Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ji ba Godai godai Dake kin Ture yara kasa ke Kin Hau Cinya ko.? Anya Inti kina so ki Girma kuwa.? Yarinya kina Girma kina kara Komawa baya koda yake ba Laifin ki bane na Alhaji ne duk ya Sangartaki.."
Ko kafin tagama Mganarta Bakin Inti ya kusa Fadowa kasa Cikin Sangarta Ta kalli Daddy Tana Fadin"Daddy kaji Umma ko..? Shiyasa nake ta Murna zan Tafi na bar mata gidan.."Ta karishe Fada tana wani Tura baki.
Umma ta tabe baki Tana Fadin"Ai chan bazaki samu Damar yin wannan Sangarta ba..Yaya Amina ba Irin Sakarkarun Matanan bane atsaye take..Ga kuma yayanki Sagir zan ce mai da kinyi wani Abu ya Zanemin ke.."Kawai ba sai Inti ta Saki kuka Kamar wata karamar yarinyar Bashir sai Dariya yake Umma ta kalleta Sororo kafin tace"Yau naga Sakalci Inti wai yaushe Zaki Girma ne..? Kin fa wuce Shekara ashirin Kina Shirin Shiga Jami"a kina Tabara Yau ko aurar dake mukayi Badi war haka kin Haihu.."Ai jin haka sai Inti ta kara Sautin kukanta Tanayi Tana Fadin"Ni ba zanyi aure ba..Kuma bazan Haihu ba.."Kai Dagajin kukan kasan na Sangarta ne Daddy ke Lallashinta yana Fadin"To daman yaushe Autana  ta isa aure..!? Ai ba yanzu zaki aure ba sai kin kara girma...Shima sai naga Dacewar Mijin da Zaki aura wanda zai Rikemin ke ya Rika Lallabaki kamar yadda nake Lallabaki sai yayimin alkawarin kula da Hakan kana zan yarda na Bashi Autana.."Ya karishe Fada yana Shafa Kumatunta da Sauri ta Washe baki Lokaci Daya Tana Fadin"Shiyasa nafi sonka..Akan Umma Daddy..Kafi sona..Ita kuwa ssi ta cemin wai ni Shagwabbiyace.."
Daddy yace"Rabu da ita...Duk yan Bakin ciki ne.."Ya Bashir na Dariya yace'Hardani Intin Umma..? Tana wani mele baki Tace"Ni ba Intin Umma bace..Intin Daddynta ne.."Umma na jinta Tayi tsaki Tana Fadin'Nabarmai yayi ta kaya..Ni ai Bashir ne D'ana..Ni Daman ba Mamanki bace Daga Gidan Marayu Alhaji ya Dauko ki.."Baki ta Bare zata kara sakin kuka Daddy ya Riketa yana Fadin"Au kukan zaki mata..? Daman ta Fadane don ta saki kuka..Haushin kinfi sona ne Autana Rabu dasu.."
Washe baki Tayi tana Fadin"Yauwa Daddyna..Ammh zaka Kira Inna Amina kamata mgana ko..? Kaji fa umma nacewa Zata saka D'anta wai ya Rika Dukana.."Tafada Idanuwanta na Cika da kwallah Domin inti akwai Tsoron Duka.

Kanta yake Shafawa yana Fadin"Waneshi ya Dakarmin Auta guda..? Sha kurumin ki ni Dakaina zan kai ki Har kano gaban Innan naki na Bada Amanarki kana naja ma D'an wajen nata kunni komai kikayi kada ya Dakeki ya Lallabaki ne Saboda ke Auta ce.."Murna Ta Farayi ta Rumgumeshi Tana Fadin"Ina Kaunarka Daddyna."Kanta yake Shafawa yana Fadin"Nima haka Auta Daga ke ba Kari Intin Babanta.."Umma Dake Goge ma Abidin Baki Daya bata da Madara tace"Uhm..Bashir tashi ka Tafi gidanka kada ka Biyema wannan Shirmen na Alhaji da yarsa..Kabar Hauwa ita kadai gashi kuma kasan Halin Datake Ciki.."Yana Kokarin mikewa yace"To Umma..."
Yafada yana Mika mata Abida Data Fara Barci ta karbeta Lokaci Daya yana Fadin"Daddy zan tafi..Sai Allah ya kaimu.!
Daddy yace"Shikenan Bashir.Ya ake  Ciki kan mganar Tafiyar Inti din..? Kunyi mgana da yaron Wajen Innan naku..?
Bashir yace"Eh Daddy munyi mgana..Lokaci fa ya tafi Tuni sun Fara Lacture ya kamata Cikin Satin nan Tatafi tayi Registration Sati na Sama ta Fara karatu gaskiya.."
Daddy ya Jinjina kai yana Fadin"Shikenan Zuwa Jibi sai muje na kaita..Insha Allahu kafin Lokacin Komai ya kamallah ko Autana..?
Inti ta gyada kai Tana Fadin"Daddy ai kagama Siyan min komai fa Abu Daya ya Rage f..? Yana kallonta yace"Menene shi Autana..? Cikin Daga kai tace"Sabuwar waya Daddy...Taya zan je da Wannan Tsohuwar wayar Jami"a ai sai su raina maka ni.."Ta karishe Fada tana wani Hura Hanci Umma ta saki Baki Tana kallonta kafin Tayi mgana Daddy yace"Hakane kuma fa..To kada ki Damu zuwa gobe Bashir zai je ya Dubo miki wata iri kike so.? Da sauri tace"Samsung Daddy..Ina sonta sosai.."Daddy yace"Shikenan Angama Intin Daddynta..!
Dariya ta saki mai kayatarwa Tana Fadin"Nagode Daddyna..!
Umma dake zaune tace"Ka biye mata kuma..? Wayata fa ko wata Biyar Batayi ba Daka Siya mata bafa..Haba Alhaji bai kamata kana Biye ma yarinyar nan ba..Yakamata ka Rika Duba Rayuwa in yau mune gobe bamu bane Haka koda yaushe Daada na Fadamaka in mukaje Gaishesu taga Inti na wannan Tabaran ko bakomai watarana Gidan wani Zataje.."Yana jinta bai yi mgana ba Illah kallon Inti Dayayi wacce ta batarai yace"Autana jeki ki kwanta kinji ko..? Sai da Safe.."Batayi Gaddama ba ta Mike Tana Fadin"Gud Night Daddy..Umma sai da Safe Ya Bashi ka gaida Anty Hauwa.."Dukkansu suka amsa mata Umma tace"Zo ki Dauki Abida wajen ki zasu kwana..'Baki ta Tura tana Fadin"Wajena kuma Umma..? Tab ni wlh A"a Shegun kukane dasu..Hanani barci fa suke Cikin Dare.."Ta fada kamar Zatayi kuka Umma tace"Allah..? Naga yadda zaki kare in kika Haifi naki..!
Inti na Dariya tace"Daddy na zai Daukan min mai Reno.."da Filon Kujera Umma taRakata dashi Inti ta kwashi Gudu Zuwa Dakinta Tana Dariya Bashir ma Dariyan yake Shi da Daddy,sallama yayi musu ya Biya Kicthen ya Gaida Talatu daya Tarar tana wanke wanke Kafin yayi mgana ma Ta mikomai kulan Umma ta gayamata ya Fice Su Umma ya karama Sallama suka Rakashi da Allah ya kiyaye ya Fice Zuwa Haraban gidan ya Shiga Motar sa Kiran 4matic ya Zuba Hon megadi ya Bude mai get ya Fice Daga Gidan ya Dauki Titin anguwan Rimi inda gidansa yake.

Sai da sukaji Tashin Motarsa kana Daddy ya juyo yana kallon Umma yana Fadin"Meyasa koda yaushe kike maimaita mgana Dayane Salaha..? So nawa zan gayamiki ki Daina Ganin abubuwan da Inti ke yi a wani abu kar ki manta fa yarinya ce fa In ta girma Zaki ga Duk ta Daina wadanan abubuwan kuma kada Ki manta Sai da Bashir ya Shekara Goma sha Biyu aduniya muka Sameta alokacin da muka Fidda rai da samunta ita kadai ce Mace awajenmu menene Laifin in mun bata kulawa da gata..? Ai hakan bai Hanata zama mai Tarbiya da ilimi ba ina alfahari da ita da kananun Shekarunta ta Sauke qur'ani yanzu kan Haddatanta take,Kuma kina gani Da kuruciyata gashi Zata shiga Jami"a Alhamdulillah bata Taba Jawo mana mgana ba Salaha ni banga abun Damuwa ba.."
Ya karishe Fada yana kure ta da ido,Umma ta Sauke Numfashi Tana Fadin"Uhm..Alhaji kenan wai kana Bani mamaki in kace Inti yarinyace..? Wacce ta Haura Shekara ashirin ce yarinya Alhaji..?
Cikin Halin ko inkula yace mata"To in ba yarinya bace Babba ce..? Shekara ashirib Duka Duka nawa take..? Don Allah ki Daina wannan mganar..In bamu kula da yayanmu ba..Ai samun mu ya zama na banza sai mu Daina Fita Neman Salaha..!
Sanin bazai Taba Fahimtarta ba yasa ta bar mganar ta Mike Dauke da Abida Tana Fadin"Bari na kai Abida Daki tayi Barci.."Daddy yace"Ga Abidin ma yayi barci ajikina.."Batayi mgana ba ta wuce Ciki Dakinta ta kai Abida ta kwantar kan gadonta kana ta Dawo ta Dauki Abeedin Shi ma takaishi ta kwantar ta Rufa musu bargo ta Rage musu Sanyin Ac ta kuma Rage Hasken Dakin kana ta Rufo musu kofa ta Fito Ta samu Daddy zaune in da Ta barshi ya maida Hankalinsa kan Talabijin yana kallon Labarai Kitchen ta wuce ta samu Talatu na Goge goge Sannu da aiki Tayi mata kai tsaye Fulas din Dake Kan Cabinet din kitchen din ta Nufa ta Dauki karamin mug ta Tsiyayo Ruwan lipton din Dayaji kayan Itatuwa da Ganyen Na"a Na"a ta Fice dashi Zuwa Falo Tana Zuwa Taja Center Table din Dake Tsakiyar falon ta ijiye Tana Fadin"Alhaji ga Ruwan Lipton din nan..!
Dago kansa yayi yana Fadin"Yauwa Nagode..'Daukowa tayi ta mikamai ya karba ya Fara Kurba sau Biyu yayi ya Dauko yana kallonta yace"Wata anguwa Su Yaya Aminan suka koma ne Bayan Tashin su Daga zoo road..?
Umma tace"Gadan kaya suka koma..Gidan Marigayi din da Sagir din yagada Ta koma Ciki suna zaune.."Daddy ya gyada kai yana Kurban Tea din yace"Sai nake ganin kamar Nauyi zamu kara mata Salaha..!
Umma ta kalleshi a kaikace tace"Wani irin Nauyi kuma..? Sai da ya kara Kurban Tea din yana Fadin"Kai mata Inti da zamu yi ta zauna wajenta Tayi karatu..Ga Wahalan Rayuwa ga Kuma Rigiman Diyar taki..! Umma Tayi Mirmishi Tana Fadin"Wlh ko Daya Alhaji..Bakaji da na kirata na gayamata Intisar ta samu addmission anan BUK ba..Kafin na Furta mata ina son Inti ta zauna wajenta sai dai ta rika zuwa Tana Dawo in anyi Hutu sai Tazo mana nan tayi mana Hutu ita ta Fara Cemin ammh wajena Zata zauna ki..? Kasanta da son Diya mace kuma Allah bai Bata ba Danta kenan kwara Daya Sagir..Bayan mutuwar Mahaifinsa kuma tace bata Sha'awar kara aure ba yadda su Baba Bala basu yi da ita ba tace baxata kara aure ba Shiyasa taki Dawowa ta Fara sana"arta achan tana kula da Danta har gashi yana Karatu shima kuma yana Sana"ar dole suka sakamata ido.!.
Daddy ya jinjina kai alamun gamsuwa yana Fadin"Hakan ma yayi. tunda wani Lokacin sai kiga karayin auran ma wani abu ne Dabam..Badai shi yaron Dangin Mahaifin nashi na waiwayansa ba..?
Umma tace"Eh suna iya bakin kokarinsu..Ai kanin Babbansa Daya Wani Manu..Ko Yaya Aminan wh suna mata kokari..Ita Dayake bamai jira bace macece mai neman na kanta Ko Daga nan gida zaka ga ba kasafai take kira Tanemi wani abu ba.."Daddy yace"Allah sarki..Rabona da kano Tun Rasuwar Mahaifin yaron nata.."Umma tace"Sai gashi Dalilin yarka zai kai ka ko.? Yana Dariya yace"Zaki fara ko..! Kin san bana samun Zama ne..Allah ma ya Taimakeni Bashir yanzu yana kula da komai.."Umma tace"Gaskiya fa..!
Daddy ya mika mata Mug din yana Fadin"Naji Dadi da Inti Tana da inda Zata zauna..Dama bana son zaman Hostel sam kinsanta Tana da Tsiwa kuma bata saba Zama cikin mutane ba..Uwa uba da kuma D'an wajen nata ko bakomai zai rika Taimakata awasu abubuwan Tunda Bashir ma yace shima nan yake Karatun nashi.."Umma tace"Eh Haka Yayan tacemin..Ya kusa gamawa tace shi.."Daddy ya Mike yana Mika yace"Shikenan dai..Zuwa gobe ki kamalla mata komai jibi zamu tafi insha Allahu.."Umma ta mike Itama Tana Fadin"Allah ya kaimu..Miya ce zan mata..Dambun namanta na Soya mata..Sai su Snaks Datace Tana so nayi ma kawata Mgana Gobe za"a kawo.."Hanyar Dakinsa ya Nufa yana Fadin"Ina jiranki aciki.."Hanyar Kitchen ta Nufa Dauke da Mug din Tana Fadin"Gani nan Tafe..Baban Inteesar.."Yana jinta yayi Mirmishi ya Shige Cikin Bedroom din Dayake mallakinsa,Umma Data fito Daga kitchen din Kashe Tibin Tayi Kafin ta Rufamasa Baya.

*******

Yusuf ne ke Tallafe da Abba yana Bashi Tea abaki Munari  na Gefensa Tana mikamai Buredi mai yanka yanka yana Bama Abba Imran na Tsaye Daga Jikin Wardrope din Dake Dakin Abba yana Sanye da Farar Singelet da Wani Bakin wando 3quater,Hannunsa sanye Duka Cikin aljihun wandonsa Allah ya Taimaka yau ba"a Busa abun Ransa ya Hade Tamau kamar bai Taba Dariya ba yanayin yadda yake Tsayen kiris yaje jira atabashi ya Fashe.

Har Yusuf yagama Bama Abba Tea din ya bashi mgangunansa yana kokarin maidashi ya kwanta Imu Dake Tsaye yace"Ka barsa ma Ruwan zafi yabi Jikin nashi.."Yafada Cikin muryansa mai Cike da Amo da zati.
.bai yi gaddama ba Munari ta sakamai Karamin Filo a bayansa suka Jinginshi ya Dago yana kallonsu yana Fadin"Allah yayi muku albarka.."Yusuf yayi Mirmishi ya amsa da Ameen Abba Allah ya baka Lafiya Dukkansu suka amsa da Ameen kafin Yuauf ya Zarce da Fadin"Na Fara Tunanin ko mu Sauya ma Abba Likita ne..?
Imran Dake Duke da kansa yace"Saboda Mene..? Yusuf yace"Bana ganin wani Cigaba..Kullum Abba jiya iyau..Kamar ma Baya yafi akan yanzu.."
Imran ya shafa Gashin kansa Dayayi Uban Dada yace"Ai ba Laifin Likitan bane.."Yusuf ya Kalleshi yana Fadin"Kake gani..? Imran yace"Kaima ka sani ko..?
Yafada yana kallon Maimuna Dake kallonsa Cikin Hararanta yace"ke Lafiya kike kallona kamar Wata mayyah..? Da sauri ta kauda kanta karamin Tsaki yaja yana Fadin"Tashi ki Fita ma..Kinsan bana son yawan kallo ko..? Kwalkwal Tayi da ido kamar Zatayi kuka Zaburo mata yayi yana Fadin"Au bazaki tashi ba kin tsayane kina neman min kuka.? Fice anan kafin ki Tunzurani na Miki Dameji da Fuska.."Da Sauri tatashi Ta Fice Dauke da Mug din da Abba yasha Taa da Bread din.
Yusuf ya kalleshi yana Fadin"Wai waya bata maka rai ne..Kazo ka sauke kan Munari.?
Bai samu Zarafin mgana ba sukaji Muryan Abba yana Fadin"Kabi ahankali IMRAN...'Yafada ahankali Cikin Sanyin Murya duk sai Jikin Imran din yayi sanyi Kawai sai ya gyada kai yana Fadin'"Mubar Abba ya samu barci..Muje Dakina muyi mgana achan..!
Daga Haka ya Fice yana Takunsa na Daya Bayan Daya.
Sai da Yusuf ya ggyarama Abba kwanciya kana ya Baro Dakin Gidan Shuru kamar ko Yaushe Munari yassn ta kwanta Tunda Imu yayi mata jan ido.
Dakin Imran din ya Shiga Cikin mamakinsa ya samesa yana Busa abar tashi Girgiza kai yayi yana Fadin"Wai kai baka gajiya da Busa Hayaki ne..? Kada ta maka illah Fa Imran..!
Cikin Lumahe ido yace"Me yayi saura..? Ai ni Daman Tuni Illah ta gama illatani Hayakin Saura ya samu!
Jin haka yasa Jikin Yusuf yayi sanyi kawai sai ya zauna Gefensa yana Fadin"Hakane..Ammh akallah muyi kokarin ganin mu Rayu Cikin Farinciki ko Saboda Abba.."
Har ya Fidda rai da zai bashi amsa sai yaji yace"Ya mganar Tura mgabatanka gidansu yarinyar nan..?
Yusuf ya sauke ajiyar rai yana Fadin"Nima bansan ya za"ayi ba..Kuma Mahaifin nata niyake Sauraro.."
Imran ya Busar Tabarsa yace"Wazaka Tura..? Yusuf ya kalleshi yace"Bansani ba..Ammh nafara Tunanin kiran gida na Sanar dasu inda muke da kuma abunda ke Faruwa akallah koda bamu koma wajensu ba zasu zo sukaga inda muke kuma Duniya Zata shaida bamu kadai bane AGIDANMU  muma muna da Ahali.."

Kamar wani Kumurci haka ya Mike yana Fadin"Kar ma ka Fara Ya Yusuf Kada ma fara nace....! Yafada da karfi yana Nuna yusuf din da Yatsa Mikewa yayi shima yana Fadin"Nima ba yadda zanyi ne hakan shine mafita..Domin aure ai ba wasa bane.."Imran yace"Ko ka kirasu sunzo babu Abunda zai Sauya su bazasu Taba Fahintarmu ba muma bazamu Fahimcesu ba..Zasu zo ne su kara Daukan Hauka su Dora ma Abba..Su Rika Bleeming dinsa kan Abubuwan da suke Faruwa..Muma ai ba Laifinmu bane Kaddaran Allah ne da Jarabawansa Saboda haka kada ka sake ka kira wani Ballatana a Fahimci inda muke gwara mu Cigaba da Rayuwar ahakan Tafiye mana zama inda baza"a Taba Fahimtar mu ba ballatana abamu Uzuri..!
Ya karishe Fada Cikin kunar rai yana ji kamar alokacin ne abubuwa suke ta Faruwa.
Dafasa Yusuf yayi yana Fadin"Na Fahimce kayanzu ina Mafita...?
Kai Imran ya Shafa Lokaci Daya yana kai ma Gemunsa Wutan Taban Dake hannunsa da Sauri Yusuf ya Buge hannunsa Taban ta Fadi kasa Cikin Fada yace"miye haka..?Zaka yi ma kanka Lahani da kanka fa..!
Mirmishi Imran ya saki yana Fadin"Common Bro..It's Normal fa.."Karamin Tsaki Yusuf Yaja yana yin baya Lokaci Daya yace"Kayi ma yi wanka yau kuwa..? Wlh duk warin Taban kake yi bakin ka kuwa kamar sokaye.."
Imran bai Damu ba sai ma Dariya daya saki yabi Yusuf din yana Busamai iskan bakinsa Yusuf kuma yana mtsawa bayana Fadin"Don"t Come close..Imu Bari..Allah zan yi Amai.."Cikin Dariyan keta yace"Aman nake son na gani.."Da gudu ya Bisa shi kuma ya kwasa Zuwa Tiolet dinsa ya Rufo yana sauke Numfashi Dariya ta kama Imran ya Dinga kyakyatawa Cikin mamaki Domin ayanayinsa sai kace bai Taba Dariya ba.
Kofar Tiolet din yaxo ya tsaya yana Fadin"Matsoraci Fito..Wasa ya kare..".daga ciki Yusuf yace"naki wayon...!
Imran yace"Baka yarda dani ba..? Yusuf yace"Kace Wlh ka bari..!
Imran na Danne Dariyansa yace"I swear na bari.."Sai alokacin Yusuf ya Bude kofar ya Leko da Sauri Imran ya Turo Kofar ya Jawosa suna Dariya gabadayansu kan gadon Imran din suka Fada Yusuf ya Mirgina gefe yana Fadin"Imu kazami..Matarka zata sha waharka..!
Imran yace"Daman shi tazo yi..!.
Yusuf yace"Wahalar..? Imran ya Zakuda kafada yace"Ofcourse..!.
Tashi Zaune Yusuf yayi yana Fadib"To Allah ya shirye ka..!
Imran yace"Ameen Shirin Allah bata Jigidan mata ba.."
Yusuf dau sai dariya yake kafin yace"Tashi..What is d Solution.."
Imran na kwance Rigingine yace"Baban Sagir zamu je muyi na mgana Shi zai nemi mutane su Shige maka gaba..!
Yusuf yayi shuru kafin yace"Baba Manu..?
Imran ya gyadamai kai Da sauri yace"Kana ganin zai yarda..? Imran ya Mike yana wani Tangadi kamar wanda yasha Giya yace"Kada ma yarda..Yagani..!
Yafada daidai Lokacin Daya abude Kofar Tiolet dinsa Yusuf ya Kallesa yana Fadin"Naga kana layi..Anya Imu baka Fara Kora Giya ko Tabar wiwi ba..?
Yana jinsa yamasa banza sai da ya Shiga Tiolet din kana ya leko yana Fadin'"Ban fara ba ammh Sai da Kafada naga ya kamata na Fara Tanque for ur Advice Bro..! Lokaci daya ya maida Kofar ya Rufe Yusuf yayi Dariya ya Jinjina kai yace"Imu...Imran...Ta bakin Abba yace Imran..Imran Rigima.."Daga haka ya Fice Daga Dakin zuwa nashi yasan Kila Safiya nata kiran wayarsa Daya barta adaki.




*Tanque Masoyana naji dadin yadda kuka karbi wannan Labarin I promise u bazan baku kunya ba..*



*Shakira...*
3/22/22, 23:03 - Ummi Tandama😇: *GIDANMU..!*
_(Our House)_
*Book1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️*


*DEDICATED TO:*
*Aisha alto(Sisinah)*
*Chubado muhammad(Uwar dakina)*
*Yahanasu Soupnass(Qawalli1)*
*Kausar salis(My jika)*
*Rahma Ladingo(Dota)*


*🅿?4*

"Ya fito Daga lacture din da suka shiga ta safe kenan yaji wayarsa Dake cikin Aljihun wandonsa na kara yana Fitowa da wayar yaga Sunan mai kiran nashi DAN ISKAN ABOKINA..!
Sai da yayi mirmishi Daya ga sunan mai kiran Saboda ya Tuna sanda Abun ya faru,Ranar suna zaune ashagonsa ne Sai Wayar Sagir din ta Fada cikin kayan Dinkin mutane Dake kasa akayi ta Nema ba"a gani ba sai ya karbi Wayar Imran din da Niyyar ya kira Wayarshi yana saka Lambarsa yaga Sunansa ya Fito da BANZAN ABOKINA..!
Galala yayi yana kallon Imran din Dayake kallon wani barayi Kamar ma baisan da Mutane a Shagon ba an ci Sa"a Ranar bai shigo yana zukan Taba nasa ba Daga dukkan alamu akwai abunda ke damunsa Ranar kuma bayaso Tattaunawa da kowa kuma baya son ya zauna agidan Shiyasa ya fito yazo shagon Sagir din ya zauna batare da ya Tankama Sagir din ba Duk da Tarin Tambayoyin daya rika Jefansa dashi.
Cikin Jin haushi Sagir yace"Nine ma Banzan ko..?
Batare da ya kalli Sagir din ba yace"Eh Ko kana da wani suna ne Bayan Banza..?
Sagir ya kada kai yana Fadin"Wlh nima sai na Rama..! Yafada daidai Lokacin da ya kira Wayar tasa yaji kaaranta nan cikin kayan ya Tafi ya Dauko Yana Fadin"Kaima sunan banzan daka sakamin zan saka maka..Me ma zan saka maka ne..?
Yafada da Sigar Tunani Batare da Sagir yayi aune ba Imran ya karbi Wayarsa Bayan ya taso Ya Goge sunansa da Sagir ya saka mai Ya maida masa da Da'n iskan Abokina kana ya mikamai yana Fadin"Gashi na Rama maka..!
Ya karba yana gani kafin yace"Kai..! Dan iska ne kenan da gaske..?
Imran ya Zakuda kafada Lokaci Daya yana Saka Duka Hannuwansa Cikin aljihun Wandonsa,ya Kama Hanyar Ficewa Daga Shagon yana Fadin"Eh ai Dan iska ne..!
Daga haka ya fice Daga Shagon bai Damu da kallon da Sagir ke Jifansa dashi ba,Bai yi mamaki ba Sanin Halin Imran kai fi Dayane shi Gashi bashi da Tsoro,baya karya domin ka so shi ko ka yabeshi baya jin Nauyin gayamaka Gaskiya komai Dacinta baida Boye Boye ko Kumbiya Kumbiya shi Mutum ne Street Forword baya Munafunci Ballatana gulma baya jin kunya yace yana aikata wani abu koda Zaka Tsireahi ne,Wannan Hallayar nashi suna matukar Birge Sagir dashi shi kanshi ya san Imran Jajirtattace ne kuma Jarumi ne sai dai abu Dayane ya kasa ganewa game dashi..Menene Takamemmen Abunda ya Faru dashi..? Domin in bai manta ba Imran din da kansa ya Fadamai abaya ya Tsani mai Shan Taba ko Warinsa Baya son ji ammh Saboda kaddaran Rayuwa yanzu yafi kowa jin Dadin Shanta aduniya.
Ko haduwarsu Allah ne ya Hadasu Tunda suka Dawo anguwarsu basu Taba Mu"amala da kowa ba sun kebe kansu iya su kadai Gidansu da suke zaune yanzu Babu Nisa da gidansu Sagir din gidaje kalilan ne Tsakani kuma ada asalin megidan Rasuwa yayi sai aka Siyar da gidan kila Lokacin ne su Imran suka mallaki gidan.
Tun Dawowarsu anguwan Sagir yake ganin Imran da safe in ya Fito Jogging,shi kuma lokacin bai Dade da Bude shagon sa Dake kofar gidansu ba alokacin bashi da wani yaro shi kadai ne yake Dinkinsa da keke guda Daya.
Akullum da safe yana ganin Imran Haka kuwa Allah ya Doramai kaunarsa Duk da basu Taba mgana ba ammh  Shi kanshi Imran din in yazo wajen Shagon na Sagir sai ya tsaya sun ma juna kallo kallon kafin ya wuce.
Watarana ne Imran din ya zauna yana Shan Taba abakin Shagon Sagir din Abunda ya kara bama Sagir mamaki bai Dace ace kamar Imran nashan Taba ba Daga ganinsa bai rasa komai na Rayuwa ba a kallon Farko ya Fahimci Imran yana da ilimi da Wayewar sanin Rayuwa haka kurum yaji yana so ya samu kusanci da Imran din Dalilin haka yasa Washegari da Safe da Imran din ya Fito Jogging Shima ya Fito har ya samu nasaran suka Bangaji juna kalma ta Farko da Imran ya Fara gayamai bayan sun gama karema Juna kallo
"Kai baka ganina ina Tahowa ne..?
Sai Sagir ya Ballamai Harara yana fadin"In na ganka sai me..? Hanyar ai bata gidanku bace..!
Sai kalaman suka bama Imran Dariya Har sai da ya Murmusa ganin haka yasa Sagir ya bashi Hannu yana Fadin"Sunana Sagir kaifa abokina..?
Kamar bazai bashi Hannun ba Saboda baya Bukatar wata mu"amala da kowa ko afarkon Rayuwarsa bai yi Abota ba ballatana yanzu da abubuwa suka Sauya sai dai ya kasa Kin bama Sagir din hannu Kamar Zuciyarsa na Jansa..Kaunarsu da abotarsu Daga Allah ne Mikamai hannu yayi yana Fadin"Imran..!
Daga haka bai kara cewa komai ba Sagir ne ya Dingamai Zuba yana Nunamai gidansu,Har da gayamai wasu Tarihin Rayuwarsa na Rasuwar mahaifinsa da kuma Inda yakezaune shi da Mahaifiyarsa harda matakin karatunsa Shidai Imran Jinsa kawai yake yana mamakin Sagir daga Haduwa dashi sai ya fara gayamai wani abu a kansa..? Yana so yace ya kyaleshi ya Dameshi ammh ya kasa Haka kurum yaji bazai iya Wulakanta Sagir ba
Duk iya kokarin Imran na kada Shakuwa ta Shiga tsakaninsa da Sagir sai da ta shiga,Shi sagir mutum ne mai barkwanci Da kuma Raha gashi bai da Zuciya da Fushi kome Imran zai Fadamai baya Damuwa Haka zasu Rabu Baram baram ammh Gobe zasu nemi junansu,Duk iya Kokarin Imran na kada Sagir ya shiga Gidansu sai da ya Shiga,Yaya yusuf ya sansa haka ma Maimuna da Abba,Sai dai har gobe Sagir bai san Asalin Labarinsu Koda ya Tambayi Imran baya Fadamai,Labarin da Sagir ya Dinga Bama Inna Amina Na su Imran yasa taji tana son ganinsa Ta shirya Sagir yakai ta har Gidan,Shi kuma Imran din Sagir ne ke jansa Gidansu da karfin Tsiya,Akwai wani al"amarin, da Allah ne kadai ya sani Duk da Imran na Zillewa ammh Sagir da Mahaifiyarsa basu Nuna sun gane ba sun Daukesu Tamkar yan"uwa Duk da Zamewarsa yana zuwa gidansu Sagir din in yajasa,Su shiga ya gaida Mama su kuma ci Abinci in Sagir ya matasamai barin ma in Tayi Abunda yafi so na Danwake.

Ajiyar zuciya Sagir ya Sauke,Yana kokarin Daga kiran ta yanke sai yabi bayan kiran Shima Gabda zata Katse Imran din ya Daga kiran yana Fadin"Kai dai banza ne Wlh..Kana ina ina ta kiranka baka Dauka ba.?
Yafada cikin Kaushin muryansa Wacce bata da Laushi Sagir yace"Dilla ina makaranta fa!
Imran yace"Ok..Gani kofar Shagon ka..yanzu zaka dawo ne ko na Shigo School din na Same ka..?
Da sauri Sagir yace"A"a gani nan Dawowa daman Lacture din Safe ce kadai garemu..Ka shiga ka gaida Mama kafim na Shigo..!
Shuru Imran yayi bai yi mgana ba Jin haka yasa Sagir yace"Dom Allah ka shiga ku gaisa..Mama nata Tambayanka kwana Biyu bata ganka ba..!
Imran yayi karamin Tsaki yana Fadin"Ba wani bata ganni ba kai ka mata wani Munafuncinka..!
Sagir na Dariya yace"Ka tsargu ne..? Tsaki Yaja kafin ya yanke kiran Yana Fadin"Ina jiranka kawai mallam..!
Imran bai yi Niyar shiga Gidansu Sagir ba sai dai bazai iya Juya alfarma da Kimar Mama ba Macece mai kirki da Dattako Yana Bala"in ganin kimarta Duk kuwa da irin yanayinsa.
Cikin Takunsa na Sassarfa da Kazarkazar dinsa ya Nufi Gidansu Sagir din yaran Sagir Dake Shagon suna Nuna sa da baki,suna mamakin yadda Oga sagir ya iya abota dashi Tunda suke dashi bai taba Musu mgana ba kogaishesu sukayi baya amsawa sai dai ya kalli Mutum ya kauda kansa Ko da zai zoSagir baya nan bazai Tanka kowa ba Ko Sallama acikinsa yake,Suna ganin Miskilan maza ammh wannan nashi Miskilancin sun Dangantashi Harda Wulakanci

Ya Dade tsaye a zauren gidansu Sagir din ya kasa Shiga yana Tunanin ya Shiga ne koya koma..? Sai dai yana Shirin juyawa ya koma yaji Muryan Maman Tana Fadin"A"a

Please Login or Register in order to submit comment