Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Gida yafi a barsa chan inda bai da kowa abakin Daada yaji Labarin Rashin Lafiyar Sajida shi kanshi in da Zai kwanta adubasa Wlh Jininsa ya Hau har suka gama mgana Da Daada baya Cikin Hayyacinsa Hawaye da kuka sun Rufemai jinsa da ganinsa Allah yasa yana gida kwana Biyun bai je ko"ina ba.
Sai da ya Samu Natsuwa ya Kira Abba da Daddy ya gayamusu komai suma Hankalinsu ya tashi Daddy yace Da kansa zai hau jirgi zuwa Anambara Gobe zaiTaho da Khamis Basai Abba da Baffa Kabiru sun taho ba Yace Baffa Kabiru ya turamai Address din nan da nan kuwa ya Turamai sun Rabu kan Gobe zai tafi Sajida kuma Zai je Har makaranta ya Taho da ita Gida.
Ashe abunda basu sani ba Khamis bayan ya Dawo Daga Hayyacinsa budurwansa abokiyar Watsewarsa Tasa mai suna Suzana,Ta sanar dashi Zuwan Mahaifinsa da Halin Daya Tarar dashi,Batasan Baffa Kabiru ba ammh Kamarsu da Khamis da kuma cemata da yayi shi babansa ne aranar Dayazo bayan ta Budemai kofar Falon Gidan.
Gabadaya Jikin Khamis ya gama yin Sanyi Tsoron Allah ya kamashi da wani ido zai kalli Dad dinsa..?wata amsa zai bai bashi in ya Tambayesa meyasa ya koma haka..?yace Saboda Rasa Mace..?ya koma Sabama Allah..?wannan duka ba Hujja bane ya karya Zuciyar uban Daya Dora yakini akansa Tir da Rayuwar Daya Zabama kansa Tundaga Ranar ya Tattara komai ya Watsar Tare da alkawarin Har Abada bazai kara ko Busa Sigari ba ballatana Har ya Daga wata kwalba ya Rufe babin mata da komai na Harkan Shanshanci Har Abada ya Fara Shirin Tahowa gida Domin ya Nemi Gafaran Daad ya yafemai Laifin Daya aikata.
Aranar da Baffa Kabiru sukayi mgana da su Abba da asuba Khamis ya Sauka a Filin Jirgin Abuja Taxi ya samu zuwa Gida sai dai Baffa Kabiru da Umaima suka gansa Kwatsam Allah Sarki Rayuwa Khamis yayi kuka sosai Dayaga yadda ya tafi ya bar Baya da Kura Mami Ta Dade bata gida sun Rabu da Daad Sajida Tana makaranta Cikin Halin Ciwo shi kuma yana chan yana Shanshanci Kai consa,Abakin Umaima yake jin komai Domin Sanda ya iso Dad na cikin Dakinsa sai da ya Fito ya gansa..
Haka Khamis ya Duka ya Rike Kafafun Baffa Kabiru yana kuka yana Rokonsa Gafara Tare da alkawarin ya Daina Duka Abunda yake yi Har Abada bazai koma ga aikin Daya baro ba Me ya kamata Baffa Kabiru yayi banda ya Tallafi D"ansa da Allah ya Dubesa ya Karkatomai da Hankalinsa kan Hanya Madaidaiciya ya Rumgumesa yana Godiya ga Allah Hawaye na Ziraromai bai bari Khamis din ya gani ba yayi Saurin Dauke hawayen..
Nan da nan Baffa Kabiru ya Kira Daddy ya Fadamai ya Dakata da Tafiya Anambara ga Khamis ya Dawo gida da kansa jin haka yasa yayi Hamdala Daddy ya Kira Abba ya Fadamai Khamis ya Dawo gida Abba ma Nata Hamdala sun isa Barka.
Aranar ma Baffa Kabiru bai Fita ba yana Tare da ya"yansa Khamis da Umaima Domin ya Dauki Daraman Gyaran Duk inda ya Kuskure Domin Dawo da walwalan ya"yansa sun yanke Shawaran gobe da safe dashi da Khamis zasu je makarantan su Sajida su Taho da ita sai dai Misalin karfe Daya na Dare Sai ga wayar Mami Asma"u ta Kira Baffa Kabiru karo na Farko Bayan Lalacewar abubuwan Daya ga Kiran bai Dauka ba Tunda Idonsa Biyu Har Lokacin bai yi barci ba Mugun Haushinta yake ji Gani yake Munfuncine ba Tuban Allah da Annabi bane gani tayi ba Sarki sai Allah ta kuma Rasa komai Shiyasa ta Dawo Tana Rabe Rabe Macijiya.
Sai da yaga Kiran yaki ya kare kana ya Daga afusace ya auna mata ashariya ko Ta kyalesa sai da jinta Cikin kuka Tana Fadamai gasu a asibitin Specialist Hospital inda aka kawo Sajida bata da Lafiya Tana ta Tari da Jini Jin haka yasa Hankalin Baffa Kabiru ya kara tashi Cikin Tsananin Tashin Hankali ya Zura Jallabiya ya Fice Dakin Khamis ya shiga ya tasosa hankali Tashe yake Fadamai Halin da ake Ciki,Shima Hankalinsa ya Tashi Umaima ma Muryansu ya tasheta Daga Barcin Daya kwasheta itama jin Abunda ya Faru da yar"uwanta sai kuka Gabadayansu suka Dunguma suka Tafi.
Koda suka je sun Iske Mami Asma"u da Hajiya Turai da Justice Tafida yarkace yarkace sai kuka Take TanaTuma kamar Mahaukaciya Idanuwanta sun Kole saboda kuka Ita jenefer ta Kira saboda itace Lambar Karshe da Sajidan Tayi mgana da ita suna Kwance adaki Sanda Tarin ya Sarke Sajidan da Zafi Har ta Fita Daga Hankalinta Jenefer ita taje ta Fadama Maman Hostel dinsu ita kuma ta Sanar da kuma Hukumar makaranta aka Kwaso su zuwa asibiti bayan an Shiga Da Sajida Emergency ne Ta samu Wayar Sajidan ta Kira Mamin Ta Fadamata wanda Kurruwanta ya Fito da Justice da Hajiya Turai jin Abunda ke Faruwa yasa suka Rankayo Gabadayansu Cikin Tashin Hankali.
Ita uwa uwace ko ya ta Zama Haka Umaima da Khamis suka isa ga Mami Asma"u suka Dagota suka Rumgumeta suna Lallashinta Data kyalla ido Taga Khamis sai Rauninta ya bayyana ta Fada Jikinsa Tana Fadin"kaima ka Gujeni Khamis..Dad dinku ya sakeni Sajida Zata Mutu ta barmu Aman jini fa take..an shiga da ita Likotoci basu Fito ba Har yanzu na shiga ukuna na Lalace..!
Haka take fada Cikin kuka tana Rike Jikin Khamis da shima yake jin kamar ya Fashe da kuka Idanuwansa sun yi Jajir kukan Mami kuka ne da zai Kassara Duk zuciyar mai Sauraranta Ammh banda ta Baffa Kabiru bayan gaisawa da Justice Tafida da Hajiya Turai bai kara mgana ba sai gaisuwan abokiyar Karatun Sajida Jenefer Daya amsa ko Barayin Mamin bai kallah ba Ballatana ta saka Ran wani Rahma Daga bangaransa.
Gabadaya Hankula basa kwance Fin Mintina arba"in kafin Likitocin da suka Rufu kan Sajida su Fito basu tsaya amsa ma su Baffa Kabiru Tambayansu ba sukace jictice Tafida ya Biyosu Office shi da Baffa Kabiru Matan su Tsaya a waje.
Baffa Kabiru ya Razana Dayaji bayanin Likita kan Abunda ke Damun Sajida ta Hadu da Heart problem Ciwon Zuciya Wanda har ta Fara Tabuwa saboda matsanancin Halin Datake Ciki Ta fara ganin jini in tana Tari bata zo asibiti ba har abun yayi yawa,Ammh dai yanzu ta Fita Daga Cikin Hatsarin Datake ciki sai dai Duk Abunda akasan Tana son gani ko Tana so a kawo matashi gabanta da Zarar ta Farfado in ba Haka ba zata samu Heart Attack arasa ta gabadaya.
Baffa Kabiru Haka yake sharan kwallah Da Gaske Sajida take Tana son Imran Asma"u ta rabata dashi Gashi Soyayyarsa zai Zama ajalinta Shi kanshi Justice yaji Mganar sosai Jikinsa yayi sanyi shine ya iya Fita yayi ma su Khamis Bayanin da Likita yayi musu ai sai Wajen ya kara Rikicewa Mamin Har wani Suu Tayi Zata Fadi Hajiya Turai da Khamis suka Tarota kasa takai hannunta Saman kanta ta manta asibiti suke ta Kwarara Ihu Tana Fadin"Na shiga Uku..Na Shiga uku Ni Asma"u na lalace..!
Baffa Kabiru da Ransa ya baci Tana Neman Tara musu jama"a Allah yasa ma Dare da sanin su manyan Mutane ai da ba haka ba wata Gigitattaciyar kara ya Daka mata Cikin Kaushin Murya ya fara fadin"Dillah kima Mutane Shuru..Kukan Uban me kuma Zaki mana..?kukan karya da munafunci..?ko na nadaman Dole..?duk abunda ya Faru da Sajida kece Sila...ke kika Rabata da abunda take so kika yi Sanadiyar Shigarta wannan Halin sannan kizo ki Damemu da kukanki na Banza Baki bani kin Lalace ba Asma"u Sai Y'ata ta Rasa Ranta ta Dalilinki na Rantse da wanda Raina ke Hannunsa sai nayi Shari"a dake sai kin Biyani Diyar kashemin yata da kikay Muguwa kawai azzalumuma mai Zuciyar Zalunci wacce batasan komai ba sai kanta.!
Ya karishe Fada Cikin Sakarmata Jajayen Idanuwansa da suka Rine Saboda kuka
Ba wanda iya mgana sanin ai gaskiya ya Fada Mami Asma"u jikinta na rawa da bakinta ta kasa mgana Jikin Khamis ta koma ta Lafe Umaima ta Kwantomata Tana kuka ai ita kukan natama ya Tsaya ta shiga wani yanayin da bawa bai isa ya Fassara ba.
Hajiya Turai ne cikin Damuwa tace"Haba Kabiru don Allah ka Ragama yarinyar nan mana..Tafuskanci abubuwa da yawa ko baka Ragamata ba Saboda Zaman tare ba ai ka Ragamata saboda Daranjanmu iyayenta Dake Tsaye da su kansu Yayanku gasu nan da kuma Wacce ke kwance cikin nan Cikin Kokawaa da Numfashinta..!
Ai in ma ya Bude baki yace wani abu Allah Zagin Hajiya Turai zai yi shiyasa yayi Shuru ya Dauke kansa yana ajiyar Zuciya
Sai Wurin yayi Tsit sai Jan majinan Umaima ake ji Mamin kamar ai Wutarta ta Dauke justice kala bai ce Daman ba kuma zai ce ba Wanda bai ji bari ba bazai ji Hoho ba
Dukkansu Zaman jiran Farfadowam Sajida suke Gabadayansu suna asibitin aka Kira sallar asuba kana Mazan suka tafi masallaci cikin Asibitin Harda matan sukayi Sallah Kowa Zuciyarsa ba Natsuwa Jenefer sai alokacin Tayi musu sallama ta koma Cikin makaranta su kuma tunda suka Dawo Sallah ba wanda ya Mtsa suna Fatan Sajida ta Farfado Cikin Hankalinta.
Saboda Tashin Hankali yasa Baffa Kabiru ya mamta da Kiran kowa Sai da Sajida ta Farfado Daman Tana Emagency din har alokacin Likitoci sun Rufu kanta ammh ba sunan Datake Kira sai sunan Imran kuma Rashin Ganinsa Cikin Lokaci Mtsala ne haka Likita ke sanar dasu Baffa Kabiru Hankulansu ya kara tashi an basu Izimin Shiga su ganta Mami ce kan gaba Kamar Zata Kifa Tana Shiga Tafada jikin Sajida dake kwance Rai kwakwa Duk ta Rame tana mai Fashewa da kuka Tana Fadin"Ki yafemin Sajida..Dom Allah ki yafemin..!
Sajida Tana kuka Tana Rike Saitin Zuciyarta Tana Fadin"Mami Ku kiramin Imran in ban gansa ba Mutuwa Zan yi..!
Take Fada Tana kuka Gabadayansu Sun Zagayeta masu Saurin kuka irin su Hajiya Turai da Umaima suna ta Faman Sharbawa Justice Tafida ne ke Fadan Mami Ta Daga Sajida bata ga bata da Lafiya bane kuma ta Danneta Tana kuka Khamis kuwa Gefen Gadon ya Durkushe yana kokuwa da Numfashinsa.
Baffa Kabiru waje ya Fita yana Dauke kwallarsa bazai iya Juran ganin Sajida ahaka ba ba ita ya kamata ta Fuskanci wannan ba Asma"u ita ya kamata ta karbi wannan Hukunci.
Kai Tsaye Abba ya Kira da Daddy ya Sanar dasu abunda ke Faruwa Hankalinsu ya tashi Kwarai Tare da Tsausayin Dan"uwansu dukkansu sun Tabbatar mai gasunan zuwa yanzu zasu kamo Hanya.
Daga su sai Imran Baffa Kabiru ya Kirasa Lokacin ya bar Gida zuwa Wajen aiki ne Jiya gidan Abba suka kusa Raba Dare Khalil ne jiya ya zo Daga Lagos wajen Munari mgana har Taje kunnensu Abba Tunda Dr.Ali argungun ya Kira Abba sun yi mgana,Wajensa ya Tsaya suna Hira da kuma Rigiman Inteesar na da sai ya barta ta Kwanan anan ya Tubure mata ya dawo Mata a Imran dinsa da baya Daukan Raini ballatana Wargi Dole ta biyosa suka Dawo Ko yau da Safe ya Fita ya barta Tana ta Fushi ya Fita Batunta daya dawo ya Fara Lallashinsa Zata mamta komai ta bada kai Bori ya hau.
Lokacin da Baffa Kabiru ke Fadamai Halin da ake ciki jikinsa yayi Sanyi sai bai kara yin sanyi ba sai da yaji Baffa Kabiru na Rokonsa Allah da Annabi kan yazo yaga Sajida kafin ta bar Gidan Duniya yana mgana Daga jinsa kuka yakeyi Imran bai taba Jin Tsausayin Baffa Kabiru ba irin na Wannan Ranar ba har baisan Sanda ya Tabbatarmai da Insha Allahu yana Tafe yanzu da yardan Allah..
Jikinsa a sanyaye ya Tattara kayansa ya Biya Office din Manaja ya Fadamai Uxurin Rashin Lafiya ne yamai Izinin Tafiya ya Fito Daga Bankin kenan yaji Kiran Abba ya Dauka sukayi mgana Abba yana Fadamai Halin da ake Ciki yace Yanzu Baffa ya Kirashi shima Abujan zai tafi yanzu Abba yace yaje ya Dauko Inteesar gabadayansu Zasu Tafi da haka suka Rabu.
Gida ya koma Inteesar na Kwance da Matashin Cikinta yace ta tashi ta sa Hijabi su tafi shi ya Zata gidan Abba zata zauna kafin su dawo jin Tafiyace ta Mike da Murna ta saka Hijabi suka Tafi koda sukaje sun iske har Ya yusuf shima dashi Za"a tafin bai je aiki ba Khalil ma yace dashi Za"aje Kowa yace sai yaje harda Munari Anty Safiya ce kadai aka bari agida Tana jego Saboda Yadda Labarin ya same su sun matukar Tsausayamata da Halin Datake ciki,ganin haka yasa Itama Inteesar tace sai taje itama Imran bai da yadda zai yi ya Hanata zuwa ammh bai so bayaso gudan Jininsa ya Wahala sosai ammh baida yarda zai yi.
Ashe Labari Tuni ya Zaga Dangi suna Shirin Tafiya sai ga Wayar Sadam shima zai je basheer ya Kirasa ya Fadamasa yace ya Kira sa"id shima ya Tabbatarmai da yana Hanya Duk wanda yaji Halin da Sajida Take Ciki Sai ya Tsausayamata.
Sadam suka Tsaya jira ba Dadewa sai gashi Shi kadai ne Aneesa na Gida da Yara Imran ya Kira Sagir yace ya Shirya su tafi Daman jiya su ukun suna Tare sun Hade shi da Khalil suna ta Caccakasan yayi musu banza.
Imran a Motarsa ya Dauki Khalil da Sagir Ya Hada matan chan Motar Yusuf,Abba dagashi sai Direbansa hakama Ya Sadam suka Dauki Hanyar Abuja,suka bar Anty Safiya Dayake Tasleem na Tare da ita ga kuma Mama
Achan kaduna ma Daddy Da Umma sai Ya Basheer Dake Tukasu suma din duka Hankalinsu ya tashi goggo Bintali da goggo Maimunatu suma sun ji labari Daddy ya Kirasu ya Fadamusu,Daada ce kadai basu Fadamawa ba Gudun Tashin Hankalinta,Dukkansu sun kamo Hanya basu zauna ba Domin Haka suna da kara iin wani abu ya Faru da nasu kwansu da kwakwartansu.
Daddy su suka fara isa Abuja waya kadai yayi ma Baffa Kabiru ya basu kwatancen Inda suke,Daman yasan asibitin nan take sai gasu sun iso Lokacin an kai Sajida ma Daki na Musamman kebabbantacce.
Koda suka iso an mata Alluran barci Ta samu barci ganinta Tana ta kuka da Sambatun Kiran sunan Imran Umma ta kara jin jikinta yayi Sanyi ganin yadda Mami Asma"u ta koma Kunya Ya hanata ta iya Daga ido ta kalli kowa Kukan ma ya Daina zuwar mata sai ajiyar zuciya kawai ta Jeme kamar ba ita ba Shi kanshi Daddy sai da ya Jinjina.
Gudu sosai sukayi a Hanya kafin su iso,wajen azahar suma Direct asibitin suka iso,Mami Asma"u ta kasa Iya Hada ido da su Abba ballatana Imran Kusan Lokaci Daya suka iso da Inna Maimunatu da Mijinta ,Inna Bintalo ma ta iso
Daddy da Abba Dan"uwansu suka Rumgume cikin Damuwa da ganin yadda shima Duk ya Jeme Saboda Damuwa su Sadam suka isa ga Khamis shima abun Tsausayi Umaima ta Rumgume Munari Tana ta kuka,ba Dadewa sai ga Sa"id ya iso Shi da Fareesatu da Hafsah da yara Inteesar dai na makale da Umma itama Duk jikinta yayi Sanyi,Khamis kuwa Sau Daya ya kalli Inteesar bai kara ba haka itama Imran na Tare da abokansa Sagir da Khalil,Sai dai Kuma karo na Farko da yaji Taausayin Mami ya Darsun mai ganinta a rakube Duk ta Fige ta Rame kamar ba ita ba Rayuwa kenan Dayake Justice da Hajiya Turai sun Koma Gida Dazu bada Dadewa ba
Kamar Sajidan ta sani suna isowa ta Farka ta Fara Kiran sunan Imran,gabadayansu suka Nausa Cikin Dakin Baffa Kabiru ya bangaje Mami yana Hararanta wacce ta isa ga Sajidan Tana Riko hannunta Mami kanta na kasa ta kasa dagowa ma ta kalli kowa sai Hawaye dake bin Kumatunta Kowa adakin sai da ta bashi Tsausayi Umma ce ta Rikota zuwa gefenta ganin Tana neman Faduwa.
Baffa Kabiru ya isa ga Sajida ya Riko Hannunta yana Fadin"Sajida ga Imran nan yana jinki..Gashi nan kin gansa..?
Yafada yana Nuna mata Imran wanda Abba ya jawosa Gefen da Baffa Kabiru ke Zaune daga ido Tayi tana kallonsa Shima kallonta yake yi cikin Kallon Kuduran ubangiji ganin yadda Sajidan ta koma Lokaci Daya..
Idanuwanta na Zubar kwallah ta Kira Sunansa..!

Imran..!

Sai Hawaye sharr..Baffa Kabiru ya tashi Daga kujeran Dake gefen Sajida ya nunama Imran alamun ya zauna ba Musa yaja ya zauna Cikin bayyana Jimaminsa sai dai bai nuna afuska ba,inteesar na gefen Munari duk sai taji Kishi ya kamata kada fa ace Mijinta ya sake auran Sajida..?domin bazata iya zaman Kishi da ita ba..!
Sajida ce ta kara kiran sunan Imran yasa ya amsa mata Cikin Muryansa mai Cike da Zati tana kallomsa Tace"Imran nasan ka Tsane ni ko..?
Sai kuka wiwi sai tari mai Hade da Jini Imran yaji wani iri acikin Ransa Hannun Sajidan da ba"a sakama Drip ba ya Rike gam yana Fadin"Wlh ban Taba Tsanarki ba Sajida..!
Yafada yana jin Rauni da Taausayinta sai dai ba wai don yayi Nadaman Sakinta ba A"a baya sonta bazai aureta ya Cutar da ita ba.
Sajida tace cikin muryan kuka.."Meyasa ka sakeni..?meyasa baka sona..!
Imran ya Runtse ido kafin ya Bude yace"Na sakeki ne saboda bana sonki na aure ki in na Zauna Dake zan kwareki..Inteesar nake so..Kinga bai kamata na Zauna Dake ahalin ina son Wata ba..Kuma ni zuciyata Tana Girmama Ra"ayina mganar na Tsaneki bata taso ba..Ina sonki Soyayya irin ta yar"uwa da Dan"uwanta..!
kafesa Tayi da ido kafin tace"Kana sona Kamar kanwarka Munari.?ko haka na samu ma na gode..!
Take Fada Tana Hawaye Hannu ya saka yana Dauke mata Hawayen Lokaci Daya yana Fadin"Ki Daina kuka..Munari ta zama Old kece sabuwar kanwar tawa Tilo....!
Tana Dariyan DAuriya tace"Ko yau na Mutu naji Dadi..!
Imran yace"Ba mutuwa yanzu kamwata..Maza kitashi Aure ma zan yi miki da yardan Allah..!
Cikin Rinanun idanunta tace"Wazai aureni...?
Bai amsa mata ba ya Dago kansa yana kallon Khalil Dake kallonsa Shida Sagir Gabadaya ma Dakin Hankalunsu na kansu Banda Inteesar da Kishi ya Turnike tun sadda ya Rike hannun Sajida ta kauda kanta.
Tashi yayi Tsam yaje ya Riko Hannun Khalil wanda ya saki baki yana kallonsa Munari ma haka dasu Abba Har gaban Sajida ya Zaunar dashi inda ya tashi ya Dauki Hannunsa danata ya Hada yana kallonta yace"Ga Mijin dana Zaba miki kanwata ina Fatan bazaki bama yayanki kunya ba..!
Yafada yana kallomta kafesa Tayi da ido kafin tace"yana sona ne..?
Imran ya kalli Khalil dayayi sunan Zaune Kafin yace"Sosai ma..Tambayesa kiji..Wazai ki Zangadediyar yarinya kamarki Diyar Lauyoyi jikar Lauyoyi..!
Ya karishe Fada da Sigar Zolaya.
Sajida ta kada kai Tana dariya da Hawaye Lokaci Daya Tana kallon Khalil da jikinsa ya gamayin Sanyi ya Imran zai mai haka ya manta da Munri ne kamar yadda Itama Munarin ke Tambayan kanta haka suna kallon juna ita dasu Hafsah da inteesar.
Sajida na kallon Khalil tana Fadin"Kana sona da gaske..?
Tafada Cikin karyayyiyar murya Cikin Rauni da saka rai Imran ya Daki Kafadan Khalil bayan ya Dago ya kallesa Kallon ya zakamin haka.?
Bazai iya watsamai kasa a ido ba yasa ya Gyadamata kai yana Fadin"Indai kin amince ko gobe ne A Daura mana aure..!
Sajida Sai Farinciki ya kamata ko bata auri Imran ba ko bai sota ba ya Fadamata bai Tsaneta ba sannan itama Zatayi aure kamar kowa sannan Zata auri abokinsa Daman haka Rayuwa ta gada ba Lalle ne sai mun samu abunda muke so ba..
Ido ta Runtse sai Hawaye gabadaya Kowa sai jikinsa yayi sanyi Khalil ya Kasa Hada ido da Munari Lokacin Datake kallonsa na yaya Zakayi Dani..?
Imran ya isa gaban Baffa Kabiru yana Fadin"Baffa Khalil abokina ne..Zaka bashi Auran Sajida..?
Baffa bai san me zai ce ba iya Kafadan Imran Daya Dan Daka yana Fadin"Allah ya sanya alheri..!
Abun fa na Imran ba wasa bane kamar yadda wasu suka Dauka.
Gaban Mami ya isa kafin yace"Mami Zaki bama abokina Khalil yarki..Kin gansa ko Sigari Bai taba Shaba..Sai dai Ma"ikancin banki ne kamata babansa kuma Malamim Jami"a ne kamar Mahaifina ba Lauya bane kuma ba Jikan Lauyoyi bane..!
Yafada yana kallonta Mami kuka ya Kamata batasan Sadda ta Durkushe kasa ba Tana Fadin"Ku yafemin don Allah ku yafemin.!
Yadda Take kukan sai ta bama kowa Tsausayi Imran ya Saka Hannu ya Dagota yana Fadin"Haba Mami..Bai kamata ki Dukamin ba..Nima ya kamata na Duka miki nima ai nayi Miki Rashin kunya ki yafemin.?
Mami na Kuka Tana Fadin"Wlh bakamin komai ba Ni nayi muku..Maimunatu Malami da Mustapha ku yafemin Kabiru kaima ka yafemin da duka sauran wadanda na Batawamawa ku yafemin.!
Kuka take jiri neman gadata Imran ya Riketa da Sauri Khamis yazo ya Taimakamata Daddy yadauko mata Kujera ta Zauna Abba ya Miko Ruwa suka Bata ta karba tasha Tana Dauke kwallarta Tana Musu Godiya Abba da Daddy sukace su bata musu komai ba sun yafe mata.
Inna Maimunatu ma haka Inna Bintalo ma sai Hawaye ganin yadda Mami ke kuka itama ta Roki yan"uwanta gafaran Abunda Tayi ta yi na Gulma da Bin bayan karya sukace sun yafemata.
Munari dai ta kasa mgana kanta na kasa Khamis ya bama Imran hannu suka yi Musabaha bayan sun ma juna Sallama
Khamis ya Kalli Munari kafin ya kalli Imran yana Fadin"Babban yaya Tunda dai am min kafa awajen Inteesar sai ka bani Dayan kanwar Taka Tunda naga kana ta badasu ka manta Dani..!
Gabadaya sai da kowa ya Murmusa Har Sajida dake kwance.
Imran ya shafa kansa yana Fadin"Wacce Daga ciki..!?
Hafsah dai Na Riga na bama Abokina Sagir..Sai Autar Abba Daman ta ishemu na baka ita..!
Ya juya wajen Munari Dake Hawayen wannan Karfin Halin na an rabata da masoyinta za"a likamata wani.
Yace"Ke..Ga Khamis nan shine mijinki bana son gaddama..Saura ki rainasa yayanki ne kuma sojane kinsan sauran..kai kuma in tayi maka ba Daidaita ba ka sauya mata kammani ni na baka Umarni..!
Khamis ya Ramkwafa yana Fadin"An gama Babban yaya..!
Imran ya Dafa kansa yana Fadin"Yauwa dan abarka..Kafi sauran ladabi..!
Yafada yana Hararansu Khalil Gabadaya Wajen sai da aka Saka Dariya ganin yadda Imran yayi Harda Mami da Murna da kunya suka kamata Ita taki Imran saboda yana shan Taba yau ga Malami zai bama D'anta Yarsa wanda har da mata yayi mu"amala Mami ta ji kunya Nadama Ta kara shigarta.
Khamis gefen Munari ya koma yana mata mgana Sagir na gefen Hafsah Hakama Khalil yana gefen Sajida ya Duka yama mata mgana Domin Lamarin Tsarin Ubangiji ne matar Mutum kabirinsa.
Imran ma Wajen Inteesar ya koma ganinta Tana Tura baki Ido ya kanne mata yana Fadin"Sorry..!
Tura baki Tayi ta kauda kai yana Dariya ya rikota su Abba kam suna ta kara bama Baffa Kabiru baki kan ya saurari Mami Asma"u su yusuf kam komai yayi daidai suna ta mgana dasu Sadam Umma na Tare dasu Inna Maimatu kafin Lokaci kadan gabadaya an samu Fahimtar juna gaban kowa da kowa Mami ta Duka ta bama Mijinta Hakuri ya Dagota yace ya yafemata kuma yashaida mata ita din Matarsace tun sadda ya Saketa yan"uwansa suka saka ya maidata Mami ta karajin kunya ashe haka su Abba suke..?yadda taci ma Daada Zarafi basu Riketa aransu ba da sun Riketa da basu ceci auranta ba Hakan ba karamin Dadi yayi ma Khamis da Umaima ba suka Hadu suka Rumgume Mamin da Baffa Kabiru Sajida na kwance Tana Miko hannu suka Tafi gareta suka Rumgumeta Mami nata kuka tana share ma yarta Hawaye
Kowa sai Dauke kwallar Farnciki yake yi Munari ma Tuni ta Daina kuka suna ta mgana da Khamis Domin ta ma Cire Khalil Daga Lissafinta Lokaci Daya Taji Khamis din ya kwanta mata kamar yadda Shima anashi Barayin yaji Sajida tayi mai daidai dashi Duk tun a hanya sagir ya bashi Labarin abunda ya Faru da komai da komai.
Likita ne yazo ya Korasu waje suka Duba Sajida suka mata allura Barci Likita ya Fito da Murnan ganin Chanji Tare da tabbatar musu indai Sajida Zata kasance Cikin Farinciki Zata Samu kanta dayardan Allah
Sai da suka baro Dakin ne Imran ya Radama Yusuf wata mgana akunne shi kuma yaja Daddy da Baffa Kabiru ya Fada musu suna Dawowa suka kalli Abba Daya Tsargu Baffa Kabiru yace"Malami kaima aure zam maka nagaji da ganin ka ahaka..!
Abba ya Zaro ido gabadaya wajen aka Saka Dariya Daddy yace"Eh musan zaka ce baka da wacce ka Tsaida mu muma dashi..Imran da Yusuf sun ga Chanchantar Amina yayar Salaha..Maman Sagir Saboda haka ita muka Zaba maka itama musan bazataki ba..!
Abba zai yi mgana kenan Imran yayi Zaraf yace"Kuma saboda Daada..Allah ta kusa Mutuwa gwara dai ta Fara Daukan sauran ya"yanku kafin namu!
Abba ya kaimai Duka yana Hararansa ya Goce jikin Yusuf gabadaya aka saka Dariya Yusuf ya Daga hannu sama yana Fadin"Ba ruwana Abba Imran ne..!
Yadda yayin ne Zaka gane bai da gaskiya Dariya aka kara sakawa Sagir ma Farinciki ya Cikasa Abba ai Mutum kwarai ne kowacce mace Zata so ya Zama bangonta.
Inna Maimunatu ta Kira Daada ta Labarmata komai Daada nata Kukan Farinciki

Please Login or Register in order to submit comment