Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana da Mata da Ya"ya uku sunan Matarsa Fareesatu suna zaune da kanwarsu Wacce batayi aure ba Hafsatu,Karima da Zainabu sun yi aure anan cikin garin Bauchi kuma suma sun samu zuwa..
Kowa yaji mgangansu kuma yasan kan gaskiya ne,Baffa Mustpaha yayi Shuru yana Tunani yayinda Baffa Kabir bai ma Damu da mganarsu ba Mgana suke kasa kasa Shi da Diyarsa Umaima Dake gefensa.
Ganin haka yasa Itama Inteesar ta Nufi Wajen Dadynta ganin Anty Hauwa tana Tare da Matan su Sa"id Umma kuma na kusa da Mami ita kuma bata ma kaunar kallon barayin Jikin Daddynta ta Raba tana gaida Baffa Kabir ya amsa mata hankalinsa nakan wayarsa kafin ta maida kanta kan Daddy tana Fadin"Daddy am so tired..Ina Daadan take ne..?
Kanta ya Shafa ya Mike yana Fadin"Tana barci tasha mgungunanta sai tatashi Inteen Daddy..Ko zaki je ki kwanta ne..? Bata samu Zarafin mgana suka Hada ido da Umaimai sai Tayi mata Mirmishi itama Tayi mata Daidai Lokacin da Baba asabe ta Fito Daga wani Daki Dauke da Manyan Dardume Tana ta Maraba kafin ta Shimfade su nan Tsakar Falon ta koma Kitchen tana Jido wasu manyan Flaks da Kayan tea da Sauran Kololi Inna Maimunatu ce ta Kalli Autarta Hafsatu tana Fadin"Sannu da aiko Baba Asabe..Ke Hafsa tashi ki Taya Baba asabe jigilan kayan nan ai da yawa gayyar..!
Tsam ta Mike bayan ta Sauke Yarinyar Hamida Abul Dake ke Jikinta Tun Dazu itama kamar sa"ar Inteesar ce,Umma na jin haka ta Kallo Inteesar Tana Fadin"ai bama ita kadai ba Maimuna Ga sauran yan"uwanta nan tashi..Intee kema ki kama mata..!
Inteesar batayi gaddama ba ta Mike tana Ciro jakarta ta baya ta Mikama Daddy Baba Asabe tace"Da kun kyalesu ai na gama komai..Nasan kun sha Hanya ku samu ku karya ku watsake kafin Daada ta tashi..ga Dakunan fa Hajiya Mami da Umman kaduna Tunda ko zuwan yau ne ku shiga ku samu Hutu..!
Umma ce kadai tace"Kada ki Damu Baba asabe..Gasu nan su Tayaki miye amfaninsu..!
Ganin haka yasa Umaimai ta Mike Tana Fadin"Nima zan tayaki Baba asabe..!
Mirmishi Tayi tana Fadin"To yar gidan Baba asabe..!
Daidai Lokacin da Khamis ya Dawo Falon bayansu kawai ya gani sun shiga Kitchen Mami ya kalla yana Fadin"Mami wadanchan fa ina zasu..?
Yafada yana Zama gefen Sajida Lokaci Daya yana kallonta Mami Tace cikin ko in kula"Zasu taya Baba Asabe Dauko Breakfast ne..!
Kamis ya kalli Sajida yana Fadin"And ita kima wannan Zaman me take yi..!?
Mami tayi kamar bata jisa ba Cikin Bada Umarni ya Zungureta da Kafada yana Fadin"Oya Comon Mike kema kije yayi aikin Dake mai shegen son jikin Tsiya..!
Sajida ta Fara Kokarin kuka Tana kara Lafewa Jikin Mami tana Fadin"Mami kingansa ko..?
Mami ta Dago ranta bace Tana Fadin"Khamis zan fa bata maka Rai..Meyasa kakeson Takuramata ne..?ko agida kaga ina sakata aiki ne ballatana ka mtsa mata sai tayi aiki anan..?







*Shakira..*
3/22/22, 23:06 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*Soyayyar da masoyana ke nuna min kan wannan labarin sai godiya kawai..Domin bani da kalmar da Zan Biyasu da Tarin Alkhairansu zuwa gareni sai dai kalmar Godiya ya Biyo baya Hakika ina ganin duka Sharhinku Sosai nake jin Dadi Nagode kwarai Allah ya bar Zumunci Wannan Shafin kacokam sadaukarwa ne ga Masoyan Oga Imu da Inteen Daddy sunce suna Godiya Khamis ma yace ace muku Hy Sajidan Mami tace nace muku ita fa tagani Tana so🤣*

*🅿?25*


Kowa afalon sai da ya juyo yana kallon Mami Asma"u cike da mamakin kalamanta ba ga yaran Dake Zaune ba har ga manya irin su Inna Maimunatu dasu Umma,ammh ba suyi wani mamaki ba sanin Halinta daga ita Har Mijinta da yarda suke gudanar da Tarbiyan ya"yansu.
Ko ayanzu din ma yana gefe yana ji ammh kanzil bai ce ba Sai Khamis din ne da kunyar kalaman Mamin suka Rufeshi ya kasa mgana illah kada kai da yayi ya tashi ya koma Kan kujeran Dake Fuskanta Hanyar Kitchen din Dake Falon Daada so yake ya kara Kallonta Domin tagama Tafiya da Duka Tunaninsa.
Mami Asma"u ta yatsina Fuska Hannunta kan Fuskar Sajida tana Shafawa tana fadin"Am sorry dota..Kada ki damu kwanta abunki bamai Takura miki indai ina Raye..?
Tafada Tana kara Kwantar da Jikinta a gefen kafadanta Cikin bayyana Soyayya da kauna da Sangarta Da suka nuna mata..
Kowa kauda kai yayi bai yi mgana ba Sajida kuwa ta kara nanikewa Jikin Uwarta Bata da Niyar tashi Inna Maimuna taga Abun ya wuce Misali Ta kalli Mami Asma"u Da hankalinta ke kan wayarta tace"Hajiya Mami ai gaskiya Khamis ya fada..Da kike fadin ko agida bamai sakata aiki ba kanshi yake ji ba sai ita yau Sajida mace ce tana gabanki gobe gidan auranta Zataje in yau kin tsaya mata Zaki gidan Mijin nata ne ki ZAuna mata ki bar naki Gidan...? Tsakani ga Allah fa Mu Tuna ya"yan nan Amana ne agaremu ko ba gaskiya ba..?in na Fadi ba Daidai ba ayi hakuri..!
Tafada kanta Tsaye Ran Mami Asma"u ya baci ta Dago Tana kallon Baffa Kabiru itama ita yake kallo Zatayi mgana ya Girgiza mata kai sai shine ya Kalli Inna Maimuna yana Fadin"Maimuna kina Nufin ban bama Ya"yana Tarbiya mai kyau ba kenan..?
Yafada Cikin Bacin rai da Sauri tace"A"a ko Daya ni ba kai nake nufi..!
"Ok bashi kike Nufi ba sai ni..Tunda nice Bare shi kuma Dan"uwanki ne ko..?
Mami Asma"u ta katseta Cikin Fushin mganarta Daman ga Takaichin Zuwa ba Shiri,Inna Maimunatu ta Kalleta Cikin mamaki ta Bude baki Zatayi mgana Sa"id Dake gefe yace"Mommy plz..!
Yamaata alamun hannu a saman bakinsa ganin haka yasa ta kada kai kawai tayi shuru,Inna Bintalo Dake gefe Tayi Yar dariya kafin tace"Nifa ina mamakin wasu mutanen Shikenan da Zarar ka bama yayanka Jin Dadin Rayuwa sai ace ka batasu to waya ki jin Dadi da Rayuwar Hutu..Ke Maimuna da kike Fadin Watarana Aure Zatayi in da kudi Yan aiki zasu bika Duk inda kake Sai dai ka sa ayi maka kana Bada Umarni..!
Jin Haka yasa Mami Asma"u ta samu bakin mgana Cikin gatse tace"gayamata dai Binta..Naga alamar kin fita saurin gane abubuwa..Shikenan in kana Bama ya"yanka Duka Tarbiyan daya kamata Kana basu jin Dadi duk sai ido ya koma kanka..? Domin wa muke aiki Koda yaushe..? Saboda ya"yanmu ne kuma Dadin abun nima ina aiki Ballatana ace da jikin wani na Dogara ko bana aiki mu yan gidan na gada ne ba na Haya ba..kuma Alhamdulillah ko acikin Dangi ya"yana sun fita Dabam dana kowa..!
Tafada lokaci Daya tana Sakin Siririn Tsaki Lokaci Daya ta maida kanta bisa Wayarta Umma Dake gefe ta kada kai kawai domin aHalin Mami Asma"u wanne ne bakonta..?.
Ba wanda ya kara cewa komai sai Falon yayi Shuru,Sai ya"yan Inna Bintalo ne keta mgana kasa kasa Baffa Mustapha kuwa maamakin yayan nashi ya kamashi ganin ko Sau Daya bai Tsawarta mata sai Fadin mgana Take son ranta.
Inna Maimunatu dai tunda Sa"id yayi mata mgana bata ma nuna tana Wajen ba jikanta ne a Hannunta yaron wajen Karima An yayeshi Daman Wajen sati biyu kenan Uban da uwar suka kawosa Bauchi yana Wajemta,Madara take bashi Ta Toshe kunnenta Bata ma nuna taji ba ballatana tace wani abu ba.
Falon ya dau shuru na wani Lokaci Sai su Sa"id ne ke mgana da Basheer sama sama sai Inna Bintalo da ya"yanta Sai ga dawowar Baba Asabe Falon Dauke da manyan Kololi,Bayanta Hafsat ne Dauke da
Filtes da Cokula,Sai Umaimah Dake Dauke da Mug din Kofuna a hannunta Daga baya kuma Inteesar ce Dauke da Kananun Vowl a hannunta Tana Tafe Cikin Sanyinta da Natsuwarta Gefen hannunta kuma Dauke da Katon Kwalin Tissue.
Tunda suka fito Idanuwansa ke kanta Ita ajikinta taji ana kallonta ta Duka Zata ijiye abunda ke hannunta Ta Dago suka Hada ido sai ya Daga mata Gira,Ganin haka yasa ran Inteesar ya baci tayi saurin kauda kai Tana Mikewa Lokaci Daya Tana gyara Zaman After drees din Dake jikinta Sam bata yarda da Khamis ba kallon Dayake mata ya Sabama irin kallon da addini ya amince ya shiga Tsakanin Namiji da mace shiyasa duk ta Tsargu kanta,ita ana ta Tunamin bai dace yana kallonta kamar zai Cinyeta Danya ba.
Wajen Daddy ta karisa ta Karbi Jakarta Hafsah ce ta kariso wajenta Tana Fadin"Kawo jakar muje Dakin da muka sauka..!
Kamar Inteesar zatayi mata Musu sai suka Hada ido da Umma ta gyada mata kai Shiyasa ta sakarmata Jakar Umaima ma na ganin haka ta kalli Mami Tana Fadin"Mami ina kayan mu..?nima Dakin su Inteesar zan sauka..!
Wani Harara ta Sakarmata kafin ta saki karamin Tsaki Tana Fadin"Kibari Ki sauka inda zan sauka keda Sajida..!
Baba Asabe Dake duke tana Bude kololin Da ta kawosu take fadin"Ai bamu da mtsalan Masauki kun sani..Daada tasan tana da Zuru"a kowani Daki ta sa an gyara mata shi..Ke Umaima ki sauka inda Hajiya Zata sauka ita da Sajida ke kuma Inteesar sai ki sauka Dakin da Hafsat ta sauka Umman kaduna ta sauka Dakin Daada,Wadanan surukan namu kuma sai su sauka Daki daya,Inna Bintalo da ya"yanta Daman suna Daki Dayane Inna Maimunatu ne jiya ta kwana Dakin Daada,Mazan kuma suna Wanchan Flat din na korido Daman chan su Sa"id suka sauka Jiya da suka iso..!
Ba wanda yayi gaddama da Hukuncin Baba Asabe saboda duk abunda tace kamar Daada ne ta Fadeshi.
Umarni da ta basu kan su sauko suyi Breakfast,rana tayi ba musu Iyayan suka Fara Saukowa Kafin Matansu sai ya"yan Daga baya Khamis duk yadda Zai yi sai da ya Zauna Facing din Inteesar saboda ya rika Morema Kallonta ita kuwa duk sai ta Takura ta Kasa Sakewa duk Dagowan da Zatayi sai sun Hada ido yana Binta da wani Mayattacen kallonsa Dataji kallon bai Burgeta.
Ganin haka yasa Tea kadai tasha sai Soyayyah Dankali tatashi bayan tace ma Hafsah wani Daki takai mata Jaka na nuna mata Dakin Dake kusa da Dakin Daada Tayi,Daddy ne ya Kalleta Tana Shirin wucewa"Intee Daddy badai har kin koshi ba..?
Kai ta gyadamai Tana Fadin"Eh Daddy nasha Complex kafin mu fito Daga Gida..!
Kai ya gyadamata bai ce komai ba Gabadaya da kallo aka Bita,Inna Bintalo Harda tabe baki,Umma na Lura da ita aranta tace kya yi dai ki gama Binta.
Sai da ta Fara Lekawa Dakin Daada taga kan gadon ba Kowa alamun Zubar ruwa a bandaki yasa Tayi Tunanin tatashi Tana Tiolet ne sai ta Fice ta isa Dakin da Hafsah ta nuna mata komai Neat akwai gado sai Katifa babba Dake kasa Dakin bakomai sai Cafet din Daya mamaye Dakin sai Tiolet Dake gefe wajen jakarta ta Nufa Da Hafsah ta ijiye mata nan kan gado,Zama Tayi agefen gadon Tana Tunanin yadda Zata iya kwana agidan Daada yau tagama Fahimta akwai abunda badai dai ba..Dazu fa sun fara karyawa Suka Hada ido da Sajida ita har ga Allah bata ma lura da ita akazo ba sai alokacin kallon kallon sukayi ma Juna kafin kowacce Ta dauke kanta Inteesar mamakin Sajida ya kamata ganin yadda Kowa ya Zauna a Matsayinsa ammh ita Tana Nanike da Mami Asma"u kamar wata yarinya ganin Haka yasa ta saki karamin Tsaki abun ba tsari kwata kwata tasan Tana da Shagwaba ammh nata na masu aji ne ba na irin nata ba.Shiyasa duk zaman wajen ya Gundureta da kuma Kallon da Kamis yake Binta dashi ita haka Kurum taji kallon bai mata kama da kallon Mutanen kwarai ba Daga ganin idanuwansa Ya saba kallon mata koda ga yadda yake wani Kashe mata ido.
Karamin tsaki taja acikin Ranta tace Dan"iska kawai.
Daganan Wayarta ta Ciro a jaka tadan Kishingida Munari ta Kira sukayi mgana ta Fada mata suna Dukku in sun Dawo gobe kila Jibi ta Tadawo in kuma basu dawo ba Dole sai Saturday ko sunday ne dawowarta.
Sun dade suna mgana kafin suyi sallama Daganan game ta farayi da wayarta sai barcin gajiya ya kwasheta ta Bingire ta fara barci batasan tayi barci da yawa ba sai da Taji Hayaniya akanta kana Taji Ana kiran sunanta Tana Bude ido Taga Anty Hauwa Tsaye akanta Mikewa tayi tana Mutseke ido,Tana kallom Anty Hauwa Kafin tayi mgana sai taga wasu na Sallah Ido ta Zaro tana Fadin"Anyi Sallar Azahar ne Anty Hauwa..?
Anty Hauwa na saka Hijabi jikinta tace"Eh mana gajiyan Hanya ne yasa baki san kinyi barci mai yawa haka ba..!
Mikewa tayi tana Mika saboda Bayanta ya Sage,Hafsah ce ta Fito Daga Tiolet tana kallon Inteesar tace"Kin tashi..?
Inteesar tace"Eh wlh..ashe nayi barci da yawa haka..!
Hafsah tace"Nima na shigo na ganki kina ta barcin nace gajiya..Nima jiya da muka iso haka nasha Barci na Har sai da nagaji..!
Mika Inteesar tayi kafin tace"Daada tatashi Daga Barcin..?
Ta daga mata kai Tana Fadin"Tun dazu..Tana Ma Falo ana ta Hira da ita ta Shige cikin ya"ya da Jikoki..!
Inteesar ta kalli Hafsah kafin tace"Wai Kiran menene Daada ke ma kowa ne..?
Hafsah tace"Wlh bansani ba..Ko muma da muka iso Tun jiya taki cewa komai tace sai gabadaya an gama Haduwa Zatayi mgana..!
Inteesar kai kawai ta jinjina ta Tura Kofar Tiolet ta shiga Domin ta Dauro alwala,Yadda taga Tiolet din Tsab a wanke yasa ta kwabe tayi wanka Saboda Jikinta ya saki Daganan ta Dauro alwala koda ta Fito su Anty Hauwa sun idar da Sallah da Aneesa Matar sa"id da Faree matar Sadam suna Hira sama sama,Hafsah kuma na Gefe kan Darduma.
Wajen jakarta ta Nufa ta Bude ta Dauko Wata Doguwar riga Ja da gyalenta,ta koma cikin Tiolet din ta saka kana ta Fito ta maida kayan Nata Data Cire cikin jaka.
Hijabinta kwara Daya da tazo dashi ta Dauko ta sanya ta Tada Salla nan gefen da Hafsah ta matsa mata.
Bayan ta idar da Sallar Tana Zaune shuru Hafsah ce ke mata mgana Sama Sama take bata amsa saboda Ita bata da Sakin jiki Tana Tambayanta kan Karatunta ne,tace mata Buk kano take ita kuma Hafsah tace Dutse take Karatu Federal Univesity Dutse Tana ZAune agidan ya Sadam.
Umma ce ta shigo Dauke da Abida sai kuka take ta mikama Anty Hauwa tana Fadin"Uwarta take son gani..!
Dariya tayi ta sunne kai kafin ta Karbeta sai ko yarinya tayi shuru ta Lafe jikin Uwarta Umma ta Rike baki Tana Fadin"Ikon Allah..Yaran Zamani ita anan ta san uwarta..!
Inteesar tace"Umma kema ai kene kiyi ta Wahala dasu bafa ya"yanki bane..Ni ce nan ya kamata ki rika Wahala dani ni da nake Autanki..!
Ta Karishe fada Tana Tura baki Umma ta Aikamata da Dakuwa tana Fadin"Damam nasan zaki yi mgana ai Kishiyoyinki ne dasu kike Kishi..Inteesar Allah ya Shiryaki..!
Dariya su Anty Hauwa suka saka Daidai Lokacin da Baba Asabe ta Shigo Tana Fadin"Nam kuma Wata Hira ake yi ana Dariya shine ba"a Kirani ba..?
Umma ta Waiga tana Fadin"Ni da jikar nan takice Baba Asabe..Kishi take da ya"yan Wajen Basheer!
Baba Asabe ta Kada baki tace"Aiko nice nayi Kishi..Tunda fa kikazo kike Dauke dasu ita kuwa ko kadan baki kulataba..Jika dai bai fi D"a ba atoh..!
Jin haka Yasa da Sauri Intee tace"Yauwa Baba Asabe kema kin gani ko..?
Tace"Kwarai na gani kuwa mai sunan Uwar Dakina..!
Umma tace"Kidai na kama mganar yarinyar nan..Shigen son jiki ne da ita Tana Gamsamemiyar Budurwa da ita Zan kama Dauka ina Sakama jikina..?indai jika bai fi ba D"a ba to ai D"a bazai fi jika ba..!
Dariya aka saka gabadaya ganin Inteesar ta Tura baki Baba Asabe tajuya tana Fadin"Gaskiya dai mune bamu yarda ba..Kufito Falo Daada Tayi kira fa..!
Jin haka yasa Dukkansu suka mike Suka Fice Inteesar ne Karshen Fita da kamar zata Cire Hijabin datayi sallah sai ta Tuna kallon kurillan da Khamis ke Binta dashi sai ta fasa ta Dauki Wayarta ta Zura Hannayenta Cikin Hannun Hijabin ta Fice zuwa Falon.
Daada na zaune saman kujera Tana Sanye da Hijabinta Fari,wanda yakai mata Har gwiwa Casbaha ne a Hannunta tana ja,Daada duk ta Rame ta kara Fari Tsufanta ya kara Bayyana Daga gani bata da Cikakkiyar Lafiya. Daga kasanta kuma Baffa Kabir ne da Daddy sai Chan gefe kuma Inna Bintalo da gayar ya"yanta Inna Maimuna na kusa da Umma,sai su Any Hauwa da matan su Sa"id,Su Ya Basheer na Daga gefe suma a kasan Cafet din suke zAune su hudu harda Khamis Sai Hamshakiya Mami Asma"u Tana Zaune ya"yanta Guda Biyu Umaima da Sajida sun sakata a Tsakiya ganin haka yasa Inteesar taNufi Kusa da Inna maimuna inda su Karima ke zaune gefe Hafsha ne nan ta Zauna Abiden na ganinta ya baro Wajen Umma ya Rarrafo wajenta Ganin haka yasa ta Dagosa Tana Fadin"Nifa ba Daukan kaba Shegen Karfi ne Dakai..!
Daada Dake zaune tana Nazarin kowa sai da Murmusa tace"Ba"a dai san mai sunan Maryama da Rangwanta ba..!
Dago kanta Inteesar tayi tana kallon Daada Cikkn Tura baki tace"Daada kada mu fara fadan nan dake..kinga dai baki da Lafiya ki samu dai mu Rabu Lafiya muzo muci gunban Mutuwarki..!
Daddy ne ya juyo yana Fadin"Intee..!
Ya kirata alamun tayi Shuru sai ta Dukar dakai Daada Tayi Mirmishi Tana Fadin"Kyaleta Mustapha..Daman ai wasan jika da kakan nake so nayi da Jikokina bana samun Daman..Dukkanku kuna wata uwa Duniya..Bana ganin ya"yanku sai dai ku..Kusan yadda nake jin Farincikin in na ganku kunzo Tare da ya"yanku..? Baku sani ba Shiyasa baku Damu da ku kawosu wajena ba sai dai wanda ya Girma ya kawo kansa kamar su Basheer sai Megidana Akali sai su Sa"idu sauran yaran kuwa bana ganin kowa..!
Ta karishe Fada Muryanta ta Fara kamar ta saka kuka Baffa Kabir ya Dago kansa yana Fadin"Daada don Allah ki daina saka wannan aranki..Mune fa Ahalinki Duk Duniya baki da kamarmu..Mganar yara kuma Daada kin sani ba domin karatu ba Da zaki rika ganinsu akoda yaushe..!
Daada tamai wani kallo kafin tace"Kayya Kabiru kullum mganar kenan Karatu..Naji karatu..Ba sa samun Hutu ne..?suna samu meyasa alokacin baza ku kawosu ba yanzu anan Wajen ba Domin kiran da nayi muku ba na Tabbata ku kadai zaku zo..Matayen ku ma ba Sosai suke zuwa ba sai wani abu ya taso..Na tabbata Wasu anan Rabonsu da Dukku sun manta wasu kuma kila yau suka fara ganin junansu a Mtsayinsu na yan"uwa ina amfaninshi...?kunga hakan ya Dace kai ne Babba Kabiru kafi kowa sanin yadda Mahaifinku marigayi Alkali yake da Riko kan Zumunci sai gashi yau bashi da rai Daga Gidansa ma Cikin ya"yansa Zumunci ya Lalace kuma yayi Rauni..!
Kowa afalon yayi Shuru yana Sauraran Daada mgangunta sun kashe ma kowa Jiki Inna Maimuna ta Kada kai tana Fadin"mganarki gaskiya ne Daada..Ni kaina Rashin Zumuncin nan namu na cimin Tuwo a kwarya Daada..Ace muna da yawa fa gamu da ya"ya ga jikoki zmunci duk mun Sakeshi kuma Laifin yana Wuyanmu ne muke da alhakin Nuna ma ya"yanmu gidajen yan"uwanmu Domin susan kowa..Koda muka yi Nisa muna da Rufin asiri daidai Gwargwardo Muna da abun hawa zamu iya Tashi muje duk inda muka ga Dama..Allah na Tuba cikin mu ba wanda yabar kasar nan Baban Sajida yana Abuja in anso arika Ziyartar juna Abuja ai kamar zuwa Dukku ne sai Ya Mustapha yana Kaduna ina Kaduna ina Abuja,Sai ya binta Dake gombe nan da Gombe ma Allah na Tuba Menene aciki Tsakani ga Allah..? Ammh bamu yi wwnnan kokarin ba..Daada ce kadai muke zuwa Dubata mu da ta zame ma Dole bamu yi Tunanin suma ya"yanmu Dolensu ce ko banza nan din Tushensu ne Sai kiga ammh suna Ziyatar sauran Dangin nasu na uba ko na uwa mu bamu damu da susan kowa ba gaskiya akwai gyara ban Cire kaina ba Har ni ina Da Laifi kuma ko Daada batayi wannan mganar ba ni zan yita ko Saboda Mganar Barin Ya Malami Dashi Da iyalansa Daga cikin mu wani Abun Takaichi ne da Abun mu Zauna musanta ina zamu bulloma Al"amarin..? Nasani kun sani Wlh ko Kaffara bazan yi ba Rashin Lafiyan Daada Tana da alaqa da rashin Sanin Takaimaiman Wani Hali ya malami ke Ciki da Iyalansa ne ko nayi Karya Daada..?
Takarishe Fada tana kallon Daada wacce Har hawayr ya fara wanke ma Fuska Cikin Muryan kuka Daada tace"Kin yi gaskiya Maimunatu..Wani Lokacin in kikayi mgana kamar yayanki Malami haka yake da Sanyin Hali da Hangen nesa..Hakika abunda ke Cikin zuciyata kenan kuma Dalilin kiran danayi muku shine kan gaba sai yadda Zamu taru mu gyara Kuskuran da muka Bullo dashi acikin Ahalin mu Tukafin mu Kara yawa abubuwa suzo suki gyaruwarmana yadda muke so..Ko kuma na Fadi na bar Duniya ku Watsar da Zumuncinku Gabadaya..!
Ta karishe Fada tana Sharan Hawaye da Gefen Hijabinta Daddy Cikin Sanyin Jiki ya Dafa Kafafuwan Daada Yana Fadin"Don girma Allah Daada ki Daina kuka..Mun gane kuskuranmu kuma mun miki alkwarin zamu gyara..Mganar Ya Malami kuma Na Rantse miki har ga Allah Dagani har Barrister bamu zauna ba muna ta Cigiya kuma da yardan Allah za"a dace ina ji ajikina Ya Malami ya kusa Dawowa garemu..!
Daada ta Kwace jikinta Cikin Bacin rai tace"karya kakeyi Mustapha..!
Gabadaya falon sai da aka juyo ana Kallon Daada yadda Tayi mgana Cikin Fushi Daddy ya Dukar dakai Yana Fadin"Allah ya huci zuciyar Daada..!
Daada bata tsaya Sauraransa ba ta Cigaba da Fadin"Koda yaushe kalaman ku kenan kaida Dan"uwanka In nayi mgana sai kuce kuna iya bakin Kokarin ku..?yau ne ya bar gida..? Yanzu fa Kimamin Shekaru uku har da wani abu da Bacewarsa shi da Iyalansa Ammh ba wani Labari sai Faman Fadamim kike yi kuna iya bakin kokarinku..Ina Kokarin yake..?ba wani Kokarin da kukeyi kowannenku yana chan yana Harkan gabansa Kawai Shi ya Dameshi baku Damu da Dan"uwnku Daya bar gida Cikin Lalura da Raunin Rashin Daya Fuskata ba..To bari kuji na Fada muki ba iya Kokari nake so kuyi ba Sama da Kokarinku zaku yi ku dawo min da Dan"uwanku gida in ba Haka ba Nima Zaku wayi gari kunyi Sanadiyar Rasani Kamar yadda kukayi Sanadiyar Barin Dan"uwanki Cikin Ahalinsa yabar komai nashi yayi Nesa Damu saboda yadda kukayi ta Tafiyar dashi..!
Ta karishe fada Tana kara Goge kwallarta da Haban Hijabinta Kowa afalon ya kasa Motsi saboda Shesshekan kukan Daada,Baffa Kabiru da tunda aka fara mgana bai ce komai ba sai alokacin ya gyara Zama yana kallon Daddy Lokaci Daya ya maida Hankalinsa wajen Daada yana Fadin"Haba Daada wannan wani irin mgana ce ya zaki dora mana Alhakin baarin Malami gida..? Wannan ai ba mgama bace ya bar gida ba saboda komai bane sai baya son a Fadamai gaskiya sannan ya Biyema Mganar ya"yansa Har ya iya Tafiya har yau bai nemi kowa ba..Daada ki Dora duka Laifin akan karansa shi da ya"yansa ba akanmu ba..!
Mami Asma"u dake gefe tace"Nima abunda Zan ce kenan Baban Sajida What all d Bleming akan ku kuma..? Wanda ya tafi batare dayayi Shawara da kowa ba..Shi ya kamata a Dora ma Duka Laifin ai Daada..!
Inna mainunatu ta Kalleta Tana Fadin"Sam bai kamata ba abunda kuma kikayi ba Daidai bane..Bai dace Manya na mgana ba kina saka baki ba..Koda kike Matar ya kabir wannan ba Hurumin ki bane mganace ta Tsakaninsu bai kamata ki saka baki ba gaskiya...ko kuwa nayi Laifi Jama"a..?
Tafada tana kallon Daddy kai ya gyada mata kafin yace"baki Laifin komai ba Maimunatu..!
Daada ta Dago daga Sharan kwallar Tana Fadin"Kabiru ka tsawartama Matarka..Kada ta kara sakamin baki in ina mgana da Ya"yana..!
Bai da yadda zai yi Dole ya juya wajen Mami Asma"u data gama cika Da mganganun Inna Maimuna sai Harare Harare take bai mata mgana ba da ido kadai ya Kalleta alamun kada ta kara Mgana sai ta koma tayi Laushi Lokaci Daya Tana kara Rumgume Sajida Dake jikinta Inteesar Dake rumgume da Abiden tayi Tsaki acikin Ranta kafin ta Juyar da kanta Karaf suka Hada ido da Khamis ya Kureta da ido Saurin Kauda kanta tayi acikin Ranta tana Ayyana wannan kodai Maye ne wlh kurwanta kur indai itane.
Daada ta kara Gyara Zama cikin Shakewar murya tacigaba da Fadin"Zakace min kada na Dora alhakin barin Malami gida akanku Kabiru..? Musamman ma kai Domin Mustapha In yana da Laifi Kadan ne na Biye maka da yayi bai fadamaka gaskiya ba. ni kuma har ga Allah bana sanin abubuwan Dake Faruwa wani Lokacin.'
Ran Baffa Kabiru ya baci cikin Fushi ya kalli Daada yana Fadin"Daada Kifa Daina dora alhakin komai akaina ki Dorashi kan Malami Da ya"yansa Musamman yaron nan nashi Kanin Yusuf Mara jin mgana ga shi yana ganin yana Daidai da kowa Tun kafin hakan ta Faru daman baya son Zama Cikin Danginsa Bazan ga Laifi in sun Tattara sun tafi wata uwa Duniya ba..!
Daada cikin tsawa tace"Yimin shuru anan wajen Kabiru kada ka kara cewa Tak..in ba haka ba sai na saba maka..!
Kowa

Please Login or Register in order to submit comment