Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba domin shi ba ya Rantse har ga Allah bamai sakashi zuwa Dukku yau.
Yusuf ya kalli Abba yana Fadin"Gama Imu din nan Abba..!
Kai Abba ya gyada kafin ya juya yana kallonsa yana Tahowa Hannunsa Daya Cikin aljihun wandonsa Dayan kuma karamar wayarsace a hannu yana Dannawa ba Abba kadai dayake Dansa ba kowa awajen sai da ya tsaya yana kallon Imran koda yanayin Tafiyarsa zaka Fahimci shi din Namiji ne ballatana Cikar Zatinsa da Kwarjinsa na dabam ne.
Inteesar dake tare da su Ya Basheer tana Rokonshi suna son zama amota Daya ita da Munari da Hafsah, bata san ta shagala da kallonsa ba sai da taji Basheer na fadamata to su shiga Motar Sadam shi zai tuka su Umma.
Kana ta iya dawowa cikin Hayyacinta Tana Sauke Nunfashi.
Imran kuwa gaban Abba ya karisa Ya gaishesu ina kwananku yace sau daya bai kara cewa komai ba ya Dauke kansa sama Daddy ne kadai ya amsa sai Abba ammh Baffa kabiru na gefe yana Waya..
Abba ya dafa kafadansa yana Fadin"me ka tsaya yi kaifa kadai muke jira..!?
Imran yace"Abba Sagir nake jira..!
Abba da Yusuf suka kallesa cikin  mamakinsa Kafin Abba yace"Sagir kuma..?
Kai ya gyada batare da yayi mgana ba suma basu ce komai ba sai Yusuf dayace"Ka kirasa zamu wuce ne..!
Bai yi musu ba ya koma Gefe yana Kiran Sagir ta waya.
Su kuma su yusuf suka fara tsara yadda Zaman Motan zai gudana.
Abba da Daddy da Baffa Kabiru zasu shiga Motarsa Direbansa yajasu wanda ya kwana nan wajen Iro megadi.
Sai Umma da Mami Asma"u zasu hau Motar Sa"id.
Yusuf kuma zai Dauki Imran da Sagir,Sadam kuma zai Dauki Fareesatu da Aneesa da Safiya da yaransu sai Basheer zai dauki Su Inteesar.
Kowa ya yarda da Tsarin banda Mami Asma"u data bata rai tafiso tayi tafiya Mota Daya da Mijinta sai dai bata samu Fuska ba Wajen Baffa Kabiru ko yaya naka yake ai naka ne tuni sun shige Mota shi da yan"uwansa Dole itama ta shiga Motar Sa"id gidan Baya Umma ta shiga gaba abunta.
Imran bai shiga Mota ba sai da Sagir yazo kana ya yarda ya shiga gidan gaba Sagir ya shiga baya.
Motan su Abba ce ta fara fita Daga gidan sai Motar su Umma sai ta Sadam sai ta Basheer sai ta Yusuf ta Karshe,Iro nata daga musu hannu da Fatan Allah ya kai lafiya.
Da suka dawo sallar asuba Yusuf ke fadamai zasu yi tafiya na kwana Biyu kafin su dawo ya kula da gida yace bakomai Cikin gida kuwa daman sun kulle kulle ko"ina kafin su tafi.
Sai da suka Dauki Hanya kana
Baffa Kabiru ya kalli Abba yana Fadin"wanchan da naganshi Tare da Imran waye..?
Abba yace"Sagir..?abokinsa ne..!
Baffa Kabiru yace"Tafiyar ta Shafesa ne..!?
Abba yace"Imran yace yazo yamai Rakiya..D'a na kowa ne ballatana Sagir ba bare bane na gida ne yaron wajen Yayar Salaha ne matar Mustapha Dalilinsune ma kuka san inda muke zaune..!
Baffa Kabiru bai kara mgana ba Daga gani zuwan Sagir din bai mai Dadi ba Daddy dai da Abba suka cigaba da Tattauna mganarsu.
Suna Hanya sun kusa shiga Gombe Inna Maimunatu ta Kira waya tace gasu fa a dukku koda ta iso ta iske Inna Bintalo da ya"yanta sun iso sun gama Gayama Daada Komai ga Daadan nan sai kuka take tana cewa Ta kosa taga Malami ko Hankalinta zai kwanta.
Daddy yace ai gasu nan sun kusa isowa da yardan Allah har aka bama Daadan ya kara Lallashinta bai dai bama Abba Wayar ba yafiso suga juna Ido na ganin ido.

Sun tsaya a Gombe sunyi Sallar azahar wajen karfe Biyu na rana kana suka Dauki Hanyar Dukku ba Dadewa suka iso Cikin Haraban gidansu na Dukku Abba na kallon Haraban gidan yana ganin komai kamar baya babu abunda ya Sauya sai ma sauye Sauye da aka samu,Idanuwansa suka ciko da kwallah na kewar Gida da Ahalinsa gabadaya da Daada dayake matukar jin kunyar Hada ido da ita.
Sai da kowa ya fito daga Mota kana Imu ya fito yana cin mgani Sagir sai bin Gidan da kallo yake yi yana Auna wasu abubuwa acikin ransa,Da Inteesar suka Hada ido suna Shirin Shiga Cikin gidan gira ta Dagamai Kafin ta dagamai hannu kau ya kauda kai kamar bai ganta ba,nan kuwa sun yi ma juna sako ta waya Inteesar sai mai Tabara take wai ta gaji da Zaman Mota shi kuma yace ta ce a sauketa in ta gama Hutawa sai ta hayo wata Motar ta samesu achan tunda bayan Shagwaba da Rigima ita din Raguwa ce sai Dariya take dayacemata haka.
Daddy ya Riko Hannun Abba gaba gaba zuwa Babban Falon Daada.
Wanda tunda sukaji isowarsu suka Firfito falo Daada da kafarta ta Fito Tarban Abba su Inteesar suka Fara shigowa sai su Aneesa da su Umma Mazan suna Baya ya"yan Inna Mainunatu su zainab natayi musu maraba su kuma suna ta Neman inda zasu ga Dan"uwansu,sai gashi Sun shigo shi da Daddy Baffa Kabiru na Binsu ta baya,Su Basheer na takemai baya Imu da Sagir ne abaya shi yana Tafiyama kamar bazai taka kasa ba.
Inna Maimunatu ce ta fara isa wajen Abba ta Rikeshi da Murna tana kwallah ita da Inna Bintalo,Daada na Bayansu Baba Asabe na Riketa Cikin Mika Hannu take fadin"Ina Malami..Taho nan naji Duminka na Tabbatar da yau Allah ya amshi addu"ata..!
Tafada cikin murya Tsufa Dakyar ya saki Hannunyensu inna Bintalo ya Nufi Daada cikin karayan zuciya,Hannayenta ya Riko yana Fadin"Daada...Daada..ki yafemi...!
Sai Hawaye Daada ta Rumgumesa tana Shafa bayansa Lokaci Daya Tana Fadin"Har Abada banta rike ka acikin Raina ba Malami..Addu"q da Fatan alheri ne tsakanina dakai naji dadi nagodema Allah dana ganka ka dawo Cikin Koshin lafiyarka Abubakar..!
Daada ta fada Cikon muryan kuka Duka suna Tsaye cikin Tsasayawa da Fuskar farinciki.
Ta dagosa Tana kallonsa kafin ta Shafa kanshi Tana Fadin"Allah na gode maka..Zan hada kan iyalaina kafin nabar gidan Duniya..Ina yaran nan Yusuf da Maimunatu..!
Abba ya juya yana Kiran Yusuf ya Taho da Sauri Munari ma haka Abba yakira Safiya itama ta kariso zuwa gaban Daada.
Daada na Hawaye ta Rike yusuf Tana Fadin"Yanzu wannan Yusufa ne..?
Kamkame hannunta yayi yana Fadin"Nine Daada..!
Idonsa ya ciko da Hawaye Ta dafa kansa Tana fadin"Masha Allah naji Dadin ganinku cikin Koshin lafiya..!
Tafada kafin ta maida Dubanta kan Munari dake Hawaye Daada ta Dafa kanta Tana fadin"Mai sunan Auta ta zama Budurwa itama Maimunatu kin ganeni..? Nice karki Daada..!
Tafada cikin karaya da tsufa jin haka yasa Munari ta Rumgumeta Tana Fadin"Eh na ganeki mana Daada..Daadam Dukku..Daadan Anni..!
Jin haka yasa kukan Daada ya Karu ta Rike Maimunatu tana fadin"Allah ya jikan Zuwaira da gafara..Allah ya jikansu ita da ya"yanta da suka rigamu gidan gaskiya..!
Gabadaya aka amsa da Ameem jikin kowa a sanyaye.
Daada ta dago da Munari daga jikinta Tana fadin"Ina yar tselen uwar nan Maryama da akace kun hadu Tuntuni baku gane juna ba..?
Munari na Dariya ganin Inteesar ta Hade rai tana fadin"Kai Daada bama kiji Dadi ba sanadina kin hadu da Baffa ba..!
Daada na Dariya tace"Naji dadi kwarai sai dai abu dayane bai min dadi ba..Yadda kika hadu da yan"uwanki baki sani ba wannan Dalilin ya kara Zaburar dani gyara wanu Gibi dna barsa a Bude insha Allahu..!
Baffa Kabiru ne yace kowa ya zauna Kada Daada ta gaji da Tsayuwa kowa ya samu waje ya zauna,Munari ta makale kusa da Daada Abba kasa ya zauna saman Cafet kusa da kafufuwan Daada shi da Yusuf.
Daada Mirmishi yaki barin Fuskarta sai Hamdala take acikin Ranta haka Yusuf da Munari bakinsu yaki Rufuwa Safiya sai waige waige takeyi Tana kallon kowa aranta Tna fadin ina Abbu yazo yaga Asali da kyakyawan Ahalin irin ahalin su Yusuf wadanda suka fisu komai na Rayuwa.
Daada ce ta ganta bata santa ba ta Kalli Abba Tana fadin"Malami wacece wannan..! Badai aure ka kara ba bamu sani ba..?
Mirmishi yayi Safiya sai taji kunya ta Sadda kanta  Abba yakalli Daada yana Fadin"Yaushe na Warken ne Daada da zan kara aure..? Matar Yusuf ce wattani Baya ya aureta..!
Daada ta washe baki Tana fadin"Masha Allah taho nan Yata bana Jikar dake ni..!
Safiya ta Rarrafa wajen Daada ta Shafa kanta tana tasaka albarka.
Daada ta fara Wurga wurga ido tana neman wanda take son gani Sai dai bata gansa ba yana ta bayanta Shi da Sagir suna Tsaye kamar wasu sojoji sagir na son zama Imran saboda Mugunta ya hanashi.
Cikin dan Rage fara"a Daada tace"Malami ina cikon Dayan..? Ina jikana Imrana..!
Abba ya dago shima yana Wurga Idanuwansa cikin Falon hakama kowa afalon ke wurgawa sai gashi an Tsintosa chan baya kamar wani bare Baba Asabe ne Dake gefe tace"Daada gashi nan a bayanki..!
Duk da bata wani sanshi ba ammh yanayinsa yasa tasanshine Imran din ballatana ai tana jin Labarinsa Wajen Daada.
Abba ya kalli Baba Asabe yana Fadin"Baba Asabe ya bayan rabuwa..?
Baba Asabe na Dariya tace"Sai alherin Malamin Daada Tunda gaka ka dawo Ciwon Daada ya Kare..!
Yana Mirmishi yace"Da yardan Allah.
!Daada kuwa Juyowa tayi Tana fadin"Ina imranan yake ne..?ko nima baya son ganin nawa ne kamar yadda yace baya son ganin Baffaninsa..!
Kowa sai ya fara mamakin ina Daada ta samu labarin abunda ya faru a Kano Mami Asma"u ce ta labartama Inna Bintalo yau da safe data Kirata ita kuma Tana zuwa ta Saukema Daada da ya"yanta.
Abba ya kalli Imran dayake Tsaye ko Motsi yana Fadin"Kai baka ji Daada na mgana bane..? taho mana..!
Ba yadda Imran ya iya Dole ya Jawo Hannun Sagir yana Tirjewa yana wani balle mai Harara Dole ya Biyosa suka Zagayo zuwa gaban Daada a Dofane Imran ya Durkusa kusa da Abba Sagir dai zama yayi domin Tsakani ga Allah ya gaji.
Kansa na kasa yake gaida Daada Mirmishi tayi kafin tace"Bazan amsa wannan gaisuwan ba Imrana..Matso kusa na jika kusa dani..!
Bayadda ya iya Abba ya mtsamai ya Karisa Kusa da Daada ya Durkusa kasan na kasa ta shafa kanshi Tana Fadin"Imrana..Har yau baka Sauya ba kana nan a yadda na sanka ko..!
Imran ya Dago yana kallon Daada Kafin yace"Asan ka da Hallayarka Shine Cikakken Mutum Tsohuwa Daada..!
Daada ta Murmusa Tana Fadin"ina nan ina ta ciwon rashin sanin inda kuke..Kai kuma Ahakan har kana cewa Babanka bazai zo inda nake ba ko Imrana..?
Kai Tsaye ya rike Hannunta Guda Daya yana fadin"Ban isa na Hana Abba zuwa ganinki ba Daada..Ban kai wannan mtsayin da zan raba Uwa da Danta ba ai nasan Radadin rashin Uwa Daada..Kuma ko ina ganin Laifin kowa bana ganin naki Daada Lokaci bayan Lokaci ina Tunaki har nayi miki addu"a acikin Raina..!
Daada taji Dadi ta Washe baki Tana fadin"Allah yayi muku albarka Naji Dadin ganinku haka..Kun kula da Mahaifinku da Kanwarku Allah ya saka albarka..!
Gabadaya aka amsa da Ameen Sagir ya gaisheta ta amsa cikin rashin Sanin Abba ne yayi mata bayani ta jinjina kai Tana fadin"Oh yaron wajen Amina kenan Yayar Salaha dake kano wanda Maryama ke wajenta ko..!
Abba yace mata Eh ai abokin Imran ne Daada tace"Masha Allah sannunku..Allah yayi muku albarka ina Maman naka take..? Kansa na kasa yace tana gaisheta tace tana amsawa..
Baffa Kabiru ya Duba agogon Azurfan Dake hannunsa yana Fadin"An kusa Kiran Sallar la"asar mu bari muyi salla sai muci abinci sai mu zauna ko ya kika gani Daada..?
Daada tace"bazamu zauna batare da kowa ya Hallara anan wajen ba..!
Kowa ya kalleta da Mamaki kai ta gyada Tana fadin"Binta ki kira su karima su iso suma kaima Kabiru ka Kira me sunan megidana Hamisu Da sauran yaranka Sajida da Umaima suma sai sun zo sannan zamu taru muyi wannan Zaman da yardan Allah.!
Bai da tacewa illah Shikenan Daada Mami Asma"u tamai kallon ya zakace haka kasan yaran na makaranta Shi kuma yayi mata kallon ba Mafita sai Bin Umarnin Daada.











*Janafty..*
3/22/22, 23:13 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�3*

*Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488*

Daganan aka tashi zuwa sallah,Mazan gabadaya masallacin kusa da gidan Daada sukayi sallah wanda Tsohon masallaci ne Tun marigayi Alkali Hamisu dukku nada rai.
Bayan sun dawo aka Hadu a falon zaman cin abincin da Baba Asabe ta girka da Taimakon su Zainab, suka kamallah komai,Daada da ya"yanta suna cikin Dakinta sun kule kansu,suna Hirar yaushe gamo Daada Tana Zaune su Abba sun Zagayeta Farinciki ya cikata yau Allah ya cika mata Burinta malami ya dawo cikin Ahalinsa,Tana kallonsu tana Sharan Kwallah ta gefen Hannunta Cikin bayyana Farincikinta,ko abinci ma nan ciki Baba Asabe ta kawo musu yara yaran ne ke Falo suna cin Abinci.
matasan mazan kuma Haraban gidan suka Fita Baba Asabe ta Kawo musu babbar Darduma suka Shimfida suka Zauna suna cin Abinci banda Imran Wanda yake gefe zaune kamar Dole jakarsa Har Lokacin Tana Sagale a bayansa yaki yarda ya ijiyeta.
Lokacin da aka kawo abincin da Yusuf yamai mgana sai yace bazai ci ba su Sadam mamakinsa ya ishesu ganin Tun suna Kano basu ga Imran yaci komai ba Ta yaya mutum zai Rayu ba abinci.
Haka Sadam yayi ma Yusuf wannan Tambayar Lokacin da suke cin Abincin Mirmishi kawai yayi yana kallon Imran dake chan gefe kan wani Dakalin gini da aka yi domin Zagaye Fulawowin haraban gidan kafin ya Daga ido yana kallon Sadam yace"Abinci bai damesa ba..Sai ya kwana ya Wuni haka bai damu ba..!
Sa"id na kai Lomar Shinkafa yace"Tab..Kuma lafiyarsa kalau..?
Wannan karon Sagir ne ya kada kai yana fadin"Shi yafi bama Ruwa Muhimmanci fiye da abinci..Sai kuwa Busa Hayaki..Abu na karshe Fruit da kila dasu daya ci ko bada yawa ba..!
Kowa kai ya jinjina suna kara mamakin Imran na wani Lokaci daya suna Juyawa suna kallonsa shi kuma Tunda yaga haka jikinsa ya basa Mganarsa akeyi,Daman Haushin Sagir yake ji yadda ya wani Sharesa ya shige cikin su Sadam suna Hira kamar sun Shekara tare,Sai faman aikamai da Harara yake yi shi kuwa baima bi ta kansa ba cin abincinsa kadai yake yi suna Hira Sama sama.
Imran da ya gaji da zaman hakan nan ba wani abun tabawa ya Dauko Karan Sigarinsa dake cikin Aljihun wandonsa ya kunnata ya shiga Zuka yana Fesar da Hayaki Ya Basheer ya kallesa yana Fadin"Ikon Allah shi kuma nashi Abincin kenan..?
Gabadayansu suka juya suna kallonsa shi baima san sunayi ba Idanuwansa suna Lumshe ne yana jin Dadin yanayin Dayake ciki.
Sadam ne yace"Gaskiya ya kamata Yusuf ayi wani abun da zai sa ya rage shan wannan Hayakin ko saboda Lafiyarsa..!
Yusuf yace"Ina ta rokon Allah ya yayemai shanta kamar yadda Allah ya Doramai shanta Lokaci Daya..!
Jin ya Fadi haka yasa suka amsa da Ameen Tunda ya ambaci Allah ai ya gama komai.
Gefe kowa ya koma ya Fiddo wayarsa Lokaci daya suna Taba Hira,Yusuf dashi da Sadam ne suke ta Hiransu Yana bashi Labarin group dinsu na WhaApps nan da nan yace ga Lambarsa ya sakasa shi kuma Basheer dashi da Sagir suke Hiransu Sa"id yana saka musu baki Lokaci bayan Lokaci.
Sun juma suna Hiransu kafin Hauwa ta kira Basheer a waya ya tashi zuwa Gefe suna mgana sai Hiran ta Koma kadan saboda Shima Sa"id ya maida Hankalinsa kan wayarsa ne ganin haka yasa Sagir ya mike ya isa Inda Imran ke Zaune ya gama Busa Hayakin ga Sauran Sigarin nan a kasa Daya gama ya Taketa,gefensa ya Zauna yana Fadin"Abokina ka dinga shiga Mutane don Allah..!
Kamar ma baisan yana Wajen ba kansa na kallon gefensa sai chan yace"Ai shiyasa naga kai ka shiga Cikin su ka manta dani..!
Sagir yace"Ah to tunda kai baka san shiga mutane ni sai naki shiga..!?
Imran ya waigo yana kallonsa yace"Eh saboda ni na gayyatoka..!
Yafada Lokaci Daya yana wani Dakuna Fuska Sagir yace"Eh ai ban ce bakai ka gayyatoni ba ammh su Ya yusuf ne fa ba wasu ba balle kace..!
Imran yace"Ya yusuf din shi kadai ne..? Wadanchan ba wasu bane..?Sagir ya saki baki kafin yace"Su waye wasun..? Chan fa duk yan"uwanka ne Imu..!
Baki ya tabe kafin yace"Eh ammh ai ban saba dasu ba..! Sagir yace"To ta ina zaka saba dasu baka Shiga cikin su ba..!
Imran yace"Ashe kuwa bazamu taba Sabawa ba indai sai na Shiga cikinsu..Kai ni ko Ya Yusuf a wasu Lukutan ban son zama dashi nafi son zama ni kadai..!
Sagir yace"Allah ko ya rabamu da zaman kadaici..Sai kayi ta zama ni dai sai na shiga cikin mutane..!
Yafada yana Shirin mikewa Imran ya dago kansa yana Fadin"Baka isa ba..Dawo ka zauna..!
Sagir ya kallesa kallon Mamaki kafin ya Girgiza kai yana Fadin"To Ubana Tasiu..Ko Uwata Amina..!
Yafada yana komawa ya zauna cikin dan bata Fuska yadda Sagir ya Fadi mganar ne ya bama Imran Dariya Har sai da ya washe fararan Hakoransa a waje wadanda bakasaifai ake cika ganinsu ba Sai ga dariya Lokaci Daya mai Sautin da Har sai da ta bayyana Su Sadam dake gefe suka Juyo suna kallon Abun mamaki
Sadam ya kalli Sa"id shima ya kallesa Kafin su kalli Yusuf Sadam yace"Kai ashe yana Dariya..Tun haduwarmu ko Mirmishinsa ban gani ba sai yanzu naga yana Dariya..!
Yusuf na Dariya yace"Yana Dariya mana..Ammh Tana da Wahala kaga yayi irin wannan Dariya bakomai ke Burge imu ba ballatana ya sakashi Dariya haka..Yafi yin Mirmishin Fatar Bakinsa in hakan ya zama kamar in muma mgana dashi haka..Irin wannan Dariya kuwa da Sagir kadai yake yinta ko dani in na Tsokaneshi..!
Gabadaya kai suka Jinjina Basheer ya kada baki yace"Allah mai iko..!
Sadam yace"Kuma mai Mutane kala kala..!
Dariya suka saka gabadayansu Sa"id yace"Tunda munsan Halinsa sai mu ci mganin zama dashi..Azauna Lafiya In ji Sadam daya Karishemai suna mganar suna kallonsa yadda yake Dukan Kafadar Sagir yana Dariya shi kuma ya saka Kafa ya Taka takalminsa yana Hararansa.
Lura da yayi suna kallonsa yasa Dif ya Dinke Dariyan tasa ya koma ya Hade rai kamar yaga Mala"ikan Daukan Rai su abun ma sai ya basu Dariya suka koma suka cigaba da abunda sukeyi Lokaci Daya suna Hira sama sama Shima din Hirarsu da abokai suke shida Sagir wanda Rabin Hirar Sagir ne Sauran mganar Imran din duk Gatse Gatse ne cikin yanayin mganarsa.
Sai da aka Kira mangariba suka tashi Daga wajen nan zuwa masallaci shima sai da su Abba suka Fito ne suka Tasasu zuwa masallacin basu koma Dawo gidan ba sai da sukayi Sallar Isha"i abunda yakara bama su Daddy mamaki Imran da Jakarsa yaje masallCi ya ijiye ta agefensa da zasu Fito ya Dauko kayansa mamakin hakan Yasa sai da Daddy ya maganta suna Hanyar Dawowa ya cema Abba"Shi Imran bai yarda da kowa bane..?
Abba yace"Saboda me kace haka..?
Daddy yace"Duba fa kagani Tunda muka iso bai sauke Jakar nan ba Duk inda zashi da ita yake zuwa..!
Abba yayi yar Dariya yana Fadin"Kyalesa in ya gaji zai samu waje ya ijiyeta..!
Yafada yana bayyana Dariyansa Shima Daddy dariyan yayi kafin su Wuce suna cigaba da mganarsu Baffa Kabiru kuwa yana baya yana ta gwada Kiran Khamis bai samesa ba sai ya Turamai sako.
Bayan sun dawo Mazan da iyayen nasu Falon Daada suka yada Zango Imran dai wani Daki ya samu ya Shiga ya ijiye Jakarsa yayi wanka ya saka Jallabiya ya kwanta yana Hutawa achan Falo kuma Baba Asabe Tuwon Shinkafa Tayi da Miyar Zogale yan matan suka Tayata dasu Anty Safiya aikuwa kowa yaji Dadin Tuwon nan sosai Daada Farinciki ya cikata ganin Ahalinta Zaune Waje Daya sai dai bata ga Imran ba yasa ta juya tana kallon Sagir Tunda ta gansa shi ya saki Jikinsa Cikin su Sadam tunda damab ba Bare bane Tace"Sangiru ina Abokin ka Imrana Shi kadai ne yayi saura bangani ba..?
Sagir ya kalli Daada yana Fadin"Daada yana cikin Daki ya kwanta..!
Daada tace"To baka fadamai ya Fito yaci Abinci ba..!
Yusuf ya karbe mganar da cewa"Daada ki kyalesa in yana Bukata da kansa zaki ga ya fito..!
Daada Tayi Shuru Tana Tunani Inteesar dake gefe itama ta Damu Tun dazu bata gansa ba Har sako Ta Turamai yana ina..? Yace mata gashi goye a bayanta ya saka mata bakar mgana Daganan ta kyalesa sanin bazai Biyemata ba.
Kokarin Mikewa Daada Take Tana Fadin"Ai baza"a kyalesa ba Yusufa ni bari naje da kaina na Fito dashi..!
Ba yusuf kadai ba Kowa da kallo ya Bita na mamaki,Da Sauri Inteesar ta Mike ta isa kusa da Daada ta Riketa ta Mike Tsaye dakyau Inna Maimunace tace"Yauwa jeki Daada..Kila in ya ganki ko kila ya Fito ya zauna cikin yan"uwansa..!
Sadam yayi karaf yace"Mom Wlh Tsausayi yake bani Duk da haka Allah yayi sa ammh akwai ciwo fa rashin Shiga Mutane..!
Kafin Inna Maimuna tace wani Abu Inna Bintalo ta tabe baki Tana Fadin"Sai kace Wani yaro Daada da sai kin je kin Lallaso yaci abinci..? Ai yunwa bata da sabo da yajita Zaki ga ya Fito..!
Kamar Mami Asma"u na Jira ta kada kai Tana fadin"Umh ai nama kasa mgana Binta..Gardin Namiji ba yaro ba Ana damuwa dashi sai wani Lallabashi akeyi kamar shi kadai ne jika kwara Daya Tal..!
Tafada Cikin jin HUshinta wanda sai da Abba ya Dago yana kallonta ya Kada kai baice komai ba Hakama Daddy yana Jin Takaichin Yadda Mami take Shiga mganar da ba nata ba,kuma Yaya Kabiru na zaune bazai Tsawarta mata ba.
Daada bata ce komai ba ta kalli Sagir Tana Fadin"Sangiru wani Daki Kaga ya Shiga..?
Mikewa yayi yana Nuna mata Wani koridi Lokaci Daya yana Fadin"Dakin farko Daada..Muje na rakaki..!
Da sauri Inteesar tace"A"ah Zauna abunka Ya Sagir zan rakata da kaina..!
Jin haka yasa ya koma ya Zauna ita kuma Inteesar ta rike hannun Daada suka Nufi Koridon Kowa ya Bita da kallo Mami Asma"u harda Hararan kasan ido aranta tana Fadin Tsohuwar nan akwai rigima ba wanda ya kara mgana kowa ya cigaba da cin Abinncinsa.
Yana kwance Ringingine yana kallon Rufin Dakin ya saka Duka Hannuwansa Biyu yayi Filo dasu idanuwansa sun kankance kamar mai jin Barci Su Inteesar suka Shigo Dakin bayan sun kwankwasa Lokaci Daya da Sallama.
Bawai bai ji bane yaji Mamaki ne ya kamashi na waye zai zo ya Damesa bai kawo ma su bane duk a Tunaninsa Sagir ne yasa ya Juya baya kawai bai ko Dago kansa ba.
Daada ta Murmusa tana Fadin"Nine baka san gani Imrana..!
Jin muryan Daada yasa ya Dago kanta yana kallonta karaf suka Hada ido da Inteesar dake kallonsa Ido Cikin ido.
Lamgwabe kanta tayi kamar zatayimai kuka Saurin dauke kansa yayi Lokaci Daya yana Mike Zaune yana Fadin"Daada..!
Kafin Daada Tace wani abu Inteesar Tayi Saurin cewa"Daada ta damu baka ci komai ba Shine tazo da kanta..!
Kura mata ido yayi yana kallonta Daga sama Har kasa sanye take da Doguwar riga mai Ruwan kasa Kirar Armani mai Roba ta dan manne mata ajiki sai ta saka Vail din Rigar ta yane kanta dashi Zuciyarsa taji tana Bugawa yasa yayi Saurin kauda kansa Kafin ya Zuro fararan kafafuwansa kasa ya Sauko Daga kan gadon ya isa ga Daada yana Fadin"Daada ai ba sai kin taso ba..bana jin cin komai shiyasa..!
Daada tace"a"a kana jin yunwa sai dai in bazaka ci ba..Ko Tuwon ne baka so sai Maryama gatanan ta dafa maka wani abu ammh ai zama da yunwa bai da wani amfani Imrana..!
Imran yasa mezai ce Inteesar ya kallah ta Dagamai gira Hararanta yayi kafin yace"Daada..!
Bata bari yace wani abu ba tace"In baka son zama cikin mu sai ta kawo maka nan Dakin ba shikenan Damuwar ba..!
Kansa ya shafa kafin yace"Zan ci muje Saboda ke Daada..!
Taji dadin haka ta shafa kanshi Tana Fadin"Allah yayi maka albarka..!
Ya amsa da Ameen yana kallon Inteesar dake danne Dariyarta Hade rai yayi yana Fadin"Ke..Dariya kikemin ko..? Yarinyar nan kin rainani saboda banta Sauya miki kamanni bane shiyasa..!
Daada Tayi gaba bata jisu ba Inteesar tayi Raurau da ido kafin tace"Am sorry badakai nake yi ba..!
Bai tsaya ce mata wani abu ba ya Nuna mata Hanya da Hannunsa Dole ta wuce sum sum shi kuma yabiyo bayanta Duk Takunta yana Kallonta kamar kuma da Zuciyarsa take Tafiya Har zuwa Falon Daada.
Suna Fitowa kowa ya Dago yana kallonsa Shifa ya Tsani kallo wani Lokaci Fuskar nan ya Hade ba Fara"a su Abba kadai yace ma sannunku sai Inna Maimunatu Inna Bintalo baima Lura da ita ba yasa bai gaisheta ba Yana Shirin karisawa Kusa da Daada ya Zauna yaji Tana Fadin"Ni kuma Kashi nayi maka agado  da ko sannun bansamu ba..!
Shifa bai ma zata dashi take ba yazauna kusa Daada yana dan Wurga Idanuwansa,Yaji Abba yace"Imran ka gaida Goggonka Binta gatanan..!
Yafada yana nunata Sai Lokacin ya Dago yama kalleta Wani Kallo ta sakarmai shi kuma yayo mata kallon Kyahuwa..,? Irin to me ya Hadasu da zata mai wannan kallon Dakyar ya iya ce mata Sannu goggo..!
Ta Bude baki zatayi mgana Daddy ya Dakatar

Please Login or Register in order to submit comment