Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne..!
Safiya Tayi Shuru Tana kallon Munari Kamar Zatayi mgana sai ta fasa aranta Tace kada tace Na dameta da son jin kwakwaf,sai ta Share mganar Ta kara Damke Hannun Munari Tana Fadin"Amtsayina na Bakuwa bani Labarin Ya yusuf da Ya Imu..? Wanne yafi kula dake wa kuma kika Fiso..? Saura kuma Kice My Dear baya Kula Dake sosai sai na ciki Tara..!
Munari ta samu abunda take so wanda ZAta ganta Gata tana Hira da Dariya ta saba Rayuwa ita kadai adukan Shekarun da suka Dawo kano da Zama Banda Yaya yusuf bata samun Sakewa da kowa sai kuwa Abba Shi kuma Bashi da lafiya in kwana Biyu ya samu Sauki Zuwa Chan sai abun nashi ya kara Rikicewa Dama Ya Imu bamai sakashi a lissafi ko abaya ba abokin Hirarta bane Shi,Ballatana yanzu da abubuwa suka Lalacemai sosai.
Ko amakaranta ya Jamata kunni Kada ta kuskura ta yi wata kawa ko Wani Mutumcin da zai ka ga Har a san Gidansu,Sharudda ya kafamata Sosai kafin ya yarda ma Ya yusuf ya biya Kudi mata kudi a wata Makarantar Kudi ta Rubuta WAEC Da NECO,Da Jamb Har ta samu Gurbin Karatu a Jami"ar Bayero Tunda Lokacin da Suka Baro Lagos Tana SS2 ne,Duk somta da Mutane ta Ware kanta Tun yan ajinsu na Shigemata tana kauce musu Har sukayi banza da ita kowa ya kama kansa bata da Lambar Kowa Itama ba wanda ke da nata sai dai ta karbi Na Class Rep dinsu saboda In wani abu ya taso ta Rika sani Har Group dinsu na Department dinsu na Wasop ya sakata Tana gani ana Hira da Dariya bata da ikon cewa wani abu,sai da ta Shiga tagani in an bada Wani Assigment ko wani Infomartion mai amfani ta Duba Duk yadda taso Rayuwarta Tatafi yadda Hallitar take bazata iya Bijirema Umarnin Yayyinta ba itama Bazata zo ta Fuskanci Wulakaci da Tozarcin da Yayyinta ke Fuskanta kan Gidansu ba.
Safiya ce ta Girgiza hannunta ganin Ta Shiga Dogon Tunani Da Sauri ta Dawo Hayyacinta Tayi Saurin Zare Hannunta Tana Goge Ruwan Hawayen da suka Fara kokarin Zubomata Cikin Dariya Dariya ta Fara Fadin"Ai baza ma ki Hada ba Anty Safiya..Abaya Ni yar gatace ta gaba da Baya..yar gatan Abba da Anni yar gata kowa agidanmu..ayanzu kuma Ni yar Gatan Abba ne Duk da bai da Lafiya Dagashi sai Ya yusuf,Bai Hadani da komai ba..Zai iya yin komai Saboda Farincikina Baya iya Runtsawa sai ya Tabbatar da naci Abinci na kwanta sannan zai iya barci..Ya yusuf Mutum ne mai Zuciyar Zinare,mai kirki mai Dattako mai Sanyin Zuciya Dana Hali bashi da Hayaniya ballatana Saurin fushi Zan iya ce Miki ban Taba ganin Fushinsa ba yana da Raunin Zuciya kamar mace Irin Zuciyar Abbanmu garesa suna da Bala"in Sanyin Hali da Dadin Zama ga waanda ya Zauna dasu..Zasu iya Sadaukar da komai Saboda Ahalinsu,ZAsu iya Sadaukar da Dariyansu da Farimcikinsu Saboda Ahalinsu,Anty Safiya bawai ina Kuranta Yaya yusuf bane Domin yana Yayana ba A"a sai Domin Halin Mutum ka Fadeshi bai taba ganina Cikin Damuwa ya barni ba sai ya Tabbatar da Fuskatata cika da Farinciki Shiyasa nake matukar sonsa acikin Zuciya naji Dadi da kika Kasance Abokin Rayuwarsa Anty Safiya Ki Rikemin Yayana Amana ina mai Tabbatar Miki Baza ki Taba yin Nadama ba Domin yana Sonki kuma Shi din Tamkar Misalin mijin Maraniya ce.!
Ta karishe Fada Hawaye suna wanke mata Fuska Lokaci Daya tana Riko Hannuwan Safiya wacce itama kalaman Munari suka kara Raunana Nata Zuciyar Dayake Daman a Raunane.
Safiya ta Saka Hannu Tana Share ma Munari Hawaye Lokaci Daya Tana Fadin"Shii..Ki Daina kuka..Bayan Ya Yusuf yau nima gani Zan ninka Kulawar da yayanki yake Miki Fiye da Sau Goma Nayi Miki alkwarin Zaki Sameni mai kyautatawa da kulawa da abun da Mijina yafi so da kauna.!
Sai ga Munari na Dariya da kuka Tace"Da gaske..?Zaki zame mana Haske a wannan gidan Anty Safiya..? Wlh Farinciki ya Dade da Kaura a wannan Gidan Don Allah kizama Sanadiyar Dawomana da Farincikin da muka rasa..!
Sai kuka Jikin Safiya ya kara yin Sanyi ta kama Munari ta Rugume tana Lallashinta Lokaci Daya Tana Fadin"Da yardan Allah.ammh sai kin Bani Dukkan Hadin kai!
Munari ta Dago Tana Fadin"Insha Allahu ina Tare Dake..!
Safiya Tayi Mirmishi Tana Fadin"Yauwa..To maza Share Hawayenki Kuka ya Kare..Bani Labarin Ya imu..?Shi dai Duk da ban Zauna Dashi ba Yusuf na bani Labarinsa yafi ye Fushi da Zuciya ko..?
Munari na Share Hawayen tace Cikin Dariya,"Rigimamme kenan.ai Ya imu Dabam yake acikin Gidanmu..Bamai irin Halinsa..Shifa Ya Imu bakomai ke Damunsa ba Baya Shiga Abunda ba Ruwansa Ko kuma yayi shisshigi kan Rayuwar wani yafi Damuwa da kamsa Fiye da kowa abaya..Ya Imu yana da Wuyar Sha"ani ko kema sai kinyi a hankali kin bi a Sannu Zaki iya gane wasu Daga Cikin Hallayarsa,Yana da Murdaddan Halin Da bamai iyamai sai Allah Daya Hallicesa ko Abba sai dai ya Kada kai ya Bisa da Allah ya Shirya Ballatana Ya Yusuf Shi din kaifi Daya ne In yace Abu to baya barci sai ya Tabbatar Dashi Baya Saba mganarsa Mutum ne Dabaya karya,Baya kuma shayi ko Tsoron Fadin mgana koda Za"a Kashesa ne yana Da Dakakkiyar Zuciya irin na Jaruman Maza,Bashi da Fara"a ballatana yawan Dariya Miskiline sosai na Bugawa a ajarida Bashi da Sakewa da Mutane infact ma Baya son Mutane ya Imu yafi jinDadin Rayuwa Shi kadai Fiye da Cikin Mutane ko da yan"uwansa ne Bashi da Sakewa da Mata koda kannensa ne Koda Nice Bashi da Sakewa dani..Tsakanina Dashi ke ina wasa Dake ni..?ni sa"anki ne..?kin Raina mutane ko..? Tashi ki tafi Dakinki ki ba Mutane waje kafin na Sauya Miki Kammani..! Ya tsani Raini Shiyasa Tun yana amsa sunan Imran dinsa Baya Harkan Mata Nifa ko Daidai da Rana Daya bantanajin Yayi Budurwa ba,Ammy nasan a Yadda yake Kyakyawan nan wannan bazai rasa masu Sonshi ba Ni kaina Wasu Hallayar nasa suna Burgeni Barin ma Kaifinsa yana da Zuciya Bakar Zuciyar da in Ta tasomai kowa sai ya Tsorata,bazan Tsaya Misalta Miki ya Imu ba sai dai nace Miki Shi din na Dabam ne da Duk yadda kika ga kai ga Hangenki baki isa ki iya Ganosa ba Duka ba sai dai ki San wanda kika sani Shidin kamar Wahainiya ce kullum Chanza Launi yake..Baya Lallashi sai dai Shi a Lallasheshi bashi da Rauni ko kadan Dakiya garesa da Kafiya In aka Taba wani nashi nan ne Za"a ga waye Ya Imu Bashi da Sakin jiki da Ahalinsa ammh Acikin Kirjinsa yafi kowa sonsu..Na Rantsw har ga Allah ba wanda ya isa ya Dagama Gidanmu yatsa kafin ya Saukr ya Imu bai karyasa ba Salon Soyayyarsa ba irin Takowa bace tashi Salon ta Nuna kwanji ne..!
Munari ta karishe Fada Tana Sakin Mirmishi Safiya Tace"Ai nima nagani DAyazo Gidanmu Duk Fadan Abbu Sai da ya Sauraramai..!
Munari tace"Haka yake..Bashi da abokai Rayuwar Duniya bata Damesa ba..Baruwansa da kowa Shi kawai Rayuwarsa ya sani shi kadai sai Abokinsa Daya Sagir wanda Mamansa Abba yace ta Rakoki..Shi ne kadai abokin Ya Imu..Shima din abotarsu Wani kaddararran Lamari me Daga Allah..Allah ya Riga ya Hada Jinsu Bayan Kaunar abota akwai Kauna wacce Allah ya Hadata a tsakaninsu Duk yadda Imu yakai ga yakice Sagir bai Yakican mai ba,Dole ya Rabu Dashi zasu hadau suyi Fada kuma Duka Fadan Ya Imu ne ke jansa Shi Mutum ne da in ba kansa ba ko Allah sa ba bamai iyamai ammh Kuma ahakan suke Tare ko Daya bai Nemi Daya Daya zai nemi Daya kuma Dashi da Mahaifiyarsa kadai Muke Mu"amala kuma sune suke Shigowa Gidan nan kai Tsaye Batare da wani Shamaki ba..!
Safiya ta jinjina kai kafin Tace"Tabdijam..Wannan matar da zata aureshi nake Taausayamawa..!
Munari ta kwashe da Dariya kafin tace"Ai ba Matar da Zata iya Zama Dashi.. Nifa aganina..Shifa bai Damu ba..Da ya Imu yayi aure mace ta Rainasa Ya kuma zama akwai wacce yake kula da ita bayan kansa gwara ya To ya Mutu bai yi auran ba bari ma Kiji na gayamiki..!
Safiya ta Zaro ido tace'Bala"i..!
Me Munari Zatayi ba Dariya ba sai itama Safiyan tabiye mata suka yi Dariya Sosai Har da Tafawa Hira Tayi Dadi.
Safiya tace"Nidai bani Dan satan amsan yadda Zan zauna dashi..Kada watarana nayi mai Ba daidai ba ya Chanxamin kamani..!suka saka Dariya atare kafin Munari tace"Bazai Dake ba..Ai Baya Duka sai Ransa ya baci..Ko ni bai taba Dukana ba yasha Dai Fadan zai Dakenin a baki,Sai da mari ko tokari..kawai ki kiyaye baya son yawan gaisuwa,Baya son Hayaniya bayason ana Bugamai Kofar Daki ko kwana yayi bai Fito ba Kada wanda ya Nemeshi,Bai cika Cin Abinci ba yafi shan Fruit sai abu na Karshe Yana Shan Sigari kuma yana bata Muhimmaci..sannan koda baka son Warinta indai yana wajem Dole kayi Hakuri ka Shaketa ya tsani ka Toshemai Hanci Saboda gani yake Kamar shi kake kyama in kika Kiyaye wannan Babu wani abunda Zai Hadaku kila sai kuyi Sati Baku Hadu ba..Shi bamai Sakewa da mutane bane Yafi jin Dadin Rayuwarsa Shi kadai ko afalon nan baya Zama a koda yaushe in bai Fita ba yana Dakinsa ne..!
Safiya ta jinjina kai kafin tace"Ai indai Wannan ne zan kiyayemai kada Watarana yace Min Safiya Kin rainani ko..?
Gabadayansu suka Saka Dariya Suka Tafa jikake Tass..Har sai da kaji karan hannuwansu in ka kallesu alokacin kamar sun Shekara da sanin juna.
Safiya ce tace batayi Sallah mangariba ba jin ana kiran Sallar Isha"i Ita kuma Munari tace Tayi mangariba Saura Isha"i su tashi suyi Sallah kafin Ya Yusuf ya Dawo.
Nan suka Mike Safiya ta Fara Shiga Tayi alwala itama Munari Ta Shiga Tiolet din Yusuf tayi Alwala Dayake ita ke gyaran Dakin koda yaushe ba inda bata sani a ba adakin.
Tare sukayi Sallar adakin Safiya tayi mangariban ta Ta Dora da Isha"i Ita kuma Munari Tayi Sallar Isha"i din da batayi ba,bayan sun idar suka Dasa kuma wata Sabuwar Hira Zuciyoyinsu ta Cika da Farinciki ita Munari ta Murnan Zuwan Safiya a Rayuwarsu Farincikin da suka rasa zai Dawo ta kuma Samu abokiyar Hira ita kuma Safiya Tana Murnan Ta samu kanwa Bayan Tasleem,Bazata yi kewa mai yawa ba,kuma nasan Ta Tabbata bazatayi nadaman Auran Yusuf ba.
Suna tsaka da Hiran nasu
Daidai Lokacin Yusuf ya Turo kofar ya Shigo da Sallama da Ledoji Guda Hudu a hannunsa na Tambarin kamfanin Gidan Abinci.
Yadda ya gansu sai da yaji Zuciyarsa Tayi sanyi,Suna ganinsa suka Mike Ita Safiya Tana gyara Zaman mayafin kanta Ita kuma munari baki ta washe Tana fadin"Sannu da zuwa Ya yusuf..!
Lokaci Daya tana karisa garesa da Niyarvkarban Kayan Hannunsa.
Bakinsa Shima a washe ya amsa mata Lokaci daya yana kallon safiya yace"Babe kina samu akun Abba ko..? Nasan munari tayi keeping dinki Company..Nasan kanwata akwai son Hira..!
Safiya kanta na Kasa ta Murmusa Tana wasa Da Gefen Mayafinta tace"Yes She so so Nice..I love her..!
Munari najin Haka ta saka Tsalle Tana Dariya Shima Yusuf din sai da ya Dara Lokaci Daya yana Fadin"Ke kullum baki san kin girma ba Lilsis..? Above 20 fa..Kuma kina Yar jami"a Nan da Shekaru uku masu zuwa u are Going to become a Graduated in Ecocomics..!
Sai ta Daina Tsallan Ta koma ta Natsu Tana Fadin"Wlh kuma hakane Yaya..Na bari..Yanzu ai am Mature ko..?
Tafada Tana nuna masa kanta Dagashi Har Safiya sai da suka Dara Ledan Dake hannunsa Guda Uku ya mikama Munari Dayan kuma ya ijiyeta nan kasa sai dai ta karba yace mata"Ur Dinner..!
Munari ta karba Tana Fadin"Allah yasa Fride rice ce Ya yusuf..!
Yana Dariya yace"Mayar Fride Rice itace..Ki Dauki Dayan Ledan Is Urs..Daya kuma na Abba ne ki Tabbatar kin Bashi yaci yasha Mgani ya kwanta..Dayan kuma is for ur Brother Imran..!
Munari tayi Narai Narai da ido Tace"Is He at Home..?
Yusuf yace"Check his Room..!
Munari ta Kara narke fuska Tana Fadin"Kasan He warning me kan Bugamai Room dinsa ko Ya yusuf..? In ba so kake ya Sauyamin dis My Beatifull Face ba is ok sai naje..!
Yusuf ya kada kai yana Mirmishi yace"Shikenan ki aijiye Cikin Frigde din Kitchen if He Wanta Zai Shiga ya Dauka..Daman Choice dinsa ne Kayan Lambu!
Munari tace"Tanque Ya yusuf..Sai da Safe..Anty Safiya see u Tomorrow..!
Tafada tana Daga mata Hannu itama Safiyan Dagamata Hannu Tayi Tana Fadin"Ok see u Lilsis..!
Daga haka ta Sa kai zata Fice yusuf ya Kirata ta waigo yace mata"U make Sure kin kwanta da Wuri..No Chart no Reading ko..?
Kai ta gyadamai Tana Fadin"I promise u bazan yi ko Daya Daga ciki ba sai Barci..Basai kazo Dubani ba Ka zauna ka kula da Anty Safiya Dakyau asha Amarci Lafiya..!
Tana Gama Fadar haka ta Fice da Gudu ta Rufo Musu kofar suka Bita da Dariya dukkansu.
Sai alokacin Yusuf ya juyo zuwa ga Safiya ya Fara takawa Zuwa gabanta Idanuwansa kyam a kanta Ita kuma gabanta na Fadi kanta na kasa.
Sai da ya iso gabanta bata Tsammaci Haka ba taji ya Rumgumeta Kamkame kamar wani Zai kwaceta sai kuma Taji ya saki kuka Cikij kukan yake Fadin"Tanque so Much Babe..Kin yimin Abunda Har na koma ga Allah bazan manta ba..Allah ya bani ikon Rike ki Cikin Aminci da kauna kamar yadda kika Nunamin..!
Sai kuma ya kara Sakin mata kuka Tuni Taji ta Rude itama bata san Sadda Ta Saka hannu ta Rumgumeshi ba ta Saki nata kukan Tana Fadin"Basai kamin Godiya ba..Ka Chanchanta My Dear..Kaunarka gareni ce ta Sanya ka ganni Tsaye acikin Dakin nan a kuma Cikin Gidanku nidai Fatana ka Rike da Amana My Dear Ka soni Sosai Fiye da yadda nake sonki..!
Yusuf na jan Majina yake Fadin"I do..Wlh I do..!
Haka kurum yake Fada Kamkame Juna Sukayi kowannensu na kukan Fitar da Abunda ke Cikin Ransu Har sai da suka gaji suka koma suna Lallashin Juna gefen gado ya jata ya Zaunar da ita kan Jikinsa yana Fadin"Babe don Allah kiyi alfarman bazaki gayyatomin kowa Daga Barayinki ba Nan kusa Har sai na gama Gyara Miki Bangaranki na Saka miki komai na kuma yi miki kayan Lefen da kowani Namiji ke yi ma wacce yake matukar so ya ganta Zai Aura..!
Safiya ta Sakarmai Ido Cike da kwallah Kafin tace"Ban yi maka wannan alfarman ba My Dear..!.
Cikin mamaki ya Tambayeta"Saboda Mene Babe na..?
Safiya ta Runtse ido ta bude kafin tave"Kayan Lefe na yafe maka su..Kayan Daki kuma ai ba Harumin ka bane na Iyayena ne..Ni ka kyaleni nan Dakin bai Ishemu Rayuwarmu bame Dagani sai kai..?
Ga falo chan ga Kitchen ga komai na Bukatar Rayuwa..?me kuma nake nima Ni Safiya banda Kwanciyar Hankali da Zama Lafiya da Mijina da Sabon Gidan dana Tsinci kaina..!
Ta karishe Fada Hawaye suna kwanroyomata Da Sauri Yusuf ya Rumgume tsam yana Fadin"Ba Saboda Ke zan yi kayan fa..Saboda kaina ne ki Rika sakawa kinamin kwalliya Dasu..Mganar Kayan Daki kuma ba Ruwanki Zamu koma wanchan bangaran nan da wani Lokaci ba Saboda ke saboda kyawawan Ya"yan da Zaki Haifamin nan gaba..Ni su Abbu sun gama min komai Tunda suka Bani ke bana Kuma Bukatar Komai Daga Wajensu!
Ta Dago kanta ta Bude baki Zatayi mgana ya Hanata bayan ya Dora Hannunsa saman Lebenta yace"Shii...Zamu je mu gaishesu in muka Samu Natsuwa..Ammh all i say hakan ne Zai Faru..!
Bata da ikob Sake mai gaddama sai ta koma Bisa Kirjinsa ta Lafe yana Rike da ita kamar wani zai kwaceta.
Ahaka ya sauko Da ita saman Cafet ya jawo Ledan dan ya Fito musi da Takeway din Daya yi musu sai kaZa Gashashiya da yourghot,mai Sanyi Dakyar taci Shinkafar ya Hadamata da Kazan da Madaran sai da ta kusa amai ya kyaleta kana Shima yaci Sosai yasha Madaran Daga gani kila ya Wuni bai ci komai bane Kamar Tayimai Hawaye,bayan sun gama Tana Nokewa ya kwasheta zuwa Tiolet ya sakarmusu Shower Dole suka yi wanka Bayan sun gama Nanikan juna Duk da Yusuf din bai mata komai ba sai dai Rumguma da Kiss haka.
Alwala suka Dauro,ya jasu Sallah Raka"a Shida Bayan sun Idar yayi musu addu'o"i sosai na Zaman lafiya kafon suyi Shirin Barci Shi ya Bude akwatin Safiya ya Dauko mata Wata Rigar barci guda Daya wacce wajen Tuso kayaneta Shigo ammh ko Barayin kayan Barcinta bata Bude ba Tana Nokewa Tana komai ya Dauketa ya aza kan gado ya Cire mata Doguwar rigar Data sakata yanzu Tunda kayanra sun Jike suna Tiolet Yusuf ya Shanya mata.
Hakan nan ta Runtse ido ya sakamata Rigat barcin Shima ya Tube Dagashi sai Boxers ya Hayo gadon ya Ciccibita ya sakata Cikin Jikinsa ya Nadesu Cikin Blanker Bayan ya Rage Hasken Dakin yana jinta yadda Take Mutsu Mutsu da kuma yadda Zuciyarta ke Bugawa.
Cikin Mirmishi ya Sunkuya kunnenta Yayi mara Rada yana Fadin"Relax babe Babu Abunda Zan yi miki ayau din nan..Ban kuma ce Gobe ma haka ba kawai dai kafin mu Zama Daya Dani Dake nake so na baki Labarin GIDANMU..labarin da kika so kiji ban Taba Fadamiki ba Labarin da ban Taba Gayama kowa ba sai ke yau din nan..Ba saboda komai ba sai Saboda Daga yau din mun Riga mun Zama Abu Daya Komai nawa naki ne Komai naki nawane haka Sirrina naki ne kamar yadda Sirrinki yake Nawa Babe na..!
Safiya Dataji Abun kamar a Mafarki ta Dago da kanta bata ganin Fuskarsa Saboda Duhu sai dai tana iya ganin Shedar Fuskar tashi Cikin Tsananin Farinciki ta Damke hannunsa Tana Fadin"are u Serious..!
Kai ya Gyada mata kafin yayi mata Kiss a goshinta cikin so da kauna Rumgumesa Tayi sosai Tana Fadin"Tanque Dear..Uhm...Am all Hears..!
Yusuf ya kara Riketa ajikinsa Bayan ya zagayo da Hannyensa Bayanta zuwa Saman Cikinta lokaci Daya ya Sauke ajiyar rai Dana Zuciya Tuna abunda ya Faru dasu Shekaru uku Zuwa Hudu da suka gabata.






*Shakira...*
3/22/22, 23:04 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*DEDICATED TO:*
*Aisha alto(Sisinah)*
*Chubado muhammad(Uwar dakina)*
*Yahanasu Soupnass(Qawalli1)*
*Kausar salis(My jika)*
*Rahma Ladingo(Dota)*


         *🅿?13*

*DR.ABUBAKAR HAMISU DUKKU* (Malami) shine Asalin sunan Mahaifinmu,Dr ne a bangaaran Ilimi kuma Malami ne Daya shafe fin shekaru Goma yana koyawar a Jami"ar Lagos, Wato a University of Lagos Fanni Sanin Hallayar Dan Adam Wato Phsychology
Sunan Malami kuma da Abbanmu ke Amfani Dashi ya samu asali ne akan Tun yana karami yake kaunar Zama Malami Dalilin haka yasa Mahaifinsa Marigayi Alkali Hamisu Dukku ke kiransa da Malami Tun yana amsa Sunan Abubakar Hamisu Dukku Har Dukkun ya bace bat ya koma amfani da Abubakar Malaminsa Duk wanda ya sansa da wannan Fitattacen Sunansa ya sansa.
Mahaifinmu asalin Bafullatanin Gombe ne ta Uwa ta Uba,Daada da Marigayi Alkali Dukkansu Haifaffun gombe ne,A karamar Hukumar Dukku Dake Jahar na Gombe.
Awajen Mahaifinsu su Biyar ne Uku Maza Mata Biyu Abba ne D"a na Biyu awajensa,Akwai Baffa Kabir,sai Baffa Mustapha,sai Goggo Bintalo sai Karamarsu wacce Munari taci Sunanta Maimunatu.
Abaya kafin Rayuwa ta Juyamana Gidanmu Gida ne na Soyayya da kaunar Juna da kuma Hadin kai.
Mahaifiyarmu Hajiya Zuwaira auran Zumunci ne Tsakaninsu da Abbanmu,Domin Daada Mahaifiyarsu Diyar kanwartace ta Dauketa ta Riketa awajenta Har ta aura ma Abba ayadda Anni ta sanar Damu Lokacin Abba ya kawo wata tace da Niyyar ya aura Wata Shatu wacce suka Hadu da ita a Jami"ar Jos,inda yayi Karatu Sai Daada Ta nuna A"a ta kuma wanke Mahaifiyarmu Anni ta bashi bai Mata Gaddama ya saka Hannu Bibbiyu ya karba Domin Shi Mutum ne mai Sanyin Hali da Biyayyah.
Da Farko ba a Lagos su Abba suka Fara Zama ba sai da suka zauna a nan Cikin garin Gombe,Lokacin yana Assistan Lacture ne a jami"ar Gombe Bayan Kamallah Degree dinsa na Biyu ne Ya samu aikin Bayan auransa da Anni kuma ya Daukota Zuwa Gombe.
A garin Gombe aka Haifi Yaya Nura da Ni da kuma Imran Sai Zuwa Lokacin Abba ya gama Hada Phd dinsa Ya samu Sauyin aiki Daga Jami"ar Gombe da Tuni Daman ya koma mataayin Senior Lacture.
Muka Tattara muka koma Lagos da zama acikin Tsakiyar garin Lagos A wata anguwa mai suna Vitoria Inland..!
A lagos muka Dora Sabuwar Rayuwa,Daman Tun a gombe Ya Nura da ni mun Fara zuwa makaranta Dayake Dukkanmu Har Imu Haihuwa Kai kai ne Cikin Shekaru Hudu Anni ta Haifemu mun taso Gabadayanmu kanmu Daya ne,Da muka koma Lagos ne Abba ya Sanyamu a Wata makarantar kudi mai kyau mukaci Gaba da Zuwa,A kuma garin ne aka Haifi Asma"u da Salima sai Munari Itace Auta.
Yusuf Daya kawo nan a Labarinsa Safiya Taji shuru Tana jinsa ta Muskuta ta Dago tana kallonsa jin yayi Shuru Duk da bata ganin Fuskarsa Tace"Ina jinka My Dear sai akayi yaya..? Ina Anni ina Ya Nura da Salima da Asma"u..? Ina kuma yan uwanku na Dukku Sauran Yan"uwan Abba..? Kuma wani Dalili ne ya Dawo Daku Rayuwa A kano Bayan komai naku yana Lagos..? Me kuma ya Faru da Abba Har ya samu wannan Rashin Lafiya..? Kuma meneme ainihi yake Damunsa..?
Ta karishe Fada Cikin zumudi da son Jin karshen Labarin Gidansu Yusuf.
Yusuf Da Jikinsa yayi sanyi Baya son Tuna Labarin nan ko kadan Ammh Ya Zama Dole ya Karishe ma Safiya Labarin nan ko Zata Fahimci ba Wai Da gangane ko Rashin asali ne ya Maidosu Rayuwa su kadai ba Wani Kadaddaran Al"amari ne da Allah ya Riga ya Rubuta sai ya Faru.
kara kamkameta yayi ajikinsa Kafin ya Cigaba da mgana Cikin Sanyin Murya da Sarewa.
Mun taso Cikin Soyayya da kauna ta Kowani Fanni Abba Mutum ne mai Dattako da Sanin ya kamata mai kula da Iyalansa da Danginsa Duk da muyi Nisa ammh kusan Duk wata yana Hanyar Gombe zuwa ganin Daada Bayan Rasuwar Mahaifinsu Alkali Hamisu Wani Lokacin Tare da Anni suke Tafiya wani Lokacin kuma Shi kadai mu kuma muna Zuwa makaranra Tun safe sai yammah in mun Dawo gida akwai malamin da Abba ya Daukar mana yana Koyamana Karatun addini Sakamakon ba Lokaci sai ya kasance sai mu Fi Shekara bamu Taka garin Gombe ba,gwarama ya Nura Dani mukam bi Abba Gombe in zai je Hutun Karshen Shekara sai abar Anni da su Asma"u a gida Kafin mu Dawo Shiyasa Duk Cikin mu muka Sanin Dangi Dangi ma suka fi Sanin mu.
Lokacin gaskiya Zumunci yafi karfi ta Bangaran iyayanmu mu ya"ya bamu Damu dashi ba Kowanne ya"yansa na makaranta gashi ba"a zaune waje Daya,Ballatana arika Ziyarar juna akai akai Ballatana asan juna Sosai.
Bamu san kowa ba sai Abba da Anni sune Duniyarmu Gaba da Baya Abba ya Sadaukar da komai nashi Saboda mu Anni kuma ta Sadaukar da Lokacinta da Lafiyanta Wajen Tarbiyantar damu da kula da mu,Lokacinta da komai namu ne Muna Matukar sonta da kaunarta Domin Duk Fadin garin Lagos Daga Anni sai Abba sai sauran yan Gidanmu kadai Muke Dashi Duka Dangi Basa kusa Baffa Kabiru yana Abuja Baffa Mustapha yana Kaduna Sai Goggo Bintalo tana aure a gombe ne Goggo Maimuna kuwa Tana aure a Bauchi ne Daada kuma Tana Asalin Gidansu na Dukku ne sai dai Aje Chan adubata.
Duk Cikin mu Imran ne kadai yayi makarantar kwana acikin Garin Lagos yayi karatun Karamar Secondary Dinsa har Zuwa babba Primary ne Kadai yayi ta Jeka ka Dawo,Ba wanda Yayi mamakin Zabinsa Saninsa Shi bamai Son Sakewa da Mutane bane da Hayaniya Shiyasa yana garin Lagos ammh Sai an Samu Htu kamar Sauran Dalibai yake Zuwa Hutu Gida Shiyasa Gwara Kowa Dashi Ko Dukku Sai ya fi Shekara uku bai Taka ba,ko ya Dawo Hutu in Abba yace ya Shirya aje Dashi Sai yacFara Ciwon karya Saboda Bayason Zuwa Ballatana ya Shiga Mutane ko acikin Gida kowa yana Zaman Falo banda Imu Shi din Hallitarsace Miskilanci da Rashin Son Sakewa,Kowa Daya Fahimci halinsa ne sai kowa ya kiyayemai Ammah banda Asma"u itace Sakon sa Shiyasa Take Shan Wahalansa Kusan in ya Dawo Gida Hutu Kafin ya koma Sai ya Barta da Tabbai Akwai Lokacin da Ya Daketa Har sai da ya Sumar da ita Ran Anni ya Baci ta Mareshi Shine Imu yayi Fushi Lokacin yana Farkon Shiga SS3 NE daya Koma makaranta bai kara Waiwayan Gida ba sai da ya Zana Jarabawarsa Duka ya gama da makaranta ya Dawo Lokacin Ni da Nura Mun samu Gurbin Karatu a Jami"ar Lagos,Tsakanina Dashi Shekara Daya ne shiyasa Karatun namu yake Tafiya kai da kai.
Abun bai bama Kowa mamaki ba Da Imran ya Cike Jami"ar Ibadan,Sanin Halinsa Chan ya Tattara ya Tafi karatu inda ya Zabi bangaran accounting,Wani Lokacin sai ayi Hutu Nawa bai zo Gida ba sai dai Abba Ko mu mu kai Ziyara Abba ma yafi Zuwa wani Lokacin in ya Dawo Daga Gombe yana Biyawa ta Wajensa Tunda Shi ya Haifi Abunsa yafi Kowa Sanin Halin kayansa Anni

Please Login or Register in order to submit comment