Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauri yace"Oya muje..Bana son wata mgana kafin ki fashemin da kuka Shagwabbiya kawai..!
Yafada yana Kauda kansa dan Dariya Tayi kafin ta wuce yabi bayanta Sahu Sahu kafa kafa kamar wani mai tsa ranta Har Kofar gidan su Sagir Ita kuwa Gabadaya ta saka gane yanayinta jinta take kamar tana yawo Saman gajimare sai da suka iso kana yaja ya Tsaya ita kuma ta Waigo Tana kallonsa,Shima ya kallentan sai da ya Dauke kansa Mirmishi tayimai kafin tace"Nagode..!
Dahaka ta juya ta shiga Gida,dan Bakinsa yadan Cija kafin ya Juya zuwa Gida Aransa yana Fadin"Batajin mgana yanzu ba ban rakota ba wani abu ya Kara faruwa fa..? Da sauri ya Kauda wannan Tunanin jin har Zuciyarsa ta fara rawa.
Tana Shiga gida tama Mama sannu da gida ta Shiga Tiolet ta Dauro alwala tazo Tayi sallah bayan ta Idar ne ta Duba wayarta Taga Kiran Ya Sadam da Anty Aneesa,Da Mayen nan Khamis karamin Tsaki taja kaawai Ya Sadam ta Fara Kira ya dauka bayan sun gaisa ya Fara bata Hakurin rashin Dawowarsa tace bakomai kana ya bama Anty Aneesa ta yi mata ban gajiya Tana Tambayan Munari tace Yanzu ta Dawo daga Rakata Daga haka suka yanke kiran bayan Ya Sadam din yayi ma Inteesar Alkawarin sunan nan zuwa.
Aneesa Tayi ma Sadam mganar Munari tace"Honey ni kuwa naso ka Dawo dazu kaga wani abun mamaki..?
Yana kai Lomar abinci bakinsa ya Dakata yana Fadin"Mamakin me..?
Gyara Zama Inteesae tayi Tana Fadin"Kawar Inteesar da suka zo Tare take min kama da karamar yarinyar nan ta Hoton nan da Daada ta nuna mana adukku..!
Kallomta yayi kur kafin yace"Kina Nufin Hoton iyalan Kawu Malami..?
Aneesa ta Daga mai kai sai taga yayi Dariya yana Fadin"Daga ganin..Hoto sai kiga yarinyar mutane kice itace..?Ai da itane da Inteesar din ta Fara sanin hakan..!
Aneesa tace"To in ba itabace kamar har ta baci Wlh..Saboda haka nace muyi Hoto bari ka ganta..!
Cikin Halin ko in kula yace"Yauwa muga Hoton..!
Ta Lalubo Hoton Munarin kenan zata mikamai Waleeda Dake jikinta ta kwabe hannunta Wayar ta Fadi kasa ta Watse Ran Aneesa ya baci ta Maketa Ya sadam ya fara fada yana Fadin"Saboda Wayar banza zaki Daki yarinya..!
Cikin Kufulawa tace"in ta Lalatamin fa..? Banza yayi da ita ya Dauketa yana Lallashi ita kuma Aneesa ta Duka Tana Tattara Wayarta bayan ta Hadata Tayi tayi ta ki kawowa sai Ranta ya baci ta Shige Dakinta ta Jefa Wayar Cikin Wardrope shikenan ganin Hoto bai samu ba.

Tafiyar Mama ya tashi Ana gobe Zata tafi Taje gidansu Munari da kanta Inteesar ta Rakata ta gaida Anty Safiya wacce ke fama da kasala,da Amai kana ta gayama Abba Zataje Biki Zata bar Inteesar Wajensu Abba yace bakomai bama sai tazo ta Taambaya ba,Inteesar kamar ya take a wajensa,Munari da Inteesar sun fi kowa Murnan hakan,Washegari Tun Safe Sagir ya Raka Mama tasha tahau Motan Kaduna,Inteesar kuma sun Tafi makaranta sai da suka Dawo Munari ts Tayata Debo kayan da Zatayi amfani Dashi kafin Mama ta Dawo,Sagir daman baya Zaman gida yana Shago Abinci kuma Siya zai rika yi Shima Ranar asabar zai tafi kadunan.
Imran baisan Inteesar ta Dawo Gidansu ba sai da Sassafe ya Fito zai Tafi jogging ya ganta Tana goge Dining Abun ya bashi mamaki har tsayawa yayi yana Kallonta baki sake Data gaisheshi Abun sai ya kusa saka Inteesar Dariya ta Rufe bakinta ta Shige Kitchen da gudu Munari Dake Feran Dankali ta bita da kallo.
Daman saboda ta gansa tace ma Munari bari ita ta gyara Falon ta Goge,Ita kuma ta Soya Dankali da kwai Kada su makara Karfe 8:30am suke da Karatu,Anty Safiya kuma Lafiyan sai Hankali bata Girki a asibiti ance ta Huta sosai kafin ta fara aiki.
Kuma ta gansa Taji sanyi acikin Ranta ita kanta akwanakin nan ta rasa meke Damunta jinta da ganinta Imran ne in bata gansa ba ta rika Shiga Damuwa kenan sai ta gansa take jin Sanyi,Sabida ta gansa tazo gidan ta Wuni bata tafiya sai duhu yayi Saboda ya Rakata tasan bazai taba barinta tabi Hanya ita kadai ba Kamar ma Dakonta yake yi Data Fito zata gansa yana Binta abaya koda bazai ce mata komai ba har sai ta Shiga gida zai koma ya Lura batajin mgana ga Tsoro ga Taurin kai bayason yayi mgana ta sakamai kuka ya Lura ta Fiye shagwaba Shiyasa Ya gwammace ya Rika gadinta Kullum in tazo takai yammah agidansu.
Har ya Dawo Daga Jogging yana Mamakinta Yana Shigowa Haraban Gidan ya gansu Yusuf ya daukesu zuwa makaranta Sai da ya Shiga Gidan ne ya Shiga wajen Abba yana so ya Tambayeshi ammh ya kasa sai ya bar Abun aranshi.
Sai dai ya samu amsar Tambayarsa Wajen Sagir Tunda ya fadamai Gobe Zai tafi kaduna Daurin aure Mama ma tana chan Tun jiya Shiyasa Inteesar ta koma Gidanku maimakon ada da bayason wani ya Rabesu,sai yaji Salama da wani Natsuwar da bai taba jiba.
Washegari Asabar da kanshi ya Raka Sagir tasha akan Mashin dinsa ya Daukesa Sagir yamai Tayin zuwa yace bazai jeba bai bar wajen ba sai da Motarsu tatashi kana ya koma Gida.
Kamar yadda suka saba kwana Biyun nan Suna Falo ita da Munari suna Kallo suna Hiramsu Anty Safiya na Barayinta ita da Ya Yusuf Abba ne Kuma yanzu yana cikin Dakinsa In suka gansa sai su Natsu suna Raba ido Da ya shiga Daki sai su Fara Dariya.
Hakaman yake jin Dadin ganinta a kusa Dashi koda bazai mata mgana bane baya ma son Mama ta Dawo ace ta koma Gida,Ranar asabar da yammh Tasleem tazo ita da Mommy da Anty Saratu suka zo Duba Safiyar basu jima ba Mommy da Anty Sarati suka tafi suka bar Tasleem Datace nan zata Kwana sai Monday Zata koma Taga su Inteesar.
Suka Hade su uku suna ta Bidrinsu Inteesar ne ke jansu zaman Falo Saboda Taga Giftawan Imran Munari kuwa bata so saboda Imran bayasom Hayaniya tafi son su zauna Shashen Anty Safiya yafi susha Hiransu kala kala bamai Takuta musu.
Adakin Munari suka Kwama Dukkansu Harda Tasleem Dataki kwana Shashen Anty Safiya.
Washegari Lahadi suka zage suka gyara Gidan
Inteesar ta matsa ma Munari su Zauna afalo su kunna Kallo,bayan sun Karya Abba na Samam Dining shi da Ya Yusuf suna Cin Abinci suna Hira su su kuma suna saman kujerin falom Sun kunna Arewa24,lokacin ana Maimaicin kwana Cha"asin suna ta Hayaniya Munari da Tasleem nata bama Inteesar Labarin Film din Tunda ita ba wani Kallo take sosai ba Daman Saboda Taga Imran ne yasa ta Mtsa musu su Zauna.
Yana cikin Dakinsa Hayaniyarsu duk ta Cikamai kunni Tun yana Sharewa Har Ransa ya baci ya tashi ya Fito a Fusace Jikinsa ko Riga babu Daga shi sai 3Quater,kamar Walkiya suka gansa gaban Kayan kallon ya Zare Soket din gabadaya ya yar a kasa ai kafin ya juyo Munari tayi ta kanta Tasleem ma ta mara mata baya Inteesar ne ta Tsaya tana Raba ido Hararanta yayi kafin yace"Bar nan Wajen..!
Da sauri ta Mike tana Kokarin Hana kanta Dariya yana kallonta aransa yace"Shikenan ta gama Rainani.!
Abba suna gefe suna kallobsu Abba ya Sa baki ya Kirashi ya Juyo yana kallonsa Cikin Mirmishi yace"kai da idon sani da bako Duk Dayane awajen ka ko Imran..?
Dakuna Fuska yayi kafin yace"Abba Hayaniya suke min akaina..!
Yusuf yace"Ai ba Dakinka suka shiga ba Ishasshe..!
Bata rai yayi ko mgana bai kara ba Ya shige daki har yana Bango Kofa Yusuf yayi Dariya yana Fadin"Na tabo Yaron Abba..!
Mirmishi kadai Abba yayi bai kara mgana ba.
Su kuwa Shashen Anty Safiya suka koma suna Sauke Numfashi Munari Ba bakin mgana Inteesar na Dariya ta Daka mata Duka tana fadin yau daya Daketa kanta zata rama ta kusa jamata masifarsa Ita dai Dariya kawai takeyi Burinta ya Cika Tunda ta gansa,sai da yanayin Data gansa ayau din ba Riga Gabadaya yasa ta jin wani iri Imran yana da Cikar Zatin da kowacce Lafiyayyiyar mace in ta gansa ahaka Taji wani iri hakan ne ya Faru da Inteesar wacce ta Wuni Tunaninsa bai bace mata ba.








*Shakira*
3/22/22, 23:07 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️*



             *🅿?29*

Har garin Allah ya waye Inteesar bata kara saka Imran a idonta ba duk da kuwa yadda taso ta kara ganinsa,Gashi yau din ta kama Monday ne suna Class da safe shiyasa suka Shirya da wuri Ya yusuf ya daukesu yakaisu kafin ya wuce wajen aiki basu kuma dawo ba sai yammah Tun suna makaranta Inteesar sukayi Mgana da Umma ta fadamata Su Mama sun kamo Hanya tun dazu shiyasa da suka dawo nan ta Tsaya tunda sun dawo gama Sagir nan a kofar Shagonsa shida Imran suna mgana.
Sun gaisheshi Sagir ya amsa cikin Fara"a yana Tambayansu karatu sukace Alhamdulillah,Inteesar na Tambayansa ya Kaduna yana Fadamata Hargidansu yaje Imran na Gefe ya Kauda kansa yau din ko sau Daya bai kalleta ba bayaso Zuciyarsa ta Saba da kallonta alhalin yau zata koma Wajen Mama,lokacin da Sagir ya Kirasa ya gayamai sun dawo bai ji dadi ba ko baya ganinta yana Samun Natsuwar Sanin Tabbas Numfashinta yana Kusa da nashi,yanzu din ma ita yake son gani yasa da Sagir ya kirasa yace sun dawo ya Fito suka Hadu Tunda yaga Munari bata dawo ba ya tabatar da suna makaranta in ma kuma sun dawo suna gidan su Sagir ya Tabbatar ma kansa zai ganta..
Har suka wuce cikin gida kansa na kallon wani waje,Duk da Satan kallonsa da Inteesar din Tayi tayi bata Samu Nasara Hada ido dashi ba.
Sagir na lura dasu acikin Ransa ya Dade yana mamakin wani abu Shi dai bazai ce soyayya suke yi aboye ba..?sai dai ya Fara Lura da wani abu ko Rakotan da Imran yake yi Sagir na ganinsu bai dai taba ma Imran din mgana bane sai shi kadai yayi ta mamaki yasan waye Imran ya Tabbata Baya abunda Ransa bai so ba Bamai sakashi yayi abu Dole duk abunda yayi ko ya aikata yayi Niyya ne kuma Ra"ayinsa ne Sai dai in ya Tuna Kaifin Imran sai yaga da kamar Wuya ace Soyayya suke shi da Inteesar sai dai yabar abun acikin Ranshi ya zura musu ido yana Bin Duka Takunsu itama ya Lura da kallon Data dinga bin Imram din dashi kallo ne na samun Salama da sukuni ya shiga Rudani shiyasa ya kasa Dora komai a inda ya dace ya bar Lokaci ya bayyana komai.

Tare da Munari suka shiga gidan tayi ma Mama sannu da zuwa,bata wani jima ba Inteesar ta Rakota Kofar gida,Sukayi sallama da cewa sai gobe Inteesar zata zo ta kwaso kayanta  Leda baka karama a hannunta cike da Goriba da gyada Tsaraban Mama ce ta bata ta kai gida,Lokacin da ta rako Munari Daga Sagir din Har Imran din sun tashi Daga wajen har Leke tayi bata Hangosu ba ajiyar zuciya ta Sauke Ranta duk ba Dadi yau data bar Gidan su munari batasan meke damunta ba ita kanta abunda ta sani Shine Imran yana cikin Ranta da Tunanin wanda komai take sai ya Fado mata arai ganinsa kuma Tamkar karin kuzari ne da Farimciki agareta Rashin ganinsa kuma sai taji gabadaya batajin Dadin jikinta da Zuciyarta tarasa Dalili sai dai ta Danganta haka damai kula dakai kaima ka Kula dashi ko bakomai Imran ya mata komai arayuwa Tunda ya ceci Rayuwarta.
Sai washegari da suka dawo makaranta taje ta kwaso yan kayanta ta Dade agidan saboda Tasleem na nan Har yanzu bata koma ba,Anty Safiya Taji sauki sosai Sai dai Rashin cin Abinci komai taci sai ta dawo dashi Sai dai zuwa in an kwana Biyu Laulayin yabi jikinta.
Tasleem da Munari suka rakata Har gida da kayanta,tayi ta waige waige agidan su Munari bata ga Imran ba Shi kuma ya ganta Saboda yana Haraban Gidan Lokacin da suka Fito bayaso su Fahimci ya tsayane kallon Inteesar yasa Lokacin datake waige waige ya Boye jikin Motar Yusuf har suka Fice daga gidan yana Kallonta,yana jin kamar yaje ya Riketa Kada tatafi karamin Tsaki yaja acikin Ransa ya rasa Meke damunsa..? Abubuwansa bama raguwa sukeyi ba sai ma Karuwa kan baya.
Haka suka cigaba da Karatunsu cikin maida Hankali Tasleem Sati Daya tayi ta Koma gida Tunda Anty Safiyan ta Warke sosai har tana aiki ma da kanta,Munari kuma basa zama sai Weekend tun safe in suka Tafi makaranta sai yammah basu da wani Ishashen Lokaci.

******

*Bayan sati daya..*!

Yau Alhamis tunda sai 6pm suka Dawo Daga makaranta tun safe sun Wahala daga Newsite suka tafi Class Oldsite,gabadayansu sun dawo jikinsu na Ciwo shiyasa yau kowa ta wuce gida.
Inteesar sai dai tayi wanka ta gasa Jikinta kana ta iya shan Ruwan Tea domin Karatu bai barsu sun Tsayama cin wani abu yau a makaranta ba.
Kwance take kan gado Tun bayan data idar da Sallar Isha"i take nan Zube kamar kayan wanki tagaji kafafuwanta Ciwo suke mata sosai inda zata samu mai mata Tausa da taji Dadi sosai ido kawai take Lumshewa ga barci Tana ji ga gajiya data Lullubeta ta Saukar mata da kasala.
Wayarta ta Dauko Data Tuna da wani abu Dazu suna makaranta ta Dauki Wayar Munari ta saci Lambar wayar Imran Bata sani ba Kwanakin nan bata ganinsa koda gidan taje ballatana ta Rage zuwa saboda Wuni suke Zungur acikin makaranta..
Haka kurum take son ta adana Lambarsa acikin Wayarta ko bazata Taba Kiransa ba Zuciyarta ta aminta da Hakan sai dai me..! Yadda ta kurama Lambar ido haka take ganin Gilmawar Fuskarsa ta cikin Wayarta,Kurama Fuskar wayar ido Tayi kowani Dakika jikinta na kara Saki Cikin yanayin kasala..? Meke Faruwa dani ne..?
Bata samo amsar tambayanta ba Hannunta ya kubce ta Danna ma Imran kira batare data ankara ba da Sauri ta Mike tana Shirin kashewa sai dai me...? Kiran Tuni ya shiga har ta fara Ringing gabanta ya yanke ya kanta ta Dafe kanta Dayake Saramata Jikinta ya Fara rawa bata da kwanan Amin taji ya Daga Kiran duk da kuwa Bai Taba Daga Bakuwar Lamba ba.
Yadda take kwance Tana Tunaninsa Haka shima yake kwance yana Tunaninta Sai dai shi yana Rage ma kansa wasu abubuwan in ya Busa Sigarinsa yanzu ma Tabance a Hannunsa yana Busawa cikin kwarewa yana Kwance ya Kishingida da Filo,Dagashi  sai bakin dogon Wandojikinsa bako Riga kwantancen Gashin Kirjinsa mai Santsi ya kwanta Sai kyalli yake..
Yayi mamakin ganin bakuwar Lamba Tana Kiransa shi ba wanda ya sani masu Kiransa Daga Sagir sai Yusuf acikin Contact din nashi ma Kwaya uku kadai garesa Daga ta Yusuf sai ta Sagir sai ta Munari ita da bai cika Kiranta ba sai Lambar Baba Manu kuma ya Dade da gogeta Tun sanda ya gama amfani da ita.
Da farko kamar bazai Daga ba sai Zuciyarsa taki bashi Daman haka haka Kurum yaji ta Rinjayesa ya Daga Kiran sai dai bai yi mgana ba yayi Shuru yana Sauraran Bugun zuciyar Inteesar da yadda ta Dafe Kirji Tana Ajiyar Zuciya.
Mamaki ya kamashi jin an ki mgana kuma yana jin Saukan Numfashi acikin kunnuwansa Ransa ne ya baci ya kashe wayar batare da yayi mgana ba Inteesar ta Rumgume wayarta Tana jin kamar Imran ta Rumgume saboda yadda Saukan Numfashinsa yasa Taji ta kasa Controling kanta.
Zama ta gyara ta sake Kiransa bai Dauka ba Sai da ta kara Kira kana ya Daga Cikin Dakakkiyar Muryansa yace"Ko waye ke kirana yafadamin kai Tsaye.. kada ya bari Raina ya baci na Bincikosa da kaina..!
Yafada Cikin Kaushinsa kamar yadda ya Saba maimakon tace wani abu sai taki ta Damke bakinta Tana Dariya Farinciki ya cikata dataji Muryansa ganin an ki mgana yasa ya Dago Wayarsa yana Bin Lambobin da kallo acikin Ranshi yana Tunanin wanene? Bai samu amsar ba yaja karamin Tsaki ya datse kiran Lokaci Daya Da kashe wayar nashi gabadaya Zai iya Zuwa Mtn office kan wannan lambar ya Tsani arainamai wayau,kuma abun
da ba"a tabamai ba Dole wani wanda yashanshi ne ko dai Sagir ne...?
Anya shine kuwa..? To in bashi bane Waye? Yusuf dai basa irin wannn Dashi Kodai Munari ce..?ai ita yana da Lambarta To kodai kodai yarinyar nan ne Mara jin mgana..? Zai iya Zama itace saboda yaga ta fara Rainasa Mirmishin Saman lebe yayi ransa ya tabbatar da itace ba wata ba zai bita a sannu zai kamata.
Ita kuwa yana kashewa ta saka Dariyan jin dadi acikin ranta tace ko bazai daga ba zata kirasa sai dai ta kara kira wayar tana kashe,ta kasa Samun shi,sai ta Hakura zuwa Gobe ta maida wayarta ta ijiye ta koma ta Kwanta Hannunta Rumgume akirjinta,Bata Dade da ijiye wayar ba sai kira ya shigo wayarta da Sauri ta dauko da Murnan ko Imran ne sai taga Khamis ne karamin tsaki taja Lokaci daya tana ijiye wayar Wani Takaichi yana kara kamata bata san Dalili ba ta tsani Khamis din,Sau daya ta taba Daga wayarsa bata Kara ba data Fahimci shine achart kuwa ya Tura mata sako ba adadi bata taba Budewa ba.
Messages kuwa ta waya ya turo ba adadi bata taba Budewa ba Bashi ke gabanta ba ita Mu"amala da ya"yan Mami Asma"u kwata kwata bazata iya ba Saboda basu da hali mai kyau har gwarama Umaima,ammh Sajidan nan ai tafi kowa Iskanci tama fi Uwarta Komai ta Damata ta Shanye,haka shekaranjiya Hafsah ta Kirata tana Fadamata Wulakancin data kirata ta mata saboda ta yi adding dinta a group din data Bude musu na mata Zallah Shine ta Fita ita kuma ta sake adding dinta shine ta fita ta Kira Hafsah a waya ta fada mgangun marasa Dadi kan kada ta kara adding dinta saboda ita bata da wannan Lokacin kuma ita ba sa"arta bace da zata Zauna tana wannan Shirmen kada ta kara mata haka bataso Daga haka ta kashe Wayarta ta kuma Sake Fita Daga group din Hafsah na gayama Inteesar taji Takaichin ba ita Sajida ta Kira ba da ta gane bata da wayau da sai ta Raina kanta ta rika ma Hafsah Fadan meyasa ma ta Sakata aciki..? Abu ne na Zumunci ba Dole aciki wanda ya dama ya shiga ayi dashi wanda bai ga Dama shi ya sani,ba wanda ya kara bi ta kanta su Anty Hauwa dasu Aneesa suna cikin Group suna Haduwa ayi ta Hiran Zumunci Inteesar ta kan Jefa mgana Daya biyu ba sosai ba.
Tana cikin wannan Tunanin ne taji karan Shigowar sako Bata ma yi kokarin Dubawa ba,saboda tasan ko waye sai da asuba ta duba Khamis ne Yana magiya ta Daga Kiransa Tsaki Taja ta Share duka Sakonninsa bata ma Tsaya karanta su ba.
Allah yasa basu da Class din safe shiyasa tasha barcinta ta Huta sosai sai 12pm suka shiga cikin makaranta ita da Munari,achan ma makaranta Haka Khamis yayi ta Kiranta taki Dauka Har yabama Munari tsausayi ta Roki Inteesar data Dauka tace mata Wlh bazata Daga ba sai ta Kyaleta..
Tundaga Ranar Inteesar ta samun Abun yi duk dare sai ta Kira Imran ko da bazai dauka ba sai dai yana Dagawa Dukkansu suyi shuru suna jin Numfashin juna,Har ya gaji ya katse Kiran sai ya kashe kiran Tayi da Dariya ita kuma batasan ya ganota ba Ya karbi Wayar Sagir ya saka lambar ya yana Danna kira sai ga Sunan Inteesar sai ga Lambarta ta bayyana Mirmishin Saman baki yayi shi ya sani itace ba wata ba..
Yarinyar nan ta rainashi wlh ammh zai yi mganinta
Sai da sukayi wajen Sati Daya tana kiransa Ranar tana Kira ya daga tayi Shuru taki mgana shi kuma cikin Dakakkiyar Muryansa yace"Yarinyar nan kin rainani ko..?! Ni sa"an wasanki ne da zaki rika kirana kina kin mgana..? Cartoom kika maidani ko karamin yaro irinki..?
Yafada mata Cikin Kaushinsa Koda yaushe Tsoro ya kamata ya akayi yasan itace sai ta fara Kifta ido ta rasa abun cewa Mirmishi yayi kafin yace"Kina mamakin ya akayi na gano ki ko..? Duk abunda Imran yaci alwashin sani sai ya sani..!
Kifta ido take yi kamar yana gabanta ta kuma kasa cewa komai Yasan daaman bazata iya mgana ba Ganin haka yasa yace"Oya jeki kwanta Tunda baki da abun fada..Ki daina Kirana kiyi Shuru bakya iya mgana Am not a Child kamar ki ok..!
Daga haka ya datse kiran Yana Mirmishi har cikin Ransa baisan meyass ransa bai baci da duk Abunda take yi mai ba sai ma Nishadi Dayake jinsa Ciki.
Ita kuwa yana Kashewa ta Fada kan gado tana Sauke Numfashi kamar wacce Tayi gudun Tsira,afili ta Furta"ya akayi ya gano ni..? Na bani..!
Take fada tana Dariyan Nishadi.
Tunda ga ranar bata kara Kiransa ba ya dauka ba sai dai ta Kira data shiga sai ta Katse kiran,ko kuma Daya Dauka sai ta kashe Imran baisan meyasa ba baya damuwa da abubuwan da Inteesar keyi da wani ne kemai Rainin wayau nan bazai Dauka ba sai gashi ita tana yimai bai taba Daukan wani mataki ba in ta Dameshi sai ya Kirata sai ta Dauka taki mgana Shi kuma sai yace"Kin raina ni ko..?
Oya ki je kiyi karatu ki kwanta bana son wannan Shirmen.!.daga haka zai yanke kiran ko ahakan aka Tsaya He make her Night sosai,shima ana shi barayin hakane.
Ta dubasa a Wsop taga bayayi saita koma Turamai sako ta Messages sai tana Zaune ta Turamai sakon"Ya Imu kaina na ciwo..? Ya imu ina jin yunwa..?
Ya imu kana ina..?kaci abinci..? Allah yasa yau baka sha sigari ba..?
Na dawo makaranta nagaji Ya Imu..? Yarinta kala kala take Zubamai mai shi kuma ya kasa Dakatar da ita in ta Turomai sakon zai karanta baya ce mata komai sai tace mai ta dawo makaranta ta gaji kanta na Ciwo sai yace mata tayi wanka tasha mgani ta kwanta,in ta Tambayeshi yasha Taba..?sai yace mata Eh yasha Koda Ranta zai baci sai ya gayamata Gaskiyansa Shiyasa yake kara Burgeta Dukkansu sun Shiga Tarkon son juna batare da sun sani ba.
Ranar asabar basu da makaranta Tunjiya data dawo daga makaranta Taji Cikinta na ciwo kadan kadan sai dai bata maida kai ba bata taba Tunanin Period pain dinta bane yadawo mata wanda abaya Tana Fama Dashi sosai in zatayi kamar ta Mutu to Tana karban mgunguna sai abun yayi mata Sauki sanda Tana Kaduna sai ta shafe wata Uku Tana Period  batayi mugun ciwon maran nan ba sai dai kadan kadan wanda bai Shahara ba Shiyasa ko Mama bata taba sani ba kuma ganin Tunda tazo bata Taba yi ba ko sau daya ba sai Mgungunanta wannan Hutun data koma gida ta maidasu.
Abun yana mata Kadan kadan ne yasa bata Dauka zai yi Tsanani ba Ranar ita tayi duka aikin gidan,Tace Mama ta Huta Jinin bai zo ba sai Zuwa Dare,Munari bata zo ba yau itama bataje ba tasan gajiya ne na makaranta sai dai zuwa gobe zasu Hadu..
Tana ganinsa tayi wanka ta gyara Jikinta tazo ta saka kayan Barci ta kwanta sai dai mai Tun tana ganin abun wasa wasa har ya Fice Tunaninta ta Fara rike ciki tana wayo Wayyo Allanta Tun tana ciki a Hankali har ya fito Fili Mama Dake falo taji Da Sauri ta shigo Ciki ganin Inteesar kan gado ahannunta kan cikinta Tana Birgima tana kuka Lokaci Daya sai ta Rude ta isa gareta ta Tarairayota Tana Sallami Cikin Kaduwa take fadin"Na shiga ni Amina Maryama meke damumki..? Meya sameki..?
Inteesar na kuka Hannunta kan cikinta Tace"Mama ci..Cikina..marana ciwo..!
Hankalin Mama ya tashi ta Rude Tana Fadin"Daman kina ciwon mara ne in zaki jini..!
Kai Inteesar ta Dagamata Bata samu bakin mgana ba..
Mama ta rasa yadda zatayi Fita falo tayi ta Kira Sagir a waya Tana Fadamai Halin da ake ciki shi kuma Lokacin suna Tare da Imran awaje sai da yagama wayar ne yake fadamai Inteesar ce ba Lafiya Tuni yaji Hankalinsa ya tashi kamar yabi bayan Sagir din sai kuma ya kasa,Ya fara Safa da marwa a waje yana Jiran Fitowarsa shi kuma Sagir yana Shiga ganin Halin da Inteesar ke ciki yasa yace Mama ta sakamata Hijabi bari ya Sami adaidaita su tafi asibiti ta amsa mai da Sauri ta Bude Akwatin Inteesar ta dauko mata Wani jan hijabinta ta kamata ta sakamata.
Shi kuma Sagir yadda yaga Imran ya Rude ne ya kara bashi mamaki bai ma Tsaya yaji wata mgana ba ya fara Tambayansa ya jikinta..?shi kuma ya Fadamai tana jin jiki Adaidaita zai sami su tafi asibiti da Mama kai Tsaye Imran yace basai Mama taje ba Bari su samo adaidaitan sai su kaita bai iya cewa komai ba Sagir sukaje bakin Titi suka sami mai Adaidaita zuwa Kofar gidansu Sagir din kana ya shiga cikin gidan ya

Please Login or Register in order to submit comment