Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mama ta kama su Imran ta Rike gam kamar ya"yanta Abba kuma yahada kan Iyalansa Waje Daya Sagir Daya kasance Dan Gida ne bai da wata Mtsala Anty Safiya na jin Dadin Zama da Mama sosai Gabadaya Renon Imran karami ya koma Hannunta ashashenta yake wuni Ta Tabbatar ita da Abba zasu kwaceshi ne Ita kanta Anty Safiyan in ba Abba ko Ya yusuf ne ya dawo ba tana Wajen Maman.
Sagir ma shi da Hafsah suna Gidan kusan kullum sai da Abba yayi musu irin na Imran yace su zauna Gidansu kada su kara zuwa kana akaji Shiru Gabadaya Imran Dayaji Labari yana ta Dariya Harda gwalo.
Munari ta Bude musu Group isu isu Ita Hafsah,Inteesar, sajida Nasara da Tasleem Nasara itama an saka Ranarta anan Kaduna Zatayi aure wani ma"aikacin NNPC zata Aura Saura Tasleem da itama Zata Fara Karatu anan jami"ar Bayaron Inteesar nata Murnan ta samu yan uwa sunan Group din SISTER"S FOREVER❤️,Chan suke Haduwa suna Baza Iskancin su son Ransu suna Tadin mazajensu da yarda zasu kara Zama Taurari a Wajensu da bama Juna Shawara Kowa Tana Fadin in Mijinta na kwararamata Ihun Dadi Inteesar taki cewa komai suna ta Tambayanta To ai in Ta Fada ta gama Tona asirin Ya Imu Daya Dade a Lullunbe bazata so kannensa su ji wannan mganar ba ganin Taki Fada suka Zageta suka Kyaleta ita sai dai Dariya kawai.
Ba Dadewa Hafsah ta samu Transfer ta Fara zuwa makaranta ba Depatment daya suke da Inteesar ba haka ma Tasleem data Fara zuwa sai dai kusan Kullum suna Haduwa Tasleem Direba ke zuwa Daukanta ita kuma Inteesar watarana Imran in yazo suna Tare da Hafsah ya Daukesu Dukkamsu in kuma sun tashi da Wuri kowacce Tayi gidanta Domin sun Fara Biya biyen Gidajen kansu ko na Abba Imran ya Tsawatar yace kowa ta Zauni Gidanta.
Sannu Sannu bata Hana zuwa sai dai a Dade ba"a je ba Gashi har Cikin Inteesar ya isa Haihuwa, Tana zuwa awo a wani asibitin kudi Ciki yayi Kato yayi Girman da bata iyama kanta Komai Allah yasa sun samu Hutun shiga aji Uku Daada Dataji Labarin Halin da Inteesar ke Ciki ta Kira Umma Tace tazo ta Dauke yarta ta Haihu agabanta Imran yaso ya Hana sai dai Abba yayi mai mgana Dole ya Kyaleta Daman ta Zama abun Tsausayi Ciki ya hana komai..
Umma tazo ta tafi da Inteesar ta Dawo gabanta ko kwana Goma batayi da dawowa ba ta Haihu a asibitin Barau Dukku Dake kaduna Yan Biyu ta Haifa mace da Namiji masu kama da Imran Murna Wajen Wannan Ahalin sai wanda ya gani Imran kamar ya Zuba ruwa akasa yasha a Kaduna akayi Shagalin suna Yara sukaci sunan Abba da Anni Wato Abubakar da Zuwaira kuma da Abba da Anni Za"a Rika Kiransu,Hafsace kadai tazo suna Sajida da Munari ba wacce tazo duk da sun so zuwa Munari Laulayi ne ya Hanata Sajida kuma Suna Jarabawa Domin ta Fara Karatunta Hafsah kuma Daman Tana da Karamin Cikinta..
Imran yayi bajinta sosai a Haihuwar Inteesar ya siyamata kyauta Mota karama 206na Murnan Haihuwan yan Biyu nan tayi jegonta Cikin Kulawar Umma da Daddy Kamar ya maidata Intee Ciki su Anni kuwa suna ganin gata Bayan Tayi arba"in bata koma Kano ba sai da ta Zaga Dangi sune har Abuja,Gidan Baffa Kabiru sai da suka Kwana Biyu suka Dawo Taje Bauchi Wajen Inna Maimunatu taje Gombe Daganan ta Karisa Dukku Burin Daada ya Cika ta Dauki Ya"yan imran da Inteesar jikokin Malami da Abubakar Sauran Jikokin Malami da Kabiru.
Har Dutse sai da Inteesar taje gidan ya Sa"id bayan dawowarta Daga Kadunna ammh shi ita da Imran sukaje suka kwana Daya suka Dawo Ta Dawo da Kwana ashirin ta koma Bikin Nasara sai a wannan karom Sajida da Munari suka zo murna ba"a mgana da suka Hadu sai Tashin Hira Gabadayansu suna da ciki banda Sajida Da suke mata Tsiyan ko Tana planing ne tace musu AllaH ne bai kawo ba Dukkansu da mazajensu suka zo bayan Biki kuma kowa ya tasa abarsa suka koma Amarya nasara ta tare agidan Mijinta Dake Malali kaduna.
Inteesar mai Taya Reno aka Daukan mata Wata yar yarinya saboda makaranta Mama ta samo mata nan kasansu take kwana wajen Inteesar din sai Weekend take zuwa Gida sunanta Hanne,Inteesar Tana Wahala sosai ga makaranta ga Renon yaran har Biyu ga Ubansu bai iya Komai ba sai fadan in anyi ba Daidai ba.
Sagir ya gama Karatunsa ya Cigaba da Dinkinsa Tunda aikin bai Samu ba suna dai Cigaba da nema.
Ashekaran suka je Lagos ita da Imran da yaran su an Turasu Seminar Gidan Abba suka sauka ba Hotel ba,Tunda Matan Lurwani maigadi suna kula da gidan ko"ina Tsab,Sati Daya sukayi kafin su gama Seminar,Su Inteesar taje Gidan Sajida suma sun zo musu Har Gidan Dr Ali argungun sunje,Bayan sun dawo Sukaje Parthecourt,Harda Sagir da Hafsah suka gano Munari suka Dawo.

******

*MURFI...*!!!
_AFTER 7 YERARS BACK..._

Bayan Shudewar wasu Shekaru Bakwai da suka gabata Ahalin Marigayi Alkali Dukku ayau ya Zama abun kwantance Baffa Kabiru girma ya kara kamasa Tun bayan Rasuwar Daada Shekaru Biyar da suka gabata ammu bata bar Gidan Duniya ba sai da Ta Dauki Jikokin Malami da Kabiru ta kuma Hada kan Zuru"arta Waje daya kafin ta bar Duniya.
Rashinta ya Girgiza ya"yanta sun yi kuka sosai sai dai kuma sun Dauki Girma da Ragamar komai akansu.
Ashekarun da suka gabata an samu Cigaba sosai ta bangaran Haiyayyafa da Karin Girma ayyukan wasu.
Imran ya samu karin Girma daga Assistan Manaja zuwa Manajan Gt brach Dake Lagos inda ya Taba aiki basu da Mtsalan gida ga Gidansu nan suka gyara ya Kwashi Matarsa da ya"yansu suka koma chan da Zama Sajida tafi kowa murna sun dawo kusa da juna duk da shima Khalil din ya samu karin girma, Shekaru Biyu da suka gabata Tunda Inteesar Ta gama makarantar ta,Su da kano sai in sunzo ganin gida ga gidansu suna da Wajen sauka in sunzo garin.
Bayan Haihuwar su Anni haihuwanta Biyar acikin Shekara bakwai Saboda Gwarne Takeyi Data yaye shikenan sai wani Cikin taso ta fara tsarin Ilyali Imu yace sai ya gani Allah ya Taimaketa Hanne na Tare da ita tana kara Taimaakamata.
Daga su Abba karami tazo Tayi mai sunan ya Yusuf suna Kiransa Boy,Sai mai sunan Daddy Mustapha,sai mai sunan Baffa Kabiru,Sai Sagir da Imran yayi mai Takwara yana Kiransa Friend sai Karamarsu mai sunan Daada kuma mai sunan Inteesar suna Kiranta Afiya.
Ya yusuf ya samu karin Girma shima iyalai sun cika Gida,Abba tuni ya gida wani Gaton gida a sharadi phase 1 sun koma da Mama tare da Imran karami da Khadija diyarsu da suka kwace musu, an kara gyara wannan Gidan Sagir ya dawo suna zaune Tare,gidansu kuma sun bama Baba Manu ya dawo nan da Zama Sagir ya samu aiki sai dai har yau har gobe bai bar Dinkin ba domin kome ya Zama Dinkin ne Sila shida Imran suka Hada Hannu suka kara Fadada harka yanzu Manyan Shaguna sun fi goma Cike da kekekuna da ma"ikata yara sai dai Sagir ya Daina Dinkin sai dai yaransa shi kuma Oga sama oga kasa.
Shima sun tara ya"ya shima yayi ma Imran,takwara sai mai sunan Mama Amina da mai sunan Babansa Tasiu.
Munari ma ya"yanta Hudu itama Tayi ma Anni da Abba duka Takwara da Mami Asma"u da Baffa Kabiru Sajida kuma ya"yanta uku ita kuma sai Tayi ma su Inna Maimunatu kara da Inna Bintalo Daada kuwa mai sunanta Kusan kowa nada Daada agidansa.
Nasara ma da ya"yanta Biyu su ya Basheer dasu Sadam duk sun zama magidanta Girma ya kamasu Tasleem ma Tayi aure sai dai kafin haka sai da Kaddara ta Fadamata wani Lecture ya Ribace ya Lalata mata Rayuwa.
Sai daga baya ya aureta bayan ta Tsarkaka Alhaji Alhassan yayi ta kuka Saboda yasan Ishara ne Allah ya Nuna mai Koda ya Tuba.
Gabadayansu Mazan sun Hade kansu Matan ma haka Imran ya Daina shan Taba Kwata Kwata saboda Shekara Uku da suka wuce ya Kusa Mutuwa Hayakin Dayayi ta bankama Cikinsa ya Taba Huhunsa sai da Abba ya Fita Dashi Kasar Amurka Ya kusan Wata Shida akayi mai aiki kana ya warke ya Dawo Gida Inteesar har ta Fara kukan rasa Namijun Duniya sai gashi ya Warke sai dai Tundaga Lokacin ko Warin Taba bayaso shi da ita har Abada.
Su Inna Maimunatu kam sun Zama Goggon gaske Yanzu Baba Asabe suka kama Suka Rike itace makwafin Daada Gidansu na Dukku na nan da Ransa bai Mutu ba Baba asabe na Cikinsa Tare da yan aiki masu Taimaka mata Suna zuwa yin Hutu ko Sallah Duk shekara gabdaya kwansu da kwarkwatansu Baba asabe me Zata ga Iyaalan Daada..?illah dai Fatan su gama da Duniya Lafiya da Fatan Allah ya Jikan Daada da Alkali Hamisu Ameen.
Umaima tayi aure anan Kaduna Wani Dan kasuwa take aure mai kudi sosai har da Danta Daya.



*****
Lagos..

Yau din Ranar Lahadin Karshen mako ne Inteesar na kwance Tana Barci acikin Bedroom dinsu Ta Ninkaye Cikin Bargo Tana barcinta Cikin kwanciyar Hankali Da Salama Daga gani kuma barcin Sauke gajiya ne Domin jiya da Daddaran Ranka shi Dade Imran bai barta ta Huta ba.
Da asuba ma sai da ya kara kafi Siga kafin ya barta ta Kwanta Shiyasa ta baro Dakinta Tunda chan suka kwana Zuwa Dakin Imran saboda bata son yaran su tashi su Dameta.
Suna Tare da Hanne domin Tare da ita suka Taho Duk da ba reno take yi ba yanzu Allah ne ya Hada Jininta Dana Inteesar Da zasu dawo lagos ita da Imran suka Nemi yardan iyayanta suka basu ita suka dawo da ita nan tare da duka yaran suka Hada suka sanya makaranta In baka sani ba sai kace Kanwar Inteesar ce Duk inda Tabi yaran Anty Hanne sama Anty Hanne kasa.
Matan Lurwanu ne megadinsu Dasuke Tare dasu anan Boyquater ke Taimakamata da aiki in yaran sun Tafi makaranta Inteesar bata aiki Tunda Imran bayaso sai dai Tana alfahari da Kwalin karatunta.
Tayi nisa acikin barcinta Taji Kiran Wayarta Dakyar ta iya Zuro Hannu Tana daga kwancen bata iya tashi ba ta Dauko Wayar Daga Side drower din gadon bata Tsaya Duba mai Kiran ba ta Daga wayar Cikin Muryan Barci Take mgana.
Dagachan BAngaran Sajida Mata agidan Khalil tace"Au barci ma kike yi..?kin manta mun ce zamu shiga Kasuwa..?kinfa san Salla ta Kusa ZAmu Tafi Dukku in bamu yi wannan Siyaytar ba sai yaushe..?
Inteesar ta yamutsa Fuska Tana Fadin"Wlh nagaji ne Sajida..Gani nan kwance ammh yanzu zan tashi..Ina Zaki kai yara..?
Sajida tace"Gidan Baba Dr mana..Kema ki kawo su nan Tunda Ubaninsu ba Yadda zasu yarda mu bar musu su ba..!
Imteesar tace"Uhm..aini sai ma na kara Tambayan da nayi mganar bai ce komai ba..!
Sajida na Dariya tace"To ai sai kije kiji da Yayana kuma Saura acre Dole sai an Fita abarsa ya Huta sosai a kula Dashi..!
Inteesar tace"Uhm..Ai wannan yayanki naki sai shi..Gabadaya ya Fara Gajiyar dani..Wnnan ma gajiyar Duk tasa ce..!
Sajida na Dariya tace"Banga Laifinsa ba..!
Inteesae tace"Muguwa Allah yasa Daran yau Khalil yayi miki mugun kamu da sai kin samu Ciiki..!
Sajida Tayi Saurin Cewa"Ba Ameen ba Gwarne ai sai Inteen Ya Imun mu..!
Inteesar ta bata rai kafin Tace"wlh ina nan a Inteen Daddyna..!
Dariya suka saka gabadaya kafin su yanke Kiran Muskutawa Tayi ta gyara Kwanciyarta Inteeear din kamar ba ita ta Haifi Zaratan ya"yan nan ba.
Bata kai ga komawa barcin nata ba Ta sake jin kiran Wayarta Idanuwanta suna Rufewa saboda barci ta Daga Kiran Tana amsawa cikin Shakewar Murya.
Hajiya Munari mata agidan Khamis Kabir Dukku tace"Ke lafiyanki kike min mgana kamar me maye..?
Inteesar tace"Ai gwara me mayen a kaina..Yayanki zai kasheni Mu..!
Munari ta Kwashe da Dariya Tana Fadin"Su Ya Imu manya..Ina zai Daga kafa ai wajen akwai danko..!
Zagi Inteesar ta Dora mata kafin Tace"Allah nifa ina jin ku ne gwara Kowa da Mijina..!
Munari tace"Uhm naki dai kika sani..Kowa ma nashi ya sani..Nifa da samun cikin nawa kamar Ya Khamis zai Haukacemin Wlh Watarana Har Tsausayi yake bani..!
Inteesar tace"Kidai ji tsoron Allah..Kuma naji Sajida tana Fadamin kin ma Yaya Zainab din goggo Maimunatu mgana zata zo mana da kayan Da"a A dukku..?anya Munari zan karba kada na dawo ina Kuka Ina Rokon ya Imu zai kasheni..!
Munari ta Kwashe da Dariya Tana Fadin"Banza kizauna shine auran aie..Wlh wannan nanikewar matarba ce Intee..Gwara mu sha ance in kana da kyau ka kara da wanka..Gwara mu gyara dA haka zamu katange mazan mu Daga matan Bariki..!
Su Hafsah ma duk sun ce suna so fa Ya Sagir ai shima ba Dama..!
Inteesar ta sauke Numfashi Tana Fadin"Ke dai yi a hankali kina da ciki..Ba kyau kina wannan banke banken..!
Munari tace"Ke ni kyaleni Gwara na banka..Domin na kara Rikitashi Ina nan cikin arna da yare ina Kwato mijina suna Lasan Lebe daga waje..!
Inteesar tayi Dariya Kafin tace"Ina yarana..?
Munari tace"Sun fita da babansu yawon gari tun dazu..!
Inteesar tace"Nima yanzu zan tashi kasuwa zamushiga da Sajida..!
Munari tace"Ta Fadamin dazu da mukayi waya..Yanzu har kasuwa Ya Imu ke barinki..!
Inteesar tace"Kada ma ya barin ya gani..!
Munari tace"Allah..?wato ki matse Cinya ko..?Allah Sarki Zan sauya Miki kammani an yi Laushi Ya Imu Duniya..!
Ta Fada Tana Fashewa da Dariya Zagi Inteesar ta Dankara mata kafin ta yanke Kiran Tana Dariya Munari sai Allah ya shirya Khamis ai na ganin Duniya.
Ta koma kenan Taji kuka da Haniya a saman kanta kafin ta ankara sun Hawo Gadon da Gudu Afiya ce mai kukan Tana Fadin"Ummi..Ummi..
Kinga ya Abba ko..?
Take Fada Tana kuka Mai sunan Baffa Kabiru da suke kira Baba ya rika Jaye bargon yana Fadin"Ummi ki tashi ga Ya Abba chan na Dukan Ya Boy a Falo..!
Ai jin Haka yasa ta Mike bata Shirya ba Tana kallon ya"yanta kansu Daya Afiya Dake kuka ta saka ajikinta,Sai Baba Data Dafa kansa Ta juya tana kallon musty mai sunan Daddy Dake gefenta yayi kwal kwal da ido Shi akwai Tsoro kamar Farar Kura
Cikin bacin rai Tace"Me yayi mishi Dayake dukansa..?
Kawai sai ya saka mata kuka yana Fadin"nima bansani ba Ummi..!
Sai suma Sauran su saka mata kuka Daga ganinsu a Tsorace suke suna Bala"in Tsoron ya Abba baya Musu Dakyau in ya Fara Dukan Mutum bayaji baya gani yari dan Shekara Takwaas sai Bakar Zuciya irin ta gado.
Ranta ne ya baci ta kallesu Tana Fadin"Kumin shuru..Ina Anty Hanne..?
Baba yace"Tana Tiolet Ummi..!
Karamim Tsaki taja Tana Sauki Daga kan gadon Dauke da Afiya Take fadin"Ina Abi..,?
Wannan karon Musty ne yace"Yana Study Room yace kada wanda ya Damesa..!
Inteesar ta zura Bedroom Shoe dinta ta Fice tana Fada yaran sukabi bayanta Tafe take Tana Fadin"Wato kada a damesa ni kuma azo a Dameni kenan..?
Take Fada har suka iso Tafkeken Falon suna zuwa Daidai Lokacin da karamin yaro ya saka kafa zai Taka wani yaro Dake kasa kwance bazai wuce shekara Shida ba yana kuka Anni yar Shekara Takwas Tana gefe Zaune ta Ragume Idanuwanta sun Fito Saboda Tsoro Itama Tsoronsa Take ji Duk da abokin Tagwayenta ne
Tsawa Inteesar ta Daka mai Hade da Kiran sunansa.
"Abubakar...!
Da karfi Har sai da Imran Dayake Study Room yana aiki ya Jita Hanne Dake Tiolet itama Ta Jita da Hanzari ta Fito samin Halinta ta kuma san yanzu Zai ci Duka bari taje ta Kwaceshi bakar Zuciya garesa ko Kashess za"ayi bazai mtsa Daga Inda yake ba.
Jin kiran sunansa yasa ya Tsaya Cak yana Sauke Numfashi kamar wani Zaki Boy ganin Ummi yasa ya Tashi ya Nufeta yana kuka Jikinta ya Fada ta Rikesa Sauke Afiya Tayi Daga Jikinta ta Tarbi Danta Anni ma wajenta Tazo Tana Kifta ido tana Fadin"Ummi Aljanun Ya Abba sun tashi..!
Kamar ta maketa haka take ji yarinya sai Tsoro da Shagwaba kamar Abba Dukanta yake ya gama Raina ta wanda suka Fito Duniya Rana Daya.
Rankwashi ta bata saman kamta Tana Fadin"Matsa ki bani Wuri babban banza wawiya kawai..!
Gefe ta koma Tana Hawaye Dafe da kanta Dake Cike da suma.
Mikewa Tayi a Fusace ta Nufesa Ta saka Hannu ta Juyosa yana Cika yana Batsrewa Mari mai kyau ta sakarmai kafin tace"Don Ubanka me yayi maka Daka ke Dukansa kamar Zaka Kashehi..?
Tafada cikin Fushi da bacin rai,Yana Tsaye kikam yaki mgana sai Faman Huci yake abunda ke kara mata Bacin Rai kenan ta kara kaimasa Duka Tana Fadin"Ni zaka nuna min Zuciya..?Sai na maka Dukan Tsiya acikin Gidan nan naga mai kwatanka..!
Tafada Cikin Fusata Sagir ne yayi mgana yace"Ummi fa takan muna wasan Buya shine Ya Boy ya Boye adakin Ya Abba shine shine fa ya Fara Dukansa wai yayimai ihu akai..!
Baki ta Rike kafin tace"Eh Lalle sannu..waye kai da baza ayi maka Ihu ba..?Abubakar imran Abubakar ko..!?To ko Ubanka yanzu ya Hakura da Hayaniyar yana sonta wlh in baka Daina Tada Bakar zuciyar nan ta gado kan ya"yana ba sai naci Ubanka acikin Gidan nan..!
Ta fada Tana Murdemai kunni Daidai Lokacin Imran ya Shigo Falon bayan ya gama jin Abunda ya Faru gabanta ya Tsaya ya Riko Abba Dake Fama da Zuciya yace"Basai kin sha Wahala ba au ga Uban nasa sai kici da Hujja..!
Yafada yana Jefa mata Harara Dagowa Tayi Tana kallonsa batace komai ba ta kauda kanta Yaran suna ganinsa suka Rufesa gabadaya Fada ya fara yi musu yace su bama Abba Hakuri Kunne suka kama suna Fadin"We are Sorry Ya Abba...!
Ko kallonsu bai yi ba Imran ya Dafa kansa yana Fadin"Sun ce kayi Hakuri ok..?kai gyada Fuskarnan ba Fara"a Kumatunsa ya Shafa yana Fadin"Kadaina Sauke wannan Fushin naka kan kannen ka kaji ko..?ko ni da ake ma Gorin kayo Gadona bana Duka haka Kurum sai an Shiga Sabgata yara ne ka rika Musu Uzuri babban yaya kaji ko..?
ko kuma ku daina Mai abunda baya so kunji ko..?
Gabadaya suka gyada kai suka ce "Yes Abi..!
Kansu dukkansu ya shafa yana saka musu albarka Hanne ce ta Fito suka Nufeta suna Kiran sunanta Abba ya juya yana wani Taku kamar Imran ya shige Dakinsa Imran ya Bisa da kallo yana Mirmishi.
Hanne ta gaisheshi ya amsa mata cewa yayi ta shirya su Gidan Baba Dr. Zasu je yanzu jim haka yasa suka Fara Murna suka kwashi Gidu zuwa Dakinsu Hanne ta mara musu baya Dauke da Afiya Inteesar Tuni ta koma Dakinta Domin ta Shirya.
Imran ya mara mata baya Inteesar ta Rainasa batajin mganarsa Yana wannan Takun nasa Hannayensa Cikin Jallabiyan Jikinsa bai sauya ba sai ma kara Zama wani Matashi mai ji da Komai na Rayuwaa daya zama.
Yana shiga Dakin yaganta Daure da Towel iya Cinyarta Zata Shiga wanka Taji Shigowarsa ammh bata Dago ba Kokarin Nannade gashinta take Waje adaya bata san Jikashi.
Agabanta ya Tsaya yana Fadin"Kin kyauta..Na kuma gode da rashin jin mganata..!
Ido ta sakarmai kafin tace"Uhmm..Ina jinka me kuma nayi Sarkin Laifi..!
Yana Hade rai yace"Ni kuma Sarkin Fada ba..Wlh sai nayi mgana in naga anyi ba Daidai ba..!
baki tabe batayi mgana ba Cikin Bacin rai ya Cigaba da Fadin"sau nawa zan Miki Fadan ki Daina ZAgin yaran nan agabansu..?in ranki ya baci zaki Hukunci kina gunduma Ubansu Zagi suna jinki kinsan yaro da Daukan abu kuwa..!sai ya Zata mai kyau ne ya Dauka na Fadamiki ki Daina Bana so bana so ammh Kin Rainani kin maida mganata banza Bansan yaushe kika koyi irin wadandan manya manyan ashariyan ba.!
Batadai ce komai ba ganin haka yasa yace"baki son fada...Kuma nikam naga an yi ba daidai sai nayi mgana Kinsan Halina..!
Sai da ta gama jinsa sannan Tace"Naji Zan kiyaye ina so nayi wanka. kasuwar da na gayamaka zamu je da Sajida..!
Tafada Tana kokarin juyawa ya Fizgota sai gata kan Kirjinsa riko Kugunta yayi yana Kallon Fuskarta Cikin Wani irin Murya yace"wanka..?aai baki ga ta wanka ba..Bakin ce Zaki ci Ubansu ba gani nazo ki cini..Basai kin Wahala ba na kawo miki kaina..
Ido ta waro kafin ta Tura baki Tana Fadin"Ni fa ba ce ba..!
Yace"Me kikace..!?
Yana zagaye bakinta da Yatsunsa Hannunsa Dayan hannun nasa na Wasa da Tudun Hip dinta gabadaya ya Fara Rikitata dayasa itama ta Fada Jikinsa ta kamkamesa shima Riketa yayi yana Fadin"Ki bari ki gama cin Ubansu din kafin ki Fita Kin ji Matata..!
Inteesar na Dariya Tana sunne kanta Tace"Ni fa ba haka nake nufi ba..!
Imran yace"Uhmm to yane..?ai ko baki Fada haka din ne..!
Dariya ta saki kawai batayi mgana ba Janta yayi suka Fada kan gado Cikin Bargo suka Shige kafin ya Rabata da Towel din Jikinta yana Fadin"Mu ci Uban juna Kin ji Inteen Imu..!Babu mai ce ma meyasa..!
Yafada yana dariya Kara Nanikarsa Tayi Tana Farincikin Lokaci Daya Tana Fadin"I Love u so Much..Imun Intee..! tafada tana Kokarin Rabasa da kayan jikinsa
Shima yana Kokarin Tayata yace"Love u so much..So Much Much Inteen Imran Shi kadai Yar albarkata yar Aljannata uwar ya"yana Matata wacce ita kadai ce Burina wacce ta iya zama Dani A yadda nake Tun ina Dan jagaliyana mai shan Taab...!
Bata bari yaKarisa ba Ta Hade bakinsu Waje daya sai da sukayi sumba mai Tsawo kafin ta Saki bakin Ta Lafe Bisa Kirjinsa Tana Fadin"Ka Daina Fada..Ni nafi kowacce Mace a sa"a Duk wacce ta samu kamar Gwarzon mijina kawai tayi irin nawa Tace ALHAMDULILLAH..!
IMRAN na kallon Cikin idonta yace"Nima ko ina Fatan duk Namijin Daya samu Mace kamarki mai Shagwaba mara son Fada mai Kishin Mijinta Kawai yayi irin nawa yace ALHAMDULILLAH..!
Atare suka saki Dariya suka Rumgume juna Bakinsu suka Hade Waje Daya lokaci Daya ya Mirginata ta Dawo kasansa.
Daganan na juya ya sakayo musu Kofar na Sauke alkalamina na Sha Ruwa na Sauke Numfashi nima nace ALHAMDULILLAH...!


*Tammat bihamdullahi Godiyata Ta tabbata ga Allah Subanahu wata"ala daya bani ikon Fara wannan Littafin Lafiya na kuma gamashi yau Lafiya Allah ne abun godiya Tsira da aminci su kara Tabbata kan Fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu Salallahu Alaihi wasallam,Tare da Iyalansa da Sahabansa gabadaya Ameen summah Ameen..*

_Bazan Rufe wannan Littafin ba sai na Mika Dukkan Godiyata da jinjina kan Masoyana masu son cigabana Masoyana da suka Taru suka nuna min kauna Wajen siyan wannan Labarin Da kuma yadda suka yi jimarin Bin Rubutuna Tun daga kashi na Farko Har gashi yau mun kamallah kashi na Biyu Wato GMB2BANDGROUP Hakika naji Dadi kwarai Allah ya saka Muku da alheri Allah ya Biyaku Allah ya bar Zumunci Allah ya kara Hada Fuskokinmu da alheri,Sannan ina Neman afuwarku Kusan Dukkan Dan Adam Tara yake bai cika goma ba Allah ne Kadai Dari Bisa Dari ni Mutum ce kuma yar adam ce mai Rauni mai Kuskure in har a wannan Rubutun na bata ma wani ko wata don Allah ku yafemin kila akwai inda na Kuskure muku ko inda baku so haka ba to kuyi hakuri Ajizanci ne na Dan Adam ni ban isa nayi shi Dari bisa Dari ba Ina Fatan Sakon da kuka karanta zaku amfani da Darasin Dake Ciki akasinsa kuma ku Watsar Dashi Allah ya yafemana Kurakuran da mukayi Cikin wannan Rubutun ya bamu Ladan Dake Cikinsa Nagode kwarai da gaske sai Allah ya kaimu bayan Sallah da Rai da lafiya akwai Alkawarin Goron Sallah da nayi muku Da yardan Allah zan cikashi Zamu Fada Labarin SUNAIMA da MIJIN KANWARTA daya zama kaddaranta Shin wata irin kaddara ce..?kada ku Damu zamu fara wannan Tafiyar in muka gama azumi Lafiya Allah ya bamu Dacewa da Yantuwa acikin wannan Watan Allah ya Sa muna Cikin Salihan Bayi Ameen ya Allah Tanque all..._







*Janaftyshakira*
*31/03/2022*
*Intelligent writer"s ass*
*GMB2ONELOVE*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da

Please Login or Register in order to submit comment