Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Rasa.
Wannan Nasaran da Abba ya samu Daddy ne kan Tsani Duk da ba aikin Gwamnati yake yi ba yasan manya sosai acikin gwammati masu manya Mukamai da Taimakon su da Chachantar Abba ne ya kaisa wannan Mtsayin.
Tsayawa Fadar irin Farincikin wannan Gidan ma bata Lokaci ne sun yi Murna kuma sun godema Allah Duk da bazasu iya dawo da Ran Yan"uwansu da suka rasu ba akallah dai Zasu iya Dawo da Fiye da Farincikin da suka rasa abaya Dr.Abubakar Malami ya kara Tabbatar ma kansa mai Hakuri Shine keda riba wata Rana kuma Komai Tsanani mganinsa na Wajen Allah in kaddaran sa ta Faru dakai to akasin Farinciki da samu zasu Faru dakai in kayi Hakuri abaya ya riga ya Gama Fitar da rai da Rayuwa ballatana Har ya Cigaba da amfana da Iliminsa sai dai shi Allah mai kyauta kuma mai kari ne.
Wannan Sabon mukamin na Abba ba wanda bai jisa ba yan"uwa Sai kira suke suna Tayashi Murna Daddy da Umma Takanas ta Kaduna sukazo kano Taya Abba Murna Suka kwana Daya suka koma Tare da Mama suka Dawo Tunda Jikin Inno yayi Sauki ta Warware,Inna Bintalo da ya"yanta duk sun kira Abba haka Inna Maimunatu Sadam kuwa kullum Shida Aneesa in yau basu zo ba gobe suna gidan,Hatta Mutanen Ikko Dr.Ali isa Argugun ya Kira Abba yace a Jarida ya gani a Big Congratulation ya Chanchanta da wannan mukamin.
Banda Baffa Kabiru shi kam sai da kowa ya Kira kusan shine na Karshe ya Kira ya Tayashi Murna Abba Mutum ne bamai Riko ba sannan yana yima wadanda yake Tare dasu Uzuri ballatana Baffa Kabiru da shi ya Fita Dabam acikinsu.
Bai nuna mai wani abu ba ballatana yaga alamun ya Fahimci bai kyauta ba Shima Sai yayi amfani da kalmominsu na Lauyoyi ya Irin nuna ma Abba Hidimomi ne suka sha kansa shima Abba sai yayi amfani da Iliminsa na Sanin Hallayar dan adam ya nuna bakomai ya Tabbata daya samu Lokaci Har gida zai zo mai murna da Haka suka Rabu Labarin da Har Cikin Family Group din su sai da Sadam ya Sanar kowa ya gani Hatta Sajida wacce Take chan makaranta Bakinciki da soyayyar Mijinta sun kusa illatata Tana da Labarin samun aikinsa Ta Kirasa sai dai har Lokacin bai Sauketa Daga Sagale tan da yayi ba,Ta Riga ta gama Sarewa ta Tabbata da Mami Tayi mata mummaan Ramin da kafin ta iya Cikesa sai ta sha Wahala Tana son Imran kuma zata tabbatar da hakan bazata jura rasashi ba,shiyasa ta yanke shawaran Dukku Zata tafi wajen Daada ko kuma taje Gidan Baffa Malamin Imran din in ya ganta Dole zai karbeta tunda dai ita Matarsa ce,Sai dai kafin nan Zataje Dukku ta Fadama Daada tana son ta Tare a Dakinta Mijinta ta Tabbata in ta Cigaba da yin shuru Mami Zata kashe mata aure in kuma hakan ta Faru ta gama shiga uku ba wanda take ji take gani a farke ko acikin Mafarki irin Imran Rayuwa babu shi bata san yaya zata kasance ba ta bari ne su gama Covering semester su sai ta Shirya zuwa Dukkun koda makaranta ne batare da Mami Asma"u ko Dad sun sani ba ta Tabbata Sukaji Labari bazasu taba barinta ba.
Khamis ma yana Cikin Damuwa ganin Yadda Inteesar taki bashi Dama aiki ne yayi mai yawa bai samu Lokaci ba ammh ya Kuduri niyyar karshen Wata Zai je Har kanon zai kira Baffa Mustapha ya bashi Full Addrres din inda Zai sameta Zai je domin neman yardanta Bai ma Fahimci haka sonta yamamaye mai Ransa da Zuciyarsa ba sai da ya koma Anambara Tunaninsa duk itace tayi Daidai da Zabinsa da irin kalan matan dayake so.
Khamis bai Taba Zina ba Sai dai Bazawarin Kan Titi ne ya Fige mata da yawa asha baki yayi Romancing na Fitar Hayyaci aji Dadi da juna ammh bai Taba Tsallake iyaka ba ko kuma ya Tsallake Gonar da bata tasa ba ya riga yayi ma kansa alkawrin bazai tsallke Gonar kowa ba sai tasa.
Mami Asma"u Dataji Labari mamaki ya kamata ta Dinga maimaita lamarin a Fili,Tasani kuma ta kara Sanin Malami da iyalansa sun musu nisa ita kuma abunda da bata kauna kenan wani ya Fita ko ya fi mijinta da ya"yanta tana da Labarin samun aikin Imran Harda kyautar da aka bashi da Mota da Gida Zuciyarta tayi Sauki kan Auransa da Sajida sai dai kafin ta bashi yarta sai ta Gindaya wasu Sharruda kuma sai ya tako gidan nan ta Wulakantasa son ranta.
Ko awaya bata Kira Abba ba kuma a group da ake ta Fatan Alheri Tana gani batace komai ba Kuma Baffa Kabiru bai iya gayamata abunda ya kamata ba abunda taga Dama shi take yi shi bai isa yace wani abu Saboda Tun Farko haka suka Gina Rayuwar Zaman auran nasu.
Safiya ta Kira Hajiya Mero ta Fadamata Abun Alherin Daya samu Abba bakinta yaki Rufuwa daman wannan Ranar take jira da gayya Taje tana Fadama Alhaji Alhasan wanda Ya Razana kuma yaji mamaki Daman Sabon Deen da Jami"ar Bayero ta Fitar da sunansa Mahaifin Yusuf ne,Bai taba Tsamnani ba kuma bai Taba kawowa ba,Hajiya Mero tace ya Shirya yau Har dashi zasu tafi Gidan Taya su Murna ya Fara Kifta Ido,Wanne shi ake kira Inda ka Raina in da zaka na Ran maka ya Raina Yusuf ya Ci Zarafin gidansu sai gashi In bai yi hankali ba Kunya da Nadama zasu kamasa Lokacin hakan bai yi ba.
Ya Tabbata yasan Labarin yadda ya Basu Safiya a wulakance da yadda ya Tozarta Yusuf din Tabbas bai zo so su Fara Haduwa Cikin wannan yanayin ba Duk yadda yaso ya Zillema Tafiyar bai Samu ba Domin Hajiya Mero ta Tsaya sai yaje ita da kanwarta Anty Saratu da ta zo su tafi Tare.
Bashi da Mafita illah ya shirya Da Daddare suka tafi dukkansu har da Tasleem
Masu Karatu zan so ku Hango Fuskar Alhaji Alhassan agaban Abba kamar yayi mai sujjada ya kaskastan da kansa baya iya Hada ido da Abba ballatana Yusuf har ita kanta yarsa tasa Safiya,Gani yakevkamar Abba ya na kallonsa da abunda ya aikata Cikin Rashin sani yo cikin Rashin Sani mana in da ya san Akwai irin wannan Ranar wlh da bai fara wannan Tozarcin ba.
Sai dai ta bangaran Abba ba haka bane ya ma manta da wannan mganar Tunda akace mai ga iyayen Safiya Har da Mahafinta sun zo mai Murna Farinciki ya Kamasa Alhaji Alhassan na neman ya Dukamai ya Tarosa yana bashi hannu Cikin Fara"a Lokaci daya da godiya Domin iyayen Safiya abun karramawarsu ne Safiya Haske a Gidansu itace Sanadiyar da suka kawo yau a wannan Rayuwar Dole ne ya Godema iyayenta da ahalinta.
Lokacin da Abba ke godiya kan Alhaji Alhassan na kasa ya kasa ma Dagowa bai Taba nadamar Hallayarsa ba sai yau Ji Abba dai Daga ganinsa kaga Tsabar Ilimi da Wayewa tare da shi Wanda ko saman kafarsa bai kama ba godiya yake yimai Saboda ya aura ma Da'nsa auran Safiya a kaskaace bai Tuna da Cin Zarafim da yayi ba to shi kuma a wa..? Tabbas a wannan Gidan yaci sunansa gidan karamcin Kunya da Nadama sunki barinsa ya Saki jikinsa Su Mommy tun bayan da suka gaisa da Abba suka Rankaya shashensu Safiya Tasleem kuma Tana Tare da su Munari.
Abba da Alhaji Alhassan Suna Falo Abba ne ke tamai Hira Cikin Faram Faram da wayewa shifa sai dai Zugum da gyada kai,a Hiran Abba ne yaji Labarin Abba yayi Koyarwa a Jami"ar Lagos kusan shekaru ashirin ya Hallaci kwasa kwasa ba adadi kan abunda ya Shafi karatunsa Dr ne shi a bangaran Ilimi Babansa Marigayi Hamisu Dukku har ya rasu alkalin alkalai ne na Kotun musulunci to shi Waye..? Alhassan ne fa wanda ubansa ba kowan kowa ba almajiranci yazo yi garin Kano Allah ya taimake sa Da Taimakon Mallam yayi karatu da kuma alfarmansa ne har yau yake kan wannam mtsayin shi ko Rabin Dr bai kai a iliminsa ba,Karamin alhaki ne in kazo matakin rayuwa a kan Abba da Zuru"arsa.
Yusuf ya Fita Haraban gidan yayi waya sai ga su Baba Manu da Matarsa Kaltume da Mama da Sagir sun kawosa daman Tuni yaji Labarin komai a bakin Mama Shiyasa Dayaji wannan abun Faricikin yace ta kawosa yayi musu murna da Yusuf suka Fara jin karo yaji Dadin ganin Baba Manu saboda bazai manta dashi ba,Yayi musu jagora zuwa Falon gidan su inda su Abba ke zaune bayan sun gaisa Daga Waje Abba ya mike Cikin girmamawa Sanda Yusuf ya sanar dashi Baba Manu ne baban Sagir wanda ya karbomai Auran Safiya Alhaji Alhassan dake Zaune yana ganin Manu aransa yace Shikenan na Mutu Daman yana zaune ne yana Allah Allah kada tsagerin yaron nan ya Shigo Kada ya yagemai Sauran Rigan Mutumcinsa Dayeta ita a wajen Abba.
Sun gaggaisa Cikin Aminci da Farinciki Abba yayi ta ba Baba Manu Hakuri Da baisamu zuwa yayi mai Godiya ba Baba Manu yace Haba ba komai Shi kanshi yasan Wani kaya fa sai Amale Yusuf sun wuce Raini da Wulakanci Tunda yaji ance Yaya yake Wajen mijin Salaha kanwar Amina yasan Babban goro sai magogin karfe.
Sai da aka Natsu yama Lura da Alhaji Alhassan nan take ya Kira sunansa ya basa Hannu yana Dukar da kai da Kifta ido ya amsa mai shi bai ma Lura dashi ba sai acikin Ransa yaji Dadin Da Alhaji Alhasan din ya gane cewa Safiya batayi ma kanta Zaben Tumin Dare ba ta shiga Ahali irin Ahalin da kowa Ke Burin nashi ya kasance.
Munari da Inteesar keta Hidiman kawo ma baki abun sha da kayan Motsa baki Sagir dai Dakin Imran ya shiga ya samesa zaune kan Tsakiyar gadonsa yana ta aiki Bisa karamar Laptop dinsa nan ya Zauna suna gaisawa jin cewa da Baba Manu suke Imu ya mike ya Zira Jallabiya ko bakomai yana ganin kimar Baban Sagur din ba Dan"uwa bane ba kowa ba ammh yayi musu Ranar da wani nasu bai musu ba.
Ai yana Fitowa Falon Alhaji Alhassan yaji kamar kasa ta Tsage ya Fice ga Sanyin AC ga komai ammh Sai zufa yake yi,Imran bai ma gansa ba da Baba Manu suka gaisa sai su Mama da suka Fito Daga Shashen Anty Safiya Zasu tafi ne ma,Kawai yaji Alhaji Alhasan na gaisheshi kowa awajen sai da yayi mamaki sai alokacin Imu ya gansa yako hade rai ya amsa lokaci Daya yana Bashi Hannu sukayi Musabaha yana jin Sadda Hannunsa ya Jike da Zufa sai rawa jikinsa yake yi Dariya ta kamasa aransa yace kowa ya Tuba don Wuya ba lada Saboda Safiya bazai so asirin Mahafinta ya Tonu a Bainar nasi ba sai dai zai so ace ya Tuba kuma Allah ya Shiryesa ya Dawo uba nagari kamar kowaa yasan dai shi Imran bai jin mgana ammh Wlh bazai iya Fallasa asirin da wani ya Rufe ba har ga Allah yana mai Fatan Shiriya.
Su Baba Manu suka Fara Tafiya sai gashi Har da Ya Imu a yan Rakiya,sun Tafi kenan Ba Dadewa suma su Alhaji Alhassan suka wuce bayan yayi ta Dokama Mommy kira ta fito su tafi kunya yakeji gani yake kamar Kowa yasan abunda yake aikatawa Abba Har Bakin Mota ya rakasu Mutum mai Saukin kai inji Mommy Anty Saratu tace Dagani ya Gado Dattako da Mutumci shidai yana jinsu Tak bai ce kunyar duk ta gama kamasa sai da suka isa gida ya iya Ssuke Numfashi Anty Saratu nan zata kwana sai Gobe Zata koma Gidanta nan suka baje afalo suna labarin Karamcin Gidansu Yusuf anan me yake jin Labarin Safiya nada Ciki sai yaji Dadi ko bakomai zai yi Farinciki in ya Hada zuru"a da Abba Shi kanshi ya sani Babban Goro ai sai magogin karfe.

******

Washegari ta kama Labara ne,basu da Lecture sai 10am na safe shiyasa ma basu Shirya ba,yau basu tashi da wuri ba,Anty Safiya tayi Breakfast Tunda dai basu tashi ba suna ta barci Inteesar 7:20am na safe ta Farka Daga kan Darduman Data idar da Sallar asuba Munari na saman gado tayi Daidai tana Sharan barci tana Fashin Sallah ita kadai tatashi da asuba Tama makara saboda bsu yi barci da wuri ba sun Tsaya yin Browsing din wani assigment da aka basu kuma yau din za"a karba

Agogon Wayarta ta Duba Taga Lokaci in taci sa"a Ya Imu bai ga Fita ba kenan,Yau za"ayi ta kare tagaji da wannan Fushin nasa In Horata yake son yi Wlh ta Horu har tayi Laushi,Da Dogon Hijabin Datayi Sallah ash mai Hannu ta Fito Daga Dakin,Ba kowa afalon sai karan Tafakeken Talabijin din Dayake tayi shi kadai Falon sai tashin Kamshin Girki yake da na Turaran Wuta aikin Anty Safiya ne ta gama Jera komai asaman Dining ta koma ta Taya Ya Yusuf shirya kafin su Fito tare domin yin Breakfast.
Bata Tsaya wani Tunani ba ta Fice Daga Falon zuwa Haraban gidan illah kuwa Ta hangosa Tsaye ya Bude bayan Motarsa ya saka Karamar bakar Jakar Briefcase dinsa kafin ya Rufe ya Zagaya ya shiga bangaran Direba sanye yake da American Suit masu Ruwan Toka na kamfanin Armani ya yi amfani da Tek tie ash ya Daure wuyansa dashi kafarsa sawu Ciki ne Bakake,na Fatar damisa sai agogon Hannunsa Shima mai kyau da yarari kirar golden kansa ya sha gyara yana Sheki ko kadan bai Rage Dadan Daya Tara a kansa ba sai hakan yayi mai kyau a kallon Farko in kayi mai sai yayi maka kama da jaruman Kasar Waje na Bolloywood.
Ganin ya shiga Motarsa ne yana Neman Tada ita ya Fice Daga Gidan yasa ta tattara Hijabinta ta Zura da gudu bai da Tsammani kawai yaji Mutum a kusa da Kujeran mai Zaman banza,Kukan ta kawai yaji da Shesshekanta ya Dago daga saka ma Motar key ya sakarmata Dara Daram Idanuwansa masu cike da Sheki yana kallonta itama shi take kallo Tana mtse ido tana jan Hanci alamun kuka Duk da ba hawaye adonta nata sai Tsabar Shagwaba.
Kallonta yake Cikin Salama da wani Sukuni Idanuwansa na bayyana yarda yayi kewarta sosai ammh Saboda kada ta Fahimci haka ya Hade rai yana Fadin"Ke miye haka..?
Baki ga zan tafi wajen aiki bane kika zo kika tasani kina min kananun kukan ki na Fama ko..?
Jin haka yasa ta kara Wage Murya ya saka kukamai kuka Harda Dora hannu a saman kanta Ido ya Waro yana kallonta Cikin mamakinta ganin fa sai kara Volume take yi yasa yace"Kin rainani ko..?Tukuna ma me akayi miki na kuka..?
Jin haka yasa ta Dago Tana kallonsa Tana Sharan idon da ba Hawaye tace Cikin Tura baki tace"Ba kai bane....!
Tafada Cikin Tabara da Sangarta Shagala da yayi da kallon Dan bakinta kafin ya kada kai yana Fadin"Uhm yarinyar nan kin cika Shagwaba Umma da Baffa Sun bataki..ni me ye namiki da zaki ce wani nine..?
Inteesar najan majina kamar gaske tace"To ba kai bane..Kana Ta Fushi dani nayi ta kiranka baka Dauka ba na Tura maka sako ba adadi kaki kulani kuma..kuma!
Tafada fada tana wani kara Goge Hanci kamar kuka Dariya ta kamasa ya kanne kafin yace"Ina jinki..kuma me..? Imran sarkin Laifi..?
Inteesar Da ta Fakaici idonta ta Debi Miyau ta goga i donta saboda yaga da gaske take tunda na gasken yaki zuwa batasan yana kallonta ba Dariya ta kusa Subucemai acikin Ransa yace"Yaro yaro ne..Yaro man kaza..!
Cikin Shagwabbiyar Muryanta tace"Kuma baka bari ina ganinka kafin na fito ka tafi aiki in kuma ka dawo da Daddare ne kana cikin Dakinka ni fa kuma na baka Hakuri kaki Hakura..?
Yana Mirmishin Saman baki yace"Au ai kin gama naki Fushin ne ni na Dauka ba shikenan ba..?
Fito da idonta yaga Hawayenta Tace"Ai nace kayi Hakuri fa..!
Tafada Tana kara Tura baki Yana Danne Dariyansa yace"Ok naji..Yanzu kin Hakuran ne na Rika zuwa Wajen Sajidan..?
Kallonsa Tayi kyam Ranta Tuni ya Baci Mood dinta ya Sauya kanta ta Kauda gefe ta Murgudamai baki ya ganta Sarai shiyasa ya Hade rai yana Fadin"In kika kara Juyamin baki sai na Bike Bakin yayi jini..? Am i ur Mate..? Saboda kinga ina Miki Dariya shiyasa Kika Rainani ko..?
Tana shirin mgana ya Dakatar da ita da cewa"bana son jin Wata mgana..Bana son Raini ni bana daga Ciki yayyinki wadanda kike rainawa kina ma Sangarta yadda kikaga Dama Ina nan a Imran din da kika sani Wlh ban Sauya ba u better Behave ur Self kuma ma naje wajen Sajidan ke kin isa ki Hanani ne..!ke ce zaki bani Umarni ko ni ne zan baki..?
Baibata Zarafin mgana ba ya cigaba da Fadin"Ni namiji ne Mijin Mace Hudu..Zan iya auran mata uku nan gaba Bayan Sajida kuma infact ma ke Matatace da zaki hanani zuwa wajen wata..?
Yafada yana kallonta Saurin Sadda kanta tayi kafin Cikin cikin Sanyinta Idanuwwnta sun ciko da Hawayen gaskiya"Kayi hakuri bazan kara ba..!
Sai ta bashi Tsausayi wani abu na yawo acikin Ransa kai ya kauda yana Fadin"Is ok..Tunda kin bani Hakuri nima na Janye Fushin..!
Kallonsa ta dago tanayi ido Cikin ido Hawayen kishin Sajida suka Zubo mata Karamar Dariya yana Duba agogon Dake Daure a tsitsiyan Hannunsa yace'"Sai yanzu kukan gasken yazo..?bakya Bukatar saka Miyau bakin kii ko..?
Kunya ta kamata ta Rufe Baki Tana yar Dariya Cikin shagwaba tace"Duk ba kai bane..!
Nishadinsa ya kasa Boyuwa yace"Ni kuma..?laifi na baya karewa..Kedai Kazama ce kawai..!
Yafada yana yar Dariya ganin Zata faramai shagwabanta ne ya nuna mata agogon Hannunsa yana Fadin"8am na kusa..Kada ki sakani na Fara abunda ban saba ba plz ki goge wannan Hawayen naki ki koma gida Zamu hadu in na Dawo wajen aiki..!
Kallonsa Tayi kafin tace"alkawari..!
Tare da Mikamai karamin yatsaanta bai Rike ba yadai murmusa yace"Cikawa..!
Sai Lokacin Hankalinta ya kwanta ta Share Hawayenta ta Bude Motar ta Fito Lokaci Daya tana Rufomai Murfin Motar,Tana Tsaye a wajen Tana Dagamai Hannu har yayi Hon iro megadi ya Budemai get ya Sulala Waje,sannan ta koma Cikin Gida Cike da Wani Farinciki Tana shiga Falon Taga Ya yusuf da Anty Safiya suna karyawa Gaishesu tayi kafin ta shige ciki Anty Safiya na mata mganar Karyawa tace sai tayi wanka Lokacin Munari ta Farka Daga Barci in bata Farka ba ita zata tasheta.

*****

Shikenan Fada tsakanin Inteesar da Imu ya kare suka koma kamar baya Yawancin sunfi mgana ta Test Messages,Tunda bai da wani ishashen Lokaci,waya sai Lokaci bayan Lokaci in Bukatar hakan ta taso.
Suna Haduwa yawanci a Haraban gidan ko kuma aa kitchen in yaje Daukan Ruwa ko Zai Hada Tea ko Zai Dibi abinci Wani Lokacin kuma yanzu in yana Daki yana Bukatar wani Abu ita yake kira takaimai.
Koda basu yi wata mgana ba They are ok Tunda suna ganin juna Koda yaushe sun dai yima Mama yaji sai dai suje da wuni badai da kwana ba Tuni Inteesar ta kusa kwshe kayanta Duka Zuwa Gidan Abba Mama bata isa ta Raba Kaunar Munari da Inteesar ba,Shiyasa bata Damu ba Tunda suna kusa kuma nan din ma Gida ne ba wanda ya kawo wani abu sai Munari Domin ita tasan komai Abba bai Fara zuwa Offife ba sai Farkon Wata Lokacin komai ya Daidata Harta Motar da sukayi Shawara da Imu zasu siya ma Abba da Sauran kudinsa da na Marigayi Nura zasu siyama Abba Mota mai rai da lafiya da Direban da zai Rika jansa batare da sun Fadamai ba sun fi so yaga komai kwatsam
Karshen Wata nayi Daada ta Kira Duka ya"yanta ta Fada musu tana son ganinsu bazata mtsa sai da ya"yansu ba ammh wanda ke da Hali yazo,ta kuma ce Mami Tazo da Sajida Khamis yazo,Imran Daman suna Waya daya Kirata ta gayamai daman Wannan Lokacin yake jira ya shirya ma Hakan

Mami Asma"u dataji labarin Ta Dauka mganar Khamis ne da Tarewar Sajida Lalle Lokaci yayi da zata Tauna aya Domin tsakuwa taji Tsoro sai Imran ya Raina kansa Sajida na makaranta Baffa ya Kirata yace in ba mtsala tazo Gida zasu da ita Dukku ne Daada tace taje,Tana jin haka bata tsaya wasa ba Ta Tattaro ta dawo gida Daman Damar nan take jira Tunaninta itama ya Tafi kan mganarta da Imran Allah yasa mganar Biki ne da Tarewa da sai tafi kowa Murna.
Su Inteesar dai zasu fara Test Monday sukace bassu je ba,su aka bari agida Da Anty Safiya su Sadam su kadai suka Tafi sun bar iyalansu agida.
Ranar Jumma"a Abba da Ya Yusuf da Sadam suka tafi a Motar yusuf din Imu yana Wajen aiki yace sai asabar da Safe zai taho
Baffa Kabiru ma sai Ranar asabar yace zasu zo su Daddy ne chan su Abba suka iske su shi da Umma da Basheer Inna Bintalo ta iso ita da Inna Maimunatu wannan karan ba yaran kowacce ita kadai tazo,Sa"id ma Aranar da Daddare ya iso Daga Dutse.
Imran sai Ranar asabar da Safe shida Sagir suka hau Motar Haya zuwa Dukku agida ya bar Motarsa








*Shakira*
3/23/22, 12:02 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�15*


*Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488*

Basu isa da wuri ba,Sai wajen 12pm na rana duk da sun fito da wuri,Sagir dai nashi dan bi ne domin baima san da Tafiyar ba,ana gobe Tafiyar ya kirasa a waya yace mai ya shirya gobe Zasu tafi Dukku ya zata ma amotarsa Zasu tafi Imran din yace A"a saboda bai wani san hanya ba Yusuf ne yasan Hanyar sosai,infact ma bai yi niyyar zuwa da Motar tasa ba.
Sagir kallon Imran kawai yake Ko da bai gayamai komai irin Mirmishin Dayake ta saki na kasan Lebe yasan na mugunta ne irin Mirmishin Imran naci Nasara shifa Bai taba ganin mutum mai sa"a kamar Imran ba Komai ya sama gaba sai yaga bayansa komai yace zai yi to tabbas Zai yi ne yana da kyawawan Halayya da ba kowa ke sanin haka ba sai kana Tare dashi,Mashin dinsa Halak malak ya mallakamai Sagir din Saboda ai ya Chanchanta shi Sagir din ma yaki amsa Daga Farko Imran din ya wurgeshi da key din yace in bayaso to ya Bada ita yadai san In Imran ya Fadi mgana baya sauya mgana Mashin dai ta Zama nashi sai dai shi yayi abunda yaga Dama da ita.
Koda suka isa Tuni bakin Abuja sun iso,Hatta Khamis ya iso,Daman jiya da Daddare ya sauka a Abuja da Safe suka kamo Hanya Harda Sajida Umaima Tana gida Saboda makaranta.
Imran bai yi wata Shiga ba kamar yadda ya saba haka yayi sanye yake da Riga da wando,Rigar mai ruwan kasa ce Mai Hasken wandon kuma Shima mai ruwan kasa ne sai dai yana Duhu sosai,Wando daga kasa ya Tsuke kadan Ya kamasa.
Sun shigo Har falon Daada inda su Umma ke Zaune ita da Mami Asma"u da su Sajida dasu Sa"id da Basheer,Su Abba suna Dakin Daada tun da suka Shigo Sajida idanuwanta suka Kafe akanshi shi Wlh bai ma ganta ba yaga dai Uwarta wacce ko kallo bata isheshi ba Umma kadai ya gaisar Kadahan kadahan,Sai ya karisa wajen su Ya Yusuf suka gaisawa ta Hanyar yin Musabaha,Abun mamaki Da kansa yau ya mikama Khamis hannu suka Gaisa suna kallon Juna ido Cikin ido.
Imran kallon kayi kadan yake yi ma Imran irin na Riga na gama Dakai shi kuma Khamis Kallon Au ka Tuba ne..?Irin dai dole dai ka dawo Hanya yaro.
Daganan Dakin Daada ya Shiga ya gaida su Abba,Da Daddy sai Inna Maimunatu,Yana kallon Goggo Bintalo da Baffa Kabiru yaki gaishesu da Abba yayi mgana sai yayi Shuru ciki Ciki ya gaishesu kamar bai ganesu ba,Abun yayi ma Inna Bintalo Ciwo sai dai bata mgantu ba Kada yaron ya Zageta tasan Tsab zai iya Tunda bai da kunya,Baffa Kabiru kam bai Damu ba Domin yasan Daman yaron baya Darajasa kuma bai Dauke sa a Uba ba.
Dakin da suka sauka wanchan karon nan suka kara sauka shi da Sagir wanka Imu yayi ya sauya kaya saboda yana jin Zafi,yazo da karamar Laptop dinsa saboda aiki akwai aikin da Wani Ma"ikacin su zai turo mai Daga gyagyadi branch yau din so yana Bukatar ya Duba shiyasa yazo dashi Wayarsa ya Dauko domin yaji karan Shigowar sako Kamar yadda Ya zata Intee ce.
Tana Tambayansa ko sun issa Lafiya ya Tura mata da cewa eh suna Dukku,Daga haka ya maida wayarsa aljihu,agogon Tsitsiyan

Please Login or Register in order to submit comment