Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Da kanki..!
Wani kallo tamai batace komai ba Tasleem ta mike tana fadin"Bakomai Abbu bari na Dauko mata..!
Shima bai yi mgana ba ya cigaba da Tusa dankalinsa yana Hadawa da Kurban Ruwan tea a wani karamin mug mai kyau da yarari.
Ba jimawa sai ga Tasleem ta Dawo da Wayar Hajiya Mero a hannunta sai da ta Zauna ta mikamata Tana fadin"Gashi Mommy..!
Karba Tayi tana Yar dariya da sai da suka Kalleta gabadayansu Lambar Safiya ta Lalubo ta doka mata Kira ta saka Wayar a Speaker ta ijiyeta nan kusa da Hajiya Alhassan saman Tebir din.
Kira Daya biyu uku Safiya Daga Chan bangaran da suke Kitchen suna aikin Abincin da su Abba sukace ayi mai yawa Saboda bayan Salar azahar in in aka gama Daura auran za"a Fito da Abincin arabama Mutane.
Gefe ta koma kafin ta Dauki Wayar Tunda gabadayansu suke Kitchen din Har da Inna Maimunatu dasu Zainab dasu Aneesa da su Munari Inteesar na Cikin Daki bata Fito ba tace kanta na Sara mata.
Sallama ta Ragada kafin tace"Mommy ina kwana..!
Momny ta amsa Tana Fadin"Lafiya lau Daugher ya kuke..? Ya Dukkun..?
Tafada tana kallon Alhaji Alhassan Daya ijiye cin abinsa yana Sauraransu Da mamakin jin ta ambaci Dukku.
Safiya Dagachan bangaran tace"Lafiya lau Mommy gamu cikin sha"anin biki kin ji Hayaniya ko..?
Mommy tace"Eh fa bikin waye..?
Safiya tace"Mommy Imran za"a Daura ma aure yau da yar"uwansa Diyar wanda Abba kebi Baffa Kabiru Barrister Dake Zaune A Abuja..,!
Mommy ta Rike baki tana Fadin"Ikon Allah kice Tuwon a maina Za"ayi..Ammh abu cikin gaggawa haka..?
Safiya tace"Daurin auran kadai za"ayi Mommy Tarewa inaga sai daga Baya..Daada ta hada abun saboda kara Hada kansu Waje Daya..Mommy kinga Danginsu gabadayansu kowa yazo da ya"yansu gidansu Babban Gida ne Mommy a Dukku su din Dangin Manyan Mutane ne Duk garin Dukku ba wanda baisan Iyalan Gidan Marigayi Alkali Hamisu Dukku ba..!
Mommy Dake sakin Dariya Tana kallon Alhaji Alhassan ta gfen ido kafin tace"Masha Allah..Naji Dadi sosai Safiya..Allah bai barin Zalunci Daman Nagodema Allah yadda wani yaso ki tozarta Allah bai bari haka ya Faru ba gaki yanzu cikin Ahalin mijinki Cikin nasaba da Karamcin da Tushe da asali in arzikin ne suma sun Taka Allah ma godemaka da kika Tsallaken Siradin Tozarci sai dai Mutum ya Tozarta..!
Ta Karishe Fada da karfi kuma da gayyah ba Alhaji Alhassan ba Hatta Tasleem da Safiya susan da wanda suke.
Safiya tace"Plz Mommy..!
Tafada Cikin shagwaba Hajiya Mero Tace"Ki gaidamin da Yusuf sai kun dawo zamu zo da Saratu da Tasleem Insha Allahu..!
Safiya tace"Tom Mommy ki gaida Abu da Tasleem sai na Kiraki..!
Daga haka ta katse kiran Mommy ta Mike Dauke da wayar tana yar waka Lokaci Daya tana Fadin"Allah ba azzalumin bawa bane..Allah kana gani..!
Haka take fada Cikin Salon waka ta wuce zuwa Falon tana Hararan Alhaji Alhassan Ta gefen ido samin baida gaskiya ko Dagowa ma bai yi ba kansa na kasa gabadaya Jikinsa ya gamayin Sanyi Tsoro ya Shigesa yana Tsoron kada Hakkin Safiya ya kamasa a sirinsa ya Tonu,Domin bai fa Daina Dabi"arsa ba sai dai kalaman Hajiya Mero sun bashi Tsoro,Ashe yaron nan Yusuf dan asali ne,Lalle ne kada ka shiga Hurumin Ubangiji gabadaya ya kasa Tashi ma Har Tasleem ta gama tabi bayan Hajiya Mero zuwa Falo kunya ya hanasa wani Motsi.

****

Imran cika kawai yake yana batsewa kamar yayi Bindiga sai kunkuni yake Fuskar nan ba Fara"a ya Hade ran nan kamar bai taba Dariya ba.
Zaune yake gefen gadon dakin da suka sauka,Sagir da Yusuf na Tsaye kansa,Wasu Fararan kayane Riga da wando na Wata Shadda mai kyau da yarari,kayan Yusuf ne Abba yace ya bama Imran ya saka saboda Daurin aure,Da farko so yayi ma ya Gudu ya bar anguwa sai Abba ya Ritsashi yace mai in yasake ya Fita sai ya sabamai baida yarda zai yi Dole ya koma yayi lakwas,Sha biyu ta wuce sun fara Haraman Daurin auran tunda Har sun Daddy ya baama su Basheer kudi sun siyo goro da Minti Umarnin Daada ne Gida kuma ana ta Girki Kayattace,Mami Asma"u na Cikin Daki ta kasa Zama sai kiran Baffa Kabiru take tana so su kebe bai bata Dama ba Saboda baisan me zai ce mata bai isa yabi mgnarta ba yabar Umarnin Daada ba
Shiyasa yaki yarda su Hadu hankalinta ya shi sosai,Khamis ma ta kirasa tana Fadamai yaje ya gayama Baffa Kabiru kada ya yarda a Daura wannan auran bata amince ba Da ya fita bai Dawo ba bayason Mami Tana irin wannan sai abu yazo ya Lalace Daga baya.
Sajida kuwa Daada ta saka Inna Maimunatu da Da Inna Bintalo suka Daukota nan Dakinta Mami Asma"u tana ji tana gani bata da tacewa,Ta Kira Chan gidansu ta Fadama Tsohon Alkalin Alkalai Justice Tafida tana kuka bai biye mata ba yace Baffa Kabiru nada Hurumi da iko kan yarsa ganin ba Sa"a yasa ta Kira Hajiyarsu Hajiya Turai itacre ta Dauki ZAfi ta Kira Baffa Kabiru,bayan sun yi mgana ya nuna mata Umarnin Daada ne shi kuma bai isa ya kauce ma Umarninta ba Dole tayi Shuru ta kira Mami tana bata Hakuri Mami Asma"u ta Cika kamar ta Fashe ga ya"yanta basa Goyon bayanta Umaima ta shige cikin Danginta Ita da khamis suna ta Shirin Daurin auran

Sagir ne ya kalli Yusuf yana Fadin"Ya Yusuf inaga fa sai mun Dannesa mun sakamai kayan nan zai saka su..!
Ya yusuf yace"Naga alama..Imu tashi ka saka kayan nan kafin mu danne ka mu Maka Sintir mu shiryaka..!
Bai ko kallesu ba yana Daga Zaunen yace"Ni ba kayan da zan saka..Kayan Jikina sun isheni..Kuma infact ma ni manyn kaya ba Kayan sawa na bane zan iya kirga sakasu ma da nayi a Duniya..!
Yafada Cikin Dakuna Fuska yanajin an gama Kashe Rayuwarsa wlh.
Ya yusuf yace"zaka sa ko kuwa sai mun Danneka..,,?
Kallon irin lallene ma yayi musu kafin ya Tabe baki yace,"Uban Daya Fasa..!
Zaro ido sukayi dukkansu suna kallon Imran din wanda ya kara Hade ransa Sanye yake cikin Shigar riga da wando 3Quater,duka bakake ya gyara Gashin kansa Daadan nasa ya kara Fitowa tas dashi ahaka zai je Daurin auran domin ya gama Tsarinsa bamai sakashi Sauyawa.
Ya yusuf ya kada kai yana Fadin"Bari na Kira Abba na gayamai kace Uban da ya fasa..!
Yafada yana Fito da wayarsa ya Farra Dannawa Imran na jin haka ya Mike Cikin kunkuni yana Wani Dakuna Fuska yana Fadin"Tsakani ga Allah an Takuramin..An Takuramin an gama dani ni dai an cuceni Wlh..,!
Haka yake fada kamar yayi kuka Dukkansu dariyansu suka kanne Yusuf yace"Abba ya gode..Tunda ya Cuceka Imu..!
Yana Daukan kayan yace"Ni ban ce ba..kuma afita abani waje ko agabanku zan Tube na saka kayan masu gadi..?
Yafada Cikin bacin rai da Takaichi Dariya suka saka Imran ya Saka Kafa ya Shuru Sagir Yana Fadin"Munafuki..Shidai gefe ya matsa yana Dariya Yusuf yajasa suka fice suka Rufomai kofa abakin kofan suka Tsaya suna gadinsa sanin Halinsa zai iya Fitowa ya kara gaba.
Sun bashi Minti Talatin suka koma Dakin Wow mssha Allah haka suka Hada Baki wajen fada.
Sagir ya Kalli Imran da yayi wani irin kyau cikin mayan kayan,Ya yusuf ya azamai Hula zanna Bukar Dake hannunsa,mai zanen bakin zaren aikin Dake jikin shaddan yana Fadin"Rufe wannan Tozom gashin naka..Kada ango ya zama abun nunawa..!
Imran ya yamutssa Fuska yana Fadin"Asan Mutum dai asan cinikinsa Shine Rayuwa ba Karya da munafunci ba..Ni ban damu ba ko Duniya zata nunani am Remain Who i am..!
Ba su tankasa ba sanin yana neman Hanya ne,Sagir kuwa Hoto kawai yake Daukan Imran yana Fadin"Da kasan yadda manya kaya ke maka kyau da daga yau baka kara saka kananun kaya ba..,!
Wata uwar Harara Imran ya Aunamai yasa ya kama bakinsa yana Dariya suna cikin haka sai ga su Sadam sun shigo da Sa"id da Basheer suna ganin Imran suka Fara ihu suna yaba kyansa Suka Firfito da wayoyinsu suna ta Hotuna dashi,Suma kowanne yaci kayansa sabi duk da abun ba Shiri ammh sun shirya ba Laifi.
Duk Hoton da akayi Imran bai saki Fuska ba Sa"id ne ya Daki Kafadansa yana Fadin"Haba Angon Sajida Smile..!
Daya fadi haka Sai da Imran yaji kamar ya yarfamai mari Saboda sunan Daya ambata daga saman lebensa yace"Har Abada bazn taba zaman angonta ba ko na zama na yan a wanni ne a suna..!
Dakyar yadan saki ransa aka gama Hotunan kamar wani Rakumi da akala haka Sagir da ya yusuf suka Riko Hannunsa zuwa Falo,Sai da wayar sagir yaji ana kira ne kana ya sakesa Mama ce ke kira Domin Umma ta Kirata ta shaida mata komai tace ace ma Imran tanamai murna.
Su Aneesa da su Abida kefadin ga Ango ya Fito Inna Maimunatu ta Fito tana Guda,Gudan Daya Fadar ma da Mutane guda uku gaba na Farko Inteesar dake kwance cikin Daki na Biyu Mami Asma"u na uku Sajida dake Dakin Daada Inna Bintalo ta gama Shirya ita da ya"yanta Hamdiya ta mata kwaliya Saukakkiya suka Dauko Cikin kayan data zo dashi wani less suka sakamata bayan sun azamata Daurin Zahra Buhari sai gashi ta Fito duka Daada ta bada Umarnin hakan.
Inteesar na jin haka ta sauko Daga kan gado ta Leko Falo karaf kuwa ta Hangosa duka Mazan dake falon shi Zatinsa na musamman ne Manyan kayan Dake jikinsa sun kara Bayyana kyakyawan Zatinsa da Haibasan yayimata kyau din da bai taba mata ba.
Idanuwa shima yake Wulgawa Yana nemanta bai ganta ba kamar ance ya Kalli Kofar dakin suka hada ido wanda da Sauri tayi baya batasan ya ganta ba Wani Dum yaji acikin Ransa yana jinsa kamar bashi ba.
Daada har Falon ta Fito bakinta yaki Rufuwa Dafasa tayi tana Fadin"Allah yayi maka albrka Imrana kamar yadda Ka Bi Umarnina Allah ya baka y"yan da zasu bika kaima!
Su yusuf ne suka amsa da Ameen banda Imran da acikin Ransa yace"Ba Ameen ba kar allah ya bani da'n da zan Tursasamai yin abu yayi ba don son ransa ba..kuma ki daina Saurin jin Dadi Bacin rai zai gauraye wannan Dariyar taki.keba Uwata ba kin Rikitomin bala"i cikin Rayuwata..,!
Yana Tunanin yana wani Dakuna Fuska Daidai Lokacin da Mami Asma"u ta Fito suka Hada ido kallon kallon suke ma juna ganin yadda duk ta ZAbge ne tayi wani wuri wuri yasa Imran yaji Dadi harda Dan Taune lebensa na kasa kafin ya Daga mata Babban yatsanshi yayi kasa dashi alamun kin Fado.
Takaichi da bakinciki suka kamata bata iya yin komai ba Har suka Tarkasa suka fice Daga Falon,Sagir da Yusuf na Rike dashi kamar zai gudu.





*Shakira...*
3/22/22, 23:14 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�7*

*Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488*


A haraban gidan suka iske su Abba Shida Daddy suna mgana suma sunci manya kayansu sun sha kyau sai Baffa Kabiru dake gefe yana amsa waya Khamis na kusa dashi shima wayar ce a Hannunsa yana ta Latsawa Suma sun yi Shiga mai kyau da Tsari.
Tunda suka Fito Hankalinsu Abba ya koma kansu Zaratan SAmarin ya"yan nasu Imran duk ya Cinyesu akomai Kallo Daya zakayi mai kaga Tsabar Zati Haiba da kamala Uwa uba Kwarjini da wani baiwar Kyau da Allah yayi mai.
Abba da Daddy baki suka Washe azuciyarsu suna Fadin Masha Allah ballatana Baffa Kabiru da Khamis da suka Saki baki suna kallon Imran Duk da bai saki Fuskarsa ba ko kadan ammh Kana kallonsa Zaka Tabbatar da wannan cikakken Namiji ne inda ake Kiran Maza masu sunan Maza.
In bace maka akayi yana Busa Sigari ba akallo Farko bazaka taba yarda ba Saboda yadda kyansa ya Fito da kyakyawan Zati sukansu sun shaida Karyansu suce Sajida tafi karfin Imran Sai dai shi yafi karfinta ma sai dai in Akayi duba da abunda suke Dubawa din ba Domin wani abu ba.
Har gaban Abba da Daddy Yusuf da Sagir suka Kaisa yana ta wani Fadin Rai Abba ya Dafa Kansa yana Sakn Mirmishin Farinciki Cikin Annushuwa yace"Allah Sarki Zuwaira Allah ya jikanki da Rahma ina ma Kina Raye yau kikazo kiga Imran din ki Zai zama Babban Mutum..!
Gabadaya sai jikin kowa yayi sanyi jin kalaman Abba da kuma yadda Hawaye suka ciko Idanuwansa yayi Saurin maida su yana Jijjiga Kafadan Imran Lokaci Daya yana Fadin"Allah yayi maka albarka..!
Daga saman Lebensa ya amsa da Ameen Hakama Daddy ya sakamai albarka ya amsa Kamar mai Ciwon baki.
Sai Lokacin Khamis ya Kariso wajen ya bama Duka su Basheer hannu sukayi musabaha Daya Miko ma Imran sai ya Karkace kansa gefe kamar bai gansa ba Khamis ya karajin ya muzanta Da Sauri ya maida Hannunsa Bayaso wani Cikin su yaga wannan Tozarci da Imran ke nuna mai duk sanda ya Nemi wani Huldar Arziki ta Shiga Tsakaninsu.
Koda Baffa Kabiru ya kariso Wajen Imran Saboda kada ya gaisheshi baya ya koma,kawai ya Saka Hannayensa Cikin Aljihun wandon Shaddar Dake jikinshi yana kallon kowa Daya bayan Daya yana jinsa yau din nan kamar bashi ba,Ga wadanan kayan Dake Jikinsa ba karamin Takuramai sukayi ba.
Ganin Lokacin Sallah ya kusa ya saka duk sukayi alwala anan Haraban Gidan,Inna Maimunatu ta Fito musu da Botoci sukayi amfani dasu kana suka Rankaya zuwa masallacin Dake kusa dasu,Basheer da Sadam na Dauke da Dabino da goron da za"a Raba Kafin Daurin auran Imran kuwa Yusuf da Sagir na rike dashi kamar wani mai Laifi ransa ya baci da hakan ya Kallesu yana Fadin"Wai meye haka kuke wani Rirrikeni kamar wani Barawo..?
Yafada yana kara Dakuna Fuska Sagir ne yace"Saboda munsan Halinka Za"a iya nemanka awajen Daurin auran nan a rasa..!
Wani Mirmishin Takaichi ya saki kafin yace"Rubbish..Dilla Malamai ku Sakeni na Rantse da Allah in nayi niyyar Tafiya ba wanda ya isa ya Hanani..Daman bazan je ko"ina Saboda Abba Shi kadai ne yake iya Takama Ra"ayi Burki..So please let me go.Nasan abunda nakeyi.!
Yafada Cikin bacin rai jin haka yasa Yusuf yace su sakeshi Tunda ya Fadi haka ba inda zashi sun sakeshi yana ta Hararansu kamar ya Dakesu haka yake ji ba karamin Cutar Rayuwarsa akayi ba wlh ayadda yake fama da kansa Din nan ace za"a kara Dauramai wani Nauyi..? Ina Wlh bazai Dauka ba su dai Daura auran ai Alhakin komai yana Hannunsa ne yaga ta yadda Zai zauna da wannan Shegiyar yarinyar mai kama da uwarta.
Sai da aka idar da Sallar azahar kana aka kara Sanar da Daurin auran Daman kuma Tun safe Daddy yazo ya sanar da limamin masallacin akwai Daurin auran Jikokin Marigayi Alkali Hamisu Dukku.
Mutane duk basu Tafi ba Daman masallacin ana cika sosai nan su Basheer suka tsshi suka Fara Rabon Dabino da Goro,suna gamawa aka Fara Gabatar da Neman aure Daddy shi ya Biya Sadakin Imran Naira Dubu Dari Cif,Baffa Kabiru ya Umarci Liman Daya bada auran Daddy shi ne Uban ango shi ya karbi Auran Sajida Kabir Hamisu Dukku Yayinda Daddy ya Karban ma D'ansa Imran Abubakar Malami auranta kan Sadaki Dubu Dari lagadan ba ajalan ba.
Lokacin da aka Tabbatar da Daurin Auran sai da Imran yaji kansa ya Saramai Bakinciki kamar yayi kuka Babban Ci bayane ma ace an Taba Daura mai aure da wannan Yarinyar Har Abada bazai manta da wannan Ranar a Sahun Ranakun bakincikinsa ba.
Bazai iya Zama acikin masallacin ba Shiyasa ya Fito ya saka Takalmi kenan sai ga Sagir ya Fito rikosa yayi ganin Mutane Tundaga Ciki suna ta gaisawa dasu Abba kowa na Wurga idon ganin Ango Yusuf ne ya Hangosu Daga Waje ya nunasa nan fa Mutane ke ta zuwa da sun zo suna kokarin mikama Imran Hannu sai ya Kara Hade rai ya Kauda kai Hannayensa na Goye a bayansa ko Fito dsu bai yi ba Sagir ya bari da karban Musaban yana kuma amsa Fatan Alherin dinsu.
Da kafarsa yake zungurin Imran Wanda ya wani Dauke kai kamar ma baisan me ya aikata ba Mutane sun zata ma Sagir ne ango Imran abokinsa wasu Da dama sun tafi da Fadin kai Abokin angon nan bai da Fara"a Ko kadan shi kuma ko ajikinsa Domin tsayuwarsa a wajen ma ba karamin Takura bane ga Rayuwarsa yau Darajan Abba kadai akaci da ko Sama da kasa zasu hade bai ga Uban Daya isa yayi mai abunda akayimai yau ba.
Gajiya da Zungurinsa da Sagir yake yayi ya Wurgamai Harara yana Fadin"Mallan Lafiya..? Kafa isheni ka mtsamin Kafin na Sauke bacin Raina akanka Wlh yanzu ka tsinci kanka cikin wannan Kwalbatin Dake gefenmu..!
Imran ya Fada yana Nunamai kwalbatin da baki Sagir ya juya yana kallon Kwalbatin cike da kwata da Sauri ya matsa Yabar Kusa da Imran din Saninsa Wlh zai iya aikata Abunda ya Fada Mirmishin Fatan baki Imran ya saki Kafin murya kasa kasa yace"Better for u..!
Hararansa Sagir yayi saboda yajisa Kafin yace"Kaifa baka da Mutumci Daman na sani..Kana ta wani cin mgani Gata Daada tayi maka ta aura maka wannan Santaleliyar Budurwa batare da ko sisinka ba ya kamata ma ka Gode mata ne ba wai kazo kana wani Daure Fuska kana wani yamutsa Fuska kamar kaga kashi ba..!
Imran ya kallesa galala irin kallon Are u Mad..? Karkace kai yayi yana Fadin"Nace tamin gatan ne..?Ko Daadan Uwata ce..?
Yafada yana Tsatsare Sagir da Mayun Idanuwansa Cikin mamaki Sagir yace"Ikon Allah Ita Daadan..?
Cikin Takaichi ya saki karamin Tsaki yana Fadin"Eh ita ai ba uwata bace..Bani ta Haifa ba bata da wani iko akaina..Abba ne Da'nta meyassa shi batayimai gatan ba..? Ai naga shima bai da mata dashi tama wannan gatan bani ba..Kuma Duk Cikin Tarin Jikokinta sai ni ta Zaba..!Wato nine Maraya Uwata ta mutu Dole a Dinga Walagigi da Rayuwata to ban Dauka ba Wlh..Koda nayi Rashin Uwa baisa na Rasa kimata ba nasan Darajan kaina da Mutumcina saboda Haka ni Daada batamin gata ba wlh sai ma Kokarin Takurama Rayuwata Datayi kada ka kara cewa wai Daada tamin gata ni ban gani ba kai koma gatan tamin ban gode ba domin ban ce ina Bukata ba..!
Ya Karishe Fada a Fusace kafin ya Tada Iska ya wuce Fuu kamar zai Bangaji Sagir yayi Saurin mtsawa yana Binsa da kallo kafin ya Girgiza kai yana Fadin"Kin auri aiki yarinya..Imram..Imran ba kanwar Lasa bane..!
Fitowa kawai su Abba sukayi basu ga Imran ba Sagir yace ya wuce gida suma Daganan gidan suka Wuce Tare da wasu Mutane saboda Walimar da sukace zasu suyi.
Suna zuwa Haraban gidan suka iske Imran na saman Motan Yusuf yana ta Busa Sigarinsa ya Cire Rigar jikinsa Daga shi sai Vest ya kwabe Hula wai ta Damesa,Sai da yaga Abba ne yaji kunyar Ya Saki Taban ta Fadi kasa ammh ko ganin Baffa Kabiru da Khamis ba sa ya Fasa Abunda yake yi ba,Baffa Kabiru da Khamis Takaichi Duk ya Cikasu na ganin irin Mijin da Sajida ta aura Mutum Har Mutum ammh ba kyan Hali haka Khamis ke Fada acikin Ranshi.
Abba ne ya mikama Imran din hannunsa yace ya bashi Kwalin Sigarin da makunninta kafin ya Sabamai Dole baida yarda zai yi ya saka Hannu acikin Aljihun wandon Dake Jikinsa ya Dauko Duka ya Mikama Abba ya karba yana nuna ma Daddy,Kai kawai suka Kada acikin Ransu suna Fatan Allah ya gyara Kayanshi Domin shiriya tana wajen Allah ne.
Ganin haka yasa Imran bai Tsaya ba ya Kwashi Rigarsa da Hulansa ya wuce Cikin Gida yana wannan Takun nasa na Sassarfa afalo yaci karo Dasu Basheer su Sagir gasu Inna Maimunatu suna ta Hayaniya jin an Daura auran Sadaf sadaf ya wuce kafin a gansa ya shige Dakin da suka Sauka shida Sagir ya Rufo kafa Gabadaya ya Kwabe wandon Jikinsa Da Vest din ya Rage dagashi sai Boxers ya haye gado ya kwanta bayan ya kunna Fanka Zafi duk ya ishesa Yana jin karkashin Zuciyarsa na wani kuna Bini Bini ya saki Tsaki kamar wani Tsaka.
Achan Falo kuwa Tunda Labarin Daurin auran yazo Cikin Gida Mami Asma"u ta shige Daki tana ta Rizgan kuka yanzu Shikenan Tsagerin yaron nan yayi nasara akanta ina bazai yuyu ba Tunda aka nuna mata iyakarta itama sai ta nunama kowa nata iyakar Sai a Dauki Sajidan akaimai Tagani Indai Tana Raye ba wanda ya isa.
Sai da taji kukanta ta gaji kana taje tayi wanka ta Shirya Fuskarnan duk ta Kumbura ba wanda yabi ta kanta su Umma duk suna Falo ana ta Hidima Bata ga ko Daya Daga Cikin ya"yanta ba,Sajida Tana Dakin Daada Umaima tana Tare dasu Munari Khamis kuma suna Haraban Gidan inda suke Walimar su nacin Abinci isu isu da sauran Mutane an Shimfida manyan Dardume suna zaune suna cin Abinci ga ababen sha nan Birjit sai wanda ka Zaba Imran ne kadai bashi a wajen kuma ba wanda ya Damu Dashi Sanin Halinsa.
Bangaran Amarya Sajida kuwa tana jin Gudan Inna Maimunatu Tana Fadin an Daura aure taji wani sukuni Tare da Salama ya Shigeta,abaya kafin Taga Imran tasha Mafarkin yadda Kayattacen Bikinta zai bar Tarihi a Nageria sai dai ganin Imran da Faruwar komai ya Sauya mata Duka Tunaninta Abunda ya Faru bai Dameta ba sai ma wani Salama Dataji na Zamo warta Mata ga Imran
Ya"yan Inna Bintalo ne suka zo suna ta Daukan Hoto da Sajida su Hamida,anan ciki aka kawo mata Abinci Tunda Daada ta hanata Fitowa Daga Dakin ballatana su Hadu da Mami Asma"u Alokacin ma ita kanta Sajidan bata kaunar ma taga Mamin Saboda tasan har yanzu da aka Daura bazata Daina adawa da wannan auran ba ita kuma ayadda Lokaci Daya Soyayyar Imran tayi mata kamun kazan kuku Tana Daidai da tayi Fito na Fito da wanda yace zai Rabata da Abunda take so..!
Bangaran Inteesar kuwa tun Safe tana Kwance gabadaya ayyukan da akayi da Ifacen ifacen da akayi ta yi acikin Gidan baisa ta Fito ba kanta Nauyi yayi mata Kirjinta na mata Zfi duk sanda ta Tuna da Imran zai auri Sajida ba yadda su Munari basu yi ba kam Tatashi Tayi wanka taci abinci tayi banza Dasu,gajiya sukayi suka kyaleta,su dai bayan sun gama aiki suka shaba wanka da kwalliya Har da Umaima Data shige Cikinsu suna ta Daukan Hotuna Munari ita ko ajikinta Domin ba wani Sanin Sajidan tayi ba,sai dai ta Tsausayamata Domin har ga Allah an bata aiki babba na Aura mata Ya Imu.
Inteesar tana daga kwancen Munari tazo tana Fadamata an Daura aure gasu Ya Basheer chan sun dawo Sai Inteeser taji kamar Zata Mutu sai Hawaye Sharr Hankalin Munari ya tashi ita taje ta Kira Umma Duk ta Rikice ta Rikita Umma itama ganin tana kuka yasa ta zata Jikin ne basusan Hakikamin me ke Damunta ba ita kanta bata sani ba Ballatana ta Fada musu sai dai Kirjinta nayi mata wani Zafi kukan datake yi shine kadai Salamanta.
Umma ce ta Lallabata tarakata Tiolet tace tayi wanka ta saka Munari ta Hado mata Tea saboda tasha Cikinta ya Warware,Inteesar na Shiga Tiolet din ta Zauna saman sit din Cikin Tiolet din ta Fashe da kuka yi take ba kakkautawa kamar wacce akace wani nata ya Mutu kanta yana Sara mata ga Nauyin Kirji,tana cikin kukan Wata Zuciya tace mata"To ke Inteesar kukan me kike yi..? Ina ruwanki Domin yayi auransa bai kamata kizo kina saka kanki acikin Damuwa ba Har kina kuka ba Tunda ba sonshi take ba..,!
Sai wata Zuciyar tace mata"Ko bana son shi ai dan"uwana ne bazan so mai abunda baida kyau ba..Sajida bata Dace dashi ba Shiyasa nake Damuwa..!
Tafada acikin Ranta tana jin yes wannan ne Dalilinta,Da wannan Tunanun ta Lallashin kanta ta yi wanka ta Dauro alwala ta Fito Umma da Munari na Jiranta,mai ta shafa kafin ta saka Doguwar Rigarta baka Kirar Armani,Munari ta mika mata Tea din tasha Umma ta balla mata mgani ta bata tasha ta Dora Tea din Daman tana jin yunwa Cikinta sai kuka yake,Tagama sha sai Zufa alamun dai ta Fara samuwa ganin haka yasa Umma ta Fita ta barsu,Munari ta Shimfida mata Darduma ta Fita ta barta Bayan ta Tada Sallah.
Tana Fitowa Falon Lokacin su Abba na Shigowa nan suka gaggaisa dasu Inna Maimunatu suna ma juna Fatan Alheri da Fatan an kulla alheri kafin su Dunguma Zuwa Dakin Daada dake Cikin Dakinta taci kwalliya bakinta Har kunne Casbaha na Hannunta tana ta Lazimi ranta Fes Koyau ta Mutu Burinta ya cika.
Ganin Shigowar ya"yanta nata yasa ta Kira Hamida tace tazo ta kai Sajida wajen Mahaifiyarta haka kuwa akayi ita ta rike Hannunta zuwa Dakin da Mami Asma"u wacce bakin ciki kamar ya kasheta.
Saboda Takaichi takasa ma cema Sajidan komai kallonta kawai

Please Login or Register in order to submit comment