Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

da ita da Fadin"Badai ya gaisheki ba..? Ku rika kama Girmamku Binta wadanan yaran fa Kamar ya"yanku suke..!.
Jim haka yasa tayi Shuru bata da tacewa Shiko Imran ko ajikinsa.
Daada tace munari ta sakamai Tuwon bai yi mgana ba ya Nannade Hannun Jallabiyan Jikinsa ya saka Hannun a Filet din Daada ya Debo Tuwon yakai Bakinsa da Bismillah kowa da mamaki yake kallonsa barin ma Abba da Ya Yusuf da Sagir da Munari da Inteesar sai dai bamai San sunayi ba Ya hade ransa ya cigaba da cin Tuwonsa Daada Ranta Fes tana kallonsa Tana Sakin Mirmishi Aranta Imran in ya Gutsiro Tuwon sai ya Tura gaban Daada kamar wata yarinya haka ya dinga mata sai dai ta Dauka tace cikin Taruwar Hawaye tace"Allah yayi maka albarka Allah ya jikan Zuwaira..Kullum kukanta Daada Yaushe Imu zai sauyane..? Yayi kaza yayi kaza Baya son zama cikin yan"uwa yau data na Raye data zo ta ga Imranu yana cin Abinci kwano Daya Dani yana Gutsiromin Tuwo saboda yasan na Tsufa baya so na Wahala..,!
Da karfi Tayi mganan dayasa kowa yajita sai aka koma ana kallonsu Cike da mamaki Abba Farinciki ya cikasa shi da Ya Yusuf Imran kuma baima Kalli kowa ba bai wani ci mai yawa ba ya Zare Hannunsa ya Mike Daada ta Kallesa Tana fadin"Har ka koshi kenan..?
Kai ya gyada mata bai yi mgana ba ya Wuce zuwa Kitchen ya wanke hannu ya Dauko Ruwa Gora guda Daya yazo ya wuce ya koma Daki abunsa batare Dayace ma Kowa komai ba Daada sai Mirmishi take ita Kadai Mami Asma"u na Binta da Harara kasa kasa itafa bata Kaunar taga Daada na nuna ma wani Jika so da kulawa in ba ya"yanta ba akomai tafi so su kasance sune kan gaba da kowa.

*****

Washegari ma haka gidan ya tashi acike da yan"uwan Munari Farincikinta yaki Boyewa tana cikin Danginta ta kwana cikinsu ana Hira Imran dai Daki daya suka kwana Da Sagir,Wanda Imran kasan Cafet ya kwana ya barma Sagir gadon domin bazai iya barci da wani akan gado ba.
Basheeer kuma dasu Sadam dukkansu Daki daya sukayi kwanciyarsu ko ajikinsu suka kusa Raba Dare suna Hira.
Su Abba ma Daki daya suka kwana Abunsu hakama su Inteesar da Hafsah da Munari su Aneesa ne da Safiya da Fareesatu da su Zainab daki Daya Mami Asma"u dai ita da Umma suka Kwana Daki Daya Inna Maimunatu Dakin Daada tayi kwanciyarta.
Kamar koyaushe ma yau din Baba Asabe sukace ta Huta su sukayi Breakafast kowa ya Fito banda Imran Daada tace ahada kayan karyawansa akai mai Daki Munari ta Zare Jikinta Inteesar da Hafsah suka Dauka sai gashi sun dawo dashi sunyi ta Knooking bai bude ba Hankalin Daada ya tashi ta fara Tunanin ko wani abu ne ya sameshi Abba yace mata kada ta damu lafiyansa Kalau kana ta koma ta Zauna ammh duk ta Shiga Damuwa Bata kai Inteesar shiga Damuwa ba.
Daki ta koma ta Dauki wayarta ta Kirasa bai Dauka ba Har sau uku,sai na Hudu ya danna mata Busy sai ga Sakonsa.

"Kada ki dameni da Rigimarki da safan nan..Am not in d Mood..Barci nake yi..Kuma an sure kece kika zo kina min knooking ko..? Don't let me Catch u bazaki ji da dadi ba..!

Data ga sakon sai da ta tintsire da Dariya kafin ta maida amsa.

"Daada zaka kama ko..? Domim ita ta aikoni na kawo maka Breakfast dinka.."

Amsa ya bata da cewa"Nidai ke nace ba Daada ba..!
Dariya tayi sosai tana Jin Dadin tsokanansa Kyaleshi tayi jin yace baya cikin Mood din.
Falo ta dawo domin bata gama shan Tea dinta ba ta zauna kenan taji Daada na Fadin"Kabiru ya mganar zuwan su Hamisu ne..? Binta kefa kin kirasu Hamidan..?
Baffa Kabiru ne yafa fadin"Eh Daada na Kirasa ban samesa ba sai dai na Turamai sako nasan yan gani zai Dauki Excuse wajen aiki ya taho..Su Sajida kuma Asma"u nace tayi mgama Dasu..! Kai Daada ta jinjina batace komai ba.
Inna Bintalo tace"Su Hamida suna Hanya na Kirasu..!
Daada tace"Yayi kyau..Asma"u Su Sajidan kinyi mgana dasu..!
Cikin Mganarta Tace"Eh Daada. Nayi mgana da Sajida duk da sun kusa Fara Text nace Direbansu ya kawo su yau ita da Umaima..!
Tafada cikin jin Haushi Tsakani ga Allah an takurama ya"yanta.
Daada tace"Ai ba Dadewa bane abun Asm'u zuwa gobe ko jibi in mun gama Abunda ya taramu kowa zai koma bakin aikinsa Tunda ai kowa ma yana da ayyukan ya Saukesu ya Taho..!
Cikin hikima Daada ta maida mata mganarta Inteesar kuwa Farincikinta Duk ya tsaya Lokacin dataji ance Khamis zai zo acikin Ranta Tana ta addu"an kada Allah yasa yaga ma Sakon na Baffa Kabiru ballatana ya Taho.
Bayan sun gama Karyawan su Inteesar suka Tattara komai zuwa Kitchen ita da Munari suka Fara wankewa Hafsah taje yima yaran su Anty Aneesa wanka su Waleeda.
Su Abba kuma suna nan afalon Tare da Daada Mami Asma"u daki ta koma ta Kira Sajida tana Dagawa tace"Mami ko mu yi zaman mu ne..?.
Mami Asma"u tace"A"a ku taho kawai yanzu Sajida..Daada ta matsa sai kun zo..!
Sajida ta bata rai Tana Fadin"Mami to me zamu zo muyi..? Nifa i hv alot to do Mami kinsani Test zamu fara Next Upper week..Ina son kadaici na samu nayi karatu..!
Mami Asma"u tace"Nasani buh ai zuwa Gobe ne zamu dawo kada ki Damu bzai shafi karatunki ba ni kaina ban so ba To kinsan Daada rigimarta Tayi yawa kuma Dad din ku bazai ce komai ba ammh banga Abunda zata ce sai yara sun bar karatunsu sun taho ba..!
Sajida ta Tabe baki kafin tace"Wai to ba Baffan ya dawo ba? Ta gansa Inace ba Shikenan ba..?
Mami Asma"u tace"Uhm kya fada kema..Ina Umai..!
Sajida ta juya tana kallon Umaima Data Fito wanka tana shafa Lotion sai Murna take tace"Gatan nan tayi wanka..Sai murna take Mami kinsanta..!
Mami Asma"u tace"Bata da.wayau ne bata san ciwon kanta ba..Ku taso yanzu kada kuyi dare..Make sure kun dauko duk abunda zaku nema kuma kizo da komai na Karatunki harda Laptop dinki kinji..!
Sajida tace"Ok Mami see you..!
Daga haka suka yanke kiran Umma na gefe ta kishingida Tana jinta batace mata komai ba itama bata mata mgana ba Sanin Halinta yasa Umma ke cin mganin zaama da ita.
Imran bai fito ba sai azahar da zashi Msallaci Sagir ko ta kansa bai bi yana cikin su Basheer abunsa,bayan ya Dawo a masallaci Aharaban gidan ya Tsaya ya sha Sigarinsa Baffa Kabiru ma ya Fito ya gansa yayi kamar bai gansa Baffa Kabiru kuma bai nuna ma ya gansa saboda yadda Imran yake Tabbas zai iya zaginsa in ya cika Shigema yaron.
Bayan ya gama shan kayansa ne ya Shigo Cikin gidan ba kuma wai domin yana jin Tsoron Shanta acikin Gidan ne,A"a saboda Abba ne shi kadai ne yake Gudun bacin ransa sai Daada Dake yake ganin Girman Tsohuwan da kuma Kaunarta Dayake yi ko domin kaunarta ga Abba da Anni dasu Gabadaya.
Yana Shigowa Falon su ka kusa cin karo da Inteesar da Suke wasan banzan Ita da Munari da Hafsah Daga gyaran Falo suka Fara Wurgama Juna Cussion din kujerun falon.
Batama san ya kawo ba ta taho bata ganin gabanta,Kawai ta Fadamai da yayi baya sai tatafi luu zata Fadi ya saka Hannunsa ya Tallafota ta Fada kan Kirjinsa male male ta Rikesa gam tana Sauke Numfashi.
Munari da Hafsah suka Tsure kowacce ta Tsaya tana Raba ido Sai Alokacin Inteesar ta dago Tana ganinsa ta Saki baki Shima kallonta yake da dukkan Tunaninsa da Zuciyarsa.
Sakinta yayi kafin yadan matsa Baya jin jikinsa ya fara saki,kallonsu yayi Daya bayan daya kafin yace"Are u a kid..?manya daku kuzo kuna wasan banza..!?
Kowacce ta koma ta natsu kafin nayi kwallo da yarinya..!
Ai kafin ya gama mgana Munari da Hafsah sun bace afalon Inteesar ce ta Tsaya taki tafiya Kallonta yayi kafin yace" kin rainani ko..?Ok daman nace zan rike ki..? Kina son duka ne ko..?
Ai jin haka yasa ta Zaro ido kafin tayi narai narai da ido tace"Duka kuma Ya Imu..?
Kai ya gyada mata kafin yayi mgana ta wuce sum sum tana waigensa Dariya ta kamasa,sai kawai ya Murmusa ya wuce itama tana lekensa tana Dariya.
Cikin Ikon Allah Sai ga Khamis ya Riga su Sajida isowa ashe yana ganin Sakon ya nemi Uzurin Rashin Lafiyar kakarsa aka bashi kwana Biyu Jirgi ya shigo zuwa Gombe daganan ya Hayo Taxi zuwa Dukku sai dai aka gansa Kwatsan Mami Asma"u sai Murna Yaronta yazo ta saka Baba Asabe ta cikamai gabansa da Abun sha da ci.
Har kasa ya duka yana gaida Abba ya Dagosa ya Rumgumesa yana sakamai albarka haka suka Rumgume da Yusuf Cikin jin Dadin ganin juna haka suka Gaisa da Munri cikin Fara"a acikin Ransa yana Fadin She is Beautifull.
Imran ne bai gani ba yana cikin Daki Inteesar kuma Tunda taji Zuwan Khamis ta shige daki taki Fitowa bata Kaunar su hadu shi kuma ita yake tason gani karfin ma zuwansa Saboda itace yana so su hadu suga juna Ya gayamata Sirrin zuciyarsa Soyayyarta yana sakasa cikin wani yanayi gashi bata Daga Kiransa Ita kuwa Taki Fitowa gashi sai kiranta yake yi taki Dagawa.
Ya iso ba Dadewa sai ga Su Sajida sun iso,Umaima ce ta shigo Da Murnanta da Farincikinta banda Sajida Datake Tavwani Hura Hanci Mami Asma"u sai kai da kawo take kan ya"yanta Umaima ce taxo inda su Inteesar suka ta gaisa da Munari cikin Murnan Haduwa da ita banda Sajida wacce sai da Baffa Kabiru yayi mata mgana ta gaida Abba tana kallinsa tana Tuna kamanninsa.
Sanin Halinta yasa ba wanda ya Nemeta Cikin su Inteesar itama bata Neme kowa ba.
Imran kuma da Khamis basu Hadu ba sai da suka dawo masallaci Sallar Mangariba,ya gansa tare da Sagir yake Tambayan Sadam yamai bayani mamaki ya kamashi ganin ya mikamai hannu suyi musabaha Imran yaki bashi Hannu,sai kawai ya maida Hannuwansa Baya Sagir ne ya mikamai suka gaisa,shi kuwa Imran Kallo Daya yayi ma Khamis bai kara ba Saboda yaji bai kwantamai arai ba Shima Khamis din ransa ya baci da Wulakancin da Imran din yayi mai Da Farko yana Tunanin bai ganesa ba Ammh sai da yamai bayani sai yaga bai nuna ma wata alaman sani ba Sai Ransa ya baci Haka kurum yaji bai ji Dadin wannan Tozarcin ba sai dai bai nuna ba.
Haka suka Dawo gida suka Shigo Cikin Falon a Tare,Lokacin su Sajida da Mami Asma"u suna Zaune a Falon kowa ya samu waje ya zauna Su Abba Dakin Daada suka shige abunsu.
Kowa waje ya samu ya zauna kusa da wanda sukafi dasawa Sagir kusa da Basheer ya zauna Imran ne kadai ya Coge a tsaye Daga kofar Shigowa ya Harde duka Hannuwansa saman kirjinsa da kafarsa yana kadata Yana sanye da Riga mai Ruwan madara mai Dogon Hannu sai bakin Wandonsa wanda ya Tsukesa ta kasa Kansa yasha gyara Dadan nan ya kara yawa Fuskarssa a tamke yana Bin kowa da kallo Cikin Nazari.
Sajida dake Duba wayarta Sanye take da Riga da sikat na yan kanti pink colour kanta da Kitson galaba,mayafin data yane kanta Dashi ya dan zamo ta bayanta Kafarta Daya kan Dayane Tana gefen Mami Asma"u ne.
Daidai Lokacin data Dago kanta Shima Imran idanuwansa sun kai Kan ita Sajidan suka Hada Ido Hudu da ita Gaban Sajida ya yanke ya Fadi,yayinda ta Zurama Imran ido Tun daga sama Har kasa Tana karemai kallo cikin yanayin data kasa Fassarawa Yayinda Imran yaji Haushin Kallonta garesa ya Sake Hade rai ya Dauke kansa sama yana wani Dakuna Fuska kamar yaga Kashi.













*Janafty..*
3/22/22, 23:13 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�4*


*Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488*

Ta kasa dauke idanuwanta akansa Haka kurum bata san Dalili ba Zuciyarta ta fara Bugawa Fat!Fat!yanayinsa da komai ya tafi da Tunaninta wanda ya Haifarmata da kuramai ido ta kasa Dauke idanunta akansa.
Shi kuwa Tunda ga wannan kallon bai karama kallon Inda take ba ammh yanaji ajikinsa Tana kallonsa Tattare Naman goshinsa yayi waje daya cikin Takaichi ammh yaki yarda ya Kara kallon barayinta Akallon Farko yaji Kwata kwata yarinyar batamai ba Daga yanayinta da komai Tun kafin yasa itadin wacece Tunda shi dai Tunda yazo bai taba ganinta ba sai yau.
Ita kuwa kallonsa take Tana so Tayi Tunanin waye shi..?Domin bata taba ganinsa ba ko yana daga cikin Ya"yan Baffa Malamin ne bata sani ba..?koma waye ajinsa da  yanayinsa sun mata a irin yadda take son ganin cikakken Namiji mai cikar Zati da Haiba.
Basheer ne ya Daga ido ya kalli Imran Daya ke Tsaye kikam aransa yana mamakinsa Shi ko gajiya ma bayayi Gyaran Murya yayi yana Fadin"Imran zo ka zauna mana..Kana ta Tsayuwa..!
Yafada yana kallonsa Shi kuma dan yamutsa Fuska yayi kamar yace A"a sai yaji bazai iya Ture alfarmansa ba Haka kurum Sagir kuwa yana Shirin cema Basheer ya kyalesa bazai zauna ba sai gashi ya bashi kunya ya Fara Takawa Cikin Takunsa na isa da Sassarfa ya isa kusa da Basheer din ya Zauna Lokaci Daya yana Harde Hannayensa saman kirjinsa yana Jingina da Jikin kujera Bai saki Fuskarsa ba sai ma kara wani Hade rai da yayi,su Sadam suna gefe suna kallon komai Mirmishi kawai sukayi akallah dai ya Fara shiga Cikinsu.
Dago idon da Imran zai yi suka kara Hada Ido da Sajida dan Waro manyan Idanuwansa yayi akanta irin Lafiya..?sai lokacim ta sunne kanta A kafadan Mami Asma"u dake gefenta sai alokacin Taji kunya ta kamata Imran kuwa Dama ya Fahimci Sajida ita waye karamin Tsaki yaja Har sai da su Basheer suka Juyo suna kallonsa bai basu daman mgana ba ya Kirne Ran nan ya Kauda kansa Lokaci Daya yana wani Dakuna Fuska.
Khamis ne Dake kusa da Sa"id ya taso yazo ya zauna Kusa da Mami Asma"u suka sakata a Tsakiya kenan Kallonsa Tayi Tana Fadin"My son ya wajen aikin naka..? Hop ba wata mtsala ko..?
Tafada Cikin Kulawa da Annurinta na son ya"yanta.
Kansa ya Dora saman Kafadanta yana Fadin"Komai Normal Mami na..I miss u..,!
Sumar kansa ta shafa tana Fadin"Muma muna kewarka Our Son..!
Sajida dake gefe ta Tura baki Tana Fadin"Wai Mamina..? Sai kace Maminka ne kai kadai..?
Kallonta yayi kafin ya Dago kansa yana Fadin"Yarinyar nan baki da kunya kin Rainani ko..?Shegen son jiko kamar mage ga Umai ce ta Shiga Cikin yan"uwa ke kuma kina nan Wajen Mami kina Sakale da ita Kamar Zaki koma ciki..!
Yafada Cikin jin Haushinta Sajida ta kara Nanikema Mami Asma"u Tana Fadin"Mami kin gansa ko..?
Mami Asma"u tace"Zaka fara ko..? Kaifa babba ne..Namiji kuma Ita kuma Macece ko aure tayi a wajenmu She is a kid..!
Bai ce komai ba Sanin wacece Mami Asma"u kai kawai ya Rausayar Daidai Lokacin da idanuwansa yakai kan Imran wanda shima yake kallonsu Duk da ba suna Kusa bane sosai sai dai Yana jin duk Abunda suke Fada Haushi duk ya kamasa Matar nan yar Renin Hankali ne daga ita Har ya"yanta da Mijinta They are all Selfish.
Bawai fa bai gane Khamis bane ya gane sa Sarai domin ya tuna gabda Rasuwar su Anni da Abba ya matsamai suka zo suka kwana Biyu Khamis din ma yazo Tare da Baffa Kabiru kawai dai Shi bai son mu"amala da Khamis ne,Haka nan yaji yaron bai mai ba yana ganinsa Kamar Mahaifinsa ne,kuma shi baya Doguwar Mu"amala da wanda Ra"ayinsa da Zuciyarsa bai kwanta Dashi ba,Bakinsa ya Mele Lokaci Daya yana wani Yamutsa Fuska kamar yaga Kashi ya wani Dauke kansa Khamis shima ya kallesa a Saukaken kafin shima ya Kauda kansa Mikewa yayi ya koma cikin su Sa"id da Yusuf Sajida kuwa Tana jikin Mami ammh gabadaya Hankalinta da Tunaninta na kan Imran wanda bai ma kara Kallon Barayinta ba Sajida ko Wayar nata bata kara Dannawa ba Saboda Kallon Imran gabadaya ya Dauke mata Hankali.
Waige waige ya farayi acikin Falon ko zai ganta saboda yaga ga su Munari na Taya Baba Asabe jera abinci ammh bai ganta ba sai yaji ya Damu,Falon Dayake isu isu ne kadai su Abba suna Dakin Daada,Kamar ya share sai kuma ya kasa Kuma bayason ya Tambayi Munari ta Rainashi sai kawai ya Fito da karamar Wayarsa Ya Shiga Wajen Tura sako.

"Kina ina..? Ban gan ki ba..?

Haka kawai ya Rubuta mata ya Tura mata Sai dai Har tsawon wani Lokaci yana Duba wayarsa bai ji sakonta ya Shigo ba alhalin yana da Tabbacin Inda Lafiya da Tuni ta bashi amsa sake Turamata yayi.

"Ki amsani mana..!

Sai dai shima Shuru sai ya kasa Natsuwa zuciyarsa ta fara Bugawa baisan Dalili ba,Ganin ya kasa Daurewa ne yasa ya Mike kawai zai Fice Daga Falon da Sauri Yusuf Dake gefe yace"Imu ina zaka..!?
Yana Tsoron Kada Zarginsa ya Tabbata Sigari zai fita yasha Ya tsaya ammh bai juyo ba yace"Zan yi kiran Waya ne..,!
Ya fada Cikin jin Haushin Tambayar da Yusuf din yayimai ajiyar Zuciya ya Sauke jin abunda yace Saboda ya Tabbata da ita zai sha sai ya Fadamai gabadaya kowa hankalinsa ya koma kan Imran Daman Tun Lokacin da Yusuf yayi mgana kowa Hankalinsa ya koma kan Imran din Har ya Fice Daga Falon.
Sajida acikin Ranta ta maimata sunansa"IMRAN..! Nice Name..!
Take Fada tana dan Mirmishi Shi kuwa Sagir mamaki ya Kasheshi Dawa Imran zai yi waya..,? Wanda ya sani Dagashi sai ya yusuf yake da Lambarsu sai munari kuma Duka gasu tare,Mamakin hakan ya kamashi Sai dai bai isa ya karyata shi ba Sanin Halinsa Kaifi Daya baya karya Duk Abunda kaji ya fada to iya gaaskiyansa kenan bai mtsama kansa da Tunanin dawa Imran zai yi waya ba ya watsar da komai suka Cigaba da Hirarsu Sama sama da Basheer.
Imran kuwa yana Fita Haraban Gidan Jikin Motar Yusuf ya Jingina yayi Shuru yana wani Tunani gabadaya yaji bai da Natsuwa In kuma bata da Lafiya fa..?
Tuna haka yasa da Sauri ya Lalubo lambarta ya Kirata sai dai Har ta gama Ringing bata Daga ba Ransa sai ya Fara baci ga Zuciyarsa na masa Zafi ya kara Danna mata kira Gbda zata katse Inteesar dake kwance ta Daga Kiran cikin Kasala da Sanyin Murya tace"Hello..!
Muryan ta Dakesa sosai har sai da yaji Hakan acikin Ransa sai dai Cikin Dakewarsa yace"Meyasa nayi miki Sako baki bani amsata ba..?
Sai da yayi mgana ta Zabura ta Mike Cikin Kasala Lokaci Daya Tana Dafe kanta Dake saramata ta kara Bin wayar ta da kallo Ta kara Tabbatar da mai Kiran nata Tunda Cikin dan Barcin Dayafara Daukanta Taji kiran Wayar Idanuwanta sun mata Nauyi bata Tsaya ma Duba mai kira ba ta Daga.
Jin tayi Shuru yasa yace mata"Kina jina ina mgana Shine kike banza Dani..?kinsanni kuwa..? Bana mgana ayi banza Dani kuma bana Tambaya aki bani amsata ya zama Dole duk Abunda nake son sani na Sani din..!
Yafada mata Cikin Zafinsa bai Tsaya Jiranta ba ya Datse kiran yana Jin kansa kawai yana Daukan Zafi haka Kurum baisan Dalili ba.
Inteesar Daga chan bangaran kanta ta Dafe Cikin yanayin dan Jin jiki kamar wasa suna Kitchen suna Taya Baba Asabe aiki suda su Munari,Kanta ya Fara saramata shine ta dawo Daki ta Kwanta Dakyar tayi sallar mangariba Taje ta Fadama Umma,ita ta bata panadol tasha tadan kwanta Shine taji Kiran Wayarta da Imran yayi mata.
Bin bayan Kiran nashi tayi kamar bazai Dauka ba sai daga chan ya Dauka bai yi mgana ba yana cin mgani.
Cikin muryanta Sanyi Sanyi tace"Am sorry Ya Imu..Bani da lafiya ne..!
Sai datace haka yaji ya kara Shiga Damuwa Cikin Dakewarsa yace"meke Damunki..? Meyasa baki Fadamin ba..?
Kara Lafewa Tayi kan gado Tana Fadin"Ciwon kai ne..nasha mgani..!
Kara gyara Tsayuwa yayi  yana Fadin"Kinci Abinci..?
Kamar tana ganinsa ta Girgizamai kai Kafin tace"Ban ci ba..!
Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace"Ki fito kici wani abu kada ki zauna da yunwa..Ok..!
Da sauri tace"Tom..!
Daga bangaransa yace"Ki rike wayarki a kusa dake kada na Kiraki baki Dauka ba..!
Da tom ta kara amsamai Kafin ya Datse Kiran asaman lebenta tayi dan Mirmishi,Ko minti Daya bai ba da Katse Kiran Ya sake Kiranta Da Sauri ta Daga Tun Kafin tayi mgana Taji yace"Ki duba Sako na ki bani amsa..!
Yafada Cikin Kaushin Murya Cikin Shagwaba tace"Ya imu to ba munyi mgana ba..!
Cikin dan waro ido kamar tana ganinsa kafin yace"Ki bani amsata..ni ne kadai nake da ikon kimin sako naki baki amsarki ammh ni ya zama Dole ki kulani kuma ki bani amsata Lokacin da nake Bukata..!
Abun nasa ma sai ya bata Yar Dariya Har sai da yajita da Sauri yace"Au dariya ma kike yi ko..? Ashe kina son Duka kenan ko..?
Da Sauri tace"Ban fa da lafiya..!
Tafada Cikin Shagwaba Har sai da yaji Hakan acikin Ransa Mirmishin Saman Lebe yayi kafin yace"Do as i say..!
Yes sir..! Tacemai tana yar Dariya shima Dariyan yaso yi sai dai bai bari taji ba ya Datse wayan ya koma ya Jingina jikin Motar Wani Nishadi na kara Shigarsa baisan Dalili ba In yana mgana da yarinyar yana jinsa kamar bashi ba Ya kasa Fassara hakan sai dai ya barsa ne a karfin jinin yan"uwantaka atare dasu,Shiyasa yanan nan Tsaye yaji Shigowar Sakonta,Da sauri ya Duba.
"Ban je ko"ina ba Ya imu..Ina Daki ina kwance ban lahiya..!
Sai kuma Dayan"Ehyyee..Ya imu ya Damu dani..!
Haka ta Rubutomai Dariya yayi afili ya Furta"Shagwabbiyar yarinya kawai..!
Yafada sanda Sagir ya kariso wajen yana Fadin"Kai kuma kai da Waye kake Dariya kai kadai..?
Dagowa yayi yana kallonsa Lokaci Daya ya maida Wayarsa aljihu yana Fadin"Ina Ruwanka banza Dan saka Ido kawai..!
Sagir yayi dariya daidai Lokacin da Sauran mazan suka Fito Harda su Abba domin zuwa masallaci an Kira Sallah da Sagir yama Imran mgana su Tafi cemai yayi shi Yaron sane da sai ya Tasa agaba...?
Yaje yasan Hanya zai zo Daga baya Sagir bai damu ba ya wuce,haka ma su Yusuf suka Fice abunsu sanin Halinsa kamai gwaninta ya Dizgaka
Ganin su Abba ne yasa ya wuce da Sauri bayaso ya gaida Baffa Kabiru shiyasa yayi saurin wucewa Abba yana kallonsa kuma ya Fahimcesa Sarai Mirmishi kadai yayi suma suka Rufa Musu baya zuwa Masallacin Dake kusa da gidan
Bayan an gama Sallah gabadaya suka Dungumo suka Dawo Gidan Imran ne abaya Shi kadai yaki ma yarda ya Jera da Kowa ko Sagir daya so ya Jirasa Cemai yayi yayi gaba basai ya Jirasa ba.
Bai damu ba ya Taka ya bi su Basheer ya kyaleshi yana Tafiya kamar bazai taka kasa ba.
Gabadayansu afalon suka yada Zango Domin cin Abinci Har da su Abba Daada ma ta Fito nan falon Imran yaso ya gudu ya koma Daki Daada ta Hanashi ta Kirasa tace yazo ya Zauna Kusa da ita bai da yarda zai yi Dole yaje kusa da ita ya Zauna,Yana cim mgani Irin su Mami Asma"u sai cika take tana batsewa,Ya"yanta na Gefenta Sajida da Umai,Sajida sai Satan kallon Imran take yi shi baima san Tanayi ba.
Tuwon Semo ne da Miyar kubewa Danya Dataji Naman Rago da Manshanu,sai Ci suke suna Sakin Santin su Anty Safeya dasu Aneesa suna Gefe suma cin na su suna Hira haka suma Mazajen nasu suna Waje Dayane,Haka ma su Abba suna Zaune dasu Daddy waje daya duka dai duk suna kan Katuwar Dardumam da Baba Asabe ta shimfidamusu ne.
Daada ne ta kalli Umma Dake gefen Inna Maimuna tana Fadin"Salaha ina Maryama..? Banganta ba..!
Tafada tana kallonta kafin Umma tace wani abu da Sauri Munari tace"Tana Daki batajin Dadi Daada..!
Daada ta jinjina kai kafin tace"Ayya..Meke damunta..? Taci abinci?tasha mgani..?
Tayi Tambayar Duka Lokaci Daya,Munari tace"Eh Daada tasha Tea dazu kafin na Fito..!
Daddy ya ijiye Spoon yana Fadin"Tun yaushe ne bata da lafiyar..!
Umma tayi Saurin Taresa Tana Fadin"Yanzu da yamman ne fa Abban Intee..Ni na bata mgani kasanta Raguwa ce gajiyan Hanya ne..,!
Kai ya kada bai ce komai ba Saboda Yasan meyasa Umma ta katsesa.
Khamis kuwa Hankalinsa ya tashi jin Inteesar bata da Lafiya Daman Tunda yazo ita yake songani Cikin nuna Alhini ya kalli Munari yana Fadin"Mai sunan Goggo jikin Inteesar din da Sauki ko..?
Kai ta gyadamai kafin tace"Eh Kamar ta samu barci ne..!
Kai ya jinjina duk ya Damu yama kasa Cigaba da cin Abinci,Mami Asma"u na Lura dashi Ranta ya baci ta kallesa Tana Fadin"Kacigaba da cin Abincika Tuwo ne fa nasan kuma Kan sonsa sosai..!
Dan Mirmishi yayi ya cigaba da cin Abinsa Imran kuma Cokali Daya yayi bai kara ba,wayarsa ya Fiddo ya Turama Inteesar sako.

"Ki fito falo kici Abinci..,!

Ya turamata ya ijiye wayar a gabansa Daada Dake kallonsa Tace"Imrana kaci abincin mana..ko Baka cin Tuwon ne a sama maka wani
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment