Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta danna mai Nomba busy,ido ya waro yana bin wayar da kallo Zuciyarsa na Zafi kamar Shine Inteesar Zata kashe ma Waya..?Shi Imran..?ko abaya ba wacce ta isa ballatana ma yanzu Dayake jin kansa Daidai da kugun kowani Dan iska Shiyasa Tun Farko baya harkan mata Saboda Raini,Inteesar ta gama Rainasa Wato saboda taga yana mata Dariya Shine Zata Kashemai waya ga Dan iska ta samu ko..? Ko ma ace yaje Wajen Sajidan ne da gaske ta isa ta Hanashi zuwa ne?Shifa Namiji ne kuma yaya yake gareta ya bata Shekaru ba iyaka in Haihuwar kaji ne zai iya Haifarta Wlh shi Namiji ne Mijin Mace Hudu wata mace bata isa ta Zauna tana Raina mai wayau ba Ko Wacece ita kuwa,Ahaka ne Sagir ke cewa yana sonta..?aikin banza in taji ma wannan mganar sai Rainin nata ma yayi yawa shifa ba macen da Zata Zauna yana bata Hakuri yana Lallashinta yana da abubuwan yi masu Tarin muhimmanci da suka fi bata Lokacinsa kan Shirme Duk yadda Ransa ke Tafasa haka ya kanne ya Cije yayi ma kansa alkawarin Fita Sabgarta Domin Tsira da Mutuncinsa sai dai yadda yake ji game da ita ya Kasheshi daya zauna yana Fuskarta Raini da wannan Wulakanci a wajen yarinyar da bata wuce yar Cikinsa ba badai shi tama haka ba ko..? uhm Fushi Ta Cigaba da yi daga yau har Mahadi ya bayyana yafita Taurin kai da Zuciya.
Duk yadda yaso barci ya Kwasheshi a wannan Daran ya kasa,sai da ya tashi Sauran Sigarinsa Daya siya a Dukku,Tun Da yaje bai wuce sau biyu yasha Sigari ba yana da Sauranta ita ya Dauko ya Dinga ban kama Cikinsa Har sai da yaji Zuciyarsa ta Cunkushe Kirjinsa da Kansa sun yi masa Nauyi kana ya Hakura ya koma ya kwanta yana Sauke Numfashi Daya bayan Daya.
Ya Dade bai yi barci ba sai chan Dayayi Ruf da ciki duk da ba kyau ammh bai da Zabi,yayi Filo da Hannayensa saman Fuska sai Lokacin ya samu barci yaso ma ya makara ba Domin Abba ya Bugamai Kofa ba sanda Zasu masallaci shi da Yusuf Dakyar ya iya tashi da jan kafa ya shiga Tiolet,in ya Tsaya yin wanka zai Rasa Salla Shiyasa ya dauro alwala yabi bayan su Abba zuwa masallaci Allah ya Taimakesa an Tada Sallar ammh ba"a kai ga Ruku"u ba,Bayan an Idar da Sallar ya Dade yana addu"an Nasara a Rayuwarsa yana addu"an Samun wannan aikin Duk da Manaja Tunde ya bashi Tabbacin ammh bazai kwanta da hakan ba ayanzu yana Bukatar aikin Ko domin cikama Daada alkawarinta,Uwa uba kuma Lokaci Yayi da komai zai Sauya ko domin ya maida ma wasu martani irin su Mami Asma"u.
Sai Bakwai Saura ya baro Masallacin zuwa Gida yana zuwa wanka yayi a gurguje baya so yayi african Time Daman chan ba Tsarinsa bane bayan ya Fito ya shafa lotion dinsa ya Taje Sumar kansa bayan ya shafamata Mai gyaran gashi,Wardrope dinsa ya Bude yana Duba Jerin suit dinsa Dayake dasu wanda ya Taho dasu Daga Lagos bai Taba sakasu anan garin ba barshi da Saka Saukakun kaya.
Suit din na kamfanin DKNY ne sai na kamfanin Armani suna da kyau da Quality shiyasa Har Lokacin basu yi komai ba suna Sagale cikin Hanger wasu ma Sabbi ne suna da Leda ajikinsu bai Taba sakawa ba.
Daya Daga Ciki ya ciro na kamfanin Armani Kalan Black and White ya Dauko Daya Daga Tektie dinsa Baki,Lokacin yana Lagos gabadaya kayansa Suit ne saboda yanayin aikinsa Wlh bamai nuna mai iya saka kaya a Tsuke wannan yana ma Daga Cikin Tsarin aikinsu
Cikin Lokaci yayi shirinsa Woww..Nace Lokacin da ya Tsaya gaban Madubi yana Daura Tek tie dinsa,ya Hade har ya gaji da Haduwa Cikar Zatinsa ya kara bayyana kamar wani babban Mutum,baza kayi mai kallo Daya kace Imran ne mai Busa Hayaki ba sai ka karemai kallo kafin ka iya Tantace shine ko ba shi bane.?
Agogon Azurfa ya sanya atsitsiyan Hannunsa na Hagu,silba ne yana Kyalli,Yana da irin su Dadama sai dai baya amfani dasu,bai cika damuwa da sai Rayuwarsa ta dawo kamar baya ba ammh a yau kam gabar ta bayyana Dolene ya Dawo Imran dinsa in yana son Cimma Burinsa.
Takalminsa Rufaffa ne na Fatar Daminsa baki shima suit din baka ce haka ma wandon baki ne sai Rigar Ciki ne Fara,Imran mai kyau ne kuma shidin Dan baiwa ne Tuni ya Fito a ma"aikacin bankinsa da ba wanda ya isa ya Kallesa da kallon Raini Karamar Wayarsa ya Dauka ya Saka Cikin Aljihu yanzu bashi da komai sai dai in yaje komai ya kamkama akwai Bukatar ya mallaki wasu abubuwa kamar su Laptop,da waya saboda aikinsu baya Tafiya sai da haka Lokacin Laptop dinsa ma bazai iya Tuna ina isalinta ba,ana ta Rai wake ta abun Duniya alokacin.
Key din Mashin dinsa ya Dauka saboda shi yake dashi alokacin ya Fito bayan ya Fesa Saukkan Turaransa mai Dadin kamshi na azzaro Visit.
Dukkansu suna kan Dinning suna Breakfast,ya Fito Cikin Shirinsa Gabadayansu baki suka saki da Hanci suna kallonsa.
Inteesar kuwa kamar Idanuwanta Zasu Fado Tunani take yi anya wannan Imran ne ko mai kama dashi..?gabadaya zuciyarta wani Tsalle take yi waje Daya dashi ta kwana acikin Ranta Kiran da yayi mata Jiya tazo Dauka sai bata sani ba ta kashe Kiran batayi Tunanin bazai kara Kira ba Domin har Ga Allah ta Saki Fushin taga alamar ita ce Zata sha Wahala daga baya daga ga Shuru bai Kara Kira ba sai ta Kirashi Sharrin Network yasa bata Sameshi ba.
Yadda ta kafeshi da ido sai da gabansa ya Fadi ammh ya Kauda kai bai yarda ma ya kara kallonta,Daga tsayen bai karisa ba ya kalli Abba Dake kallonsa Cikin Mirmishi da Alfahari yace"Gud mrning Abba..Zan je wani waje bazan Dade ba zan dawo..!
Abba kai kawai ya gyada Farinciki yasa ya kasa mgana ganin Imran cikin wannan Shigar ya Tunamai da abubuwa da dama ashekarun baya Lokacin yana ainihin Imran dinsa mai ci da guminsa,Yana Fatan wannan Fitar ta saka na alheri ne yasa Addu'arsa ne Allah ya amsa Imran zai sauya zai dawo Imran din Dayake so kuma yake Fata.
Ya Yusuf ne ya ijiye mug din Tea din Dake Hannunaa yana Fadin"Woww..Long Time Imran Abubakar Malami..!
Yafada yana bayyana Mirmishinsa da kuma bayyana irin kyan Zatin da kanin nasa yayi yau daya Dade bai yi wannan Shigar ba.
Safiya da Munari suma ayyanawa kawai suke acikin ransu ko cikin Dubbam Maza Imran na Musamman ne banda Inteesar data riga ta zama gatanan ne azaune saboda wani Rauni Dataji ya kamata ganin yadda Imran din ya nuna bama ya son ganinta din

Daga Yusuf har Abba basu matsa da sai sun ji Ina zai je ba Tunda suka ga bai Fada musu ba bayanzu yake son su sani ba Har ya fice suna binsa da Allah ya kiyaye da Fatan Nasara da Sa"a,yana Fita Daga Haraban gidan Wayar Khalil ta shigomai Dakatawa yayi Daga Hawa mashin din nasa ya amsa kiran mgana dai sukayi kan aikinsu Inda Imran din ya Fadamai yanzu ya fito zai isa Bankin sun Rabu kan Duk abunda ke nan Imran din zai Kirasa ya Fadamai haka ya Hau mashin dinsa ya fice Daga Haraban Gida acikin Ransa yana jin ya Zama Dole ya sauya ko saboda Mutanen da suka Damu da ganin Cigabarsa irin su Khalil da Sagir.
Karfe 8:00am tayi ma Imran a office din Manager Turanci ne kadai ke tashi acikin wajen su biyu ne kadai Sai karan iskan AC,Manager din Bahaushe ne Sulaiman Ishaq Dawanau,Sai Imran Dake zaune kan wata Kujera Dake kallonsa gabansu wani katon Tebur ne baki mai Sheke sai ruwa da lemo,Dake gaban Kowanensu.
Tattauna sukayi sosai Duk ba Interview bane sai dai Sulaiman Ishaq ya Karu da abubuwa sosai da D'an karamin Tattaunar da sukayi da Imran ta Tsawon awa Daya,ya Fahimci Abubuwa Dadama,ciki harda Sanin Tarin Ilimin Imran da baiwarsa da Sanin Abunda ya karanta din ba Shakka Lokacin da yayi aiki an samu Zakaran ma"aikaci ya Duba Duka bayanansa da Mr Tunde ya Turo musu ta Email dinsu mganace Daga Sama ba wani bata Lokaci Bayan sun gama Tattaunawa Sulaiman ya Mike yana bama Imran hamnu sukayi musabaha bayan ya Zana sunansa a Mtsayin assistan Manager na Branch din Gt bank din Dayake ciki Suna maraba dashi da ko a gobe ne zai iya Fara aiki Office dinsa yana Ready.
Imran Dayaji haka cikin karfin gwiwa ya basa Hannu suka jinjina bakinsa nata Fadin"Thank u sir..Thank Very Much..!
Sulaiman na Mirmishi yace"U are Most Wlcm Mr Imran..!
Imran bai Tsaya bata ma kansa Lokaci ba yace ko yau zai iya Fara aikinsa Sulaiman Ishaq yaji Dadin haka yayi mai Jagora zuwa Cikin bankin yana nunamai ko"ina bayan ya sanar da Taron meeting lokacin da aka tashi break na Lunsh da masu yin Sallah yana so ya gabatar da Imran a Mtsayin mataimakinsa a wannan wajen mai kula da duka Shashen Dake Cikin Bankin.
Kayattacen Office din Imran na Hawa na Uku ne Tunda Buliding din bankin Babba ne sosai,Office ne babba mai Dauke da glass Daya Zagaye wajen,ana ganin na ciki na ciki ma yana ganin na Waje sai Tebur baki daya kusa Cika Office din,sai kujerarsa Baka mai mukami sai wasu Dake Fuskarta guda biyu wannan na karban baki ne akwai Laptop na aiki Sabuwa awajen komai ma sabo ne Tunda assitan din Dake Wajen karin girma ya samu zuwa Manager na Brarch din su Dake Abuja Shiyasa aka Daukesa adaidai Lokacin kuma sai ga Imran shiyasa Faduwa taxo Daidai da Zama,harda karamin Frige akwai da kuma Tibin bango karami sai AC masu sanyaya Waje guda uku Daga gaban Teburin an Dora wani karamin Katako mai kyalli Wato IMRAN ABUBAKAR MALAMI(assitance Manager) da sunansa makale ajiki kamar yadda suka sanya komai an Riga an Tsara kuma an gamashi.
Nan Sulaiman ya barsa bayan sun kara shan Hannu da juna Cike da Farimcikin da Imran ya Dade bai jisa a Ciki ba ya tsinci kansa Lokacin Daya ambaci sunan Allah ya Zauna saman kujerarsa Idanuwansa suka cika da kwallah aikin Banki Burinsa ne kuma Muradinsa Shiyasa wani Rauni ya bayyanamai da kewa mai Tsananin Dayaji kamar ya Fitar da kwallah.
Bai Fara komai ba sai da ya Fito da Wayarsa Abba ya fara Turama Sako..

*Alhamdullillah Imran is back..Am now a Assitance Manager GTB branch Kano..*

Bayan Abba haka yayi Copying ya Turama Sagir da khalil sune ma Masoyansa ne kafin ya kashe Wayar gabadaya yasan zasu kirasa shi kuma ayau Dayake jin kansa wani iri so yake yayi aikin Daya Dade yana kewa ko Hakan zai Ragemai jin Dadin Dayake Ciki,Har ya kashe wayar sai ya Tuna da Mr Tunde da Sauri ya kunna kamar yana Jira sai ga Kiransa yana Dagaawa ya faramai Congratulation,
Yana Tayashi Murna ya amsa mai Cikin Sakin Fuska lokaci Daya yana mai Godiya,basu wani jima suna mgana ba suka yanke kiran suna gama Wayar ya kara kashe wayar ya maida ita aljihu yajawo Computer gabansa ya kunnata komai da komai da Duk wasu bayanai da zai Bukata yana Ciki Tuni ya fara aiki ba kama Hannun yaro yanayi wani Annuri yana Fita daga Cikin Ransa Har zuwa Saman kyakyawan Fuskarsa.
Abba ne ya fara ganin Sakon na Imran Lokacin yana Falo Inteesar da Munari sun fito suna shirin Tafiya makaranta yau bada Safe suke da Lectures ba.
Abba daya ga sakon Sai da ya Daidai Gabansa ya Duka yayi Sujjada ya yi ma Allah godiya da Kirari sai da ya Dago Farinciki yasa sai da yayi kwalla nan yake Fadama su Inteesar abunda ya Faru Munari ta Daka Tsalle da Ihu Lokaci Daya ta Rumgume Abba ihun ne ya Fito da Anty Safiya Inteesar baki har kunne,zuciyarta Dake Cikin Damuwa tayi Fal da Farincikin jin Imran dinta ya Zama kamar yadda Kowa ke Bukata Allah Sarki
Munari ta Rumgume Inteesar da Anty Safiya Tana Murna ita kanta Safiyar tayi murna kwarai Tana ta saka albarka Lalle Imran wato shi dai na Dabam ne Komai sai dai aji kawai,Yusuf ne ya kira Abba ya Dauka yana Murnan gayamai Sakon da Imran ya Turomai Abba yace mai shima ya Turomai Farincikin su yaki Boyuwa Abba nata Fadin Allah nagode maka Allah ka kara Shiryamin wannan yaron ka kara Mishi Natsuwa Allah ka yayemai wannan Zuciyar dayake Fama da ita.
Haka chan ma Khalil da Sagir suke Cikin wannan Farincikin sannan dukkansu sun kirashi wayarsa tana Kashe aiki gamai kareka kenan
Sagir haka ya kira Mama yana Fadamata itama tana ta saka albarka Inteesar suna Hanyar zuwa makaranta ta Kira Daddy ta Fadamai yace yanzu suka gama waya da Abba ya Fadamai sun dan jima suna mgana inda yake Fadamata shima Abba Saura Kadan a kirashi Domin Manya Daga sama a gwannati suna Duba lamarin.
Bayan nan ta Kira wayar Imran a kashe sai ta Turamai Sako.

*You had the passion, and you had an ambition. You truly deserved every bit of the success you have achieved. Congratulations Ya Imu..*

Ta turamai Tana Mirmishi ita kadai Munari na Lura da ita sai Mirmishi take yi bata dai ce mata komai ba Tana jiran Wata rana ranar da mganar Zata shigo ko kuma ita Inteesar din ta tareta da mganar Zata Fito ta gayamata cewa Son ya imu take yi bata sani ba.

Imran bai tashi daga wajen aiki ba sai 6pm,Da suka Fita lunch da karfe 1pm Sulaiman Ishaq ya hada karamin Taro inda ya gabatar da sabon Assistan Manger wato mataimakinsa a wannan Reshen bankin ya bada kadan Daga Cikin Tarihin Imran da yarda yazo yayi aiki a Branch din su na Lagos da irin kokarin da yayi Domin duk sanda Banki Zata je Seminar shi ake Turawa kuma zai je yayi kamar yadda ya kamata Cikin Shekaru da yayi yana aiki ya jawo ma Bankin Gt Daukaka da Cigaba sosai jin Dadin haka yake wannam Mtsayin ko ba"a Fada ba Daga ganin Imran bazai yi wasa ba Yanayinsa da Cikar Zatinsa kadai ya Isa Shaida kuma Daga ganinsa He is Ready abunda ake Fada akansa duka ba karya bane,Ya gaggaisa da ma"ikata mazan dake karkashinsa,mata kuma bai yarda yayi hannu da kowata Mace ba bai ma Saki Fuska ba Fuskarnsn dai gatanan ne kadahan kadahan.
Da aka tashi Kowa na shiga Tsararriyar Motarsa ammh Mataimakin Manager ya Hau Mashinsa bai ji Wani kunya ba ya Wuce gida Sulaiman Ishaq ya gansa yayi Wani Tunani acikin Ransa Kafin ya Shiga Motarsa ya Fice Daga Bulding din bank din.
Koda ya koma gida irin Murnan Da Abba da yusuf sukayi bazai misaltu ba,Dukkansu suka Rumgumeshi suna Murna Anty Safiya da Inteesar da Munari da Sagir suna gefe suna Tafi Lokaci Daya suna Fadin Congaratulation Dear.
Mamaki ya kamasa ganin party fa suka Shirya kwarya kwarya wannan kuma Shawaran Intee ne suna makaranta Tunanin ya Fado mata ta Gayama Munari itama tayi na"am Basu Dade a makaranta ba,lecture daya sukayi suka Dawo gida suka Fadama Anty Safiya ita kuma ta shige gaba ita ta Kira Yusuf ta tafadamai yce Tabbas wannan al"amarin ya Chanchanci ayi mai Party,Abba ma Dayaji bai hana ba,Inteesar ita ta Kira Sagir ta gayamai sunyi Girke girke da Lemuka Ya Yusuf kuma bayan ya tashi Daga wajen aiki ya biya Shoprite ya siyo Sweet ba adadi,Safiya kuma da Taimakon su Intee suka Hada Tsararran cake din Dake Dauke da CONGRATULATION IMRAN..!
Basu barsa ya shiga Dakinsa ba suka jasa Saman Dining inda suka Jera komai,Duk da bai saki Fuska sosai ba ammh kana kallonsa Zaka san yaji Dadi matuka Da Hannun Abba dana Yusuf ya hada ya yanka Cake din ya Gutsira ya bama Abba,Abba ya karba bai ci ba ya sakamai a baki Sai ga Taruwar Hawaye Imran yaji Rauninsa ya bayyana ya Rumgume Abba,Abba ya Rikesa cikin Farinciki yana Fadin"Congatulatiom My son..U Deserve everthing..Allah ya bada sa"a Allah yayi maka albarka..!
Su Anty Safiya nata amsawa da Ameen Ameen Yusuf ma ya Debo zai kai bakinsa sai ya rike hannunsa suka Hada Hannu suka kai bakin Yusuf atare kafin su dawo dashi bakin Imran Kafadansa Yusuf yadan Bubbuga yana Fadin"Bravo alaika...Allah yayi jagora dan kanina.!
Dakuna Fuska yayi yama kallon Abba yce"Abba Abeg tell him bafa wani Shekaru ya bani ba..!
Gabadaya Dariya aka saka kafin Sagir ya Yanko katon cake ya Dunfari bakin Imran baya yaja yana dan Fiddo ido waje bai gama mamaki ba Sagir ya Turamai abaki har wajen Hanci Da kumatunsa dama dama da cake Dariya aka sanya gabadaya ganin yadda ya wani Tattare Fuska kamar an yabamai Kashi.
Sagir yace"Congratulation Abokina..Allah ya tayaka riko am so Happy for u..!
Wata uwar Harara ya Wurgamai yana Fadin"Kaifa banza ne tsiyana Dakai kana Girma kana cin kasa..Ya kamata ka Rika gane bambamcin Boy and Man dis abunda kayi is a Childness..!
Yafada yana nuna Bakinsa cikin kyamkyama shifa bai son Abu ya Cika Zak'i shiyasa baya mu"alama da Chaculate sai Dariya su Abba kemai Munari da Safiya suka cemai Congaratilation ya amsa banda Inteeaar da kallo Daya yayi mata ya Kauda kai duk da tayimai kyau a ido Bai Hanashi nuna mata kwanjinsa ba Tayi Shigar bakar abaya ne sai tayi Rolling da karamin Vail fari Fuskarta ba kwalliya sai dai ta shafa ma karamin Bakinta Jan jan baki,Tayi kyau matuka a acikin Idanuwansa ammh bai bayyana mata ba,Dayake ana ta Murna ne ba wanda ya kula da bai amsa mata ba,ya sulale ya shige Dakinsa sukuma suka Cigaba da Shagalinsu Inteesar duk sai taji Gwiwanta yayi sanyi itafa ta Saki wannan Fushin nata Tuni Munari ce ta katse mata Tunani bayan ta Tura mata Cake a baki Har akan Hancinta Sai ta Bita itama ta gutsiro Cake din ta Bita dashi suka Fara guje gujen suna Dariya Abba na gefe yana kallonsu Cikin Jin Dadi da godiyar Allah.
Sagir dai Daki yabi Imran yaga ya shiga wanka sai da ya jirasa ya Fito ya Dinga mai hira yana amsa mai Sama sama Saukakkun kaya ya saka karamin Wando da Riga Fita Falo yayi yaga Inteesar da munari nata Hotuna Harda Anty Safiya baima bi ta kansu ba,ya fada Kitchen ya Dauko Ruwa ya Hado Tea a karamin Mug wajen Abba da Ya yusuf ya nufa suna zaune kan Dining din Sagir ma nan ya Fito ya samesa suka fara Hira ahankali yake bama su Abba Labarin yadda komai ya Fara Sanadin khalil ne Abba nata Godiya yana saka albarka nan yace ma Dr.Ali isa ya kirasa yana mai murna kila khalil ya fadamai..
Sun dade suna ta Hira sai chan Dare suka watse Sagir ranar anan ya kwana Tunda gidan ba kowa mama Tana Kaduna.
Kamar koda yaushe Imran kan kujera ya kwana ya bar ma Sagir gado,Sagir yasha mamakin ganin Imran na Busan Sigari Cikin mamaki yace"Tab kai yanzu daman baka Hakura da shan Taban nan ba..?
Ko kallonsa Imran bai yi ba,Ya cigaba da Busa Hayakinsa,kamar bazai ce komai ba Har Sagir din ya koma ya kwanta yaji Imran yace"Ka Dauka na Daina sha ne saboda na fara aiki..?
Bai ma Sagir damar mgana ba ya cigaba da Fadin"Ma'aikacin banki baya shan Sigari ne..?
Sagir yadan Saki Tsaki yana Fadin"Wlh dai in kaje kana Busawa achan bankin kasan Sauran..!
Dariya Imran yayi har ana jin Sautinta.
Washegari tun Safe ya amsa Kiran wayoyin mutane ba dama Daddy ne Farko har Umma sai da ya bamawa tayimai Murna Kimarsa ta kara Karuwa acikin Idanuwansa,Khalil ya kira sa sun Dade suna mgana Har Mahaifinsa Dr.Ali isa argungun ya Kirasa yayimai Murna Basheer dasu Sadam duk sun kirasa kuma an bada Sanarwan a Group din marigayi Alkali Dukku ammh Baffa Kabiru bai kira Ko Abba ba ballatana Imran wanda Lambarsa ya Zaga ko"ina acikin Dangi kalilan ne ya adana Lambarsu kamar Daddy da Su basheer.
Yaga Sakon Inteesar Daya kunna Wayarsa har da ma da Kiranta ammh bai bi ta kanta in ita Nata wasa ne shi da Gaske yske yi saboda aikinsa yasa baima da Lokacin wani banzan Tunani,da tagaji da kiransa ta Hakura ta Turamai sakon ban Hakuri har tagaji,Bai taba maida kai ba ya shareta ya nuna mata Shi Namiji ne kuma Har yanzu yana nan a Imran dinsa bai sauya ba

Ranar data Damesa Sai yaTura mata Sakon cewa
"Kin gama Fushin ne..?

Da sauri tace

"Eh nagaji na tuba nabi Allah na bika Ya imu..!

Mirmishi yayi kafin yace mata

"In kin Gama ni yanzi zan fara nawa..!

Aikuwa ya fara nashi Domin Dif ya Dauke mata ya Rataye ta bata ma ganinsa tun 7:30am na safe yake Fita sai 6pm na yamma yake dawowa in kuma ya dawo yana Daki yana aiki Tunda ya siya karamar Laptop Apple Saboda aiknsa kudin nan ne lokacin Bikin Yusuf da Baba Manu ya dawo mai Dasu,Yusuf bai karba ba ya cika ya siya Computer,Sannan Abba yasa Yusuf ya basa kudi ya siya kaya da Takalma tunda har lokacin Akwai kudi a Bankin Nura sannan akwai kudin da suka saida Motocinsu da su ya kara ya siya Suit masu yawa da Takalma da agoguna Saboda yanayin aikinsa.
Mganar aikin Imran har Daada sai da taji Daddy ya Kirata ya Fadamata Tayi ta Saka albarka,Da sukayi ma waya da Abba Tayi ta addu"a Imran din basu samu mgana ba Tunda baya barin Wayarsa a Bude sai ya dawo gida.
Sati Daya da Fara aikinsa Bankin Gt ta mallakamai Gida Mai 2bedroom madaidaicin Falt,da Sabuwar Motar hawa Kirar 4matics kyauta Halak malak,saboda Sadaukarwarsa da da jajircewarsa Sulaiman Ishaq ne ya shigar da Korafin a Chan Sama Board of Directors kuma sanin Waye Imran Abubakar malami yasa akayi approving din mganar aka kuma Tabbatar.






*Shakira*
3/22/22, 23:15 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�14*

*Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488*


Da wannan Labarin Farincikin Imran ya dawo gida Ranar Cikin Sabuwar Motarsa baka 4matic da makullin gidan da suka mallakamai Sulaiman ya kaisa yaga gidan dake Anguwar Alu Venue.
Abba Hamdala kawai yake ma Sarki gagara Misali Sai da yayi hawayen Farinciki,haka ya yusuf daya dawo yaga Sabuwar Mota aharaban gidan shi kam ya kasa Boye murnansa sai Faman cema Imran yake Congratulation u deserve everthing Brother,Safiya ma ta tayashi Murna su Munari suna makaranta sai da suka dawo sukaji abun arziki,Ba kamar Inteesar a Farinciki duk da gogan nata yana Fushi da ita Sagir yazo yaga Mota ya shiga ya zauna baki yaki Rufuwa ashe ashe akaai Ranar da zai ga Imu zaune cikin Mota yana Driving ba shakka Rayuwa ta gaji haka kada kuma Kaga Mutum a wani yanayi ka Raina masa Domin bakasan Baiwar da Allah yayi mai ba kuma Dan Hakin daka Raina Watarana shi zai Tsole maka ido.
Imran ya Fadama Khalil wannan kyautar Girma shima ya tayashi Murna matuka da kansa ya Kira Mr Tunde ya Fadamai Duk ya sani shima ya Tayasa murna tare da karin wasu Shawarwari.
Duk wanda ke tare da Imran sai da ya tayashi Murna saboda ya Chanchanta Inteesar ta Test messages ta Turamai Sakonta kuma yagani ammh bai nuna mata ya gani ba wannan Shariyan nasa tana matukar Damunta har ta fara rama barci kuwa sai ta kusa Raba Dare ya kasa Daukanta ammh gogan nata baisan tanayi ba komawarsa aiki yasa ya kara zama Rashin Tabbas Fiye da baya.
Ko sati ba"a Rufe ba Sai ga sunan Abba Jami"ar BUK ta Zana a mtsayin DEEN na Department din Daya fi kwarewa Akai wato Psychology Proffesor ne suka zauna da Daktoci da Deen na Faculty da Deens na Department da shuganni masu rike da madakin ikon Jami"ar Turanci ne kawai akayi ta Zabgawa kamar ba a kasar Nageria ba,ilimi ne da manya Kwalaye yayi aiki,Abba ma sun gayyaceshi yaje sun zauna Cikin manya manyan Proffesor,bai Razana ba ko kadan Tuni tsohon Dr.Abubakar Malami Dukku ya dawo,Tattaunawa Data kwashi awanni goma kafin agamata washegarin Ranar ne aka Fadi sunan Abba A mtsayin Deen na Departarment din Psychology.
Wannan abun wani Budi ne da Ni"ima Daga Ubangijin mai Rahma mai jinkai In wata Kaddara ta sameka ka Dogara ga Allah shi din Yana mganin kowani Tsanani da Sauki In ka Yi hakuri Zaka ga sakamakon ka a wajen Allah to hakan ne ta Faru da wannan ahalin da sukayi hakuri suka Dauki Kaddaransu Hannu Bibbiyu sai gashi Allah yana Dawo musu da Ninkin ba Ninkin Abunda suka

Please Login or Register in order to submit comment