Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gushewa yayinda sha,awarta kawai ke cin ransa da wani irin tsananin tausayinta dayake jin yana ratsa masa gabobin jikinshi ahankali yake binta 'cikin natsuwa tare da samun hadin kanta bukatarsa ta biya har suka fada cikin duniyar ma'aurata..sosai suka gamsar da junansu da zuciyoyinsu da muradinsu wanda suka jima suna kewar juna byn dan wani lokaci komai ya lafa atsakaninsu .
ya dauketa sukayi bathroom dinta daita wanka sukayi atare zeenat najin wani irin matsanancin son mijinta sosai tare suka fito suna manne da juna ta sauya wasu kayan shima ya tsaya shirya kanshi Amman da kyar ya kyaleta domin manne yake daita ajikinshi dan Sam yakasa barin tayi koda kwakwaran motsi ne ...


Washegari da sassafe ya tashi ya bar dakin zeenat ya nufi dakin nablah ya budeta.
ya shiga ya dubata bacci take sosai ya ya yaye bargon daya lulluba mata, tare dage rigar jikinta ya daura kunnenshi saman 'cikin yana jin motsin cikinta. lumshe rikitattun idanunshi Yayi yana jin sanyi har 'cikin zuciyarsa ' kiss Yayi cikinta da lip's dinta sannan yabar dakin zuwa masjid .

'Cikin kwanaki nan ko office deeni yaje Allah Allah yake ya dawo gida gurin zeenat wata irin kulawa ta musamman yashiga bawa zeenat din tare da yi mata hidama sosai da fada mata kalamai masu sanyaya rai da kashe zuciyar data dade 'cikin shaukin so. duk da nata ran zafi yake mata har lokacin inda yagaya mata ta daina damuwa akan nablah shi bakomai bace agurinsa facce me aiki .. sannan yace tayi hakuri kan duk abinda Yayi mata yanzu yana son kwanciyar hankalinta da ganin farincikinta.
wani irin yanayi ta tsinci kanta ciki mara misaltuwa gabadaya ya kashe mata ilahirin jikinta da zantuttukansa masu birkita mata lissafi bbu abinda tafi so da kauna sama da farincikin mijinta dan hk ta sake rungumar mijinta da hannu biyu biyu tana zuba masa shagwaba iri iri ...

'Cikin wannan lokacin nablah taga abin mamaki me tsoratar da zuciya.. domin tun dawowar matarsa taga deeni ya rage shishige mata kmr lokacin da basu nan .
hkn Yasa zuciyarta ta dinga kitsimata abubuwa dayawa akanshi har ta yarda lallai namiji munafiki ne km bashida alkibla .
,kwata kwata ya daina zuwa Inda take indai matarsa Na gida sai dare zai zo mata yaga lfyr jikinta ya dan mammatsata da romancing dinta .
"sannan duk byn kwana biyu zai zo dakinta nan zai kwana har sai asuban faru tukun zai koma dakinsa ta kula kmr ya raba musu kwana Keenan atsakananinta da matarsa.
duk randa yake dakinta kuwa bata iya bacci kirki takure jikinta take karshen gado Yayi Yayi ta saki jikinta dashi bbu abinda zai faru km bbu abinda zai mata amman taki yarda dashi .
dan ita gabadaya atsorace take da almarin. kada matarsa tasan halin da mijinta yake ciki akanta da km 'cikin jikinta ..



Tsaye take abakin wani dan karamin lugu tana wage wage tare da neman yaron dazata aika 'cikin gidan Nasu.
can Allah Ya taimaketa ta hango tahowar wani karamin kaninsu wanda shine auta acikin gidan.. muryarta amatukar sanyaye tace abba ...

abba wanda ya kusan giftata ya dawo ahankali inda take tsaye yana karemata kallo tsab da son gano ko wacece ita sakamakon nikaf din dake manne da fuska.. can km Yayi murmushi yace kai aunty Sal.....shiiiiii ta daura dan yatsanta a saman bakinsa tun Bai karasa ba .
"Baba Na 'cikin gida ne ?
Abba ya girgiza mata Kai baya gida yana gurin dauda me kanti gurinsa ma zani yanzu .
yauwa bari nashiga Amman kada kafada masa naxo fa .. yace to aunty ta ciro naira hamsin acikin jakarta ta mikasa tayi gaba abinta ...

Da sallama bisa harshenta tashiga gidan Nasu da yanzu yasamu sauyin yanayi rayuwa .ba kmr da ba ..shr taji koina bbu motsin kowa .
Muryarta a dan tsorace tace wai Ina mutane gidan nan suke ne ?

Atare mama da nuratu wacce nablah ke bi suka fito tsakar gidan suna gamu kabo kabo mama tace tana murmushi, har yanzu Salma bazaki rabaki kanki da sanya wannan abu ba a fuskarki ba ?
Uhmmmm mama Ina zan iya da fadar baba tunda yace kada Na sake zuwan masa gida muddin ban dawo masa da nablah ba .
kinga kuwa dole na kasance hk matukar Ina son zuwa ganinku inji cewar Salma dake kokarin zama kan cement dake malale atsakar gidan Daga mama har nuratu dariya suke mata sannan sukace sannu da hanya ta amsa tana gyara zaman nikaf din fuskarta da kyau ..Ni Banga amfani wannan fadan Na baba wlh , yarinya Na can tana achieve din rayuwarta zai damu kanshi da mutane kmr an tsiyar daita.
uhmmmm nuratu bana son jin wannan mgnr Daga bakinki bashi kadai ba koni kaina yanzu Ina bukatar ganin yarinyata . wata takwas kennan fa rabon damu sanyata 'cikin idanunmu ko Yar kaza kabayar dole kadu ballanantana mutun sukutun . ban da ma Muna yin waya da hjyar ba , da tuni nasa Salma gaba na dauko yarinta ..suka kwashe da wata irin dariya gabadayansu.
kai jama'a tsakanin mama da baba narasan wanda yafi wani nacin nablah ba nuratu ta karasa fadar hkn tana tabe baki ..Ai duk son ya'ya dasu Daga baban har mama
Ina Muhammad da Kamal ne bangansu ba niji aunty Salma?

Muhammad an sakashi koyon aiki kaniknci Kamal km ya tafi gurin aikinsa Ok Allah Ya taimaka .
nuratu taje ta kawowa aunty Salma ruwa me tsanyi da sauran abincin dayayi saura sannan suka shiga hirar duniya awa daya tayi a zaune kafin daga baya suka shige kuryar dakin mahaifiyarsu suna cigaba da zantawa duk akan dawowar nablah gida da zarar ummi ta dawo ,wanda alokaci basu da masaniyar dawowar ummi din tunda bata Kira aunty Salma ta sanar mata ba ..'.

cikin hk suka jiyo muryar mlm salisu yana doka sallama yana kiran sunan nuratu ...nuratu gaban aunty Salma ya fadi wayyo Allah mama nashiga ukuna Ga baba nan ..
wai nuratu kina Ina ne hk nake ta faman kiranki ?
Nuratu ta fito da gudu ta tsaya a 'bakin kofa Gani baba Na kokarin shigawa ciki , Ina singilotocin danace ki wanke min?

shagwabe fuska tayi sannan tace shi nake son wankewa yanzu maza ki kokarta ki wanke min banida Na saka km zuwa anjima Ina son shiga 'cikin apapa .

to aima baka bani kudin sabulo ba yasaka hannushi 'cikin aljihun gaban rigarsa ya ciro dari biyu ya Mika mata yana kokari sanya kanshi 'cikin dagon parlour gida yana kiran sunan mama itama ta fito 'cikin sanyi jiki ta tsaya abakin dokin kofa dan kada yasamu damar shiga dakinta ungo wannan kisamu abinda kika dafamana daddare ya mikamata odindin dubu daya sannan yakarasa dakinsa . wanda xuwa lokacin Salma dake daskare 'cikin dakin mama kadan ya rage zuciyarta bata buga ba tsabar frigice. tana jin ya shiga dakinsa ta sauke naunauyen ajiyar zuciya tana goge gumin dake tsaftsafo mata .
mama ta zuba mata idanunta kema Salma ke maida hankali gurin dawowar yarinya nan .
nan kusa kindai San halin mahaifinku sarai bakara min aikinsa bane yabiki har gidanki ya tara miki jama'a.
nima wlh abinda nake fargaba kennan mama shiyasa kullun nake addu'a .

Saratu mlm salisu ya kwallawa mama Kira ta sake fitowa suka cikaro dashi zai shigo dakin ya'akayi ne baban Salma ?
Sai naji wata murya tamkar ta Salma a gidan nan ..?
Salma km a gidan nan ? yaushe rabon Salma da zuwa gidan tun zuwanta Na karshe dakayi mata korar kare ai bata sake zuwa ba .
bakuwa mukayi kawar nuratu ce tazo mlm salisu yayi Jim yana tunani da bin dakin da kallo shifa yasan muryar Salma fiyarsa ya jiyo sama sama koda yashigo gidan ma yaji ,yace shikennan tare da juyawa jikinsa sanye Yayi tsakar gida da babbar Riga ajikinsa da alamun wanka zai shiga ya tsaya yana gyara sajen fuskarsa .

Ki hanzarta barin gidan Salma kafin ya fito Daga wanka ya tara miki mutane to mama Salma ta Mike tsaye da hanzarta tana gyara zanin jikinta itama nuratu ta Mike tsaye tare da fitowa tana Yan dube dubenta taga abinda baban Nasu yake .

yauwa nuratu miko min singlet guda biyu Na wanke yanzu kya wanke min sauran Daga baya ,gaban nuratu ya fadi rassss dan tasan halin wanki babansu dadewa yake Bai gama ba.
ta juya da sauri jikinta Na rawa mama aunty Salma kinji wai wanki baba zai yi km yanzu ta fadi hk fuskarta tattare da damuwa gaban Salma yashiga dukan uku uku ta dafe kirjinta dan girma Allah ?
Wlh hk yace kinga shiryawarki kawai kiyi tafiyarki ba lallai bane ya Ganeki ,ince har safa kika saka inji cewar mama ? Salma ta gyada mata kanta batare datace komai ba oya maza ki wuce abinki Kin dai San halin wankisa bakarewa yake ba idan ma yaga dama zai iya cewa zai wankensu duka yanzu ...

Sautin muryarsa suka ji Wanda ya sake hautsina zuciyar aunty Salma wai Me kike yi ne har yanzu nuratu ?
Gani nan zuwa baba su nake son daukowa ta dauka da sauri ta bar dakin jikinta Na nuna alamun rashin gsky koda ta Mika masa kayan ma ta juya bynta yabi da kallo sannan ya girgiza Kai ya jika singlet din 'cikin ruwa, Yacigaba da abinda yake ..

Aunty Salmah tayi kmr zata fito ta sake komawa cikin dakin da sauri ganin inda mahaifinta ke facing. Wayyohhhyyy mama wlh tsoro nake ji bazan iya fita ba.
..Kai Kai Salma wlh kincika abin haushi sai kin bari babanku yagane halin da ake ciki wlh nima ki jawo min a tsamamin tsaraba daman kullun sai ya zageni cewar da hadin bakina akaje tsiyar masa da 'ya' idan baki bar rawar jikin nan ba fa zai iya ganewa wlh da kyar aunty Salma tayi karfin halin sake fitowa gabanta Na faduwa nuratu Na gabanta tana dan janta da hira tamkar wata kawata da gaske kirki damu zanzo miki dashi duk sanda zanzo gidanku, yayinda km mama ke bayanta tana ce mata to maimuna angode kigaida gida muryar aunty Salma har rawa take gurin amsawa .
ta gefta mahaifinta kadan taji Yayi gyaran murya ta tsaya cak jikinta Na wani irin kirrrrrrma nuratu ki siyo min hypo da kudin hannuki to baba inji nuratu wani irin ajiyar zuciya aunty Salma ta sauke jin abinda yace suka karasa ficewa Daga tsakar gida gabadaya har 'bakin kofar dagon zauren gidan mama takaita sannan ta juyo 'cikin gidan tana dauke plate din abincin da Aunty Salmah taci ..

Mlm salisu yaja numfashinsa yana duban mama wlh saratu yarinya nan data fita yanzu sak Salmata, gsky yanayinsu yaxo daya sosai .
Mama tace uhmmmm ,kawai dai dan kasata a ranka ne shiyasa har kaga hk shr kawai Yayi batare da ya sake cewa komai ba ita km ta dauki buta tashige bandaki tana jin jina hali irin Na mijinta..

Har 'bakin jection din gatankowa nuratu ta Kai aunty Salma suna hirar babansu suna dry har sai dataga aunty Salma tashiga motar ishodi sannan ta kama hanyar komawa gida ...


Rigingine nablah ke zaune a dakinta hannuta a saman fuskarta tana tunani duniya yayinda jikinta ke sanye da riga da zani Na atamfa English me ABC . Sosai tayi zurfi har batasan sanda bacci yayi nasarar dauketa ba . Zeenat dake zaune Kusa da ummi suna hira da kallo ta Kai idanunta kan agogon dake manne da jikin bangon parlour karfe biyar ta wuce.
bataga alamun saukowar nablah daura musu abincin dare ba.
ta Mike tsaye ahankali tana yatsina fuska ummi ta dubenta tana ya dai mamana ?
Murmushi ta sakarwa ummi bbu komai ummina zanje nakira yarinya nan ne tazo ta daura mana girkin dare naga alamun bata niyar saukowa .
ummi tayi shr can km ta nunfasha kana tace kibari laraba tazo takirata man , bari kawai naje ummi.. akwai abinda zan dauko a dakina Na sama takarasa fadar hkn tana juyawa ahankali tasoma tafiya tana girgiza jiki tana juyawa ummi tashiga addu'a acikin zuciyata Allah Yasa idanuta suGane mata abinda dade take son kasancewarsa.

Kai tsaye dakin nablah zeenat ta nufa tare da bude dakin 'cikin isa da takama ido hudu tayi da abin mamaki da ban tsoro dan karamin 'cikin jikin nablah dayayi mata dan kurcici dashi taci karo dashi .
dasssssssss gaban ya yanke yashiga faduwa har yana duka uku uku .
da hanzarinta takarasa shigowa dakin sosai tana sake bin 'cikin da wani irin kallo .
ciki take ganin a jikin yarinya nan ko me ?
Tasa hannuta ta murza idanunta ta sake budesu fesss still the same thing take Gani ..

ta kwallara wata irin gigitacciyar kara wanda ya farkar da nablah daga naunauyen baccin dayayi nasarar dauketa tayi wall da shanyayyun idanunta ta budesu tana kallon zeenat tsaye a gabanta tana zaro idanu.
da sauri tasoma kokarin Mikewa tsaye tana janyo hijab dinta domin suturta jikinta .
da hannu zeenat ta dakatar daita alamun kada ta saka ..mamaki zeenat tashiga yi da alajabi ta rike bakinta takasa cewa komai da kyar ta iya bude bakinta gurin furta kalmar ..

Nashiga uku ni muzeenat .. mezangani hk ?

inna lillahi wa inna ilaihi rajiun 'cikin tashin hankali tashiga Kiran sunan ummi da karfi .ummi ta zabura ta Mike zaninta a hannu tayo habyar step da sauri .

a frigice zeenat tace wayyyyyoo nashiga uku dama nasan za'a Rina muryata cike da in ...inna..tace nab..lah.. 'cikin shige zaki haifar min acikin gida.
lallai kuwa zan miki dukan mutuwa tare da antayaki waje.
kije can gurin wanda Yayi miki ciki.
tayi kukan kura zata damkota wuyan nablah...




MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗



AYSHA A BAGUDO



Wowwwww fans kuna Ina Ku garzayo Ga wani mashahurin kayataccen labari me dauke da darasi iri iri da abubuwa ban mamaki wanda ya tattara kan al'amuran rayuwar duniya . bakinciki farinciki kuncin rayuwa soyayya tausayi sadaukarwa ...ba kowane novel bane face GADAR ZARE ....



~NA~
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_


Kadan Daga 'cikin novel me taken suna GADAR ZARE



A firgice ya mik'e daga inda yake zaune, yana kallon sauran abokanan nasa fuska cike da hawaye idonsa yayi ja sosai
Buga kansa ya fara yi a bango yana ihu yana cewa " sun kashe min kowa bani da kowa yanzu, zaman dirshan yayi a k'asa, yana ihu yana yarfa hannunsa, zumbur ya mik'e ya nufi fridge ya d'auko robar ruwa ya bulbulawa kansa

Akan ido na suka k'one gidan mu, mahaifiya ta, mahaifi na, k'anne na duk suka mutu akan kunne na ina jiyo ihun su


***************


Cikin waye wannan a jikin, uban waye yayi miki ciki bazaki fad'a ba saina kashe ki, wayyo na shiga duk irin tarbiyyar dana baki abinda zaka saka man dashi kenan, cikin tace " wallahi Aunty ban sani, idan za'a kashe ni ban san wanda yayi min cikin nan ba, nima ganin shi kawai nayi ajiki na, tafiya tayi ta bud'e durowa ta d'auko Qur'an ta d'ora akan ta tace " na rantse da wanda raina ke hannunsa bansan wanda yayi min ciki nan ba.

Kanta tayo gadan-gadan tana nizaki rainawa hankali, ta shak'e ta idonta suka kakkafe


**************

Acikin gidan yarin yake ihu yana kuka yace " sunci Amana ta, sunyi min butulci, na yarda dasu amma sun ci amana sun had'a min *GADAR ZARE*

Amintattu nane suka yi silar zuwa na gidan yarin, sun raba ni da kowa nawa sun raba ni farin cikina,cikin matsanancin kuka yace " wallahi koda zan rasa komai Na rayuwata bazan kyale su ba.
Sun mun sharri, sun had'a man makirci


*************


Koken acikin kayana kuma, kafin ya k'ara sa maganar dubbun police sun kewaye shi da bindugogi,

Ana cikin haka wayarsa ta fara ringing, dakyar ya samu ikon d'agawa, ji yayi muryarsa ta tintsere da dariya yace " nine amininka, d'an uwanka, kaga yadda nayi wasa da hankalinka ko, na nuna maka halin 'yan Adam

Cikin rawar murya yace " mai yasa kaci amanata?
" saboda ina santa, ita rayuwa tace km mallakina ,

Wani irin mahaucin ihu ya saki tare da buga wayar da k'asa .

Uhmmmm kada Ku sake abaku labarin wannan azababen labarin GADAR ZARE !!!



🔜🔜🔜🔜🔜🔜🔜🔜🔜🔜🔜




Page 94




Tun kafin zeenat takarasa inda nablah ke tsaye jikinta Na wani irin mugun kirrrrrrma ummi tayi tsalle tashige tsakaninsu .tana cewa
lfyrki mamana kike wanna ihun hk ?

Meyye faru ne wai ?

Me tayi miki ? Ajire ummi tashiga jerowa zeenat tmbyr jikinta Na rawa itama .

'Cikin wata irin mahaukaciyar murya zeenat tace ummi ummi ciki nagani ajikin yarinya nan tana nunu 'cikin nablah da yatsanta...

Ummi ta dan juyo afrigice tana kallon jikin nablah Ciki km zeenat , wani irin ciki ana mazan kalau ?
Wlh ummi ki kalle yarinyar nan da kyau ciki ne ajikinta Na haihuwa.
ummi ta sauke naunauyen ajiyar zuciya kirjinta Na bugawa tare da janyo hannu nablah cike da fargaban abinda zai faru zuwa kan gado Amman nablah taki zama hakan Yasa ummi
'Cikin sanyi jiki ta xubawa 'cikin jikin nablah idanunta tana kallo tamkar batasan da zamansa ba.
kana tace tabbas ciki gareta ..to garin yaya hk ta faru nablah ?
Ciki nake Gani ajikinki fa da gaske .
Kirjin nablah Yayi wani irin mugun harbawa har dan 'cikinta ya juya tare da dungulewa ya cure agefe guda a cikinta.
Ta runtse idanunta hade da sanya hannuta ta dafe daidai gurin take km hawaye ya balle Daga idanunta yasoma tsiyayowa yana bin kuncinta ,ummi tayi saurin katseta ta hanyar cewa uhmmmm nablah ki natsu bbu abinda za'a yi miki.
yadda akayi kikayi ciki nake son sani .
Da km wanda Yayi miki?

wasu sabbin Hawaye ne masu zafi suka sake biyo kuncinta tun bata Kai Ga cewa komai ba zeenat tace haba ummi wace irin tmby wace wannan zaki mata .akwai dantirin dan iskan da zai yi mata ciki wanda ya wuce kb ....Ni nasan kb ne Yayi mata 'cikin Amman wlh kinyi hasara me hijabin sharri kawai ......
Ummi ta juyo da sauri tsaitin da zeenat ke tsaye tana fama aikin jijjiga jiki da nurfarfashi ai wlh uhmmmm yau Naga abinda yafi karfina.
shegiyar yarinya shiyasa kullun kike kinshe kanki 'cikin hijab ashe Kinsa ta'asar da kikeyi.

Banda kuka babu abinda nablah ke yi ta rasa yadda zata yi da rayuwarta musamman ma data Ga yadda hankalin zeenat din yake atashe sannan Ga ummi itama bata 'cikin natsuwarta tsoronta ma kar zeenat din ta sheketa takashe batare ta sake daura idanunta akan iyayenta ba . dan hk ahankali tacigaba da jero addu'oi kala kala akasan zuciyarta batare da tace uffan ba sai kuka take tana mazurai da ido domin xuwa lokacin zuciyarta gabadaya bbu abinda take so da kaunar Gani kmr ta daura idanunta akan deeni ko zai taimakamata kmr yadda yasha cewa duk sanda wani zai faru ..

'Cikin wata irin kasashiyar murya zeenat ta buga nablah wata irin razananniyar tsawa ke dan ubanki tsayuwar uwar me mekiyiwa mutane .
maza kije ki hada tsummankarinki yanzu ba sai gobe zaki bar min gidana dan wlh ko second biyu bazaki km karawa ba acikin gidan nan sheger yarinya mayya me kama kuruwar mutane gabadaya tun zuwanki gidan naji Na tsaneki ashe tantiriya ce ke me.... .

Tsawa ummi ta bugawa zeenat itama wacce tasa zeenat din qamewa guri daya tana kallon ummi a frigice km atsorace .

shiga hankalinki mamana banson iskanci banza wai ke meyyasa kwata kwata yanzu kika sauya hali .
Kika daukarwa kanki halin da banaki ba.
kibari muji wanda Yayi wa yarinya nan ciki Amman kinki zaki Hanna Allah ikonsa be ?
.kada ki manta fa gabana gabanki yayarta ta damka mana amanar yarinyar agurinmu.
Km duk abinda yasameta ahalin yanzu muke da alhakin akai ....

shikennan ummi nayi shr Amman wlh ni bazan cigaba da zama da wannan yarinyar ba sannan km bazan bari a haifamin 'cikin sh...karki sake kikarasa furta wannan kalmar Ida ban ba hk ba yau nida kaina zan miki dukan mutuwa tun kafin me alhakin hk ya bayyana .sororo zeenat tayi tana bin ummi da kallo me cike da tmbayoyi iri iri .

Ummi tace ke nabla wa yayi 'cikin jikinki?
kuka me karfi nablah ta fashe dashi muryarta na rawa tace ummi ki taimaki dan girman Allah wlh wlh bansan wanda Yayi ba .nima wayar gari kawai nayi naganni dashi batare da nasan tsinan........ shiiiiii ya isa hk ummi ta katseta tana cigaba da kallonta ...

Uhmmmm zeenat taja numfashi tana duban nablah Kin dai ci ribar soyayya tunda har Ga tsaraba nan kin samu wawiya yarinya kawai...

haka nablah ta dinga kuka tana nadamar zuwanta aiki tare da danasani biyyewa sharrin zuciya datayi da yanzu tana 'can cikin danginta km gatanta .

sanin da ummi tayi idan ba'a bar zance hk ba. wani abu zai iya samunta km tasan halin deeni babu hakuri ballanantana Daga kafa.
daga karshe allura ta tono garma..dan haka tace kukan ya isa hk kin nablah kwantar da hankali Kin dai tabbatar da baki San wanda Yayi 'cikin ba ko ?

Nablah tayi saurin girgizawa ummi kanta .

Ok jirani Ina zuwa yanzu
Ummi ta Mike a zabure kmr gaske takamo Hannun Zeenart ta jata zuwa d'akinta, a bakin gado Ummi ta zaunar da Zeenart.
Itama ta zauna a gefen ta, suna fuskantar juna .
Ummi tayi,shr tana kallon zeenat da nazarinta sannan km ta saki murmushi wanda Yasa zeenat cewa ya hk ummi Muna 'cikin tashin hankali ke km kina murmushi ?
Dole nayi murmushi zeenat .
Sannan wannan murmushin Nawa bana komai bane Na murna ne zeenat ....

Zeenat Ga dama tasame mu ..dama ummi ?
Wani irin dama ne wannan ummi zeenat ta fadi hk tana bin Ummi da
Wani irin kallon.
Ita Ummi kallonta take Zeenart, cikin k'osawa tace " Umm..... Hannu Ummi ta d'aga mata, fuskarta d'auke da murmushi ta dafa kafafarta ta tace " 'yata ga dama ta samu, kin san duk abinda kake addu'a to Allah zai kawo maka mafita, cikin rashin fahimta Zeenart ta kalli Ummi tace " Kamar yaya ummi nifa ban gane nufiki ba?


Kallon ta Ummi tayi tace " cikin jikin Nablah mana, cikin k'osawa Zeenart tace " Ummi nifa ban fahimceki ba,wlh gyaran murya Ummi tayi sosai sannan taci gaba " ki karb'i cikin jikin Nablah ki gayawa duniya naki n.......


Zunbur Zeenart ta mik'e " tsaye jikinta Na rawa muryarta cike da in.. inna...tace Allah ya kiyaye na rik'i d'an shege har na dangan tashi da jini na ne .
, d'an dabamusan usulin sa ba, shi zan karb'a ya rink'a kwana asaman k'irjina, kuma gado d'aya, duk abinda Zeenart keyi Ummi na zaune ta zuba mata ido....


Ummi ta sake kamo hannun Zeenart ta zaunar tace " wannan ita kad'ai ce mafita, kinga dai dangin mahaifin deeni wanda kema naki ne sun sako mu gaba daga ni harke, kuma lokacin da suka baki yana gaf da cika daman big Dady Ya tsawatar da yanzu .....


"Wallahi Ummi koma mai zai faru sai dai ya faru, da dai na rik'e d'an shege, ai gwara muje gidan marayu mu d'auko,zeeta ta katse ummi . murmushi Ummi tayi tace " shi na gidan marayun kina da tabbacin tsatsun sa?


"Ko kina da yak'ini akan

1 Comments On AUREN SIRRI
avatar
adam-ado

9 months ago

Reply

Very interested book

Please Login or Register in order to submit comment