Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

alto(Sisinah)*
*Chubado muhammad(Uwar dakina)*
*Yahanasu Soupnass(Qawalli1)*
*Kausar salis(My jika)*
*Rahma Ladingo(Dota)*

*🅿�2*

"Daga gidansu gangarawa yayi Chan kasan Layinsu bai tsaya ko"ina ba sai Kofar wani Shago mai Dan girma inda aka Rubuta DA KUDI AKE NEMAN KUDI TAILORING CENTER ababban Allon Dake kafe a kofar Shagon.

Yana Tsayawa ya zura hannu Cikin aljihun bakin Wando Dake Jikinsa ya zaro Tabarsa da makunninta ya kunnata ya Busa ya Fesar da Hayaki Cikin Shauki kafin ya Danna Hon din mashin din da karfi kamar Zai fasa ma Mutane Dodon kunni.

Shigowarsa Shagon kenan yana Duba yaransa da kuma Sallahu wasu Dinkuna da zai basu yana da Lacture karfe 10am cikin makaranta zai shiga yana Cikin yima Babban yaransa Auwal mgana sukaji wannan Gigigitaccen hon din Imran ya cika musu kunni Dafe kai yayi Lokaci Daya ya juyo yana kallon Kofar wajen inda suka Hada ido suna kallon Juna.
Karamin Tsaki yaja kafin ya juya yana kallon Auwal yace"Don Allah Auwal kuyi kokari ku gama Kafin Dare..Yau da Daddare Hajiya zata aiko Direbansu ya karba.."Auwal ya gyada kai Daidai lokacin da Imran ya kara Danna Hon din da karfi,kansa ya kara Dafewa Cikin Takaici ya Furta"Ya illahi.."Auwal Dake Dariya yace"Oga sai fa ka Fita..In ba Haka zai cigaba ne kasan Halin yan kayanka.."ya karishe Fada yana Dariya shi da Sauran yaran Shagon wani Daga chan yana kan keke yana Dinki yace"Imran kenan..Abokin Oga ko nace Amini ayi Fada aShirya hukuma sai da Lallashi..!

Yana Jinsu bai yi mgana ba sai dan Mirmishi da yayi ya Taka ya Fice Daga Shagon yana Fitowa ya kallesa yana Fadin"Kai wai meyasa kake hakane..? Ko yaushe kazo waje sai ka bada alamun kazo.."Imran ya kalli Abokinsa SAGIR,ya zuki Tabansa ya Fesar da Hayakin kafin cikin Wata murya mai cike da gadara yace"Da kudi ake neman kudi Abokina..Taken ka kenan.."Karamin Tsaki Sagir Yaja kafin yace"Naji..Ya akayi ne..?Ya jikin Abba..?
Imran ya Sauke Kafarsa Daya Dora Saman karfen Mashin kasa yana Fadin"Lafiya..Hau muje.."Sagir ya wani kallonsa ShekeSheke kafin yace"Na hau muje..? Ina kuma..? Idanuwansa ya sakarmai Kafin ya wana Mashin Din tayi Jinjin cikin Dakiyarsa yace"Malam ka Hau muje nace ko..'?

Yafada Cikin alamun ya Fara Fusata Shima Sagir din Cikin Zafinsa yace"Ni kuma nace na hau muje ina..? Wani Wawan Harara ya Jefeshi Dashi kafin yace"Zan je na kai kanka ne Domin nayi Cininkinsa.."Karamar Dariya Sagir yayi kafin yace"Ina karyanka Wlh..Kaina yafi karfinka.."Wani mirmishin Rainin wayau Imran ya saki kafin yace"Naji..Ka hau Muje kafin Raina ya baci.."Sagir yace"Muje ina wai..?Nifa daga ganni nan Lacture gareni makaranta zan shiga.."Imran yaji kamar ya Kifamai mari Cikin Muryansa mai Cike da Amo da Zati ya kalli Sagir yana Fadin"Zaka hau ko bazaka Hau ba..?
Yafada yana Tsareshi da Jajayen Idanuwansa Sanin Halinsa yasa Sagir din ya Taka ya Hau Bayan Mashin din Dariya Imran yayi kafin yace"Da kada ka hau kagani.."Sagir yace"me zaka iya..?Kai dai Nayi niyar Hawa kawai malam..!
Imran bai yi mgana ya Taka Mashin suka Fara Tafiya Gefe Daya kuma yana Tuki yana Busan Tabansa da Dayan Hannunsa Sagir na Baya yama kasa mgana,ganin yana ta Tsula gudu yana neman kadasu yasa ya Tanka."Kai malam in ka Shirya mutuwa ne ni ban Shirya ba..fakani gefe ka saukeni sai kaje ka Tari Mutuwar kai kadai ba.."

Dariya Imran ya saka kamar ta basawa kafin yace"Meyasa kake Tsoron Mutuwa abokina..? Ka manta Zaka Mutu Dolen ka..'Sagir yace"Nasan zan mutu..Ammh ina Burin kafin na Mutu na ijiye masu min addu"a kai daman bana ta kai Tunda ka Riga ka auri Taba gatanan ma ahannunka baka da mtsala.."Yana jinsa bai yi mai mgana ba ganin sun bar anguwansu yasa Sagir yace"Wai ina zaka kai ni ne..?
Har ya Cire rai da zai yi mgana sai yaji yace"Gidansu Safiya zaka Kaini..!
Sagir yace"Safiya..? Wata Safiyan kuma..? Imran yace"Safiya Buhari alhassan.."Sagir sai da ya Dafa Kafadan Imran saboda Razana Cikin Firgici yace"Budurwan ya yusuf fa kenan..? Yafada yana Bayyana Firgicinsa Dariya Imran yayi kafin yace"Sakeni Matsoraci kada kasa mu Fadi saboda Tsoron ka..!
Sagir yace"Don Allah mu daina wasa me zai kaika gidansu..?ko Ya yusuf ya aike ka..?
Imran ya saki karamin Tsaki yana Fadin"Wazai aika ?Ni Imran..Kana shan kwaya ne..Ni zan aiki kaina malam.."Sagir yace"Me zakaje yi gidansu..? Imran yace"Ka Nuna min Hanyar Gidan mallam ba Tambayata zaka Tsaya kana yi ba.."
Cikin Tsoro da Fargaba Sagir yace"Zoo road gidansu yake.."Batare da bata Lokaci ba Imran ya take mashin Har suka isa Zoo road ba wanda ya kara mgana Sagir ke nuna Hanyar gidan,Cikin Lokaci sai gasu Kofar Gidansu Safiya wanda ke Dauke da Katon Get mai Ruwan Madara Daga ganin Zubin gidan zaka Fahumci suna Rufin asiri eh mana suna Dashi Mahaifinta Alhaji Alhassan Buhari Lacture ne A BUK Dake nan Jahar kanon Dabo.
Akofar gidan Imran ya Faka Mashin din nashi Sukasauka Gabadayansu Lokaci Daya ya Juya yana Bin Gidan da kallo yana Wani Shafa Sajensa ganin haka yasa Sagir yace"Imran Me zaka yi agidan su yarinyar nan..?

Imran bai mai mgana ba Illah Tabansa daya Kara Fitowa da ita ya Kunna mata Wuta sai da ya Busa Hayakin ya Fesar kana ya Sauke kallonsa kan Sagir yana Fadin"Bafa wani abu ya kawoni ba..Kawai Kashedi zan mai da kuma Umarnin Yayi gaggawan bama Yayana auran yarsa in ba Haka ba.."Sagir Daya Zaro ido yace"in ba Haka ba mene Imu..? Don Allah ka bari kada ka Shiga gidan Mutane ka Tada wata Rigima so kake amaimaita abunda ya Faru a gidansu Asma"u..? Ka Karya ma kawunta Hannun Daga karshe ba Yaya yusuf ka bari da Shari"ar ba ina amfanin wannan Rayuwar da kaKe saka Kanka acikine..?
Yana jinsa bai taka ba idanuwansa ma na Lumshe yana Zukan Taba yana Fesar da Hayaki,Sai chan yaBude Jajayen Idanuwansa yana kallon Sagir Lokaci Daya ya gyara Tsayuwa yana Fadin"Bazan karyamai Hannu ba..? GIDANMU fa ya zaga..? Ya kira Babana Mahaukaci..? Wlh Tallahi kowaye ya nunayatsa gareni ya zagi gidanmu ya kuma kira Babana Mahaukaci sai na Karyashi in ban Nakasaahi ba Sagir.."

Ya karishe Fada Cikin Daga Murya Idanuwansa sun Sauya Launi Ganin haka yasa Sagir ya Sausauta Cikin Lallashi yace"Naji Bai kyauta ba..Ammh me ya jawo haka kuma yau..? Imran yace"Raba yayana yayi da yarsa..Can u juz imaging ya yusuf na kuka fa saboda yarsa kuma sai naje gida na kwamta ina Murna..? Ina so ya gane ya Tabani Wlh zan mai gargadi in yaji Ruwansa in bai jiba Jikinsa zai gayamai ne ba Ruwana fa.."
Ya karishe Fada yana Zakuda kafadansa Lokaci Daya yana Fesar da Hayakin Taban Daya Zuka Harta Hanci ya Dumfari get din gidan Sagir ya Bisa yana mai magiya Cikin Takaicinsa ya waigo yana Fadin"Malam don Allah ka kara gaba..Haba nifa Gidan kawai na Bukata kuma ka Kawoni zaka iya karawa gaba Bai Dameni ba"Yafada kamar zai Dakeshi Sagir ya kallesa yana Fadin"Ammh ai har kofar Shagona kaje ka Dauko ni ko.?
Imran ya juya yana Fadin"Kuma Da ka gama Biyamin Bukata nace U are Free to go ko..? Sagir yayi Kasake yana kallonsa Har ya Taka Jikin Get din yayi Knooking Sai gashi megadi ya Leko Domin ganin Waye Hayakin Taban da Imran ya Fesamai ya Faramai Maraba Baya yaja yana Fadin"Bawan Allah meye hakan..?
Yafada ya kare ma Imran kallo wanda ya tsaya kyam Hannunsa Daya cikin aljihunsa Dayan kuma ya Rike da Tabarsa yana Busa sai da Lumshe ido ya Bude kana ya Sakarma Megadin wani kallo kafin yace"Alhassan Buhari yana Ciki..?
Megadi ya zaro Ido Jin sunan Megidansa kai tsaye ya Tsorata ganin yanayin Imran din Shiyasa yayi saurin cewa"Eh..Eh..yana ciki bai riga ya Fita ba.."
Imran yace"Gud..Shiga kace mai yana da Bako a waje.."da sauri megadin ya juya zai tafi Imran yace"Ji mana..! Cikin kaushin Murya Jiki na rawa ya juyo yana Fadin"Na"am yallabai.."Domim a Tsorace yake gani yayi kamar in yayiwani gardama Imran zai Fito da wuka Domin kallonsa yake kamar wani Dan Daba Duk da yayi Mishi kama da Yusuf Saurayin Daya Daga cikin yaran Gidan Jikinsa bai saki ba.

Sai da Imran ya Busa Hayakin Tabansa kana yace'In yabukaci sanin waye kace mai IMRAN ABUBUKAR MALAMI ne...Kanin Yusuf Abubukar malami.."Ya karishe Fada yana wani Shafa Gemunsa,lokaci Daya yana Lailaya Taban Hannunsa,Da gudu megadi ya juya yana Fadin"To yallabai.."Sagir Dake gefe Tagumi kawai yayi aransa yana ta addu"an Allah ya kauda Fitina yaso ya kira Ya yusuf ya gayamai ko zai yi wani abu sai ya Tuna Lambarsa Tana Karamar wayarsa ne kuma ya manta da ita agida saboda Sauri.

Megadi Har Falon gidan ya Shiga Daidai Lokacin Alhaji Alhassan ya Fito Zai Fita Matarsa Hajiya Mero ta rakosa Megadi ya Zube yana Fadin"Alhaji kana da Bako."Cikin  mamaki yace"Bako..? Daga ina kenan..? Megadi ya Kaskastan dakai yana Fadin"Yace ace maka Imran Abubukar malami ne kanin yusuf.."Alhaji ya kalli Hajiya Mero Cikin Fushi yace"Kin ji ko..? Wannan kanin Shashan yaron chan ne da SAfiya ke ta kuka Tun jiya kan nace Bata bashi.."Hajiya Mero ta karkace kai Tana Fadin"Takadirin yaron nan dai kaninsa da muka samu Labari Alhaji..? Yana Saba Babbar Rigarsa yace"Shi mana..Bari naje Shima nayi mai Fata Fata kamar yadda nayi ma Yayansa Jiya..Ni ba karamin Mutum bane da inaji ina gani zan Hada jini da Dangin Mahaukata da yan iska.."Jakarsa ta Briefcase ta mikamai tana mai Allah ya kiyaye ya Fice yana Fada Megadi Daman Tuni ya Fice kada kai Tayi Ta koma Ciki Tana Ayyana abubuwa da Dama kan Al"amarin.

Yana Fitowa Haraban Gidan ya mikama Direbansa Jakar yana Fadin"Ina yake..?Megadi yace"Yana Daga Wajen get Alhaji.."Karamin tsaki Yaja yana Fadin"To ya shigo mana..Ko ni zan Biyo sa ne..? Yafada da Dan karfi Har Imran da Sagir sai da sukaji Domin ya Taho gabda Get din ne balle ma Alhaji Alhassan irin Mutanen ne marasa mgana Cikin Natsuwa ga Sakin Murya.
Megadi ya leko waje yana kallon Imran yace"Yace ka Shigo yallabai..'Mirmishi Imran ya saki kafin ya Saki Taban Hannunsa ta Fadi kasa ya saka kafa ya Murjeta Megadi ya wangalemai karamar Kofar ya Shige Sagir na ganin Haka ya bi bayansa Suna Shiga Haraban Gidan suka Hada ido da Alhaji Alhassan wanda ke Tsaye yana gyara Babban Rigan Jikinsa Lokaci Daya yana kare ma Imran kallo Daga sama Har Kasa
Shi kuwa gidan yake Kare ma kallo afili ya Furta.."Nifa ba ganin kyale kyalen gidanka ya kawoni ba..Mgana nazo muyi kan Abunda ya Shafemu Alhaji.."

Ya Karishe Fada yana Kafeshi da Jajayen Idanuwansa Lokaci Daya ya Zura Hannu cikin aljihu ya Dauko Tabarsa ya Kunnata hayaki ya Fara tashi Alhaji Alhassan Dake tsaye Bai yi mamaki ba Daman ya samu Labarai Dadama kan Imran din a Fusace ya Tako zuwa gabansa yana Fadin"Kai wannan wani irin Shashancin ne..? Kashigo Gidana kana Min Shaye Shaye..? Yafada Yana wani Kunfar Baki Domim ba Laifi Alhaji Alhassan akwai Fada.

Ko Tak Imran bai ce mai ba sai ma Tabarsa Daya kara Zuka ya Daidaici Fuskar Alhaji Alhassan ya Sakarmai Hayakin da sai da yayi Baya Cikin Firgici yana kallon Imran wanda yayi Mirmishi ya Dagamai Gira yana Fadin"Ya akayi..? Ka tabbatar yanzu.? Ba Wani Dogon Surutu ya kawoni ba..Miye Dalilinka na Hana yayana Auran yarka..? Ya fada Cikin Tsuramasa Idanuwansa Kamar yana Bashi Umarnin yayi mgana Alhaji Alhassan mamaki ya kara kamashi Sagir kuwa yana Gefe bai yi mgana ba sai addu"a yake aransa kada Alhaji Alhassan ya Fadi wata mgana kan Gidansu ko Mahaifinsu yanzu ayi mara Dadi kamar yadda Kwanaki ya Faru da abokinsa KB a Shagonsa Suna Hira sai Imran yazo wajensa Bama dashi ake Hiran ba Cikin Labarin ne Kb ya sako mganar wani Mahaukaci su dai basu yi Aune ba sai Hakorin Kb da Jininsa suka gani a kasa Imran ya Naushemai Baki da sunan wai Dashi yake da Abbansa yake kwatance Fadan da yaso har Hukuma ta Shiga Ciki Shi yayi ta bama Kb Hakurin har ya Hakura ammh da Imran yaji cewa yayi Duk wanda ya bama Kb Hakuri ya Hakura Uwarsa taci Uwatai.
Shiyasa yake ta Tsoron kada Hakan ta kara Faruwa yasan Imran kamar Yunwar Cikinsa zai iya komai ga Duk wanda ya aibata GiDANSU.

Alhaji Alhassan da Ransa ya gama Baci ya Fara Fada da Bambami yana Fadin"An hanashi din..? Nace an hanashi din Zaka aura masa ita ne..?ko yarka ce.?Ina ce Ni na Haifeta kuma ba wani iko da ita ba.? Ko Uban wani ya Haifamin ita ?.."Ya Karishe Fada har kumfar Miyau na Biyo bakinsa.
Imran Dake zukan Tabansa ya Dakata yana kallon Alhaji Alhassan kafin yace"Ammh dai Uban da ka zaga ba namu Uban ka zaga ba ko..? Yadda yayi mganar ne yasa Shakkarsa Ta Shiga Alhaji Alhasan ya juya kai Baiyi mgana ba Mirmishi ya saki kafin yace"Nagane..Ba Dogon Turanci nace kamin ba Malamin Kimiya da Fasaha Dalilinka kadai zaka Fadamin.."Alhaji Alhassan yace"In Kaji Dalilin sai kuma yaya..? Nace sai kuma Yaya..?
Imran ya Zakuda Kafafa yana Fadin"Sai yaya kuwa..? Iyaka in Dalilin bai min ba na saka Ka Dole ka Kira yayana ka bashi Go Ahead kan ya Turo magabatansa.."Zaro ido Alhaji Alhassan yayi kafin yace"Ni..? In hada Zuru"u da irin Mahaukata Irin Tantiranci..uwa uba ga Rashin asali da Nasaba Gidanku ba Tarbiya ba kwaba Domin Tunda kuka zo garin nan Daga ku sai Mahaifinku albarkan zaman mace ma agidan baku samu ba kuna Zaune kara Zube sai ni Saboda bani da Tunani na Dauki yata na bakku.? Ai sai kimata da Mutumcina ya...!

KAIIII...!Ihun da Imran ya Kwatsa kenan Lokaci Daya ya Daga Hannunsa sai Sauke ma Alhaji Alhassan wani Naushi wanda inda ya samesa sai ya Raunana Domin Tabbas Hakoransa na Gaba sai sun watse sai Dai Sagir ya Ceceshi Daga Hakan Ya Tare Imran Da Rikoshi da Karfinsa yana Fadin"Imran..Imu..Ka bari Don Allah..Kada ka Tabashi Don Allah.."Yake fada yana Rikesa da kyau ganin yadda yake wani Fizga Idanuwansa sun kala sun ji Jajir Tuni jijiyoyin kansa suka Daga haka yake sakin Hucin bakinciki da Hannu yake Nuna Alhaji Alhassan Dayayi gefe Tun Hargagin Imran yana maida Numfashi Cikin Muryansa mai Cike da Amo yake Fadin"Who is He da zai Fadi wata banzar mgana kan Gidanmu.? Shidin banza waye shi..? Wlh da barni da yanzu Bakinsa ya Cikada Hakoransa da Jini Kai har kana da Bakin mgana Kayi gaggawan bama Yayana Dama in ba Haka sai na Fallasaka agaban iyalanka gasunan suji su kuma Fahimci wani irin Uba ne Allah ya basu.."Ya karishe Fada yana Nuna su Safiya da sukaji Hayaniya Daga Haraban gidan suka Fito kuka kawai take Tunda Taga Imran duk bata taba ganunsa tasan sunan abakin yusuf kuma daga mganarsa ta Fahimci ko waye shi.. kanwarta Tasleem Tana Ta lallashinta Hajiya Mero kuwa Mahaifiyarsu kallon Imran take Tana kuma Kallon Alhaji Alhassan da Tunda yaji mganar Imran gabansa ya Fadi kardai yasan Sirrinsa na Neman matan Dayake yi..? In ko hakane ya Shiga uku Gwara ya basu auran Safiya daya Fallasa wannan Sirrin wanda Bayyanarsa zai yi Sanadiyar Kimarsa da Darajansa da Mutumcinsa da kuma aikinsa Dayake takama Dashi

Yin wannan Tunanin yasa Jikinsa na rawa ya matsa kusa dasu Imran yana Fadin"Kaga ba sai an kai ga Haka ba..ku Turo mgabatanku Shikenan Tunda kun nace itama ta nace sai shi.."Yafada yanawani fiki Fiki da ido na marasa gaskiya Sagir Sai da Dariya ta kusa kamashi Imran kuwa Hannunsa ya Fizge Daga na Sagir ya Tura Hannu a aljihunsa ya Dauki kwalin Tabansa Har ya karar da ita Saura Daya ya Daukota ya Jefar da kwalin ya Jawo makunni ya kunnata ya Zuka ya Fesar da Hayaki kana ya kalli Alhaji Alhassan da Jajayen manyan Idanuwansa yace"Ka kira Yayana ka sanar dashi yanzu..NAN..! Ya karishe Fada Cikin Tsawa da Sauri Alhaji Alhassan yace"Yanzu kuwa..Insha Allahu.."Yafada yana rawan Baki Imran bai Saki Fuska ba ya Taka Hargaban Safiya bai Taba ganinta ba sai sau Daya da Yusuf  ya taba nuna masa hotonta duk da bai wani kalleta ba sosai ba,da Jajayen idanuwansa ya kare mata kallo Daga sama Har kasa Tasleem kuwa bayanta ta Labe Tana Toshe Hanci Daya lura da ita tsawa ya Daka mata yana Fadin"Ke....'jiki na rawa ta Dago kanta tana kalleshi cikin Dakiya yace"Ni sa"an ki ne da kike ganina kina Tushe Hanci..? Maza Bude Hancinki kafin ki Tunzurani na Targaki yanzu agaban Iyayenki..!"Da Sauri Tasleem ta saki Hancinta Tana rawan Jiki ta kamkame Bayan Safiya Da kanta ke Duke Tana kuka Hajiya Mero kuwa gum Tayi da bakinta batayi mgana ba Duk da itama warin Tabae ta isheta sai dai ba Halin mgana ganin yanayin Imran din ya Firgitata ta tabbata ko ita ba Shakkarta zai yi ba balle ma Dataga Shi kanshi Alhaji ya Saduda

Safiya ya kallah kafin yace"Bhabi..Stop craying...Kin auri Yayana kin gama..See u sai mun Hadu a GIDANMU.."ya karishe Fada yana wani Mirmishi kafin ya Zuki Tabarsa ya Fesa musu Hayaki kana Lokaci Daya ya Juya yana wani taku Daya Bayan Daya yana wani Rangaji ya Fice Daga gidan Sagir ya maramai Baya Megadi ya Bisu da Allah ya Kiyaye sai da Alhaji Alhassan yaji tashin Mashin din Imran kana ya iya Motsi Juyawa yayi yana kallonsu Kafin ya Fara Bambamin kunya.

"Tsayuwar mu kuke yi kukama..? Ai sai ku shiga Cikin gida...Ke Safiya ki kira shi yaron kicemai ya Turo manyansa Tunda irin Gidan da kika Zaba kiyi Rayuwa kenan ke kika sani.."Daga haka ya Saba Zaman babbar Rigarsa ya nufi Motarsa Direbansa ya Budemai Bayan Bakar prado dinsa ya Shige yana jin Zufa na ketomai Kafin Direba ya Shiga Bangaran Direba yayi Rivers Ya yi Hon megadi ya wangale get suka Fice sai alokacin Safiya ta Juya Cikin gida da Gudu Tana Dariya da kuka Tasleem ta Mara mata Baya kana Hajiya Mero da Jikinta ya gama yin sanyi da al"amarin Data gani.

Imran kuwa Har ya maida Sagir bakin Shagonsa bai ce mai kanzil ba sai da ya ijiyesa kana Sagir ya kallesa yace"Mama Tana ta Cigiyarka.."Imran yayi Mirmishi kafin yace"Kace mata Zan shigo Gobe.."Daga haka ya Bama Mashin Dinsa wuta ya wuce ya bar Sagir da binsa da kallo har ya Bacema ganinsa bai koma Shagon ba ya Nufi Gidansu Dake Jikin Shagon nashi Domin ya Dauko wayarsa da Littafansa ya Shiga makaranta.

Yana Shigowa Falon ya ci karo da Yusuf sai washe baki yake Cikin Murna ya Sarke Hannayensa yana Fadin"Bro..Wai me kayi ne..?Yanzu Safiya ta kirani tace Abbanta yaje na Turo Manya..Am so Suprise Mutumin Daya gama Rantsuwan jiyanan bazai taba bani Auran yarsa ba sai gashi yau da kanshi yace na Turo manyana.."
Mirmishin Jin Dadi Imran ya saki ganin Dariya a Fuskarsa Dan"uwansa Hannunsa ya Zare kafin ya Dafa Kafadarsa yana Fadin"Imran kaifi Daya ne..Yana Cika Duk Abunda yace..So sai ka Fara Shirye Shirye ka kusa Zama ango akalla bayan Wasu Shekaru zamu samu wata mace zata karu acikin GIDANMU..!

Yana gama Fadin haka ya Sauke Hannunshi ya Wuce zuwa Dakinsa ya Shige ya Turo Kofa,Yusuf ya Bishi da kallon Kauna da Tsausayin Dan"uwansa kafin ya Girgiza kai yana Fadin"Kana Matukar Burgeni IMRAN ABUBAKAR MALAMI.."daga haka ya juya zuwa Dakin Abba Cikin Farinciki Domin ya sanar dashi Allah yayi zai yi aure wannan karan.

******

*KADUNA..*
_Area:Anguwan Sarki.._

Acikin anguwan Sarki acikin wani Tangamemen gida na Zamani Da misalin karfe 8pm na Dare wata yar Matashiyar Budurwa nagani wacce bata wuce Shekara 20 ba aduniya Doguwa ce sosai bata da Kiba Kirjinta kadai ne yake Tudu daga kasanta kuma ba wani abun kirki Sai Doguwar Fuskarta Kalar Fatarta baka ce ammh Ta samu Hutu da Jin Dadi,bata da Dogon Hanci Sai dai kana ganinta zaka Fahimci Ta Hada Jinsi da Fulani ko ta Uba ko ta Uwa tun bare ma yanayin Tsawonta da Idanuwanta Masu Dauke da gashin ido da kuma Gashinta Data Tufkeshi Har ya sauko Zuwa ga wuyanta.
Sanye Take da wata karamar Riga kamar Shimi Doguwa kanta ba Dankwali Sai Faman loda kaya take cikin wata Trolley bayan wadanda Tagama Durawa akwatuna Hudu gasunan a jere asaman Dan madaidaicin gadonta.

Har aka Bude Kofar aka Shigo Bata sani ba sai da taji Daga Bayanta ance"Auta wannan Uban kayan Duk na zuwa Kanon ne..?
Muryan wani Namiji ya Fadi hakan da Sauri ta waigo Tana kallonsa Shima kamar ita yake sai dai abun mamaki Shi Fari ne kuma ya Fita Dogon Hanci da Jikin Maza saboda yana da Dam Kiba ammh da tsawon da yanayin komai iri Dayane,Shekarunsa kuwa baza su wuce 30 aduniya ba

Zurawa Tayi da gudu zuwa gareshi ta Rumgumeshi Tana Fadin"Ya Bashir..Yaushe kazo..? Yana Mirmishi ya Shafa kanta yana Fadin"Autan Umma Kenan..Yanzu na Shigo nazo kawo su Abiden ne sun saka Rigiman wajen Umma yau zasu kwana.."Fuska Ta tabe kafin tace"Nifa ban gane musu bane..Suna so su kwacemin mtsayina wajen Umma da Da Daddy.."Yana Dariya yace"Wane su su kwace gwamnatin autan Umma da Daddy..Shalelen Ya Bashir da Anty Hauwa.."Tanajin wannan kirarin ta washe baki Tana Fadin"Shiyasa nake matukar sonka Ya Bashir..Zan yi kewarka in na tafi kano.."

Ta karishe Fada Kamar tayi kuka irin na Shagwabbun yara bai samu Zarafin mgana ba wata Mata Baka mai Fadin Fuska wacce sai da ta Shigo na Fahimci inda ta Dibo Bakin Fatarta da Hancinta irin nata ne sak,Sai dai ita bata da Tsawo a Shekaru bazata gaza 40 ba Tana Shigowa ta gansu ahaka ta Tabe baki Tana Fadin"Kana nan kana Biye Shiriritar INTEESAR KO.? tun Dazu nake mata mganar ta Rage wadanan kayan taki jin mganata Ta kwashe Rabin kayanta kamar Chaj zata koma Har Abada..!
Umma ta Fada Cikin kara Bayyana mamakinta Wacce aka kira da Intesar ta Fara Buga kafa na Shagwaba Tana Fadin"to ni Umma ba Karatu zan Tafi ba..Kuma ai ance yan Jami"a fa yan gayu ne sosai Dole nima naje da kayan gayuna kada wata ma ta Rainani.."Ya Bashir ya saka Dariya yana Fadin"Hakane fa Intin Umma..Gwara kije da Kayanki Jjc Student.."Ya karishe Fada yana Dariya jin Abunda yace ne yasa ta Nakwa nakwa kamar Zatayi kuka ta Kwashi Gudu Ta Fice Daga Dakin Tana Kukan Shagwabarta Tana Fadin"Sai na gayama Daddy..Kai da Umma kun hademin kai kuna min Dariya..!

Umma ta Tabe baki ta kalle Bashir Dake Dariya tace"Kabiya ta Kitchen ka Karbi Dambun Wajen Talatu katafin ma Hauwa"u dashi.."Cikin Ladabi yace"To Umma..Angode.."Batayi mgana ta Fice Daga Dakin Shima ya Rufa mata Baya Jin Daddy na Kiran sunansa Topa Auta ta kai Sunansa yau shi da Daddy sai Allah Dariya kawai yake kasa kasa Har ya Kariso Falon.










*Shakira...*
3/22/22, 23:02 - Ummi Tandama😇: *GIDANMU..*!
_(Our House)_
*Book1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty*â¤ï¸

*DEDICATED TO:*
*Aisha alto(Sisinah)*
*Chubado muhammad(Uwar dakina)*
*Yahanasu Soupnass(Qawalli1)*
*Kausar salis(My jika)*
*Rahma Ladingo(Dota)*

*🅿�3*


"Da sallama ya Shigo Falon yana Danne Dariyansa ganin Inteesar dare Dare kan cinyar Daddy Tana ta Zubamai Shagwaba shi kuma yana ta Biye mata yana Lallashinta ga Abideen da Abida suna Tsaye gefe suna kallonta Daga duk alamu suna kan Jikin Daddy din ne tazo ta Turesu ta Haye Daman tace wajenta ne suke Neman su kwace mata.

*ALHAJI MUSTAPHA HAMISU DUKKU* ya Dago kyakyawan Farar Fuskarsa Tar da ita kamar ataba Jini ya Fito,Hancinsa Har baka yake kana masa kallon Farko zaka Shaida Tabbas Bafullace ne,Akallah Shekara bazai gaza Shekaru 58 aduniya ba Fararsa ta goge da jin Dadi da Hutu In ka kara kallonsa zaka Fahinci inda suka Dauko Tsawo da Doguwar Fuska Daga Bashir din Har Inteesar din sai dai Bashir Hasken Mahaifinsa ya Debo wanda Gashin kansa da Gemunsa suka Fara Zama Fari bakin gashin kadan ne Daga ganin sa yana da yalwar gargasa ajikinsa.

Cikin Muryansa ta Dattako ya kalli Bashir yana Fadin"Taho nan..Naji Meyasa kuka Tasa Autana agaba kuna mata Dariya kai da Mamarka..? Yafada yana dan Hade ransa ganin yadda Inti din ke kallonsa Bashir na kanne Dariyansa ya Zauna akasa Kusa da Kafar Daddy,Da gudu kuwa su Abiden suka Nufesa ya Daukesu ya aza kan jikinsa,Daga ganinsu yan Biyu ne saboda suna da Tsananin kama da juna Shekarasu bazai Wuce 3 aduniya ba yara ne kanana sai dai sun Debo Tsawon Babansu suna da Tsayi ba Laifi.

Cikin Ladabi yace"Daddy ba Dariya muke mata bafa..Ita Da Umma ne tana mata Fadan Ta Dibi kaya dayawa Shine tace saboda kada taje yan Jami"a su Raina Sai fa kawai nace Jjc shikenan fa Daddy ta Fara Shagwabarta.."Ya karisa Fada Daidai Lokacin da Umma ta Fito Daga Bedroom din Dake Cikin Falon,Ta kariso kusa da Daddy ta Zauna Tana Kallon Intisar Lokaci Daya Tana Fadin"Ke miye haka..? Ko kunya baki

Please Login or Register in order to submit comment