Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akabama su Abba Tayi ta saka musu albarka Tana jin hadin da Imran yayi da kuma mganar Abba Daada ta Roki alfarman Azo Dukku duka a Dauran auran da Shagalin Bikin Tana Bukatar ganin Ahalinta Waje Daya Cikin Farimcikin da bata Taba gani ba nan da man kuwa su Abba suka amince Umma kuwa har ta Kira Mama ta Tsegunta mata mama kunya ta kamata in ita ina kin Abba..?Umma ta fesa Labari har kaduna Wajensu kawu Bala sukace ai wannan Labarin ya gama yi musu Dadi ba Dukku ba ko"ina ne sun yarje sun bada Dama Ko Daddy ya isa ya zama Waliyin Mama
Gabadayansu Gidan Daddy suka kwana Harda Mami Data Kira Hajiya Turai ta gayamata Komai nan da nan Tayi hamdala da jin wannan Labarin Tana gayama Justice bakinta kamar ya Tsage shima ya jinjina kai afili ya Furta Alhamdulillah!
Sajida kadai suka baro a asibitin saboda basa Bukaatar masu jinya
An kwana cikin Farimciki matuka imran da Sagir da Khalil da Khamis sun Hade waje Daya suma su Inteesar suna Tare da Umaima

Washegari Kafin suwuce sai da suka Biya ta asibiti suka Duba Sajida taji Sauki sosai kamar ba ita ba Gabadaya bakin suka koma saboda ayyuka Khalil kadai suka bari sai gobe zai bi Jirgin Abuja zuwa lagos Khamis kuwa kafin Su Munari su tafi sai da ya Tabbatar da cikin Kwana Daya shima ya kafa nashi Ginin.
Su Daddy sun Rabu kan in An sallami Sajida Daga asibiti zasu hadu a Dukku su Tattauna mganar gagarimin Bikin da zasu gudanar na Yan mata uku Zaratan Samari Uku da Daurin auran Iyayen nasu Mama da Abba..!








*Janafty*
3/31/22, 15:36 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�31*

*Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488*


Sai da Sajida ta shafe Sati Biyu a asibiti kafin a sallameta ta dawo gida bayan taji Sauki sosai ta fara maida Jikinta ganin Rayuwa tayi kyau Mami Asma'u Ta gyara Halinta ta Rumgumi ya"yanta ta Fahimci inda ta Gaza yanzu da Ra"ayin Baffa Kabiru da duka Umarninsa take aiki.
Abba da Daddy da Baffa Kabiru sun je Dukku sun zauna da Daada mganar auran dake gabansu Daada tace ita nata Fatan alheri ne da addu"a Mgana da Zartarwa Duka nasu ne sun Taru sun Tsaida Lokacin Bikin gabadaya nan da Wata Hudu kuma Duka a Dukku Za"ayi in an gama Biki araka Amare Gidan zasu zauna da Mazajensu.
Mganar Abba da Mama kuma Daddy yaje Har gida yasamu Inno da Mallam Babba kan mganar su kuma suka bashi Wuka da Nama kan lamarin Kawu Salisu yace ko shi ya isa ya Zama Waliyin Mama saboda Haka sun Amince Dari Bisa Dari indai Mama ta Amince Daddy ya Kira Abba yace yaje su gama da Mama.
Abba bai iya watsama ya"yansa da yan"uwansa kasa a ido ba yaje Har Gida ya Samu Mama suka Tattauna Mama bata isa taki Abba ba Domin wani Bango ne Allah ya Aiko mata dashi Tun bayan Rasuwar Mahaifin Sagir bata karbi Sadakinta ba sai da ta Samu Baba manu ta Fadamai komai Domin ya Chanchanta kanin Mijinta ne na baya ammh bayan kasa ta Rufe idon Tasiu ya kula da Rayuwarta ita da Sagir Shima Lokacin Dayaji Abba amtsayin Wanda zai auereta sai yafi Mama Nuna Murnansa da Amincewarsa Dari Bisa Dari Mama Taji Dadin haka Daman game da yan"uwanta bata da Damuwa Umma Tafi kowa Murna da wannan Hadin.
Baffa Kabiru shi ya biyama Abba Sadaki kamar yadda yayi alkawari Naira Dubu 100,Dakyar Mama ta yarda ta amsa da tace yayi yawa sai dai an Rage Zata karba sai da Baffa Kabiru yayi mgana da ita a waya kana ta yarda ta amsa
An Fara Daura auran Mama da Abba anan masallacin Kusa dasu inda suke Salla a wata ranar Jumma sai aka bar Tarewar Lokaci Daya dana su Munari Baffa Kabiru ya karban ma Abba Aure Kawu Salisu ya zama Waliyin Mama Aranar Bakin Imran da Sagir Dana Yusuf yaki Rufuwa Allah Sarki Rayuwa Allah ya jikan Anni da Gafara Mama tana Tare dasu Umma da Maman Nasara, Da Mami Asma"u da suka zo Tare da Baffa Kabiru da Khamis sai Mommy maman Anty Safiya duk ba Taro bane ammh Mama taci gayunta an kuma yi abinci suma chan gidan su Inteesar nata nasu Shagalin da su Anty Safiya da Munari da Hafsah da Tasleem da Nasara duk sunsamu zuwa suma sun yi kayattacen Girke girke da Ababen sha su Abba da yan"uwansa suna Haraban gidan suna cin Abinci suna ta Fira su kuma matansa suna Falo suna ta cin Abinci suna Hira Harda Sadam yazo Aneesa da yara suna Cikin Shashen Anty Safiya yan matan ba wacce ta Leko Tun bayan da suka Cika gabansu da abinci suka bace duk kuwa da yarda Samarin nasu suke ta Tura musu sakon su fito suna son ganinsu ba wacce ta Leke sanin Halin Wanda ke wajen Imu Domin Tun suna Kawo abinci yake ta Hararansu yace suyu su gama su bar nan Wajen.
Khamis ne yaje ya Duka ya Nemi Izinin Babban Yaya na yana son ganin Munari Imran ya Hura hanci kafin yace an bashi,izini ya tashi yana Dariya ya Kira Munari ta Fito suka Kebe Sagir ne yace wlh bazai nemi Izinin ba Imran yace ba kuwa zai ga Hafsah ba yace bai isa ba Imran yace To sai ya gani.
Duk da Sagir ya Kirata Tana Fitowa kallo Daya gogan yayi mata ta Koma Ciki da Gudu Sagir ya Saki baki su Yusuf na Dariya Imran ko ya Hade Rai Zaginsa yayi bai damu ba sanin ai Sagir ba Girmansa yake gani ba Khalil ya Kira ya Fadamawa shi kuma yace ya Kyalesa na Lokaci in suka yi Ciki da kannin nashi ya isa ya kafa musu Wata Doka ne,Dole ya Kyalesu suyi yadda suka ga dama.
Imran bai yi magana ba Sanin Halin Khalil in suka Hade da Sagir sai Allah,Shi da yake da Sauran mai Cutar Xuciya Kafin auran Jinya zai tayi ko nacema yana kanyi Tunda Sajida Har yanzu Tana agida Karkashin Kulawar Likita Gefe Daya Khalil na bata Kyakyawan Kulawan Datake kra Taimaka mata batare data sani ba ta Shaku dashi sosai Kamar sun Dade da Sanin juna.
Washegari kowa zai koma Inda ya Fito Da Daddare Da Imran yace Intee ta Fito su tafi sai ta yo mai gayyar su Munari da Hafsah da Nasara zasu Bita su kwana agidansu da Imran yaga haka Ransa ya bace har Intee ta koma su kwana Tare Ita bata gane ba Tana ta Murna batasan Talala yayi mata ba Washegari da baki suka Watse suka koma Gida sai da ta Raina kanta Daya Damketa sai da ta koma magiya da Ban baki kana ya Ragamata Hukuncin ta kenan na Hanasa Shagali Daran Jiya.
Inteesar sai dai Tura baki bata ta tacewa Daman haka yake mata yace Tunda bata son Fada to Hukuncin Daya Dace da ita kenan ba Duka ba Zagi zai ladabtar da ita Hankalinsa kwance.
Ta kowani Bangare sun Fara Shirin wannan Gagrumin Bikin Duk da basu yi wani Wahala ba ko Daura ma kai Nauyi ba Dukkansu Sadaki Kadai Baffa Kabiru ya Zartar Domin shine kamar makwafin Alkali Dukku marigayi Allah ya basa Girman kuma ya karba,Mami Asma"u ba Zama Zata aurar da manyan ya"yanta Guda Biyu sun Hade kai da Umma Kamar yadda kawunan Mazajensu yake a Hade Mami duk ta Zubar kawayenta ta kama Umma Hannun Bibbiyu ta Fahimci zama da Mutanen kwarai yafi Zaman da Mutanen Banza.
Wannan Karon an Raba Daddy shi ya Dauki Nauyin yima Amare Jeren Daki Baffa Kabiru kuma Baban angwaye shi ya Dauki Nauyin yima Duka Zaratan Mazan akwatuna aure Da Sagir da Khalil da Khamis Harda Abba Wannan karamincin yasa Dr.Ali Argugu ya taso Tun Daga Lagos Har Kano yayi ma su Abba Godiya Domin koda Khalil yaje musu da Labarin Chanji Daga Munari zuwa Sajida basu ce komai ba Sanin Daman ai Matar Mutun kabarinsa kuma wani baya auran Matar wani daman chan Allah ya Rubuta Sajidan da ita Za"ayi...
Mama ma Tana ta Godiya Baffa Kabiru yace bayason Godiya Da Khamis da Khalil da Sagir Duka Dayane a Wajensa.
Imran dai na gefe bai Zake ba ya Kama Girmansa na Babban Yaya Khamis ne kadai ke basa Girma yana Shawara dashi banda Sagir Daya gama Rainasa gwara ma Khalil yana Ragamai Tunda dai yana Kularmai da yar kanwarsa Sajida wacce kusan koda Yaushe yana Kiranta yaji Lafiyanta ya Dauki alkwarin Kula da ita na Musamman acikin kannensa ba Domin in ya aureta bazai yi adalci ba Daya Aurota ya Hadata da Inteesar to ya kwana da sanin baza"a zauna Lafiya ba,Rigimar Inteeear ba Ko yanzu ma Bata kaunar Taga yana Mganar Sajida ko Taga ya Kirata a waya yanzu Zata Chanzamai fuska sai ya koma yana Lallashinta Tana da Kishi sosai,shi kuma bai iya Hayaniya ba Ballatana ya jawo ma kansa aiki Masu Shirin Shagali su Intee ce ana gaba gaba sune manya.
Sajida a Lagos Zata zauna Gidan Khalil,Hafsah kuma agidansu Zata Zauna Inda Sagir yasa aka Fara Bugesa za"a Sauyamai Samfarin Ginin Zamani Falt mai kyau da Tsari Tunda Mama Gidan Abba Zata koma Shima Abba yasa an Fara Gina wani kayattacen Shashi Daga gefe nan Shashen Gabadaya zai barma Yusuf ne.
Khamis kuma porthercourt Zasu Zauna Domin ya samu Transfer Daga Anambara zuwa Porthercourt,chan zai Tafi da ita ammh sai sun yi Sati Biyu a Abuja,Ta kowani bangare Shirin Bikin ake Gudanarwa,ba kama Hannun yaro Dayake Allah ya Rufa asiri sai komai yayi Daidai ba wata Mtsala sun Tsara zasu yi Events dinsu a Dukku zasu yi Fulani Day,sai Lonching,sai Matan da zasuyi Walima.
Inteesar duk ta Fara Damuwa Munari Zata tafi ta barta ita kadai a makaranta da garin gabadaya,Saboda Chan Khamis zai nema mata makaranta in tasamu Transfer ta Cigaba Saboda Shirye Shiryen Bikin Har sun Fara wasa da karatun nasu Dayake suna Second Semester ne na aji Biyu sai da Imran yayi musu Fata Fata kana suka maida Hankalinsu.
Bangaran gyaran Amare kuma Inna Maimatu da Inna Bintalo suka Karbi Mangaran suka aika da Jarkunan mganin Sanyi da Gumbar mata Abuja da kano Da Dutse Munari da Hafsah da Sajida duk sukace su fara amfani Dashi Umma ma ta Dakema Mama kan sai ta gyara itama Tana ta Korafin wai Ta girma wannan aikin yara ne Umma tace sai fa ta gyara ita da Maman Nasara suka Hade mata kai suna Fadin ai ko Manyan ma suna son agyara musu suji Dadi Dukkansu Dole ta Fara karban gyara Daga garesu Domin kaunace ta kawo Haka.
Sagir da Taimakon Filinsa daya Gada ya Saida ya Fara aikin Ginin an Sauya Fasalin Gidan Gabadaya an Fitar da kayattacen Falt mai Dauke da 2Bedroom da falo da Kitchen sai wani karamin Shashe mai Falo Daya da Bedroom Daya,Sai Haraban Gidan da Get domin Shiga da Mota Tunda ai Cigaban Rayuwa ake nema sai Daga Shagonsa ya Bigeshibaka kara Fili aka Bude Babban Shago mai girma ya Bude Kofa ta Waje data Cikin Gida Saboda yana so nan gaba ya kara Kekuna Da ma"ikata Tunda dinkin nan Dashi Yake Rufama kansa asiri yau ko ya gama Makaranta ba Lalle ne ya Samu aiki da Wuri ba Imran ya Bashi wannan Shawaran Domin shima yayi ma Sagir alkawarin Hada Hannu Dashi Wajen Bunkusa Kasuwancinsa sosai.
Wasa wasa Biki nata Matsowa Dama kuma Hausawa sunce Duk Abunda aka Sakama Lokaci sai yazo gashi yau Bikin ya Rage Saura Wata Daya Tuni Ginin Abba Shima ya kamallah Gabadaya an sauya Fasalin Gidan An Hade Shashen gabadaya An kara Fadada Bangaran Yusuf da Anty Safiya Sannan anyi bangaran Baki Daga Ciki Daga Chan Gefec kuma Kayattacen Falt din Abba ne mai Dauke da 3bedroom Da Falo Guda Biyu Daga Bakin get kuma an Fitar ma Iro megadi Dakuna Biyu Ciki da Falo Shida Direban Abba Tunda duk nan suke kwana an Sauya Fenti Har da Duka Sabbi kayan Cikin Gidan Abba yace baya Bukatar komai sai Mama Gabadaya Kamfanin Marhaba suka zo suka kawata Bangaran sai wanda ya gani.
Wannan Karon Mami Asma"u da Umma Baffa Kabiru ya bama Kwangilan Hadama Zaratan Mazan kayan Lefe,Mami Asma"u ta bada Shawaran su tafi Dubai su Hado komai haka kuwa akayi Dubai suka Tafi Harda Maman Nasara Saboda Tasan Wajen Tana zuwa Saro kaya Sati Daya sukayi suka jiyo da akwatuna Saiti Biyar cike da kayan alfarma,Dayake kafin su Tafi sun karbi Size din Ya"yan nasu A Abuja suka Sauka nan suka Fara baje kayan Baffa Kabiru yace nan Za"a Barsu Dasu Za"a Tafi Dukku Zai Dinka musu wasu kayan Fitan Bikin na Dabam Abun fa nayi ne Bakin Aljihu kadai ya Saki su Umma na amsa suna ta Shirinsu Daga Mazan har matan kala Biyar Biyar yayi musu na kayan Fitar Biki,Harda Abba da Mama suma Baffa Kabiru bai barsu abaya ba.
Ana Saura Sati Biyu Biki Inna Maimautu tazo ta Hada kan Amaran Waje Daya ta tafi dasu Bauchi ta gyara su Inteesar harda kukanta taso taje Imran yace Ya Hakura da gyaran iya wanda ke Jikinta ma ya Ishesa jin Dadin in tatafi shi kuma ya Zauna da wa..?
Dole ta Hakura Tunda Oga ya Hana ammh Kullum suna waya dasu suna Fadamata yadda suke shan gyara Ana ta Musu Dilka da kayan gyara na Da"a Daga Sokoto Inna Maimunatu ta bada Sako aka Kawo mata tana ta gyaran Ya"yanta.
Mazan suma suna nan suna ta Shirinsu na kece Raini Imran dai Na Gefe bai Zakewa yace shi Babban Yaya ne sai dai Shawara ko bada Umarni sun Dinka angon Fitar Bika Kala Hudu Hudu wannan kuma Gudummuwar Yusuf ce yayi musu Gabadayansu har dasu Ya Basheer dasu Abba Ranar Daurin auran gabadaya ankon Farar shadda Zasu saka,,Manyansu da yaransu Matan ma sun Fitar da wani less shima mai kyau na Yinin Biki Hatta Daada ba"a bari a baya ba ya"yanta sun Dinka mata ita da Baba asabe..
Ana Saura Sati Daya Bikin Hajiya Barira da Sairan ya"yanta suka Sauka akano Fagge ta sauka agidansu Chan itama Zasu yi Taronta Dr.Ali argungu sai Saura kwana Uku zasu iso da Khalil sai bayan Biki zasu Tattara su koma Lagos har da Amarya Sajida.
Da yanzu taji Sauki sosai kamar bata Taba Wata Cuta ta bar makaranta Saboda Daman ta rasa Shekararta ta Biyu Dole baya Zata dawo in taje Chan Lagos tace ma Khalil in Ta koma Cjan Zata Dora Daga Farko ne
Tunda Lokacin ya gabato suna ta Shirin Tafiya Dukku ne bayan an gama Jerin Dakunan Amaram Daman kamfani ne suka zo suka jera komai sai abun da ba"a rasa ba Matan suka shiga Kasuwa suka kara musu Sajida ita sai sun isa Lagos din za"a siyamata komai Munari kuma bata Bukatar komai Saboda Gidan da aka bama Khamis achan Porthercourt akwai komai na More Rayuwa sai abunda ba"a Rasa ba Hafsah ce aka kawatama ta Shashenta Balle ya Hadu da Sabon Tsararran Ginin da Sagir ya Narka Dukiya aka narka mata Mama Tana Sabon Shashen mai Dauke da Bedroom guda Daya Kafin itama ta Tashi Zuwa Gidanta Inda Abba ya gama kawata mata.
Tun ana Saura Kwana Uku Taron Bikin Matan suka Fara Sauka Adukku Inna Bintalo da Tawagan ya"yanta Inna Maimunatu itace ta iso da Tawaagan Amaran da suka Sauya Saboda gyara ko"ina suka Gitta sai Tashin Kamshin Fatarsu na Santsi da yarari,Ranar al"amis Sauran suka Iso Umma da Mama da Tawangansu Maman nasara da Anty Uwani sai Mami Asma"u da Umaima da suka Taho Daga Abuja.
Inteesar Tawagan su Anty Safiya ta Biyo Ita dasu Anty Aneesa da Anty Faresatu da Tasleem sai Inna Kaltume matar Baba Manu, Nasara tana chan Daga Kaduna tabi su Umma,Mommy Tana Fagge su ke da Taron Bikin Bangaran Uwar ango Khalil Hajiya Barira.
Tawagan angayen kuma Sai Ranar Jumma"a suka iso gabadayansu Yaransu da Iyayen Ciki Harda Kawu Manu da Alhaji Alhassan da Dr.Ali Argungun da suka iso kano Tun Ranar Laraba a Kaduna suka Hadu gabadayansu suka Dunguma suka kamo Hanya gabadaya sai dai aka Rufe Gidajen.
Aranar da Yammah sukayi Fulani Day a Aharaban Gidan Marigayi Alkali Hamisu Dukku,Shigar Fulani gabadayansu sukayi matan su da Mazansu sun siya kayan banda su Abba Da suke gefe suna Kallon yayan nasu Cikin Alfahari Harda Daada sai da Ta Fito Bakinta yaki Rufuwa bata taba ganin Ahalinta sun Hadu waje Daya ba Tashin Hankali ba sai yau Ga Mami Asma"u da Yan"uwanta duk sun zo sai Shiga da Fita suke yi suna Raba Damammiyar Nono da Fura mai kyau da Aka siyo da yawa saboda irin wannan Ranar kowa kagani yana Cikin Farinciki,Amaren suna Waje Daya suma sun Cakare Cikin kayan Fulanin Kamar yadda Inteesar ma ta saka nata sai dai ta kara kiba Ciki ya Budata Kana ganinta Zaka Fahimci Tana da Shigar Juna Biyu Imran na Tare da ita yace ta kama Girmanta Duka wajen itace yayarsu har su Sagir da Khamis sudai Dariyansa kawai suke shi ala Dole sai an basa Girma ko ana so ko ba"a so Inteesar kuma Tana so ta samu Sake cikin Yan"uwanta susha Firansu Dukkansu achan akayi musu Kunshi da gyaran kai Sajida data maida Jikinta sai Walwali Take Bini bini kadan Tazo ta kawo karar Khalil wajen Babban yaya in yayi mata wani abu Shi kuma yaja kunnensa in kaga wannan ahalin Aranar sai sun baka Sha"awa kayi Musu Fatan zama cikin Farincikin nan Har karshen Rayuwarsu
Sai wajen goma Dare suka Tashi Taron suka koma Cikin Gida Mazan Matasa da Su Abba duk suna BoyQuaters da aka Riga aga gyarashi Tsab. Gari na Wayewa suka Tasshi da Hidiman Biki da Daurin auran suka Tashi Gabdaya Girke Girken duka su suka Zage sukayi kayansu Kala kala sai wanda ka Zaba ballatana ga Dangin Uban Hafsah suma da Safen suka iso Harda Mijin nata da yan"uwansa hakama Mijin Inna Bintalo Gida dai ya Cika Sosai Gwanin ban Sha"awa.
Da wuri gabadaya akayi wanka Kowa ya Cakare gabadaya matan Shigar iri Daya sukayi na Less din nan Amaran suma Shigar iri Daya sukayi suma na Less ammh kalar nasu dabam Harda Inteesar itama kamar amarya Domin tasha Kwalliya an Kashe mata Dauri kamar Amarya sai dai ana ganinta anga mai Matashin ciki.
Mai kwalliya suka Kira tazo Tayi musu Daada ma ta Ci Wakanta Itama su Inna Maimunatu sun kashemata Dauri sai Hoto suke Daukanta Bakinta yaki Rufuwa.
Mazan suma suna chan duk sun Shirya Cikin Fararan Shadda Kowa kuma da Babban Riga da bakar Hula da bakin Takalmi da bakin Agogo,Harda iyayen suma Shigar sukayi Harda yara irin su Waleed da Abidin
Daurin auran karfe 12pm na Rana ne da an Daura za"ayi Walimar maza a Wani Restauranta inda zasu ci Abinci Matan kuma nasu sai gobe ne Lonching zasu Gudanar.
Daddy shi ya bada auran Duka ya"yan nasu Hafsah da Sajida da Munari Saboda Dangin Mahaifin Hafsah sun yi musu kara sosai,Dr Isa Argungun Yayi ma Alhaji Alhassan kara shi ya Nemar ma Khalil auran Sajida yayinda Baba Manu ya karban ma Sagir auran Cikin Kankanin Lokaci Aure ya kamallah yayinda Baffa Kabiru Shi ya Biyama Duka Zaratan Mazan Sadakin Dubu 200 ne.
Nan da nan Masallacin ya Kaure da Hayaniyar fatan Alheri ana ta gaisawa da Mutane da angwayen da ba"a gane su Tunda Duka Shiga iri Daya sukayi Daganan Reception sukaje sukayi koda suka dawo har an Fara Lonching din Daman mata da Maza ne nan da nan kowa yaja Amaryansa Gefe,Imran mamaki Yaran ma suke bashi sai Wani Rawan kafa suke Saboda sun yi aure ba su Munarin ba Su Sagir din ba Shima Inteeear yaja Gefe suka kame afili ya Furta suma ai angwayen ne Dole suma su Cakare.
Anci an sha an yi Rawa sosai Sagir da Khalil da Khamis sun kwaso Shoki Abunsu da matansu Imran na Gefe yana kallon Abun mamaki ko kunya Cikin yara Inteesar sai Fushi Take yi Tana so Ta shige aammh Imran yayi mata Jam ido Yace bai son Iskanci da Cikin nashi ne Zataje Tana Girgiza kuma sannan baya son Shirme ta barma yara Dole ta Hakura Tana Gefe Tana kallo sai dai sunje a manya yayyi kamar yadda Imran yake so sun yi manni kudi an sha Hotuna kamar ba Gobe Kowani Hoto Sai an gawayen sun Rike Imran anyi dashi dasu Amaran sai Dai Fuskarnan ba Fara"a ko kadan su Ya yusuf suna Gefe a Mtsayinsu na manya yayyi.
Washegari Aka yi Walimar aure anan Haraban Gidan da Yammah,Ranar Litini kuma akayi Shirin mika Amarre Hafsah Kano Za"a kawota ita da Sajida Munari kuma Abuja zasu wuce ita da Khamis dasu Mami.
Inna Bintalo Zata Bisu Abuja Inna Maimunatu zata je kano su Da su Umma Domin mikama Mama itama Gidan Auranta.
Daganan Dukku Iyayen mazan sukayi Sallama da juna bayan Daada ta tarasu tayi ma Duka Ma"auratan Nasiha da zasu tafi harda Kukanta Domin Tana ganin kamar Kara Haduwarsu na Mutuwarta ne.
Masu Tafiya Kano Duk Tare suka Dauki Hanya Wajen Motoci Goma Sajida Tayi kuka wajen Rabuwa da Mami da Baffa Kabiru da sauran yan"uwanta Munari ma Tasha kuka ita da Inteesar haka ta kamkame Abba Da ya Yusuf Harta da Imran sai da idonsa ya Sauya ya Rumgumeta yana Shafa kanta Daga Dukku Jirgi suka Hau zuwa Abuja Ita da Inna Bintalo dasu Mami.
Suna isowa kano Mama aka Fara Rakawa Gidanta Shashenta Sai son barka Rakiyan Umma da maman nasara da Anty Uwani da Inna Kaltume Sajida kuma Mommy da Anty Saratu suka Tarbesu,Aranar suka Tafi Fagge ita da Khalil da Umma,sai Gobe zasu bi Jirgi zuwa Lagos Inteesar bata raka Ko Dayansu ba sai Hafsah,Ita da aka kaita Kusa Inna Maimunatu ta mikata Dakinta Tana ta kuka ba wanda suka kwana Kowa ya watse sauran baki suka koma gidan Abba wasu kuma Gidan ya Sadam suka koma suka kwana.
Washegari Talata Kafin su Khalil su wuce sai da suka Biyo Tanan sukayi Sallama da yan"uwa Kafin su Dunguma Gabadaya aka Rakasu Filin Jirgi Zuwa Lagos Umma da inna Maimunatu ne zasu Raka Sajida sai yayar Mami Asma"u Guda Daya.
Inteesar Tasha kuka Data Waiga ba Munari tana chan Abuja Allah Sarki Rayuwa Imran ne da suka koma Gida Yayi ta Lallashinta Tun aranar gabadaya Kowa ya watse aka bar Amaran da angwayen su samu Natsuwa,barin ma Abba da Mama,Sagir da Hafsh suma su kadai agida sun Fara Cin Amarcinsu Umma da Inna Maimunatu kwana Daya sukayi a lagos suka Jiyo Zuwa Kano Domin ai Dr.Ali argungun ya gama komai gabadaya Gidan shi ya kawatashi yace Sajida ya'tace garesa Saboda Malami kuma Shi da Iyaalan Daada ai sun Zama Daya haka suka dawo da Labarin mai Dadi sai Fatan Allah ya basu Zaman lafiya

Daga Kano Inna Maimunatu ta wuce Bauchi ya"yanta suma kowacce ta koma Gidanta Umma kuma bata Kwana ba ta koma kaduna Tunda Daddy da ya Basheer sun koma Shi da Anty Hauwa da Little Inteesar Anty Safiyama Da Imran karami Daya Fara Wayau duk sai sukaji Gidan Shiru ba Gilmawar Abba yana Barayinsa ba Munari sai su kadai Allah yasa ma ga Kirniyar imran karami.
Munari kuma Dagachan Abuja Inna Bintalo kwana Biyu tayi ta so tayi ta Koma Baffa Kabiru yace taa Tsaya ta Raka Munari Dakinta haka kuwa akayi kwanansu Uku a Abuja suka wuce Porthercourt da Rakiyan Inna Bintalo kwananta Biyu suka Hadota da sha Tara na arziki suka Sakota ajirgi sai Gombe Ta koma Gidanta Domin ta Sauke gajiyan bayan ta Kira Duka yan"uwanta tasanar dasu ta Dawo Lafiya ta Raka yarta Munari Dakinta.
Sai da suka Shafe wajen Sati Biyu suna Sauke Gajiya Domin fa an sha Zirga Zirga Munari suna waya da Inteesar da sauran yan"uwanta Inteesat tasha Korafin irin Wahalan da Abokan Mijinta suka gana ma kawayenta Harda Sajida ma suna mgana Ita tabama Imran Labari yayi ta Dariya To Daman Tunda suka auri wadanan Tazuran ai sun gama yawo sai Fatan Allah ya basu Zaaman lafiya ita kanta Inteesar din ai ta gayama aya Zaginta Domin kwanakin nan kaf sai da Imran ya Famshe ita Duk Sauke gajiyan da Kowa yayi bata samu wannan Damar ba.
Allah Sarki Inteesar ita kadai ta Cigaba da zuwa makaranta kafin Transfer din Hafsah ya samu ta dawo nan da Karatu Gidansu Imran ya kara Zama Gida Saboda

Please Login or Register in order to submit comment