Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gefe sai da kanta ya Bugu da kujera ji kake kum,Wanda ta saka Dole Munari ta saki marayan kuka Tana Fadin"Wayyo Allah na Ya Imu don Allah kayi Hakuri..Abba..Ya yusuf Ku Taimakamin..!
Take Fadi Tana kuka Abba bai Motsa ba Shima Ransa ya Baci Yusuf ne ya Riko Imran din Cikin bacin rai ganin yana Shirin kara Bin Munari ya Taka da Takalmin kafarsa,Safiya kuma Baya taja Tsoro ya kamata gashi Tana son Isa Wajen Munari Tana Tsoron kada Itama ya Illatata.
Ya Rikesa Sosai yana Fadin"Imran Wht is your Problem ne..Abba na maka Mgana ka maidashi Banza..? Me tayi maka kake Dukanta kai baka jin kunyar Dukan mace..? Macen ma Kanwarka Wacce baka da kamarta..?
Imran ya Kallesa Idanuwansa Jajir kafin ya Kwace Jikinsa yana Fadin"Ina mgana tana cemin baa Haka ba..?Zan mata karya kenan ko..! Ni ina Wasa da ita ne zata Rika bama Wannan yarinyar Labarin ina Sumar da Mutane..? Yusuf Let me Tell ur wani Abu bana son na Bata ma wani Rai Shiyasa bana shiga Shirgin da ba nawa ba..Nima na Tsani ka batamin Raina Saboda BANA SON RAINA YANA BACI..!
Yafada Cikin hargowa Lokaci Daya yana Wani Buga Kafarsa ya Cigaba da Fadin"Zan Cigaba da Dukanta Har sai ta Suma sai taji dadin bada Labarin ina Sumar da Mutane..ina na kara ganinki da wannan Yarinyar sai na Illataki..Nonsesses kawai..!
Daga haka kawai ya Daga Kafa ya wuce Fuu zuwa Dakinsa ya Shiga ya Banko Kofa ji kake Bam! Kamar zai Ballata Abba ya Jinjina kai kawai ya kasa cewa komai Yusuf ya Kallah wanda ya Daga Munari Dake ta kuka ya kalli Safiya yana Fadin"Kamata Don Allah..!
Da Sauri ta Riketa Tana mata Sannu Cikin Tsausayawa Abba ya Juya yana Fadin"Mu tafi masallaci Yusuf..!
Ba Musu yabi bayan Abba suka Fice ita kuma Safiya ta kama Munari zuwa Dakinta sai da suka Shiga ta Rufo Kofar take Fadin"Kema munari me ya aike ki bama Intee wannan Labarin gashinan yaje kunnunsa yanzu..!
Munari na kuka Tana Dafe da goshinta Inda Har ya Sumtuma tace"Wlh bansani Ba Anty Safiya..Bansan zai ji Labari ba da ban Fada mata ba..!
Safiya tace"To ita ya akayi ma ta gansa Har ta Fadamai..?
Munari na Sharan Majina tace"Bazai zama ita ta Fadamai ba..Sai dai in Tayi Zencen da Ya SAgir ne shi kuma Cikin mgana ya Fadamai kuma zai kawo nice..Daman ga Haushin Abunda Intee tamai Duka ya Hada ya Huce akaina Da kuma Haushin kawancen da muka Fara da ita Saboda yamin kashedin kada na yarda nayi kawa da kowa..Anty Safiya Taya zai ce kada nayi kawa ni ba Mutum bace da bana son Farinciki..?ko kuwa shi ba Abokin garesa ba Shi wa ya Takuramai..?
Ta Karishe Fada Cikin kuka da Tsausayinta ya kama Safiya ta Rumgumeta ta bata baki DAkyar ta Lallasheta Tayi Shuru,Ta Dauko man Zafi ta Shafa mata agoshinta Bayan ta Sake alwala ta Fice ta barta Tana Kokarin Tada Sallah Itama Shashenta ta Shiga Domin ta gabatar da Sallah aranta Tana Tunanin Duk iya Hasashenta kan Imran ya Wuce Yadda Take Tunani ko take Tsammani.
Su Abba basu Dawo ba sai Bayan Sallar Isha"i suna Fitowa Daga masallaci suka ga Imran ya Fito yana Saka Takalmi ya Sauya Kaya Daga Riga da Wando Zuwa Wata Bakar Jallabiya Sagir ne ke mai mgana yayi banza Dashi ya wuce kamar zai Tashi Sama Dashi akayi sallar mangariba Duk da Raka"a Daya ya samu sai ya Rama Sauran ya Tsaya Har akayi Sallar Isha"i yana Sahun baya ne Shiyasa su Abba basu Lura dashi ba.
Sagir ne ya gaisa dasu Abba.
Abba ya Dafa Kafadansa yana Fadin"Ka Rabu dashi Yau Zuciyar tasa ne tatashi Har gobe da wannan bakar Zuciyar sai wayi gari..!
Sagir ya Kada kai yana Fadin Allah ya kyauta da haka sukayi Sallama ya Nufi Cikin gida Duk da ya Damu yana Tunanin kan mganar Daya Fadamai n in bai Kuskure ba komai zai Dawo kan Munari ne Domin zai ce ita ta gayama Inteesar Tuna Haka da yayi ne ya Dafe kansa yana Fadin ya Illahi me na aikata ne..? Nafi kowa sanin Imran in Ransa ya baci kamar Mahaukaci yake..Kada yaje ya Duke yar Mutane fa..!

Abba bai Tada mganar ba har bayan sun Dawo sai da suka gama Dinner kana ya Taka da kansa Har Dakin Munari Domin taki Fitowa tace ma Safiya ta Koshi kan gado ya ganta Dukunkune Cikin Bargo Tana kuka bata ma san ya Shigo ba sai da ya kira Sunanta kana ta Dago Tana Kallonsa Cikin Dattakonsa ya Zauna Gefenta yana Fadin"Tashi Zaune mgana zamu yi..!
Ba musu ta yaye Bargon Data lulluba Dashi Lokaci Daya tana Sharan Hawaye.
Goshinta ya Shafa ganin ya Kumbura yace"Yana Zafi ne Munarin Abba..?
Kai ta gyadamai sai ga Hawaye Sharr Rumgumeta yayi yana Fadin"Kiyi Hakuri..Shii.Daina kuka kin ji ko..?
Kai ta gyada mai shi kuma ya saka Hannu yana Share mata Hawaye Lokaci Daya ya Dagota yana Fadin"Kalleni nan Maimunatu..!
Kallonsa Tayi shi kuma ya Tallafe Fuskarta yana Fadin"Menene Matsayin Imran a wajen ki..?
Cikin Sanyin Murya tace"Yayane Abba..!
Abba ya jinjina kai kafin yace"Duk abunda zai yi miki bai isa yace baya Sonki ba. kema baki isa ki Cire wannan Jinin daya Hadaku ba Munari..Imran baya Shiga Shirgin da bana nasa ba..Kuma baya Duka ko Fada Indai ba"a Tabasa ba. Ko..?
Kai ta gyada mai Sai ya Cigaba da Fadin"Ba ina Shigarmai bane A"a Sai don ina so na Nuna miki Laifinki D'aya a wannan abun..Shine kin yi Rashin Wayau Munari..Imran Dan'uwanki ne na Jini  da kuke Zaune Gida Daya..Inteesar kuma Kawarki ce da kuka Hadu ba da Dadewa ba..Bai kamata ki gayamata abunda ya Shafi Imran ba Munari..Menene naki na Labarin yana Duka har ya Sumar..? Waya taba sumarwa..? Marigayiya Asma"u?itama Lokacin Harkansa ta Shiga ta batamai rai ya Zuciya ya Nausheta aciki sai abun yazo da Tsautsayi ta Fadi ta suma..bayan ita kin karajin ya Sumar da wani ne..? sai dai Hargowansa in aka batamai rai..Nasan bai da kyau yana da Bakar Zuciya irin ta Fulanin Da suka Fito Daga Dukku ammh duk da haka bai kamata ki Zubar da kimar Dan"uwanki Data gidanku ba Munari..Wannan Labarin sam bai Dace kuma baki kyauta ba..Inteesar Zata Raina Yayanki Duk da nasan bazata aikata haka ba na yarda da Tarbiyanta ina mata kallon Kamar kice Munari..Ammh Duk da Haka abunda kika aikata bai yi Daidai ba sam..!
Ya kariahe Fada Cikin Taushin Murya Munari Data gano Laifinta tace"Hakane Abba ban kyauta ba..Nima ba da wata Manufa na gayamata haka ba..Insha Allahu naji mganarka bazan Kara ba..!
Abba yaji Dadi ya jinjina mata kai kafin ya Saketa yana Fadin"gud Munarin Abbanta..Yanzu kimin alkwarin da Safe in ya Huce zaki Bashi Hakuri..!
Da Sauri tace"Insha Allahu Abba zan bashi Hakuri..!
Abba ya Dafa kanta yana Fadin"Allah yayi miki albarka..Dake da Yayyinki Gabadaya..!
Munari ta amsa da Ameen Kafin ya Mike ya Fice ta Rakasa da Kallon Kauna Har ya Fice kafin ta koma ta Kwanta Shiyasa take son Abba yana da Saukin kai sosai bazai maka Fada ba sai dai cikin Sauki zai ganar Dakai Kuskuranka ta gano Laifinta kuma da yardan Allah Zata bama Ya Imran Hakuri da Safe kafin tatafi makaranta.

*****
Washegari ta kama Monday ne Karfe 7:30am na safe su Munari keda Lacture,Shiyasa ta Shirya da Wuri Safiya ta Hada Breakfast,Tea kadai tasha da Bread,Yusuf ma ya Shirya Cikin Suit Baki da Fari na Tafiya Wajen aiki Dukkansu a tare sukayi Breakfast banda Imran wanda Tun Jiya Daya Dawo Masallaci ya Shige Dakinsa ba wanda yaji Motsinsa.
Munari ta Fara Tunanin ta Bugamai kofa ne sai kuma ta Fasa sanin Halinsa kar ta kara wani Laifin Suna Shirin Tafiya yau Ya yusuf Zata Bi ya Ijiyeta makaranta sai ga Imran din ya Fito Sanye da Wando 3Quater Ba Riga ajikinsa bai ma kowa mgana ba Abba kadai yace ma Ina kwana Anty Safiya ma na gaisheshi yayi kamar bai jita ba ya Wuce Kitchen.
Yusuf Dake Tsaye ya Mika mata Hannu ta bashi Briefcase dinsa ya karba yana Fadin"Kada ki kara gaisheshi..Kanina yake ba Yaya yake gareni ba yadda Zai girmamani haka kema zai girmamaki Anty Kike a wajensa..!Safiya taji abun wani iri batace komai ba ammh aranta tace ban matsama kaina ba da sai ya kirani Anty ba
Imran Daya Fito Daga Kitchen Dauke da Goran Ruwa ,yaji Duk Abunda Yusuf yace bai nuna ma yaji ba sai ma kara Dakuna Fuska da yayi zai Wuce Munari Dake gefe Cikin Shirin Fita tace"Ya Imran gud mrning..!
Cikin Dari dari..Bai ma ko Sanda da ita ba ya Rike marikin kofarsa kana ya Juyo yana kallonta Da Sauri ta rike kunnuwanta Kafin tace"Am Sorry Y Imu..Bazan karaba Plz..!
Yadda tayi ne yasa sai yaji kuma Zuciyarsa Tayi sanyi dan Fuska ya saki kafin yace''Is ok..!
Daga haka ya bude Kofarsa ya Shige ya Rufe Abba Dake saman Dinning yana Karisa karyawa yace"Hallayarsu suna min kamanceciniya da juna..!
Yusuf yace"Abba da wane..?
Abba sai da ya Dade bai yi mgana ba kafin ya kada kai yana Fadin"Baffanku..Ya Kabiru..Barrister Baban Khamis da Sajida..!
Daga Yusuf har Munari ba wanda ya iya mgana saboda yadda Jikinsu yayi Sanyi balle Safiya Dake gefe aranta Tana Tunanin yanzu Abunda ya Rage ma wannan gidan kenan su Koma ga Ahalinsu kuma tayi wannan alkawarin sai ta cikashi da yardan Allah.
Sallama sukayi ma Abba suka Fice,Safiya ta Rakasu har Haraba suna Fita Daga Gidan Inteesar ta Kira Munari tace tana Kofar gidansu Sagir Tana Jiranta su Wuce sai ta Rasa me Zata ce mata tana jin kunyar tace mata ta Wuce alhalin kwanakin nan Duk Tare suke Tafiya.
Yusuf ne Dayake jin mganar Inteesar din ta Cikin wayar Domon Volume din wayar yana Cike ne yace"Ki gayamata gamu nan zuwa zamu Dauketa..!.
Cikin mamaki ta kallesa sai ya Gyada mata Kai Lokaci Daya yana Sakar mata Mirmishi da Sauri ta Fadama Inteesar din ga sunan zuwa ita da Ya Yusuf zai kaisu makaranta kafin ya Wuce Office.
Haka kuwa Akayi suna zuwa Kofar Gidan suka ganta Cikin Shirinta yau kamar sun Hada baki dukkansu Hijabai suka saka Inteesar ta Bude Bayan Motar ta Shiga sai da suka Fara Tafiya kana ta gaida Ya yusuf ya amsa mata Cikin Sakin Fuska,yana tambayanta Karatu ta amsa da Alhandulillah nan yace su Dake Allah ya basu sa"a suka amsa da Ameen Inteesar nata kallonsa Itafa Har yanayi yake mata da Ya Basheer in yana mgana.
Har bakin Department dinsu yakai su kana Ya basu 1k yace su siya abinci suka amsa suna Godiya kafin yayi Riverse ya juya ya Fice Daga makaranta ya Dauki Hanyar Ma"aikatansu Lokaci Daya yana Duba agogon Silban Dake Daure a Tsitsiyan Hannunsa.
Intee bata lura da Kolin goshin Munari ba sai da suka Fito daga Lacture Data Tambayeta sai tace mata kume wa tayi da Kofar Tiolet dinta Inteesar ta nuna Tsausayawa sosai har tana ce mata ko zasu je asibiti ne.Munari ta nuna bakomai ammh bata yarda ta gayama Intee komai ba Sai ma Intee din take bata Labarin jiya Bayan ta Dawo Daga Rakata ta ga Ya Imran da Sagir ta Shige gida da Gudu Munari Mirmishi kadai Tayi batace komai ba.
Ranar sai 5pm na yammah suka gama da Makaranta suka Dawo gida,Daga Bakin Titi suka Sauka suka gangaro Inteesar ta Fara Shigewa ita kuma munari ta karisa gida Bayan tasha Labarin zuwan Daddyn Inteesar din a Bakin Inteesar din yau a makaranta Itama sai taji tana son ganinsa ko Domin Tasan Yana Son Inteesar Shiyasa yake Shagwabata.







*Shakira..*
3/22/22, 23:06 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️*


             *🅿?21*

Cikin satin kaf  Ya yusuf ke kaisu Makaranta kafin ya wuce wajen aikinsa Dayake kuma an ci Sa"a duk Lacture din safe garesu,ranar jumma"a ne kadai suka tafi da Kansu saboda sai 10am suka shiga makaranta na Safe.
Wannan karamcin na Gidansu Munari Inteesar na matukar jin Dadinsa Har Daddy da Umma sai da ta bama Labarin Yayan Munari ke kaisu makaranta Kullum Duk yadda kaji wani na son naka ko yana Hidima Dashi kaima Dadin haka kake ji Abunda ya Faru da Umma da Daddy kenan Shiyasa yayi alkawarin Tabbas in yazo Inteesar zata Rakashi Gidansu Munari yayi musu Godiya.
Ranar asabar ba makaranta Tun Jiya da Daddare Daman yusuf yace Safiya ta Shirya ita da Munari zasu je anguwa Shiyasa Tun Safe suka gama Duka ayyukansu bayan sun gama Breakfast suka yi Luch suka Zuba a Kula suka Rufe Kafin su dawo.
Karfe 11am na Safe suka Fita Suka bar Abba da Imran agida wanda Gudu kadai ya Fita yayi ya Dawo gida ya Shige Dakinsa Abba kuma na Falo yana kallo Yana Debema kansa kewa.
Ashe gidansu Safiya zasu je sai da suka Dauki Hanya yake gayamata Farinciki ya cikata Duk da Tana waya da Mommy da Tasleem ammh Tana Bukatar zuwa ta gansu Duk da Tasleem din na zuwa wajenta Lokaci Bayan Lokaci in Mommy ta aikota da Wani Sakon,Bata da Mtsala da su Abbu ne mtsalanta Domin Tunda tayi aure basu Taba Haduwa ba Ta taba Kiransa Sau Daya a waya yace Kada ta Kara Kiransa ta Zauna Gidan auranta Tayi ma Mijinta Biyayyah.
Sun ko ci Sa"a Alhaji Alhassan yana Gida yana Sama yana Hutawa suka iso Mommy da Tasleem suka kasa Zama Saboda Murna suna ta ina suka Saka da Yusuf da Munari Mommy kuwa Bakinta kamar zai Tsage saboda murnan ganin yarta Tayu cikar Daki wanda ganin Farko zakayi mata ka Shaida Bata cikin Wata wahala ballatana Damuwa.
Kafin kace kwabo an cika Gabansu da abinci da abunsha,Tasleem Taja Munari Dakinta Safiya kuma Tana Dakin Mommy sai aka bar Yusuf kadai afalo.
Safiya ta kalli Mommy Daidai Lokacin Datake Zama gefen Kayattacen Gadon Daya Malale Dakin tana Fadin"Mommy Abbu baya gida ne..? Naga motarsa a parking space..!
Mommy ta tabe baki Tana Fadin"Yana Nan..Bai fito bane yana sama yana Hutawa..!
Ta Bude baki Zatayi mgana Hajiya Mero ta yanketa tana Fadin"Kin mai mganar zuwa gidan kakanin naki Rijiyar Zaki da gidan Yaya Saratu..?
Safiya tace"Eh na gayamai Mommy yace Zamu je to bansani ba ko duka Tafiyar yau ta yuyu Tunda kinga Rana mai kama ta yau yake samun Hutu..Tunda Sauran ranakun sun siyar ma gwannati Lokacin su..!
Mommy tace"Hakane kam..Kudai yi kokari kuje Alhaji da Hajiya suna ta mganarki..!
Safiya tace"Tom Mommy ai Dayake ma muna mgana dasu ta waya..!
Mommy ta Mike tana Fadin"Haka Hajiya tace min..Ki je Falo wajen Mijinki kada ki barsa Shi kadai..!
Safiya tace"Mommy Abbu fa..? Bazai Fito su gaisa da Yusuf ba..?
Mommy ta bata rai kafin tace"Shi ya ma Taba Tunawa Dake ne..?ki Rabani da mganar Mahaifin da baisan Darajan Ya"yansa da Hakkinsu Dake kansa ba..Ni kuka zo Dubawa kuma nagode ku gama abunda zaku yi ku wuce ku tafi bana son ma ya Fito ya ganku..!
Safiya bata samu Zarafin mgama ba sukaji Muryan Alhaji Alhassan yana Kwalama Hajiya Mero kira atare suka Kalli juna kafin dukkansu su Kama Hanyar Fita Daga Dakin.
Suna Fitowa Falo suka iske Yusuf duke a kasa ya sauko Daga kan kujera kansa na kasa Alhaji Alhassan kuma yana Tsaye da Jallabiya yana Mazurai..
Hajiya Mero ta Hade rai Tamau ta Nufeshi Tana Fadin"Gani Allah yasa Lafiya..?
Yabude baki zai yi mgana sai Lokacin yaga Safiya Dake bayan Mommy Baki ya Saki yana Kallonta ita kuma kanta ta Sadda ta karisa kusa da Mijinta ta Durkusa Tana Fadin"Ina kwana Abbu..!
Kada kai yayi sai Lokacin ya gane Yusuf ne yaron nan don da Farko Daya Sauko Yusuf din ya Duka yana Gaishessa bai wani ganesa ba, Tunda ba wani Tsayawa yake yana Kallonsa ba Koda yazo wajen Safiyar a baya.
Maida mganarsa yayi Cikin Cikinsa ganin Haka yasa Hajiya Mero ta karisa kusa Dashi kasa kasa Tana Fadin'"Yanzu ai kagane ko waye ko..?
mijin yarkace Safiya da kayi ma Auran Kaskasci Ma"ana Surukinka yazo yayi maka Godiyan Aura masa Safiya da kayi ne..Sai ka Natsu..!
Tafada Lokaci Daya tana Hararansa Tana kuma Dagowa sai ta Murmusa Tana Fadin"Ku tashi ku zauna kan kujera mana..Yusuf ai nan din ma Duk gida ne ko Alhaji..?
Alhaji Alhassan bai da yadda Zai yi Dole ya saki Fuska yana Fadin"Hakane..Ku tashi ku zauna Sannunku Mero sai ki gayamin yau muna da baki agidan nan Safiya Sannu da zuwa..!
Ba mommy ba Hatta Safiya da Yusuf Mamaki ya hanasu Motsi gefensu ya samu kan kujera ya Zauna Yusuf ya kara Ramkwafawa yana Gaisheshi ya amsa mai Cikin Sakin Fuska yana kara Nazarinsa ita Mero bata gane wani abu ba Shifa koda yayi ma Safiya wannan auran yasan me ya aura mata yayi Binciken kan Yusuf Yaro neNagari mai Neman na kansa Sannan kuma Dalilin wannan Tsagerin Kanin nashi ne komai ya Lalace Domin yayi Hannun Riga da duk abunda zai tabamai kimarsa Sai da Ya tattara Safiya ya mikamusu ya ke iya Barci Harda Minshari,bawai Domin baya son yarsa ba Taya Mutum zai Haifi ya yakita sai domin Zuwanta wannan Gidan Shine Rufin asirinsa kuma bazai iya Fitowa yayi ma wani wannan Bayanin ba Shiyasa ko Dayaje Fagge Goggo Tayi Fada kamar ta ari Baki kamar ta Dakesa shi dai sai ban Hakuri yake bata bai da tacewa Tunda aikin gama ya gama ya riga ya gamaba Goggo ba Ya riga yaShiryama Daukan Kowacce mgana kan abunda ya aikata yana Shiryen da hakan indai Boyayeyen Laifinsa bazai Fito a idanuwan yan"uwansa da Matarsa da ya"yansa ba Dama Sauran Mutanen Dake ganinsa da kima ba
Kallon Safiya yayi yana Fadin"Safiya ya Sabon Wuri..?kina Bukatar wani abu ne..?Ki Fadamin komai kike Bukata zan yi miki mishi.!
Cikin Mirmishi ta kalli Yusuf Shima ya kalleta kafin tace"Bana Bukatar komai Abbu..Komai Mijina ya Siyamin ina Cikin Farinciki a Sabon Gidan da nike yanzu..Ina Rayuwa ne Tmkar yadda nake Rayuwa a gabanku..!
Hajiya Mero Dake gefe taji Dadin amsansa sai da ta aikamai da kallon ba Haka kaso ji ba ko..?
Shi kuma sai yayi kamar bai ganta ba ya Shiga Saka musu albarka ita da Yusuf wanda yayi musu Matukar Dadi Ita da Yusuf din har ya kasa Boyuwa Saman Fuskarsu ita kanta Hajiya Mero Jin Haushinsa ya Ragu acikin Ranta.
Suma cikin hakane sai ga Munari da Tasleem sun Fito ta Duka ta gaida Alhaji Alhassan ya amsa yana wani kallonta Cikin kwarewa kasa kasa Tuni yarinyar tatafi da Imaninsa irin Kayan Harkan Dayake so kenan sai dai Tunaninsa ya Tsaya ne sanda Safiya ke Fadin kanwar Mijinta ne.
Miyau ya Hadiye mukut..Ya maida Kwadayinsa ko Ya haukace bazai yi wannan ganganci ba Ko bama Safiya ba ya Tabbata wannan Kanin na Yusuf yaji Labari sai ya Tabbatar da ya Kwaye mai Rigar Mutumcin Dayake yaudaran Mutane dashi..Da Mannau gara Hanau.
Da sauri ya gyara Natsuwarsa ya amsa gaisuwarta Cikin Fara"a da Dattako yana saka mata albarka basu Dade ba sukayi Haraman Tafiya,Yusuf ya Ijiyema Mommy 10k Abbu 10k Safiya kuma tace Abbu ya bar Tasleem ta Rakasu Rijiyar Zaki gidansu Hajiya Mero yanzu yake Fadamata Daga nan chan zasu je ba gaddama yace sai sun Dawo Hajiya Mero bakinta yaki Rufuwa ta shiga Ta Dauko ma Munari Turmin atamfa da Turare sai Turaran Wuta ta Diban ma Safiya da Humra,Sauran kuma tace takai ma Hajiya
Har Haraban gidan suka Rakasu ita da Alhaji Alhassan Ita kuma Tasleem nata Murna suna Daga musu Hannsu suka fice Daga Haraban Gidan
Sai da suka Fice kana Hajiya Mero Ta Daga Hannu Sama tace"Alhamdulillah..Allah nagode maka da Allah bai ma wani Damar Tozarta Rayuwar yata ba..Allah nake Roko ya Kareta yasa ta Zama a Haske ga Mijinta da Ahalinsa gabadaya..!
Tafada Lokaci Daya tana Nufar Hanyar Cikin gidan ko kara Kallon Barayin Alhaji Alhassan batayi ba Shi kuma da kallo ya Bita yana Mirmishi Gefen Bakinsa aransa yana Fadin kayi ki gama ne.
Suna Fita Daga zooroad basu Tsaya ko"ina ba sai kofar gidan su Hajiya Mero Rijiyar Zaki sun ci sa'a nan suka Hade da Anty Saratu tazo gaida su Hajiya sun ji Dadi sosai sukayi ta saka musu albarka basu wani jima ba suka Tafi Bayan Yusuf yayi musu alheri,Safiya kuma ta bama Hajiya Sakon Mommy Anty Saratu kuma tace Tunda sun Hadu anan tana Binsu bashi Yusuf yayi mata alkwarin Insha Allahi suna nan zuwa.
Daga Rijiyar zaki kuma Gidansu Sagir suka Sauka Yusuf Ya shiga Har ciki suka gaisa da Mama kana yace in Sagir na nan zai rakasu Gidan Baba Manu yamai Godiya,Mama taji Dadin haka Tana saka albarka Koda suka zo Inteesar na kwance tana Barci Tayi aiki Ta gaji yau har yan kayan Mama kala Biyu da Hijabai ta wanke ta Hada da nata Inears din ta wanke Shiyasa take kwance sai da Munari ta Shiga Har kurya ta Taddota Ta Daka mata Duka kana tatashi a gigice ganin Munari ya sa tatashi nan take Fadamata Tare da Ya yusuf suke da Anty Safiya Hijabinta ta Dauka suka fita ta gaishesu suka amsa mata Cikin Sakin Fuska.
Mama a waya ta Kira Sagir tace mai yana ina ne..? Yace mata yaje banki ne ammh gashi nan zuwa,ba Dadewa sai gashi ya shigo har gabansa ya Fadi ganinsu yusuf ya Zata wani abu ne ya Faru da Imran domin Tun Ranar da sukayi mgana basu kara Haduwa sun yi Wata mgana da Imran din ba ya Dauke Kafa da zuwa Shagonsa sai dai su Hadu a masallaci su gaisa Sama Sama ya Raasa me yasa Imran ya Dauke masa Kwana Biyun nan sun saba Fadansu su Shirya sai dai wannan karon Abun yasha Bambam
Sai da suka gaisa kana Mama ke Fadamai Dalilin sai lokacin yaji Hankalinsa ya kwanta.
Gabadaya suka tafi Harda Inteesar Tasleem Dayake chan Rijiyar Zaki suka barta Anty Saratu zata Leka Mommy Zasu koma Tare Mama kadai suka bari gidan
Wannan karon duka Matan suka Hade a Bayan Motan Sagir na gaba yana Nuna Hanyar gidan Baba Manu.
Yusuf ya kallesa yana Fadin"Sagir ina Mutumin ka..?
Sagir ya Juyo yana Kallon Yaya Yusuf kafin yace"Kai zan Tambaya Ya yusuf...Imran na Fushi Dani ko mgana nayi mai sama sama yake amsani..,!
Yusuf ya Murmusa kafin yace"Babu abunda kayi mai kuma badakai yake Fushi ba..Sai dai shi haka yake duk Lokacin da wani ya batamai rai..Yana Hada bacin Ransa na Tsawon Lokaci sai kuma Hakan ya Horasa Shi kadai..Ni kaina sai na Bisa Dakinsa nake ganinsa baya ma son Fitowa ko Falo balle a mtsamai da mgana Abba kadai Daya zamemai Dole yake gaisawar..!
Gabadaya Tayi shuru suna Sauraransu Sagir ya jinjina kai yana Fadin"na gane..Sai dai Imran nada Wahalaf Sha"ani ina Matukar Tsausayama matarsa in bata sanshi ba Zata sha Wahalansa..!
Yusuf yace"Ko ni da nike Dan"uwansa Ciki Daya yana min Wahalar Mu"amala ballatana Mace..! Sai dai kasan soyayyar Kila sai ta Sauya shi Watarana..!
Kai Tsaye Sagir yace"Imran bai yi Beleive kan Soyayyah ba bana Tunanin hakan zai iya Faruwa..!
Yusuf yayi Dariya yana Fadin"Ai karya yake yi..Nifa ina da yakinin Mace sai ta Sauyashi Shi din banza..!
Dariya Sagir ya saka kafin yace"Shikenan mu jira mu gani..!
Ammh ina da Shakku har yanzu..!
Yusuf yace"Kajira Lokaci kawai Sagir zaka ce na Taba Fadamaka..!
Su safiya na bayan Mota suna jinsu Tabe baki inteesar tayi aranta Tana Tsausayama mai Tsautsayin data yarda ta Auri wannan ta gama kashe Rayuwarta Gabadaya Mutum na Rayuwa kamar ba Mutum ba sai Kace wani Aljani.
Suna isa gida suka kuma Taki Sa"a Baba Manu na gida Lokacin da Sagir kemai bayanin yusuf sai yaji Dadi da Sauri ya Mike sukayi Musabaha Daman Wlh Safiya na Ransa Saboda yana Tunanin shine fa yayi jagaba kan Auransu in wani abu ya Faru Allah bazAi barshi ba sai dai ganin yusuf da ita Kanta Safiyar ya Ciremai kowani Shakku Kaltume nata ina ta saka dasu Ruwa kadai suka sha Yusuf ya Ijiyemai 5k suka Fito Har waje ya Rakosu yana Godiya Lokaci Daya yana Musu addu"a har sun Shiga Mota Baba Manu ya Duka Saitin Yusuf yana Fadin"ina Murdadden kanin nan naka..?
Yusuf yayi Mirmishi kafin yace"Imran..Yana gida Baba yace a gaisheka..!
Baba Manu yayi Dariya kafin yace"Kai dai ka ari bakinsa kacimai albasa..Nasan bazai ce ba..Ganin Biyu nayi mai zuwa uku ammh na Nazarcesa kamar na Shekara da Saninsa..Ku rika Sakashi yana yawan Shan Ruwan Zamzam hakan zai Taimaka wajen Saukakamai al'amuransa..In ka koma Gida kace Baban Sagir na gaishesa..Manu nake..,!
Yusuf ya gyada kai yana ta Godiya kafin su tafi acikin Ranshi yana Kara auna wasu abubuwan shifa ba Domin Abba ya Rantse mai Imran baida Aljanu ba shi kansa da Farko kallon mai Bugawar Junnu yake mai ammh yanzu kam da Baba Manu yayi mgana zai Tsaya tayin daka wajen ganin Rayuwar Imran ta Inganta kamar baya bazai zuramai ido yana da Komai na Rayuwa,ammah ya Kare

Please Login or Register in order to submit comment