Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce ke Damuwa Tayi ta Fadan Imran bayason yan"uwanshi Ballatana Danginsa Tunda bayason Zama Dasu,Abba ke Tausanta Lokacin yana Fadamata ta Cigaba damai addu"a Halinsa kenan,Tayi ta Korafin Dangi ba wanda yasan sa sai dai sunansa Tun yana karami Rabon Daya Taka Gombe Duk Zuwa sai Daada Tayi Mita da Korafi Sai dai Imu bai Damu ba yafi Damuwa da Abunda ya sakama Gaba Fiye da komai a Rayuwarasa.
Haka Rayuwarmu ta Cigaba da Tafiya Ni da Nura muka kamallah Digree din mu na farko muka Dora na Biyu da Kwarin Gwiwan Abban mu Asma"u kuma ta Fara Karatu a Lagos state university Lasu Dake Lagos, Tana karantar phamarcy Salima kuma Tana Shekarar Karshe a matakin Secondary,Munari kuma Tana baya Saboda ita din Daga Karshen Anni ta Haifeta Bayaan Salima ta Shekara bakwai a Duniya.
Zuwa Lokacin mun san Dadin Dangin mu da kanmu mukan Shirya mu Ziyarcesu ko da Abba baice ba Barin ma Nura yafi kowa son Zaman arewa Domin yace yana Burin ya samu aiki a arewa Yayi aure ya koma Chan da Zama,Shiyasa Duk bayan Wani Lokaci muna Ziyartsu Munje Har Gidan Baffa Kabiru da Baffa Mustapha da kuma Goggo  Bintalo,Da goggo Maimuna kuma sun ji Dadi Sosai Daada kuwa Muna da Lambar ta Lokaci Bayan Lokaci muna kiranta muna gaisawa Sai dai Koda yaushe mukayi Waya da ita Zencen ta Daya kenan Imu,Shi kuma Yana Chan makaranta ba Sosai ma yake zuwa Gida ba.
Sai Lokacin Daya gama Degree dinsa na Farko yazo Gida Hutu Lokacin ne Abba ya Rutsashi ya iza keyarsa Har Zuwa Dukku Gaban Daada Sai da suka kwana Biyu suka Dawo a wannan Zuwan ne Har su Baffa Kabiru sun zo Sun gansa Shima Lokacin yazo da' Wajensa Khamis Sa"an Imu din ne ammh Har suka Rabu Wata kyakyawan Mu"amala bata Hadasu ba  imran bai da Sakin jiki Sam da Mutane Daada Tayi mai Nasiha yayi bakam Kamar yaji yana komawa gida ya yi Cuku cukun ya koma Ibadan ya Dora Degree dinsa na Biyu,ya manta Da Fadan Daada.
Rayuwarmu Gidanmu Mun ginata Cikin Karatu Mai Zurfi ne Duka Dana Arabi Dana Bokon Harta Salima itama Tabi Sahu Ta Fadama Jami"ar Lagos ita Fanni Abba take karanta Wato Physchology
Muna gama Hada Degree din mu na Biyu Muka Samu manyan ayyuka Nura ya samu aiki a Federal Inland Revenua Service(FIRS)Wato Hukumar Haraji ta kasa Dake Jahar Lagos,Yaso ya samu a arewa sai kuma Allah ya Rubuta nan ne wajen cin Abincinsa.
Ni kuma na samu aiki a Hukumar INEC,rejen Jahar Lagos muka Fara aikin mu Cikin Lokaci kadan Cikin Naaara da Sa"a bamu Rufe Shekara Daya ba muka mallaki Motocin Hawa Dani da Nura,Da kudaden da muka Fara Ragema Abba Wasu Hidimdimun Ko Chan Dukku baya sanin muna turama Daada Sako Sai dai in ta Kirashi Tana Godiya ya sani.
Asma"u ma Ta gama Karatunta Har ta Fara aiki a wani State Hospital na Lagos a phamarcy, Dake Garin Lagos Salima ita kuma Tana Karatun ne bata gama ba,ita Burinta so Take ta Zama Dr.Salima Watarana Ta gaji Abba Ashe Ashe Burinta bazai Cika ba Domin Lokacinta aduniya bamai yawa bane..!
Yusuf ya Fada Hawaye masu Zafi suna kwaranyomasa Jikin Safiya yayi Sanyi Gabanta ya Fadi Cikin karyewar Murya tace"Innalillahi badai Rasuwa Tayi ba..?
Yusuf yaji Rauninsa ya Bayyana Cikin Karyewan Zuciya Dana Murya yacCigaba Da fadin"Imran ma ya gama Karatunsa ya Fara aiki da Bankin GT reshen Jahar Lagos Shima ya mallaki Motar Hawansa,da kudaden Daya Tsaya kan Kafafunsa..
Faruwar al"amarin Daya Faru damu ko nace ya afku ga gidanmu kaddaran Da bamu isa mu guje mata ba,..Gaddaran Datayi Sanadin da muka Rasa komai namu Kaddaran Dayasa muka bar komai namu muka zo nan muna Rayuwa inda bamu da kowa..
Watarana ce da Zukata da gangar Jiki bazata Taba Mantawa Dashi ba,Baffa Kabiru ne ya samu Hatsari Daga Garin Abuja zai je Dukku bai ma yi Nisa ba saosai al"amarin ya Faru aka Dawo Dashi Specialist Dake Abuja aka Bashi Taimakon gaggawa Jikin nashi Da Sauki ba karaya sai dai Yaji Ciwo Kadan kadan Motarsa ne tayi Dameji bama Zata taahi ba Hankalu suka Tashi Kwarai Abba da Anni Ranar basu Iya barci ba Abba Sai Mtsawa yake a samu Buking din Jirgi Zuwa Abuja,Allahu akbar Allah Sarki Rayuwa Nura Shi yaje Filin Jirgi yayi Cuku Cukun komai,Allah ya Rubuta Lokacin Abba aduniya Bai kare ba wani Taron Malamai ya Tsaidashi,Ni kuma A wajen aiki ba"a barni ba Imran kuma Bama wanda yabi ta kansa Sanin Halinsa Ganin haka yasa Abba yace Nura da Anni da Salima da Asma"u su  Farayin gaba Kafin mu muzo Daga Baya Tunda Lokacin Munari suna Jarabawa a makaranta,Abba kuma Zai Tsaya Taron su na Malamai sai Zuwa Gobe in sun gama Ni dashi Zamu Bi Jirgi zuwa Abuja muje mu Duba Baffa Kabiru Tunda Duka yan"uwa sun isa Chan Abuja.
Har yau bazan manta da wannan Ranar ba Imran Tun bakwai na Safe ya Fita Zuwa Wajen aikinsa Munari na makaranta Ni Abba yasa na kai Su Anni da Nura da Asma"u da Salima Filin Jirgi na Murtala Muhammed ban kuma bar Wajen ba sai da Jirgin su ya Tashi ya Lula Sararin Samaniya.
Na Dade tsaye Afilin jirgin bayan Tashinsy Na kasa Shiga Mota na koma Wajen aikina Haka kurum nake jin kaina wani iri kamar Wani abu Zai Faru Dani ashe ashe kuwa hakane Na koma Office na kasa Tabuka komai ko Cikakken Minti Talatin banyi ba Wayar Abba ta Shigomin ina Dagawa Naji Abba Cikij karaji yana Tambayana Jirgin su Anni ne ya tashi Minti Talatin da yawuce..!?
Ni kaina na Rude bansan ina kaina yake ba Cikin Rudewa nace ma Abba Eh Sune Daganan ban ji komai ba sai karar Faduwar Abu naji Da Hayaniya Daganan naji Shuru Hankalina ya Tashi na Fito Jikina narawa anan naji Labarin Dayayi barazanar Tafiya da Numfashina Wai Jirgin Airic Daya Tashi Daga Filin Jirgin Murtala Muhammed Daga Lagos Zuwa Abuja Minti Talatin da suka Wuce ya Fadi a wani Daji Bayan ya bar Lagos.
News na gani a Tv Dake ma"ikatan mu...!
Yusuf yana kawo nan ya Saki kuka mai karfi Safiya ma Tuni Ta Fashe da kukan Cikin kukan Take Fadin"innalillahi Wa"inna Ilaihirraju"un..Daman yan Gidan ku na Cikin wannan Hadarin Jirgin Daya Cinye Rayuwanka Yan arewa Da yawa..!?
Yusuf na Kuka yace"Da yan gidanmu Safiya..Da Anni da Nura da Salima da Asma"u Sun konee kurmus ko gawansu bamu gani ba kawai nidai na Farkane na ganni a asibiti Imran na Gefena yana ta kuka Kukan Da Tunda nake dashi ban Taba ganinsa yayi kuka ba,ina mikewa na Fara Tambayansa ina Abba sai dai bai min mgana ba ya Nunamin Abba Dake gefena Kwance Shima anamai karin Ruwa,Safiya bazan Tsaya baki Labaein Irin Tashin Hankalin da Muka Tsinci kanmu aciki,Abba ya Farka yana kuka yana Fizge Fizge yana Kiran sunan Anni da Nura da Asma"u da Salima Likitoci sun kasa Controlling dinsa Bamu da wani kwarin Gwiwa Domin Rashin da mukayi Babba ne wanda Babu Wani Abunda zai iya maida wannan Gibin.
Ni da kaina na kira Wayar Baffa Mustpaha na Sanar dashi ina kuka Chan ma Hankula suka taahi Domin Gabadaya Hadarin Jirgi a Karade kasa Tunda Yawanci Duk yan arewa ne da Wasu manya a gwannati.
Dagani Har Imran bamu kwana agidanmu ba Ni naje makaranrar su Munari na Daukota muka Koma asibiti muka Hada kai mu uku muna kuka Tun Munari bata gane Har ta Fahimta nan muka kwana da Abba asibiti,washegari kuma Baffa Mustpha da Baffa Kabiru Da ciwon da komai ya tashi ya Taho,sun same mu Cikin Wani Hali,Abbanmu kuma ya Fara Fita Daga Hayyacinsa Batare da Shawara damu ba suka Gama Cuku Cukunsu sukayimana Bukking din Flight Bayan sun karbi Report din Abba na asibiti din Abba Suka Tarkatamu Zuwa Gida muka Debo kayanmi Harda na Abba Dana munari Suka Tasamu agaba Sai Filin Jirgi Duk da Tsorata da Hawa Jirgi daya shiga Ranmu Hakanan muka Shiga bazan manta ba sai da Imran ya Suma Saboda Firgita.
Daga Lagos Gombe muka Sauka Mijin Goggo Bintalo yazo ya kwashemu sai Dukku Gidan Daada koda muka isa Gida ya Cika da Dangi ana ta Koke koke Daada Tayi kuka kamar Idanuwanta Zasu Makamce,anan akayi karban Gaisuwa Har akayi Sadakan Bakwai Abba Baya Cikin Hankakinsa sai sambatu da Surutai,Mukan mu gamu nan kawai ammh Komai ya Fita kanmu da Rayuwarmu Gabadaya Bama da Wani Tunani sai abunda aka Fadamana Tunanin mu da komai ya Tsaya Cak.Har gwarani akan Imran da Munari ana ganin kamar bai Damu da Danginsa ba Ashe ashe abun sai yafi Tabasa Fiye da kowa.
Saboda Halin da Abba yake Ciki yasa bamy koma Gida ba muna Dukku gaban Daada sai dai duk Sati Baffa Kabiru da Baffa Mustpaha suna Hanyar Zuwa ganin Abba ya Kamu da Cutar nan ta Depression yasa Suka Daukesa suka kaisa asibiti aka Dubasa aka bashi mgunguna da Shawarwari da Farko Abun kamar yayi aiki Daga Baya sai Abba ya Kara Rikicewa Bawanda zai Fahimci Halin da Abbanmu ke Ciki  sai mu da muka Dandanin Zafin Abun,Shiyasa cikin Yan"uwan Abba suka kasa mai Uzuri Ballatana su Fahimci Wani Hali yake Ciki basu Taba Dadanin Zafin Rashin Daya Dandana bane Shiyasa suka Fara ganin Laifinsa suna Fadin bai da Takwalli ne Dagashi har mu da kullum bamu da aiki sai mu tasaahi muna kuka ai ba kanmu Farau Mutuwa da Rashi ba Anni da Asma"u da Salima da Nura Sun Tafi kenan har Abada bazasu Taba Dawowa ba..Daada ce Kadai ta Fahimci Halin da Abbanmu da mu kanmu muke Ciki Baffa Kabiru yafi kowa Daukan Zafi Daga Karshe sai ya Zare hannunsa kan Abbanmu Tunda Likita yace Mgani baya aiki Tunda Abba bai Rage Damuwa ba kuma yaki ya manta da Abunda ya Faru Dashi..? taya zamu manta da wannan Rashin..? Ai har Abada Gidanmu ya Shiga kuncin da Bazamu Taba Fita acikinsa ba.
Tun bamu gane ba Har muka gane irin Yadda yan"uwan Abba ke kallonsa a Saboda Rashin Takwalli Ya koma Mahaukaci bashi da aiki sai Sambatu,Mukuma ya"yansa mu Bar komai nami mun dawo muna Rayuwar kawai Saboda Baffa Kabiru yayi yayi Dani da Imran mu koma Lagos Saboda aikin mu muka ki..Imran ya Nunamai Aduniya Bamu da wani abunda ya Ragemana Bayan Abba Saboda Haka ba inda Zamu muna Tare Dashi Dalilin haka yasa muka kusa Wata Shidda a Dukku,ayyukan mu Duka sun Tsaya an gaji da kiranmu an kyalemu,Munari Tuni Karatunta ya Tsaya Cak itama Bata da wani Sauran abunda Zata Dora.
Ni ban yi Tunanin Dauke Abba mu bar Dukku ba Imu ne ya kawo mana Wannan Tunanin Tun Lokacin Daya iske su Baffa Kabiru sun Tarun ma Abba suna ta mai Fadan yaki ya yarda da Kaddara ya Dawo Daidai ya Zauna yana Biyemana yana kwana kuka Mutuwa ce Dayace kuma wanda ya Mutu baya Dawowa Abba na kuka bayacewa komai Domin alokacin basu san Dacin Dayake ji ba Daada ma kukan Take ammh sun kasa Fahimtarsa,Suna cewa ya zama Mahaukacin karfi Dayaji kamar ba Musulmi ba,Baffa Mustapha baya mgana sai Baffa Kabiru yafi kowa Zakewa wannan Dalili yasa Imran ya mtsamin kan muce Zamu Tafi da Abba Lagos muje Chan muka Cigaba da aikin mu muna kula Dashi..Abun mamaki da muka Furta Daada ce kadai tayi musu ammh Banda Sauran yan"uwan Abba nan da suka amince acewarsu kila zai fi Samun Sauki batare da Rakiyan kowa ba Muka bar Dukku Zuwa Lagos,a mota muka Yi Tafiyar Domin Tun Abunda ya Faru Har Abada muka Tsani Jirgi.
Mun Dawo Gidanmu na Lagos da Zama sai dai Babu abunda ya Sauya Nidai ban koma bakin aikina ba Hakama Imran,Ballatana mu kokarta mu maida Munari makaranta Duk wani Farincikin Gidanmu sai ya Gushe sai kunci da Bakinciki Abba koda yaushe yana Daki yana kuka yana Samabtu mu kanmu bamu da Wata natsuwa.
Bayan Dawowarmu da Wata Daya Baffa Kabiru ya zo ganin mu Cikin Wannan Halin ya kara Bata ransa yayi ta Zaginmu yana mana Fada Abbanmu kuwa kamar ya Dakesa Daga karshe yace yaje yayi ta Haukansa In ya Haukace ni da Imran sai mu kaisa Gidan Mahaukata ko Zama bai yi ba ya Juya shima zuwan da yayi Daada ce ta matsamai yazo ya Dubamu.
Awannan Ranar Ran Imu ya baci ya Fita,Fitan da bai Dawo ba sai da ya kwana Biyu yana Dawowa na gansa ya iya Busa Sigari,shi kuma ya ce Dole ne muyi Nisa da Komai namu in muna so mu Cigaba da Zama Lafiya Inda ba wanda yasan Labarin Gidanmu Ballatana akira Abbanmu da Mahaukaci muyi nisa da komai nanu asali,Nasaba Dukiya aiki da Komai na Rayuwa Ni kuma na amince Domin Lokacin na Fara Tsorata da komai kada Imu ya Fada wani Hanyar Banza.
Bamu saida komai namu ba Gida Motoci Duka suna Lagos sai dai mun kai Takardan Barin aiki Daga Ma"aikatanmu da Muke aiki sai muka Tattara kudi Katin bankin mu Dana Abba dana Nura dana Asma"u da Takardun makarantarmu Dana Munari sai kayan sawanmu,muka Diba iya wanda Zamu iya muka Baro Lagos Bayan mun Sallami mai Gadi mun kulle Gidanmu bamu ma Tunanin Zamu Dwo Watarana ba sai Domin yin hakan Shine Mafitarmu Mun Taho da Abba Kano bai Cikin Hayyacinsa a Hotel muka Sauka Ni na Fita Na Bincikamana Gida Cikin kwana Biyu muka kara mallakan Wani gidan,Shine wanda muke Ciki,Muka Tattaro muka Dawo Domin Gina wata Sabuwar Rayuwa Bayan mun bar Duka Layukan mu da Wayoyim mu a Lagos Da komai inda Za"a Same mu saboda bama Bukatar Taimaakon kowa Tunda ankasa Fahimtar,Radadin Dake Cikin Babban Rashin da mukayi.
Ganin in na Zauna Haka Rayuwar Gidanmu Zata kara Lalacewa Cikin kunci,Sai na yanke Shawaran Fita Neman aiki Duk da bamu rasa komai ba Muna da Kudi,ammh ban Zauna ba Cikin ikon Allah na samu aiki a hukumar Inec ta nan Reshen Jahar Kano,Ni ne na Zama Uwa da Uban Imran da Munari na Zama Garkuwan Abba na Daukan Mai likitan Dake Zuwa Gida yana Dubasa Duk Bayan Wata Daya,koda Abba ya Fara Dawowa Hayyacinsa ya Fahimci Abunda muka aikata yayi ta kuka sai dai Bai Da Cikakkiyar Lafiyar da Zai iyq Tambayanmu meyasa mukayi hakan..?
Da albashina na Siya Motan Hawa na Siya ma Imran Mashin Tunda yace bai Bukatar Mota aiki ma yace bazai koma ba,Shi Baahi da Sauran wani Buri kuma,nayi nayi na Rabashi da Shan Sigari na kasa Saboda ya Riga ya Zama Jikinsa bazai iya Awa Daya bai Sha Sigari ba,duk Wasu Sabbin Halaye Rashi ne da Rayuwa suka maida Imran haka,Ni nayi Tunanin Inganta Rayuwar Munari Tunda ita Kadai take Ragemana na maidata makaranta..
Da farko ban Yi niyyar Fara Neman aure ba sai nayi Tunanin auran nawa Zai Tamaka ma Rayuwar Imran da Munari Sai dai kash Duk inda na Nemi aure sai mgana ta kamkama sai ta watse duk inda akayi Binciken Gidanmu aka gano wani abu duk da bama Hulda da kowa abun mamaki labarin komai sai ya fita, bamu da kowa kuma Abba bashi da lafiya yana Ciwon Hauka Dalilin haka Imran ya karya Hannun Kawun Wata Asma"u Dana Nema aka Hanashi Daga Karshe shi kawun nata yaci Zarafin Gidanmu Shari"a Dakyar na iya kasheta Na nemi aure kusan sau uku bana samu sai a kanki kema din da kokarin Imu na Sameki Tun kuma Bayan Tafiyarmu Har yau wani Daga Cikin Ahalin mu baisan inda muke ba bamu sani ba ko sun neme mu mudai bamu nemi kowa ba Har Rana mai kama ta yau..Ko naso mu nemi gida Imran ke Hanani Domin shi yafi Daukan Abubuwan da suka Faru  Fiye dani Kaina.







*Shakira...*
3/22/22, 23:04 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*DEDICATED TO:*
*Aisha alto(Sisinah)*
*Chubado muhammad(Uwar dakina)*
*Yahanasu Soupnass(Qawalli1)*
*Kausar salis(My jika)*
*Rahma Ladingo(Dota)*

             *🅿?14*

"Kinji irin kaddaran Data Fadama Gidanmu Babe..Tun bayan Faruwar Al"amarin Komai namu ya tsaya Cak Kawai Rayuwar muke gamu nan bawani Jin dadi ba Farinciki ba Walwala.
Kinji Kuma Dalilin daya sa muka Baro komai namu kinji kuma irin Halin da muka Shiga da wanda Abba ya Shiga Da Dalilin mu na barin Komai namu muka Dawo muna Rayuwa inda ba"a Sanmu ba kuma kinji Irin Lalauran Data samu Abba Shi din ba Mahaukaci bane yanayin Rayuwa da kaddaran Allah ne suka Maidashi haka.
Ya karishe Fada yana Tsiyayan Hawaye,Safiya ma Dake Jikinsa Hawayen Take,Cikin Sarkewar Murya tace"Allah ya jikansu Anni..Allah yayi musu Rahma Allah ya kyautata Makwancinsu.Hakika kunga Babban Rashi..Tabbas kun Hadu da Jarabawa Mai girma Mutuwar Rai har Guda Hudu a Lokaci Daya dole Zuciya Zata Raunana..Allah ya karbi Shahadarsu..!
Yusuf na jan majina yake amsa mata da Ameen Ameen..
Safiya ta Cigaba da Fadin"Tabbas su Baffa suma basu kyauta ba..kamata yayi su ja ku ajiki da Lallashi da Nasiha da komai sai kuFara manta abunda ya Faru..Su Rika Nuna muku ku Fauwalama Allah komai su Nuna muku Hakan bashine Karshen Rayuwar ba akwai Wasu agaba..Ya kamata ace sun Zauna sunfi Kowa Fahimtar Halin da kuke Ciki..Abba kuma ya kasance koda yaushe Suna Lallashinsa da kokarin Nuna mai Komai Daya Faru da Sanin Allah kuma Mutuwa Dayace Muma Jiranta Muke,su da suka Tafi basu yi Sauri ba Muma da muke Duniyan Jiranta Muke na Tabbata da yanzu baku kai ga Daukan Wannan Matakin ba My Dear..!
Yusuf Dake Sauraran Safiya yace"Gaskiya ne Babe..! Yafada Cikin Sanyin Murya mikewa Tayi Daga Jikinsa,Tana Fadin"My Dear Tashi muyi mgana..!
Bai mata Musu ba ya Mike Zaune ya saka hannu ya kunna Hasken Dakin Suka Kurama juna ido Kan kirjinsa ta koma ta Lafe Tana Fadin"Ina da Wata Shawara My Dear game da Situation din Abba He Need a Help..ba na kai ka dai ba..Taimako yake Nema Awajenmu Dukkanmu matukar muna so ya samu Lafiya ya Daina Tuna Abunda ya Faru.!
Da Sauri Yusuf yace"Wata Shawara ce Babe na..?
Dagowa tayi Tana Kallonsa Hannunsa ta Riko Duka Biyun Tana Fadin"Bai Kamata ku bar Abba yana Fuskatar wannan Abun shi Kadai ba..Kada kuyi Treeting dinsa kamar su Baffa My Dear..Bai dace ace Abba yana Rayuwa acikin Daki ba ko Falo baya iya Fitowa Ahalin yana da lafiyar Kafarsa..Bai kuma Dace arika barinsa Shi kadai ba..Sai Tunanin Da ba"a so Sai yaRika Samun Matsugguni acikin Zuciyarsa ..Masu irin Laluransu suna Bukatar Wani a kusa Dashi a Koyaushe..Ba kamar yadda kuke Barinsa ya Wuni Shi kadai ba Hakan yakan Kara Haifar da Ruruwan Raunin Dayake Cikin Zuciyarsa..Abba yana Bukatar ya Riks Fitowa yana Sakewa yana Walwala,Ya Chanchanci yayi Farinciki..Duk Abunda Zai sakashi Farinciki Shi zAmu Rika Kokarin Yi agabansa muyi Keeping dinsa Yadda Tunani da Damuwa baza ma su samu Damar Nukurkusan sa ba..Kaga Ta hakane kadai Magungunan Likita Zai yi Amfani ajikinsa amfanin na Har Abada ba na dan Lokaci ba..!
Tunda ta Fara mgana ya kafeta da Ido Zuciyarsa ta Cika da Farinciki Da Alfaharin Samun Macen Kirki kamar Safiya DAmam ance Duk Tunanin Namiji Ita mace Tamkar Garkuwa ce Garesa Gashi Cikin Lokaci Tana Warware Musu mtsalan da Shekara da Shekaru suka kasa mganceta.
Girgizashi Tayi ganin yana ta Kallonta bai yi mgana ba tace"Bakace komai ba My Dear..?
Yusuf ya Lumshe ido Kafin yace"Ina Jinki..Zuciyata ce ta Cika da Girma da alfaharin Zamowa Miji gareki Babe na..Ina jinki cigaba da Fadamin yadda komai Zai Tafi Wlh har na Fara Ganin Abba ya samu Lafiya na Har Abada..!
Safiya tace"Insha Allahu Abba zai Samu Lafiya indai muka Taru muka Tallafamai..!
Na farko Abba zai Daina Zaman Daki Zai kasance yana Wuni a Falo,sannan Zamu samo mai Abubuwan da zasu Debemai kewa kamar su Karatun azkar da karatun Karamin Qur"ani wanda Zai Rika Karantawa koda yaushe....Ko Jaridu Domin yarika karantawa yana Sanin Abunda Duniya take Ciki..Littafan Karatun Daya Shafi Fannin sa Wato Physchology,Abu na gaba kuma ya Daina Salla agida ya kasance yana Shiga Cikin mutane ko da bada Wata Mu"amala ba,Ya rika Sallar Cikin Jam"i hakan ma zai kara Taimakamai sosai Wajen Rage Damuwa da Tunani Sannan ya kamata Mu Rika Haduwa dukkanmu Da Daddare muyi Dinner Tare,Bayan mun gama kafin kowanne ya Shiga Barci mu Zauna dashi muyi Hira Labarai na ban Dariya wadanda Zasu Sanyashi Nishadi sannan kuma ya zama Dole ya rika ganin kowa Cikin Walwala ta hakane Shima zai yi kokarin manta komai sabi da ku..Masu irin Laluran Abba suna Bukatar taimakon Mutanen Dake kusa Dasu...!
Bata gama mganarta ba tajita a Jikinsa Ya Rumgumeta Kamkam Kamae wani Zai kwaceta Cikin Farinciki yake Fadin"Tanque so Much Babe na..Allah yayi miki Albarka..U are a Bleesing From Allah..!
Safiya itama ta saka Hannuwa ta Rumgumshi Tana Fadin"My Pleasure My Dear..Is My Duty Amtsayina na Matarka na Tallafeka a Dukkan Komai na al"amuranka Shine Zamantakewar..!
Kamkameta Kawai ya karayi yana Fadin"Alhamdulillah..Allah ne Abun godiya..!
Sun Dauki Tsawon Lokaci ahaka kafin ya Dagota yana Share Mata Guntun Hawayen Dake Idanunta Itama ta Saka Tattausan Hannunta ta Gogemai Nashi a Tare suka Sakarma Juna Mirmishi Hancinsu ya Hada Waje Daya yana Fadin"I love u Babe na..!
Itama cikin Wani Shauki Tace"Love u More and More My Dear..!
Komawa sukayi suka kwanta Bayan ya Dauketa Gabadayaanta ya Dorata Saman Jikinsa,Ya Kashe Musu Hasken Dakin Lokaci Daya ya ja musu Blanket yana Fadin"Oya Barci..Zamu karisa mganar dq Safe..!
Tana Dariya tace"Ok..My Dear..!

*****
Washegari Wasu Zukatan sun Tashi ba Dadi yayinda Wasu Zukatan suka Tashi Cikin Farincikin,Cikin Wadanda Suka kwana Cikin Bakinciki Imran ne Farko Kwata kwata Barci Barawo ne kadai ya iya sacesa Daya Runtse ido Sai ya rika ganin Inteesar Sanda Take Tofar da Miyau Lokaci Daya da. Toshe Hancinta In kuma ya yi Shuru kunnuwansa Amon Muryanta suke ji Inda Ta Kallesa Tana Kiramai Ta"awizi kamar Taga Shedan kwana Yayi Busa Sigari sai da ya karar da Kwalaye uku kana ya Saurara Gabadaya Bakincikin Yadda bai Sauyama Yarinyar nan kammani bane ya kamashi,Daya sani ko Mari ya Tsinketa Dashi ya Tattakata Wanda nan gaba bazata Kara Raina wani bama Shi ba,Ammh Takaichinsa Daya Da ya bari ta Subucemai ya Zama Dole ya Nemi Sagir ko wacece zai Santa Koma Daga ina take yana da Masaniyar komai ya Zama Dole ya Nemota ko domin yaci Ubanta ya Nuna Mata Karyanta Imran Ba wajen Wasanta bane.
Bangaran Inteesar kuwa Tayi kwanan Farinciki Hankalinta kwance Tuni ta manta da wani Imran Ballatana Abunda ya Faru Daman koda Mama ta Dawo Ta gaji ta Fara jin Barci Sama Sama Sukayi mgana tace mata ta Shiga Makota ne,Daganan Ciki Ta Shige.Bayan Ta Tatarra Littafanta,Tayi Sallar Isha"i tabi Lafiyan Gado Barci ya Fara Daukanta Taji Mganar Sagir din nan Falon Mama Ita dai bata kara Samun kanta ba sai da asuba da Mama tasheta Sallah.
Bayan ta idar da Sallar ne Tayi azkar ta Fita Tsakar gida Taga Mama na Shara ta gaisheta sai ta amshi Sharan Mama bata Hanata ba tunda Umma tace ta rika bata kowani aiki ne Saboda Ita Macece Domin amfanin kanta Watarana.
Ita ta Share Tsakar gidan Tas ta koma ta Gyara Cikin Dakin da Falo ta Share ta Goge kafin ta gama Mama ta Dafa mata Ruwan Zafi sai ta Juye tayi Wanka Koda ta Fito 7:30am na Safe kuma ta Kira Classrep dinsu yace mata 8am suke da Lacture,Shiyasa Take Sauri Ko Tea da Buredin da mama ta Hadamata bata Tsaya Sha ba Complex Kadai ta sha..Sai Cake Data Diba ta saka ajaka ta Dauki Littafanta ta Fito Tana yima Mama Sallama ta Dauki Kudi ta bata taki amsa tace Tana da Kudi a Hanunta Jin Haka yasa Mama Ta kyaleta ammh Sai ta Buga ma Sagir Kofa tace ya Fito ya Raka Intee ta samu abun Hawa Zuwa makaranta.
Haka kuwa akayi Shi ya Rakata Har Bakin Titi suna Tafe suna Hira sai da ta Samu Abun Hawa Zuwa Cikin makaranta Sannan ya Dawo yayi wanka ya karya ya Fita Zuwa Shago yau bai da Shiga makaranta sai Gobe.
Bangaransu Yusuf da Amaryansa Safiya Lafiya kalau suka Tashi Cikin Farinciki ba domin ya Hanata Fitowa da Wuri ba da Tun Safe taso ta Fita Kitchen Ta Taya Munari Hada Breakfast,yusuf ya hanata sai dai ta Tayashi Shirya wa zai tafi Wajen aiki Domin ya Sanar da yayi aure ko Zai Samu koda Hutun Sati Daya ne..Dukkansu sunyi wanka Safiya ta Shirya Cikin Daya Daga Cikin kayanta na Gida,Shi kuma Yusuf yana Sanye da kananun kaya ne,Sun Fito Falon kenan Sukaci karo da Munari ta Fito Daga Dakin Abba itama Cikin Shirin Fita Tana ganinsu ta Washe baki Tana Fadin"Mr and Mrs Yusuf Abubakar Malami.. Gud Mrning..!
Tafada Tana yar Dariya Yusuf ya Kalleta Lokaci

Please Login or Register in order to submit comment