Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Iske Mama ta shirya tana Jiransa Lokacin Inteesar din taji Sauki ta Daina Rike cikin,Nan ya fadama Mama ya samo mai adaidatan yana Waje ammh Imran yace basai taje ba Shi zai rakata su kaita tare .
Mama tace taya zata barta su tafi da ita dukkansu fa Maza ne sai dai suje tare,Inteesar na jin haka tace ma Mama ta zauna saboda Dare zata iya Zuwa Insha Allahu jin haka yasa Mama bataso ba ta barsu suka tafi har Waje ta Rako Inteesar tana Rike da Hannunta,Mama dai taga Dare yayi kuma Inteesar mace ce Sagir Namiji ne Imran ma haka sai kawai ta ce bari ta Rufe gidan tare zasu tafi ba wanda yace mata wani abu..
Tunda Mama ta Rikota yake kallonta Bata ma iya Tsayuwa sai da ta Jingina da Bango Tana Halin ciwo ne ammh Ganinsa yasa taji wani Sanyi Mama ta kulle gidan ta Kamata suka Nufi adaidaita,Mama da Inteesar suka Shiga Baya Sagir da zai shiga bayan sai Imran yayi Sauri ya Shige shi kuma sai ya zauna agaban adaidaita Wani asibitin kudi Sagir yace mai adaidaitan yakaisu.
Inteesar tana kan Kafafun Mama ne da Farko ammh da Ciwo yayi ciwo ta fara Mirginawa tana Rike da Cikinta Tana kuka tana Fadin wayyo Allah zata Mutu Tsausayinta ya kamasu Mama ta kamata ta fashe da kuka Tana fadin mai adaidaita ya yi sauri Imran kuwa yana Zaune ne kamar ya Ciro ciwon jikinta ya maida akansa Rabin jikinta yana jikinsa ne,domin ta kasa Zama waje Daya Hannunta Guda ya Rike gam yana mata addu"an samun Sauki acikin Ransa.
Tana Halin ciwo ammh Rikons na Dabam ne Idanuwanta cike da Hawaye take kallonsa Cikin so da kauna mai Zafin data shigets bata sani ba...
Koda suka karisa asibitin ta galabaita Suna zuwa aka amsheta ganin yanayinta Direct gado aka bata ma,aka sakamata Drip da allurai sai barci Lokacin ta samu sauki ba kamar yadda suka zoba,Likitan yace sai dai ta kwana sai zuwa gobe sai su sallameta agaban Mama da Sagir da Imran yayi ma Mama bayanin ciwon Mara ne ya Sarketa mai Tsanani In Jinin ya Zuba sosai zuwa gobe zataji Dama,ammh ya mata alluran zuwa Gobe in ta Farka zata wartsake.
Dole Mama ta zauna ta kwana da ita Sagir da Imran sai 11pm suka koma Gida,Sagir ya Tsaya gidansu Imran ya wuce gida koda yakoma Abba da Ya yusuf basu iya Runtsawa ba Saboda susan baya taba kaiwa Dare kuma suna ta Kiran wayarsa bai Dauka ba Shi kuma yaga Kiran sai dai lokacin suna asibiti ne.
Yana Dawowa Yusuf ya faramai Tambayan ina yaje..? Bai iya karya ba kai tsaye ya fada musu Inteesar suka kai asibiti bata Lafiya sai jikinsu yayi sanyi sosai Suka Tambayesa ya Jikinta..? Yace taji sauki tana chan asibitin Daganan ya shige daki Baida wata Natsuwa bai yi wani barcin Kirki ba sosai saboda Zullumi.
Washegari Munari taji labari Hankalinta ya tashi ita da Anty Safiya suka tafi asibitin Da ya yusuf harda Abba koda sukaje Inteesar ta farka Taji Sauki sun iske Sagir yazo da ruwan da Zafi da kayan Tea Mama ta taimaka Inteesar ta wanke baki tana bata Tea.
Hankalin Munari ya kwanta saboda Taga Inteesar tasamu sauki Mama tace likita yace anjuma zasu koma gida tunda taji Sauki,Imran yaki zuwa asibitin tunda yaji suna chan,to suna ma asibitin aka sallameta sai Yusuf ya kawosu zuwa Gida kana ya koma ya Dauko Abba da Sagir.
Munari nan ta wuni gidan Mama tana kula da inteesar wacce taji Sauki Sosai Shiyasa tace ma mama kada ta Fadama su Daddy tasan Halinsa yanzu Hankalinsa zai tashi,Tana asibiti yana ta Kira mama ta Dauka Tace mai sun shiga makaranta ta bar Wayar agida,Sai davta dawo ta Kirashi Jin Lafiyanta kalau yasa Hankalinsa ya kwanta.
Imran Tunda yaji an sallamo Inteesar sai hankalinsa ya kwanta bai Je ya Dubata ba sai dai ya kirata a waya yayi mata sannu da jiki yace ta Rika shan ngani ita duk kunya ya kamata Saboda kowa yasan Mtsalanta..
Monday bata samu zuwa makaranta ba sai Munari ne ta leka sai Ranar Talata data samu sauki sosai ta shirya suka Tafi tare.
Ranar alhamis da suka tashi makaranta basu dawo gida ba gidan Ya Sadam suka sauka gaida Waleeda Data ke ta Zazzabi sunyi waya da Aneesan take fadamata sun iske taji Sauki waleedan har tana wasanta.
Sunyi sallar la"asar sunci Abinci Daman koda suka zo Sadam baya Gida suna Shirin Tafiya sai gashi yazo Aneesa ta dinga Kiransa ta mtsamai sai yazo yaga Munari.
Yau ta kara tabbatar ma kanta Munari ce ta Hoton nan saboda ta kara Duba Hoton wayar Sadam,Shine dai bai ganta ba saboda wayar nan tata bata tashi ba wata ya siya mata Shiyasa bai samu ganin Hoton ba,Daman Waleedan taji sauki ita Aneesan abun na Ranta ne yasa ta mtsa sai Inteesar din tazo ita da munarin don Sadam ya ganta da idanuwansa.
Tabbas Shima daya ganta Sai da yayi Shock,ita kanta Munarin taji wani iri Data gansa,Sama sama suka gaisa dasu yaja Hannun Aneesa zuwa Cikin Dakinsu.
Sai da suka Turo kofa kana ya Saketa Cikin Sauri tace"Kaima ka ga..!
Bai bari ta karisa ba ya Fiddo da wayarsa yana Fadin"Aneesa kila Wahala ce tazo karshe..Tabbas wannan yarinyar jininmu ce..!.
Yafada yana Binciko Hoton sai gashi ya gani Daidai Munari yayi Zooming yana nuna ma Aneesa lokaci Daya yana Fadin"Indai kuwa ba itace bace suna mugun kama..!
Aneesa tace"nifa inaji ajikina itace..Ka duba kaga kammaninta duk da bata kai haka alokacin ba kamminta bai bace ba..!
Sadam ya gyada kai yana Fadin"Meye sunanta..?
Aneesa tace"Maimunatu..Suna Kiranta Munari..!
Ido ya waro yana Fadin"kai..Kin manta Daman Daada tace Karamarsu ita ce taci sunan Mommy..Ina da kyakyawan Zato yarinyar Diyar Kawu Malami ne..!
Aneesa tace"Nima ina da wannan Tabbacin Tun ranar dana fara ganinta..!
Kansa ya dafe yana Fadin"Ina ne gidansu..? Kenan suna garin kano ba wanda ya sani..!
Aneesa tace"Bansan gidan ba Inteesaar tace kusa da inda take zaune ne..!
Wayarsa na Hannunsa yace"jeki falo ki Tsaida mun su bari na kira Sa"id a waya muyi mgana..!
Tana Kokarin Fita tace"Shi kadai zaka Kirafa..Ka mu kira mu fada yazo ba Haka bane..!
Kai ya gyada mata yana Fadin"Nasan Abunda nake yi Aneesa..!
Daga haka ta Fice ta barsa yana Kiran Wayar Sa"id kira Daya cikin na Biyu ya Daga kiran ko sallamsa Sadam bai amsa ba ya Shiga Rattafamai abunda ke Faruwa.
Yana zaune a office ne sai da ya Mike Zaune cikin Firgici yace"Sadam kada ku bari ta subuce muku.Tunda kuka Tabbatar da kammaninta da sunanta am Very sure itace.!
Sadam yace"Nima ina Tunanin haka..ammh yanzu ya kake ganin za"ayi..?
Sa"id yace"Ka kira su Kawu ne..? Sadam yace"Ba wanda na kira sai kai..!
Da sauri yace"Yauwa..kada ka fadama kowa yanzu kada kabari su tafi su kadai ka Tsaida komai ka kaisu kada kayi sanya kasan yadda Zakayi ka Shiga Har cikin gidan nasu domin ka Tabbatar da abunda muke zato..!
Sadam yace"Shikenan yanzu daman koda Aneesa ta Kirani zasu tafi..Bari na fita nace zan kaisu gida..!
Sa"id yace"Good..Yadda ake ciki ina Jiranka sai ka kirani..!
Daga haka suka yanke kiram Jikinsa na rawa ya Fice Saboda Rudewa Cikin Bedroom din ya manta da key din Motar sai da Aneesa ta shiga ta Daukomai nan yace shi da Aneensa da yara zasu kai su domin suga inda Inteesar ke zaune.
Ba wani bata Lokaci Aneesa ta Sako mayafinta,waleeda na Hannun Munari Inteesar ta riko ma Waleed hannun suka Fice ta kulle kofar Falonta.
Inteesar da Munari da yaran suna Baya su kuma suna gaba Sadam yana Driving yana kara kallon Hoton nan na wayarsa yana kara Kallon Munari ta Madubin Motarsa Har sai da ta Fara tsarguwa Tasbihi kawai yake acikin Ransa domin ya gama Tabbatarwa wannan itace Maimunatu diyar kawu Malami.
Sa"id sai kiransa yake bai dauka ba Sai dai ya Turamai sakon suna Hanya ne basu isa ba,In sun isa komai kenan zai kirasa.
Sun shigo gadan kaya Sadam ya Juya yana kallon Inteesar yana Fadin"Bari mu fara kai kawarki gida mu shiga mu gaisa da mahaifinta  sai mudawo mu shiga inda kike zaune agaisa kafin mu wuce..!
Inteesar tace"To ya Sadam..!
Munari kuwa haka kurum taji gabanta na Faduwa kwata kwata bata yarda da zuwa gidansu ba sai dai ta kasa cewa komai.
Tafe tafe Inteesar na nuna Hanyar har Kofar gidansu Munari ya Sadam ya Zuba Hon Iro megadi ya leko cikin mamakin ganin Mota ganin bata Yusuf bane Har ya Bude musu suka Sulala cikin Haraban gidan bai Daina mamaki ba.
Imran dake duke a gaban mashin dinsa d yana gyara Wani Abu ne Daga kasa yaji Shigowar mota bai Damu Daya Dago ba azatonsa Yusuf ne shiyasa ya cigaba da Abunda yakeyi.
A parking space sadam ya faka Motarsa suka Firfito koda ya Fito idanuwansa na kan Imran dake Duke so yake ya Dago da kansa yaga ko waye..!?
Ita kuma Munari duk ta Tsure yau mai kwatanta Hannun Ya Imran sai Allah tunda ta gayyato wasu gidansu abunda ya tsana.
Imran mganar Waleed yaji yana kiran Daaddy,yasa ya Dago da kansa Lokaci Daya yana Mikewa gabadaya
Daidai Lokacin Sadam nata saitinsa suka Hada ido Hudu atare gabansu ya Fadi,lokaci Daya suka Zura ma juna ido Aneesa ma ta Juya tana kallonsa duk da ahoton ya kauda kansa hakan bai hanata ganesa ba.
Imran ya taba Haduwa da Sadam Lokacin gaisuwan rasuwan su Anni a Dukku sau daya domin da suka zo gaisuwa basu kwana ba Shida Sa"id..!Yusuf ne ya sansu sosai Tunda suna waya lokacin sannan suna Haduwa in yaje Dukku duba Daada.
Imran mamaki ne ya kamasa yana so ya Tuna Fuskar Sadam ya kasa..?sai dai yaji wani yanayi ajikinsa.
Sadam kuma sunan Imran ne ya bace masa ya kasa kamawa sai kuma gwiwansa dayayi sanyi ganin yadda Imran din ya Hade rai bamai ma Nuna ya Taba ganinsa ba.
Inteesar da Munari basu Fahimci komai ba yaran sukaja zuwa cikin Gidan Aneesa ta bara musu baya ta Kosa ta shiga gidan ta kara Tabbatarwa ko gaskiya ne duk da Shaidu Biyu sun nuna kansu.
Wayar Sadam ce ta yi kara yana Dubawa Sa"id ne shima ya kasa Natsuwa Kashe kiran yayi ya Turamai sako..!

*Sa'id ina kyautata Zaton Farincikin Daada zai dawo..Gamu aharaban gidan naga ma karin wani Shedan na Mutum daya sai dai ba Yusuf bane na manta sunansa..kada ka kirani sai na kiraka.*

Daga haka ya Turamai kafin ya Dago Imran ya koma ya Cigaba da abunda yake yi.
Ganin haka yasa ya Nufi cikin gidan yana Waigen Imran wanda ke Hangensa ta Jikin Mashin dinsa Haka kurum jikinsa ya basa wannan Dan"uwane duk yadda akayi.
Sadam na shigewa Motar Yusuf na Shigowa Haraban gidan shima yayi matukar mamakin ganin bakuwar Mota Imran dake Tsaye ya rasa abun cewa da Yusuf ya Tambayesa Kallonsa yayi bai cemai komai ba bai Damu ba ya Dauki ledan Yalon daya siyoma Safiya zuwa Cikin Gida ya bar Imran na Tunanin kila yau komai zai Zama Tarihi.
Sadam na shiga Falon ya iske su Aneesa da Inteesar zaune a Bisa kujerun falon da su waleed.
Kallon Aneesa yayi kafin yayi mgna Aneesa ta Rigasa da cewa"Munari taje kiran Abbanta mu gaisa..!
Jin haka yasa ya ja ya Tsaya yama kasa Zama Daidai Lokacin da Yusuf ya sawo kansa Falon da Sallama abakinsa.
Sadam na Facing din kofar Shigowa ya Zurama Yusuf ido shima yana Shigowa Idanuwansa ya fada kansa.
Atare suka Zaro ido Lokaci Daya kowa na nuna kowa cikin mamaki da al"ajabi suka ambaci sunan juna..!
"Yusuf...!
"Sadamm..!
Suka Fada atare adaidai Lokacin Munari ta Fito Daga dakin Data shiga Bayanta Abba ne yana gyara Hulan kansa jin Munari tacemai yan"uwan Inteesar suka zo su gaisheshi.
Sai dai ya Dakata da gyaran Hulan nashi Sanda Idanuwan Sadam suka kusa Fadowa akansa Saboda mamaki Aneesa ma ta Mike Tana kama baki Inteesar ma haka Kanta ya Kulle ita da Munari suna kallon kallon.
Cikin Rawan baki Sadam ke nuna Abba yana Fadin"K...ka..kawuu..!
Yafada cikin Rawan Murya dana baki Abba yayi jagale yana Bin Sadam da kallo Hawaye sun cikamai kwarmin ido kamar yadda na Yusuf suka cikamai Cikin wani yanayi Yusuf yace"Abba ka ganeshi..? Sadam ne Dan Wajen Inna Maimunatu..!
Yafadi haka Daidai a kunnin Imran Daya bayyana afalon bayan kasa Natsuwan da yayi a Haraban gidan.














*Janafty*
3/22/22, 23:07 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*Bazan Rufe wannan Shafin Batare dana ambaceki ba,Godiya ta tayi kad'an na Furta miki Sisina Aisha alto da Hidimar da kikeyi dani da Rubutuna kin yi jimarin Posting din wannan Littafin Daga farko har zuwa yau din nan da muka kawo karshen littafi na Farko Nagode kwarai Allah ya saka miki da gidan Aljannah Firdausi Ameen*

             *🅿?30*

Abba da jikinsa ke rawa idanuwansa sun cika da kwallah suna shirin zubowa Lokaci Daya ya fara takowa Tsakiyar falon duka Idanuwansa suna Kafe kan Sadam kamar wanda ya warke makanta..
Cikin wata irin Murya kewa da Farinciki da kuka Abba ya kalli Sadam yana Fadin"Sadam...!
Ya kira sunansa cikin wani yanayi Sadam da Hawayensa suka gangaro saman Fuskarsa yace"Na"am kawu malami..!
Yafada yana wani kada kai Abba Hannayensa ya Budemai yana Fadin"Taho nan Sadam Taho naji Dumin ka..Taho na ji dumin wani Daga Cikin Ahalina yau..!
Da gudu kamar karamin yaro ya Karisa ga Abba suka Rumgume juna Lokaci Daya yana Fadin"Kawu ina ka shiga muna ta neman ka..? Kowa ya shiga damuwa saboda kai..Daada kowa yaushe kuka take yi yau lafiya gobe babu duk saboda Rashinka..!
Abba yaji Hawayen dayake ta Tarewa sun zobomai yayi Saurin Sharewa Lokaci Daya ya dago Sadam yana Fadin"Ban je ko"ina ba ina nan a kasata..Nayi nesa da gida ne saboda Wasu Dalilai ko bamu hadu ba daman Lokacin da Zan koma cikin Dangina yayi ba saboda kowa ba ko Saboda Daada da nike kwana ina tashi da ita..!
Kada kai Sadam yayi Lokaci Daya yana Dauke kwallarsa Dagowa yayi suka Hada ido da Yusuf dayake sharan Kwallah Wajensa ya nufa yana Fadin"Dan"uwa Yusuf..!
Lokaci Daya suna Rumgume juna Inran na gefe yana Binsu da kallo Fuskarsa bata bayyana Wani Hali yakeciki ba na Farinciki ne ko na bakinciki.
Inteesar da Munari gabadaya sun Shiga Rudani sai bin kowa da kallo sukeyi ita dai Munari ta Fahimci Yau boye boyensu ya kare ne Dangin sun san inda suke ita kuma Inteesar ta Shiga Rudanin kada dai ace Munari yar"uwanta ce..?Abba shine Baffa Malamin da su Daddy ke wahalan nema Daada na Rashin Lafiya Saboda shi ammh take zaune dasu tsawon Lokaci bata taba Sani ba.
Aneesa na gefe farinciki ya cikata Harta su Waleed sun natsu ganin yadda Abbansu ke kuka yana Rumgume da Yusuf,sun dau tsawon Lokaci kafin su saki juna Sadam ya Bubbuga kafadarsa yana Fadin"Shekaru uku ba kwana bane..Duk ka Sauya Yusuf..!
Yusuf na Dariya yace"Kaima haka duk ka Sauya..!
Dariya suka saka gabadayansu Abba na Gefe yana kallonsu Lokaci Daya yana karama Allah godiya daya sa Daada bata bar gidan Duniya ba Tana da Rayuwarta zai koma mata..
Sadam ne ya juya yana kallon Imran Lokaci Daya ya Karisa gabansa yana Fadin"Imran ko .?
Yusuf ne ya bashi amsa ammh Imran Sai ya wani basar Kallon ma wani barayin yayi kamar ba dashi yake ba ganin haka yasa sadam bai Rumgumesa ba illah ya Dafa kafadarsa yana Fadin"Dan"uwa kai bamu san ka sosai ba..Ko a da chan Yusuf ya fika son zumunci .!
Kamar yana mgana da gunki haka Imran yayi mai Abba ya Kalleshi yana Fadin"Imran sadam ne dan Wajen Goggon ku Maimunatu ta Bauchi..!
Dakyar ya iya bude baki yace"Na ganshi..!.
Daga haka ya dauke kansa Sama Sadam bai damu ba ya jinjina kai aransa yana ayyana abubuwa Dadama kan Imran din .
Inteesar ne data gama Shiga Rudani ta Kalli ya Sadam Tana Fadin"Ya sadam...Abba..!.
Tafada Tana kallonsu dukkansu da Sauri Sadam ya Karisa gabanta ya Riko Hannunta yana Fadin"Inteesar baki gane su ba ko..? Baki ga Hoton da Daada tace a nuna ma kowa lokacin da mukaje dukku ba..?
Inteesar cikin kosawa tace"Bangani ba meya faru..?kamin bayani ka sani a duhu naji kana cema Abba Kawu..Kawu malami kardai kacemin Baffa Malami ne..!
Ta karishe fada cikin wani yanayi gabadaya sai kallo ya koma kansu harda Imran daya natsu yana so ya Fahimci wani Abu..
Abba ya Kallesu cikin mamaki yana fadin"Sadam..!
Lokaci daya yana nuna Inteesar da Hannunsa,Sadam ya kamo Inteesar zuwa gaban Abba yana fadin"Kawu  baku gane juna ba..Abba Inteesar itama yarka ce..!
Cikin mamaki yace"Yata kuma..?
Imran ya waro ido yana so ya Fassara mganar hakama Yusuf Munari kuwa Hawaye take yi na Farinciki koda ba"a Fadi komai ba ita ta san kaunar dake Tsakaninta da Inteesar ta jini ce.
Sadam ya dauki hannun Inteesar ya saka cikin na Abba yana Fadin"Kawu Inteesar ce Diyar Kawu Mustpaha na kaduna..!
Abba yaji wani sanyi jiki ya kamashi Lokaci daya da Sauri ya damke hannunta yana Fadin"karamar yarinyarsa..Wacce taci sunan Daada..!
Sadam ya dagamai kai yana fadin"Itace kawu..Inteesar ce kana Tare da jininka ammh baka sani ba..!
Abba ya Ji hawayensa suna Kokarin kara Zubowa ya Rike Duka Hannuwan Inteesar yana fadin"bamu rike zumunci ba sosai ba...Ace yau na hadu da Diyar Mustpaha na wani Lokaci Tana Tare damu ban ganeta ba..Sai dai Wlh har ga Allah Tun ganin Farko da nayi mata naji wani abu acikin Raina ban taba mata kallon bare ba Daya na Dauketa ita da Munari Ashe Ashe itama Diyata ce..!
Yafada cikin Raunin Murya da Sauri Inteesar da itama ta fara Hawaye tace"Baffa....!
Tafada kafin ta fada jikin Abba tana fadin"Nima ina jin haka duk sadda na kanga sai naga kamar Daddy na..Yanayin mganarku da komai iri Dayace..In nazo gidan nan ji nake kamar ina Gidanmu in ina tare da Munari kamar ina Tare da yar"uwata uwa daya uba Daya..Ashe Gidanmu ne ku din Jinina ne Wayyo Dadi Abba..!
Take Fada tana kuka Shima Abba Hawayen yake yi Shi da Sadam da Yusuf Da Aneesa da Kukan Farinciki ya Kamasu Lokaci Daya,Imran ne kadai ke Tsaye idanuwansa ba alamun Fitar kwallah sai dai yadda abubuwan suka Juye ne suka sakashi Tsintar kansa a wani Hali Tabbas Jini yafi Ruwa kauri,ko shi yasa Yafi damu da Inteesar fiye da kowa..? Ashe ita din jininsa ce..!
Anty Safiya Dake gefe tana sharan kwallah Tun dazu ta fito ba wanda ya Lura da ita Hayaniya taji ta Fito tana Kwance afalo acikin Shashenta sai ta iske Abun Farincikin daya samu wannan Gidan ayau na cikon Abu Dayan da ya Rage gidan ya cika ya zama Gida irin kowani gida.
Yusuf ne ya hangota da sauri ya isa gareta ya Rumgomta yana fadin"Noor Boye boye ya kare..Danginmu sun same mu..!.
Tana rike dashi Tana Fadin"Alhamdulillah..Duka Burikana sun cika my dear..!.
Take fada cikin Farinciki.
Inteesar na kuka ta dago kanta tana Kallon Munari cikin kuka tace"Dilla ke baki zo muyi kukan tare ba. ?
Tafada Lokaci Daya Hawaye da Dariya da sauri Munari ta wani taho da Sauri ta Fada Jikin Abba dukkansu ya Hada ya Rumgume sai ga Hawayen Farinciki sharr.
Sadam Wayarsa ya zaro Tun dazu Sa"id ke kiransa bai dauka ba cikin Farinciki ya kirasa yana kiransa Ringing daya ya daga da Sauri yana Fadin"Sadam ya ake ciki..? An dace kuwa. !?
Sadam na kallon Abba yana fadin"Sa"id an dace gani ga Kawu Malami..Alhamdulillah gani cikin gidansu Zagaye da iyalansa..!
Sa"id ya mike da Sauri yana Fadin"Finally Alhamdulillah..!
Bai ma jira cewar Sadam ba ya Katse kiran Murta ta sa ya rasa nayi,Komawa yayi ya zauna yana Hamdala afili kafin kuma ya Fara Tattara kayansa yau komai Dare sai ya Shiga kano Sadam ya kara Kira yana Dauka yacemai kada ya bar gidan nan yanzu zai tashi daga Office yana zuwa Gida zai taho kano ayau din nan bai iya cemai kada ya Taho ba domin ya kamata yazo din.
Abba kuma yana Rike dasu Inteesar Hawayensa yaki tsayawa yana Kaicon wannan Zumuncin na wannan Zamanin da har yakai mu ga Lalacewar da jininka na tare dakai ammh baka sani ba.
Waje aka samu aka zazzauna Saman kujerun falon Abba ya fara Tambayan Sadam sauran yan"uwa yana Fadamai kowa Lafiya Imran na gefe bai Zauna ba ya Harde Hannayensa saman Kirjinsa yana jin duk abunda ake fada sai dai kalma Daya Tun bayan na Dazu bai kara Furtawa ba bama wanda ya Damu dashi sanin Hali Sadam ne ke yawan kallonsa Lokaci bayan Lokaci yana mamakin shi wannan Haka yake.?
Abba ne ya kalli Aneesa yana Fadin"Wannan mai Dakin ka ce..?
Sadam yace"Eh Abba..ga yara na nan Waleed da waleeda. !
Abba ya mikama su hannu yana Fadin"Ku taho nan wajen kakan ku da baku sansh ba..!
Basu da bakunta suka karisa Wajensa ya Daukesu asaman jikinsa.
Munari da Inteesar na gefe sun rike hannun juna baki yaki Rufuwa Safiya na Cikin su da Yusuf cikin Farincikin da bazasu misalta ba,Shiyasa tunda ya Fara ganin Inteesar wlh jininsa ya bashi Intadin kamar jininsu ce,bai taba mata Wani kallo ba ashe jini jini ba na waaasa ba.
Abba na kallon Waleed yace"Nasan sanda aka Haifi babban..Lokacin Maimunatu ta Kirani take fadamin Matarka ta Haihu wacce muka je cikin garin Azare muka karbo Auranta..!
Sadam na dariyan Farinciki yace"Anyi haka kawu tabbas baka manta ba..!
Abba na Mirmishi jin dadi yace"Ina Yayanka Sa"id da sauran kannen ku mata..? Kayya zumunci sai a hankali duk ban sansu ba..!
Sadam yace"Sa"id na Garin Dutse Abba chan yake aiki yana zaune da matarsa da ya"yansu uku..Karamar kanwarmu Hafsah tana Wajensa saboda Tana karatu nan Federal Univestiy dutse. !
Abba ya jinjina kai yana Fadin"Ku kiramin yan"uwana inaso na Hada dasu yau..Gobe ina so naje ni da duka Iyalaina naga Daada na Roketa gafara..!.
Imran na gefe ya kalli Abba irin Kallon nan nasan za"azo wajen bai dai ce komai ba Sadam ne yace"Kawu saboda Murna ban ma kira kowa ba Sa"id ne kadai shima yace yana Tafe yau din nan bari na fara Kiran Mommy na Fadamata..!
Inteesar dake gefe tace""Ni kuma bari na Kira Daddy na fadamai..!.
Dukkansu atare suka Kira wayar Sadam na Kira Mommy ta Daga Cikin Murna tana Fadin"Sadam yanzu nake shirin kiranka gama wayata kenan da Dan"uwanka yana gayamin wani Labari mai dadi kaga Yaya Malami da iyalansa..?
Tafada cikin wani Shauki Saukewa wayar yayi daga kunnensa ya saka Speaker yana Fadin"Wlh Mommy gani ga kawu ga yusuf ga Imran ga Inteesar Mommy ga Matar yusuf din dan wajen kawu malamin har yayi Aure .!
Inna maimunatu tana kwallah tace"Hadani da dan"uwana naji muryansa..!Sadam bai yi gaddama ba ya mikama Abba wayar ya Karba yana Fadin"Maimunatu Autan Daada..!
Tana jin muryansa sai kuka tana Fadin"Ya ya Malami ashe kana da Ranka..? Ka samu lafiya Allah abun godiya..!
Cikin wani yanayi yace mata"Na warke Maimunatu..Na samu Lafiya da ikon Allah..!.
Inna maimunatu tace"Allah mun gode maka da kakaddara Haduwa Tsakanin daada da Ya malami..Nima bazan iya zama ba bari Alhaji ya shigo na gayamai yau din zan taho kano..!
Da sauri Abba yace"A"a Maimunatu kada ma ki fara Dare yayi..Ki bari insha Allahu gobe bazan kara kwana agarin nan ba sai a dukku gaban Daadarmu sai mu hadu achan.!
Inna Maimunatu na sharan kwallah Tace"Shikenan Ya malami daman Sa"id yace min ya kira Kawunshi kabiru na Abuja yafadamai shima yace zai kamo Hanya in ya Samu jirgi shikenan in kuma bai samu ba zai yi Tafiyar Mota..!
Abba na Dauke Hawayensa bai so su kara zuba yace"Barrister..Yaya kabiru ashe baya Fushi dani..! Da Abba ya Fadi haka kamar Imran ya Mutu haka yake ji,baima san sadda Abba ya gama Wayar ba sai da ya tsinci Muryan Inteesar tana mgana da Daddynta.
Alhaji Mustpha shigowarsa Gida kenan Shida Basheer Inteesar ta Kirashi Kokari ma yake ya shiga gida yayi alwala ya samu Sallar mangariba Domin yaji ana ta Kira Basheer kuma ya Biyosa gida ne saboda akwai Lissafin da zasu yi yaji kiran Inteesar.
Suma shiga Falon ya Daga Kiran irin yadda yaji yanayinta cikin Murna yasa yace"Inteen Daddynta me ya Faru ne najiki cikin Annshuwa..?
Inteesar na kallon Abba tace"Daddy Albishirinka..!
Yana zama kan Daya daga cikin kujerun falon yana Fadin"komai Intee na take so shine goron albishir dinta..!
Yafada Daidai Lokacin da Umma ta iso Falon dauke da Ruwa da Kofuna Basheer na gefe  zaune yana Latsa waya a Hannunsa..
Inteesar tace"Daddy gani ga..Baffa Malami gani kusa dashi..!
Daddy yaji mganar asama adaidai Lokacin kuma Ana ta Kiransa a waya Call Waiting,.
Cikin Dan daburcewa yace"Wane kikace Intee Daddy..!?
Da sauri ta kara Fadin"Baffa malami Daddy gashi ma kuyi mgana..!
Tafada tana mikama Abba wanda ya karbi Wayar yasa a kunni lokaci Daya yana Fadin"Mustapha Baban Basheer Mijin Salaha..!
Kamar a mafarki haka yaji muryansa da Sauri ya mike jikinsa ba inda baya rawa,har yana Ture Umma Dake duke gabansa Tana Tsiyayamai ruwa.
Suka Mike atare suna binsa da kallon mamaki.
Cikin In ina yace"Yaya Abbakar..? Kai ne da gaske..!
Abba na Mirmishin jin dadi yace"Nine Mustapha..Abun

Please Login or Register in order to submit comment