Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsabar tashin hankalin daya tsinci kanshi ciki.
gabadaya komai na duniya ya rigada ya tsaya masa cak , sai km taimakon Allah yake nema da zuba ido yaga ta inda sauki zai zo masa.
"murya a marairaice yakewa big dady bayanin abinda ya faru atsakaninsa da nablah byn komawarta .
da halin dayake ciki da zeenat .
" big dady ya numfasa yana sauke ajiyar zuciya sannan yace shikenan Bari na tashi mutafi yanzu gurin mahaifin nata daman naso abari mu hadu da sauran kawun nan ka domin muhada karfi da karfi muje , sbd rashin kyautatawar da akayiwa mahaifin yarinyar.
Ita kuwa zeenat kabarni daita Nata me sauki ne Inji Cewar Big dady. wanda oready yarigada yagama mikewa tsaye suka fito tare da deeni yace su biya su dauki mahaifin fk dana zeenat da ita ummin karankata ..
Hkn ce kuwa takasance big dady da kanshi ya sanar mata data shirya maza maza daita za'a je gidansu nablah.

Ummi tace zeenat ma ta taho suje tare motor ummi daban ita da yar gaban goshinta Direbanta adekule Najansu.
yayinda deeni da big dady da yaran duka uku suna cikin mota daya , mahaifin zeenat dana fk cikin mota daya
sai motocin escort dinsa dake biye dasu agaba da baya .
Deeni zaune akan kujera me zaman bazan agaban motarsa renge Rober ya dan kara karfin AC motor sbd wani irin gumin dake tsaftsafo masa ta koina ajinkisa.
anan rungume ajikinsa. ciro wayarsa yayi agaban aljihun gaban rigarsa yashiga dieling number sule .

Kira daya Sule direbansa ya dauka yana ambaton sunan boss cike da girmamawa .
deeni yace sule kuna daidai ina yanzu?

Bangaren sule kuwa cewa yayi muna daidai underbrige din oshodi express.
OK idan kun kai daidai ladipo kasan yadda Zaka Yi kujerani agurin ganinan zuwa yanzu OK boss .
deeni ya katse kiran Tare da ajiye wayar kusa da giyar motor .
gabadaya hankalinsa yayi mugu mugun tashi yarasa yadda zai Yi da rayuwarsa da yadda zai fuskancin mahaifin nablah da zance dayen aikin da yayiwa diyarsa..
Ya juyowa ahankali yana sauke naunaiyen ajiyar zuciya tare da bawa direbansa umarnin ya taka Motar sosai ......
big dady yace dan me zai taka mota sosai kmr ya dibo dabbobi.
sannan ya maida hankalinsa kan direba yace yayi tuki ahankali ..


nablah dake zaune a byn mota taga sule direba yana rage gudun motar da yake hade da gangarawa gefen titi ya Tsaya yana jujjuya kai alamun motor ta samu Matsala, ta dan gyara zamanta kana tace lfy baba sule naga ka tsaya?
Wani abu zan dan duba a motar yabata amsa da hkn .
taja bakinta ta tsuke batare da ta sake cewa dashi komai ba.
dan ita kanta hankalinta a matukar tashe yake da wannan ranar dazatakoma gidansu dauke da wani cikin wata shida da wani abu ...


Lokacin da su deeni suka kusan kawowa ladipo oshodi ya sake kiran sule direbansa yace yashirya gashi nan karasowa .

Suna wuce ladipo oshodi deeni ya sake kira sule yace ya biyosu abaya OK boss ai naga wucewar motocinku yanzu .
nablah tayi shr tarasa gane kan inda zance sule direba ya nufa kawai ta kawar da kanta gefen titi da kawar da zance dan gabadaya burinta bai wuce taganta acikin gidansu km gaban mamanta da babanta da yan'uwanta zaune ba.. Sunkai daidai iyana paja ta gane kmr tare suke da motocin deeni ranta abace ta juya bayanta aiko taga Motar escort dinsa abayanta tsaki taja kawai tare da hada uban tagumi...


Cikin minti talatin motatocin su deeni suka shigo unguwarsu nablah yayinda Jama'ar dake zaune akan layin unguwar kowa ya maida hankalinsa akan hadaddun motacin dake kokarin shigowa cikin geto area din tasu da kokarin son yin parking a akofar gidan mlm salisu me wanki hula .......

Cikin ikon Allah suka ci sa'ar samun mlm salisu me wanki hula akofar agidansa. Wanda yake ta faman kokarin yin alwala ba dan lokacin sallah yayi ba sai dan yin alwala akoda yaushe ya zamemai jiki.. .


Ahankali su deeni da Big Dady tare da sauran jama'a da suka zo tare ke kokarin fitowa daga cikin motor daya byn har suka gama fitowa gabadaya har nablah wace ta dan yi jimmmmmm kafin ta sanyo zara zaran yatsun kafafunta zuwa waje. Kana ta fito da jikinta.
aiko junior nayin arba daita ya nufi gurin yana murmushi sauran yan'uwansa ma suka marasa baya.
" yayinda mlm Salisu wanda ya kammala da alwalarsa dayake ya dago kanshi ahankali da zumar mikewa tsaye idanunshi karaf suka sauka akan deeni dake tsaye tare da wasu mutane wayanda bai san ko su waye ba .
Gefe daya km diyarsa ce nablah tsaye jikin mota yake kallonta zagaye da wasu kyawawan yara masu mugu mugun kyau da daukar hankali sak masu tsananin kama da deeni. Idanun mlm salisu kyam akanta yana kallonta a matukar tsoroce domin idan ba gitso idanunshi ke masa ba diyarsa yake kallo tsaye km kmr ciki ne ajikinta....... Ga km yara
ahankali mlm salisu yake kallon deeni da nablah da sauran mutanen dake tsaye cirko cirko da ya'yan dake jingine jikin nablah suna manne daita Ya sake kai dubansa ga Anan...... take yaji wata irin mummunar muguwar faduwar gaba from no where .........
tayi masa ruf da dubu aka .
Hankalinsa yayi maseefa maseefar tashi .
tunani kawai yake to meye yahaddin nasuruldeeni da nablah guri daya .
Dayaga ta fito daga cikin jerin motocin da suka fito.
shi dai asaninsa da yayi deeni gurinsa yazo ya nemi auren nablah batare daya tafi daita ba .
to ina nablah taje tasamo ciki km har da ya'ya har guda uku.... Wani irin tsoro ne me cike da tsansar frigici da fargaba yayi mugu mugun shigarshi ya dinga jin Wani Abu na taso masa yana hawa kanshi.
take yashiga addua acikin zuciyarsa hade da Kane abinda yaji yana tasomasa gabadaya mahaifin nablah ya kasa motsi daga inda yake itama nablah wacce sai yanzu hankalinta ya kai ga mahafinta gabanta ya shiga faduwa at the same time zuciyarta tashiga tsinkewa da harbawa.
deeni yayi saurin karasawa inda mlm salisu yake tsaye ya mika masa hannu.
jikin mlm salisu a matukar sanyaye ya bashi hannu suka gaisa sai dai har lokacin idanunshi nakan diyarsa nablah yana kallonta zuciyarsa cike da frigici.
murya deeni a kasalance yace baba gurinka muka tare da dagina.
Mlm salisu yayi saurin kawar da tarin damuwarsa .
sannan km take zuciyarsa tashiga Yi masa wasi wasi akan batare suke da nablah da nablah.
da dan hanzarinsa ya shiga cikin gida sannan ya dawo yayi musu iso ciki.

Byn sun shiga gidan aka gaisa zuciyar kowa cike da fargaba ..
mahaifin nablah ya boye tarin fargabansa hade da nuna matukar murnarsa da zuwan deeni big dady ya numfasa yace to deeni gamu a gaban mahaifin yarinya sai kayi masa bayani komai game da abinda yakawo mu Dan waka abakin meshi tafi me...?
Sauran mutane dake zaune agurin suka amsa da tafi dadi..

Jikin deeni yayi mugu mugun sanyi ya sake sunkuyar da kanshi kasa sosai wanda daman tun sanda yashigo parlour 'n kanshi sunkuye yake kana muryarsa a sanyaye a raunane yasoma bayani tundaga kan farkon aurensa da zeenat da labarin zubar masa da ciki da zeenat take Yi masa har zuwa kan yadda akayi aurensa da nablah da yadda asiri ya tono kowa a daginsa yasani har zuwa yau din nan dayake bashi labari.
Hankalin mahaifin nablah ya tashin kwarai da gaske zuciyarsa ta dugunzuma guri daya ta yunkuro abinka ga me zuciya..
ya Mike tsaye jikinsa na tsananta rawa tare da cewa Zance banza zance wofi.
"Zance banza inji mutane banza.
Oh ! byn kungama cutar min da yar kun mata ciki ga ya'ya har uku ta haifa sannan ga wani ciki.
shine kuka kwasota kuzo min daita.

to kuzo in muku me?

AI banida wani amfani yanzu ko ina dashi amfanina ya rigada yakare.
mlm Salisu ya meda idanunshi kyam akan deeni tunda da ina da amfani agurinka ko km kasan darajata da yadda kaxo ka aureta agurina kamata yayi ka dauketa ahannuna ba wai kaje ka rike min ita agidanka ba .
kayi mata ciki agidanka ta haihu ka sake dirka mata wani cikin ba.
Sam wannan ba adalci ne bane km wallahi azim nasuru baka min adalci ba yanzu yartawa ce tazama hk kmr a gidan magajiya nasamota ?
Ranshi a bace ya dinga zazzaga masa tujara iri iri wallahi nasuru kaci amanata.
" Domin bansaka ba ban San asalinka ba na amince maka har nabaka auren diyata.
a fusace yashiga nuna deeni hannushi yana nuna masa kofar fita ni maza maza ka tashi anan kabar min gidana bana ko son ganinka acikin idanuna na daukeka mutumin arziki mutumin kirki ban tsaya tmbyr ko kai waye ba.
na dauki yarta nabaka wacce ma acikin yayan nawa itace mafi soyuwa araina shine zaka min irin wannan sakayyar?
Daman da niyyar dakazo auren nablah Kennan dan ta haifa maka ya'ya?
Amman babu komai kaje kawai Allah ya ........ Kafin yakarasa deeni yayi saurin mikewa tsaye ya katse shi ta hanyar cewa dan Allah dan annabi baba karka min Allah ya isa.......nasan matsawar kamin Allah ya isa zata bini.... Sbd nasan nablah yarkace .

Dan girman Allah ka taimakeni karka min Allah ya isa kar ka Kai karata gurin mahalicina..

A matukar fusace mahaifin nablah ya furzar da wata iska me zafi me cike da tsansar tashin hankali mara misaltuwa idanuwanshi suka rine suka jawur ya cire hular kanshi tare da goge gumin dake tsaftsafo masa sannan ahankali ya maida idanunshi kan nablah yace Kalli yadda kika maida rayuwarki......abin kwatance kanki kika cuta bani ba duk abinda yasameki ke kika jawowa kanki.. Muna zaman zaman mu lfy bamu rasa ci ba bamu rasa sha ba bamu rasa gurin kwanciya ba .
duk da talaucina Allah ya rufawa min asirin da zan dubaku .
km da talaucin nan nawa dakika raina na rufawa sauran yayyeki asiri har suka rayu suka zama abin alfahari agurina har namusu aure Amman ke kika daurawa kanki buri da son kwadayin duniya wai ke a dole sai kinyi karatu me zarfi to yanzu wa gari ya waya.
karshe ga kaddarar abinda son karatuna nan ya fada miki nan..

GA kaddararki nan kin je a miki wulakaci abanza a wofi an wulakanta rayuwarki .
an dirka miki cikin da baki san ma kowaye ubansu ba.
" kika haifi ya'yan aka kara dirka miki wani cikin... Uhmmmmm kaddaraki Kennan da kika jawa kanki.
Amman bada kowa zanyi bakiciki ko nayi Kuka ba.
dake zanyi kuka yanzu da badan Allah ya yanke miki wahala ba da yanzu ahaka zakiyi tayin ciki kina haihuwa batare da sanin kanki ba ballantana mu iyayenki da kikabar mu cikin fargaba da tashin hankali dubi yadda mahaifiyarki ta dawo kalar tausayi kusan damuwarta har ta zarta nawa kullun zanceta akanki nabeelah kowa kika kalla agidan nan bashi da kwanciyar hankali..
Sosai ya dinga zazzzaga mata itama nata tujarar har ya kusan dukanta yayi mata gabadaya ranshi yagama baci idanunshi suka rufe wata irin jawowa yayi mata da tshon ciki mahaiifin zeenat ya kwaceta ahannushi.
shi km deeni gani aika aikan da mahaifin nablah ke shirin masa yasa hankalinsa yayi kololuwar tashi da sauri sauri zuciyarsa ta dinga dokawa tana bugawa da karfi.
mlm Salisu yace ku miko Mara jin mgn na sabautata na huta me zanyi daita.... Arayuwata.
yarinya ta dinga janyowa mutane maseefa da ciwon zuciya duk cikin ya'yana nafi son wannan shegiyar yarinyar da amincewa daita dabata yardata da amanata Amman Kalli abinda tajawo min tajawo kanta tuzarci banda a Gaban shedu da Jamar arziki na daurawa yarinyar nan aure da me mutane gari zasuce .
kinje an rike min ke har kika haifi yaya uku me kike son nacewa yan'uwa na da danging da abokan arxiki Dan wani ko ka rantse masa ba yarda zaiyi ba cewa zai Yi cikin shege tayi.
deeni yayi saurin runtse idanunshi dan shi kwata kwata ya tsanani jin wannan kalmar arayuwarsa.
idan kuwa akwai abinda yafi tsana nan duniya tana byn wanna kamal... Wallahi yau sai kin gane Taurin kai bai inda yake kai mutun sai nadama da danasani gara na kasheki na huta, daga ita har cikin dake jikinta....
Deeni fa yaga da gaske mlm salisu so yake yayi masa hasarar cikinsa .
ga km tarin mugun son dayake WA nablah na sake fizgarsa take yashiga bawa mlm salisu hkr yana karawa.
zuciyarsa kadan ta rage bata buga ba
hade da yin wani irin tsalle .
cikin kirjinsa sai luguden tashin hankali da fargaban abinda mlm salisu ke shirin Yi masa yake.
zuciyarsa ta dinga tafarfasa ranshi yayi maseefar maseefar tashin ya dinga jin jikinshi na wani irin tsuma tsabar tashin hankali yayinda nablah data fixge daga hannun mahaifin zeenat .
tayi byn deeni ta kamkameshi ajikinta tana wani irin kuka me ban tausayi tana kuka tana furta dan Allah ka taimakeni wallahi babanmu nada zuciya zai iya kasheni tunda yace zai kasheni zai iya kasheni ya huta.. Nasan halinsa zai iya kasheni tana kuka tana sake kamkame deeni ajikinta wannan ririkewar datayi masa ya sake jefa zuciyarsa cikin rudani da mawuyacin damuwa shi kansa afrigice yake da ganin yanayin mahaifin nata.
wanda tunda yake zuwa gurinsa bai taba ganin wannan sifar atare dashi ba .
Ahankali tausayinta da wutar sonta ke sake shigarsa da ingizashi .yayinda zuciyarsa ke cigaba da bugawa da karfi... Sbd yadda take gogar jikinsa da nata jikin...


Ahankali big dady ya mike yana duban ummi da wani irin yanayi yayinda deeni ke ta faman aikine bawa mahaifin nablah hakuri shi km yana furta sai ya kasheta.
da bata bijirewa maganarta ba .
da bata kai kanta gidanka har kaganta kaxo yin *AUREN SIRRI* daita ba... Zuciyar mahaifin nablah fa ya dugunzuma ya dinga kokarin ture deeni ya fixgo nablah ..
a zafaffe ya dinga cewa nasuru ka miko yarinyar nan idan ba hk ba wlh har kai zan hada inyaso duk abinda za'a Yi ayi..
Big dady daya mike da kyar yace mlm salisu ka dubi girman Allah kadakata ka zauna miyi mgn..
Wannan mgnr da big dady yayi ita ta dakatar dashi daga abinda yake shirin aikatawa ko babu komai girman Allah da mutumin ya hadashi dashi da km ganin Girmansa wanda akalla shekaru zai kusan daya da kwatan nashi.. Shiyasa hankalinsa ya Dan dawo jikinsa tare da kokarin son sanyawa jikinsa natsuwa daga tsumar datake ba kaukautawa..
Sannan ahankali ya nemi guri ya zauna zuciyarsa na zafi da radadi yana huci zufa na sake karyo masa ta koina ajikinsa mahaifiyar nablah na kuka nuratu na kuka hatta yaran kuka suke ganin za'a dukar musu uwa .

Cikin sanyi murya big dady yace kayi hakuri mlm salisu ka yarda da kaddara datazo maka.
ka dubi girman Allah da cikin dake jikinta da km wayan nan ya'ya dake kuka kayi hakuri ka godewa Allah da wannan Abu daya faru da ya'yan data haifa da cikin jikinta ba'a titi ne tasamoshi ba.
aure tayi .
Aure km na Sunnan ma'aiki wanda kaine da hannuka ka daura shi.. Duk abinda Allah yakaddara bawa sai ya faru ..
km duk abinda Allah ya kaddara maka ka amsheshi da hannu biyu biyu.. Shine cikar imanin mutun.
Ka sake godewa Allah da nablah ba cikin shege tayi ba wanda hakan shine abu mafi muni gareka damu gabadaya..

Da Allah bai Yi hikimarsa ta zartar da aure tsakanin nasuru da nabeelah ba dafa tabbass sai an haifi yaran nan duka atiti wanda zuciyoyinmu bazai taba lamunta wannnan bakar maseefar ba .
amman alhamdullahi tunda abin nan ya faru nake godewa Allah da ya'yan nan ya'yan sunan ne.
ba shegu bane .

idan ya'yan gaba da fateeha ne idan km cikin shege tayi me zakayi?

yaza'ayi dole dai hakurin nan zakayi har gara yanzu ma kana da hujjar Kare kanka da bakin mgn acikin jama'a.
Kai kmr ba babba ba ina hankalinka da tunaninsa suka je ai idan rai ya baci hankali ke nemoshi ka tuna akwai yarda da kaddara acikin cika cikan muslinci mai Kyau ko mara Kyau.
soaai big dady shima ya dinga bashi baki har zuciyarsa ta dunga kasa tana lafawa da yin sanyi ahankali big dady ya dinga masa nasiha zuciyarsa tayi sanyi sosai Amman duk da wannan nasihar da big dady yayi masa bai hanashi mikewa tsaye yace naji km nagode sai dai bazan taba karbarta ba takoma can inda tafaro rayuwarta tayi cikin har ta haihuwa batare da sani ba.
Ba munyi alkwari dake ba akan wata uku zakayi ki dawo gareni ba ?
Nablah ta girgiza masa kanta...mlm salisu yacigaba Kana ganin yarinyar nan sbd auren dana mata bada saninta ba yasa lokacin data rokeni akan nabata wata uku zata je gurin aikinta ta dawo nabata bisa ga kyautatawa Amman shine tayi zamanta sai data haihu ta dawo min da wani cikin dayake makira ce ita..
Km tasan abinda tana son shuka.
nabeelah shi kanshi mijin daya zagayo gurina aureki km ya dinga zagayawa yana miki ciki kina haihuwa dame zai daukeni ?
tunani ma zai inda ace bashi ne yayi miki cikin ba hk zan km daukarki da ciki na bashi .
nabeelah kin cuci kanki kin zubarwa da kanki da mutunci da kima ki bari azo gurin mahafinki aureki akai ki gidan mijinki kmr yadda akewa kowa ce budurwa me mutuncin da kimarki da daraja Amman kika cuci kanki .
sbd da baki bijirewa mgnta ba, kin zauna lokacin dana ce miki karki sake kije koina da bai ganki ya zagoye ya aureki agurina da wata manufa ba.
nablah na wani irin kuka ta rarrafo zuwa gurin mahaifinta .
Tana kuka mlm salisu yace wacce irin ya Mace ce me mutunci da daraja da kamun kai zata aikata irin abinda kika Yi domin cikar burinta ?
Tana kuka tana girgiza masa Kai alumun babu kana muryarta cike da kuka tace wlh baba bansan komai ba ...ban San komai ba akan cikin jikina da ya'yan dana haifa ni kaina wayar kaina nake nagani dashi dan Allah babana kayi hkr ka yafe min bazan sake kinji mgnrka ba duk abinda kace nayi shi zanyi bazan sake sabawa umarninka ba.. tana kuka tana rokonsa furzar da iska yayi yana girgiza Kai .

zeenat tayi shr tayi zugun azaune tana kallon ikon Allah yau ga talaka me zuciya tagani .

Ashe daman talauci bayasa mutun ya kaskanta da wulakanta yazamo Mara galihu?

A she daman talauci bayasa mutun ya
tozarta kanshi?

A she daman talauci bayasa mutun ya daydayta yazamo abin tausayi ?

A she talauci bayasa mutun yazama kasasshe har zuciyarsa ta mutu.
Tasashi jin bazai iya kwatarwa kansa yancinsa ba ?

A she talauci bayasa mutun yazama me matacciyar zuciya km Mara zuciyar kanshi.

Yau ga deeni me tarin arziki tsohon retaya soldier me tarin camfanoni da tarin dukiyar da shi kanshi bai san adadinsu ba .
tsaye GAban wani wulakantaccin talaka me wakin hula yana masa fada da maseefa har da rantsuwa..
Yau ga big dady shugaban plant nuwaun rows family estate shugaban dagin gabadaya na nesa dana kusa ya zauna a gidan talakan dako inda me gadinsa ke rayuwa yafishi daraja Amman ya zauna yana masa tujara yana rokonsa dan Girman Allah yayi hakuri ajiyar zuciya taja da karfi zuciyarta ta sake yin ladab akan rayuwar duniya sai lokacin km tasan lallai ba komai kudi ke wa mutun arayuwa ba..
Hk kazalika ba komai kudi ke sai maka ba lallai akwai talakan dayafi me arziki zuciya da tunani .. Atunaninta yadda motocinsu suka shigo unguwar da yadda arxiki ya nuna ajikinsu yaci ace ko tarin kirki mahaifinta bazai ba akan mgnr da suka zo masa daita Amman sai gashi ya dage iya karfinsa da gaskiyarsa yana surfa musu tujara..

Hk ma ummi tunanin datake Kennan Ashe tagudu bata tsira bane datace a auri yar talaka Mara gata da galihu kaskantacciya. Ashe baban nablah ba kaskantacce bane Mara galihun datake tunani mutun ne sak me zuciya ba wanda za'a iya cin galaba akanshi bane domin yadda take kallonsa a irin wannan zuciyar tashi ko shara'a zai iya Yi dasu duk kudinsu.
lallai yau tagamu dagamonta.
aranta ta dinga jin idan baban nablah me arziki ne da basan me za Yi ba. tana cikin wannan tunanin nata na wuncin gadi mahaifin nablah ya gyara tsayuwarsa sosai yace yanzu sai ki Mike ki bisu ku koma inda kuka fito tare .
da son kokarin barin gurin mahaifin zeenat yayi saurin tararsa ta hanyar shan gabansa yace Dan Allah kayiwa iyayenka ka sauraremu. Mahaifin nablah yace ku daina hadani da Allah da iyayena akan cutar da'aka min kana ganin abinda nasuru danku yayi min kana ganin irin yaudara da cin amanar da nasuru danku yayi min wasu irin iyaye za,a yiwa irin hk a wanna duniyar da muke cike su lamunta ?
.Da kyar da Allah da big dady aka samu aka shawo kanshi har yazo ya km zama .
itama ummi jikinta a sanyaye tashiga bashi hakuri tare da ce masa wlh duk wannan laifina ne sannan kuskurena ne ba laifin deeni da nablah bane .
asalima nabah batasan komai ba kmr yadda tagaya maka domin kuwa batasan deeni na kwamciyar aure daita ba sbd magani yake mata amfani dashi kafin komai ya wakana a tsakaninsu sosai ummi ta dinga vashi hkr akan Abunda daya faru.
sannan km tace yayi hkr ya yafewa nablah batada laifi komai idan ma akwai me laifi to itace babbar me laifi domin itace silar komai.
hatta zeenat ma da jikinta yagama yin sanyi da lamarin sai data saka bakinta gurin bawa mahaifin nanlah hkr Takara yarda da sanin Duniya da abinda ke cikinta ba komai bane ta dinga tunanin matsayi na big dady da deeni da sauran mutane dake zaune agurin Amman gabadaye kowa hkr yake bawa mahaifin nablah jikinta yayi mugu mugun sanyi ta bude baki tace Dan girman Allah baba kayi hkr ka yafemana gabadayanmu dukkaninmu masu laifi ne km masu kuskurene ko agurin Allah Amman kayafe mana Dan Allah.

Deeni ma ya matso sosai yace baba munayiwa Allah laifi ubangijin daya halicemu yabamu ci da sha yabamu lfy sannan km yabarmu da rayukanmu km muyi masa laifi km rokeshi yafiya ya yafemuna sosai deeni ya dinga bawa sirinkin nasa me kafiya da daurin zuciya hakuri yayinda nablah dake durkushe tana kuka .
ta rike kafafuwan mahaifinta tana fadar babana ka yafemin sau daya tak nasan nataba Saba umarninka aduk tsawon rayuwata Amman Kalli yadda rayuwata ta dawo baba?
idan ka cigaba da fushi Dani bansan yadda rayuwata zata dawo ba. ta dinga risgar kuka tana rokonsa yafiya gabadaya jikin mlm salisu ya sake yin sanyi sosai .
nuratu da mama mahsifiyar nablah suma kuka suke suna nabashi hkr muryasa a raunane ya dubi gabadaya mutane gurin yace shikenan na Hakura na yafe mata....
take hankalin kowa dake gurin ya kwanta.
take Kuma mlm Salisu ya bugawa Manyan ya'yansa waya da wasu daga cikin danginsa na nan kusa waya sannan yakira waliyan da suka daurawa nablah aure.
duk akazo aka hadu da dattawan unguwa har yayyenta da kannanta da aunty Salma .

Amman mlm salisu bai fito ya gaya masu gaskiyar lamarin ba sai yayi musu karyar cewa tun sanda aka daura auren.
deeni yazo daga baya ya dauki matarsa Amman sbd wani dalili yasa bai fitO ya sanar wa kowa ba sai yau din nan gashi nan har sun haihuwa ga MA wani cikin nan ajikinta ga danginsa nan....


To byn yan unguwa Sun fita .
sai yagawa daginsa da ya'yansa gskyr ainihin abinda ya faru nan dai aka sake neman yafiyar juna aka yafewa juna sosai .

byn komai ya natsa mahaifiyar nablah tace dan Allah abar mata nablah zuwa wani lokaci har ta haifi cikinn jikinta zuwa lokacin hankalinta zai kara kwanciya.
da kyar deeni ya yarda ya amince da barin nablah agidan Amman banda yaransa .

bai samu damar kebewa da nablah ba Suka koma gida zuciyar kowane cike da farinciki Amman banda zeenat wace duk da abinda ta dinga Yi

1 Comments On AUREN SIRRI
avatar
adam-ado

9 months ago

Reply

Very interested book

Please Login or Register in order to submit comment