Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ok..!
Baffa Kabiru yace"Is ok..Allah ya kaimu ya nuna mana Allah ya bada Zaman lafiya..!
A saman lebe Imran ya amsa kafin ya Katse wayar.
Shuru yayi yana wani Tunani kafin yace a fili"Su Baffa Kabiru an ji wuya..!
Yafada yana yar Dariya afili,Ko Dazu Sagir sai da yayi mai mgana da Safe kan mganar Lokacin Tarewar bai bashi amsa ba,Sagir din kuma Daman Munari ce tamai mgana ta Fadamai yadda Imu sukayi da Inteesar Sagir yace ai mganar banza ce zai mai mgana Dayayi mai sai bai wani bashi Amsa mai kyau ba.
Abba Kwana Daya sukayi a Dukku Ranar asabar kowa ya kamo Hanyar Gida,Baffa Kabiru Direbansa Daya kawosa ya Daukesa zuwa Abuja Bayan sun Tsaida lokacin da Imran din ya Fada nan da kwana Ashirin da Biyar Abba da Daddy Motar Haya suka Shiga suka koma Gidajensu,Su ka tafi suka bar Daada Cikin jin Dadi Tana saka musu albatka.
Zuwa Washegarin Ranar dasu Abba suka Dawo Mganar Lokacin Tarewar Inteesar da Imran ta yada Dangi da Abunda Baffa Kabiru yace Zai Dauki Nauyi,Kowa yaji sai yaji Dadi ana ta Fadin ai da haka yake yi da Ba asamu waniFada acikin Dangi ba.
Daddy ya Fadama Umma ita kuma ta Sanar da yan"uwanta su Munari abakin Anty Safiya sukaji Shima Abba ne ya Fadamai Ya yusuf Imran dai bai ce mai komai ba,Sagir kuma Mama ta Fadamai shima Imran bai Fadamai ba Shiyasa ya Sharesa.
Ranar Monday Abba ya Fara Shiga Office An samo mai Direba Musa wani Dan kasan Layinsu su Sagir ne Matashi ne mai mata Daya da yara Biyu,Zaratan Ya"yansa suka Rakasa Yusuf da Imran da Munari da Inteesar Harda Anty Safiya suka Raka Abba Har zuwa Babban Office dinsa na Department of Physhology.
Sukayi addu"a suka saka albarka kana Kowa ya wuce Wajen aikinsu Munari da Inteesar kuma Daman Gida suka zo suka wuce Department dinsu suka wuce suna da Test,Munari sai Rawan jiki take suna ta waya dasu Hafsah suna ta Tsara Event din da zasu gudanar tun jiya Munari ta Bude group a Manhajar WhatApps mai Suna *IMSAR*❤️💫 ta saka Hafsah,Da Nasara da Tasleem da Sagir.
Inteesar bata ce komai ba Gabadaya zullumi ya isheta Tana Tunanin Saura kwanaki kadan su Zama Miji da mata na Hakika Tsakaninta da Imran su Zauna agida Daya su kadai a mtsayin miji da mata.









*Shakira..*
3/26/22, 22:59 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿?22*

*Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488*


*After 1 week*

Bayan Sati Daya da Tsaida Lokacin Bikin Tarewar Inteesar da Imran ta kowani bangare Shirye shirye yana ta Gudana,Domin Baffa Kabiru yace Umma Zatayi Taron Bikinta a Kaduna ne,Yayinda Inteesar zata koma Wajenta Angawaye zasu Dauko Tawagan Amarya zuwa kano Gidan Abba inda Suma zasu shirya nasu Taron Bikin.
Imran Dayaji haka mamaki ya kamashi yace shi kuwa ba zai je kaduna ba,Wannan ai Wahala ce Abba yace sai dai kada yaje ammh Tabbas Inteesar zata koma gaban Iyayenta achan zasu yi Taron Bikinsu,Shuru kawai yayi ammh acikin Ransa yace ba Inda zai je kafar Daya kaita sai ya Daukota ya Dawo da ita.
Baffa Kabiru shi ya karbi Ragaman komai gabadaya Tsarin komai sshi ya Tsara shi da Daddy sun zo har Kano sun ga Sabon Office din Abba sun saka albarka suka kwana Daya suka koma a kuma zuwan ne Baffa Kabiru bai Duba Girma da Shekarunsa ba ya nemi Gafaran Imu saboda yasan yaKullace shi kuma shima yasan bai kyauta ba.
Imran bai isa yace bazai yafe ma Baffa Kabiru ba Tunda ya gano kuskuransa,Daman kuma Mami Asma"u duk ita ke kara sakashi aikata Wasu abubuwan,Yanzu kuma bata nan Yusuf ya kyankyasamai Rabuwar Baffa Kabirun da Mami Asma"u Dalilin Zuwan Abba Kaduna suka Tafi Tare da Daddy a Abuja har acikin Ransa Dadi yaji kuma acikin Ransa yana addu"an Allah yasa Kada su Daidaita sai Daga baya ya Fahimci itace kan Macijin Shi kuma Baffa Kabiru ne gangar jiki kuma kai Shike Sarrafa Dukan jiki.
Inteesar Amarya kuma ba Lokaci Saboda suna ta Test da sun gama kuma Zasu Fara Jarabawa da suka Lissafa zata tare Ranar Lahadi,Ranar Monday da Safe zasu Fara jarabawa basu da Lokaci Zamansu kadan ne shima na Karatu ne ga kuma Shirye Shirye.
Basu cika Haduwa da Imran ba Saboda Sanda zasu Tafi makaranta Shi ya Tsufa a wajen aiki in suka Dawo kuma wani Lokacin suna Gidan Mama,In kuma suna gidan Abba Shi kuma yana ciki yana aiki Bisa System dinsa.
Sai dai kamar yadda Munari ta bata Shawara bata yar ba Tana Turamai Sako Kullum da Safe na Gud Mrning da kuma na Gud Night Tana Kiransa bayan kwana Biyu Taji Lafiyarsa,Kuma hakan yana ma Imran Dadi sosai yayi mata Uzuri Domin yasan Karatu ne yayi Zafi ga Test kuma yasan sun kusa Fara Jarabawa abakin Sagir yaji Tunda shi Sagir din suna ma Jarabawar ne ta shiga aji Hudu Shiyasa basu cika Haduwa ba Dukkansu basa Zama.
Akallah dai yana jin Dadin ta basa Girmansa kuma ta Daraja Mtsayin Miji Dayake awajenta shima in yajita Shuru yana Kiranta yaji Lafiyarta Bai isa ya karyanta yana son Inteeaar ba Domin Duka Motsinsa Tana cikin Ransa ne Ko wajen aiki yaje itace makale acikin Ransa,Tayi kane kane Zaman da bazata iya Fita da karfi da yaji ba Domin ta shiga a Hankali ne Batare Daya sani ba.
Batare da Sanin Imran ba Sagir Ya Dauki Lambar Khalil a Wayarsa ya Kirasa ya Fadamai Halin da ake Ciki Saboda Imran yaki yarda ya basu Halin kai ga su Munari sun Dage sai sunyi Shagali a taron Bikin nan.
Khalil bai yi mamaki ba Domin Lokacin yaji labarin Auran Imran din ammh a bakin Abbansu Dr.Isa Ali Argungu shima Abba ya Fadamai ammh Shi da Imran bai Fadamai ba,kuma alokacin Auran Sajida ne so bai san an samu wani Sauyi ba kuma shima Sagir din bai Tsaya mai Bayani ba.
Khalil yace kada ya Damu,ya bada Lambarsa a sakasa cikin Group din sai su Tattauna,Daya fadamai abunda Imran yace bamai mai Bidi'a abikinsa khalil yace wannan mganar Banza ce sai anyi Bidia ko yana so ko baya so Ai ba Jiransa zasu yi ba su zasu Shirya komai.
Haka kuwa akayi Sagir ya baama Munari Lambarsa ta saka cikin IMSAR Together,Sun ji Dadin Tattaunawa da Khalil She is Very Friendly,Duk da shima yana da Miskilanci Sai dai bai kai Imran ba,Dashi da Sagir kadai ne abokan ango Su kuma suka Dauki Ragamar Tsara komai,Sum bama su Munari Damar su Rubuto Abunda Zasu Shirya na Event su kuma su Duba su ga abunda zai yuyu din
Munari da Tasleem da Hafsah Da Nasara suka Zauna suka Tsara abubuwan da zasu yi,Sunce zasu yi Bridal Shower sai kuma Lonching,Da suka Fada musu Khalil yace su kuma Zasu Shirya Dinner da Walima mata Ranar Lahadi in an kawo Amarya da kuma addu"an Bude Sabon Gida da wannan Shawaran suka Tsaya Kuma duk wannan Tsara Tsaran Imran bai san anayin su ba Daga Sagir din Har Khalil din ballatana Inteesar da sai sun Tattauna Take jin mganar a bakin su Munari.
Umma ta shirya ma wannan Bikin na Autarta ita da Daddy shima ya Sakarmata kudi sosai,Inna Maimunatu ita ta fito da ankon yinin Biki,Less ne Rantsattse mai kyau Daga Bangaran Umma Tunda ita Zatayi Tarinta Ranar Jumma"a ne asabar da Safe Zata taho da Inteesar Kano Akuma Ranar ne Anty Safiya Zata Gudanar da Taronta itama Wanda ya Yusuf da Abba suka bata goyon baya Itama ta Fidda ankon Material Mai kyau mai yarari na yinin Bikinta Shiri suke sosai Domin Yusuf yace suma Harda Taron Bikin da basu yi ba nasu Zasu Hada suyi Tare zasu gayyaci Mutane Dabam Dabam domin suzo su tayasu Murna.
Baffa Kabiru Inna Maimunatu ya bama Kwangila Hada kayan Lefen Inteesar Kudi kawai ya Tura mata Lokaci Daya sai dai ta Kira Intee ta Tambayeta Size din abubuwan amfaninnta,Ita da ya"yanta suke Hada kayan Zainab da karima Tsadaddun kaya na gani na Fada sai Wanda ya gani ba Ha"inci ba zamba cikin Aminci.
Mganar kayan Gida kuwa sun gama mgana da Kamfanin Marhaba Kudi kawai suke jira ya Tura musu zasu zo su Kawata gidan sai wanda ya gani Dagachan bangaran Umma kuma Tana Siyayyan yan abunda ba"a rasa ba,Mama taje ma tayi Sati a Wajenta suka gama Shawara bayan ta dawo ta Dawo da kayan wanka na Lalle da su margaya ta jikama Inteesar aka Zuba Ruwan Turaruka Kala kala Inteesar tana wanka Dashi Safe da Rana sannan ga mgungunan Infection na Gargajiya shima Maman ta Dake ma Inteesar din tana amfani Dashi.
Yan"uwa kowa yana ta zumudin Bikin banda Inna Bintalo da abun bai Dadata da kasa ba Dataji Labarin Abun Alherin Baffa Kabiru cewa Tayi bai da zuciya Tunda har za"ayi ma yarsa wannan Sakin Wulakanci kuma yazo yana Rawan jiki,Ba wanda yasan Tanayi bama abi ta kanta ba Itace ta Fara Kiran Mami Asma"u ta Labartamata komai,Jikinta yayi Sanyi ta kuma kara Tabbatar ma kanta Kabiru dai da gaske yake ya Rabu da ita Tunda gashi ya Shareta har yau bai nemeta ba kuma gashi ya Daidaita da yan"uwansa Har yaje yana Kashe kashen Dukiya saboda wanda ya Lalatama yarsa Rayuwa ya maidata Bazawara duk da Taji mganar Tarewar abakin Umaima bata Zata Lokaci kadan aka Saka ba Mami Asma"u da Inna Bintalo kadai take waya a Dangin Baffa Kabiru kowa ya kamasa kansa da ita da yawa ma basu san abunda ya Faru ba itama Inna Bintalo Ta Kira Mamin ne tana mata Tsegumin da Saninta Baffa Kabiru ke Kashe kudi haka Sai kuma taji Labari mara Dadi ita kuma ta Fadama Inna Maimunatu wacce ta Tabe baki afili ta Furta Ya kabiru yayi min Daidai Wlh..Allah ya kara mganinta kenan!
Ganin Bata samu Fuskar da Zata kawo Wata mgana ba yasa ta kama kanta Musamman ta Shirya taje Dukku Tana yima Daada mganar ita azatonta bata Sani ba Daada ta nuna mata Babba babba ne bata nuna mata ba Taji ba Sai ta Nuna mata abakinta ma take ji ballatana ta Fadamata yadda sukayi da ya"yanta nata taja bakinta ta Tsuke sanin Halin Bintalo akwai Daukan mgana sannan suna Dasawa da Mami Asma"u tana kuma da Tabbacin Mamin Asma"un ne ta gayamata yadda akayi ammh tasan Kabiru Ko Mustapha ko Malami ba wanda Zai kira Binta Domin ya Fadamata wata mgama shiyasa tayi mata abun nan da ake cewa ta yaro kyau take bata Karfo.


*******

Sajida Tana makaranta bata san Abunda ke Faruwa ba saboda ta yanke alaqa da duk wani abunda zai Karamata Mikin Dake cikin Ranta Da Umaima kadai sai Dad take mgana ta Sauke Duka Kafar sada zumuntar Dake Wayarta sun gama Test suna gabda Fara Jarabawa ammh bazasan Hakikanin Abunda ta Rubuta ba,Gadai Tanan nan kaawai Ta Rame Duk ta lalace kamar ba Sajida yar gayu bai ji da kanta da Takama da komai ba.
Ita kanta sani Tana da Cuta acikin Zuciyarta Har ta koma ga Allah Bazata Daina son Imran ba ba ita ta Dora ma kamta ba Allah ne ya Dora mata kuma bata isa tace Zata yaye ma kanta ba,Sai dai ta Dauki alhakin komai ta Dorama Mami itace Silar komai Sannan Daya Daga Cikin Ayyukan Mamin ne ita ta Girban mata Sakamako ne take gani ta Dauki hakan a Mtsayin kaddaranta Tunda Duk Zuwan da Dad zai yi wajenta ko ya Kirata a waya Nasihar shi da ita kenan yana Shiga Damuwa in ya ganta Ta Rame duk ta saki Ta Zama wata iri kamar ba Sajida ba
Bata da kuzari kamar mara Ishashen jini ajikinta ko Ruwa bata Farinciki Koda yaushe Cikin kunci in Ta gaji da Boye abun acikin Ranta tayi ta kuka Karatun ma bata Fahimtar sa kawai yinsa Take yi ba wai tasan ina Take ba ko ina Zata ba..!Jenefer kamta da suke Zaune Daki Daya tasan Sajida Ta Sauya haka ma abokan Karatunta da kawayenta Kowa Sajida What Wring..?me zata ce..!nayi aure ban Tare ba Mijin ba ya Sakeni..?kuma Duka Uwata Data Haifeni ta Ja Faruwar haka?bata da karfin Gwiwan bada wannan labarin amsarta Dayane bakomai ba abunda ke Damunta alhalin ita kanta ta sani Tana da Cuta acikin Zuciyarta Cutar da Sanadinta Mami Asma"u indai ta Fara Bin Ra"ayinta Tun Farko da ta Tabbata abunda ya Faru bazai Taba Faruwa ba.
Abakin Umaima take jin mganar Tarewar Inteesar din da Imran alokacin Sauran kwana Goma Sha Biyar,Ta zo Dubata tayo mata abinci da Miya Direba ya kawota Ranar asabar,ita kanta Umaima tayi ta ma Sajidan Korafin Ramarta Sai tace mata Stress din Karatu ne anan nema Umaima ke Nuna mata ankon da Munari ta Turo mata Guda Uku Less,na Dinner sai Wani Material na Bridal Shower sai Atamfa na Yinin Biki shi kuma za"a saka aje Lonching ta Nuna ma Dad yace ta zo ta nuna mata In tana Bukata sai a Daukan mata Sajida tace Bata Bukata bazata samu zuwa taron Bikin ba Saboda Lokacin sun Fara jarabawa Umaima bata Mtsa mata ba nan ta wuni Tare da ita akallah dai ta Debe mata kewa Umaima ta Tambayeta ko suna mgana da Khamis tace mata basa mgana Tun Dawowarta makaranta Cikin Damuwa Take sanar da ita basa samunsa ta waya Harta kuwa da Baffa Kabiru baya samun Khamis din Waya Sajida ta ce kila yanayin aikinsa ne kamar yadda Umaima ta Tambayeta Baffa Kabiru ma ya Kirata ya Tambayeta tace basa mgana bata Duba ammh Tana da Tabbacin shima yana chan yana Fama da Zuciyarsa kamar yadda itama take Fama anya Mami ZAta gama da Duniya Lafiya kuwa..?Tabar ganin Tana da Mtsayin Uwa a wajensu kamar yadda Take da Hakki a kansu suma suna da Hakki a kanta Sai dai bata Duba wannan ba Daga ita Har Khamis batayi musu adalci ba.
Umaima Tazo asabar Mami Asma"u ta shigo Cikin makarantar Ranar Lahadi,Daga Office take taje Duba Wasu Takardu shine ta Biyo ta makarantar su Sajidan Tunda ta Rufe Duk Hanyar da Zata sameta suyi mgana Mami Asma"u ta yanke Shawaran ta zo ta samu Sajidan suyi mgana Taji menene Nufinta..?ta sauya taa ne a Mtsayinta na uwa ko yaya..?
Har Hostel din ta shigo Dakin da su Sajidan suke Sajida na kwance Tana Fama da Tunanin Data Saba a koda yaushe Karatu take yi ammh bata Fahimta Sai da ijiye ta koma Tana Tunani Zuciyarta na mata suya Hawaye suna Zubomata in ta Tuna da kalaman Imran akanta Son maso wani Take yi Domin a gabanta a gaban Kowa da kowa ya Tabbatar mata da baya sonta kuma bazai Taba Sonta ba Har Abada.
Duk Sadda Ta Tuna da Wadandan kalaman sai ta kwana kuka Kirjinta yayi mata Nauyi yana Suya yanzu din ma kukan take ita kadai acikin Daki Jenefer ta tafi gida Weekend bata nan Sai ga Mami Asma"u ta shigo.
Dukkansu sunyi Shock da ganin junansu Sajida tana kallon Mami yadda Ta koma duk ta wani Fige kamar ba ita ba,Idanuwa sun Zurma Daga gani bata Samun Cikakken Barci Ballatana Kwanciyar Hankali ita kuma Mami Asma"u ta Firgita sosai na ganin yadda Sajida ta Rame tayi baki ta koma kamar Wacce take cikin Wani Cuta.
Sajida ta gabatar ma da Mami Ruwa da Lemo Tunda suna da Fridge acikin Dakin,Mami bata iya ko shan ruwa ba Ta Fara Tambayan Sajida me ke Damunta..? bata da lafiya ne..?meya sameta..?
Sajida kallonta kawai take yi Lalle ne ma Mami Tambayanta ma take yi me ke Damunta..?ita bata sani bane..?
Ai tafi kowa sanin Damuwarta Tunda itace Silar Shigarta Cikin Wannan Halin batacemata komai ba illah Shuru Da tayi mata tana Binta da ido.
Ta Zata Sakin da Dad yayi mata zai saka ta Sauki ta gane kuskuranta Sai dai a kalaman Mamin Gabadaya ba Nadama Illah kara Kaucema Hanya.
Tunda tazo take Zagin Daada Tana Dora alhakin komai akanta
Sajida Tagumi Ta Zabga Tana kallon Mamin Sadda take Fadin"Sajida kema kin Gujeni ko..?kema Daada ta Rabani Dake kamar yadda ta Rabani da Babanku..Ga Yayanku shima Tunda ya Tafi ban kara Samunsa a waya ba..Sajida nasan kina jin Haushina ko.?miye Laifina na..?miye Laifina Domin na so ya"yana na Nuna ma Duniya kune Duniyata..? Sajida wannan yakin saboda ke nake yinshi Kalleki yadda kika koma da Kuruciyarki da komai an Bata Miki Rayuwa an maidake Bazawara da karfi Da yaji wannan wani irin Abun kunya ne..?in na Tuna wannan abun sai naji kamar na Kashe kaina Saboda Takaichi kuma na mike Zan kwatar Miki Yancinki Dad din ku ya Sakeni Sajida kuma kun juyamin baya,Nasan kan wannan yaron kike Rama Sajida ki Kwantar da Hankali kefa Diyar Asma"u ce da Kabiru Gangariyan Miji yana nan zuwa Miki wanda yafi wannan yaron komai da komai ki cireko aranki Domin bakya gabansa Bikin Tarewarsu ma da yar Wajen Salahan ya kusa Babanku na chan yana Kashe Kudi Kinga fa Bintalo ta gayamin Shi zai yima Mara Mutumcin yaron nan Kaayan Lefe Ita kuma Inteesar din shi zai yi mata kayan Gida Gabadaya shi bama ta ya"yansa yake ba yana chan yana Kashe kudin Inda aka ci Zarafinsa aka Sauke Darajan yarsa Sajida ina Cikin Damuwa bana iya barci Babanku bai Nemeni ba bai Nemeni ba Yana Nufin ya Rabu dani gabadaya kenan..?Umhm..Shikenan ai Barrister Asma"u bazatayi kwantamai ba Zan samu Mijin Dayafisa komai da komai Tunda shi Daada ta shiga Tsakanina dashi ita da su Mustapaha..!
Take fada Tana Hawaye kallo Daya Zakayi mata kasan bata cikin Hayyacinta Surutai kadai take yi bata san me take fada ba Damuwar take cinta ne take Furta batare Data sani ba
Ance Uwa uwace ko da kuwa Mahaukaciya ce,Tuni Tsausayinta ya Sarke Sajida duk da kuwa Tana Fushi da ita Tun bayan Faruwar Lamarin ammh ganinta Cikin Wannan Halin Tana kuka ya karya mata Zuciya Rauninta ya bayyana ta Rungume Mamin Tana Fadin"Mami u are not Well..Bakya samun barci muje asibiti a Dubaki plz..!
Mami Asma"u na kuka Share Share kukan da Tuntuni take son tayi bata samu Kafadan da Zata Kwanta Tayi kukanta ba,Tabbas Tayi Rauni ta kuma gaza Duk kuwa da Taurin kanta wannan karon ta gaza ta yardan ma kanta Mijinta da ya"yanta ne Duniyarta Da kuma su take Takama yau da basu Tare da ita Rayuwarta ta Zama cikin Wani Hali Halin kakanikanin da bata Taba Tsammanin Zata shigesa ba batama Dauka abubuwan zasu Dakule mata haka ba.
Sajida kuka Mami Asma"u nayi Kafin Sajida ta Tsagaita da kukan ta ta Share Hawayenta Mamin na Bukatarta a wannan Lokacin,Fiye da yadda ita take Bukatarta.
Mikewa Tayi Tana Fadin"Mami Tashi muje asibiti a dubaki..Bakya barci Idanuwanki sun kumbara..!
Mami Asma"u batayi gaddama ba bata Barci,Ga ciwon kai Datake kwana Dashi batayi ma Sajidan Musu ba ta Jirata ta sako Mayafinta Ta Riko Hannunta bayan ta Rufe Dakin...
Specialist Hop suka je inda suke da Fayel Dr.Barau ya Duba Mami Asma"u ya Tabbatar mata da jininta ya Hau Saboda Damuwa da Rashin Barci ya Rubuta mganguna sosai da Shawarwari ga Mamin,Bayan an dubata ta Mtsa Sajidan ta Zauna itama a Dubata ta ki yarta tace ma Mamin itafa bakomai Strees ne na Karatu kawai ba Domin Mamin ta yarda ba ta kyaleta sai da Mamin ta koma ta Maida Sajida makaranta Kana ta Tuka kanta zuwa Gida.
Da hajiya Turai ta ganta ta Dawo Cikin wani yanayi shine take Tambayanta tace mata Wajen Sajida Taje Daganan ta Rakata asibiti taga Likita Jininta ya hau.
Hajiya Turai ya kyabe baki Tana Fadin"Uhmm..Asma"u kenan kaza mai ya"ya..Ai kulafacin Kabiru da ya"yansa Kadai aka barki ba Jininki ne bane zai Hau ba har Bugawar Zuciya Zaki iya samu..yarinya kina Wahala kanta bata sani ba..Ta Debeke ta Watsar ke kuma kin kwashi jiki kin Bita kamar itace Uwar..Wannan Bakin Halin na Fulanin Dukku sun kwasoshi Wajen Ubansu shi kuma ya kwaso wajen wannan Kafaffiyar Tsohuwar..!
Mamin dai na jinta bata Tanka mata ba ta Shige Ciki gabobinta sungaji so take ta kwanta Maltina ta Dauko ta sha ta Sha mgani ta koma ta kwanta Tana Sauke Numfashi sai kuka Allah Sarki Rayuwa yau ina Brr Kabiru..?ina Khamis..?ina Sajida..?ina Umaima..?
Basa Tare da ita Sai ita kadai Tayaya ko Zuciyar Karfe ce da Barrister Asma"u bazata Raunana ba Ya"yanta da Mijinta fa sune Duniyarta.

*******

Kwanci Tashi babu Wuya a Wajen Allah duk kuma abunda aka Sanyama Lokaci sai yazo,gashi yau Bikin Tarewar Inteesar da Imran Saura Kwana Shida a kuma Ranar ne Inteesar da Munari suka Sauka a Dukku Daganan zasu wuce Kaduna sai kuma an gama Taron Bikin.
Tuni Inna Maimunatu ta gama Hada kaya sai da aka kawoma Daada ta gani Ta saka Albarka Baffa Kabiru yayi kokari kuma ya Cika Uba wajen Imran akwatina Goma sha Biyu Tsala Tsala Cike da kayan Alfarma,Inna Bintalo da Inna Maimunatu ta Kira suka Hadu Gidan Daada Tunda Daganan Kaduna zasu kai kayan,Da Farko Baffa Kabiru yace afara kai su Kano Abba yace Dawainiya Zata yi yawa akai su kaduna Gidan Daddy.
Ganin irin Uban Dukiya sai da Taji Tsoro,Gulma na cinta Harda Vidoe tayi ma Mami Asma"u Ta Turamata Wacce Datagani Sai jiri ya Kwasheta ai ko Khamis Dansa Daya Haifa da Cikinsa sai haka Hawan Ruwa ne ya kusa kamata Data ga kayan.
Daga Inna Maimunatu sai Inna Bintalo sai Baba Asabe suka kai kayan nan Kaduna Dangin Umma suka karba su Mama da matan Bala da Salisu da su Anty Hauwa kowa yaga kaya sai barka ana ta ma Baffa kabiru Fatan gamawa da Duniya Lafiya Inteesar ma suna kano basu ga ko Kalar kayan ba sai dai ta Waya da su Zainab suka Dauka suka Dinga Turama Mutane Har Imran ya gani Yusuf ya Nunamai ya saka albarka Hae acikin Ransa ya yaba da Kokarin Baffa Kabiru a kansu.
Gida kuwa Tuni Anty Safiya da Mama da Matar Baba Manu Kaltume da Anty Saratu da Mommy da Anty Aneesa sukaje suka Tsabtace ko"ina washegari kamfanin Marhaba tazo ta jera kaya,2 Bedroom ne sai Falo guda Daya da Kitchen kowani Daki akwai Bandaki..
Falon Har Bedroom din Kalan Red and Black ne Zabin Amarya Inteesar,Bedroom din Imran kuma Kalan Baki da Fari ne kowa da Zabinsa Gida sai wanda ya gani.
Katin Biki kuwa kayattace Hadadde mai kyau na Zamani irin na ya"yan masu kudi Baffa Kabir ya Bugashi Copy 300,ya aiko ma da Abba 50,Inteesar da Imran 100,Yusuf 50,Daddy kuma y 50,Duk da Umma ma ta Buga nata Katin Anty Safiyama Ta Buga nata Katin Safiya Yusuf Hamisu Malami na gayyatan Kowa da kowa zuwa wajen Daurin auran kanin Mijinta Imran Abubakar Malami da amaryansa Maryam Mustapha Dukku(Inteesar)
gayyata Har Gidan Radio sai da Anty Saratu takai Safiya tayi gayyah Makota da yan"uwa da abokan arzuka Mama ma tayi nata gayyan Domin tace ita Uwar ango ce Tana Kaduna,Saboda komai Anty Safiya ita take sakawa a gaba ita da Anty Saratu.
Sagir ya sa an Buga Katin Waya wanda su Munari sukace suna so saboda Turama Kawayensu dake nesa yan Makarantar su,Sannan kati nan da Baffa Kabiru ya aiko Dashi Imran Ya Kirasa Inteesar ya bata bayan ya Tura mata 100k na gyaran Jiki Cikin kudin Albashinsa na Farko.
Sauran Katin kuma ya bama Sagir Tunda dai ba wanda zai bama wa Sagir kuma Daman sun Buga wani Shida Khalil na Events.
Imran bai sani ba bai da Labari sai dai yaga Kati Da programme of Event Daya so yayi ma Sagir hauka sai ya Hasada sa da Abba shi kuma yace kul Imran din ya Kyalesu suyi abunda suka Shirya Tunda shi bai da kara Dole yaja Bakinsa yayi Shuru.
Sagir yayi kokari sosai ya D'inka musu Shadda Kala Daya da Boyel Kala Daya shi da Imran da Khalil Duka kuma shi ya Dinka sannan su suka Shirya Dinner,Lonching da Bridal Shower a Kaduna za"ayi Dinner ne za"ayi a Kano Ranar asabar in aka kawo Amarya,Ranar Lahadi kuma agidan Inteesar Za"ayi Walima Tunda Ranar Jumma"a Umma Zatayi nata Taron Nan kano kuma Ranar asabar gabadaya Dangi kaduna zasu je Daganan ne zasu Dawo kano,Aneesa ce kadai take Kano suna ta Shirye Shirye ita da Anty Safiya,Anty Fareesatu kaduna zasu Sauka dasu Inna Maimunatu kuma Duk kowa yayi ankon Fitar Bikin na Kaduna dana Kano,Su Sadam ba"a barsu a baya suma duk zasu ce kaduna Daganan su kwaso Tawagan Amarya Zuwa Kano.
Imran bai sani ba Duk Sagir ya gama Satan Lambobin su Mr Tunde da su Mr

Please Login or Register in order to submit comment