Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaddama..? Jika aiki bata Mari koda guda uku ne ladan batamana Lokacin Datayi..!
Bai gama mgana ba ya Daga hannu Zai wanke Inteesar da mari wacce Har ta Runtse ido Tana makyarkyata tsoro Taji shuru Lokaci Daya Da tsayawan Wata inuwa agabanta Da Sauri ta Bude idanuwanta Duk da Bayansa Tagani jikinta da yadda Zuciyarta ta amsa ya Tabbatar mata da Imran ne
Bayan sun idar da Sallah ya Tsaya Kofar Shagon Sagir suna mgana Duk da Hirar duk Sagir keyinta sai dai gabadaya Zuciyarsa ta kasa Natsuwa yana jin Wani abu na Faruwa Domin gabansa ne ke Bugawa Fat..! Fat!
Wanda ya Rasa Dalili ganin haka yasa kawai yama Sagir Sallama ya biyo Hanya Tunda Daga nesa ya Hangosu,Da fitilan Wayarsa yayi amfani ya Haska kasa Da Zai wuce sun Shagala da aikata barnan su basu lura dashi ba.
Zuciyarsa ta kusa Bugawa Daya Fahimci Inteesar ce Maza Biyu suka Zagayeta Daya na Shirin kaimata Duka Cikin Zafin nama ya Dira gabansu Lokaci Daya yana Rike Hannun wanda zai kaimata Dukam Cikin Bacin rai da Zafin Zuciya.
Cikin mamaki suke Binsa da kallo na Gaban ne yace"Mallam lafiya..? Kada ka shiga abunda ba ruwanka ka barmu muyi aikinmu mu gama in ba so kake yanzu Jikin ka yayi Lahani ba..!
Bai ma tsaya Sauraransa ba ya yarfar da Hannunsa Cikin Fushi wanda sai da ya Ja baya kamar zai fadi cikin mamaki suka Dago suna kara Kallonsa.
Inteesar Data ga haka cikin Sauri ta Taso ta Rumgume Imran ta baya tana Mkarkyartan Tsoro da kuka Tana Fadin"Ya Imran sun karbemun waya..Sun fito da wuka zasu kasheni..!
Gabaadaya ta Rukumkumesa Kukanta kuwa ji yake kamar wani Dalma na Shiga Cikin kwakwalwarsa.
Ransa na baci Zuciyarsa na Zafi kamar Zata kama da Wuta Jijiyoyin kansa sun tashi Radau.
Mai Wukan ne yace"kai jika aikin zaka Ma haka..?lalle ka kira Ajalinka yau..!
Yafada Lokaci Daya yana Ciro wuka dake jikinsa ya Nufi Imran da ita yana zuwa ya daga zai Chakamai ya Damke hannunsa da Karfi Har sai da Wukar ta Fadi kasa ya murde hanun ka ya Saka Gwiwan kafarsa ya Daki bayansa sai da ya Fadi kasa,Dayan na ganin haka ya ja baya Cikin mamaki.
Imran ya Mika masa Hannu yana Fadin"Bani Wayar da ka amsa..!
Cikin Kaushin murya Tsoro ya kamashi ammh ya Dake yana Fadin"Wata Waya kuma mallam..!kai Waye..?
Imran ya kara Mikamasa Hannu yana Fadin"Bani nace..Kada ka bari na Sake maimaita mganata bazaka ji da dadi ba.Kuma ni ba wanda ya isa yamin Tambaya sai dai ni na isa nayi Tambaya kuma Dole abani amsataaa .!
Ya karishe Fada Cikin Tsawan da gayen da Sauri ya mikamasa Wayar yana Fadin"Baba mu gudu..Ina jin Soja ne..!
Yana fadamin haka ya taketa Shima Wanda aka Daka din ya Mike nan yabar wukar nashi yabi bayan Dan"uwansa suka Ari na kare basu Tsaya ba sai da suka bar Layin..
Ajiyar Zuciya ya Sauke ganin sun Tafi ita kuwa Inteesar kuka Kadai Take yi Tana kamkame dashi Tsoro ya Riga ya kamata..
Dan Raba jikinsu yayi Saboda Gabadaya wani Iri yake jin kansa Ammh taki sakinsa sai ma kara Rikesa datake yi Tana Shasshekan kuka
Ganin bata cikin Natsuwarta yasa ya Saka Hannunsa Guda Daya ya Dafa kanta yana Fadin"Shiii...Sun tafi fa..!
Yake fada yana dan Buga kanta alamun Lallashi.
Sai da yaji ta dawo cikin Natsuwarta ta Daina kuka ta koma ajiyar Zuciya.
Kana ya Dagota yana kallonta Fuskarta Tayi kace kace da Hawaye da Majina..Cikin Kaushin murya yace"Me yasa kika kai Dare..?baki da Hankali ne..?yanzu da ban zo ba Allah kadai yasan me xasu yi miki..? Ila ma su Illataki..!
Yafada cikin Tsawa da Takaichi yana jin Zafi acikin Ransa yana auna da Wani abu ya sameta vaisan yadda Zai yi ba.
Kuka ta kara sakamai tana Rike da Hannunsa tana Fadin"Wlh bansani ba..bansani bane..!
Take fada kamar ranta Zai fita ganin Mutane sun fara wucewa suna Kallonsu ne yasa yace"Naji is ok..Share Hawayenki ki wuce kije gida..!
Yafada yana Mika mata Hanky din Dake Hannunsa tana Kallonsa ta Karba ta Goge Hawayenta ta mikamai ya girgizamata kai Lokaci Daya ya Mikamata Wayarta yana Fadin"Ga wayarki..!
Karba Tayi hannunta na rawa tana Waigo Waigo ganin haka yasa yace mata"muje ko..!
Tafiya ta farayi tana Waige waige Cikin Tsoro ganin yana Binta abaya ne yasa Taji dan Sanyi suna cikin Tafiya Ledan Pure water da aka sha aka wurgar iska ya kadasa ya Hau kafarta ta Saka ihu ta Dawo baya ta Rirrike Imran cikin Tsoro.
Kallonta yayi yana Fadin"Ki bar rike in ba Haka ba zan koma na barki ke kadai..!
Tana jin haka ta sake shi ammh taki sakin hannunsa Cikin mamaki yace"Leave my Hand..!
Tana shan majina tace"Don Allah ka barni na rike..Ina jin tsoro ne kamar Zan mutu..!
Take fada Tana tsiyayan kwallah sai ta bashi Tsaiusayi bai kara mgana ba Har suka zo kofar gidan har Zaure ya Rakata Kafin ya Kalli Hannunsa yadda ta kamkame yace"To sakeni ki shiga gida..!
Sai alokacin ta Sakeshi kwallah na Zubomata tace"Tanque so much For Saving my Life Ya Imra..Nagode..!
Tafada Tana kuka kai ya Girgizamata kafin yace"Bana son kuka nan..Ki share Hawayenki ki shiga gida..Kada ki Fadama kowa abunda ya Faru kin ji ko.?
Kamar yadda yace haka tayi Tana Share Hawayenta tana Dagamai kai kafin ta Fara Tafiya zuwa Cikin Gidan Tama yi tana Waigensa Har ta shige sai da yaga Shigarta kana ya Juya yabi hanyar gida cike da Tunane tunane
Inteesar Allah ya Taimaketa Mama na Bayi shiyasa ta Lallabata ta shige kurya ta Haye gado ta Dunkule tana kuka Data Runtse ido Wukanan take gani Gabadaya Taakasa Natsuwa sai kuka Takeyi dataji motsin mama ne sai ta yi Shuru ta koma Ta Lafe.






*Shakira..*
3/22/22, 23:07 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️*


*🅿?28*

Shigowar Mama cikin dakin yasa Inteesar ta kara nokewa kamar tayi barci ganin yanayin kwanciyar nata ne yasa Mama ta kalleta tana Fadin"Inteesar lafiya kuwa..? Yaushe kika shigo.?
Bata da yadda zatayi Dole tayi saurin goge Fuskarta ta Dago kanta Lokaci Daya da mikewa Zaune tana Fadin"Yanzu na shigo kina Bayi Mama..!
Mama tace"Eh ammh Lafiya naganki wani iri..?
Tafada Tana kallon Kwayan idanuwanta da Sauri tace"Bakomai Mama ina tafiya a Hanyane wani karo ya Shigarmin ido ammh ya fita..!
Mama tace"Ayyah hala mai Shegen yajinan Ido yayi ta Hawaye..Sannu in bai bari ba ina da wani mganin ciwon ido sai na Diga miki..!
Inteesar ta gyada kai Ita kuma Mana ta Nufi kwabarta ta Dauko hajibi ta Tada Salla bayan ta Shimfida Darduma Komawa Inteesar tayi ta Kwanta Lokaci Daya tana kamkame Kirjinta da Hannayenta,Tsoron ya Fara Sakinta sai dai yanayin Data Rumgume Imran yaki barin Tunaninta Data Runtse ido Shi take gani,Jikinta yana amsawa ko"ina ya Saki Kasala ya kamata.
Lumshe idanuwanta Tayi kamar mai barci nan kuwa ba barci take ba Fuskar Imran ke Gitta mata Cikin kowani yanayinsa,ba domin yau ya Ceceta ba kila da sai Buzunta ammh ya Sadaukar da Rayuwarsa saboda ita Bazata taba mantawa dashi ba.
Ta tuna sanda ta Rikeshi da cewar da yayi ta sakeshi,da yanayin kallonsa Sai da Tsigar jikinta tatashi afili sai da ta Murmusa ta Furta"He is so nice..Yana da Kirki sai dai kirkinsa Boyayye ne bakowa ke sanin haka ba..!
Tafada tana jin wani nishadi acikin ranta tama manta da Mama acikin Dakin sai da ta juyo tana Fadin mgana kike ne Inteesar. ? Kana ta tadawo Cikin Hayyacinta tace A"a Mikewa Tayi Daga kan gadon bayan ta Sauko a kasalance ta Fita zuwa Kitchen ta Duba Flaks taga ba ruwa sai ta kunna Gas ta saka So take yi tayi wanka ko taji Dadin jikinta.
Kan kujeran Tsugguno ta Zauna acikin Kitchen din Ta Zafga Tagumi Tana Tunanin Abunda ya Faru awanni kadan da suka Gabata Tsoro duk ya cikata ammh da Ta tuna Imran sai taji wani irin Sanyi aranta.
Ya nemi alfarman kada ta Fadama kowa kuma tayi mai wannan alfarman bawanda zai ji koda Daddy ne,sai dai tana ganin kamar Godiyar Datayimai yayi kadan ya kamata ta Fara Tunamin Hanyar da Zata kara Godiya Saboda yadda ya Ceceta Daga Mutuwa.
Sai da Ruwan ya tafasa ta Diba sauran ta Juye a Flaks,ta Dauka takai Tiolet ta saka Ruwan sanyi ta surka Daidai tayi wanka Dashi,Bayan ta gama ta Dauro alwala ta Fito ta shafa Lotion dinta ta saka Kayan barcinta Riga da wando masu Ruwan madara masu Taushi, Lokacin ana ta Kiran Sallar Isha"i a wasu maaallatan sai ta Shinfida Darduma ta Tada salla,ta idar kenan Lokacin Mama na Falo Kiran Umma ya Shigo wayarta Daman tana kan gado ta jawota ta Daga suka gaisa Ta Tambayeta Daddy tace bai riga ya Shigo ba bayan Tambayan Karatu sai ta bama mama Wayar daman ita Ummn ke nema bai wuce kan mganar Bikin Yar wajen Kawu bala Domin yazo tana ma Tunanin wannan Satin ne Anty Jamila,Inteesar suna Chart Sama sama suna gaisawa ba Sa"arta su bane ta Girmesu sosai ita da Nasara da ace Tana kaduna ne Zataje Bikin ammh yanzu kam datake Makaranta sai dai in sun samu Hutu ta koma suje suga Daki ita Nasara Tunda nan cikin Kaduna Zata zauna..
Mama da Umma sun Dade suna mgana suka rabu kan Maman Zata taho Kaduna Tun Ranar alhamis sai kuma Bayan Biki in Allah ya yarda da Zata dawo,bayan sun gama Wayar Umma ke fadama inteesar wacce ta Hada Complex tana sha Inteesar ta bata Fuska wai bazata iya Zama ita Kadai ba..
Mama tace ba Damuwa in bazata iya ba sai ta koma Gidan su Munari har ta dawo Sagir ne kuma Tana Tunanin Shima Ranat asabar zai shigo Kaduna Daurin auran sai ya Jirata su dawo Tare Sai da Inteesar taji haka kana Hankalinta ya kwanta.
Da wuri ta kwanta Saboda bata Cikin Natsuwarta ta Dade barci bai kwasheta ba Tana Tunanin Abunda ya Faru kuma koda barcin ya kwasheta Cike da mafarkinsa Kala kala Abun har ya soma bata mamaki.
Da safe har ta ma manta da Zencen zuwa Gidan Ya Sadam wayar sa ya tasheta Daga Barci yace ta shirya zai Shiga asibiti in yagama abunda yake yi Zai Taho ya Dauketa Dole ta Mike ta yi Sharan Daki ta gyara ta wanke Tiolet ta gyara Tsakar gida,Mama kuma ta gama Abun Karyawa kunu da kosai sa ta sha kunun da Buredi ita,kana ta Juye ruwan Zafin da Mama ta Cika Flaks dashi tayi wanka Bayan ta Fito ne ta Dokama Munari kira Lokacin ma barci take bata tashi ba Sai da ta mata Kira Biyu ana ukun ne ta Dauka Tana Muryan barcin Inteesar ta Auna mata Zagi tana Fadin tatashi ta Shirya Ya Sadam ya Kirata jin haka yasa Dole Munari ta Mike.
Falo ta Fita taga ba kowa yau Lahadi Ya Yusuf suna ciki Dakin Abba ta Shiga ta Iskeshi yana ta Karatun Qur"ani sai bata kateshu ba ta Fito ta Shiga Kitchen ta fere Dankali ta Dora Ruwan Zafi kana ta Fito ta dan gyara Falon itama ta Share ta goge ko"ina kana ta koma ta Soya Dankalin ta soya kwai sai ta Dafa Ruwan Tea,ta jera saman Dining ta shige Dakinta ta fada wanka a gurguje ta Shirya,Daman Inteesar tace su saka Kayan da Umma ta Dinkamusu shi ta saka ta Sagalo Mayafin kayan Sea green.
Har zuwa Lokacin ba wanda ya Tashi,Tea ta Hada ta sha ta Hada da Dankalin kana ta koma Dakin Abba ta Iskeshi ya gama Karatun yana Zaune kan Darduma yana jan Cashaba ta Duka ta gaisheshi ya amsa mata yana Shafa kanta Nan take yagamai Zata je gidan Mama Inteesar ta Kirata Abba yayi mata Fatan Dawowa lafiya ta Fice Tana Fadamai Ta Hada Breakfast tun dazu yace mata Allah yayi mata albarka ta amsa da Ameen bayan tace mai in Anty Safiya ta fito ya gayamata ta tafi yace tom.
Koda ta Fito Daga Gidan nasu 10 ne da wani abu na Safe,batayi wani Tafiya sosai ba ta iso Gidansu Sagir a kofar gida ma ta Ganshi yana mgana da wani suka gaisa ta shiga Ciki ta iske Mama na gyaran Wake a Tsakar gida ta Rankwafa ta gaisheta Ta amsa mata Cikin Fara"a Tana Tambayanta Mutanen gidan nan ne mama take Fada mata Zataje bikin Diyar yayanta kaduna Kafin ta tafi zata zo tama Abba Mgana Inteesar zata zauna dasu kafin ta Dawo Munari baki kamar ya Tsinke saboda Murna...
Haka ta shiga ta iske Inteesar ta Shirya itama cikin irin kayanta tayi kyau sosai.
Zama gefen gado Munari tayi Tana Fadin"Ke Mama tace zaki dawo gidanmu kafin ta dawo Daga kaduna..!
Inteesar na Saka Sarka a wuyanta Tace"Eh nima jiya take fadamin..Bazan iya zama ni kadai ba,Ya Sagir ma Ranar asabar zai tafi Daurin aure..!
Munari tace"Wai bikin waye za"ayi a kaduna..?.
Inteesae tace"Bikin Anty Jamila Diyar Kawu Bala shine babba a Dakin su Mama..!
Munari tace"Allah Sarki Shine ke bazaki ba ko..!
Hararanta Inteesar tayi kafin tace"Sai na bar miki karatun nawa kenan ko..?
Munari batace komai ba Tana Dariya,Suna Hiransu Sama sama har Inteeaar ta gama Shiryawa,Tana so ta Tambayi Munari Imran sai ta kasa sai chan wata Dubara ta Taso mata ta Kalli Munari tana Fadin"ya su Abba..? Ina Anty Safiya da Ya Yusuf ina Dan Rigiman gidan ku Ya Imran..?
Munari tace"Ban hadu da kowa ba yau sai Abba..Kinsan yau Lahadi su Anty Safiya basa Fitowa da Wuri..Ya Imran kuma ina Tunanin ya Fita Jogging Tun dazu har ya Dawo..!
Inteesar tayi shuru Tana Tunanin tama manta yana Fita Da Safe Motsa Jiki,Data fita ko kofar gida da Safe ne taga ko Zata gansa..? Wata zuciya tace ki gansa a saboda mene..? Da sauri ta ba kanta amsa saboda in karamai Godiya ya Ceci Rayuwata.
Daganan bata kara cema Munari komai ba ganin sun gama Shiryawa yasa ta daga waya ta Kira Ya Sadam sai dai wajen kira Hudu bai Dauka ba Sai ta Kira Anty Aneesa take Fadamata Tana jin haka tasan aiki yayimai yawa a asibiti in tace su jirasa zasu kai wani Lokaci kawai sai tace su Fito su samu mai adaidaita su Kirata su bashi tamai kwantace in suka zo Zata Biyasa
Haka kuwa sukayi bayan sun ma Mama Sallama suka Fice wajen 11am naSafe suna Fita Kofar gidan bakin Shagon Sagir suka ci karo da Imran yana Tsaye sanye cikin Riga da wando na Jc Mai ruwan ganye ya Tusa duka Hannuwansa cikin Aljihun wandon,Kafarsa sanye cikin wani Takalmi mai kama da Silifas Gefensa Sagir ne kamar suna mgana ne Munari ce ta Fara ganinsu ita Inteesar nachan tana Kokarin gyara Zaman Karamar Jakar Dake hannunta
Yafito Inteesar tayi tana nuna mata Imran Lokaci Daya Tana fadin"Mun shiga uku Intee Ya Imran..!
Da sauri ta Dago Tana kallonsa Shima Daidai Lokacin Daya juyo suka Hada ido Dukkansu sai da sukaji Zukatansu sun amsa Ajiyar rai Imran ya Sauke na Samun Natsuwar zuciya daya ganta haka Tun jiya Daya koma Gida ya kasa Barci Saboda Tunanin Halin da Inteesar ke ciki Tun da Safe ya Fito Joging har Kofar gidan nan ya zo ya Tsaya ko zai ganta Shuru,bai ganta ba ya kasa Natsuwa yana so ya ganta ya Tabbatar da baatayi ta kuka ba kuma Lafiyanta kalau ya koma Gida ya kasa Natsuwa,Abakin Abba yake jin Munari bata gida tazo wajen Inteesar zasu anguwa yana Fadama Ya Yusuf da Matarsa Shiyasa ya Fito Domin ya ganta ya samu Sukuni yana ganinta yaji kamar anyimai gafara.
Itama anata Barayin hakane wani Sanyi Sanyi taji yana Shiga Jikinta Basar da su yayi ya Dauke kai kamar bai gansu ba Sagir ne ya gansu ya Saki Fuska Inteesar ta kamo Hannun Munari suka karisa gabansu Dukkansu suka gaisheshi Sagir ne kadai ya amsa su Gogan kuwa sai ma Dauke kai kansa da yayi kamar bai gansu ba nan kuwa,ya gansu yana ma ta Satan kallon Inteesar ne ta Gefen ido.
Har suka wuce suka Fara Tafiya zuwa Bakin Titi yana Kallon Gefensa baya so Sagir ya Fahimci ya Bisu da kallo sai da suka dan Dade da wucewa kana ya Hangesu Daga chan suna Tafiya Kadafa da kafada da Munari sun rike hannun juna acikin ransa sai da yaMurmusa yace"Ji besu kamar wasu yara..Kaya iri Daya kuma sun wani rike hannun juna..!
Shikadai abun ke bashi Nishadi,ganin ya Riga ya ga abunda yazo nema yasa Sagir namai Hira sama sama yake jinsa Daga Karshema yace mai Zai je gida sukayi sallama Daganan Sagir ya Koma Cikin Gida shi kuma ya Nufi Hanyar gida.
Suna zuwa bakin Titi suka Samu mai adaidaita suna Shiga Anty Aneesan na kira bayan ta dauka take Tambayanta suna ina ne..?
Tace suna cikin adaidaita sai tace ta bashi wayar ta mikamai ta mai kwantace yace ya gane wajen gasunan yanzu zai kawosu,nan ya mikama Inteesar tace mata sai sun iso.
Sun dauki Hanya kenan Wayar Inteesar tashiga kara tana Hannunta ne Tana Dagowa taga lambar mai Kiran ta Saki wani Siririn Tsaki batayi Sarving din Lambar ba ammh nacin Kiran Dayake mata yasa ta Haddaceta Saboda bata so ya Kira ta Daga..
Haka ake ta Kira bata Dauka ba Munari Dake gefenta tace"Wai hala baki ganin ana ta Kiranki ne..?
Inteesar ta tabe baki kafin tace'Ina gani bazan dauka bane..!
Munari tace"Eyye ko an yi sabon gaye ne Shine ba"a son Daga wayar agabana..!
Inteesar ta Harareta tana Fadin"Allah ya kyauta wannan ya Zama Saurayina..Ya khamis ne Dan Baffa Kabiru na Abuja Tunda mukaje Dukku lokacin nan ya nace min ya Samu Lambata ban huta ba yayi ta Kirana ni kuma Wlh bai min ba sam..!
Munari tace"To miye aciki Don ya Kiraki ku gaisa..!?ai ba cewa yayi yana sonki ba Besty..!
Inteesar tace"In na bashi Dama haka zai ce..Ni kuma bai burgeni ba Asalima Haushi yake bani..!
Munari tace"Kedai kowa ma sai kice yana Baki Haushi..Naga mijin ki kuwa..kilama Gajere ne baki mai Katon kai da..!
Inteesar ta katseta da Fadin"Ba Ameen ba Muguwa insha Allahu Mijina Ba kamarsa yarinya..!
Dariya Munari ke ta mata ita kuma ta sha mata kunu gashi Khamis din yaki Daina Kiranta sai kawai ta Kashe wayar In sun isa ta kunna Kila in yaji Tana Kashe ya Hakura.

Cikin Lokaci sai gasu sun iso,layin Ashe su Anty Aneesa suna Farko Farko ne,Tun da suka taso ta Fito bakin Get din Tana jiransu Suna ma Cikin Tafiya Inteesar ta Hangeta Ita da Waleeda sabe a Kafadanta tace ma mai adaidaita ya Tsaya sun kawo.
Sai dai ta gansu kawai agabanta suka Fito Daga Cikin adaidaita Cikin murna sika Rumgume juna ita da Inteesar suna Murna ganin juna ta Karbi Waleeda Dake hannunta ita kuma ta Karisa ta bama adadaita kudinsa,ta nufosu Inteesar tana musu maraba tayi musu Jagora zuwa Cikin Gidan sai alokacin ta Lura da Munari sai da gabanta ya Fadi ta Kuramata ido Tana kallonta wannan tayi kama da na Hoton nan da Daada ta nuna musu a Dukku karamar ciki ammh in hakane meyasa Inteesar bata ganeta ba Ammh Tabbas wannan tayi kama da ita..
Tana ta kallon Munari,Har Munarin ta Tsargu ganin haka yasa sai ta Waske,gidan dan madaidaici mai kyau da tsari sai gasu acikin Falon gidan Anty Aneesa tace su Zazzauna Tatafi Kicthen ta kawo musu Ruwa da Abun shq kana ta Zauna suna Kara gaisawa.
Anty Aneesa ta Kalli Inteesar Tana Fadin"Itace kawar naki da kikamin zaku zo tare..?
Tafada tana kara Kallon Fuskar Munati wacce ke wasa da Waleda dake hannunta.
Inteesar tace"Eh itace sunanta Maimunat..Munari ga Anty Aneesa matar Ya sadam yaron autansu Daddy ne.inna Maimunatu. !
Munari ta Dago tana Fadin"Allah Sarki..Ina yini..?
Anty Aneesa ta amsa tana kara kallonta sai dai tana yi da taku kada Munarin taga kamar tana ta kallonta.
Inteesar tace"ina su waleed hala..?
Aneesa tace tana Mikewa"Ya bi Abbansa Asibiti..ai nasan in ya Shiga asibitin nan sai Allah Shiyasa nace ku Taho kawai..!
Inteesar tace"Gaskiya kam..gwara da muka Taho ba gashi mun zo ba..!
Aneesan tace"Wlh kuwa..Allah sa dai ya dawo kafin ku tafi..!
Inteesar tace Amin daganan ta koma Kitchen ta barsu nan Tana Hada musu Brekfast Tana ta Tunanin Munari itama in bata manta ba Kamar Fuskar ne tagani a Hoton nan sai dai hoton yana Wayar Baban Waleed ne Daya nan ne data Dauka ta Kara Dubawa ba kodai ba ita bace..?in da itace da Tabbas Inteesar zata fara sani kafin ita ammh in ko hakane kamar har ta baci.
Ferfesun kayan ciki ta kawo musu da Waina da Miya datayi da Safe,sai kunun Aya,da Soyayyan Naman kaza,Tazo ta zauna suna ta Hira da Inteesar ta rika jan Munari da Hira har itama ta Saki jikinta suka Zauna sukaci Wainan sosai da Ferfesun nan,suka kara komawa saman kujeru suna Hira sai da aka kira azahar kana suka Tashi zuwa Sallah Dakinta takai su tace suyi sallah ita kuma ta shiga Dakin Baban Waleed,waleeda Tana Manne dasu musamman ma Munari kamar ta santa.
Bayan ta idar da Sallah Kitchen ta Shiga ta Dora musu Dambun Cuscus na Zogala Cikin Lokaci ta gama shi suna Cikin Dakin suna Hira sai dai tazo tace su Fito suci suna ta mamaki.
Dambun yayi Dadi sukaci suna ta Santi,Sukace basu iya ba zasu dawo ta Koya musu Tace sai sun zo.
Bayan sun gama cin Abinci ne suka Dora da Zobon mai Dadi Data Hadamusu cikin su ya cika ammh Dadin Zobon yasa sai da sukaji ba Wajen Shiga kana suka Hakura.
Inteesar ta kunna Wayarta ta Kira Daddy tana Fadamai gata gidan Ya Sadam sai dai baya Gida sai Anty Aneesa Har ta bata suka gaisa Harda Umma,Daganan Ita Anty Aneesan ta Kira Anty Hauwa suka yi mgana da Inteesar ashe suna waya sosai Zumunci ya kullu Masha Allah.
Sai da sukayi Sallar La"asar kana sukayi Shirin Tafiya Tunda Ya Sadam shuru bai dawo ba,Aneesa nata Kiransa yace mata cikin wadanda suka ma aikin ido ne ya samu mtsala sai da suka kara komawa dashi su jiransa nan da Minti Talatin.
Sai dai har Ta wuce bai Dawo ba sai Inteesar tace bari su tafi Ranar Dayake gida Zata dawo ba yadda Aneesa ta iya sai dai taso yazo yaga Munari kila shima yaga abunda tagani ganin zasu tafi yasa tace su Tsaya suyi Hoto in ya Dawo Zata Nunamai haka kuwa akayi sukayi ta Daukan Hoto ta Daukesu Munari da Inteesar da yawa ta Dauka na Munari ita kadai itama Aneesan Inteesar ta Daukesu itada Munarin da Waleeda..
Kana ta Rakasu bakin Hanya suka Hau adaidaita zuwa gida ta basu 2k tace su biya mai adaidaita suka karba suna ta Godiya.
Gidan Mama suka yada Zango da suka Dawo sun gaji gashi Cikin su ya cika sun kasa Tafiya Munari bata koma Gida ba sai da Cikinta ya Sarara kana Inteesar ta rakata Gida,Koda suka je Abba ne kadai agidan Ya Yusuf da Anty Safiya basa nan Bata da Lafiya ashe Tun Safe take amai ya tafi ya kaita asibiti.
Jin haka yasa Inteesar ta zauna Har sai gabda mangariba suka Dawo Jikin nata da Sauki sai da Labari mai Dadi Tana Dauke da juna Biyu na kimanin Wata Uku Ba kunya Yusuf sai murna yake da bakinsa kuma ya Fada ma Abba.
Ana cikin Murnan sai ga Imran ya Fito Daga Dakinsa Da Sauri Yusuf ya Rumgumesa yana fadamai ya kusa Zama Baba sai alokacin Inteesar ta ga yayi Dariya Harwasu Daga Cikin Hakoransa sun Bayyana waje ya Bubbuga bayansa alamun Farincikin.
Su suka Rike Anty Safiya zuwa Shashenta suna mata Sannu Abunda yasa Inteesar ta manta da Abunda ya Faru da ita Jiya har ta kaiwa Bayan Mangariba.
Sai da su Abba suka dawo masallaci ta Tsorata ta tashi tace zata tafi Gida,Yana Dakinsa yaji Tana ma Abba Sallama Daman itace aransa yana Tunanin ta koma gida ko bata koma ba...?.sai yaji mganarta agogon Fatan Dake hannunsa ya kallah 7pm tayi Duhu ya fara Shiga Ransa ya baci ya Fito Lokacin har ta Fice Daga Falon Munari taso ta rakota tace mata ta Zauna Wajen Anty Safiya yau ma ba wayar nata agida ta barta.
Ta fito Gabanta sai fadi take tana ta Waige waige,Taji Tafiya a bayanta da Sauri ta Juya suka Hada ido dashi Sai taji wani Sanyi kamar an yi mata Gafara Tsayawa tayi tana Kallonsa yana Sanye da Riga da wando Baki da Fari,Ta lura blck and White kalansa ne Domin yawancin kayansa kalansu kenan sanan bata taba ganinsa da Manyan kaya ba Tunda ta Fara ganinsa bayan Jallabiya.
Ganin ta Shagala da kallonsa ne yasa ya Tsaya Hannayensa Cikin Aljihunsa yace"In kin gama Kallon nawa sai muje na Rakaki tunda ke baki jin mgana..!
Daga sama taji mganar sa Sai taji kunya ta Sadda kanta kasa Tana Fadin"Bansan Dare yayi bane..!
Da

Please Login or Register in order to submit comment