Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nasa ba Fuskarta yake gani,Mikewa Zaune yayi Cikin Duhun Dakin Sai dan Hasken Dake shigowa ta Labulan Dakin Dayake Dagawa ta Window.
Kansa ya Dafe yana Fadin"meke Shirin Faruwa dani ne..?taya ya ko ina nake ganin Fuskarta..?
Kodai ba Mutum bace Aljanna ce..!?
Wata zuciya tace"Mutum ce ba Dazu kaga Kafarta ba..Bata da Kofato..!
Sai kuma ya Saki Mirmishi kafin ya koma ya kwanta Ringingine yana mai Dora kansa saman Hannayensa acikin Ransa yace"Koma aljannace...Ni Imran nafi karfinta..!
Daga haka barci ya kwasheshi Dakyar ammh Abun mamaki masu cike da mafarkin Inteesar

Washegari sai 10am suka shiga makaranta Shiyasa Ya Yusuf ya tafi ya barsu sai da suka fito Daga Lecture suna Hanya zasu masallaci Munari ta Kalli Inteesar data ganta Yau wanu iri bata da Kuzari kamar ko yaushe tace"Besty wai duk fushin ne... ? Am Sorry..Wlh am just kidding..!
Inteesar ta kalleta kawai batace komai ba Sai Munari Taji wani iri Riko Hannun Inteesar tayi yasa suka Dakata da Tafiya Munari ta kalleta Tana Fadin"Meke damun ki ne..?
Inteesar ta Saki Mirmishi kafin tace"Bafa komai..Kece wai kika bani mamaki kina wani ban hakuri..? To miye na ban hakuri..?
Munari tace"Ai naga jiya baki ji Dadin nganata bace kuma..!
Manta kawai..!
Inteesar ta Katseta Lokaci Daya tana jan Hannunta suka Cigaba da Tafiya Munari dai sai kallonta take tana Naxarinta ta Tabbata wani abu na Damun Inteesar Ta san ta Tana da Sakin jiki da wanda suka saba kuma Tana da Kuzari da kazar kazar ba kamar yau data ganta sai a Hankali ba
Ganin yadda Tayi ne yasa bata kara Tambayanta ba ammh Haka suka Wuni acikin makaranta Inteesar bata da Kuzari sai chan ne na ta Dan saki suka Fara Hira,
Abunda Munari bata gane bane Inteesar Tunanin Abunda ya Faru jiya yaki wucewa acikin Ranta,itama Har mafarkin abun ta Sake yi,wai gata Rumgume ajikin Imran sai abun ya Dameta sosai Tana ganin ya gama da ita ne Tunda ya Rumgumeta kuma abun da bata saba dashi ba Shiyaasa duk ya Sakarmata Jiki da kwarin zuciya.
Sai dai ta saka aranta bazata Kara yarda su hadu da Imran ba Domin ai Tunda ya Rungumeta yaji Tudun Nonuwanta ya gama da ita Har Abada.
Tun kuma Daga Ranar Inteesar ta Yanke duk wani Hanyar Haduwarta da Imran ta Rage shiga gidansu in zata Shiga kuma sai ta Tabbatar da Baya gida,In kuma ta Hangesa sai ta Boye kanta saboda Bata so ya ganta.
Imran daya Daina ganinta bai Damu ba Sai Daga baya sai ya fara jin ya Damu Saboda ya daina ganinta agidan kuma bazai tambayan Munari ba,Yana Tsoron kada ace ta Koma Gidansu ne,Ya ma rasa Dalilinsa na Wannan tsorom Ranar har kiran Sagir yayi yana Tambayansa Wannan yarinyar fa..?
Daman Sagir na jin Haushinsa a Gadarance yace mai"Wata yarinya kuma..!Rainin Wayau ne baya so Shiyasa ya Datse Kiran yana kara jin Haushin kansa me ye hadin da ita..! Da zai ji ya Damu Domin ya Daina ganinta da wannan Tunanin ya Watsar da komai shi kuma Sagir bai maida kai kan mganar Imran ba yana Tunanin wani Wulakancin nashi ne ya Tashi kan Inteesar shiyasa ya Nunamai bai ma Fahimcesa ba.
Sai dai mai Imran yaji Duk Duniya Fuskar Inteesar yake son gani Duk da ya gama Haddace Fuskarta Inda ya Iya zane zai iya Zama ya zana sai dai Haka nan yake son kara Kallon Fuskarta Kamar za"ayi mai gafara Dalilin haka ya koma Zuwa Shagon Sagir,wanda yaransa Har sun Fara Sakewa suna Murnan Takurarre ya Daina zuwa sai gashi Ranar kwatsam ya Dawo,Ai Ranar ba wani wanda yayi Wani Motsi mai Karfin Sanin Halinsa Mganarsa kamar yankan Takobi ne in yace Dole sai takai Sara ne.
Ba domin kowa ya dawo ba sai Domin Inteesar ya gama yanke ma kansa mganar Cewa Inteesar ba haka ta barsa ba indai ita ba Aljannah bace to Akwai wani abu akasa.
Taya ya haka kurum rana Tsaka Zai Dawo ba Wacce yake son gani sai ita a Baya yadda da ana cewa Ana ma Mutum asiri sai yanzu ya Fara Tunanin asiri tamai ya Zama Dole ya ganta ko yatambayeta Me yasa tamai asiri sai dai bai samu ganinta ba,Ko makaranta suka Dawo bata yarda ta Sauka ta Kofar Shagon Sagir sai takara Chan gaba in kuma a kafa suka Tako da Sauri take wuce wajen bata ma ko kallon Barayin Duk da tana ganin Imran din ammh shi baya ganinta,sai sau Daya kuma kafin ya yi wani yunkuri ta Shige shi kuma bazai iya Binta ba.
Ana cikin haka suka Fara Test basa Samun Lokaci domin suna gabda Fara Exams din Farkon Zangon Karatunsu.
Daddy yazo ya ganta Sau Daya shima amakaranta ya Bita bai gayamata zai zo ba,Kawai ya Kirata yace ta ina..?murna kamar Inteesar zata Shida aka kuma yi Rashin Sa"a Munari ta Shiga Masallacin yin Sallah ita kuma Inteesar sai bataje ba ta Zauna anan Department dinsu tana Duba littafanta Daddy ya kirata.
Ashe ma ya shigo Cikin makarantar yana Office din abokinsa Wani Daurin auran Yar abokin su da sukayi karatu Tare ya kawosa,chan taje ta samesa suka ga juna,bai wani Dade ba yace zai tafi Har Department dinsu suka Dawo Neman Munari bata ganta ba Ta Kira wayarta sai ta Tuna ai jakar na Munarin gata a Hannunta,Kuma har Masallacin taje akace mata ta Fito,Karshenta Dai Daddy tafiya yayi basu hadu da Munari ba sai bayan tafiyarsa ne ta ganta ashe itama Nemanta Takeyi kuma ba waya ballatana ta Kirata Cikin Rashin jin Dadin Inteesar ta Fadamata Zuwan Daddy da Tafiyarsa ta bata 5k din Dayace ta bata Ita kuma 15k ya bata 10k yace takai ma Mama Munari ta karba Tana ta Godiya Tare da Cizon Yatsan Rashin Ganin Daddy a Karo na Biyu.
Sati biyu da gama Test dinsu suka Fara Jarawabawarsu Cikin Kwarewa Dama Tuni sun shiryamata basu sha Wahalanta ba,Inteesar nata Murnan Zuwa Gida Kaduna yayinda Munari ke alhinin kewar Inteesar din.
Sai uku sukayi suna Jarabawa kafin su gama sun samu Hutun Sati uku kafin su Dawo su Dora a Karatun Zango na Biyun aji Daya
Aranar da suka gama Inteesar Kamar Zata Suma saboda Murna ta gama Hada kayanta Ya Basheer da Safe zai zo ya Tafi da ita.
Munari duk ta shiga Damuwa Saboda Tafiyan Inteesar din itama Tana jin Zatayi matukar kewar Munarin.
Bayan sun Rabu aranar Inteesar Tayi Tunamin ta bama Munari wani abun Da Zata Rika Tunawa da ita sai ta Dauki wani Dankunnen gold dinta mai Sarka da Zobe da awarwaro ta saka ajaka zata kaima Munari ba Domin bata dashi ba sai Domin Wani abun da Zata Rika Tunawa da ita in ta koma Kaduna itama Zataje Munarin ta bata wani abun da In ta koma Kaduna ta Kallah Zata rika ganinsa kamar Munarin.
Karfe 5pm tayi ma mama sallama ta Fito tana Sanye Cikin bakin Wando plazo da wata Riga Mai Dogon Hannu ammh Tana da dan Tsawo,sai ta Sanya Farin hijabinta mai Hannu wanda yakai mata Har Gwiwa.
Karamar Jakar data saka Dan kunnen aciki sai Kafarta Sanye cikin Takalmi Sahu Ciki Fari kalan na mata.
Tun fitowarta Gidan ya ganta Lokacin ya Fito Daga Shagon Sagir Karan Sigari rike a Hannunsa yana sha Gida Zai tafi Domin yagaji da Zaman sai ya ganta Tanufi Hanyar gidansu Gabansa sai da yya fadi,Tun bayan mganar Data Fadamai na ya Daina shan Taba Kowa yasan ya Rage shanta sai dai Yanayin Dayake ciki na bukatuwan son ganinta ya kara maidashi Ruwa..
Jikinsa har wani mazari yake Zuciyarsa na Ingizasa yabi bayanta Cikin Takunsa na Sasasarfa ya Taka mata Baya Kowani Dakika na Takunta Sai Zuciyarsa ta Buga,kawai ya gama Sakama Ransa yarinyar nan asiri tayimai kuma yau sai ya Shaketa ta gayamai inda ta Binne koma Menene taje ta Hakosa Imran yafi karfinta bama Itaba yafi karfin matan da suka Fita komai da komai da duk Abunda suke Takama.





*Janafty*
3/22/22, 23:06 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️*



*🅿?23*


Inteesar Tafiyarta take cikin Natsuwa Kwata kwata bata ji takun Sawun Imran ba Ballatana ta Fahimci He is after Her,Saboda Shi Yana tafiyarsa Cikin Sassarfa da mazantaka irin na Jaruman Maza sai dai yana komai Cikin Natsuwa ne da baka isa yana Tafiya kaji takun Sawunsa ba Shiyasa bata jiba har ta iso gidansu Munari,Karamar kofar tana Bude ne Ta saka Hannu da Niyyar Bugawa sai Kofar ta dan Bude shiyasa ta saka kanta kai Tsaye ta Shiga gidan Imran Shima alokacin ya Mara mata baya.
Iro megadi bashi a Haraban gidan ya Kewaya.
Hankalinta yayi gaba kawai taji ansha Gabanta da Sauri Cikin Tsoro taja baya Jikinta ya fara rawa da ganin wanda ke gabanta ya Kafe ta da Idanuwansa yana More Kallonta Da dukkan zuciyarsa Sai alokacin yaji Salamar Daya Dade bai samu irinta ba wani Natsuwa da Farinciki suna kara Kwaraya acikin Ransa wanda ada yake jinsa kamar yana yawo asaman Gajimare,Duk adalilin rashin ganin fuskar Inteesar wanda ya kara Tabbarar mai da Asiri Inteesar tayi mai kuma yau sai ya Tabbatar da koma Miye,sai ta Hako shi Duk inda ta Binnesa.
Inteesar da gabanta ke Fadi saboda Ganin Imran taja baya tana Kara Rike Jakar Hannunta Dakyau Wuri Wuri Take da ido Tana Neman Hanyar Gudu Har ga Allah bata son ta Hadu Dashi gani take kamar yana mata kallon na riga nagama Dake.
Imran ya Lura da yadda take Neman Zurawa da gudu da Sauri yace"Don"t Ever Try it..Ranki zai baci in kika Gudu ban yi mgana Dake ba..!
Yafada Cikin Dakuna Fuska da Kakkusan Muryansa.
Miyau ta Hadiye da Sauri Kafin ta Sadda kanta kasa Tana Fadin"Ba..ba guduwa zan yi ba..Ina yini..?
Tafada Tana kallon kasa bata so ta Dago su kara Hada ido Jikinta wani iri yake mata kamar ba nata ba.
Karkace kai yayi yana Kallonta Cikin Nazari kafin taji yace cikin Kaushin Murya"Ina kika Binne asirin..?
Da sauri ta Dago Tana kallonsa Cikin mamakin kalamansa tace"Asiri kuma..?
Tafada Lokaci Daya tana Zaro mai ido Kai ya gyada mata kafin yace"Eh asirin da kikamin wanda yasa nake son ganin Fuskarki koda yaushe..!
Yafada kai Tsaye domin shi daman Dan kai Tsaye ne Baya karya Domin ka so shi.
Inteesar ta saka Hannunta Guda a Kirji ta Dafe Lokaci Daya Tana Fadin"Ni nayi maka asiri..?
Ransa ne ya fara baci Cikin Dakuna Fuska yace"Eh kefa..Kina Nufin zam miki karya ne..?
Inteesar datsoro ya kamata sai Idanuwanta suka Tara kwallah Cikin kwalkwal take fadin"Wlh..Wlh..Allah ni ban yi maka asiri ba..Ni ban taba sanin ma a ina ake asiri ba..Kayi Hakuri..!
Sai hawaye Sharr duka Idanuwan Biyu Lokaci Tana Jan majina,Mamakinta ya kamashi ganin Daga mgana sai kuka yasa ya kasa ce mata komai.
Kanta na kasa ta shiga Furta"Ban yi maka komai ba..Wlh bansani bane..Bansani ba..!
Tafada cikin kuka Har tana Shan majina da Shessheka.
Sai jikinsa yayi sanyi ganin yadda take kuka da Sauri yace"Ke daga mgana sai kuka..? Stop it kada wani ya fito yace ni na Dake ki..!
Jin haka yasa ta fara share Hawayenta Tana Kara jam majina Kafin ta Dago Tana Fadin"Ka yarda ban maka asiri ba..? Wlh ban san ma inane ake asirin ba..In Umma taji wannan mganar Gobe in na koma Gida Zata min Fada ni kuma bana son Fada..!
Tana kallon kwayan Idanuwansa Tana mgana Sai kuka kuma Sharr ta Kara Rike Jakarta Tana kuka,jikinsa sai ya Saki ya kasa Dauke ido Daga kanta Haka kurum yau karo na Farko yaji bai kyauta ba yasa wani kuka,Yau yaji Bai kyauta ba Daya Tareta da wannan mganar gashi tayi kuka ko Daga ganin yanayin mganarta bata san komai ba.
Cikin Sanyin murya yace"Bazata ji ba..Kuma bazata miki fada ba..!
Yafada karo na Farko Cikin Sigar Lallashi Jin haka yasa ta Sauke Numfashi Tana Fadin"Ka yarda ban yi maka komai ba..!?
Tafada Tana Kallonsa Kallon Dayajisa Cikin wani yanayi,Kai ya dan kauda kafin yace"Eh..Share Hawayen ki .!
Yafada yana Kokarin Saisaita kansa Domin yanajin kamar ya Fara Fita Daga asalin Imran din sa yana komawa kamar bashi ba.
Jin abunda ya Fada yasa tayi Saurin Saka Hannu ta Share Hawayenta Shi kuma yana ta kallonta tana Dagowa suka Hada ido da Sauri ta Sadda kanta Kafafunta na rawa.
Aransa kuwa ayyana Shagwaban yarinyar kawai yake Daga mgana sai kuka..?
Baisan Dalili ba kawai yaji yana ce mata"Gobe..ina zaki..?
Bata Dago ba tace"Gida..yau mun gama Exams..!
Cikin wani yanayi yace"Ina ne gidan naku..?
Kanta na kasa Sitll tace"Kaduna..!
Tsam yayi yana Kallonta jin Zuciyarsana so taji Rashin jin Dadin Tafiyarta bai san sadda Bakin sa ya Subuce ya Furta"In kin tafi sai yaushe Zaki Dawo..? inteesar ta Dago cikin mamakinsa Tana Kallonsa sai kuma ya Hade rai yana Tunanin meke Damunsa .?
Kai ta Rausaya Kafin tace"Hutun Sati uku garemu..So kila bai fi na kara 1 week ba kafin na dawo..!
Har tagama mgana bai ce komai ba Idanuwansa na kallon Gefe yana Tunanin yadda zai iya Zama har na Tsawon wata Daya kafin ta Dawo
Cikin Idanuwansa yake kallonta Kafin yace"Ki dawo alokacin da kukayi Resuming..? Promise..?
Yafada kai Tsaye yana Sakarmata Duka Idanuwansa wadanda suka Sake Rikita taji bazata iyamai gaddama ba. Da sauri tace"Tom..!
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya Bata Hanya batare da yayi mgana ba Kanta na kasa ta fara Tafiya shi kuma yana Gefe ya Harde Duka Hannunsa a Kirjinsa yana Binta da kallo yana ji kamar in tatafi shikenan kamar an Daukemai wani gafara,kamar ya Hanata Tafiya baisan yaushe ne ba..? Sai dai kallonta na mantar dashi Dukkan wani kuncin Duniya.
Kamar ance ta Waiwayowa tana Juyowa suka Hada ido,Da sauri ya Dauke kansa ita kuma sai ta Murmusa kawai ta Tura Kofar da zai sadata da Falon Gidan tana jinta Cikin yanayin Data ke Tsintar kanta indai Tana gaban Imran.
Sai da ta shige kana ya Sauke Idanunsa ya koma Kan Mashinsa Dinsa Dake Fake a haraban Gidan ya Haye Samanta Aljihun wandonsa ya saka Hannu ya Dauko kwalin aspen da Lether ya Kunnata ya shiga Zuka so yake yaji baya Tunanin Inteesar ballatana Gilmawar Fuskarta ko son ganinta so yake ji He don"t care in Tatafi sai dai ina Hayakin na Shiga Cikinsa Kamar baya saka Komai gabadaya komai ya Tsayamai Cak Mood dinsa ya sauya yana so yayi Tunanin kan karan kanshi ammh ya kasa Kowani Dakika yana jin Tsorom Tafiyarta na Tsawon kwanaki bazai ga Fuskarta ba.
Bai san adadin Lokacin Daya Dauka yana Zaune yana Busa Hayakinsa ba Har sai da Ya Yusuf ya Dawo Daga Wajen aiki,Har mgana yayi mishi Imran din ya Daakuna Fuska ya Kaida kai ganin haka yasa ya Girgiza kai kawai ya Rataya Jakar Briefcase dinsa ya Nufi Cikin Gida aransa yana Tunanin zai samu Abba da Mgana ya Lura Imran abubuwansa basa Raguwa sai ma Karuwa da sukeyi.
Afalon yaci karo da Inteesar Munari ta Rakota Da ita da Anty Safiya sai Abba Dake zaune Sallama Tayi Musu Abba nata saka mata albarka.
Kallonta yayi yana Fadin"Me sunanki na gaskiya..?
Inteesar na Mirmishi Cikin Ladabi tace"Sunana MARYAM Abba sunan Kakata naci wacce ta Haifi Daddy na shiyasa yake kirana da Intee har sunan ya Bini..!
Abba ya Kalleta Cikin Dattakonsa yana Fadib"Masha Allah ai nima sunan Mahaifiyata Gareki..Daga yau kin tashi Daga yata kin koma Uwata..Allah yayi albarka..!
Inteesae bakinta Har kunne tace"Na zama Maman Daddy da Abba kenan..!
Su Munari nata Dariya ta gaida ya Yusuf ya amsa yana Kallon Safiya yace"Naga kamar kuna Sallama ne..?
Da sauri Munari tace"Gobe zata koma Gida Hutu ya Yusuf.!
Tafada Cikin nuna Rashin jin Dadinta Kada kai yayi yana Fadin"Ayyah..Munarin Abba zaki bari da kewa...Anywhy..Allah ya Kiyaye Hanya muna gaida kowa da kowa..!
Abba ma ya Karbe da cewa"Kice ina gaida Daddyn naki..In Allah ya Nufa zamu hadu..!
Inteesar tace"Zaiji Abba..Ka manta bakace agaida Umma ba..Umma Sarkin Fada..!
Tafada Tana Tura baki Munari ta Zungureta tana Fadin"Ke kuma Sarkin Shagwaba da Laifi ko..?Dariya suka sakamata Anty Safiya ta Mikamata Leda Hannunta Tace takai ma Umma Turaruka ne Dana Daki da Humra Inteesar ta Karba Bakinta Har Kunne Sallama sukayi ta karbi Jakar Hannun Ya Yusuf suka Nufi bangaransu Itama Daganan tayi ma Abba Sallama ya Bita da Allah ya Kiyaye hanya Ana gabda da kiran mganariba yasa ya tashi ya Shiga ciki Domin ya Dauro alwala,ita kuma Munari ta koma Bedroom dinta ta Dauko Mayafinta ganin ba kowa afalon yasa Inteesar ta Fice zuwa Haraban gidan ta jirata Hannunta Dauke da Ledoji guda Biyu Daya Sakon Anty Safiya ne Daya kuma na Munari ne kaya ta bata Da Hijabi Sabo ne bata taba sawa ba ya yusuf ya Dinkamatashi itama ta bama Inteesar in ta koma Kaduna in ta gansu ta Tuna da ita.
Tana Tsaye tana Mirmishi Gefe Daya Tana ayyana gobe i uwar haka tana Jikin Daddynta tana Zubamai Shagwaba kamar an ce ta Waiga sai taci karo da Imran zaune kan Mashin dinsa karan sigari a hannunsa idanuwansa suna Lumshe yana Busawa Hayakin yana Fita ta Hanci ta baki.
Tsam tayi tana kallonsa,tsausayinsa ya kamata ganin yanayinsa wanda yasa bata san sadda ta taka zuwa gabansa ta Tsaya ba ganin har ta Tsaya bai Lura da ita ba yasa ta san yayi nisa Cikin yanayin Dayake ciki.
Kawai sai ta saka Hannunta guda Daya ta Zare Karan Sigarin Dake hannunsa Daidai Lokacin daya Ware Idanuwansa akanta.
Dam! Gabansu ya Buga atare, Suka kurana juna ido Cikin Bugawar Numfashi da Muradi mai girma,
Ita ce tayi Saurin Janyen idanuwanta Saboda tana ji kamar Kafafuwanta bazasu iya Daukanta ba
Cikin Sanyinta tace"Ka manta na Fada maka Ita shan Taba Illah take ga Lafiyar Dan adam..?
Ko ka manta na taba Fada maka Shan Taba bata dace dakai ba..?
Har tagama mgana yana kallon Dan bakinta ko Kiftawa bayayi ita bata ma Kara Kallonsa ba ta Saki Taban a kasa ta Mutsuketa Tana Fadin"Bazan barka da ita ba..Bani na aljihunka i know akwai wasu aciki..?
Tafada Cikin Kamewa Lokaci Daya Tana Mikomai Zararan Hannayenta..
Galala yake Bin Hannun nata da Kallon Mamakinta na kamashi Cikin Dakiya ta kara Fadin"bani na aljihunka nace...Kadai san nasan ba wannan bace ita kadai ba ko..!?
Dariyarta ma yake yi acikin Ransa yana mamakin yau rana ta Farko da Mace ta Tsaya gabansa Tana bashi Unarni haka.
Yaji bama zai iya yimata gaddama ba Ya saka Hannu a aljihu ya Dauko Kwalin Taban ya saka mata a Hannu Harda Letthe din gabadaya.
Kwalin tabi da kallo kamar tana kyamkyami nan da nan Zuciyarta ta Fara tashi Daman Daurewa take,Da Sauri ta Bude ledan hannunta ta Watsashi aciki Tana yamutsa Fuska tace"Kamar itace abincinka..? Bantaba Ganinka baka shan Taba ba sai sau Daya..Plz ka bari In ba so kake Huhunka ya samu mtsala ba .!.
Tafada Tana kallon Gefe domin bata so ya Fahimci bakinta ya Cika da Miyau..
Mirmishi ya Sakarmata mai kara Har sai da ta Dago Tana kallonsa Cikin mamakinsa Saukowa yayi Daga Mashin din yana Fadin"Ban ce miki Daman zan daina sha ba..!
Inteesar ta gyara Bakinta tace"To yanzu kayi min alkwarin zaka Daina shan Taba..!
Kallonta yayi kafin yace"No..Ni bana haka ba. bazan yi miki alkwarin da bazan cika ba..Zan daina shanta Duk Ranar da Allah yace..!
Mamaki ya kamata ta Kada ido Tana kallonsa yace"Yes bana yima Mutum alkwarin da na san bazan cika ba..kuma bana so nima ayimin alkwarin da baza"a cikamin ba..Kuma ni bana karya agaban mutum saboda ya soni..Ina Fadin gaskiyatane gaban ko Waye Allah ne kadai nake jin Tsoro ba Mutum ba..!
Daga haka kawai ya wuce ta yana Tafiya Cikin Sarsassafa kafin taji yace"Kada ki sake ki mana Amai Gida..!

Da kallo ta Bisa Har ya shige cikin Gida Mirmishi ya kamata Miyau ta Zubar Daya cika bakinta afili ta Furta..'He is nice..ashe ya Lura ta kusa amai..!
Bata san da zuwan Munari ba sai taji kawai ta Dafa ta har ta Tsorata sai da ta Waiga ta ganta ta Sauke Numfashi Tana Fadin"Har kin bani Tsoro..!
Munari tace"Hala Ya Imran kika gani..? Yanzu na gansa ya shiga gida yana Cika yana batsewa..!
Inteesar tace"Kamar wani kabewa..!
Dariya suka saka Harda tafawa kafin su kama tafiya suka Fice wa Daga gidan.
Suna tafe suna Hira har gidan Mama akofar gidan sukayi sallama da Munari akan Gobe zata zo kafin Intee din ta wuce,Sai dai Inteesar ta Boyema Munari abunda ya Faru tsakaninta da Imran haka kurum taji bazata iya fadamata ba
Haka Inteesar ta shiga cikin Gida Tana nuna ma Mama Abunda Anty Safiya ta bada akai ma Umma ta Karba tagani Tana ta Godiya.
Ranar barci barawo ne ya sace Intee Saboda Murna asuban Fari tatashi Tayi ma Mama sharan Daki ta Share Tsakar gida,Ta zo ta saka Kettle daya Tafasa ta Juye tayi wanka Kafin ta Fito Mama ta Hada mata abun kari Saboda Murna ko Yunwa ma bataji sai da Mama ta Mtsamata ne tasha Tea kadan da Buredi.
Koda karfe 11am na safe Basheer na Falon Mama shi da su Abiden yazo,Shi daman dan akida ne baya son Tafiyar Dare kuma bayason bata Lokaci shiyasa suna gaisawa da Mama yace Intee ta Fito su Dauki Hanya
Sagir ne ya Fitar mata da kayanta akwati Daya zata koma dashi,sai Sakon Mama na Umma da nasu Inno,sai na Anty safiya,bawasu kaya me da yawa ba.
Tun tana cikin gida ta Kira Munari ta Fadamata ya basheer yazo zasu tafi Munari tace gatanan zuwa sai dai Shuru Har Ya Basheer din da Sagir suka Fita waje aka gama Saka kaya a Booth Munari bata zo ba,Ita kuma Har ta kawo Falo Taga Imran ya Fita Haraban gida sai ta Labe ta Leka taga ko ya Fita sai taga yana Jingine jikin Mashinsa yana Danna Wayarsa karama bashi ma da Niyar tashi,Ballatana ta samu ta Fita kuma ta Tabbata in ya ganta bazai barta ta Fita ba.,Sai ta tsaya nan falon tana Lekonsa Gashi ta bar Wayarta acikin Bedroom dinta Inteesar nata Kira Bata Dauka ba.
Ga ya basheer nata mata Fadan su tafi bayason Tafiyar dare ga yara yazo dasu,Dole tana ji Tana gani ta Fada Gidan Gaba Tana Tura baki Domin tasan ko giyan wake tasha bata isa tace su jira zuwan Munari ba ko kuma su Biya gidansu ba Dama Daddy ne yauwa tasan shi zai mtsamai ammh yau ba Daddy bata isa ba.
Saboda Haushi ma Abiden na Hawa Jikinta ta Harareshi ta Mtsa jikin Kofa Tana Tura baki Basheer bai Damu ba Kallonta kawai yayi ya kada kai,Abida Tana Jikinsa Ta lafe ita akwai son jiki ne Abiden din ne Sarkin wasa.
Haka suka tafi Sagir na Daga musu Hannu da Mama na Daga Zaure Itama Tana Daga musu hannu Allah Sarki Sabo Turken wawa.
Munari dai Dole Daki ta koma tana Cijon yatsa,Wayarta ta Daga taga Kiran Inteesar sai tabi baya,Inteesar na ganin kiran Munari taki Dauka sai da ya Katse ta Turamata Sako.

*Muna hanya..Nayi ta Jiranki baki zo ba..*

Munari na ganin Sakon sai da taji wani iri da sauri ta Rubuta mata da Amsa.
Am sorry Besty..Naso na Fito Ya Imran na gani aharaba shiyasa..Allah ya kiyaye Hanya ki gaida Daddy da Umma..!

Ta turama Inteesar wanda Tana gani sai da ta Murmusa da ta Tuna da Imran cikin Dariya ta Turama Munari..

Is ok..Ameen zasu ji..Ki kula da kanki da kowa da kowa Expecially Muradaden yayanki IMRAN..!
Tana gama Tura mata ta maida wayarta jaka tana Mirmishi Basheer na kallonta bai ce mata komai ba sanin ko yayi mgana bazata Tankasa ba Yau yasan Karansa Wajen Daddy Fada sai ya Toshe kunne.
Munari kuwa Tana ganin sakon ta Zaro ido a fili ta Furta."ni ai bazan iya Kula da Ya Imran ba Tabdijam..!

*****

Koda Inteesar ta Dawo Daddy baya gida,Umma ce Kadai sai Anty Hauwa Inteesar ta makale Umma Tana Murnan ganinta,Haka ta Rumgume Anty Hauwa Tana Murna ya basheer ta bari da Shigo mata da kayanta Murna ya mantar da ita,Shiyasa akace No place Like Home Inteesar ta Fahinci hakan
Umma ta yi mata Shinkafa da Miyar Kaza,sai kunun Aya,Inteesar ta Zauna taci ta koshi sosai,Daddy bai Dawo gidan ba sai Dare Intee ta Rumgumesa Tana Murna ganinsa shi kansa Bakinsa yaki rufuwa Saboda Dawowar yar Lelen nashi.
Ranar kusan raba Dare sukayi suna Hira,Daddy yasha Hirar Makaranta da ta Mama data Ya Sagir sai Hirar Munari da yan gidansu da sakon Gaisuwan Abba zuwa garesa.
Ta kuma bama Umma sakon Anty Safiya Umma ta Karba tana ta Godiya da Sakon Mama na Garin Dan wake,da Yaji sai Daddawa Dakakkiya da kuka da Kubewa,Haka ma Wanda ta aiko ma su Inno harda Garin Kunu Umma sai Murna take..
Inteesar sai da ta Duba ledan Kayan da Munari ta bata taci karo da sigarin data Karba Hannun Imran da Lether dinsa Saurin Dauka Tayi ta Jefa Cikin Tiolet tayi flooshing kada wani ya gani ta Shiga uku.
Inteesar

Please Login or Register in order to submit comment