



Washegari garin ranar mlm salisu ya iske Nablah kwance a dakin mama ta lullube jikinta da bargo duk tunani duniya ya adabi ruhinta .tana ganin mahaifinta ne ta Mike Daga kwanciyar datayi ta zauna sosai kanta a sunkuye tana gaidashi ya amsa yana dubanta shi kansa yasan yana matukar sonta duk 'cikin yayansa km bayason damuwarta sannan ya zauna Yayi tunani sosai akanta Dan hk sbd jin dadin abinda tayi masa ahankali ya zauna abakin gadon ya kamo hannuta yana nazarinta muryarsa a kausashe mlm salisu yasoma mgn 'cikin natsuwa nabeelah duk 'cikin yayana bbu me mun biyayya kmr ki ba me son farincikina kmr ki dole nima naso farincikinki tamkar yadda kike son farincikina a bisa biyayyar da kika min na auren dana miki baki min gardama ba ko nuna min kinki ko ki mutsa min ko kin kangare min ba shiyasa nima zanyi kokari naga Na faranta miki.
kije byn wata uku ki dawo ubangiji Allah Yayi miki albarka duniya da lahira ubangiji Allah Ya tsareki da tsarewarsa ubangiji ya kareki daga dukkanin wani sharri ko wani abin ki .
Allah yakaiki lfy ya dawo min dake lfy sannan kitsare min mutunci ki da martabarki kin dai Ga yadda mahaifinki yake bakowa bane facce mlm salisu da Allah Ya rufa masa asiri yanzu .. nabeelah kimin alkwarin byn wata uku zaki dawo gareni kada kisani jin kunya ..tana kuka muryata rawa zuciyarta bugawa tace Nagode banana km inshallahu zan dawo kmr yadda kace ..kibar kukan nan hk yanzu yaushe zaki koma can din ?
Inshallahu zuwa jibi to to shikennan Allah Ya nuna mana naga tsabar da hjyr tace akawo Masha Allah idan Kin koma kiyi mata godiya sosai ya Mike tsaye jikinshi a sanyaye ya fita Daga dakin ..


Nablah tasamu natsuwa ta kwantar da hankalinta tashiga 'cikin yan'uwanta anata shan shafta daita ko yau din nan sai da Kule yazo Sau biyu tace mishi ita batashirya ba sai gobe hk ya juya ya koma ya sanarwa ummi hankalinta Yayi matukar mugun tashi sosai ,ZUCIYAR deeni kuwa kadan ya rage ta buga , tun sanda ummi tasoma sanar masa da abinda Nablah tace yakasa mgn da kwakwaran motsin sai ma runtse idanunshi da Yayi.
yana jin yadda kirjinshi kemasa zafi da radadi ya dinga aiyanawa aranshi Anya kuwa *AUREN SIRRI* bazai tashi ba ya dawo AUREN BAYYANE ba? Shiru kawai Yacigaba dayi batare da yace komai ba domin idan yace zai yi mgn komai zai tabarbare , umminsa ce zatashiga damuwa da tashin hankali bashi ba hatta uwar gayya zeenat hankalinta atashe yake matuka sai surutai take xubawa tana tsinewa Nablah a kasan zuciyarta ganinta nablah kawai tana neman rusa masu shirinsu ne .
byn yanzu kowa yagama sanin ciki gareta ..

Washegari daga gurin aiki Kai tsaye unguwarsu nablah deeni ya nufa yasamu guri nesa kadan da gidansu Yayi parking batare da ya fito Daga 'cikin motar ba Yayi waning din glass din motarsa yasamu wani matashin yaro da baifi shekara goma xuwa Sha biyu ba ya aika 'cikin gidan yaje yace ana kiran nablah .
byn kmr minti biyar yaron ya fito yasanar masa wai bata nan take yaji zuciyarsa ta buga da karfi gaske .

A hargitse ya sake tura yaro jeka please ka tmby Inda taje muryarsa Na rawa .
yaro yashiga ya sake fitowa wai ance ba'a San inda take ba .
gabansa ya km bugawa da matsanancin sauri ya rantse rikitattun idanushi ya budesu fesss akan yaro yace wa yace maka hk?

yayarta nuratu ce .
take deeni yagane amsar rainin hankali nuratu tabawa yaron 'cikin wannan halin sai Ga abba autansu nablah ..yazo shigewa

deeni yace yauwa abba zo nan ya, ya futoshi da hannushi dayake abba yasanshi km sun dan saba dashi tunda yana zuwa gurin mlm salisu time to time da murna yakaraso yazo ya tsaya jikin motar deeni yana gaisheshi deeni ya katse shi ta hanyar ce masa duba min 'cikin gidanku nablah Na ciki.. abba Yayi murmushi har gibinsa ya bayyana yace la......wai aunty kake nema Ai yanzun ma narakata jection zata shiga motar ko ina ni ma wlh nama manta Sunan gurin .

deeni ya zaro rikitattun idanunshi waje.
wasu zafa suka shiga karyo masa hankalinsa ya sake tashi yashiga jero addu'oi kala kala sannan yasoma yiwa motarsa key cike da hanzari ya tada motar Bai sake cewa abba komai ba Yayi gaba da mugun gudu .

abba da wannan yaron suka bi byn motar da kallo kafin Daga bisani suka kama gabansu ..

Abban nashiga gidan yake gayawa nuratu wannan mutumin da baba yake cewa mijin aunty nablah ne.
yazo yanzu yana tmbyr aunty nablah Amman nace masa yanzu narakata shiga mota.
nuratu ta juyo da wani irin mahaukaci sauri tana kallon Abba Dan Allah ?
Wlh .daxo da zanshigo gida naganta da jaka shine tace naraka . Yanzu km byn Na rakata km.... ubanka naji naji ba wannan dogon surunta naka nace kakaranto min ba, ai nasan da zance tafiyarta ,shi dai mutumin dakace yazo nemanta ne nace karya kakeyi .
mutumin da Bai San da dawowar Nablah ba ta ya'ya zaice maka kakirata masa ita.
Allah kuwa Aunty shine ya aiko musa sannan yace nima nakirata , ayya aiko wlh ban San shi bane ,ta fadi Haka tare da dafe goshinta har aika masa da bakar mgn nayi fa arashin sani .Na dauka wani ne wlh ....
Abba ya tabe bakinsa to ke aunty meyasa kike yin irin hk ne ?
Komai fada fada da bakar mgn yakarasa fadar mgnrsa tare da shigewa 'cikin dakin mama yana mata gunguni ta juya tabi bayansa da kallon tana mamakinsa sannan yace Dan rainin hankali kawai ni kake fadawa hk taja tsaki tacigaba da aikin gabanta. ,




Gudu sosai Deeni yake sulawa akan express din oshodi zuwa kan bridge din obalende gabadaya a rude yake addu'a kawai yakeyi a bayyane Allah Yasa estate dinsu ta nufa ba wani guri ba ji yake tamkar ya fly yaganshi a gida km yaganta wani irin tsalle zuciyarsa ke yi sakamakon rudanin daya shiga.
" jikinsa Yayi mugun yin sanyi tamkar ana masa wanka da ruwan kankara da kyar yake iya hadeye miyo makoshinsa.
dai dai 'bakin checking point din da zai Kai mutun zuwa jakonde first get ya hangota zaune gaban wata dalleliyar motar fuskarta dauke da murmushi har wushiryarta ta bayyana .da sauri ya runtse idanunshi tare da sa hannushi ya murzasu .
ya sake budewa tabbas ita din dai yagani zaune gaban motar wani shima mutumin ciki sai dariya yake bulbula mata yana shafa sumar kanshi da hannunshi.


Da sauri deeni ya bud'e murfin motarsa yana shirin fitowa, kafin ya gama fitowa aka basu hannu da hanzari ya koma cikin motor tamkar wani zarar re yayi mata key, yabi bayan su, aguje sosai Deeni yake zabga uban gudu akan titi, dan shi kanshi bai san gudun mutuwa yake ba.


Ajiyar zuciya ya sauke ganin sun nufi titin estate d'in su, ci gaba yayi da binsu baya , ahankali ahankali har suka k'arasa ko'far estate d'in daga can baya Deeni ya tsaya yana hangen su yana son yaga abinda zai faru a tsakaninsu .


Zuciyar sa ce ta buga da k'arfi gaske lokacin dayaga Nablah tana sake yiwa matuk'in motar murmushi, wanda har sai da dimple dinta ta bayyana, sai da ta kusan wajen 15mnts da tsayawar motar sannan ta fito, har ta fara tafiya, mutumin ya k'ara yi mata magana ta juya ta rufe motar ta sunkuya ta window motar.


Mutumin yace " dan Allah ki bani phone number ki mana idan babu damuwa,sbd idan zanzo gurinki dariya tayi sosai dimple din ta ya sake lotsawa, muryarta a sanyaye tace " bani da waya wlh a gidan mu ba'a bari na rik'e phone, nagode sosai da taimakon dakayi min, ya bude motarsa ya fito ya tsaya agabanta yana gyara wuyar rigarsa tare da karemata kallon tsab sannan yace Ok to ko zan iya samun card din shiga estate din Ku .
Ta sake yin murmushi ai ba gidanmu bane aiki nake yi aciki ,can unguwar daka daukoni to anan gidanmu yake. yashiga yi mata wani irin kallo yana mamaki acikin ranshi yana maimaita aiki aiki nake yi anan .....kennan duk wannan kyawun nata a geto take rayuwa ? Take km
Wata zuciyarsa tace masa kada kayi mamaki daman mata masu tsantsar kyau da hankali suna geto km ya'yan talakawa ne ..... we'll shikennan yace babu damuwa koma dai menene naji nagani Ina sonki hk da fatan zaki karbeni ..... muryarta a shagwabe km a sanyaye tace uhm Nagode da soyayya ya dauko iPhone x ya Mika mata ki karbi wannan wayar so that idan zanzo sai Na Kira ki .
Ta girgiza masa kanta alamun bataso wayyohhhyyy kadan ya rage manager deeni Bai sume ba zaune 'cikin mota tsabar jarabar kishi mutumin Yayi ta karba taki karba sai daya matsa mata sosai tukun ta karba ta juya tasoma bada steps din tafiyarta me kashiwa mutun jikinshi ta shiga estate din .


Tunda Deeni yaga yadda Nablah keyiwa mutumin nan murmushi da dariya har fararen hak'onranta na bayyana, dimples d'inta suna lotsa, yaji kamar ya mutu, wani irin abu yaji ya tokare masa k'irjinsa, yana caccakar ruhinsa da tsokar jikinshi take km zuciyarsa ta shiga bugawa, idonsa suka dena gani sosai sai dishi-dishi, wani irin mugun zafi gami da d'aci yaji yana taso masa daga zuciyar sa zuwa k'irjinsa, nan da nan bak'in ciki gami da zafin zuciyarsa suka k'aro, yana ganin Nablah ta shiga gida ya fito da hanzari, ko motar bai tsaya rufewa ba, wata irin tafiya yake, ya nufi mutum dake shirin shiga motarsa .


A kansa Deeni ya tsaya cak yana k'are masa kallo tsana .
, iska ya furzar gameda yarfa hannunsa yace " kai mlm wannan yarinyar daga ina ka d'auko ta?
, wani irin wulak'antaccen kallo mutumin yayiwa Deeni sannan yace " malam lafiya dai?


Wata irin razananniyar Tsawa Deeni ya daka mishi yace " ban iskanci ba tamabayar ka nake ba.
cikin isa mutumin yace " daga gidan su, Deeni yace " meye tsakaninka da ita?

" Santa nake kuma auren ta zanyi mutumin ya bawa Deeni amsa kai tsaye, sai da Deeni ya dafe saitin zuciyarsa saboda wata muguwar bugawa da tayi da k'arfi, tana barazanar fasa k'irjinsa, hannunsa ya luma cikin sumar kansa, yana cizon leb'en sa da k'arfi, a harzuk'e yace " waye uban ka?


Ido mutumin ya zaro, shima cikin zafin rai yace " dalla malam waye kai dazaka zo kaina ka tsaya kana min wasu surutai marasa kan gado?


Deeni ya nuna kansa yace " ni......?

sai kuma yayi guntun murmushi yace " dan uwarka uban waye ya baka izinin tsaya min da mata ta,?
ido mutumin ya zaro yace " matar ka fa..?


"Kwarai kuwa matata ce, baka da hankali ne da baka lura da cikin dake jikin ta ba?


" dan girman Allah kayi hak'uri wallahi ban san matar aure bace, kuma Nablah bata gaya min tana da aure ba asalima yau nasoma ganinta har ma narage mata hanya .


Jin mutumin ya kira sunanta yasa Deeni k'ara harzuk'a, nan yabar mutumin ya nufi gida, a parlor ya sami Ummi da Nablah suna hira, dayake ummi tazo gidan maida kayan Nablah ...a fusace ya shigo parlor, hannunsa dafe da zuciyarsa, idonuwansa sunyi mugun yin nauyi , tafiya yake yana tangad'i tsabar jarabar kishi dake cin zuciyarsa..


" Subhanallahi Ummi ta fad'a ta mik'e tsaye ta nufe shi da sauri , dan bata tab'a ganin Deeni cikin mawuyacin hali,i Rin hk ba kuma cikin tashin hankali irin na yau ba, da ganin baya cikin hayyacinsa, gadan-gadan kan Nablah ya nufa, itama tayi masifar tsorata da ganin yanayinsa da sauri ta mik'e tayi bayan Ummi da gudu. Wayyohhhyyy nashiga uku..


Ummi na tambaya lafiya? amma ina ita kawai yake san ya kama, itako ta b'oye a bayan Ummi, kwata-kwata ya manta da wani cikin jikin ta, idonsa ya rufe, cikin zafin rai ya fisgo ta daga bayan Ummi ya zuba mata lafiyayyun kuma kyawawan marika guda guda biyu , then yana shirin rufeta da duka Ummi ta shiga tsakanin su tana rufeshi da maseefa ....



Nablah ta zube kasa tana kuka kamar ranta zai fita, hannunta Ummi ta kama takai ta d'aki, a bakin gado ta zaunar da ita, fridge taje ta d'auko mata ruwan me sanyi ta bata, sai da tasha Ummi ta kalle ta tace " mai kika yi mishi?


Cikin kuka Nablah tace " wallahi Ummi banyi mishi komai ba.,

"To naji yi shiru kinji, sosai Ummi ta lallashi Nablah sannan ta fita, a parlor ta iske shi, a tsaye yadda ta barshi, kallon sa Ummi tayi tace " me tayi maka son?


Shiru yayi, tare da furzar da iska,me zafi yayi ruku'u, ya mik'e a galabaice cikin rawar murya yace " wai yarinyar nan dan iskanci da aure na a kanta take kula samari, harta hau gaban motar sa suna hira tanayi masa murmushi, shi kuma d'an iska na tambaye meye tsakanin su, yace min wai santa yake, auren ta zaiyi, babban abin haushin ma har sunan ta ta fad'a mishi da karbar waya a hannunshi ...


Murmushi Ummi tayi irin na manya ta kama hannunsa ta zaunar dashi ahankali a tsanake take kallonshi tace"..........


MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗




AYSHA A BAGUDO



Dedicated to
*HAUWA A usman*
( JIDDARH)



Page 96


Tace idan ance maka kana son yarinyar nan nablah kace Sam baka sonta.
" yanzu gashi nan tsabar kishi ji yadda gabadaya yanayinka yakoma.
tunda Na haifeka deeni har zuwa yanzu ban taba ganin kamanninka sun sauya kazama wani irin mutun abun tsoro kmr irin yau ba .
"kama manta da cikar burinka wato 'cikin dake tare daita sbd tsabar kishi idanunka sun rufe kazo ka kwakwadawa yarinyar mutane mari.
in banda ma Allah Yasa Ina nan nashiga tsakani da sai kamata dukan dakayi asarar bby'n cikinta .
"idan ance kana sonta kace Kai ba Haka ba yanzu meyye wannan kayi ?



Deeni Ga son yarinyar nan karara Ina Gani acikin kwayar idanunka tare da zunzurutun kishinta .
Wanda Yasa har zuciyarka ke bugawa da karfin.
alokacin fa daka shigo dafe da tsaitin kirjinka kake sbd tsabar jarabar kishi da kunar da zuciyarka ke maka akanta ...

Deeni kana son yarinyar nan ko ka yarda ko karka yarda.
kanawa nabla wani irin mahaukacin so ka duba yadda kishi Yasa zakawa yarinyar nan nakaso.
ka duba yadda kake huci kmr zaki , ka duba yadda ka kama Yar mutane zaka mata dukan mutuwa kana kokarin son illata musu 'ya deeni ..
tunda ummi tasoma mgn deeni Yayi shr kawai yana sauraronta batare da Yayi yunkurin cewa mata komai ba.
sai ma rikitattun idanunshi daya tsura mata yana mata wani irin kallo me cike jin tsoron furucinta ...
uhm kayi shr kana dubana kaki cewa dani komai.
sbd kana tunanin zance nah ba hk bane.. muryarsa a sarke km can kasa kasa yace first love ....sai km Yayi shr ..
Deeni kennan karyata mgnta zakayi ko ?
Ba wai karyatawa zanyi ba first love Amman ni bana jin hkn atare dani km har cikin zuciyata da ruhin jikina bana jin wai sonta nake ..Ni dai nasan Ina matukar kishin igiyoyin aurena dake kanta yakarasa fadar Haka zuciyarsa Na tsananta bugawa da sauri da sauri....
Babu komai lokaci shi zai nuna Haka .
can km ummi tayi kasa sosai da muryarta nidai Dan girman Allah ka sausautawa kanka akan lamarin yarinyar nan..
Sannan km karage wannan mugun son dakake mata sbd gaba.. domin idan har yadda nake hango tsagwaron kaunarta 'cikin idanunka,idan suka zarta hk akwai matsala wanda gaba banida abinyi ....
Sannan ka tausayawa zeenat dina kada ta fuskanci wannan son dakake mata.
" ka boye mata kada ruhinta Yayi baki wanda nasan sanadiyar hkn zata iya shiga 'cikin wani hali ......hakika Ina tausayawa diyata ummi takarasa mgnrta tamkar zata zubda hawayen tausayin zeenat.
jikinsa a matukar sanyaye ya kamo hannuwan ummi dukka 'cikin nashi sannan ya Kira sunanta ... first love ki daina ce min hk sannan ki daina cewa Ina son yarinyar nan.
kada bakinki ya kamani ..
"bawai bakina zai kamaka bane deeni oready karigada kayi wannan saken...
Saken daka fada tarkon soyayyarta .
Ni farincikinka shine nawa ka nutsu kadaina takura kanka akanta dayawa ....
a Dan zafafe ya Mike tsaye ta riko hannunshi dake 'cikin nata Ina zuwa km sbd nace ka daina takura kanka akanta ne kayi fushi ..?
runtse rikitattun idanunshi Yayi sannan ya bude fess yana duban fuskar umminsa .. Sam wlh ba hk bane my first love zuwa zanyi nayi wannan yarinyar worning da kyau "
Dan wlh first love zan iya ilatata a duk sanda Na sake ganinta da wani Kato ...
karka sake ka km taba lafiyar jikinta ..
'Cikin jin zafin abinda ummi tace Ya kamo lips dinsa na kasa yana cizawa yana zame hannunshi cikin nata tare da hawa step ...
yayinda duk wannan dramar da'ake madam zeenat Na can dakinta ta manne kunneta da earpiece tana faman aikin chatting..


Yana shigowa dakin ya isketa zaune tana kuka sosai har da shesheka wani irin kallo wulakanci yajefo mata wanda Yasa kirjinta bugawa da sauri ta yunkura ta Mike tsaye da Dan saurinta jikinta Na kirma takoina .. a fusace deeni ya nuna Nablah dake tsaye da Yatsansa daya kana yace Daga Ina wannan mummunar mutumin ya daukoki ?

Tayi shr taki cewa komai sai hawaye ne ke silalowa.
ya furzar da isaka ta bakinsa yana cigaba da mgn 'cikin bacin rai Dan wulakanci km da tsabar iskanci Na tura Kule har so ba adadi gidanku ya daukoki Amman dayake ke Yar rainin sense ce kikace bazaki xoba ko? sbd kinsa iskancin da kika shiryawa kanki ko ?
Amman yanzu kin iya biyo wani katon banza har kina washe masa baki .
....to dariyar uwar me kike masa ?
Tayi shr nan ma taki yin mgn sai wani hawaye ne sharrrrrrr ke sake fitowa Daga idanunta.
shiiiiii ya daura yatsansa akan lips dinsa yi min shr munafuka kawai kukan munafurci me zaki min byn ki bude baki ,ki amsa min questions dina .
aiko take nablah tasoma maida kukanta da sauri ...
wai ke stupid har da wani fari kike masa da wayan nan banzayen shanyayyun idanun naki masu kama dana mayyu ko... ?
'zo nan zo nan ki kawo min wayar da wacen Dan iskan mutumin yabaki me kama kwado .. tayi saurin girgiza masa kanta alamun bazata zo ba.
Ok bazaki zo ba ?
bari ni nakaraso da kaina yasoma nufota ransa abace.
muryarta na rawa tace Dan girman Allah ka tsaya a nan karkaraso gareni tsoranka nake ji km ni wlh .... Tambayoyinka sun min nauyi wlh bazan iya amsa maka ba.
Kinsa Allah sai kin amsa min km a yanzu 'cikin kuka tace wlh bazan iya ba.
Zaki iya ne ya fada yana karasowa gabanta Daga inda yake yana jiyo bugun zuciyarta da sauri kmr yadda yake jin nasa zuciyar Na tsananta bugawa da sauri tana ganin Yayi kusa daita sosai .
taja baya sannan ta tsura masa shanyayyun idanunta 'cikin nashi wanda hkn yayi sanadiyar fitowar wasu abubuwa Daga idanunta suna shiga 'cikin nasa wani irin shock ya dinga ji ajikinsa .... muryarta a raunane km a shagwabe tace to..to..ka natsu ka daina fushin nan ka zauna zangaya maka wlh ... Nablah karki sake ki kawomin rainin hankali.
Wlh kinyi kadan ki wulakanta deeni ..
Sannan Ina son ki sani ni ba lusarin namiji bane wanda Bai San ciwon kanshi ba da kimar nauyin dake kansa ba .
cikakken namiji ne Ni wanda zai iya gwada kunjinsa a muhalinsa daya dace..
" gabadaya ta rude takasa fahimarta inda zancesa suka dosa yakarasa fadar hk. muryasa 'cikin da fada fada .
gabadaya ta sake rudewa tarasa yadda zatayi dashi.
domin bata son yanawa lamarinta shishigi da abinda yashafi rayuwarta .
Ganin yanayinsa Na sake birkicewa Yasa take wata idea tazo mata tayi saurin dafe gaban goshinta da hannuta tare da yin kasa luuuuuuuu zata fadi ..nan da nan deeni hankalinsa ya tashi karasa karasowa Yayi gareta yana kiran sunanta tare da rungumata jikinshi taki amsa kiran dayake mata .
Ke nablah .. nablah yana kiran sunanta ya girgiza fuskarta tana jinshi ta sake lafewa ajikinshi tana shakar daddaden kashin turaren jikinsa.
ya Mike tsaye daita ajikinshi ya kwantar daita a saman gado .
Da"" hanzari jikinsa Na rawa ya nufi fridge dauko ruwa ... nablah naganin hk ta Mike tsaye da sauri tayi hanyar waje da hanzarinta sai dai tana fita Daga dakin taci karo da zeenat wacce ta fito yanzu Daga bedroom dinta.
da sauri nablah tace yi hkr Dan Allah aunty tana goge Hawayen fuskarta ..

Me yabiyo hk Daga dakin ? Zeenat
Ta fada tare da rike mata kafardata.
muryar nablah cike da matsananciyar tsoro tace shiiiiiiiii shine ...

Shine wa ?
Daidai lokacin da deeni ya fito Daga dakin nablah a frigice yana haki

1 Comments On AUREN SIRRI
avatar
adam-ado

9 months ago

Reply

Very interested book

Please Login or Register in order to submit comment