Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rayuwarsa Cikin Wani Hali ba.
Daganan Sagir da Inteesar suka ijiye agida suka karisa suma.
Suna Dawowa abinci suka ci suka yi Sallar La"asar Abba da Yusuf kuma Daman masallaci suka tafi,Imran kuma yana Cikin Dakinsa ba wanda yaji Motsinsa kuma ba wanda ya Neme sa yaji sanin Halinsa.

*****
Washegari ta kama Lahadi ne Tun Safe Inteesar ta tashi da Murna Domin Tayi mgana da Daddy yace suna Hanya shi da Ya Basheer ammh sai sun gama abunda ya kawosu zasu zo nan gidan Maman,Gabadaya ta kasa Zama Saboda Murna Mama natayi mata Dariya Ya Basheer na son Alala shi tayi mai Abba kuma Tuwon Semo Tayi mai miyar Kubewa Bushashiya Sai wajen 1pm ta Gama komai ta shiga wanka ta Shirya ta Zauna zaman jiransu Ko abinci ta kasa ci,Mama sai Fada Take mata kan ta Rika cin Abinci ammh ta kasa ita Haka in tana Zakwadin Abu abinci ma Baya gabanta.
Duk bayan Mintina sai ta Kira Daddy taji ko sun gama abunda ya kawosu suna Hanyar zuwa Gidan Mama sai yace Mata A""a har ta gaji da kira ta Hakura tana ganin kamar bazasu zo bane Har Munari ta Kirata Tana Tamnayanta ko Daddy ya iso tace eh Yana cikin kamo sai dai basu kariso ba
Tace to bara tayi wanka gatanan zuwa,Da haka suka rabu kuma sai ta Jita Shuru karfe 3:00pm na rana Daddy da Ya Basheer suka iso ho zo kuga Murna wajen Inteesar ta makale Daddy gamgam Tana Fadin tayi kewarsa Hakama Ya Basheer ta Rumgumesa shima ya Riketa Cikin Farinciki Mama itama Murna Duk ya kamata ta rssa ina Zata sakasu haka take akwai son Yan"uwanta sosai.
Bayan sun zauna sun sha Ruwa da Inteesar ta gama jera musu aka Fara gaisawa Sagir na gefe Daman yana Shago yaga Isowarsu shi yayi musu Jagora zuwa Cikin Gidan.
Mama da Sagir suka basu Waje su gana Da Inteesar nan ta zauna tana Zubamai Shagwaba da Tambayoyin ina Umma..!? Talatuwa..? Anty Hauwa ina su Abiden ya Basheer gajiya yayi da amsa mata yayi Shuru yana cin Alalansa Dakyar ta bar Daddy yaci Tuwonsa  yaci sosai jin Intee tayi mai,bayan ya gama ya Kira Umma ya bata sukayi mgana inda tace ta bama Dadynta sakon Dambun nama da Kayan Snkas,Roba Biyu ne Daya nata Daya na Mama nan tace ma ta kaima Mama Wayar suyi mgana nan ta Fice Tsakar gida ta Mikama Mama Wayar sukayi mgana da yar"uwanta sun Dade suna mgana barin ma mganar Kan auran Yarinyar Wajen kaw Bala ne nan da Wata Biyu.
Daddy sai da sukayi Sallar La"asar sukayi Shirin Tafiya bayan ya cika Mama da kudi Tana ta godiya kuma sun sauke mata kayan abinci Inteesar harda Lemonta Freshyo,Katan uku Daddy ya Taho mata dashi ya bata 20k a Hannunta Ya Basheer 10k ya bata Kuma ko Sati ba"ayi ba Daddy ya Turamata 20k ta bankinta ko Tabata batayi ba.
Sam ta manta da Munari sai da Su Daddy suka fito ta Rakosu ita da Sagir Daddy ya Kalleta yana Fadin"Banga Kawarki da muke jin Labarinta ba Intee..Ko bata nan ne..?wanda kikace yayanta na kai ku makaranta..?
Sai alokacin Inteesar ta Tuna da Munari ta Bude baki Tana Fadin"Laa..Daddy kaga zuwanku ya sa na manta..Munyi mgana da ita Tun dazu tace zatayi wanka tazo bari na kirata naji plz Daddy..!
Daddy ya Murmusa kafin yace"Anything For my Angel..!
Ya Basherr na gefe yana waya da Anty Hauwa Tana Tambayansa suna Hanya ne yace yanzu dai zasu taso.
Inteesar Tana ta Kiran Munari Tana Ringing bata Dauka ba ganin yadda ta Dakuna Fuska ne yasa Daddy ya kalleta yana Fadin"Baki same ta bane..?
Inteesar tace"Na sameta bata Dauka ne Daddy..!
Tafada cikin Shagwaba ya Basheer Daya kamalla wayarsa ya Kalleta yana Fadin"Sai ki bari Next time in muka Dawo..Yanzu pass4 kuma kinsam Kaduna muka Nufa..!
Inteesar ta Marairaice Tana Fadin"Kai ya Basheer..Tafa ce zata zo wlh..Gidansu nan nan kusa Daddy naje na Kirata..?Itama tana so Taga Daddyna ne fa..,!
Kafin Daddy yayi Mgana Basheer yace"No Daddy..Lokaci na tafiya in ka Biyema Shirmen Intee zamu yi Dare a Hanya..!
Sagir yayi Saurin cewa"Ai gidan ba Nisa..Nan fa kusa ne..!
Daddy ya kallesa yana Fadin"Ai mun Riga mun yi Daran Basheer barta taje ta Kirata..!..
Basheer bai ce komai ba kada kai kaawai yayi,Inteesar taji Dadi ta Fara Tafiya Tana Fadin"Tanque Daddy..!
Gudu Gudu Sauri Sauri Take Tafiya Har ta isa Gidansu Munari Saboda Saurin Datake yi ne yasa bata Tsaya kula mganar Iro ba shi kuma yana so ya gayamata ba kowa agidan sun Fita Har da Abba Amotar Yusuf.
Tana ta Sallama Bayan ta Turo kofar Falon ta Shigo ba"a amsata ba Tayi mamakin rashin ganin Abba zaune yana Kallo ko yana Karatu Falon tabi da Kallo alamun Shuru ba kowa Tayi Tsam kafin aranta tace ko basa nan ne..!
Tuna haka yasa kawai ta Juya Zata koma sai taji Karan Bude kofa Tana Juyowa suka Hada ido Hudu dashi.
Imran ne yana Tsaye yana kallomta Yana Sanye da Dogon Wando baki da Wata Farar riga amles,Hannunsa Daya Cikin Aljihun wandonsa Dayan kuma Karan Sigari ce tana kunne Hayakinta na Turiri.
Gabanta sai da ya Fadi Data gansa Haka Duk gabar jikinsa tana waje sai ta gansa wani Kato dashi.
Baya taja cikin Rawan jiki zata kara Juyawa Taji yace Cikin Kaushin murya"Wa kike nema..?
Yafada Lokaci Daya yana wuceta zuwa Saman Dining.
Ruwa ya Dauko a wani Jug ya samu karamin Kofi ya Tsiyaya ya Dago yana kallonta Daga sama Har kasa Lokaci yana Kurban Ruwannsa Hade kuma da zukan Hayakin Sigarinsa..
Inteesar Dataji gabanta na Dukan Tara Tara bakinta yayi Nauyi ta kasa mgana.
Shi kuma Ransa ne ya Fara baci da Yarinyar lokaci Daya cikin Dakiyarsa yace"Ke kurma ce..? Ina mgana kina min banza..I Hate it..Ya zama Dole in nayi mgana abani Amsataaa..!
Yafada cikin Tsawa da Daga Muryan Dayasa da Sauri ta Dago Tana kallosa Itama Mamakinsa take ji yadda yake Zukan Taba Kuma yana Kurban Ruwa anya wannan yasan abunda yake yi kuwa..! Itafa duk sadda zata gana yana Shan Taba ne ko Lafiyarsa ma Bayaji..?
Ganin kamar ya fara Takowa ne yasa da Sauri tace"Ina yini..Wajen Munari nazo..kuma inta kiranta a waya bata Dauka ba..!
Kwayar idonta yake kallo yaso ne ya isa gabanta yayi kwallo da ita sai kuma yaji ya kasa Muryanta da Idanuwanta kamar wani Kaifin Dafi ne garesa sai yaji ya kasa komai.
Dakyar ya iya kauda kai yace"Bata nan..!
Kallonsa Tayi ta gefen ido kafin tace"Ina taje..? Abba fa da Anty Safiya..!?
Yaso ne ya Daka mata Tsawa sai kuma ya kasa Cikin kosawa yace"Suma..!
Daga haka ya tsuke bakinsa Cikin mamaki take kallonsa tace"Suma basa nan..?
Kai ya gyada mata Domin ta Fara Takuramai da mgana.
Abun sai ya bata mamaki tace"Ina sukaje haka..?
Yana jinta yayi kamar bai jita ba Har ta Juya sai taji yace"I don"t know..Kamar dai sun shiga cikin gari ne..yama sunan wajen wasannin nan.?
Da sauri Inteesar ta waigo tace"Shoprite..,!
Kofin Hannunsa ya Ijiye bai yi mgana ba Inteesar an samu waje sai ta karkace tace"Wato Family Outing sukaje yau kenan..? To kai me ya Hanaka Zuwa..?
Da sauri ya Dago Jajayen Idanuwansa yana Kallonta Sauri ja da baya Tayi Domin Warin taban ya Isheta zuciyarta ta Tafara tashi kuma ba Halin Toshe Hanci.
Cikin kallon kin Rainamin wayau yace"Ni nayi miki kama da yaro ne Dan goyeko mai Tatata..?am not a Boy kin gane..?
Yadda yayi mganar kamar ta saka Dariya sai ta kanne nan kan Dinning din ya Mutseki Sigarin ya wuce zai shiga Dakinsa,bayansa tabi da kallo Haka kurum taji Tsausayinsa itafa har ga Allaj kallon mara Lafiya take mai.
Cikin gwarin gwaiwa tace"Don Allah ka Daina shan Sigari bata dace dakai ba Sam..!
Cak ya Tsaya Daga Dora Hannunsa kan Handle din bedroom dinsa ya Waigo yana kallonta
Sagir da yusuf suna Fadamai shan Sigari bata dace dashi ba bai taba jin mganar ta shigesa ba sai yau.
Ba karamin Juriya tayi ba wajen Kallon kwayan idanuwansa ba ta Cigaba da Fadin"Ba domim Iyalanka ba..Ko Domin Lafiyanka Don Allah kabari..nasan ka sani sai dai zan kara Sanar dakai a likitance Shan Sigari Tana Illah ga Lafiyar Dan"adam..Domin Lokaci Daya take yima Huhun Mutum illah..!
Tana Gama Fadin haka ta Juya da Sauri ta Fice jin wayarta na Vibration kuma ta Tabbata ko Daddy ko ya Basheer ne suna jiranta.
Ficewa Tayi Daga Falon tana Sauke Numfashi Miyau ta Zubar Jin Hancinta na Budewa Tana so ta Shaki iskar Haraban gidan ne ko Hancinta zai Daina Shako mata Warin Sigarin Dake Neman sakata amai.



*Ina godiya masoyana na WhaApps da yan Wattpadian ina ganin Sharhinku Allah ya saka da alheri sai dai ina so nadan yi wani Tsokaci ne kan mganganun wasu masu Sharhi kan Suna Tantama Anya Imu kansa Daya..?wai ko yana da Aljanune..?ko kuma yana da mental problem..?Amsa itace Imran Lafiyayyan Mutum ne kamar kowa,Bai da wata Cuta ko Nakasu in kun Duba Labarin Tun abaya ba inda na saka yana da wani mtaala sai Mtsalansa D'aya na Rashin Controling kansa in Ransa ya baci,Kuma akwai mutane irin haka yana da zuciyar Fulani ne ajikinsa,in kun lura Saboda Sanin Halinsa yasa bai shiga Harkan kowa kuma baisan batama mutane rai koda ahalinsa ne,in kun karanta ko da yan gidansu bai Doguwar mu"amala saboda gujema bacin Ransa,Baya kaunar a batamai rai shiyasa yake gujema bacin ran Wadanda ke Zagayo dashi a labarina ban nuna inda Imran yayi wani abu haka kurum batare da an shiga Harkansa ba,Yana da zuciya mai kyau kuma ka in kiyayemai zaka ji Dadin Zama Dashi mganar ko Imran baida Lafiya to Lafiyarsa Kalau Tsarin Hallitarsa ne haka Team Imran da Team Inteesar duka sun ce suna Godiya Son so Fisabilillah*









*Shakira..*
3/22/22, 23:06 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*🅿?22*

Tun bayan fitan ta bai motsa Daga inda yake ba Mganganunta sun kashe mai Jiki duk ba wannan ne Karo na Farko da aka sha gayamai shan Taba bai dace dashi ba kuma ba yau ya Fara sanin Smooking yana da Matukar illah ga Lafiya ba sai dai karon Farko ne ya Farajin Tasirin mganar acikin kansa da kwalkwalwarsa.
Kofar data Ficen ya kurama Ido Lokaci Daya Zuciyarsa na Bugawa da karfi da karfi a duk Lokacin Daya ganta ko yaji mganarta wani abun mamaki mganarta Tana da matukar Tasiri acikin Zuciyarsa.
Cikin kasala da Sanyin jikin da Kalaman Inteesar suka Sanyasa ya Tura Kofar Dakin nasa ya Shiga Kafin Fitar sa Yayi Niyyar Daya dawo zai Dora Daga inda ya tsaya na Busan Hayakinsa Tunda Kishirruwa ne ya Fitar dashi sai dai kuma Ya kasa Daukan karan Sigarin ballatana ya kunnata Haka kurum yake jin amsa Kuwwar mganar Inteesar tarika Tasiri acikin Jikinsa da Zuciyarsa yasa yana ji yana gani bai kunna karan Sigarin ba sai ma Tattarasu da yayi ya Tura Cikin Side Drower din gadonsa ya koma ya kwanta Ringigine yama Rasa wani Tunani zai yi ko zai kama.

Inteesar kuwa Tana Fita taci karo da Daddy da Ya Basheer da Sagir ya Rakosu a Mota sun gaji da Jiranta Tana Fitowa suna isowa kofar gidan Fitowa Daddy yayi yana Fadin"Bata nan ne..?
Kai Inteesar ta Daga kafin tace"Eh Daddy sun fita..!
Daddy ya Bi gidan da kallo Haka kurum yake jin wani irin yanayi Tare Dashi Kafin yace"Harda shima Yayan nata Dake kaiku makaranta..?
Inteesar tace"Harda Abba da Anty Safiya suka fita..Ya Imran kadai na Tarar a gidan..!
Daddy zai yi mgana Ya Basheer Dake Bangaran Direba ya Leko yana Fadin"Plz Daddy..Lokaci fa yatafi..!
Daddy yayi ajiyar Zuciya kafin ya Kalli Inteesar yana Fadin"Shikenan ki gaishesu in sun dawo..Shiga Mota sai mu sauke ku mu wuce..!
Yafada yana kara Bin gidan da kallo kamar kada ya tafi Zuciyarsa Tana jansa Tana jin kamar akwai wani abu mai Muhimmanci da in ya Tafi Daga Wajen zai rasa,Sai dai bai da wata Masaniya kan haka,Komawa Gidan gaba yayi ya Zauna yayinda Inteesar ta shiga Gidan baya inda Sagir yake.
Ba wanda ya kara mgana har suka kariso kofar Gidansu Sagir aka sauke su Inteesar sai da Idanuwanta suka cika da kwallah Lokacin Datake Dagama su Daddy Hannu har sai da Motarsu ta Kule ta Daina ganinta kana ta Juya Zata koma Cikin gida.
Sagir ya Kirata ta Juyo Tana kallonsa Kai Tsaye yace"Kinga Imu..?
Kai ta gyadamai batare da tayi mgana ba ganin yanayinta yasa bai kara magana ba Har ta Juya ta Shige gida.
Koda ta Shiga Mama ta Zagaya Makewayi Daki ta shige ta Fada Kan gado Cike da kewar gida Tana nan kwance Mama ta Shigo Tana Tambayanta lafiya ta ganta Kwance tace Lafiyalau nan take Fadama Maman bataji Dadi ba Daddy basu hadu da Munari sun gaisa ba Har gidan Taje basa nan..
Mama tace kada ta Damu akwai wani Lokacin zasu hadu su gaisa Tunda ana tare da juna.
Sai bayan Mangriba Munari ta Kira Inteesar tana bata Hakuri Dawowarsu kenan Salla kadai tayi ta Duba wayarta Sai taga Kiranta nan Inteesar ke gayamata Har gidan tazo bata Isketa ba Daddy ne yazo zai Wuce yace a Kirata su gaisa Munari ta Ciji yatsa tace ta zata bazasu Dade bane,Sai gasu sune Har gidan Zoo Shiyasa suka Dade basu Dawo ba Inteesar tace bakomai akwai gaba Kamar yadda Mama tace Daganan sukayi Sallama Akan sai Gobe In Munarin ta Biyo mata Tafiya makaranta.
Washegari Monday da Safe 8am suke da Lecture 7:30am suka shirya Ya Yusuf ya ijiyesu Kafin ya wuce Wajen aiki Har shi sai da Inteesar ta Fadamai Zuwan Daddy su gaisa jiya basa nan Shima bai ji Dadi ba yace sai dai Wani Lokacin da yardan Allah zasu Hadu su gaisa.
Ranar da Wuri suka Fito Daga Cikin makarantar,Shiyasa Inteesar taja Munari zuwa Gida ta Diban mata Dambun nama da kayan Snaks din tace ita dasu Abba Munari nata Godiya sai da Tayi Sallar La"asar suka ci abinci kana Inteesar ta Fito Zata Rakata Zuwa Gida sukayi Kicibis da Imran da Sagir akofar gidansu Imran din suna mgana,Da suka gansu Munari tafi Tsorata Domin jikinta sai Rawa yake yi Inteesar kuma mamaki take na yau Kadai da Tataba ganinsa baya Shan Sigari.
Yana Sanye Cikin Riga da wando,Rigar mai ruwan kasa Mai gajeren hannu sai Wandon baki ne Wanda yadan Kamasa ta kasa Kafarsa Sanye Cikin Wani Tattausan Takalmi,Kamar Koda Yaushe Hannayensa Zube cikin Aljihunsa.
Sagir kuma yana Gefensa Har Kafadunsu na Dukan na Juna duk da Imran din ya Fisa Girman jiki da Tsawo.
Tundaga Nesa ya hangesu sai da gabansa ya Fadi Daya ganta yarinyar nan Kamar Aljanna Jiya wuni yayi Tunaninta Haka kurum baisan Dalili ba Fuskarta na yawan Gilmamai acikin Idanuwansa.
Yau a tsarinsa bai ma yi niyyar Leko waje ba,ko Sallah acikin Dakinsa ya Dinga yi shi kadai yau din yana Son ya Zauna shi kadai baya son yaga wani Wanin kuma bazai gansa ba sai da Zuwan Sagir yasa Dole ya Fito,Har ciki ya shiga suka gaisa da Abba da Anty Safiya bayan ya Kirasa har ya gaji bai Daga ba Shi ya Bisa Har cikin Dakinsa ya jawosa nan waje yana Tambayansa Laifin me yayi mai ya Daukemai kafa..? Bai ma kai ga bashi amsan bane ya Hangi Tahowar Munari da Inteesar.
Ganin inda ya Raja"a Kallo ne yasa Sagir maida Hankalinsa wajen sai ya Ci Karo da Munari da Inteesar.
Karisowa sukayi gabansu Munari ce Cikin Rawar murya ta fara Fadin"Sannun ku..Ina yini Ya Imran..?Ya sagir ina yini..?
Tafada Cikin rawar Baki Tana kara Damke Jakarta Dakyau tana Jiran Imran yace kyat ta Zura da gudu Daman Ledan da Inteesar ta sakamata Su Dambun Naman yana Hannunta ne.
Imran kallo Daya yayi ma Munari ya gauda kai bai kara Kallonta ba kansa na kasa ya Kurama yan Yatsun kafar Inteesar Kallo da sukayi kyau Cikin wani Falt din jan Takalmi yatsun Dogaye ne suna da Haske sai jan Lallen data Cike Fararan kumbunanta dasu bai Taba Tsayama ya Kare ma Fuskar Mace kallo ba Ballatana Kafarta sai gashi yau ya shagala da Kallon Kyakyawan yatsun kafafun Inteesar Batare daya sani ba sai dai yaji Zuciyarsa na son Kallonsu Sun Burgesa sosai.
Sagir ne kadai ya amsa yana Tambayansu Karatu sukace Alhamdulillah Inteesar kuwa Ina yini Ya Sagir..! kadai tace aranta tace bazan gaisheka ba ka Dizgani Kanwarka ma bata Isheka kallo ba Ballatana ni Maras Mutumci mai shan Taba kawai Duk aranta take wannan Zencen cikin Takaicinsa.
Ita ta kama Hannun Munari suka Buga Kofar get din Iro ya leko ganin sune ya Bude musu suka Shiga Da Karamin kallon Gefen Fuska Imran ya Bisu dashi kafin ya Sauke ajiyar rai yana cije baki yace"Yarinyar nan bata kunya naga alama..!
Sagir ya Kallesa Cikin mamaki Kafin yace"Wata Yarinya..?
Ido nacikin ido Imran ya Kallesa kafin yace"Wata yarinya kake Tambaya..?kanwaka din nan wacce take zaune agidanku mana..!
Sagir ya karbe da cewa"Da tayi maka mene..!?
Imran yace"Bata gaisheni ba.ko kana Nufin Abunda tayi mai kyau ne. ?
Sagir ya saki karamin Tsaki kafin yace"Eh mai kyau ne..Saboda Halinka...Agabanta Munari ta gaishemu kaki amsawa kayi kamar ma baka ganta ba..kana Tunanin ko Nice zan gaisheka bayan agaban idona naga abunda kayi ma kanwarka..?
Imran ya Dakuna Fuska kafin yace"Wannan ba Hujja bane..Gaisuwanta Dabam na Munari Dabam..!.
Sagir yace"Duka Dayane Mallam..Kai dai kawai kace ka Tsani yarinyar nan Shiyasa naga ba tun yau ba kake Neman kowani Laifi ka goga mata..!
Tsaki Imran ya Saki kafin yace"Eh na Tsaneta ko zaka Daukan mata mataki ne Ubanta..?
Yafada yana Jefan Sagir da kallon kada ka karamin wannan mganar Banzar..
Sagir yace"Inafa..Ai Allah ne yakadai zai iya mganinka bani ba..!
Imran ya Murmusa kafin yace"Bettter Daka Fahinci hakan..Mallam zan shiga Ciki in baka da tacewa..?
Sagir yace"Yaushe zaka Dawo shago..?ko kuwa gabar da kake yi dani baka Saki bane...?
Imran ya Dakuna Fuska kafin yace"Gaba..? Ni Imran bana gaba da Wani ko wata..Sai dai in nagaji da Zama da Mutum nayi nesa dashi..Kai im zan yi gaba dakai Gaba da gaba Zan Tareka nace maka baka bani..Tunda kai ba Ubangijina bane Bana Fatan Watarana naji tsorom wata Hallita ba Allah na ba..!
Ya cigaba da Fadin"Kuma ba Daina zuwa shagon ka nayi ba saboda kamun wani abu ba..Kawai ina Bukatar Kadaici ne..In na Dawo Daidai zaka ganni kai dai ka Girma ammh kullum kana Dawowa kamar wani yaro..saboda cin kasa!
Ya karishe Fada yana Kara Hade rai Baki Sagir ya saki kafin yace"Nine wanda ke cin kasan..?
Imran ya juya ya fara Tafiya yana Fadin"To da waye..? Ya fada yana yar Dariya Kafin ya shige gida ya bar Sagir nan tsaye yana Binsa da kallo Tsaki yaja yana Fadin ba Laifinka bane nawa ne da nake binka kana gayamin mganar banza..daganan ya Juya Fuu ya Fara Tafiya aransa yana Fadin bazai Kara Neman Imran ba In ya Nemesa Shikenan in kuma bai Nemesa ba He don"t Care.

Imran na Sawo kansa Cikin Falon suka Ci mummunar karo da Inteesar Da Sai da Kafadarsa ta Daki kanta Tunda ya Fita Tsawo,bata san dashi ba da Karfinta ta Jefa jikinta Munari na Binta zata Rakata Haraban gidan,Kafadarsa ba kadan bace kuma Shima da Sakin jikinsa ya Sawo kansa Falon baisan da ita ba Shiyasa ya Bangajeta Bangazan da ta kasa Tsayuwa da Kafafunta tatafi Luu zata Fadi ta Gefenta da Wani Zafin Nama ya Saka Lallausan Igarman Hannayensa ya Tarairayota ta Fado kan Kirjinsa da karfinsa Har Karan Hancinta da Kirjinta suna Dukan Faffadan Kirjinsa.
Munari Dake tsaye har ta Sadakar Inteesar ta gama shan kasa,sai kuma ta kame gefe Daya tana kallon Inteesar Rike hannun Ya Imran hannayensa Zagaye da Kugunta Yayi mata Riko sosai.
Inteesar abun ya Faru cikin Lokaci kadan ne shiyasa bazata iya Tantance komai ba,sai da taji wani Ingarman Namiji mai Zatin jarumta yayi Saurin Tareta kuma ya Tallafota zuwa jikinsa Maida Nunfashi take sama sama Inteesar akwai tsoro ta Tsorata da Fadin da Zatayi yasa ta Saka Hannayenta Guda Biyu ta Rike Rigar Imran dashi Idanuwanta a Lumshe Tana maida Numfashi.
Imran kuwa wani Sanyi yaji yana Shiga Jikinsa da Zuciyarsa wanda Tunda yazo Duniya bai taba jiba ba..Kirjinsa Duka kawai yake yana Fat..! Fat..! Da karfi kamar wanda yaga wani abu tsoro..
Fuskar Inteesar ya Kurama ido Wacce ke kan kirjinsa Tana Rirrike dashi Da karfi,Kallonta yake kamar yana son ya Haddacr komai na Fuskarta Kada ta bacemai,Yana jin kamar Rikonta wani Salama ne da Farinciki awajensa kamar in ya Saketa zai Tagayyara ko zai Lalace yana jinta acikin jikinsa kamar Wani gafara ne Daga Allah.
Abba ya Bude Kofar Dakinsa ya Fito Dauke da karamin Littafin azkar Jikinsa Sanye da Wata Farar shadda Dinkin Riga da wando har da Hula.
Ganin Imran da Inteesar a wannan yanayin sai da gabansa ya Fadi Cikin Azama ya Karisa Cikin Falon yana Fadin"Kai Imran Lafiyar kuwa ka Rike Diyar mutane..,?
Yafada da dan Karfi wanda ya Dawo dasu Dukkansu Cikin Hankalinsu.
Inteesar jin muryan Abba asama yasa ta Dago Tana kallon Fuskar wanda ke Rike da ita ai Tana ganin Imran taji wani Yam! acikin jikinta da Sauri ta Kwace Jikinta Ta mtsa baya tana Maida Numfashi
Shi kuwa Daman jikinsa ba Karfi ga Kasalan data Rufeshi shiyasa Inteesar ta iya kwace Jikinta..
Da Lumsassun idanuwansa ya Kalleta Kafin ya juya ya kalli Abba batare da yayi mgana ba ya Fara tafiya zai shiga Dakinsa,Abba ya Daga baki yace"Kai IMRAN ya ka nan ya ina maka mgana kana wucewa..?
Yafada cikin bacin rai baya Fatan ace Ya Doke yar Mutane ne Juyowa yayi yana jin mganar tamai nauyin ya Fada Munari ce tayi Saurin cewa"Abba Karo sukayi da Intee...Basu ga juna ba Shine zata Fado ya Rikota..!.
Ajiyar rai Abba ya Sauke Kafin ya Maida kallonsa kan Inteesar Dake Jin wani iri acikin jikinta yace"Sannu Baki dai ji ciwo ba ko..?
Inteesar Dakyar ta iya Bude baki tace"A"a Abba..Sai da safe..!
Tafada tana Juyawa,ta gefen ido Take kallon Imran yana Shiga Dakinsa Abba yanata ta gaida Mama,Ta fice Munari ta Bita abaya suna Fitowa Munari ta Riko Inteesar tana Fadin"Kai Besty kinga yadda kikayi ajikin Ya Imu..? Na Rantse har ga Allah kunmin kyau kamar a Indian Film din nan irin Jarumar zata Fadi Jarumin yayi AzAman rikota ta Fadomai..!
Ta Kariashe Fada tana Dariya Inteesar ta Harareta Lokaci Daya tana Tuno yanayin data Fada kan kirjinsa sai da jikinta ya amsa domin Bayan Muharramanta wani namiji bai Taba koda taba Hannunta ba sai yau wanda Komai ya Faru bisa Rashin sani.
Ganin taki mgana yasa Munari ta Cigaba da Fadin"Nayi mamakin Ya Imu yau..? Kun bala"in dacewa kamar ace ku din Couple ne..!
Da sauri Inteesar tace"Da wa..?Allah ya Tsareni baki man fatan kwarai ba..Indai na auran wannan Muradadden yayan naki ne..!
Munari zata kara mgana Inteesar ta Dakatar da ita da Fadin"Kinga ni kyaleni..Nagode Daya Taimakeni Daga Faduwa kawai..Sai da safe ki koma gida malama..!
Munari ta kada kai Tana Fadin"Daga waasa..? Allah baki Hakuri..!
Inteesar ko kulata batayi ba ta wuce Munari ta Bita da kallon Cikin Rashin jin Dadin yadda ta Bata mata rai ita Har ga Allah waasa take mata kada kai Tayi ta koma Cikin gida Tana Fadin gobe zata bama Inteesar hakuri banda Abunta Ya Imu ai ba Aure ma yake da Ra"ayin yi ba Ballatana wannan mganar ta Dameta.
Inteesar har takai gida ta rasa yanayinta Kowani Dakika abunda ya Faru ne yake Dawowa mata Kuryan Daki ta Shige ta Fada kan gado ko Hijabin Jikinta bata iya Cirewa ba,gabanta sai Fadi yake Data Runtse ido sai ta ganta Rike da Imran Kirjinta yana Saman kirjinsa Runtse ido Tayi a Fili ta Furta"Shikenan Mara Mutuncin nan ya gama dani..!
Take fada tana kara jin wani Takaici Da ta Tuna abun sai ta Saki Tsaki kuma abun yaki bace mata acikin Ranta da Zuciyarta Har Mama Sai da ta Tambayeta ko Lafiya jin yadda Lokaci Bayan Lokaci take sakin Tsaki Sai ta sanu kanta da Boye abunda ya Faru tace bakomai.
Bangaran Imran kuwa ya kasa Gane Yanayinsa In ya Runtse ido Sai yaji Fadowar Inteesar a Kirjinsa sai gabansa ya amsa Yana jin alokacin Yanayinsa ya sauya kamar bashi ba yana Tuna yadda ya Saka Hannayensa ya Zagaye kugunta dashi,yana kwance da Silasin Dare ya kasa barci Ya Busa Sigarin nasa Ammh duk a banza Yana kwance yana Tunani kafin ya Murmusa afili ya Furta"Kugun nata ma D'An karami ne kamar yadda take karama da ita..!
Yafada yana Bin hannuwansa Daya Daga da kallo.
Kafin ya kara Juyawa yana Yin Filo da Hannayensa yace"Sai Rashin kunya kuma..!
Yafada shi kadai kuma yayi Mirmishi kamar wanda ya zare,Rufe Manyan Idanuwansa yayi Yana Fatan barci ya Daukesa sai mai gabadaya Fuskar Inteesar ne take mai Hazo da Gilmawa acikin Rufewar idanuwansa,Sai Mirgina yake yi yakasa Barci in ya Bude Idanun

Please Login or Register in order to submit comment