Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya Dauro auran kuma ya Hadomu da ita..!
Cikin mamaki Mama tace"Topha..kamar ana yaki..?to matar waye..?
Baba manu yace"Ina abokin Yaron nan Sagir..? Wayake da suna na manta..!
Mama ta Zaro ido Tana Dafe Kirji Lokaci Daya tace"Aure Imran yayi..?
Baba manu yace"Ba Imran din ba Yayansa..Na manta sunansa ko Wayake da suna ma..!
Mama da al"ajabi yagama kamata tace"Yusuf sunansa..?nifa na shiga rudu garin ya haka ya Faru..?
Baba manu ya gyara zama ya Shiga Rattabama Mama yadda komai ya wakana Tun daga farkon zuwansu Gidansa Sagir da Imran har yau da abunda ya Faru gidan Alhaji Alhassan.
Mama ta saka Salati da Salallami ta Dire Tana Fadin'"Wlh baban Sagir bansan komai game da wannan mganar ba..Yaron nan Sagir bai gayamin komai Yau Tun Safe ya tafi makaranta salaha da sukazo da megidanta kawo autan ta karatu suka Daukesa shi da Inteesar din zuwa Cikin makarantan har yanzu bai Dawo ba!
Baba manu yace"Wajen ki Zata zauna tayi karatun kenan..?.
Mama tace"Eh Wlh..!
Baba manu yace"Allah ya bada sa"a..Kin dai abunda ya faru yanzu ya zamu yi ne..?Me kika sani game da Gidansu yaron nan Amina..?
Mama ta gyara Zama Tana Fadin"Wlh bana ce maka nasan komai ba..Ni dai na san Imran din abokin Sagir ne Allah ya Hada Jininsu..Sai kuma nasan basu da kowa Daga Mahaifinsu sai shi Imran sai kanwarsu sai Mahaifinsu Dake kwance ba lafiya Domin na Taba shiga Gidan Sau Biyu na gaidashi..!
Baba manu yace"Ina mahaifiyarsu..?ina yan"uwansu da Sauran Danginsu..? Kuma laluran meye Mahaifin nasu ke Fama dashi..?
Mama tace"Wlh nidai bansani ba..Sagir dai ya gayamin yace Daya Takurama Imran din ne da Tambaya ya gayamai mahaifiyarsu ta rasu mganar Danginsu kuma Wlh shi kanshi Sagir din bai sani ba Imran din baitaba yarda ya gayamai komai ba Laluran Mahaifinsu kuma Ni bansani ba ammh Tabbas Bashi da lafiya yana Cikin Daki kwance ko Falo baya Fitowa..!
Baba manu yayi Shuru bai yi mgana ba illah Ajiyar rai Daya Sauke Lokaci Daya ya Zaro Wayarsa yana Fadin"Bari na Kira Sagir din yazo ya kira shi abokin nashi..!
Mama ta kada kai Alamun hakane din ne.
Baba manu ya kira Sagir,Shi kuma Lokacin yana cikin Makaranta ammh sun Dade da Fitowa daga Lacture,Inteesar yake jira saboda kada ya tafi ya barta bazata iya Dawo wa gida ba.
Yana Dagawa Baba Manu ya Tambayeshi ko yana ina..? Yace yana cikin makaranta nan da nan Baba Manu yace in babu Abunda yake yi ya zo gidansu gsshi yana Jiranshi
Hankalin Sagir ya tashi Dagajin muryan Baba Manu ba waasa acikinta,Gashi kuma Inteesar sun Fito Daga Lacture sun shiga wata kuma yana ma Department dinsu yana jiran Fitowar ta.
Ya rasa ya zai yi sai Allah ya Taimakeshi sai gasu sun Fito yamike ya isa bakin Hall din nasu sai gashi Inteesar din ta Fito Dauke da Jakarta da Wayarta sai Takardun Dake hannunta.
Tana ganinsa ta kariso gabansa Tana Fadin"La ya Sagir..?
Badai kana nan Tun dazu kana jirana bane..?
Sagir yayi Mirmishi yana Fadin"Eh mana..Kada ki Fito baki ganni ba ki fara kuka..!
Abun sai ya bata Dariya Sai data Dara kafin tace"Sai kace wata yarinya ya sagir..!
Yace"Eh mana ai yarinyar ce kada ki kira Babanki kice na barki ke kadai baki gane Hanyar gida ba.!
Inteesar tace"Laa..Zan iya fa komawa Gida dakaina Allah..Kuma ai in ina gaban Daddyna ne nake Shgwabata in ya barni ni kadai Am Mature ya Sagir..!
Mamakin Surutun yaji kafin yace"Wato Shagwabar ma Kinsan inda kike yinta ko..?
Dariya kawai tayi Tana Sunne kai Agogon hannunsa ya kallah Daya na Rana ta kusa ya kalleta yana Fadin"Daman gida nake son Tafiya an kiranibshine nake Tunanin bazaki iya gane gida ba in an tashi Ki kirani sai nazo Mu Dawo Tare..Tunda ni na gama da makaranta sai kuma Jibi in Allah ya kaimu..!
Da sauri tace"A'a kada na Wahalar dakai zan gane ba Gadon kaya ba..?in na samu mai adaidaita yana kawoni anguwan zan gane layin ina da Saurin Dauke abu akaina..!
Cikin son Tabbatarwa yace"Kin Tabbata zaki gane..?
Inteesar tace"Insha Allahu..!kai ya kada duk da haka bai yarda ba sai ya Fiddo wayarsa ya kirata sai ga wayarta na kuka acikin Jaka ganin tana kiciniyar Fitowa da wayar ne yasa yace mata"Nine na kiraki ga lambata nan ki kirani in baki gane ba..!
Kai ta gyada mai Tana Fadin"Thanks..!
Jinjina mata kai yayi kafin yace"In zaki yi sallah ki bi ayarin mata yan"uwanki zuwa masallacin Cikin makaranta in wani abu zaki siya ga Cafteria chan..Sai mgana karatu tunda an wuceki da yawa in kika Dawo sai mu Tattauna Dole sai mun samu Wani ko Wata Cikin Course mate dinki da zai mataimaka miki..!
Cikin jin Dadi ta amsa mai da haka sukayi sallama ya kama Hanya.
Minti Talatin ya bata saboda ya samu go.slow kafin ya kariso Gidan yana Shigowa ya iske Baba Manu har lokacin suna Tattaunawa da Mama Tuni ya Fita ya Sallami Alh.Sadi da Niyyar sau sun yi mgana ta waya ko sun hadu.
Yana Shigowa ya Durkusa yana gaida Baba Manu Mama ta kallesa Tana Fadin"Ina ka baromin yata..?
Sagir yace"Tana chan basu gama Lecture ba..Ammh ban barta ba sai da ta tabbartamin da zata iya Dawowa da kanta..Na dai bata lambata nace in bata gane ba ta kirani.!
Mama ta kada kai kafin tace"Allah ya dawo da ita lafiya..!
Ya amsa mata da Ameen kafin ya maida Hankalinsa kan Baba Manu Daya gyara zama yana Fadin"Ina abokin ka..?
Sagir yace"imran baba..? Ban sani ba ammh ina kyautata Zaton yana gida Duk jiya bamu hadu dashi ba..!
Baba manu yace"Kirasa a waya..Kace masa yazo nan gidan gani Ina tafe da Matar dan"uwansa..!
Sagir ya zaro ido yana Fadin"Mata kuma Baba..?
Mama ta karbe tana Fadin"Eh suna zuwa uban ya Daura auran.Kuma ya hado su da yarinyar tana nan cikin Dakina zaune..!
Sagir yayi Sakace yana bin Mama da Baba Manu da Kallo Cikin mamaki kafin ya Zaro wayarsa a Fili ya Furta"Dankari...!


_Masu cewa wai auran Safiya da Yusuf kamar yar tsana..? In kun bibiya labarin zaku iya Fahimtar Dalilin da yasa Auran ya faru cikin Lokaci Alhaji Alhassan yana matukar Daraja Mutumcinsa akan mutumcinsa kada ya zube zai iya yin komai,Kuma yarda yaga Imu ya tabbata zai iya bangala Sirrinsa yayi Tirere dashi acikin Farantin ya gama yawo dashi kowa yagani kuma ya saani bazai mai Wahala ba Shiyasa ya Daura auran ya yarda Kwallon mangwaro ya Huta da guda.._🤣





*Shakira..*
3/22/22, 23:03 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*DEDICATED TO:*
*Aisha alto(Sisinah)*
*Chubado muhammad(Uwar dakina)*
*Yahanasu Soupnass(Qawalli1)*
*Kausar salis(My jika)*
*Rahma Ladingo(Dota)*

*Ina godiya masoyan GIDANMU Allah ya saka da alheri Allahu ya bar zumunci Ameen,Musamman yan gidan Gidanmu comments Section 1&2,Janaf Novella,Zauren Janafty Shakira da sauransu Tanque so much*


*🅿?10*


"Lokacin da kiran Sagir ya Shigo wayar Imran yana kwance akan gado acikin Dakinsa ya gama Busa Sigarinsa har yagaji ya koma ya kwanta.
Gidan nasu ba kowa Yusuf ya tafi wajen aiki,Munari kuma Ta tafi makaranta shi kadai ne agidan,Daya tashi Dakin Abba ya leka ya sameshi yana zaune shuru Shi kadai shi ya taimakamai yayi wanka ya sauyamai kaya ya Hadamai Tea mai kauri da Soyayyan Dankalin da Munari ta soya kafin ta fita bayan ya bashi yaci ya koshi ya Doramai da mgungunansa,wanda ko Minti Goma bai yi ba ya Sulale yana Barci,wannan watan Chanjin mgungunan da Likita yayi mai kamar sun fi yimai amfani,Saboda ya na samu Ishashen Barci Kwakwalwarsa tana samun Hutu sosai Fiye da baya kuma suna ganin Chanji Sosai.
Bayan yayi barcin ne ya Fito Falo nan kan Dinnig ya Hada Tea yasha da Soyayyan Buredi,yaci ya koma Daki ya Dora da Busa Hayaki bayan ya gama ne ya koma ya kwanta sai ga kiran Sagir ya shigo wayarsa karama Kirar Nokia ce Rakani inda Zani Domin Imran bai tabaa Damuwa da sai ya mallaki Babban waya,Shi dai a kira ya Daga kawai kuma Mutanen dayake kira Daga Sagir sai Yusuf ko Munari yana da lambarta ammh ba sosai yake kiranta ba.
Cikin kasala ya Zura hannu ya Dauko wayar,ganin sunan mai kiran yasa yadan saki karamin Tsaki ya Daga kiran yana Fadin"Ya akayi ne Banzan Abokina..?
Dagachan bangaran Sagir dake kallon Baba Manu yace"Kana ina ne..? Ga Baba Manu na gidanmu yana jiranka..!
Imran ya lumshe idanuwansa kafin ya Bude su yace"Kaga mallam gajarta Zencen..Meya faru?
Domin duk da yasan mganar Neman auran yusuf haka kurum yaji ajikinsa da wani abu.
Baba manu ne yayi ma Sagir alamun Daya Fadamai Shi kuwa ya karkace kai yace"Kazo fa Domin Baban yarinyar nan Ya Daura auran Kuma ya Hado su Baba Manu da ita!
Imran bai wani ji mamaki ba sai ma wani Mirmishi Daya saki Kafin yace"Dakyau..Yanzu ta na ina..?
Sagir da mamaki ya cikasa yace"Tana Dakim Mama..!
Imran ya mike Zaune yana Fadin"Gani nan zuwa..!
Daga haka ya katse kiran,Cikin Sassarfa Ya Sauko Daga kan gadon afili yake wani Mirmishi kamar na mugunta aransa yace ya Rage ma kansa aiki..Shifa baisan komai akan Alhaji Alhassan ba Daga farko sai da ya Shiga Gonarsa kudi kalilan ya bada aka Zayyanemai Labarinsa bai sanshi bane shi kanshi a baya baisanhaka yake ba,Sai yanzu yake kara jin Tsoron kansa Sosai in yayi wani abun
Wanka ya shiga a gurguje,ya fito ko Mai bai shafa ba ya Bude Wardrope dinsa Dake cike da kayansa ya Zari Riga da wando Ruwan madara da da bakin wando ya saka,bayan ya saka karamin Cum ya taje kansa ya Dauki Wayarsa bayan ya saka wani Budadden Takalminsa baki na Fatar Damisa.
Dakin Abba ya leka ya iske har Lokacin bai tashi ba yana ta Barci yasa ya juya ya fice bai Nemi Hawa Mashin dinsa ba ya Taka da kafarsa ya Fice zuwa gidansu Sagir a kafarsa duk da dan Nisa bai damu ba,Kafin ya isa Gidan su Sagir ya Biya wani Shago ya siya kwalin Sigari da Lether ya manto nasu agida kuma yau yadda yake jin Nishadi ya kamata ya Busa Hayaki sosai.
Acikin aljihun wandonsa ya saka kafin ya isa kofar gidansu Sagir.
Waya ya Dauko ya kirashi yaceya Fito yana waje yana jiransa,Kafin Sagir ya Fito ya kira Yusuf sau Biyu bai Daga kiransa ba sai ya kyaleshi tunanin kila yana wani aikin ne
Ba dadewa sai ga Sagir ya Fito Hannu ya bashi sukayi Musabaha kafin Sagir yace"Meyasa ka tsaya Daga waje baka Shigo ba..?
Imran ya Dakuna Fuska yana Fadin"Kawai sai na kama Shiga Gidan Mutane kai na Tsaye..? Bar gani na D'an iska D'an iska nasan Abunda nake yi ina da Hankali..!
Sagir ya kusa sakin Dariya sai dai ya kanne kafin yace"Aifa ga Hankalin nan nagani..!
Kansa Imran ya Daka ya Duke yana Dariya kafin su Nufi Cikin Gidan.
Sagir ne agaba Imran a baya Da yayi sallama iya sallaman Lebensa Mama na Kitchen Baba Manu ne ke zaune yana Shan Ruwa Sagir ne ya zauna gefensa shi kuma Imran din Daga chan gefe ya Durkusa yana gaida Baba Manu ya amsa mai,Daidai Lokacin da Mama ta fito itama ya Gaisheta ta amsa Cikin Fara"a tana Tambayansu Mutanen gidan ya amsa mata da Lafiya
Baba Manu ya gyara Zama yana Fadin"kaji dai abunda ya faru ko..? Kamar yadda Sagir ya Fara gayamaka..Muna zuwa da niyyar Neman aure sai kawai aka Daura auran..Baisan me ya faru ba..Ammh naji ban ji Dadin Sanadiyar irin auran da yayi ma yarinyar ba haka ya Hadomu da ita ba Rakiyan kowa gwanin ban Tsausayi.!
Baba manu ya karishe Fada yana Bayyana Jimamin Abun.
Imran yayi Mirmishi kafin ya kada kai yana Fadin"Hakan yayi kyau..!
Dukkansu sai da suka kallesa yayi kamar bashi yayi mganar ba,Baba Manu yazaro Sauran Kudin Imran ya Mikamai yana Fadin"Dubu Dari ya karba Sadaki sai dubu Ashirin da aka kashe na Siyan Minti da Sauransu Ga Ragowar Dubu tamanin dinka nan..!
Kai kawai Imran ya Girzgiza kafin yace"Ka barshi kawai.!
Baba manu ya zaro ido yana kallonsa hakama Mama da Sagir Cikin mamakinsa Baba Manu yace"bangane ba? Ni don Allah nayi muku komai karbi kudinka yaro..!
Imran ya kara kada kai alamun bazai karba ba,Baba Manu yace"Ikon Allah..To in kabarmin wannan Zunzurutun kudin kai fa..?
Imran ya kauda kai kafin yace"Ni ina da kudi..!
Baba manu yace"Kana aiki ne.,? Ni a sanina Sagir ya Fadamin Yayanka kadai ke aiki..!
Wani kallon ya Sakarma Sagir kafin yace"Ina da Sauran kudin Albashina dana ke Tarawa.!
Gabadayansu mamaki ya Cikasu barin ma Sagir da bai taba jin Imran yayi mgana kan Abunda ya Shafeshi ba.
Cikin karin mamakinsa Baba Manu yace"A ina kayi aikin..?
Imran kamar bazai Tanka ba sai Chan yace"Ba anan bane..A lagos ne..!
Gabadayansu suka Zuba musu ido,ganin haka yasa yayi Saurin Basarwa,Da sauri Sagir yace"Wai daman ku yan Lagos ne..?
Da sauri Imran yace"A"a..
Daganan ya Tsuke bakinsa bai ce komai ba Sagir zai kara mgana Baba Manu ya Danne mai hannu ganin yadda Imran ya Hade kamar ya kuma matsa gefe kamar za"a ce wani abu ya tashi ya Fita.
Cikin Basarwa Baba Manu yace"yanzu ina shi yayan naka..? Ina bukatar ganinsa..!
Imran ya sauke ajiyar Zuciya kafin yace"Baya nan yana wajen aiki..!
Baba manu yace"To ka kirashi..!
Imran cikin kosawa yace"'Na kirashi bai Daga ba..!
Baba manu ya jinjina kai kafin yace"Shikenam..Daman domin na Damkar amanar yarinyar nan ahannunshi..Duk da bamu hada komai daku ba naji ina kallon ku kamar kowa..Yanzu a ina zai ijiyeta..?
Imran ya wani kallesa a karkace kafin yace"Yana da inda yafi GIDANMU ne..!
Chan zai ijiyeta akwai Dakuna bazai gagaraba..!
Baba manu ya jinjina kai yana Fadin"Shikenan Allah ya basu Zaman lafiya..Gata nan Dakin Amina ni zan wuce saboda zan fita gareji nagode kwarai..!
Yafada Lokaci Daya yana Mikewa Dukkansu suka Mike Imran ya kalli Baba Manu kafin yace"Nagode..!
Kafadarsa ya Dafa kafin yace"Bakomai Kada ka Damu!
Lokaci Daya ya Turamai kudinsa Cikin Aljihu yana Fadin"Kada kace wani abu..Bazan iya karban ko Sisi Daga wajen ka ba..!
Dole Imran yayi shuru bai kara mgana ba Tare suka Fice Bayan Baba Manu yayi ma Mama Sallama Safiya na Daki tana jin mganganu sama sama,Tana Zaune afalon Mama bata fito ba.
Suna Fitowa Bayan Baba manu ya tafi Imran ya kalli Sagir yana Fadin"Zan je gida na Dawo..Na bar Abba shi kadai..!
Jinjina kai kawai Sagir yayi kafin yace"To ya za"ayi da amaryan ya Yusuf din?
Imran yace"Ya kuwa.? Bari naje gida zan kirashi muyi mgana in ya Dawo yazo ya Dauki matarsa yanzu dai ta zauna wajen Mama pls..!Sagir yace"Kada ka damu ai an zama Daya..!
Daga haka sukayi sallama,Sagir ya Dawo Cikin gida suna ta maida Zence da Mama.
Imran kuwa har ya koma Gida Abba bai tashi ba sai yayi Zamansa afalo yana auna wasu abubuwa,Alhaji Alhassan mahaifin Safiya yana Tsoron Tonon asirinsa wanda wannan Dalilin ne yasa yayi gaggawar Dauran auran,ya kawo yarsa a Wulakance kamar bata da gata Hallacin da Safiya tayi ma Yusuf dasu kansu Shi zai sa su riketa Riko na gaskiya da Watarana sai Mahaifinta yayi Nadamar Abunda ya aikata ya Dawo yana bata Hakuri kuma ko bajima sai asirinsa ya Tonu Domin Shi Sharri ai Dan aikeni Inda ka aikashi sai ya Dawo.
Sannan kuma Itace Mace ta Farko da Zata Shigo Gidansu a Lokacin da suka yanke tsammani da komai Ya Tabbata Yusuf ya Chanchanci yayi Farinciki Tun Bayan Afkuwar Kaddaran Data Fadamusu shi yake ta Wahala dasu ya Dauki Ragaman Abba Gabadaya akansa,Shiyasa zai Tsaya har sai ya ga ya samu abunda yake so koda shi zai rasa nashi Farincikin ne,Duk da daman Shi yariga yagama bamkwana da Farinciki.
Yana nan zaune sai ga kiran Yusuf sai ya Dauka bayan ya Daga sun gaisa yace mai suna Meeting ne shiyasa bai Daga kiran ba.
Nan Imran ya gajerce Mganar ya gayamai Abunda ke Faruwa Yusuf yana Zaune Cikin Officr dinsa sai da ya Mike Zaune Cikin mamaki da al"ajabi yace"An Daura auran kuma Imu..?
Imran yace"Eh...To miye aciki ya saukaka ma kansa ne..!
Yusuf na Sharan zufan Goshinsa yace"A"a Imran bamu shirya komai ba Infact ma ko Abba bamu Fadamawa ba..Ballatana Kanwarmu Munari ni bama wannan ba kai ina zan ijiye Safiya Imu..?
Imran bai wani bama mganar Muhimmanci ba yace"In ka dawo sai ka Fadamai Abba bashi da Mtsala hakan ba abun alfarinsa ba ne..Mganar inda zaka ijiyeta kuma ai ba wani abun Damuwa bane..Sai ta fara zama adakin ka kafin mu gyara mata Falon nan da 2 bedroom din nan dake korido din Dakin Munari..!
Yusuf yayi shuru kafin yace"Ok..Hakane Allah ya bani ikon Rike Safiya da Amana..!
Imran yace"Ameen ya yusuf Domin She Loves u.!
Yusuf ya saki Mirmishi kafin yace"I know..Zuciyata ta cika da Alherinta Imu..Ina ta kiranta Tun dazu bata daga ba yanzu tana gidan Maman Sagir din ne..?
Imran yace"Bakajin Hausa kenan..?
Yusuf yace"May be..!
Imran bai tsayama Sauraransa ba ya Datse kiran ganin Yusuf zai fara Zolayansa da bakwarcinsa shi kuma Baya cikin Mood din.
Dakinsa ya koma ya zauna kan kujera ya Shiga Busa Sigarinsa Hankalinsa kwance Sallar azahar ya tadashi yayi alwala yayi Sallah,sannan yazo ya adana Sauran kudin da Baba Manu ya maido masa,da niyyar zai bama Yusuf su ne yayi amfani dashi.

******
Bayan La"asar Yusuf ya baro wajen aikinsa zuwa gida,ko da ya Dawo ya iske Imran na Dakin Abba yana bashi Tea,Tunda Munari bata dawo Daga makaranta ba ballatana Tayi abinci.
Yana Shigowa gidan Dakin Abba ya Fara shiga nan yake Imran ya Dago yana kallonsa Mirmishi ya sakarmai Ammh Shi Imran din sai ya kauda kansa Abba ne Cikin Fara"a yace"Yusuf...Ka dawo ashe..? kariso mana ka tsaya Daga bakin kofa..!
Jin haka yasa ya shigo Dakin Yana Sabe da Jakarsa ta aiki a Kafadansa Gefen kafafun Abba ya Zauna Tunda Imran ya Zaunar dashi shi kuma yana Zaune gefensa.
Yana zama yace"Abba ya jikin ka?
Abba yace"Jikina da sauki Yusuf..Yau dan"uwanka yayi ta kula dani..Dukkan ku Allah yayi muku albarka,ya jikan yan uwanku da Mahaifiyarku..!
Gabadayansu sai da sukayi mamakin kalamansa Domin ya Dade baya Fadar haka tun Farkon Lamarin,Kallon juna akayi Tsakanin Imran da Yusuf Mirmishi ya Bayyana Saman Fuskarsu da Sauri Imran ya mike Tsaye rike da Mug din Tea din yana Fadin"Da alamu dis Time around Abba ya fara samuwa..!
Yusuf ma kusa da Abba ya Dawo ya Rike Hannayensa yana Fadin"Abba ka samu lafiya ne..? Abba Don Allah ka warke..Ka Dawo Abban mu da muka Saba Dashi..,!
Abba ya saki Mirmishi kafin ya Dafa kan Yusuf yace"Na samu Sauki Yusuf..Dole na manta da komai na Fuskanci Rayuwar da Allah ya zabamim ko Saboda kai da Imran da kanwarku Maimunatu..!
Dukkansu Bakinsu yaki Rufuwa Yusuf ya kara Jimke hannun Abba yana Fadin"Abba Daman na dawo ne na Fada maka wani Daddaan Labari..Abba nayi aure..Abba Imran ya Girma shi yabiyamin Sadaki shi yayimin komai na aure na Abba..!
Abba yayi jim yana kallonsa kafin ya sauke Numfashi yana Fadin"Duk a yaushe akayi neman auran har akayi Auran ni bansani ba..?Kuma shi Imran din ne ya Shige maka gaba har aka baka auran.?
Yusuf ya girgiza kai Kafin ya Fara Bama Abba Labari Kamar yadda Imran ya Bashi Labari da irin yadda Alhaji Alhassan ya hanashi Auran Safiya sai da Imran yaje kana..!
Abba kafin yusuf ya gama Bada Labarinsa yaji Hawaye sun Fara kwaranya acikin idanuwansa Cikin Muryan kuka da Sarewa yace'Waye ya Gorantamuku Rashin asali..? Ku din yan asali ne ya"yan Dangi..Ba laifi na bane Bakuma ni na gayyaci Kaddran Data Fadamin cikin Rayuwata ba.
Allah ne ya Doramin kuma Wlh ba Kamar yadda Sauran yan"uwana ke Fadi bane na yarda da Kaddara kuma na yarda da Allah da ya bani Zuwaira shi ya Karbi kayansa..Haka kuma Allah da ya azurtani da Haihuwan Nura da Asma"u da Salima shi ya karbi kayansa..Sai dai wannan Gagarumin rashi a lokaci Daya basan yadda zan iya Daukan Lamarim ba..Wlh ban sani ba..!
Ya karishe Fada cikin gunjin kuka wanda ya kusa saka Yusuf kuka da Sauri ya Rumgume Abba Imran kuwa yana gefe tsaye ya Coge yana kallon kasa ba wanda ya iya Fahimtar wani Hali yake Ciki ba.
Yusuf ya Dago Daga Jikin Abba ya Saka Hannu ya Sharemai Hawaye kafin yace"Ka daina kuka Abba...Don Allah kada muma ka sakamu..!
Abba yayi Mirmishi Lokaci Daya yana Kara rike hannuwan Yusuf kafin ya Dago yana kallon Imran Lokaci Daya ya fara mgana"Yusuf..Imran..Babu abunda Zan ce muku sai godiya..Allah yayi muku albarka na baku Wahala akan Lalurata..Ga rikon kanwarku..ammh Duk da haka Ban ji Dadi da kuka yanke Shawaran neman auran yusuf Batare da kun nemi Daya Daga Cikin Iyayenku ba..Duk da ko Dawowarmu wannan gidan Ban ji Dadi ba..Ina jira ne na kara Samun Sauki Dole zamu koma Gida na nemi yan"uwana kuma ku nemi yan"uwanku Kowa Rayuwa ta koma mai yadda ya fara..!
Wannan Karon Imran ne ya Motsa kafin yace"Abba Ka bar wanman mganar..Mutanen da sukayi ta Bleming din ka akan ka Zama mahaukaci saboda Rashin Daukan kaddara..Basu Tuna kai Dan"uwansu bane alokacin basu Duba Halin da kake ciki ba basu Duba irin rashin da mukayi ba su Rika Zargin ka suna ganin Rashin Hakuri ne da kaddara ne ya jefaka Cikin Halin dakake ciki..Ai gwara da mukayi nesa dasu muka dawo nan muma Rayuwa a inda ba wanda yasan Labarin Mu yafi yemama Zama inda ansan Laluranka ammh kuma baza"a Taimaka masa wajen ganin ya Rabu da Lalurarsa ba sai kara Doramai Cuta.Abba ka bar wannan mganar ni Na rantse ko Komawa zakayi sai dai Yusuf da Munari su Bika ni ina nan ba Inda Zani..!
Ya karishe Fada Cikim kumfar baki Lokaci Daya kamar wani Kabubuwa ya Fice har yana Banko Kofar Dakin
Daga Abba Har yusuf da kallo suka Bisa kafin su girgiza kai Abba ya Cije baki yace"Ashe har yanzu Imran bai Chanza ba Yusuf..?
Yusuf yace"Sai ma abunda yayi gaba Abba..!Abba ya koma kawai ya kwanta kafin yace"Allah ya Shiryesa..Yanzu ita yarinyar tana ina..?
Yusuf yace"Tana gidan Maman abokinsa Sagir yaron nan Dake zuwa Dubaka..!
Abba ya gyada kai kafin yace"Allah ya bada zaman lafiya..!
Daga haka bai kara cewa komai ba yayi dai Shuru ya Lumshe idaanuwansa kamar mai Barci ganin haka yasa Yusuf ya mike ya Fice Jiki a sanyaye sai da ya Fita ne kana Abba ya Bude idanuwansa yana Bin Kofar Dakin da kallo wasu Siraran Hawaye suna Biyo kunnuwansa a Fili ya Furta"Kiyi Hakuri Daada..Ki yafemin..!
Yusuf Dakinsa ya wuce yayi wanka ya sauya kaya zuwa wata Farar Shadda Riga da wando da Hularsa Zanna Bukar,Yasa Bakin Takalminsa Rufaffe na Fatar Damisa.
Ya fesa Turare yana Tashin Kamshi Dakin Imran ya Shiga ya Iskesa ya Turnike Dakin,da Hayaki sauri Yusuf ya karisa Shiga Dakin da Sauri ya Zage Labulyen Windows din Dake dakin ya Dage Glass din Yana Fadin"What Wrong with u ne Imu..? Kana zaune acikin Daki Hayaki ya Turnike ga na Cikin ka ga na Sarari illah Nawa kake so kayi ma kan ka ne.?
Imran na Zaune yana jinsa bai tankasa ba sai ma kara Zukar Sigarinsa da yayi ya Fesar da Hayaki bai ko kalli barayin Yusuf din ba.
Karamin tsaki ya saki kafin ya Tako gabansa ya saka Hannu ya karbe Sigarin yana sakata Cikin Farantin Dake gefen Imran din inda yake kashe sauran Sigaran nashi da wani Jajayen idanuwa Imran ya Dago yana Kallonsa Kafin yayi mgana Yusuf ya Rigashi da cewa'"Kafi kowa sanin Shan Taba tana da illah ga Lafiyar Dan'aman Imu..A baya Lokacin kana Banker Imran Abubakar malami na sani ko Warin taba baka so..Ammh Rana tsaka na tsinceka ka fi wadanda ma suka dade cikin shanta iya Zukanta da Shanta ma..Don Allah ka Rage shanta hakanan Tunda ba Abinci bane..!
Saboda Bayason Hayaniya baya Cikin Mood mai Dadi yasa yace"Naji..!
Da haka ya dauke Kwalim Sigari da bai fi Saura Daya ba Da Lether din ya Tusa cikin Aljihin wandon Dake jikinsa
Yusuf yace"Yauwa..Tashi ka rakani gidansu Sagir din.!
Imran ya wani Dakuna Fuska kafin yace"bazan je ba..Haka kurim sai kaje dani Daukan Amaryan taka..?
Yusuf ya Dafa kafadarsa yana Fadin"Ai ba cewa nayi ka Daukomin ita ba rakani kawai zakayi bazan gane gidan ba..!
Yafada da Sigan Lallashi
Imran kamar bai zai tashi ba sai da yaga Dama kana ya tashi ya Fice batare Dayace ma Yusuf din komai ba Shima sai yabi bayansa a Haraban gidan suka Hadu sai da Yusuf yayi Riverse da Motar yazo gaban Imran kana ya Bude gidan gaba ya shiga suka Fice Daga gidan
Shi ya nunamai hanyar gidansu Sagir din sai gasu sun iso sun iske Sagir din a Shago ya Taso da Sauri yana gaida Yaya yusuf kana yamai Jagora zuwa Cikin Gida Domin Imran yace yana waje shi bazai Shiga ba,Dole Yusuf ya Shiga shi kadai Mama tayi ta ina ta saka dashi har Falonta Safiya na Ciki inda tayi Sallah Mama ta bata abinci taci kadan Tayi ta mata Nasiha harta Daina kuka Bayan sun gaisa ne Sagir yayi ma Mama bayanin Wanene Yusuf Ta washe baki suka kara gaisawa,kan yusuf na kasa yace"MAMA nazo tafiya da ita ne..!
Mama ta mike tana Fadin"Masha Allah..Ammh ai bana

Please Login or Register in order to submit comment