Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana jin bazata iya rayuwa bbu su ba ....


Amman Ga tashin hankali da uwarsu tazo mata dashi wanda take jin bazata iya jurawa ba .. Amman duk da Haka durkusawa wada ....
gabadayan ilahirin jikinta yayi mugun sanyi jikinta banda kirma bbu abinda yake tsabar tsoro da rudani .
Ga mamaki deeni da ummi har nablah.
suka Ga zeenat ta zube a gaban nablah tana kuka tare da rike kafafunta tana rokonta Dan girma Allah nablah ki rufa min asiri kada ki min Haka wannan ita kadai ce damata da zata min katanga tare da yi min shingi da kishiya arayuwa ta.
Dan girma Allah kibar min yaran wallahi nafiki bukatarsu zan kular miki dasu fiyye da tunaninki .
zan basu gatan duk duniyar nan .
zan kaunace su fiyye da ke kanki da kika kawo su duniya ..
Dan Allah kibar min su Karki fasa kyautar mana dasu kmr yadda kikace ummi Dan Allah kisa baki tabar min su .. my hrt kaima kayi shr kaki cewa komai please kuyi mata mgn kozataji nafita bukatarsu takarasa mgnr tana fashewa da wani irin matsanancin kuka.

kuka zeenat take tana rokon nablah akan tabar mata yaran ... ahankalin deeni ya Mike tsaye Daga zaune dayake yaje har gaban nablah ya mika mata hannunwansa duka alamun tabashi yaran Amman taki .

Yayi yayi tabashi yayan taki sai ma matsawa da tayi Daga kusa dashi tana jijiga yaran da zuwa yanzu hayaniyarsu tasoma tayar dasu .


da kyar deeni ya shawo kanta ta hanyar ce mata bbu inda zanje da yaran nan nablah zan kwantar dasu ne kawai ko bakiga yadda kika matsesu ba ajikinki ba kar wani abu yasamesu .
sannan ta Mika masa mace da Na namiji zuciyarta cike da tsoro da fargaba yaje ya kwantar dasu .
ya dawo ya amshi dayan ma ya kwantar dashi kusa da yan'uwasa kana ya janyo hannuta ciki sanyi jiki Ya zaunar daita akan gadonta ya tsura mata rikitattun idanunshi yana kare mata kallon tsanake .
sannan yasoma magana 'cikin sanyi rai da zuciya...




MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗




AYSHA A BAGUDO


Dedicated to
HAUWA A USMAN
JIDDARH



Page 100



Nablah ki natsu ki dawo 'cikin haiyacinki muyi mgn 'cikin tsanake da fahimtar juna da farko kin amince da zaki bamu abinda zaki haifa wanda har muka sanyawa rayuwarmu son abinda ke cikinki.
" to meyyasa yanzu kika canza ra'ayinki alhalin duniya tagama sannin wayan nan ya'yan ya'yanmu ne nida matata ?

Ilahirin jikinta da bakinta wara suke gurin cewa nidai kawai ji nake a halin yanzu bazan iya kyautar dasu ba.
. saboda kinsha wahala gurin haihuwarsu shiyasa bazaki iya badasu ko me ?
Kai tsaye taji ya 'aiko mata da tmbyr datasa ta tsura masa shanyayyun idanunta da suke cike da ruwan hawaye taki ce masa komai sai kallonsa kawai take ..
"jikin deeni Yayi sanyi sosai sbd ganin yadda yanayinta ya sauya . yarasa ta inda zai bullo mata.
ta kalleshi sosai Yayi matukar bata tausayi Amman har 'cikin zuciyarta bata jin zata amince tabashi yayanta kyauta .
" tacigaba da dubansa can km yace kina jina ko kiyi hakuri kibar mana yaran nan nida matata nayi miki alkwarin zan raba tarin dukiya biyu Na baki rabbi akansu kije kicigaba da rayuwarki .
Sosai ta sake tsareshi da shanyayyun idanunta tamkar zata cinyeshi tana mishi wani irin kallon rainin wayo.
hakan Yasa gabansa cigaba da faduwar dayake .
shima kallonta yake yana jira Daga gareta tare da mamakin canzawarta a'cikin zuciyarsa .
idan wani ya fada masa zata rikide ta dawo masa Haka wallahi zai rantse da Allah yace karya ne ranta a matukar bace tace Kai dukiya ta dama km take rudarka har kake jin Kai wani ne .
Amman ni bbu abinda za'a bani a duniyar nan da zai Saka Na iya kyautar da ya'yana har UKu ba daya ba.
ko mahaikaciya ce Ni bazan soma yin wannan dayin aikin ba ballanantana Ina 'cikin haiyacina, yakarasa fadar hk tana nuna brain dinta da yatsan hannuta.
kana tacigaba nidai Dan girma Allah Na rokeku daku barmin ya'ya Na Ina sansu nima a duk yadda suke.

deeni ya runtse idanushi gam tare da furta ya Allah akasan zuciyarsa ....yasoma cizan lips dinsa da karfi .
gabadaya komai Na 'cikin duniyar nan yasoma tsaya masa Bai taba tunani sanadiyar yarinyar zai taba shiga 'cikin tashin hankali irin Haka ba.
ya dauka rashin son 'cikin jikinta datake tun farko zai tsaya a Haka ne .
Amman a kalmomin bakinta na yanzu komai ya sauya agareshi yagane shi din bakomai bane a duniya nan .
sannan ya soma fahimtar Bai isa yace zai ma kaddarsa wayo ba .
Yau din nan tazo masa da tarin abubuwa da daya farinciki dake tattare da tashin hankali mara misaltuwa .

Shin yanzu ya zaiyi da kaddarar data fada masa ?

Ya'yan da zai fara samu a duniya sunzo masa da wani irin salo na daban .
yanzu mezai cewa danginsa da yan'uwa ?

Hakika Komai yagama dagule masa ahankali ya juya saitin da zeenat take tsaye surusuru tana aikin barin jiki da marairaice wa .
yana aika mata da wani irin matsiyacin kallo me frigita zuciyar wanda akawa sannan muryarsa a fusace yace kinga ni ko ?
Kinga irin abinda sakacinki ya haifar mana ko ?
Me kike tunani zai faru gaba idan har taki amincewa tabada yaranta ?

Zeenat da jikinta ke mugun kirrrrrrma ta sake fashewa da wani irin matsanancin kuka tana yarfe hannuwa .
yanzu dakin yi hakuri kin haifi wanda Allah yabaki da duk hk Bai faru ba.
da km baki samu 'cikin tsaka me wuya ba. Amman bbu komai duk 'cikin wannan lamarin ni akafi cuta yakarasa mgnrsa yana jin kunar rai acikin zuciyarsa yayinda kirjinsa ke wani irin buguwa da karfi .
Shi kanshi kuka yake son yi ko zai daina jin radadin azabar ciwon zuciyarsa keyi .

banda kuka bbu abinda zeenat keyi ita kanta tasan ta cuci kanta da kanta.
Ta ruguza rayuwarsu sbd sakacinta da son zuciyarta ta Mike Daga inda take ahankali tana layi ta rungume ummi ajikinta tana matsanancin kuka.
Ummi kiyi hakuri a rayuwa nasan Na cutar daku Amman ko daidai rana daya ummi baki taba kina ba .
Sai ma sabuwar kulawa da kike bani hakika ke uwace guda har da rabi samun irin Ku ahalin yanzu zai yi wuya ummi kiyi hakuri abida nayi ki ya femin Na cutar dake domin ba irin tarbiyya da kika bani ba kennan ta sake tsanata kukanta.
ummi itama ta rungumeta sosai tana zubda hawayen tausayin diyarta arayuwa ta tsani abinda zai saka zeenat dinta zubd hawaye matukar tana da yadda zatayi.
kasa cewa komai tayi Sai aikin rarrashita datake tana shafa bayanta ..

Ahankali deeni ya dauke idanunsa akansu ya juyo sosai tare da gyaran zamansa yana fuskantar nablah da kyau ya kaskantar da kanshi da muryarsa agabanta yana nuna mata shin din bakomai bane facce me nema agurinta .
a wannan fani har ya mance dako su waye tsaye akansa.
Domin Bai San sanda ya kamo tafin hannunta 'cikin sanyi jiki ba yana kallon 'cikin kwayar idanunta muryarsa cike da rauni zuciya tare da mayyen sonta ya Kira sunanta.. nabeelah ...kiyiwa Allah ki mallaka mana bbys din nan.
badanmu ba Sai saboda Allah ki duba tashin hankali da zanshiga akan yaran nan .
sannan ki duba halin da mahaifiyata da matata zasu shiga ki tausaya nablah ki duba yadda mahaifiyata tagama gayawa duniya akan nida matata muka haifi bbys din nan .Kinsa idan akaji sabanin hk zatashiga tashin hankali da rudin rayuwa ..
nablah nasan kina da saukin Kai da sanyi hali hade da hakuri akan komai Na rayuwa .
Na rokeki da Allah kibarwa zeenat bbys din nan .
Allah zai duba lamarinki ya sake baki wasu da yardarsa ...
a fusace ta fizge hannuta 'cikin sauri Daga nashi tana jin takaicin mgnrsa . ..

Kana ji har mara hankali matarka ta kirani dashi akan ya'yan dani kadai nasan kalar wahalar dana Sha akansu tunda Daga cikinsu har zuwa haihuwarsu.
idan har nabar mata yaran nan wallahi azim Na tabbata mahaukaciyar gaske deeni .
zeenat ta bar jikin ummi tamatso gareta sosai tana kuka tana rokon nablah.

ZUCIYAR deeni tasoma rawa yasoma jin Wani irin ajikinshi hakika ya tausayawa zeenat duk da yasan itace silar rugujewar rayuwarsu da yi musu katangar karfe da burin ransu km farincikinsu Amman fur nablah taki amincewa tare da cewa aunty kiyi hakuri wlh nima Ina son ya'yana.
idan nabaki su ni km yazamanto su kadai ne ya'ya da zan haifa a duniya ni km Sai nayi ya'ya ?

Kiyi hakuri kawai kema Allah zai baki naki da yardarsa Amman zance nabar miki ma su yanzu bbu shi .

kibar min nawa nayi rayuwa dasu , sune duniyata ayanzu bazan iya rayuwa bbu su ba .

deeni ya juyo a tsukwane ya kafe zeenat da idanushi yana kallon yadda ta dawo wata kala abar tausayi bbu wuya tashin hankali ya canza mata kammani .
Ummi takaraso ahankali itama ta zauna kusa da nablah ta dinga bata hakuri da yima dabarunsu irin Na manya da siyasa iri iri Amman fur nablah taki Sai ma fashe musu da sabon kuka datayi ni kibarni Haka Dan Allah Dame zanji .
yanzu zan bar muku gidanku akan na bada yaran nan gara na komai
kan bola Na rayu dasu 'cikin kulawata .

gabadaya deeni yasoma tsorata da yanayinta har yasoma aikawa kwalkwaluwarsa tmbyr Anya kuwa wani abu Bai samu brain dinta ba kuwa gurin haihuwa ?

Sosai Ya xuba uban tagumi tare da jefa Dan karamin yatsansa 'cikin bakinsa yana cizawa da karfi yana kallonta yana nazarin reaction dinta ..
sosai ya jima yana kallonta kafin Daga bisani yace first love barta kawai akawo mata abinci yaci da alamun tana jin yunwa tun da muka shigo gidan nayi nayi daita taci abinci taki ci a she rigima take ji shiyasa.
jikin ummi a matukar sanyaye tace zeenat goge Hawayenki ki natsu kada mutane su gane Muna 'cikin damuwa da matsala.
muje maza ki kawo mata abinci ni zan Dan tsaya saboda kauda idanun mutane akanmu.

Tare suka fita .
ummi Na sake rarrashinta akan ta kwantar da hankalinta ..

Suna fita deeni ya juyo gareta ya hade da jikinshi ya rungumeta zuciyarsa Na harbawa da sauri da sauri .
tare sa sakin naunauyen ajiyar zuciya bakinsa yakai daidai saitin kunneta sosai.
Yace Na yaba da jarumtarki Na yaba miki da yadda kike son baby's dinmu .
daman Haka yakamata duk wata uwa tayi akan yayanta .
km hakan da kika yi ya sa naji kin birgeni sosai. Sai dai me zai hana ki tausaya kibarwa zeenat dina baby's din please zata kular miki dasu ..ki tuna sanda kike kuka kike rokona akan azubar da ciki Na hana batare da saninki ba .
ki tuna irin taimakon dana miki akan ni zan karbi 'cikin da bansan wanda Yayi miki ba domin gujewa kunyar duniya
Da karfina da dukiyata duk sa sadaukar akan Na inganta 'cikin jikinki da rayuwarki .
Amman kirasa abinda zaki sakayyar min dashi .
Sai hanani bbyn dana gama wahala akansu.
Meyasa zaki min hk ? Yakarasa mgnr da
Ki bar mata sake of me please nablah zanji dadi idan har zaki iya min hk .kina jin yadda zuciyarata ke bugawa da karfi akanki .
,akanki zan iya yin komai ciki har da fallasa sirrin dake boye wanda hakan bazaiwa first love dadi ba.
please nablah sake of me jikinta Sai kirma yake tana zubda ruwan hawayen tausayinsa muryarta a dashe tace nasani deeni kataimaka min a rayuwa km zan iya yi maka komai a rayuwa Amman bazan iya kyautar yaran nan Ga kowa ba ciki kuwa har da kai ..
Ni kaina Haka kawai Na tsinci zuciyata da matsanancin kaunarsu tunda Na daura idanuna akansu .kasa samun natsuwa .
Ya zanyi nabaku kennan ni zauna hk ?
Byn tarin wahalar dana Sha akansu .
ahankali ya sausauta rungumar da Yayi mata ya ciro hanky Daga gaban aljihun rigarsa yashiga goge mata hawayen dake tsiyaya akan kuncinta .
bakinsa ya Kai kan lips dinta ya tsotsa yana kallon 'cikin idanunta .
Lumshe shanyayyun idanunta tayi tasoma kokari cire bakinta Daga nashi .
Jikinsa a sanyaye ya xuba mata rikitattun idanunshi kawai yana kallonta yana imagine dinta.
har sanda zeenat ta dawo dakin hannuta rike da cool food flasks da flasks din ruwan zafi da plate ..

Deeni ya janyo wata Yar karamar stood tsakiyarsu ya bude cool da zeenat tashigo dashi.
miyar dayafi tsana arayuwarsa yasoma cin karo dashi wato miyar kuka wace Tasha naman kaza da kayan kamshi makewa Yayi ya ciro karamar ta sama ya ajiye yacigaba da bude cool yaga tuwan samiviter ne aciki Whit lailon ya ciro tuwon yasaka akan plate ita km zeenat jiki Na rawa ta hada mata tea me kauri ta mikowa deeni.
" ya karba ya ajiye a gefen plet din.
abin zeenat nabashi mamakin sannan km yana jinjina girma al'amarin.
lallai sanadin wayan nan baby's din Yasa zeenat dinsa tasoma sauya halinta wanda yajima yanasonta dashi .

Muryarsa a matukar sanyaye yace Bismillah nablah kici abinci .
taki ci ta xubawa masa idanunta ya Mika mata cup din tea shima taki karba.
Yayi shr ya tsura mata rikitattun idanunshi bazaki ci abinci ba ?
Ta girgiza masa kanta alamun eh saboda kina tunani zamuyi poison naki ko ?
Tayi saurin sake girgiza kanta to meyasa bazaki ci ba alhalin nasan kina jin yunwa ?

Muryarta a shagwabe tace nifa bance zakuyi min wani abu ba .. zeenat kawo min spoon.
.
Zeenat ta juya da sauri taje takawo masa spoon ta Mika masa .
mamaki ne yakama zeenat Ganin deeni yasoma tura tuwon samiviter da miyar kuka abakinsa the most abincin dayafi tsana kennan arayuwarsa ballanantana dai miyar kuka wanda ko sunan miyar akafada agabansa Sai ya yatsuna fuska tsabar baya sonta .
Amman yau shine zaune yana ci hankali kwance dago rikitattun idanunshi Yayi masu tsantsar cike da tashin hankali ya daura akan nablah dake zaune tamkar an dasata tare da yi mata alama da spoon din hannunshi .
, zeenat tasoma itama sosai ta tsoma hannuta sbd ganowa datayi lallai nablah bata yarda dasu ba.
tasoma ci Sai da nablah ta tabbatar dayaci sosai hk ma zeenat sannan ta tsoma hannuta ciki tare da yin bismillah tasoma ci ahankali aranta tace idan ma mutuwarce ba zan mutu ni kadai ba Sai dai abarwa ummi baby's din .
ko tea din ma kin Sha tayi Sai da zeenat Tasha deeni yasha sannan Tasha itama .
deeni ya kalleta yana tabe baki girgiza Kai .
sbd muraran km azahirance nablah ke nuna kuruciyarta a filli . Idan har wani abu zasuyi mata .
Ai tayi kadan ta kare kanta .


number wayar ummi deeni yakira .
Byn kmr minti goma Sai gata tashigo dakin first love yakama ayiwa yarinyar wanka hk fa da duk abinda yadace.
ko bakace ba deeni duk za'a yi mata daman wannan tashin hankali ne Yasa nakasa samun natsuwa nayi mata ai nablah tamkar diyar cikina Na dauketa .

Da zai fita ya janyo hannu zeenat ya nufi dakinsa daita ya rungumeta tsam tsam ajikinshi zeenat yakira sunanta Ina so ki tattaro natsuwa ki sanyawa gangar jikinki sannan ki kwantar da hankalinki da sannu zan shawo kanta 'cikin sauki batare da wani hargitse ba har ta amince .
domin wannan harbin iskar da kike da tashin hankalin ba zai saka tabada ya'ya 'cikin sauki ba .
as far as tasan wahalar daukar ciki da radadin haihuwa kema kinsa bazai yiwu a karbi yaran 'cikin sauki ba.
ki dinga lallabata ta yadda taza yarda ta amince da ba cutar daita da yaranta zakiyi ba ..

narkewa tayi sosai ajikinshi , zanyi komai my hrt matukar yaran zasu zamo nawa Dan wlh wani irin mugu mugun son yaran nake ji 'acikin zuciyarta .
Nima sun shiga raina zeenat fiyye da ita kanta uwar data kawo su duniya.
Amman duk da hk ba zai yiwu muyi mata dole ba .
tana bukatar rarrashi da caring kema kinsa haihuwar nan is not easy ballanantana irin nata datayi kwana biyu tana abu daya sosai deeni ya kwantarwa da zeenat hankali har ta Dan samu natsuwar zuciya tare da sake jin kaunar yaran daram acikin zuciyarta ..


Kowajen wanka ma kememe nablah taki yarda ummi ta rufe kofa toilet tayi.
Dan kofar a bude aka barta tana hango wutsil wutsul din yaranta akan bed Dan gabadaya atsorace take dasu ummu.
yayinda zuciyar ummi tashiga watsi watsi datashin hankali anya kuwa ba wata maseefar ce ke shirin faruwa dasu ba.
duba Ga yadda nablah ke nuna son yayanta mura mutane da yin kafa kafa dasu ...



Daren ranar gabadayansu Daga ummi har oga deeni da zeenat adakin nablah suka kwanna sbd yaran a cewarsu .
bbu wanda ya runtse acikinsu.
yaran Sai kuka suke nablah zaune tana feeding din mazan duka biyu zeenat km tana tsaye tana hada abinci yara a fidda.
shi km deeni yana tsaye rungume da bby girl dinsa yana jijigata sbd kukan datake ya saka mata lips dinsa abakinta yana Dan jijjigata har takoma bacci ya mannata ajikinshi sannan ya koma ya zauna .
Ya jin yadda zeenat ke cigaba da rokon nablah Amman tayi mata banza taciga da feeding din yaranta tana jijiga kafa .zaune kawai deeni yake Dan Bai San me zaice ba .
ya kwantar daita zeenat ta karbi bby daya Daga hannu nablah tashiga bashi abincinsa.
ita dai ummi zuru tayi tana aikin binsu da ido kawai.
sbd al'amarin yarinyar ya daina bata mamakin ya dawo bata tsoro .
Haka 'cikin daren ummi da deeni sukayi ta mata naci da rarrashi akan yaran .
nablah kema tamkar diyata nake jinki 'cikin raina sannan km bazan iya takuriki ba Amman idan kinsa yadda yaran nan suke 'cikin zuciyarta dakin mallaka manasu Kai tsaye bazan taba gajiya gurin rokonki akan kibar mana su ba .

nablah tace uhmmmm azuciyarta , ummi kennan bazaki tabagane value din yaran nan a raina ba .
ni kaina bantabasani Haka yaya suke acikin zuciyar iyayensu ba Sai dayazo kaina .
wayan nan yaran sune duniya ahalin yanzu .. zeenat ma sake saka baki ciki nablah zan kular miki dasu Dan girma Allah kiyi hakuri kibar minsu wlh nafiki bukatarsu sannan Ina rokon ki Dan Allah kibari a dinga sauka da baby's din nan kasa sbd Yan zuwa barka ..
Wani irin mugun kallo nablah tabi zeenat din dashi sannan tace nifa wlh bazan wani bayar da ya'yana ba .
duk me son ganinsu yazo sama idan ya matsu Amman wlh idan kuka takurani zan ban bar muku gidanku Gobe goben nan , Dan nima wlh atakure nake daku.

gaban deeni ya buga da karfi ya tsurawa Dan karamin tsukaken bakinta ido .
Muryarsa a sanyaye yace nablah no duk zance Bai kai hk ba .
Ba Sai kinje koina ba ke zeenat gobe kiyi zamanki anan dakin kawai duk me son ganinki da bbys yazo nan yasameki. jikinta a sanyaye tace to shikennan my hrt.



Washegari gidan yacika tap da dangi tana ji yadda kowa yake fadar irin kyawun yaran Amman wai macce ce kawai bata biyo deeni ba suko mazan tamkar an tsaga kara ne dashi .
Ita ko nablah tana kwance su ummi gabadayan sun rasa gane kanta domin ranta a matukar bace yake taki yarda tayi magana da ummi ballanantana wata zeenat.
Barta deeni ko kallo Bai isheta ba sbd magiyar dayake mata akan yaran aranta kuwa kwata kwata batason ta kara daidai da second daya agidan.
tunanin kawai yadda zata gudu take da yaranta 'cikin sauki batare anganta ba ..



Tundaga ranar duk yazo barka ya nemi ganin baby's Sai dai subada uzirin Doctor yace bbys din suna bukatar hutu yawan daukar da'ake musu yana saka su zazzabi dare wasu sun yarda da zance Sai dai wasu basu wani amince ba .
km suka dinga cewa iyayi ne kawai irin Na deeni Dan duk sunsa sharrinsa ne ...

Sosai ummi ke bawa nablah kulawa ita da yaranta .ta gasata sosai da sosai duk da kasancewar nabla irin matan ne masu tsukaken jiki wayan da da zarar anagama cinsu suke hadewa take Amman duk da ummi Na kula da kasanta .domin zuwa yanzu ta hade gam tamkar ba itace ta haifo Yan uku ba .sosai km take da nuna mata yadda zata kula da yaranta.
Itama nablah duk abinda ummi tasanar tana kiyayewa sbd daman ita can me kaunar yara ce nawasu ma ta bauta musu ballanantana nata .ita kuwa zeenat gabadaya fargaba da tunani hade da tashin hankali ya maidaita wata iri .
tayi wujiga wujiga daita tayi wata irin rama tayi duhu kallo daya zakayi mata kasan tana 'cikin taskon rayuwa da tsaka me wuya. Yayinda kullun kwana duniya take like da nablah tana yi mata naci da magiya akan tabar mata baby's din ta .ita km ta rufe idanunta taki wani lokacin idan abun ya isheta tasaka mata kuka .abu goma da ashirin Ga kewa gidansu datake Ga taushin hankali da fitinar zeenat.


Ta fanni deeni ma gabadaya ya susuce ya rame tsaye kawai yake da kafafunsa Amman zuciyarsa cike da rudani .
Tunda akayi haihuwar yagagara fita koina . abokansa sukayita zuwa taya Shi murna karuwar daya samu .
Yayinda ,gida da office takoina ka kalli fuskar jama'a murna haihuwar manager suke .
,sadaka kuwa deeni Yayi shi har bai San iyakacin abinda ya raba ba .hutu sati guda akabawa ma'aikata companies har sai byn suna .


Fk ma yazo ganin baby's da kyar deeni yasamu ya karbi a gurin nablah yakai masa km har yakai su ya dawo dasu kuka take .tana ganin ya dawo mata da yaranta ta bar kuka datake tana sakin numafashi da karfi da ajiyar zuciya 'cikin jikin nasa yakaraso gareta yana cizan lips dinsa yace yanzu har rashin yarda takai Haka nablah ?
Bazan cutar dasu domin nima sune duniyata kalli yadda kika dawo nablah akan yaran da nabaki ba .wata katuwar harara ta zabga masa sannan ta turo masa tsukaken bakinta gaba bangane yaran da banawa ba?
Kana ganin duk duniya akwai wanda ya isa Yayi claiming din yaran nan nashi ne ?

Ya Dan yi murmushin takaici ya zauna gabanta ya tsotse lips dinta cike da shaukinki kaunarta yace akwai ubansu km mahaifi ko ba dade zai bayyana kansa garesu Amman dai kafin zuwansa kiyi hakuri ki bar min su.


Ranar da bbys suka cika kwana hudu da haihuwa tafiyar gaugauwa taka ma deeni zuwa abuja tun safe deeni ya tafi abuja amman aranar zai dawo.
,tunda nablah taji zance tafiyar sa .
Ta kasa zaune ta kasa tsaye .
hankalinta Yayi matukar mugun tashi .
Duk ta frigice ..
taki sakarwa ruhinta salama .



Karfe shida daidai
deeni yashigo gidan kai tsaye dakin jikin nablah ya nufa yana bude kofar yayi turus jikinsa a sanyaye sbd ganin da Yayi nablah tsaye rungume da yaranta biyu akirjinta ,sannan

1 Comments On AUREN SIRRI
avatar
adam-ado

9 months ago

Reply

Very interested book

Please Login or Register in order to submit comment