Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaima kasan bazan iya cewa banason shi ba, ko dan ummi dan haka kace masa kawai na amince .


Fk ya saki murmushi murna yayi hamdala a zuciyarsa hade da godiyar cin nasara yace Shikenan ni zan wuce sai kin jimu .

A ranar ummi ta nemi ciwon Zeenat ,tarasa duk tana zargin ciwan nata bazai wuce akan DEENi bane ,da daddare har nafila Zeenat tayi dan Mika godiyar ga Allah. ummi tayi murmushi tace yau km ibadar ce ta motsa har da sallar dare ?

Zeenat tayi mata banza kmr bataji ba tacigaba da sallarta, Ummi ta sake cewa Allah yasa a dore in km nasamun NASURULDEENI ne nasan daga yau Shikenan .

Abinda ke sake bawa Zeenat mamaki bai wuce Ganin yadda kullum yaya DEENi ke nuna ko in kula akanta ba gabadaya ma Gani take kmr baisan da zamanta ba .
ko magana ta fatar baki bata hadu su, idan ma yana guri kennan ita kanta batason zama in da yake yanzu ,Allah Allah take tabar wanje dan juriyarta takusan karewa .


Fk bai samu ganin deeni ba, sakamakon wani aiki daya taso masa ,Amman Yace masa yabari zuwa weekend ,ya same shi a gida .sai da fk yakirasa a waya ya tabbatar masa da yana gida sannan yazo .
zaune suke cikin parlour deeni byn sun gaisa fk yayi masa bayani duk yadda suka yi da Zeenat a boye DEENi ya sauke ajiyar zuciya ,sannan Yace ta taimaki kanta da kanta , kennan , fk yabishi da wani irin kallo sannan yace kai fa dan rainin wayo ne abinda yakamata kace kennan, deeni Yace nifa bawai na matsu dole sai ta amince da aurena bane .
asalima ita din ba irin kalar type dina bace zan dai aureta ne kawai ,a rashi samun choice dina fk ya saki baki yana kallon deeni ,Yace Amman friend kasan itama tana kyawunta daidaina , sai da ya dauki lokacin sannan yace ni nace maka dan kyawunta zan aureta?
Ai bata da kyawun da zai rudeni ,km wlh har ga Allah da bata amince ba na hakura , har zuwa sanda zansamu type dina.

MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗



AYSHA A BAGUDO



Page 21-22



Wani irin kallon mamaki fk yake masa , ,gabadaya ya zamo tamkar mutun mutimi a zaune a gurin ,

Yarasa meke damun brain din DEENi , mutun Sai girman kan tsiya da nuna isa " wai shi DEENi wani irin bahagon mutun ne ?
Shi sam bbu ruwan shi da fadar duk magana da tazo bakinsa .

In a low voice fk yace yanzu duk wahalar danayi akan yarinyar nan yatashi a banza kennan?

A'a bakayi a banza ba tunda gashi "zan aureta gaskiya ce dai na gaya maka,dan kasan ita din ba ra'ayina bace .
Amman narasa dalilin da yasa zuciyata ke muradin kasancewa tare daita " fk ya sake dubanshi sannan yace dan rainin wayo kawai kar mai dani kmr wanda bai san komai ba mana .
,tunda har zuciyarka ta iya amincewa daita, har kaji zaka iya aurenta definitely kana sonta" ko yaya ne" ,.
deeni yaja tsaki hade da furzar da iska ta bakinsa" matsala dakai kennan rashin saurin fahimta fk yace idan son da kake mata ne ,na fahimta ,Amman kace wai kai baka sonta km kake kokarin aurenta , wannan ne fa bazan taba fahimta ba , DEENI ya sake first da huci may zafi ranshi tasoma baci muryasa a sarke" yace da alamun kana son musamu matsala dakai fa" muddin baka daina cewa Ina son yarinyar nan ba .

Idan km kafin son haka ya daga kafadarsa alamun Shikenan , parlour ya dauki shr na wani "dan lokaci yayinda deeni ya jingina bayansa da kujera da yake zaune, hade da runtse idanunshi ya dan jin daci maganar fk 'ta yaya ma " zai nace akan yana son yarinyar byn shi yasan aure kawai yake da bukatar yi bawata ,aba soyayya ba ...
maganar fk ce ta daki dodon kunnenshi" to yanzu meyye solution tunda yarinya ta rigada ta amince ?


Ahankali ya bude rikitattun idanunshi ya sauke su ,akan fuskar fk sannan yayi magana cikin sanyi tamkar wanda aka takura masa. Yace karkadamu zan samu yaya mahamud ,Ai kagama may wuyar "ya maida idanunshi ya sake lumshe su tamkar dai yadda yayi dazu .
girgiza kai kawai fk yayi uhmm shi wannan bazai taba canzawa zai ba .
halinsa, na nan kmr dai yadda yasan shi" haka km yataso " shi komai baya so matsawar ba ra'ayin sa bane" duk yayi magana ne akasan ransa,,.
Ganin ya bawa banza ajiyarsa yasa shima ya mike yayi masa sallama .


Daga gurin DEENi kai tsaye fk part dinsu shemah yayi yaja ya tsaya byn ya tura ayi masa kiranta fk tafito sanye da doguwar rigar material puppy colour mai shegen kyau hade yane kanta da karamin mayafe baki ahankali take isowa gareshi duk step daya Sai kirjinta ya motsa tun fitowarta ya zubawa kirjinta ido kyam yana kallon yadda kirjinta ke motsawa lumshe idanunsa shi yayi na wani lokacin sannan ya sake budesu ahankali mutuwar tsaye a gurin har takaraso inda yake ta gaisheshi cikin sanyi jiki bai dauke idanunshi akanta ba yacigaba da da binta mayataccen kallo da sallamarta iso inda yake ta gaisheshi ya amsa yana sake bin koina na jikinta da kallo cikin sanyi tace yaya faruk Gani Yace Ai naganki ,daman nazo ne na fayace miki abinda na dade Ina boyewa akanki ,nan dai yasanar mata koma , tunda yasoma magana tayi shr kawai hade da sunkuyar da kanta badan tana jin dadin abinda yake kokarin fahimtar dai ba ahankali ta dago ta zuba masa idanunta Sai data tabbatar ya gama fadar abinda yakawoshi sannan tace ,dan Allah yaya kayi hakuri wlh akwai wanda zuciyata ta dade da kamuwa da soyayyarsa , Amman kayi hakuri idan maganata ta bata maka rai ,yace Ina Gaza bata min rai Ai iya gaskiyar ki kika fada Sai dai ki sani zuciyata bazata iya hakura dake ba Amman zan baki lokaci yi tunani akai tace nifa bawani tunanin dazanyi akai ka dai yi hakuri ka nemi wata ,ta juya ta wuce tabar sa nan tsaye ,da mamaki yabi bayanta da kallo ya dauki lokacin tsaye a gurin batare yasan abinda zaiyi ba , Ganin tsayuwa nasa bata da wani amfani yasa yasoma kokarin daga kafafunta ahankali tafe yake yana saka da warwara da tunanin malomasarsa a gurinsa ,a fusace shemah tashiga part dinsu tana zuba tsaki da zage zage har mmnta ta tambayeta abinda yasameta tace matabakomai.

Byn kwana biyu

Da misalin karfe takwas na dare fk ya km samu shemah da zance shi fa ba zai iya wani hakura daita ba kawai tayi hakuri ta amincewa da bukatar domin shi yana matukar son ta km aurenta yake son yi ,tace dan Allah yaya kayi hakuri wlh da bbu wanda nake so ne ,zan iya soka dan kaima baka rasa komai da zankika ba , kadai yi hakuri kawai .
al'amarin dayayi matukar dagawa fk hankali kennan ,yayi shr kawai yana kallon yanayinta tare da nazarin kalamanta masu kokarin tarwatsa masa zuciyar rasa yadda zanyi daita yayi can dabara tazo masa,ya tsareta da idanunshi Yace ke banso iskanci da rainin hankali fa ni zaki cewa kina da wanda zaki kike so byn Banga uban da kike saurara ba ,lafazinsa yayi mugun bata mata rai dan haka a ranta abace tace to dole ne Sai na aurenka kaje Kanemi wata mana ko ana soyayya dole ? ta juya a fusace zata bar guri ,ya fizgota hannuta , gabadayanta ta fado jikinsa , idanun ta zaro a tsorace, ,take taji wani irin faduwar gaba , .
Hannuwansa dukka yasa rungumeta tsam ajikinsa yana sauke ajiyar zuciya daidai kunneta ya kai bakinsa Yace maimaita abinda kikace Ina jinki cikin tsiwa tace wannan wani irin iskanci dazaka wani rungume mutun ? Ok nine ma nake miki iskanci ?
Uhmmmm fa shemah karkibari muyi haka dake zaki amince ta girma da arziki ne ko km na jawo soyayyata ta karfin tsiya ,.batare da na wahalar da kaina ba muryarta na rawa tace anki a amince da soyayyarka .
ko ana so dole ne ?
, dan Allah ni kasake ni ,ya zuba mata manyan idanunshi kawai ,yasoma yawo da hannushi a jikinta gabadaya jikinta ya dauki kirma abinda bai taba faruwa daita ba kennan tunda take arayuwar ta ,wai namiji ya rabi jikinta har takaita ga runguma ,dan takaici ma batasan sanda , kwalla ta cicciko a idanunta ba , hawaye yaga yana silalowa daga idanunta ahankali ya sauke ajiyar zuciya, ya dan sausauta rungumar da yayi mata yasa yatsansa ya dangwalo hawayen dake bin fuskarta yana kallo Yace duk wannan kukan akan nace Ina sonki ne kike zubda hawayen ki?
,tayi shr taki cewa komai dan haushi ji tayi kmr ta daura hannuta akanta ta kurma ihu , ahankali ya sake maida ita jikinsa ya rungumeta yana shinshina wuyanta daidai nan Sai ga big dady dake dawo daga masallaci , a tsorace yake binsu da kallo cike da mamaki da alajabi abinda yagani , meke shirin faruwa km yau acikin zuri'arsu ,fk yacigaba manneta da jikinsa yana rarrashi ta amincewa aurensa , dagowar nan da zai lyi karaf idanunsa suka sauka kan big dady dake tsaye duk da duhu ne hakan bai hana gareshi ba gabansa yaji yayi muguwar faduwa jikinsa ya dauki kirma duk da ya tsorata Amman yaji dadi Ganin da big dady yayi musu ,yasan hakan zai sa a aura masa shemah batare da bata lokaci ba tsabar frigice yasa yakasa rabata da jikinsa gabadaya jikinsu rawa yake shemah da batasan wainar da'ake tuyawa ba sake lafewa tayi ajikinsa saboda irin rungumar dayayi mata ba wacce zata iya kwacewa bace har big dady ya wuce su a gurin shemah batasa big dady yagansu , ahankali fk yasoma rabata da jikinsa har zuwa yanzu hawaye bai daina bin fuskarta ba hannuta yakamo yasoma tafiya ita kum tana biye dashi bbu wanda ya iya cewa dan'uwansa komai har yakawo part dinsu yaja ya tsaya ahankali Yace shemah kiyi hakuri dan Allah kibar kuka ba nufi na kuraki ba Ina matukar kaunarki bansan lokacin dana fara sonki ba Amman zan baki lokacin kiyi tunani akai ,zan dawo zuwa jibi yana gama fadar haka ya juya da kyar yake iya daga kafafunsa tsabar frigice da nauyin da suka masa zuciyarsa tamkar zata buga , dan fargaba haduwarsu da big dady shi yasan ba makuwa tunda har big dady yagansu aure kmr anyi an gama Amman kunya fa ,har ya iso part dinsu wanda kusan nan samari suke zaune wayanda basuyi aure ,


Itama tana shiga dakisu ta wuce kai tsaye tana kuka , mamanta dake zaune a parlour tace ke lafiyarki Amman ko juyo batayi ba fadawa tayi kan gado tana risgar kuka to meye yaya faruk yake nufi daya sonta alhalin ita DEENi take mutuwar so ..... Dan haka bata taba aurensa ba ,tunawa datayi ba'a musu auren dole a family dinsu sai sun amince da juna yasa taji hankalinta ya kwanta Amman gabadaya jikinta yayi bala'in sanyi haka ta wuni a daki batare data sake fita ko parlour ba ,fk bai dawo ba kmr yadda Yace mata kusan sati tsakani shiyasa tayi tunanin ko yayi wa kansa fada ne ya hakura daita dan haka ta sake abinta kwasam Sai gashi a wani daren lahadi byn tagaishi a dage ,yayi murmushi yace yazo ne akan maganar su ,a fusace tace wata magana kennan i tough mun gama da wannan zance tunda nace ban sonka , Yace haka kika ce ,tace eh ko dole soyyaya dakai ,Yace uhmm Amman dolenki ki aureni ya wuce batare da damuwa ,



DEENi yasamu yaya mahamud yayi masa bayanin shi kuma ya samu big dady da zance tsohon yaji dadi Sosai jin sun hada kansu yace Shikenan bbu damu zai tuntubi yarinyan tukun asan abinyi .



Nan dai aka saka ranar aure tare da yanka sadaki yaya mahamud ne yayi komai ko sisin Kobo bata fita daga aljihun ogo deeni ba ko mahaifin zeenat yayi murna sosai da jin DEENi ne zai aure diyarsa

Anyaka sadaki da dukiyar aure naira duba dari biyar wanda duk a aljihun yaya mahamud suka fita .


Da kyar big dady yashawo kan Ummi dan tuburewa tayi ita sam bata yarda da wannan aure ba big dady yace Ai tunda dai yara sun hada kansu km suna juna Ai Ina Gani magana takare fatanmu Allah ya zaunar dasu lfy .

Lokacin da aka sanar da DEENi ansa ranar wata biyar deeni Yace wa yaya mahamud lokacin nan bai yi yawa ba kuwa ?

Dan akwai aiki da zai kaini akwaibon Ina Ganin zaifi kyau a takaita lokacin koma ba dan haka anawa raayin nafi son ayi nan da wata uku yaya mahamud yace Shikenan kabari dai zan samu Ummi da maganar .


Zaune take a cikin extra room dinsu wanda kusan yanzu can tafi zama tunda aka sa musu rana da yaya DEENi ta zabga uban tagumi tana mamakin hali irin na yaya DEENi yau kusan wata biyu Keenan dasamusu rana Amman ko sau daya bai taba kiranta da sunan zance ba haka nan ko cikin part din Ummi yashigo bata ishe shi kallo ba takan ji tsoro da frigice sun shigeta a duk sanda taga yaya DEENi nuna rashin damuwarsa akanta ,a kasan ranta tace, anya kuwa banyi kuskure da wautaba wajen saurin amincewa aurensa ba domin fa zuwa yanzu tasoma sarewa anya kuwa yaya DEENi yana sonta ?
kullum miskilancinsa sake gaba yake har zuwa yanzu dabatason cikakken matsayin ta a gurinsa ba ,son auren yasoma fice mata arai domin ita kadai tasan fargaban da take cikin zuciyarta ga ,gorin da Ummi kebinta dashi kullun garin Allah ya waye , dan haka ta yanke hukunci samun yaya faruk dan ta inda aka hau tanan ake sauka .ta shirya taje har part dinsu tace daman tazo ne akan maganar mu da yaya DEENi idan fa abin nan bazai yiwu ba gara tun yanzu abarshi .

Fk ya gyara tsayuwa sannan yace wani abu ne ya faru ? Tace to yaya faruk a haka ne zamu fahimci juna in San abinda yake so shima yasan wanda banaso shi fa aure ba banza bane kmr yadda ya dauki komai tacigaba bai taba kirana ba km ko gida yashigo ban ishe shi kallo ba shi bashi da lokacin kowa sai na kansa fk yace kiyi hakuri bawai zangoyi bayansa ba aikine yayimasa yawa kiyi nasa uziri Amman kina ranshi zeenat ta tabe baki dan tasan karya ne yace wai tana ran yaya DEENi Ai abinda kake son baka sakaci dashi fk yacigaba komai yakusan zuwa karshe da zarar kin zama a gidansa nasan dole ya baki dukkan lokacin sa ,zeenat tayi shr ne kawai ba wai dan maganar tashigeta ba , fk yace tayi hakuri zai masa magana da sauri ,zeenat ta dago tace dan Allah yaya kar kace ni nayi maka maganar ya sake dubanta sosai yaga duk ta wani frigice yace karki damu ni nasan abinda zanyi .


Fk yakira deeni a waya Amman ba'a daga ba

Da misalin karfe goma na dare fk ya amsa kiran DEENi tare da yin sallama byn sun gaisa yace friend dazo inata kira baka daga ba DEENi ya runtse ritattun idanunshi tamkar na may jin bacci sannan yace wlh aiki ne yasha kaina lafiya dai ko ya fadi cikin kasala dan duk a gajiye yake fk yace lfy dama akan maganar yarinyar nan ne yakama mushirya muje zance gurinta , ,anhakali DEENi ya bude idanunshi jin abinda fk yace muryasa a sarke yace wacce yarinyar km?

Fk yace sai karinka yin kmr baka san da zance ba ,byn nasan tana ranka DEENi yace dan malam karkadameni go to the point dan bangane wacce yarinyar kake nufi ba fk yace Ai dole ka manta da ko wacce yarinya ce tunda kaga kasameta cikin kwanciyar hankali km Ummi ta amince ,tsaki yaja kana yace wai zeenat kake nufi ?
Yasake jan wani tsakin mtssss wani irin hira kum kmr muna kauye byn angama magana sai jiran lokacin fk yace kai mugun dan iska ne Ai duk da haka yakamata muje dan ita yarinyar tasan raayinka kai ma haka ku samu fahimtar juna DEENi ya katse shi da itace Keenan ta aiko ka fk yace ko daya ni dai naga dacewar haka DEENi yace to baza'aje ba ... Kar Allah yasa mu fahimci juna, ita tun tasowarta, bata san abinda nake so da wanda ba,fk yace idan ita tasan abinda kake so da wanda baka so kai kasan nata ?

DEENi ya sake jan tsaki hade da kamo lip's dinshi na kasa yana dan ciccizawa sannan ahankali yace to sarkin yakinta ni ba haka taarina da raayina yake ba Ina tunanin in har zanje zance gurin budurwar ,zanje ne dan tallar kaina in samu gindin zama to ni narigada na samu shigar ,bbu dalilin da zai sa na takurawa kaina me kadauki ni ,nafa san irin son da yarinyar nan take min ,kawai dai ni banda lokacin wannan shirme dakace km nasan ita ta aiko ka fitowa ne kawai bazakayi kafada ba .


Fk yaja tsaki shima yace kai ,dan Allah wani irin bahagon mutun ne?

To wlh ka canza wannan budadden halin naka, to ko waya ce ka tsiya mata ,DEENi yace shima din baza'a tsiya ba ,duk abinda zai faru ya faru ciki har da fasa aurena ,fk yace kai fa kafiyye kafiya ,da maida karamar magana tazama babba ,. yace sake cewa yanzu dai kayi hakuri dan girman Allah ka Sai mata ko karamar waya ce.

DEENi yace kasan Allah ko game bazan Sai mata ba , ballanantana waya , tunda har taiya zuwa ta sameka da maganar bana kiranta fk yace kadaina cewa tasameni ni kawai Gani nayi ya dace muje DEENi ya tabe baki tamkar fk din na ganinsa Shikenan kai ka sani ni km kar ka sake damuna da maganar wata yarinya ya kashe wayarsa batare da ya tsaya jin abinda fk zai ce ba .

Wasa wasa lokacin bikin ya dinga karatowa da kwanaki ya wattani har zuwa yanzu dayayi sauran wata cif cif ayi daurin aure to Ganin kurewar lokaci yasa DEENi yasamu Ummi da maganar shifa baya son zamansa cikin estate din taje Ummi tayi kicin kicin da ranta sannan ta dago tana dubansa tace bangane abinda kake nufi ?
Sai da ya sake maimaita mata tukun Ummi tace sam ita bata yarda ba salon yaje yana dinga cin amanar Yar marainiyar Allah ga babbin gurin bid dady yasa an Gina musu shida sauran enuwansa shine kai dan iyayi zaka ce bazaka zauna ba ,to wlh kaji na rantse anan zaku zauna Sai naga yana yin zaman naku cikin yin kasa da murya yace Shikenan first lov na hakura duk abinda kika ce shi za'a yi tace da dai yafiye ma a yi mutun Sai girman tsiya da iyayi yace to kiyi hakuri .

Zeenat dake sauransu ta lumshe idanunta jin Ummi bata amince ba dan tana matukar jin tsoro zaman daga ita Sai shi ahankali cikin sanyi jiki ya mike idanunshi suka sauka akan inda zeenat ke kwance suka hada ido da sauri ta gaidashi hade da dauke idanunta ,bai sake kallonta ba bare ya amsa gaisuwar ta .


Shirye shiryen biki ya tashi gadan gadan enmata duka a tare suke shirinsu dan yanzu zeenat ta saki da shemah sun koma kmr da ganin da tayi wanda ma take haukar akansa bai san da zamanta ba wata safiya suka shirya zuwa siyayar su irinta amare mutun biyu ne abayanta mota Maryam da shemah yayinda zeenat ke gaba kai tsaye kasuwar Lagos suka nufa sukace derive yayi parking a idimota su kum suka shiga cikin market din


Derive yaja ya tsaya suna fitowa da yaya kamil suka soma cin karo tun shigowar motar dayaga hango zeenat zaune ya zubawa motar ido har sanda ta fito ahankali suka jiro suna hira Amman banda zeenat dataji gabanta ya yanke ya fadi dan tun lokacin da aka mata rana ,rabonta dashi dai dai sun kusan geftashi yakira sunnanta zeenat..... tacigaba da tafiyarta dan batason abinda zai km hada ta dashi cikin sassarfa ya biyo bayanta yasha gabanta cak taja ta tsaya suna kallon junansu,yayinda su Maryam suka cigaba da tafiyarsu suna tsaye batare da dukkansu suyi yunkurin yin magana ba kamil ya gyara tsayuwa ya tura hannuwansa duka cikin aljihun wandonsa ya kafeta da idanunshi ta sunkuyar da kanta kasa sannan tace lfy yaya ka tsayar dani muryasa a dashi yace lfyr ce takowa haka yanzu zeenat kin kyauta kennan ki zabi wani kibarni byn duk lokacin dana dauka Ina fama da soyayyarki ,a she kinsa bakya sona kibarni inata faman hauka akanki tace Allah yaya ba haka bane Amman kayi hakuri dan Allah, ya sake gyara tsayursa , yayinda idanunshi ke kanta har yanzu yace iya hakuri ne kawai zai wadatar da zuciyar da tayi sama shekara biyu tana mata da miki so.... yace Shikenan bbu komai Nagode Kwarai da abinda kika saka min tace ka dauka haka Allah yaso ni din ba matar ka bace yayi murmushin karfin hali sannan yace haka ne fa al'amarin ubgj Amman agaskiya DEENi ya cuceni ,tace kabar cewa ,tayi ta dago suna kallon juna fuskarta dauke da murmushi ta bude baki kennan Sai ga motar DEENI ta kuno kai cikin compound din km shi suke facin Ai take maganar ta ta tsaya sakamakon DEENi data Gani zaune a mota yana kallonsu duk kasancewar akwai dan duhun magariba hakan ba zai sa takasa gane bscin ransa ba , gabanta ya yanke ya fadi , ,shima kamil din shr yayi bai sake yin magana va kusan minti goma yayi yana kallonsu koda bata ga fuskasa sosai ba tasan a daure take ,har sanda DEENi ya fito yayi matarsa key idanunshi na kansu ,cikin tsoro da frigice zeenat tace ni zanshiga ciki ,kamil yace Shikenan Allah yabaki zaman lfy ta gefensu yazo yazo ya gifta hade da jan tsaki sannan ya wuce . a filli ta furta wayo Allahna nashi uku kamil ya sake yin murmushi dole sannan yace da'aka me,da kika shiga uku, nifa Banga abinda ya birgeki a DEENi ba,har da kika iya zabarsa , kalli fa yadda jikinki ke rawa saboda Allah tamkar kinga wani malaika tsaki taja hade da zabga masa harara dan Allah kabarni naji da damuwa Ai duk kai kaja min matsala Ina zaman zamana da yanzu Ina cikin gida💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗



AYSHA A BAGUDO



Page 21-22



Wani irin kallon mamaki fk yake masa , ,gabadaya ya zamo tamkar mutun mutumi ,a zaune a gurin ,

Yarasa meke damun brain din DEENi , mutun Sai girman kan tsiya da nuna isa ,fk ya dinga masa kallon bahagon mutun wanda
Shi sam bbu ruwan shi da fadar duk magana da tazo bakinsa .

In a low voice fk yace yanzu duk wahalar danayi akan yarinyar nan yatashi a

1 Comments On AUREN SIRRI
avatar
adam-ado

9 months ago

Reply

Very interested book

Please Login or Register in order to submit comment