Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

karo ya sauke ajiyar zuciya da karfi yana dubanta tana sauri tana hada kayan bby Na haihuwa Dan jiya daddare basu tafi da kayan haihuwa ba sbd a rude suke.
tana ganinsa duk ta dabirce tasoma kuka muryasa Na rawa yace Ina nablah da ummi 'cikin sharar hawaye tace suna hospital prioucion s .
Tun jiya batada lfy amman doctor yace nakuda ce ....inna lillahi wa inna ilaihi rajiun yana tafiya yana furta hakan acikin zuciyarsa atare suka shiga mota gabadayansu a rude suke .

sanda ya iso asibiti nablah ta jigata iya jigatuwa bbu kowa agurinta sai nurse nurse ne tare daita.
deeni ko gaisawa bai tsaya yi da ummi ba.

Hankalinsa a matukar tashe yace Ina nablah take ?
Suka nuna mishi dakin haihuwa Kai tsaye yashige 'cikin labour' room din wata doctor ce tace please sir kayi hakuri ka Dan jiramu awaje hankalinsa a matukar tashe yace madam Dan girma Allah kiyi hakuri nima Ina son naga matata .
Ai yana dora idanunshi akanta Bai san sanda hawaye suka shiga siyayo masa .
ya mannata ajikinshi ya rungumeta yana kuka da aikin jero mata sannu bbu kaukautawa addu'a kawai yake mata yana zubda hawayen tausayinta ya dinga jin daana kar bar wa mutun nakuda daya karbarma ta huta tun daren jiya ake abu daya har yanzu . tamkar shi nakudar take jira ta tashi zanga zanga Amman haihuwa shr bbu labari .

Hankali likitoci Suma yayi matukar tashi sosai tun daren jiya suke tsaye akanta , zeenat kuwa a ranta tace tun dai shekaranjiya Dan dai bamu gaya muku gsky bane .
.. likitoci suka tabbatarwa deeni zata haihu zuwa karfe goma shabiyu ranar Amman gashi har yanzu shr Ga dai 'cikin Na motsa alamun bby 'cikin Na raye.
Sosai hankalin deeni yakai karshe gurin tashi tsigar jikinshi har tashi suke tsabar tausayin yarinyar .
ganin har biyu tayi ta wuce bbu sauki sai wahala datake Sha Yasa Shi cewa doctors din suyi mata aiki su cire mata abinda yake 'cikin ta huta .
tunda sauran karfinta yazamo yanzu ko nishin bata iyawa sai shanyayyun idanunta datake jujjuyawa wal wal dasu .

Hudu daidai aka yi mata shirin aiki sai addu'a ummi keyi ita ko zeenat kuka take sosai har da shesheka .


A dakin tiyata sabon ciwo yatashi 'cikin zafi zafi ta dinga jin bayanta tamkar ana Sara mata da ada jikinta wani irin rawa har gadon datake kwance akai shima sheking yake .iya wahala nablah tasha sai dai Allah sauketa lafiya ..

Deeni rike da hanuta yana kuka yana mata addu'ar .Shi yanzu bata 'cikin jikinta yake ba ,ita din yafi bukata .domin duk yadda yakai da son haihuwa sai daya ji ta fita aranshi tausayinta da kaunarta ke zariya a gangar jikinshi.
wani irin uban nishi tayi da karfi sai Ga kan yaro ya fito fit .
Jim kadan wani kadan wani yaron ya sake fitowa sororo deeni yayi yana kuka yana kallon ikon Allah Wani sabon kukan farinciki ya kufce masa ya rike hannuta gam yaki saki sai sumar kanta yake shafa ahankali yana mata sannu can km sai Ga wani sabon ciwo nakuda take doctors din suka gane Yan uku ne suka taimaka mata aka fiddota agalabaice duk tafisu shan wahala Dan ko kuka batayi.
nan suka fita da yaran duka uku Dan gyarasu ummi tayi matukar farinciki da saukarta lfy an shirya yara ummi nata murna .


Shi kam deeni bbu wanda yake son Gani kmr nablah doctors sukace masa kada ya damu ana kimtsa ta ne suka mata allurar bacci sannan suka kaita dakin hutu bacci take sosai Dan batasan irin hidimar da'akeyi daita ba .koda zeenat taga bbys sai kirjinta ya buga sbd tsabar kamanin da suke da deeni sak sak komai Nasu Na deeni har ma gara ta mace ta dauko kamanin uwarta sai sai farin Na deeni ta debo .'aiko take tasoma yiwa ummi mitar kamanin yaran .Kai zeenat wlh Kin fiyye matsala Wani kama yaran nan sukayi da deeni kawai idanunki ke ganin hk Amman ni Banga hk ba ..


Tun asibitin ummi ta dinga kiran dangi tana sheda musu zeenat ta haihu sauka lafiya tasamu yan uku .

Sannan ta tilasawa doctor kan sai ya sallamesu a ranar doctor yace a'a sbd uwar tana bukatar hutu .ummi tace bbu damuwa abar uwar anan zasu wace da yaran doctor yacika da mamaki Amman dayaga ai sune suka kawota yace shikennan .

Suna komawa gida nan dangi sukayi matuka murna da farinciki saukarta lfy kowa sai albarkaci bakinsa yake fada Kai Kai zeenat gsky kin iya haihuwa tamkar bake ce kika haifi yaran nan ba.
Kai Masha Allah Yara sak ubansu takoina deeni yaran nan suka dauko ita dai sai dai tayi murmushi kawai tana duban yaran dake kwance masu tsantsar kamanin da mijinta tun asibitin gabanta ke faduwa sbd tsabar kamanin da yaran ke yi da deeni ..

ita kam nablah tana can hospital batasan hidimar da'ake da bbys dinta a gida ba.
Dan batama San yan uku ta haifa ba .


Tana farkawa idanunta suka sauka akan deeni ya taso da sauri sannu nablah kin tashi ?
Kallonsa kurum tayi .
Ta kauda fuskarta gefe ya wanke mata baki 'cikin wani dan karamin kwanan siliva tare da tayarda ita zaune yaje ya ajiye kwano ya hado mata tea me kwari yazo yana bata da kanshi ..idanunta kawai ta tsura masa tana kallonsa tana tea din .
ahankali ,shi kanshi yagane mgn take son yi .. 'cikin sanyi jiki ta kauda bakinta Daga cup din . alamun takoshi .
Ya ajiye cup ya dawo gefenta ya zauna ya kamo tafin hannunta 'cikin nashi yana mammatsa mata magana take son yi Amman bakinta Yayi mata nauyi ..

Ya kafe da rikitattun idanunshi gabadaya tayi wata irin muguwar rama acikin kwana biyn din datayi tana nakuda muryarsa a sanyaye yace kina son wani abu ne akawo miki ?
Ta girgiza masa kanta. ahankali .

Ok kimin mgn mana naji muryarki ko wani guri Na miki ciwo ne,?
Nan ma ta girgiza masa kanta ..can km muryarta a raunane tace Ina abinda Na haifa ?

Gabansa yayi Wani irin tsalle Dan baiyi tunanin zata tambayi abinda ta haifa ba .take
Zuciyarsa tashiga harbawa da sauri da sauri muryarsa can kasa kasa yace Suna gida gurinsu ummi .
ta runtse shanyayyun idanunta da suka sake shanyewa tsabar wahala dataci .
yabita da wani irin kallo tunhuma Haka kawai yaji gabansa Nacigaba da dukan uku uku sautin muryarta ya sake ji nima Ina son zuwa gida .yace Ok bari nasamu doctor . Ya Mike tsaye ya sumbaci goshinta kana ya fice da sauri yana waigenta .


Byn deen yasamu doctor yayi masa bayanin ko za'a iya sallamarsu bbu wata matsala doctor yace bbu komai ai zasu iya wucewa ..


Sai yamma liss suka shiga estate din ta kofar baya deeni yashiga daita sbd taron mutane dake 'cike da gidan.
Yan taya murna bai samu damar kaita dakinta ba .
ya nufi dakinsa na kasa daita zuwa lokacin da jama zasu tafi ..



misalin karfe tara Na daren deeni yaje gadon kwanciyar yaran ya dauko mace da namiji ya rungume yaran yana jin matukar son yaran nabin jiki da jinin jikinshi yana mamaye ruhinsa da zuciyarsa .. ummi ta dauko daya suka nufi dakin da nablah take .
Da sallama suka shigo dakin nablah .
suka zauna tare da saka nablah a tsakiyarsu muryar deeni cike da farinciki yace nablah kinga arzikin da Allah Ya ...wani irin kallo ummi tayi masa yakasa karasa abin zaice take km yagane ashe yaso ya kwabsa ne..kwantar da yaran sukayi akan bed .wayanda suka Sha wasu haddun kaya sanyi masu shegen kyau da tsada da daukar hankalin farare tas tas dasu tamkar ya'yan turawa ,sosai ta tsurawa bbys din ido tana masu Wani irin.kallo kamanin yaran take kallo 'cikin tashin hankali taki dauke idanunta akansu yanzu itace ta haifi wayan nan kyawawan bbys din masu kyawun kyau hk ganin yadda yake kallon baby's din Yasa ummi tashi ta fice shima can deeni ya Mike tsaye yana amsa wayar Yan taya Shi murna ya bar dakin .

Dakin ya saura Daga nablah sai bbys dinta da suke kwance reras akan gado abin sha'awa. kallon yaran tacigaba tana jin Wani irin sanyi Na bin jikinta take km taji Wani irin mugun son yaran yashiga ranta tare da ratsa kowane shashi Na gangar jikinta tundaga tafin kafafunta har 'cikin kwalkwaluwarta nan take taji idan dukiya zata taru bazata iya rabuwa da yaranta ba ,daidai da daya Daga cikinsu bazata iya bayarwa ba ballanantana dukansu kawai ta fashe da wani irin matsanancin kuka tare da rungume yaranta tasoma sabatu , wallahi tallahi bazan iya rabuwa daku ba yarana Ina sonku ina kaunarku km zan rayu daku.
koda kuwa duniya zatakini .
ta zageni akanku Ina sonku takarasa fadar hkn tana sakin Wani irin kuka me cin rai ahankali take cigaba da kallon baby's dinta hawayenta Na tsaya ahankali tasa hannuta ta goge tana sakin ajiyar zuciya 'ta daura mazan duka a saman cinyoyinta mace km ta daurata akafadarta tana jin Wani irin dadi mara misaltuwa aranta tare da jin duk abinda zai faru sai sai ya rafu Amman bazata rabuwa dasu ba ....



Uhmmmm nah wa oooooooooo







MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗




AYSHA A BAGUDO


Dedicated to
HAUWA A USMAN
JIDDARH


Page 99



'Cikin wannan halin datake ciki deeni ya km shigowa dakin fasukarsa dauke da wani irin maganadisun murmushi .ta koina ka kalleshi kasan yana 'cikin tsantsar farinciki da murna samun wayan nan kyawawan bbys din masu matukar kyawun da daukar hankali .

Ahankali yakarasa inda take zaune rungume da ya'yanta duka .
ya tsura mata rikitattun idanunshi yana kallonta da jin Wani irin mugun sonta da yaran yana tasoma masa .
Yanayin daya ganta ciki yasashi shan jinin jikinshi .
zama yayi kusa daita sosai har cinyoyinsu Na gugar juna ya amshi ta mace Daga hannuta ya daurata saman cinyarsa yana kallonta yana kallon fuskarta nablah dayaga gabadaya ta canza ta dawo wata iri . muryarsa a sanyaye ya Kira sunanta nabeelah ....bata amsa masa ba sai ma juyo da tayi inda yake zaune tayi masa kallon second 2 kana ta dauke idanunta Daga kanshi.
ta maidasu kan yaranta dake cinyarta .
,sautin muryarsa taji a matukar sanyaye fiyye da farkon shigowarsa dakin .. nablah kinga kyautar da Allah Yayi mana ko?

Adakike ta amsa masa da uhmmmm . gsky kin iya haihuwa.
arayuwata bantaba ganin macce data iya haihuwa kmr ki ba .
Gsky kinyi kokari sosai . nan ma tayi masa banza ta sharesa gabadaya ma taki cewa dashi komai .
yanzu mekike bukata akawo miki ?
muryarta can kasa kasa tace babu tare da kamo lips dinta Na kasa tana cizawa ahankali ahankali tana Dan jijjiga kafarta daya akasa .

Gabadaya deeni ya rude yarasa abinda ke masa dadi tunda ta haihu yarasa gane kanta sai wani shashsharesa take tana basar dashi da ciccin magani wanda yarasa dalilinta nayin hk . runtse rikitattun idanunshi Yayi sosai .
ciki Mutuwar jiki sakamakon tuno da kyawawan bbys dinsu data haifar masa masu tsananin kamadashi km yake tare dasu ahalin yanzu.
To me zai dameshi da duk abinda zatayi arayuwa tagama masa komai tunda tabashi abinda yafi so da kauna a rayuwarsa ta duniya . sumbar bby girl din yayi yana jin wata irin natsuwa ta daban tana ratsa kowane shashi Na gangar jikinshi sosai yake son yaransa Amman yafi jin kaunar mace fiyye da sauran acikin zuciyarsa .
Jikinasa cike da rauni soyayyarta yakamo tafin hannuta 'cikin nashi yasoma murzawa ahankali ahankali 'hade da shaukin kaunarta yace meke damunki nablah naga duk kinyi wani iri hk ?

Ki sanar da deeni abinda ke damunki banason ganinki 'cikin wannan damuwa da tashin hankalin please ...
yanzu kin zama wata bangare Na rayuwata da farincikina gabadaya sbd wannan kyawawan bbys din dakika bani ..

Kimin abinda wata matar takasa jura ta min arayuwa .
Kin bani kyautarsu alokacin danafi bukata . akan wayan nan yaran bbu abinda bazan iya miki Shi ba , matukar Bai shafi addanina ba .
ban ji dadin yadda naganki ba yanzu.
idan akwai wani abu dake damun zuciyarki ki fito ki sanar min.
ni km nayi miki alkwarin zan yi miki maganinsa kowani iri ne .. yakarasa fadar hk yana matse laulausar tafin hannunta 'cikin nashi yana jin yadda sonta ke fizgar zuciyarsa gareta ..


So take tayi mgn Amman maganar taki fitowa sakamakon wani yanayi data tsinci kanta ciki ,ita fa bbu abinda ke damunta s halin yanzu wanda ya wuce son rabata da ya'ya za'a yi.
ta lumshe shanyayyun idanunta kana ta budesu ahankali ta zubesu 'cikin nasa still takasa tabuka komai shima lumshe rikitattun idanunshi Yayi sannan yace Ok kingama ganin yaran zan maidasu kasa sbd masu zuwa ganin bby ..
take zuciyarta ta buga da matsanancin karfi har sai data taji zubowar gudan jini Daga kasanta . afrigice ta zare hannuta 'cikin nashi tana kallonsa a tsorace bakinta da alamun son yin mgn .
kanshi ya girgiza mata yana kokarin mikewa tsaye .


Muryarta cike da inn inna ta fizgo mgn da kyar tace nifa.. nifa ..ban bada ya' yana.

what ? Bai San sanda yakoma ya zauna ba .yana kallonta da matukar mamaki .

Wallahi wallahi deeni idan duniya zata taru akaina idan sama da kasa zata hade idan za'a yi ruwan jini deeni bazan iya bada ya'ya nan ba.
kai ni daya Daga cikinsu ma bazan iya bayarwa ba ballanantana duka .
deeni koda duniya zata kini ciki kuwa har da mahaifana dakai deeni koda zan dawo kwanan akan bola Ina tsince tsince in ciyar da kaina da ya'ya Na ,bazan iya bada ya'yan nan ba wlh. duk da Allah yasani bansan waye mahaifinsu ba Amman Ina ji ajikina mahaifinsu ba wulakantacce mutun bane duba Ga yanayin ya'ya.
take gaban deeni ya fadi rassss rassss rassss yashiga bugawa da karfi karfi .zuciyarsa tashiga tsalle da kururuwa neman dauki da agaji .

muryarta ahankali 'cikin sanyi jiki tacigaba da mgn tunda Na kalli fuskar ya'yan nan narasa meyasa naji Ina mugun kaunarsa wanda bansan dalili ba narasa meyasa tun sanda Na daura idanuna akansu kawai naji bazan iya rabuwa dasu ba .
takarasa mgnr tana fashe masa da wani irin matsanancin kuka me cin rai da Daga hankalin .

Jikinta Na matsanancin rawa ta kwantar da yaran daya byn daya akan gadon.
da kyar ta sauko Daga kan gadon datake ta zube masa a gabansa ta dinga kuka Dan Allah deeni karku rabani da ya'yana Ina son su ko zan rasa raina bazan iya rayuwa bbu su ba.
Wallahi bazan iya rabuwa da yarana ba aduk yanayin da suke Wallahi azim bazan iya rayuwa bbu su ba ni Ina son su a Haka .
kuka take sosai tana rokonsa akan kada surabata da yayanta .


Gabadaya jikin deeni yayi Wani irin mugun tsayi km ilahirin jikinshi suka mace murus yarasa abinda ke masa dadi a zuciyarsa .
Ga koshi Ga kwana yunwa.
hankalinsa ya Kai kololuwar gurin tashi gabadaya yarasa abinda yakamata Yayi ahalin dayake ciki .
kukan farinciki zai yi ko haushinta zai ji Na sabon salon iskanci data tsiro ... sai kallon bbys din yake yana kallonta tsugunne agabansa tana risgar kuka tana rokonsa .
shima ajiye bby' girl din dake hannunshi yayi .
ya tsura mata rikitattun idanunshi da kyau yana cigaba da kallonta hade da nazarinta wato dai da gaske mutuwar son yaran take kmr yadda shima yake matsanancin son su .
duk Shi a tunaninsa yafita son su da bukartasu arayuwarsa ..
a zuciyarsa yaji wani irin matsanancin sanyi ya ratsashi tundaga tafin kafafunshi zuwa kwanyarsa , kennan idan yace zai isar da sakon zuciyarsa gareta bazai Sha wata wahalar shawo kanta ba adalilin wayan nan yaran ..

take km burin mahaifiyarsa ya fado masa .
yaya zaiyi da ummi wace oready tagama gaya duniya da shelar cewa zeenat ta haihu ?
..yaya zata ji idan tasamu wannan mummunar labarin ?

Kuka take Sosai ta rike kafafunshi gam deeni kayi hakuri nasan ban kyauta ba akan abinda nayi Amman Ina son ya'yana duk da kasancewarsu shegu wlh ba zan iya kyauta dasu ba kmr yadda nayi maka.. shiiiiii Karki kara kiran ya'ya Na da she.. shegu ni..Ni..ne ...sai km yayi shr ya datse harshensa da hakorinsa gam jikinsa Na wani irin matsanancin rawa idanunta dake cike da ruwan hawaye ta xuba masa tana kallon bakinsa .. zuciyarsa gabadaya gaskiya take son fada mata Dan ta daina danganta ya' yansa da kalmar shegu Amman yana jin matsanancin tsoron tashin hankali dazata shiga fiyye da wanda take ciki ahalin yanzu.. Shi dai yasan xuwa yanzu ya Mika duk rayuwarsa gareta sbd kaunar dayake mata ita da yayanta ...

'Cikin wannan halin zeenat da ummi suka shigo dakin atare turus sukayi ganin nablah durkushe gaban deeni rike da kafafunsa tana risgar kuka da iyakacin karfinta .

Da sauri suka karasa garesu suna tmbyr deeni lafiya meke faruwa ?

'cikin rawar jiki nablah ta Mike tsaye ta nufi gurin ummi tana layi tana kuka muryarta cike da kuka tace Dan girma Allah ummi ku min rai wallahi bazan iya bada ya'yan nan ba kumin abun alkhari nasani km Na gode da karamcinku gareni Amman kada Ku rabani da ya'yana .....

A zubure zeenat ta dafe kirjinta tare da cewa what ke kina da hankali kuwa ?

Ke wace irin mahaukaciya ce yaza'a yi kice bazaki iya bada ya'yan ba .....
take nablah ta fuskanceta sosai a fusace tace gaki nan babbar mahaukacirya da batasan abinda takeyi ba da sanin ciwon Kanta ba.
ke kinsan zafin haihuwa ne?

ko kinsa zafi ya'ya ke kinsa wahalar dana Sha akan wayan nan ya'ya?

to nace bazan bayar ba km idan sama da kasa zata hade bazan bada ya'ya nan ba ke ni akan ya'yan nan banki duniya takini ba ciki km har da iyayena wallahi wallahi dana bada ya'yan nan gara narasa rayuwata gabadaya.
ke indai kika ga nabada ya'ya nan sai dai idan bana numfashi a doron kasa .

rassss rassss gaban ummi yayi wani irin matsanancin bugawa da karfi ..Hk ma deeni gabansa ya km bugawa zuciyarsa tacigaba da rawar datake tun kafin shigiwarsu ummi ..

Zeenat tace Wallahi wallahi baki isa ba nablah kinyi kadan km sai kin bada yaran nan tunda tun farko ke kika amince km kinyi alkawarin zaki bada su muryar zeenat Na rawa takarasa fadar hk .


Wani irin kallon tababbiya nablah tayi mata sannan muryarta Na rawa rawa tace to..to.. yanzu nafasa badasu sbd nima Ina son abuna dama can danayi kyautar su bansan zafinsu bane yanzu kuwa sai dai nabawa wasu labari .
Baki isa ba wallahi sai dai kuwa ki rasa ran naki dakike ikirarin rasawa akansu Amman kmr kin bada ya'ya kingama .. Ok zanga wanda ya isa dazai rabani da ya'yana ..

ke nifa nafiki zafin Kai da rashin mutunci akan yaran nan zan iya miki duk abinda yazo zuciyata inji cewa zeenat .

baki nablah ta saki tana kallon zeenat da mamakinta hakan yabawa zeenat damar cigaba da maimaita kalmar dole abasu yara tunda tun farko an rigada anshirya hk da surutai kala kala tayi kan baby's cike takama zata dauka nablah tayi kuka kura ta dire gabanta cike da maseefa tace ubanwa yabaki damar taba min yara ?

Ubanki da km uban Yayi miki ciki a gidan nan .
a fusace ummi tashiga tsakaninsu tana jan zeenat baya.
ummi ta dinga mamakin abinda nablah tayi duk da tasan Yar tatace da fadan rashin gsky Amman batayi tunani nablah zata iyawa zeenat rashin kunya da tsiwa Haka ba .


Ni zaki kawo danyen Kai da ranshi kunya ta fadi Haka tana nuna nablah da yatsan hannuta Dan girma Allah ummi ki matsa Na canzawa wannan Yar iskar yarinyar halitata dama Ina da ciki daita Ina takaici ta wlh.

kallon kasa da sama nablah ke bin zeenat dashi ahankali wanda ke nuna alamun bata isa ba .

Kina takaicina ai sai kixo ki kasheni ki huta banda mijinki daya nace akan zai taimakamin da tuni ban san inda dare Yayi min .
zeenat tayi sororo tabi deeni da wani irin kallo tana jiran taji yakarya mgnr yarinyar .
Amman taji Yayi shr yana binsu da idanu kawai .
my hrt ummi kuna jin fa abinda yar iskar yarinyar kecewa ko.
ummi tace munji ai zance nata duk shirme ne bakya ganin duk abinda take bata 'cikin haiyacinta tasoma jijjga zeenat din kiyi shiru mu yanzu bawannan shirme bane agabanmu yadda yara zasu zama naki shi kawai .kiyi shr ki natsu asan abin yi .


nablah najin Haka ta buga kafarta daya a kasa ta nufi gurin da bbys dinta suke kwance gadan gadan tasa wani irin mahaukatan kuka tana cewa wllahi tallahi ban bada ya'ya Na .
ya'yan guda uku ta rungumesu ajikinta tana sake sakin wani irin matsanancin kuka me ban tausayi da taba zuciyar ma aboci saurare ..

Tashin hankali wanda ba'a saka masa ranar zuwa .
zaune kawai deeni yake yana kallon sarautar Allah.
Yana mamakin daman zafin kan yarinyar nan yakai hk Shi Bai sani ba ....abu kmr a film yarinya tana kokarin birkice musu da dagula musu lissafi.
hatta ummi tsaye kawai take sake da baki tana kallon ikon Allah da yadda nablah ke nuna reaction dinta akan bby din da batasan taka maimain wanda yayi ma 'cikin su ba .
,to wannan idan km tasan ya'yan deeni ne km jikokinta me zai faru ? Tayi wa kanta tmbyr tana cigaba da kallon nablah rungume da yara tana kuka .
tamkar wata zautaucciya .
Gabadaya Daga deeni har ummi kasa tabuka komai suka yi sai idanu da suke bin nablah dashi ...

Wani irin tausayinta ne me gyaraye da tsansar soyayyarta ke sake huda kirjinsa da mamaye gangar jikinshi da zuciyarsa .
alahakikanin gaskiya Bai taba tunani yarinyar zata canza salo irin Haka ba.bai dauka zata so ya'yan da ta dinga hauka akan acire mata su ba .
Wani irin gumi ne me zafi ya shiga tsaftsafo masa ta koina ajikinshi yazama tamkar wani mutun mutumi a zaune yana kallon nablah kwakwume da bbys ajikinta duk tayi firi firi tafita haiyacinta .


Take zeenat ta dinga jin zuciyarta tamkar zata fashe ta tarwatse kan takaicin nablah.
ita kanta wani irin mugu mugun son bbys din ne yashiga ranta tun sanda suka zo duniya ta daura idanunta akansu taji sun shiga ranta.
duk da duk sanda ta kallesu gabanta Na tsananta faduwa akan tsananin kamanin da yaran keyi da mijinta.
Dan ko mahaukaci ya kalli yaran yasan kamarsu daya da deeni babu wani bambanci launi ko sura daidai da yatsun kafafun yaran dana hannusu irin na deeni ne sak .
bakinsu da hanci komai Nasu irin nasa ne .
sosai take taji wani irin mugun son yara Na sake ratsata har 'cikin zuciyarta

1 Comments On AUREN SIRRI
avatar
adam-ado

9 months ago

Reply

Very interested book

Please Login or Register in order to submit comment