Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kunya Inteesar na tare damu na tsawon Lokaci ban gane yata bace..! ?
Yafada abun na karamai ciwo Daddy daya yi mutuwar Tsaye yace cikin son Tabbatarwa
"kai..kai ne Baban Munari kawarta..!?
Abba yace"Ni baban Mai sunan Daada ne..sai dai in kaine Baban Mai sunan Autan Daada..!
Sai ga Daddy na Hawayen Farinciki cikin murna yake kallonsu Umma yana Fadin"Wlh shine Salaha Basheer..Babanka ne ya Malami ne fa muke mgana dashi..Ya malami fa Alhamdulillah Alhamdullilah..!
Su Abba suna ji daga alamu ma ya manta yana waya ne ya Gama Rudewa Inteesar ta karbi wayarta ta kashe nan take ta Kira Mama tace ita da Sagir suzo gidansu Munari hankalin Mama ya tashi ta Zata wani abu ya samu Abba Sagir na Kofar gida Yana kokarin Daura alwala ya shiga Sallah Tunda an kira Mama ta Fito da Hijabi a Rude tana Fadamai Halin da ake ciki Sallar da bai shiga ba kenan ya Rufa mata baya zuwa gidansu Imran.
Su Umma mamaki ya cikasu da Daddy ke maida Zencen ya kasa Zama Umma tana ta maimaita Allah gagara Misali Daman Munari yar"uwan Inteesar ce..? Koda tace ramar data fara ganin Hotonsu tare sai da taga kamarsu Data fada kuma ba wanda yabi ta kanta.
Suna cikin haka Baffa Kabiru ya kira Daddy ashe shi yake ta Kiransa yana waya da Inteesar yana Dagawa Cikin Farinciki ya gayamai labari mai Dadi sai yaji yana Fadamai Cikin Farinciki Daddy yace"Wlh nima har mgana ma munyi da ya malami Barrister...Inteesar ta Hadani dashi Allah sarki Rayuwa..!
Baffa Kabiru Daga chan bangaran yace"Yanzu haka ina hanyane ban sanu jirgi ba Tafiyar mota ce ni da Ma"u ce,kaima kayi kokari ka Tashi yau din bana so mu kuskure ya sake bace mana kuma ka da ka kira Daada so nake mu bata mamaki har Bintalo na gayamawa yanzu muka gama mgana da ita..chan zamu kwana Gobe in Allah ya kaimu sai mu hadu da kowa da kowa a Dukku..!
Daddy yace"Yanzu kuwa zamu kamo Hanya..!
Daga haka suka yanke kiran Daddy na Kallon Umma yana Fadin"Salaha Shirya..Ko kuma ke Salaha ki bari gobe Direba ya taho daku keda Hauwa da yara mu a hadu a dukku..Kai Bashir kira matarka ka Fadamata bari na shiga ciki na fito yanzu zamu dauki Hanyat kano ba sai gobe ba..!
Baima Tsaya Sauraransu ba ya Shige ciki kamar zai kifa saboda Sauri.
Umma ta Kalli Basheer tana Fadin"Kai duk tare zamu tafi..Nima bazan iya Zama sai gobe ba kira matarka mu biya mu daukesu ayi tafiyar gabadaya..!
Basheer yace"Umma anya Zata iya..? Kunsan yanayinta ko zamu Kyaleta kawai mu muje..!
Umma ta kada kai tana Fadin"Kuma fa hakame..Shikenan kirata ka Fadamata sai muje din..!
Daga haka ta bi bayan Daddy shi kuma ya Dauko wayarsa Domin ya Kira Hauwa ya fadamata Halin da ake ciki.
Mami Asma"u ta kalli Baffa Kabiru bayan ya gama mgana da Daddy Tana Fadin"Yanzu daman duk wannan uban Wahalan neman da kuke ma wannan bawan Allah yana kano zaune abunshi bbu abunda ya Dameshi..!.
Take fada Lokaci Daya tana kara gyara zaman gilashin dake idonta suna Kishingide a bayan Motarsu Kirar prado Direba na gaba yana jansu.
Cikin wani yanayi ya kalleta yana Fadin"Bari kawai. Ni kaina naji abun haka..Ace yana nan kusa ammh ya kasa neman kowa..?
Kuma daga alamu he is Fine now..!
Mami Asma"u ta tabe baki Tana Fadin"This is Selfish yana chan yana Jin dadinsa ya manta da ku..Alhalin kuna nan baku huta ba wajen nemansa..!
Baffa Kabiru yace"Saboda Daada nake komai kuma kinga all the blemming akaina Daada ta maidashi so yanzu zan yi amfani da wannan damar na Daukesa na maida mata..!
Da sauri tace"Shikenan kuwa..Ammh sam bai kyauta muku ba..!
Shidai bai kara ce mata ba sai Dannan Wayarsa yake yi Khamis ya Tura ma Sako ya kira Wayarsa bai Dauka ba..
Umaima da Sajida suna gida suka barsu Umaima ce ma taso zuwa Uwar ta Hana Sajida kuma bata manuna Concern dinta ba she is telling cewa Test zasu fara karatu take bata da Lokaci.
Mami Asma"u ita da kanta tayi Ra"ayin zuwa saboda tana so taje taga komai kuma Komai za"ayi so take ayi shi agabanta bayan ikonta da izzanta na akwaita da son gulma da kure Mutane.

*****
Gidan Abba cike da Mutane sai godiyar Allah haka Mama da Sagir suka zo sukaji Abun al"ajabi Sagir yace Wlh ranar daya fara ganin Daddyn Intee sai da ya ga yamai kama da wani sai dai ya rasa ta ina zai kama kamannin,Ashe ashe suna kusa da Danginsu basu sani ba Mama sai mamaki take ashe Abba yaya yake wajen Mijin kanwarta Salaha Allah ne abun godiya,duk da Sun shiga rudanin Dalilin wannan lamarin sai dai basu ce komai ba suna da Tabbacin yadda wannan ya fallasa to sauran Dalilan ma Zasu jisu in Lokaci yayi.
Sai murna ake da Farinciki ana maida Zence,Sadam kuma Tuni ya Hau WhatApps ya shiga Group din Marigayi Alkali Dukku ya bada Sanarwa da gargadin kada wanda ya Kira Daada ya fadamata sai Gobe kowa da kowa za"a hadu a Dukku.
Basu an kara ba sai dai sukaji kiran Sallar Isha"i kana zaman ya tashi Matan suka Shiga ciki domin gabatar da Sallolin da suka Subuce musu mazan kuma suka Dauro alwala suka Ja Sahu anan Falon Yusuf yayi musu limanci Abba da Sadam da Sagir da Imu suna Binsa abaya wanda Har zuwa wanna lokacin bai ce komai ba yana so ne sai an zo gabar da zai tanka yanzu ba Lokacin mgana bane.
Bayan sun idar ne aka sake Fitowa aka Hadu afalo ana jiran sauran Baki,saboda Murna ba wanda ya Nemi abinci sai Imu daya Shige daki ya Busa abarsa,abu daya ke sashi Farinciki zuwa Biyu ayau dinan Shine na Farko yaga Inteesar Cikin Farincikin da bai Taba gani ba na Biyu yau din Ranace da zai Rama wasu abubuwa da suka Shude shekarun baya yana Fitar da Hayakin Taba yana Mirmishinsa na saman Lebe Lalle ya yi Shuru shekaru uku da suka gabata ammh awannan gabar ba wanda ya isa ya hanashi mgana koda Abba ne da kansa.
Safiya ta Kira Mommynta tana Fadamata abunda ke faruwa jin haka yasa Hajiya Mero murna tana farinciki ko banza Alhaji Alhassan zai ji kunya Daga yadda Safiya ta bata Labari Dangin yusuf din ba mutaenan banza bane suma wasu ne Ita ta roki Hajiya Mero da ta saka yan aiki suyi musu abinci mai yawa saboda baki abama Direba ya kawo da Sauri Hajiya Mero ta amsa mata suna Sallama ta Fita zuwa Kitchen tana bama masu aiki Umarni kafin ta afito Ta Nufi Dakin Tasleem ta Fadamata wannan abun Farincikin.
Sa"id shi ya fara iso Tunda shi yafi kusa,yana Shigowa ya Kira Sadam shi yamai kwantace cikin Lokaci sai gashi ya ya iso shi da Yusuf suka Fita Tarbansu.
Sa"id ya Rumgume Yusuf suna Murnan ganin juna,da iyalansa yake tafe Harda Hafsah dataji Labari tace sai tazo itama.
Dukkansu suka Dumguma zuwa Cikin gidan sai ga Sa"id sun Rumgume da Abba suna murnan ganin juna Fareesaatu ma ta gaisheshi ya amsa yana Daukan ya'yansu na Karshe ne Abubukar takwaranshi kafin ita faresan ta Karisa Wajen matan ana ta gaisawa Hafsat suka Rumgume juna da Inteesar,bayan ta gabatar da junansu da Munari suka Rumgume suna Murnan Haduwa da juna Anty Safiya Tana ta ina ta sakasa dasu,mama da Sagir suna nan zaune suna ganin ikon Allah..
Sa"id kam shi sai da ya Rumgume Imran ammh yaki tabasa shi baima Tsaya Wani lura da lamarinsa ba.
Akwai salloli agabansu yasa Safiya taja Fareesan zuwa Shashenta Sa"id kuma Da Sadaam Yusuf ya sauke su Tsohon Bedroom dinsa
Ba Dadewa sai ga Direban gidansu Safiya da kololin Abinci manya manya Daman Tun tasowarsa Mommy ta Kira ta fadamata to da iro ya shigo yana Fadin an kawo sako tasan kwanan zencen iro kuwa sai Raba ido yake tun sanda Bakin Motoci da Mutane keta shigowa gidan nan Abunda bai taba gani ba so yake yaji ina ba"asin Lamarin..!
Anty Safiya dasu Inteesar suka Taimaka mata suka Shishigo da kololin Abinci zuwa Kitchen da suka ce a zo aci abinci ba wanda yabi takai ana Jiran isowar su Daddy.
Karfe tara da rabi na Dare goma Saura su Daddy suka shigo Anguwan gadon kaya,Dayake susan gidan Zuwan bai musu Wahala ba.
Abba najin Dan"uwansa ya iso baima Tsaya ba ya fice zuwa Haraban gidan Tunda ya fito Daddy dake gaban Mota ya kyalla ido ya gansa ya balle Murfin Mota ya futo suka Nufi juna suka Rumgume sai kuka,Sauran duk suka Biyosa abaya banda Imran daya na chan Dagachan gefe...
Yusuf da Basheer suka Rumgume juna suna Murna Inteesar ta Rumgume Umma cikin Murna kafin suka Rankaya zuwa cikin gida..
Abba da Daddy suna Rike da Hannun juna ganin kamar mafarki ne nan aka Shiga gaisawa da juna Umma ta Rike Mama suna kara mamakin wannan al"amarin ta Rumgume Munari tana jinta kamar Inteesar,suka gaggaisa da Su Sadam da matansu da Ya yusuf da Anty Safiya Imu na gefe chan Saman Dining ya Harde Hannayensa saman Kirjinsa yana kallon kowa Daya bayan Daya ba ma wanda ya Damu dashi.
Sai da Daddy ya tambayesa ne kana aka fara Waigen waigen nemansa chan aka gansa Zaune Daddy bai jirasa ba ya Mike ya isa garesa yana Fadin"Asshe ashe..Imran din da Inteesar ke bamu labari ashe jininta ne yayanta ne Salaha..!
Gabadays kowa sai mamaki daman Inteesar na basu Labarin Imran ne Ita kuma sai kunya ya kamata ta Noke bayan Umma Tana Leken Imran da Daddy ya Rumgume abun mamaki yadan Saki Ransa kadan sai dai suna Hada ido da Inteesar ya Hade rai bayan ya Harareta aranshi yana ayyana Rainin da yarinyar nan tamai.
Daddy ko awa daya basu yi da isowa ba Baffa Kabiru suka iso  suma da kwantancen suka iso Gidan Abba.
Tundaga Haraban gidan Mami Asma"u ke karema komai na Gidan kallo acikin ranta Tana fadin ashe yama samu wani jin dadin Rayuwar duk da yabar komai nashi abaya.
Shima Abba da Daddy da sauran Mazan suka Fito Tarbansu Baffa Kabiru yayi mamakin ganin Abba Shar dashi Cikin Koshin Lafiya ya Zata zai gansa duk ya lalace ne saboda Halin Rayuwa hakama Mami Asma"u take kallonsa kamar bashi ba ya kara Kiba ya samu jin dadi ya bar Mijinta na Wahalan nemansa.
Duka suka Dunguma zuwa cikin Falon a karo na ba adadi.
Baffa Kabiru yayi mamakin ganin Yusuf da Munari da Imran dey look so nice daga gani basu da Wahala ko daga Gidan da suke ciki Dukkansu sun gaisheshi banda Imu dayayi kamar ma bai ganesa ba Yana daga chan inda yake Zaune Hannayensa a Harde yana Kallon kowa sama da kasa.
Mami Asma"u sai bin kowa take da kallo Mamaki bai kasheta ba sai taga Matar Yusuf Safiya abun ya kara bata Haushi Bata Damu da yaran dake Wajen ba ta Bude tace"Ba shakka..Abban Sajida kuke chan kuna Wahalan nemansa bakwa barcin kirki Daada kuma na chan Hawan jini ya kamata tana kwana kuka Saboda Tunanin dan"uwanka Shi kuma yana nan ya samu Sabuwar Rayuwa da Sabon gida.ba shakka..!

Take fada kanta Tsaye tana gyara Zaman gilashin idanuwanta Kowa sai da ya Kalleta Abba ya Murmusa yana kallonta yace"Barrister Asma"u Tafida kina nan da Halin nan naki kenan..!
Kallonsa Tayi cikin ido kafin tace"Dr.Abubakar Hamisu Malami ashe baka manceni ba..!
Tafada Lokaci Daya tana dan Sakin Dariya ganincyadda aka Sako mata Ido Mirmishi ya saki Cikin natsuwarsa yana Fadin"Ban manta dake ba..!
Yafada Lokaci Daya Daddy da Baffa Kabiru suka Bisa da kallo komai nashi bai sauya ba Hatta mganar Abba da Tafiyarsa kana gani zaka san baida Hayaniya Ballatana Fada.
Imu na gefe yana jin Abunda Mami Asma"u tace aransa yace anzo wajen ya ganeta Sarai duk cikin matan Baffaninsa yafi saninta da kowa saboda Lokacin da Su Anni suka Rasu suna Dukku duk zuwa da ita ake zuwa ta kuma Taya Mijinta aibata Abba agabansu abaya in sunyi sunci riba wannan karon sai ya Tabbatar musu da ba wanda zai kai Labari..
Kafin suci abinci sai da su mami Asma"u suka gabatar da Salollin dake kansu aka baje afalo aka ci Abincin da Hajiya Mero ta aiko dashi Abinci kala kala sai wanda ka Zaba.
Bayan sun gama ne yara yaran suka Kwashe komai zuwa Kitchen aka kara zaman Hira Abunda yabama Mami Asma"u mamaki Imu ne ganin kowa yaci abinci bandashi da Daddy yayi mgana sai Abba yace haka yake bayason cin Abinci Tana gani daya tashi Zai shiga Dakinsa kamar Hararanta ma yayi kafin ya shige.
Tasan yaron abaya da Tsaurin ido bata Taba Zaton Abunsa yakai haka ba.
Isu isu ne zaune afalon Mama da Sagir tun zuwansu Daddy ba Dadewa sukayi musu sallama zuwa gida mama tace sai da safe.
Ana ta Hiran yaushe gamo Inna Bintalo ta kira har sunyi mgana da Abba ita da megidanta suka Rabu kan sai gobe in sun hadu a Dukku.
Baffa Kabiru ya gyara Zama yana Fadin"Malami ka samu Lafiya sosai..?
Abba na Mirmishi yace"Alhamdulillah..!
Baffa Kabiru ya jinjina kai yana Fadin"Alhamdulillah duk da akwai mganganu da yawa a bakina ba Lokacin Fadansu bane yanzu sai In allah ya kaimu gobe mun isa gaban Daada..!
Abba ya gyada kai baice komai ba Baffa Kabiru ya cigaba da Fadin"Gobe sai ka shirya kaida iyalanka..Damu gabadayanmu zamu isa Dukku da yardan Allah..!
Kamar daga sama sukaji Muryansa cikin Amo da Cikar Kaushin kamar yadda ya saba.
"Ba inda Abba zai je..Kuma muma bazamu mu biku ko"ina ba..!
Gabadaya falon aka juyo ana Kallon Barayin Inda mganar ta Fito.
Imran ne tsaye a kofar dakinsa ya Sanya Hannunsa guda daya cikin Aljihun bakin wando dake jikinsa Hannu Daya kuma Tana kan bakinsa yana Rike da Karan Sigarinsa.
Bai damu da yadda ido ya dawo kansa ba ya lumshe manyan idanuwansa kafin ya Bude su tas kan Baffa Kabiru Lokaci daya Hayakin daya zuga ya Fesar dashi ta Hanci ta baki zuwa Saitin Fuskar Baffa Kabiru.
Gabadaya Falon jikin kowa yayi sanyi,ido kowa ya Fiddo waje cikin mamakinsa da ganinsa acikin wannan Halin Banda Abba da ya yusuf da suka Dafe kai cikin Tsantsan Takaichi da bacin rai.




*Alhamdulillah Godiya ta Tabbata ga Allah Subuhanu Wata"ala daya bani ikon Fara wannan labarin kashi na Farko gashi yau yazo karshe Ina godiya ga duka Masoyana da suka Taru suka nunamin Soyayyarsu kan wannan Labarin nawa Nagode kwarai Allah ya bar zumunci ina godiya ga Tarin Zaurinka da suke jimarin Bin wannan Labarin da kayattacen Sharhin su nagode kwarai Allah ya Biyaku da aljannah Firdausi Ameen*


_Nayi muku labarin Gidanmu Kashi na Farko kyauta sai dai kashi na Biyu na kudi ne kuyi hakuri kila hakan bazai yi ma wasu daga cikin ku Dadi ba sai dai daman chan bai kamata Labarin Imu yazo duka a kyauta ba,Acikin wannan Labarin ko Rabinsa ma bamu yi ba,kuma bama muce komai ba akwai Sauran Rina akaba Kina Bukatar son ganin wani al"amari ne zai Faru a Falon gidan su Yusuf..?Imu zai yarda su bi su Daddy zuwa Dukku..?in sun isa mezai Faru..?Mami Asma"u tana gefe ga Sajidan wacce ta kyasa Imu batare datasan ba wanda ya Tsana sama da iyayenta ba,Kun Hango Badakala da Chakwakiya a falon Daada..?yaya mtsayin makauniyar soyayyar Intee da Imu..?Imu zai gane yana sonta..? Zai sauya saboda ita..?Na Tabbata Imu kuka sani ayanzu baku san shi a anihin BANKER IMRAN ABUBAKAR MALAMI ba,na Tabbata zaku so ganin Imu ya Juya Harshensa Cikin Tsaddacen Turancinsa kuna kuma son gani yadda Soyayya zata kai su shida Intee in sunyi aure ya zasu yi
Zaman auransu..?kada ku manta akwai Khamis fa agefe Daya gashi Daada Tayi alkawarin Daidaita kan Zuru"arta kafin ta bar Duniya kada na Cika ku da Surutu Akwai abubuwa Dadama da Zasu Faru mai bukatar cigaban wannan Tafiyar Saboda Ku masoyana da kuma yanayin Rayuwar da muke ciki zaku biya Kudin karatu akan #300 Kachal zaku turo kudin karatu ta wannan asusun bankin 0552179550 JAMILA UMAR GTB,,Sai aturo shedar biya ta wannan Lambar 09069067488,masu katin waya kuma zaku iya Turo hoton katin ku ta wannan Lambar 090690674488,Zan Fara posting din Book2 da Zarar Mutane 100 sun yi payment Insha Allahu ina godiya Masoyana kuma ina Maraba da ko akoda yaushe._








*Tanque*
*08/03/2022*
*Janafty*
*Intelligent writer"s asso*
3/22/22, 23:13 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�1*

*Ki biya ki karanta cikin Salama da Aminci,Ki sani ki kara sani Mace mai aji mallakan komai nata take yi bata jiran abun sata wannan Littafin na kudi ne kan Naira 300 kachal ki biya ta wannan asusun bankin 0552179550 gtb ko kuma a Tuntubi wannan Lambar kai Tsaye 09069067488*


Bai damu da yanayin kallon da ilahirin falon suke binsa dashi na mamaki ba banda Yusuf da Abba da su munari wadanda suka sansa suka san zai iya aikata abunda yafi haka.
Mami Asma"u cikin mamaki da al"ajabi ta juya tana kallon Baffa Kabiru bata samu bakin mgana ba,Imran ya kara gyara tsayuwa Hannunsa guda daya na cikin aljihun bakin wandon dake jikinsa dayan hannunsa kuma yana rike da karan sigari kansa Tsaye idanuwansa basu Rusuna ba yake bin Fuskar kowa da kallo kai Tsaye Fuskarsa bata bayyana Fara"a ko sakewa ba,ya hade ran ya dakuna Fuska kamar an aikomai mala'ikun mutuwa.
Daddy ya kalli Baffa Kabiru cikin mamaki shima ya kallesa,Kafin su maida kallonsu kan Abba wanda ya Dafe kai cikin Takaichi.
Imran ya kara Kausasa Muryansa yana Fadin"Eh da gaske nake yi..ba inda Zamu je bama bukatar zuwa ko"ina wannan shine gidanmu..!
Yafada yana Kai sigarin bakinsa ya zuka ya sake Fesar da Hayakinta Cikin kwarewa.
Yusuf ne ya mike da Hanzari ya isa garesa Lokaci daya yana Fadin"Imu..Imu saurareni..!
Kallonsa yayi ido cikin ido ganin haka ya sa Yusuf yace"Ka koma Dakin ka wannan ba mganarka bace..Mganar Abba ne da yan"uwansa bakai bama ko mu da muke gaba dakai bai dace mu ce wani abu ba..So ka koma cikin dakinka don Allah..!
Yana mganar ne Imran namai kallon Tara saura kwata gira daya ya Dagamai cikin Salon rainin wayau kafin yace"Oh Really..Sai yanzu ne su sakansa shi dan"uwansu ne..? Meyasa lokacin dayake bukatar Taimakonsu suka Juyamai baya..?meyasa alokacin basu nuna ma Duniya su din Ahalinsa bane suka yasar dashi,suka Kyalesa suka Rika aibatasa da kaddaran da bashi ya Dora ma kansa ba wani kokari ko Himma sukayi wajen Sauya wannan al"amarin nace ka Fadamin wani kokari sukayi..?
Yafada cikin Tsawa Ransa ya fara baci Idanuwansa sun sauya Launi Tuni jijiyoyin kansa suka Mike Radau suna Harbawa.
Gabadaya kowa shi ya zuba ido yama kallonsa yana Sauraransa,Daddy ya sunkuyar da kansa aransa yana Fadin anzo wajen dayake ta gudu Tuntuni Baffa Kabiru kuwa mamakin Rashin kunya irinta Imran kadai yake,Matan kuwa kowa sai mamaki Mami Asma"u kuwa bawai ta kasa mgane bane mamakin al"amarin ne ya isheta Abba Take kallo Tana ayyana Abuubuwa da dama ganin yadda ya zauna yayi Shuru Yaronsa na Diban albarka ya kasa mgana.
Yusuf dayasan Imran in ransa ya baci zai iya Fadar komai yasa ya Rikesa Gam yana Fadin"Is ok muje ciki don Allah Imran..!
Kwace jikinsa Imran yayi yana Fadin"Wlh ba inda zan je..ai da Farko bam ce komai ba saboda ba"a kawo gabar da zan yi mgana ba yanzu ne Lokacin da zan ce wani abu..Daman Tuni ina jiran wannan Ranar da wani Daga cikinsu zai zo yace Mu koma Gida to bazamu koma ba..Naji dadin da kuka zo kuka ga Abba ya warke yasamu Lafiya yanzu kun Tabbatar da Ko da ku ko bako zamu iya Rayuwa..?kun tabbatar da Abbanmu ba Mahaukaci bane kaddarace ta Fadaamai kuma cin jarabawa da Daukan kaddara duk na Allah ne wanene acikin ku zai iya jure daukan Girman Raunin da muka Dauka?
Abba ya rasa Anni mata take garesa Uwar ya"yansa ta rasu ko gawanta bai gani ba Ya rasa ya"yansa uku aLokaci daya acikin ku waye zai iya daukan girman wannan Raunin..?waye zai iya Tsayuwa da kafafunsa in wannan Jarabawan ta Fadamai ehe?Masu cewa Abba yaki yarda da kaddara su in haka ta faru dasu zasu iya daukan..? Masu cewa Abba ya zama Mahaukaci su in haka ya faru dasu waya sani ko zasu kashe kansu ne..? Masu ce mana muma bamu da amfani muna kara Raunana Abba su din sun manta Muma Uwa muka rasa da Ginshikin Ahali har uku..?sun manta muma muna sonsu ko sun manta muma muna da Zuciya da kwanjin in muka rasa namu mu nuna?ko shikenan mu ba Mutane bane Dabobbine da zamu yi wannan Babban Rashi kuma mu dawo muna Dariya Lokaci daya..?meyasa baku jamu ajiki kun Lallashemu ba..? meyasa baku nuna mana gata da soyayyah ba..?
Meyasa baku rika nuna maana amfani Hakuri ta Lallashi da nasiha da ban baki ba..? Wlh har yau har gobe ina jin kunar kalmar Mahaukaci da wannan Mutumin ya Kira Abba dashi ina jin zafin hakan zafin daya kan kusa kona Kirjina in na Tuna Nayi ma Daada Uzuri yafi sau saba"in saboda Raunin Tsufanta ya bayyana kuma kamar yadda muke da Rauni haka take dashi itama Tana neman Mai Tallafamata ne in nayi ma Baffa Mustapha uzuri bai wuce Uzurin ya kasance mai Sanyi Hali kamar Abba kuma bai taba aibatamu saboda Kaddaran data Fadamana sai dai ina ganin Laifinsa na Hana Baffa Kabiru Aibata kaddaranmu na Hana sa Zagin Abbanmu da kiransa Mahaukaci Laifinsa na kin gayamsa gaskiyan kan Abunda yake Aikatawa abunda baitaba Tunanin yaya mu ya"yansa zamu ji acikin kirjinmu ba Ko ka manta Cewa Yadda ya"yanka suke awajenka Haka na kowa suke..?ka taba Tunanin ya ya Nauyin mganarka zata Kuntatamana..? Ka taba Tunanin yaya ya'yan Dan"uwanka zasu iya juran wannan Tozarcin naka..?baka taba Tunani ba Shiyasa kake komai naka kanka Tsaye shine yau zaka zo kace Abba ya bika ka kaima Daada shi Saboda tace ka dawo mata shi..? To ba inda Abba zai je Gari na wayewa kowa ya watse ya kama gabansa nan ne Gidanmu yanzu duk wanda ke son ganinmu sai dai ya tako yazo kamar yadda kuma kuka zo..!
Ya karishe Fada yana Sauke Numfarfashi Cikin zuciya Idanuwansa sun kara sauya kala har sun cika da kwallah Saboda Tuna Abunda ya faru Baya,Gabadaya Falon kowa jikinsa yayi sanyi masu Saurin kuka Irin su Munari har ta Fara Inteesar na Lallashinta itama kwallar take ganin yadda Duk kafiyar zuciya iri nta Ya Imu yau Rauninsa ya bayyana Su kansu su Sadam jikinsu yayi sanyi basu da sani kan Abunda ya Faru Lokacin ammh indai Hakane Tabbas ba"a kyauta musu ba kuma suna da Ikon suce wani abu a wannan gabar.
Baffa Kabiru ransa ya baci saboda kara kara Imran ya ambaci sunansa ya Nuna dashi yake cikin bacin rai ya mike yana kallon Abba Lokaci Daya yana fadin"Malami a gaban idonka kama ji kana gani D"an daka Haifa yana neman cin Zarafina ka kasa ceewa komai..?
Yafada cikin mamaki yana kallon Abba Kafin Abba yayi mgana Daddy ya Rigasa cikin Kwantar dakai Yace"Barrister mganar gaskiya Imran gaskiya ya fada..Daman Ranar da nake ta Tsoron zuwanta kenan Ranar da wani Daga cikin ya"yan Yaya Malami zasu Tuhume mu da Laifi da kuskuran Gudumuwarmu wajen Nesanta kansa da yayi damu ina ta jin Tsoron wannan Ranar..Kada ka manta ko Zuwan mu dukku na Karshe kiran Daada kenan kuma ta fada ta kara Laifinmu ne laifin mu ne Ya Kabiru kaima ka sani..!
Yafada cikin wani yanayi Umma ta Jinjina kai Batayi mgana ba,Sanin duk abubuwan da suka Faru,Baffa Kabiru yana da kaso mai tsoka kan Faruwar komai bai daukan abu da Muhimmanci indai bai Shafi matarsa da ya"yansa ba bazatace dai komi baa Saboda ba Huruminta bane bata taba mgana Kan Lamarinsu Daddy indai bashi ya tace wani abu ba.
Mami Asma"u da mamakin kalaman Imran suka Daskaran da ita ta kasa wani Motsi tafa san gaskiyane saboda ai Da ita ake komai da gudummuwarta a Lokacin tana gayamai bai kamata ya zauna yayi ta Wahala da Abban ba ai ba yaro bane kuma baida ilimin sanin Mutuwa ce da zai zauna yana wani abu kamar mara Hankali Tana nunai ai da gangane saboda su ya rika Hanasu Harkokin gabansu da irem iren wasu maganganu alokacin koma meya faru da saka Hannunta ammh Dayake ita Macece mai son kanta bata iya ganin hakan ba sai take ganin kawai ana neman cin Zarafinsu ne.
Mikewa tayi Tana Tafa hannu Cikin mamaki kafin tace"Au har dakai Baban Basheer..?Yau da bakin ka kake Bude baki kana Fadin Abban Sajid bai kyauta ba shi keda laifi kai ka cire kanka..? To Tunda shi keda alhakin komai meyasa alokacin daka Fahimci haka kai bakayi kokarin gyara komai ba tunda kai ka Fahimci shi ya bata komai..?
Tafada tana kallonsa bai yi kaurin baki ba

Please Login or Register in order to submit comment