Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Tana matukar jin dadin Hutunta agida,kwananta Hudu da Dawowa taje gidan su Nasara Ta wuni Daga gidan ta Biya badarawa ta gaida Inno da Mallam Babba sai Dare Muda ya Rakota ta Dawo gida aranar ne da Daddare Munari ta kira Suka gaisa da Umma Harda Anty Safiya bayan sun gama mgana ne Inteesar ta Nuna ma Umma Hotonsu ita da Munari da suke Dauka a makaranta Umma ta kurama Munari ido a Fili tace Kuna kama da kawarki taki Inteesar.
Inteesar tace mata haka kowa ke Fadi Umma kinsan ance kawayen juna wani Lokacin kamarsu na Rikidewa Umma na Dariya batace komai ba Suna Cikin hakane sai ga Daddy ya Shigo Daya Tambayi me suke ma Dariya Umma ta Fadamai bai ga Hoton ba Umma tace ya bari ya Huta Daganan ya manta itama Inteeesar din sai ta sha"afa.
Har gidan Ya Basheer taje ta kwana Biyu Dakyar kamar tana kan kaya ta Mtsa sai da ta koma Gida,Suna Waya da Mama Da Sagir Lokaci bayan Lokaci suna gayamata sunyi kewarta..
Munari kuma kusan kullum sai sunyi mgana da juna ta waya ko ta WathApps.
Kwanan Inteesar goma da dawowa Daga kano ta fara Zazzabi mai Zafi Wanda sai da ya kwantar da ita a asibiti.
Maleria ce ta mata mugun kamu,Sauron kano sun Debi Rabonsu Daddy nata Fadan meyasa ba"a saka mgani agidan Mama tunda akwai sauro Inteesar ta dawo da Maleria.
A dakin da aka kwantar da Inteesar din ne a kebantattacen Daki na Musamman,Asibitin kudi ne,Ya Basheer da Umma da Anty Hauwa da ya"yansu su Abiden din adakin Daddy ke ta Fada Tunda Likita yace Maleria ce ta kama Inteesar mai Zafi.
Ran Umma ya baci ta Dubu Daddy Tana Fadin"Haba Abban Intee kadaina Fadin haka fa kamar baka yarda da kaddara ba? Kuma daka ke Fadin an barta Sauro ya Cijeta Ita Ya Aminan zata zauna tana kula ita kada Sauro ya Cijeta ko..? Kuma ita da Sagir Da suke gidan Su ba Mutane bane Inteesar ce kadai Mutum Tunda yar so ce..!
Tafada Tana Bayyana Bacin Ranta Har Daddy zai yi mgana Basheer ya Girgiza mai kai ganin kada su Fara Fadansu na Fama gaban Suruka.Dole tasa Daddy ya bar mganar Ammh Umma sai Huci take ranta yagama baci.
Wasa wasa dai sai da inteesar ta Kusa Share Sati a asibiti,Saboda da taji Sauki Likita yace zai Sallameta Daddy ya Hana yace sai ta kara Hutawa kwana Shida tayi ta koma Gida Munari ta sani Tunda Data Kira Wayar Inteesar din Umma ta Dauka Ta gayamata Tana asibiti bata da Lafiya Hankalin Munari ya tashi Ta kuma tashi Hankalin su Abba bata Kwantar da Hankalinta ba sai da Taji Inteesar Ta samu Sauki har an sallamo su Daga asibiti ta Dawo gida..!







*Shakira*
3/22/22, 23:06 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️*




*🅿?24*

Duk abunda ya faru Imran bai sani ba Kowani Dakika da kuma Wayewar gari Inteesar na cikin ransa yana kuma Kirga kwanaki da Ranar da Hutunsu zai kare,Domin tun yana Daukan Lamarin wasa har ya fara ganinsa da gaske ne,Domin baisan wani yanayi yake ciki ba ammh Tabbas da Tunaninta yake kwana dashi yake tashi yana jinsa kamar ba Daidai ba in bai ganta ba yana jinsa kamar ya rasa wani kuzarinsa ne da Tatafi.
ya zauna yayi Tunanin meye Hadinsa da ita da Har Tunaninta yake Hanashi Sukunu ya kasa gano bakin Zaren yanzu ya daina Tunanin Tayi mai asiri sai dai yafi Tunanin kila shine Aljanun suka shigeshi Shiyasa ya kasa Gane kansa Kwata kwana.
Afarke yake ko cikin Barcinsa Inteesar ce take giftamai abum kamar almara Ko yana zaune ne yana Kallon wani Waje Fuskarta yake gani Mganarta kuma namai amsa kuwwa acikin kunnuwansa Saboda ita yanzu ya Rage shan Sigari koda ya Daukota zai kunnata sai ya Tuna da mganarta yaji kawai bazai iya Saba mganarta ba Duk da bai mata alkawari ba sai da yaji yana son ya Daraja mganarta akalla ko bata Dawo ta gansa ya Daina sha ba ta Gansa ya Rage shanta Fiye da baya ba kuma domin yana Tsoron kada Tamai Lahani ga Lafiyarsa ba wannan baya gabansa Ya sani Shi Tuni Lafiyarsa ta Samu Tawaya.
Ko alama baisan bata da Lafiya ba Saboda ko Sagir bai taba mai Zencenta ba kuma Saboda ita yake zuwa Shagon akai akai Koda Hirarta ne yaji Sagir din yayi mganarta shi kuma ko Sau daya bai taba mai ba Shi kuma Ego dinsa bazai taba barinsa ya Tambayeshi ba.
Ko agida bai taba jin Mganarta ba Saboda baya zama cikin su Munari ce Ke da Labarinta kuma baya Sakarmata Fuska ba,ballatana yaji wani Zencenta kuma bashi da Lambarta ballatana ya Kirata Ko da ma yana Dashi bazai iya Kiranta ba Saboda yana ganin ai bashi da wata alaqa da ita Abun na Dauremai kai Ko Lokacin dayake amsa sunansa na Imran Wata mace bata taba Burgesa ba Ballatana yanzu Daya Juyama Rayuwar jin Dadi baya,Abun kunya ne babba agareahi wani ya Fahimci Halin Dayake ciki Dalilin haka yasa ya Rage yawan Walwalwarsa Fuskarsa kullum tana Hade ba Fara"a koda bai da yawan mgana ballatana Yawan Dariya Ya yusuf da Abba sun Fahimci wani abu na Damunsa sai dai sun sani koda sun Tambayesa bazai taba Fada Musu ba Imran yana da Ego gayama wani abunda ke Damunsa koda Damuwar abun zai kasheshi ne ya Gwammace ya bar abun shi kadai baya son yadda Ransa ya baci kan al"amarin ya Raba Bacin ran da wani nashi.
Shiyasa yake ta Kokarin yakice abun acikin ransa,Bayason Tunanin Inteesar din tarabi Tunaninshi Sai dai ya kasa Controlling kansa da Tunaninsa Kowani Tunaninsa da Motsinsa Tana makale acikin Ransa da Zuciyarsa Kamanninta da mganganunta sun kasa bacemai acikin Idanuwansa da Kwakwalwarsa.

***
Sunday.
10:03am na safiyar Ranar Lahadi.

Abba ne da Ya yusuf sai Anty Safiya da Munari zaune kan Dining suna Breakfast,tunda yau din Lahadin karshen mako ne,Ya yusuf na Gida cin abinci Sukeyi batare da kowa yayi mgana ba bakajin komai sai karam Cokula da karan Mug din Tea.
Ya yusuf ne ya Kurbi Tea kafin ya maida Mug ya ijiye yana kallon Abba Dayake cin Soyayyan kwai ahankali ammh Rabinsa Hankalinsa baya kan abunda yake yi ya tafi wani Tunanin nadabam.
Ya yusuf ya gyara Zama yana Fadin"Abba badai Tunanin zaka Dawo dashi ba..?
Yafada yana kallonsa Abba Daya Sauke ajiyar Zuciya ya ijiye Fork din Hannunsa yana Fadin"Kunyi mgana da Dr..?
Yusuf yace"Eh jiya na kirashi yace...!
"Wannan watan da kaina zan je asibitin..Kuma ina Fatan ya zama na Karshe Tunda alhamdulillah na Warke da yardan Allah..!
Abba ya katesshi yana fadin hakan Yusuf ya kalli Safiya itama ta Kalleshi Kafin ya maida kallonsa kan Abba yana Fadin"Alhamdulillah Abba haka nake son ji..Allah ya kara Lafiya Gobe Kafin na wuce wajen aiki sai muje Tare In Allah ya kaimu..!
Abba ya gyada kai bai yi mgana ba Munari Dake gefe ta Tusa Dankali da kwai bakinta tace"Abba Am so Happy..!
Kamta ya shafa yana Fadin"Ki daina mgana hakan kada ki kware Munarin Abbanta..!
Kada kai tayi tana Kokarin Daukan Mug din Ruwan tea din Dake gabanta ta kurba ko abunta ta saka abakinta yawuce mata.
Abba ya Dauki Tissue yana Share Bakinsa Lokaci Daya yana Fadin"Yanzu ai nafi kowa sanin Illar Damuwa da Tunani Tunda Sanadinta yasa nayi nesa da komai nawa Ciki Harda yan"uwana da Mahaifiyata..Nasan Zafin Rashin naka sosai na kuma san Zafin Mutuwa Wanda cikin Zafinta nake har yau har gobe..Sai dai na Dauki kaddaranta nasan Mutuwa ta Allah ce kuma Kaddara Musulmi takaci..Mu kanmu Watarana zamu mutu duka munbar Duniyar muje mu Tarar dasu..Ni yanzu Addu"ata garesu Allah ya jikansu da Rahma Allah yasa sun Huta..!
Gabadayansu suka amsa da Ameen Cikin wani yanayi Abba na Shirin mikewa Yusuf yace"Abba Daman Ina son mgana Dakai..Kan Imu ne..!
Abba ya koma ya zauna yana Fadin"Meya samu shi Imran din..?
Yusuf yace"Abba kafi kowa sanin Imran na Bukatar Taimakon mu sosai..bazamu zura ido Rayuwarsa ta tafi a banza a Shan Taba ba Abba We hv to do Something..!
Abba yayi Shuru yana wani Tunani kafin ya kada kai yana Fadin"Kamar wani mataki kake ganin zamu iya Dauka kan Hana Imran Shan Sigari Yusuf...?
Kafin ya bashi Amsa Safiya ta Mike Zata bar wajen Abba ya Kirata ta Dawo Cikin Dattakonsa yace"Koma ki Zauna ina zaki..?
Cikin Ladabi tace"Abba zan koma Daki ne..Naga kuna mgana ne..!
Abba yace"A"a koma ki Zauna..Meye baki sani ba..?wannan gidan kema Kamar Gidanku ne zauna mganar Dukkanmu ta Shafemu..!
Bazata iya ma Abba gaddama ba, yasa ta Koma ta Zauna tana gyara Zaman Vail din Data yane kanta dashi.
Abba ne ya maida Hankalinsa kan Yusuf yana fadin"Umh ina jinka Wata Hanya kake ganin zata Bullemana..?
Bayan Nasihan Dakemai nima kuma inamai ita bai Daina ba..?
Yusuf yace"Eh to kamar mu nema mai Taimako wajen Malaman addini na addu"a Abba..Ko da bana shan sigari ba..Na bakar zuciyar nan Abba da rashin son zama cikin Mutane..!
Abba ya kalli Yusuf sosai Kafin ya dan Murmusa Cikin Dattakkonsa yace"Ba wani Taimakon da zamu nema mai Yusuf..Kafi kowa sanin Imran kamar yadda nasanshi bazai bamu hadin kai ba..Taimako Dayane kawai ya Ragemin agareshi zan koma cikin Ahalina Ina da Mahaifiya Hakkin Daada yana kai na matukar ina da rai da Lafiyata In na koma gareta Cikin yan"uwana zan basu dama su Zartar da Hukunci kan Rayuwarsa na Tabbata bazasu barsa haka ba..!
Yusuf ya kada kai kafin yace"Abba Inran din zai yarda wani bakai ba ya Zartar da wani abu akan Rayuwarsa..?bama haka ba Abba Bana jin Imran zai yarda ya koma cikin Yan"uwanmu Domin kullum ikirarinsa kenan..!
Abba yace"Shi ne zai bani Umarni ko nine zan basa..?
Ya yusuf ya kada kai kafin yace"Kai ne zaka bashi Abba..!
Abba ya Cije baki kafin yace"To bai isa na bashi Umarni ya Tsallake ba..Koda kaga ina Dagamai kafa na Dan Lokaci ne..Zamu koma Cikin yan"uwana Lokaci kadan da yardan Allah In yaga Zai iya Binmu ya kyauta ma kansa in kuma Taurin kansa ya Hanashi sai yayi Ta zama ni baruwana dashi..!
Yana gama Fadin haka ya Mike Da sauri Munari tace"Abba Lagos zamu koma ko Dukku..?
Ya waigo yana Kallonta kafin yace"A"a ba inda zamu ai nam din shine GIDANMU munari..Lagos kuma Zaman achan ya kare bazan iya Zaman garin ba..Dukku kuma Zamu jene ganin Daada da Sauran yan"uwana In Allah ya yarda..!
Munari tace"Abba kenan nan zamu Cigaba da Zama har Abada..!?
Gyada mai kai kafin yace"Da yardan Allah..Shine gidanmu..!
Washe baki tayi tana Murna kanta Abba ya Dafe kafin ya wuce bai Tsaya afalo ba ya shige Daki Daga gani mganar Imran ta Dameshi Sosai.
Yusuf ya Sauke Numfashi batare da yayi mgana ba ya Mike shima ya Wuce Shashensu Itama Safiya ta Mike tabi bayansa bayan ta bar ma munari Sallahun in ta gama ta Kwashe komai takai Kitchen tace mata Toh
Chan taje ta bama Yusuf baki Domin Taga Shima duk ya Damu,Abunda ta Dade Tana Nusar dashi kenan kan Neman Danginsu sai gashi yau Abba ya Furta da kansa sai mganar Imran shi kuma Wata mganace ta Dabam baka isa fa ka Chanxa Abunda Allah ya Hallicesa ahaka ba sai dai kayi iya Bakin kokarinka ka barshi yadda yake.
Sai dai kila Mace zata iya Sauyashi Watarana Indai yana sonta.
Haka Safiya ta Fadama Yusuf mganar Dariya ta bashi sai da ya Murmusa kafin ya Kalleta yana Fadin"Wata Macen ne zata juya Imu..?ban jin akwai wannan macen Baby..!
Bata iyamai gaddama ba Tunda ko ta Fada bazai yarda ba su suna ganin bamai iya Lamkwasa sa ita kuwa Tana Hange Imu Wani Lokaci anan gaba da Mace zata Zama tanajan Ragamar Rayuwarsa.

*****

*Dukku local goverment*
Area:Balikaje.

Kamar yadda take Ranar Lahadi a garin kano haka take Lahadin karshen Satin agarin na Dukku.
Yau gidan na Daada yana Cike da Mutane ne kama Daga ya"ya zuwa Jikoki,Tun jiya asabar Wasu suka sauka kamar su Inna Maimunatu da Inna Bintalo su da gayyar ya"yansu da marasa auran da masu auran duka suna Gidan Daada,Tun safe kuma Baffa Kabir ya sauka shima Tare da Mami Asma"u da ya"yansu duka Uku Wato Sajida da Umaima da Khamis wanda wannan karon Dolensa ya bar Aikinsa ya Taho Saboda Kiran Daada.
Baffa Mustpha ne karshen Zuwa Misalin karfe 11am na Safiya suka iso Bashir ne ke jan motar Umma da Inteesar da Hauwa suna Baya sai su Abiden Dake jikin Umma.
Inteeesar tun da suka Dauko Hanya bata iya cewa kala ba Bakinta kuwa ta gaji da Turasa ma ta Hakura ne bata so zuwa Dukku ba har ga Allah hakan baya Cikin Adanjanta Gobe ne suke Komawa Makaranta ta Fara Shirya kayanta Zata dawo ko Laraba ko alhamis Domin har mgana sunyi da Munari Zata dawo haka Kurum taji bata Kyauta ba in ta sabama Ya Imu alkwarinsa kuma ya gayamata Baya alkawari in yasan bazai cika ba kuma Shima bayaso ayimai in har baza"a cika ba..
Bata so ta karyamai Zuciya da Saba alkawarinta shiyasa ta Fadama Daddy zata koma Ranar Alhamis ko Laraba kuma ya amince mata har yayi mata alkawarin zai maidata kano da kansa Har Umma ta fara mata Shirin komawa Tunda har Mama ta kano sun yi mgana tace mata Intee na tafe Cikin Satin nan mai shiga kawai Rana Tsaka Ranar jumma"a Sai ga Kiran Baffa Kabir yana Fadama Daddy Daada Tana chan tana kuka Baba Asabe ta Kirashi ta gayamai shine yace abama Daada Wayar yana Tambayanta me ya faru nan take fadin Tana son ganinsu dukkansu kwansu da Kwarkwatansu Bata son ace mata wani baya nan ko yana makaranta ko yana Wajen aiki Dasu da duka ya"yansu take son gani kafin gobe a Dukku Domin Tana so ta Hada kansu ne kafin Ajali ya Risketa.
Ba Lallashin da bai mata ba ta Kafe kan mganarta Dole ya Kira Daddy ya Fadamai bayan ya Kira Su Inna Bintalo ya Shaida musu Halin da ake ciki Shine nan fa Kowa ya Tarkato Iyakansa ya Yada Zango adukku Gidan Tsohon Marigayi Alkalin Alkalai Hamisu Dukku.
Baffa Kabir Daman Khamis yazo Gida a Ranar zai yi kwana Biyu ya koma sai ga Kiran Daada Sajida kuma suna Hutu Tana gida Umaimace Take makaranta ba Halin adauje ma Tafiyar Duk yadda ko suke Girmama Karatun ya"yansu wannan karon basu da Tacewa Dole suka Tarkato har su sai sun Rasa aikinsu Gobe Monday Tun ba lalle bane su koma aranar sai takai su Gobe Tunda basu san Dalilin Taruwar da Daada ta Hada Lokaci Daya ba
Tun suna Hanya Mami ke ta Fada Tana Fadama Baffa Kabir Tana san bai wuce kan malami ba,tasa sukabar Komai nasu suka taho Mutumin Daya Gujeta da kansa kuma Miye abun Damun kai,Shidai yana Jinta bai ce komai ba sai Korafi take zata Rasa aikinta Gobe kadai Sajida ma Ranta bace saboda bata son Wahala ballatana Hayaniya gidan Daada kuwa komai da kanka Zakayi ba yan aikin da zaka saka suyi maka Khamis kuwa Da Umaima Ransu Fes Suna Farincikin zasu mahaifarsu suga Daada Daman Shima yana da Niyyar Zuwa sai ya bari sai wata watan in ya samu Huti bazai ma je Abuja ba Direct Dukku zai wuce yayi Hutunsa na Karshen Wata awajen Daada tunda Har ta gama Shan jinya bai Zo ba sai da ya Tura mata sako kuma Sunyi mganata ta waya..

Aharaban Gidan Basheer Ya faka Motar kusa da Tsala tsalan Motocin Ya"yan na Daada,Sai da kowa ya Fito Daga Motar kana Inteesar ta Fito Tana Tura baki Fuskarta ba Fara"a ko kadan Sanye da wani Riga da wando,Rigar Top ce Baka mai Dogon Hannu sai Wandon nata ja ne mai Tsuke ta kasa ya kamata ba sosai ba Sai kafarta Cikin Red Talkami Sawu Ciki Ta sanya After Dreess Baka Ta Saka Red din Vail din Mayafi ta yane kanta dashi haka kuma karamar Jakar Bayanta,Mai ratsin ja ce itama wacce ta ke goye abayanta kayanta ne ke Ciki Kala Daya da sauran kayan amfaninta.
Inteesar Tana bala"in son Best clour dinta Shiyasa yawancin kayanta Red ne.
Daddy ne akan gaba Sai Ya Basheer Dake Dauke da Abiden sai Umma Dake bayansu Dauke da Abida,Anty Hauwa ce ke baya Tana Tafiya a Hankali Saboda bata jin Dadin jikinta sosai,Laulayi Inteesar na bayanta kamar Tana Kirga takunta Gabda zasu Shiga Falon gidan ne Umma ta Waigo Tana kallon Hauwa Dake tafiya Sannu sannu ga Jaka ahannunta Inteesar na Bayanta bata karban mata Jakar ba.
Dakatawa tayi su Daddy suka Shige Shi da Basheer sai da Hauwa ta Kariso kana Umma tace"Hauwa basai ki bama Wannan Sangartattaciyar Rikon Jakar naki ba?
Kina tafiya Dakyar Dakyar Dauke da Kayan Nauyi kuma ga yanayinki..!
Anty Hauwa ta Murmusa tana Fadin"Bakomai Umma zan iya..!
Tafada Tana Sadda kanta kasa Domin ita akwai kunya.
Umma ta kalli Inteesar Data ke Tafiya kamar kwai ya fashemata acikin Ciki ta Aikatamata da Harara kafin tace"Abun da kika iya kenan..Kina ganin ta tana Tafiya Dakyar bazaki karban mata Jakan hannunta ba..?
Inteesar ta Tura baki Tana Fadin"Nima fa Umma ina Fama da tawa Jakar ba wanda ya karban mun..!
Umma ta aikamata da Dakuwa Tana Fadin"kin ga naki nan mara Mutumci..Ni ko Ubanki ko yayanki ne Zamu karban miki jakan..?
Kinga Inteesar ki kama jikinki ina gayamiki nan dai Dukku ne ba Kaduna ba..ki kama Jikinki Dangi sun Hadu kada atafi Dake a baki..!
Daga haka ta mikama Hauwa Hannu Tana Fadin"Bani jakar ni na Rike Miki Hauwa..!
Anty Hauwa ta Girgiza kai Tana Fadin"Umma don Allah ki barshi Zan iya..Kina fa Dauke da Abida nauyin zai Miki yawa..!
Umma ta Mika hannu ta karba jakar Tana Fadin"Bakomai bani ai ni bana Dauke da Lalurar dakike Dauke da ita..!
Dole ta sakarmata Jakar ta Dauka Daman ta kayansu Abiden ne da Madaransu sai ruwa jakar nasu kayan Tana Booth din Mota tare da nasu Umma..
Ko bi ta kanta Umma batayi ba ta Wuce zuwa Kofar da Zata Sadaka da Babbam Falon na Tsohuwa Daada.
Anty Hauwa ce ta Juya tana Kallon Inteesar data kusa Sakin kuka Saboda Haushi ta Murmusa kafin tace"Intee Daddy kawo jakar taki na Rike miki..!
Kunya ta kama Inteeaar sai ta sunne kai Tana Dariya Anty Hauwa ta kamo Hannunta Tana Fadin"Ai sai na Daukan Miki yar kanwata..!
Inteesar tace"A"a barmin abata kafin Umma ta ganki ta kusa tsireni gaban yan Uba..!
Dariya suka saka gabadayansu kafin su fara taku zuwa Cikin falon Anty Hauwa ce agaba ita kuma tana Binta abaya Tun daga Wajen kake jin Hayaniya nata tashi da kananun kukan yara yamutsa Fuska Inteesar Tayi aranta tana jin Zata Takura Tsakani ga Allah bata son Hayaniya wani Lokaci.
Ta Saka kanta Cikin Falon kenan Shima ya Sako kansa zai Fito wayace a makale a kunnensa yana mgana Basu san Da junansu ba yasa Inteesar ta Bige hannunsa Wayar dake hannunsa ta fadi kasa ta Watse Da Sauri gabadaya Jama"ar Dake Falon na Daada suka Dago kansu zuwa Bakin Kofar Falon.
Inteesar Dake Tsaye ta Dago Dara Daram Idanuwanta ta Sauke su kan na Dan"uwanta Khamis Kabir Hamisu Dukku Dogon Namiji kakkarfa mai Cikar ZAti da kamala Fari ne ba sosai ba yana da Duhu akallon Farko in kayi mai kamar Baffa Kabir yayi kaki ne ya Tofar saboda yadda suke kama kwata Kwata kamar ba Mami ta Haifesa ba ko alama baya kama da ita kamaminsa ta asalin Fulanin Dukku ne.
Yana sanye da Rigar Fara sai Wandon Sojiji Dake jikinsa,Kamar yadda Take karemai kallo itama haka yake kallonta sama da kasa wani irin Kallo wanda lokaci Daya Inteesar taji kallon bai mata ba da Sauri ta kauda kanta bata sanahi ba sai dai tana ganinsa bata Bukatar karin bayani Dan Baffa Kabir ne.
Kauda kanta Tayi kafin ta Duka kasa ta Fara Tattaramai wayarsa da Sauri ta Dago tana mikamai Cikin Sanyin Muryanta tace"Sorry..!
Tafada Lokaci Daya tana Mikamai Sake baki yayi yana kallonta da Duka Tunaninsa Inteesar taji Haushi ya kamata kamar ta kara Wurgi da Wayar nashi a kasa,wannan kallon har ina..? Sam bai dace ba yanayin yadda yake kallonta.
Kamar Daga sama wata Murya Daga Cikin Falon ta ratsosu Tana Fadin"Khamis karbi phone dinka mana..!
Kamar an Dawo dashi Daga Duniyar daya shiga ya saka Hannu ya karba Tare da Shafa Gefen hannun Inteesar din wacce tayi saurin janye hannunta Tana kallomta Lokaci Daya ta ballamai Harara asaman lebenta tace"Allah ya isana Dan iska..!
Shi yaji Sauttin Allah ya isan sai dai bai ji karshen ba ta kauceshi Zuwa Cikin Falon yabi bayanta da kallo Cikin mamakinta.
Kafin ya kada kai yafice Wayarsa Dauke a Hannunsa
Sawu cikin kafarta ta Cire kafin ta Fara Taka Lallausan cafet din Falon da Kyawawan kafafunta Gabadaya a Tsarge take ganin yadda kowa ya Zubo mata ido gabadaya Falon yana Cike Dakyar ta iya Daga ido ta Hango Inna Bintalo kusa da ita Inna Maimunatu ne suna Zagaye da yara da alamu jikokinsu ne Tuna Huduban Umma Tun kafin su Fito yasa bata Tsaya ba ta karisa gabansu ta durkusa Tana Gaishesu Inna Maimunatu ta Dafa kanta Cikin Fara"a Tana fadin"Allah mai iko..Mai sunan Daada ce ta koma haka Ya Mustapha?
Yana Daga chan gefen Kan Daya Daga Cikin kujerun falon. Kusa da Baffa Kabir ya Dagamata kai yana Fadin"Ga tan fa MAimunatu..!
Masha Allah take ta Fada Inna Bintalo ce ta tabe baki Tana Fadin"Basu son zumunci Salaha bata nuna mata Darajan mu ba..har gwarama Basheer yasan Hanyan gidajenmu..Ammh ita kam bata sani ba ni Rabo na da ita ma Tun batakai haka ba Wlh.!
Yarta Hamida Dake aure a Katsina Dake gefe tace"Mama ko mu ta ganmu ahanya bazata gane mu ba..Bata kuma je gidanki ba ina ga mu namu gidajen..?
Yar"uwanta Siyama Dake gefe Tana Shayar da Jaririyanta ta Karbe da cewa"Gaskiya akwai mtsala..Nifa sai wannan Haduwar ne ma nake ganin wasu..Har gwarama Ya"yan Barrister Baffa kabiru ana ganinsu..!.
Kamar an tsokane su haka suke ta Tofa albarkacin bakinsu Inteesar Haushi kamar ya Kasheta Umma Dake Kusa da Mami Asma"u ta kada baki tace"Kayya Bintalo bai ko kamata ki ga Laifina ba..Intee ai taku ce Dukku Tun Tana karama take zuwanta In Babanta zai taho Data Girma ne saboda Karatu ta Dauke kafarta..!
Inna Bintalo baki ta tabe batayi mgana Domin ita daman in ta Raina Kurarka akwai Wulakanci basu yima Mami saboda bata Raga musu sun santa Sarai kan ya"yanta sai ajita Dakai Shiyasa tana Zaune ko Tankasu batayi ba Farin gilashi ne a idonta Tana Kallon Wayarta bama ta Lura da Abunda ke Faruwa ba,Tun bayan Shigowar Inteesar da Karon da sukayi da Babban Dan"ta Taga irin mayen kallon Dayake Binta tayimai mgana Domin Ita bazata taba bari Wani abu ya Shiga kansa ba yarinyar sam ba ajinsa bace.
Sajida ce zaune gefenta Ta Dota kanta Saman kafadarta Idanuwanta suna Lumshe kamar mai barci Alhalin Idonta Biyu ta gaji ne kwanciya Take so yi bata son Damu da Takura.
Inteesar dai Dataga Cin Mutumcin bazai kare ba sai ta mike Fuskarta ba Fara"a ko kadan ta Wuce Inna Bintalo ta Bita da kallo kafin ta Rike baki Tana Fadin"Ikon Allah..ji yadda take Kumburi Yi hakuri yar nan kada ki Dakemu don munyi mgana..!
Baffa Kabiru ne ya Dakatar da mganar yana Fadin"Binta kibar mganar nan hakanan..Taruwarmu anan Saboda Daada ne bawai zaman kace nace ba..mu bari Daada tatashi Daga Barci muji Dalilin Dayasa tayi mana wannan Kiran gaggawan..!
Inna Maimuna ta kada kai Tana Fadin"Baban Sajida..Ai itama Uwace ko bata zo ba ita ai sai taje ko..? Ammh itama Shekarar ta nawa Rabonta da gidan Ya Mustpha..? Bafa yaranmu nee keda mtsala ba abun Daga Wajen mu ya Samo asali bama Ziyartar junanmu sai dai in Mun hadu anan Wajen Daada imu imu fa to ta yaya ya"yanmu zasu san muhimmancin nasu Tunda basa ganinmu muna Ziyartasu lokaci Bayan Lokaci..!
Kowa falon sai da ya Natsu da mganarta.
Sa"id Dake gefen Basheer zaune ya jinjina kai yana Fadin"True Talk Mommy..Kin fadi gaskiya ni kaina naji Dadin wannan Kiran na Daada ina so nima na fadi wanna mtsalan su Kawu su Duba su gani ataru a gyara Shiyasa nazo da Iyalaina suma suga yan"uwana..!
Sadam Dake gefensa yace"Nikaina Kana kirana ka gayamin na Tattaro Anisa muka taho dasu Waleed Domin sau Daya muka taba zuwa Dukku dasu..!
Ya"yan Inna Maimunatu kenan suke mgana Mazan na ta fari Tuni sun Girma sun zama magidanta Sadam din likitan Ido ne a kano yake Zaune anan asibitin Makka yake aiki yana Zaune da Matar Anisa da ya"yansu Waleed da Waleeda shi kuma Sa"id yana Zaune ne a garin Dutse yana aiki da Hukunar Wutar lantarki ta Jahar gabadaya,Ammh basu san suje gidan kowa ba sai Bauchi,sai kuwa in sun Leko Dukku shima

Please Login or Register in order to submit comment