Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Cikkn Dakakkiyar Murya yace"Kai ina Zaku..? Cak suka Tsaya sun kasa gaba Ballatana Baya,Cikin Daure fuska da Yanayinsa yace"Tsayuwar Uban me kuke yi anan..? Ku zo nan..!
Yafada Cikin Kaushin Muryansa na koyaushe ba waasa.
Inteesar tazaro Ido Tana kallon Munari itama ita take kallo Kafin Tace"Sai muje wai Besty..!?
Munari tace"Tafiyarmu karin wani Babban Laifi ne..Wato Raini gwara Muje kawai Insha Allahu bazai mana Komai ba..!
Inteesar tace acikin Ranta"Tabdijam wazai je..?ya sumar dani..Dole ne na Sama ma kaina Mafita.
Da wannan Tunanin taji Munari ta Fara Janta suna Nufarsa Sai da suka kusa kawowa garesa Inteesar ta Kara Rike wayarta sosai a Hannunta Ta Danke Takalminta Dakyau Munari ba Zato kawai taji Inteesar ta Warce Hannunta ta Kwasa da Gudu Kamar Walkiya sai gata Bakin get Ta Tsaya Tana Haki Munari da Imran suka Bita da kallon Mamaki.
Kallon Imran Tayi ta Juyamai ido Kafin ta Rike kunnuwanta ta Marairaice Fuska Alamun ban Hakuri kana ta Juya da Sauri ta Fice Har da Gudunta Gudun kada ya Biyota..
Munari ta Tsure Tana Tunanin Kila yau Kafin su Abba su Dawo Ya Imu ya kusa Kasheta Ga Laifin Fitowa ga Laifin Inteesar Da zai hau kanta.
Ammh sai mai Data saci kallonsa Karo na Farko Tun Bayan Dawowarsu Kano Dataga  mirmishi Saman Fuskar Imran sai abun ya bata mamaki Inda yake Kallo tabi da kallo Bakin get ne inda Inteesar ta Wuce.
Sai abun ya kara bata mamaki Matuka ganinsa yana kada kai yana Mirmishi Haka kurum yaji Wani Nishadi da abunda Inteesar din Tayi duk da ba Komai ke basa Nishadi ba.
Munari ne taga kamar ya manta da ita yasa Cikin Rawan Murya tace"Ya Imu g..Gani..!
Sai alokacin ya kalleta Cikin Daka mata Tsawa yace"Da kika Fito ina Zaki..?
Munari taja Baya Jikinta na Rawa tace"Dama..Da..man ina so Zan Rakata ne..!
Wani kallo ya watsa mata kafin yace"Shiga Ciki kafin nayi kwallo Dake..!
Ai da gudu Munari ta Nufi Cikin Gida aranta Tana ayyana ai ta isa Barka da ya Kyaleta bai Tabata ba itama da Gudun ta Shiga Cikin Falon suka yi Kicibis da Anty Safiya ganinta haka yasa ta Tambayeta Lafiya nan take Labartamata Abunda ya Faru Safiya Tayi Dariya batace komai ba Illah Allah ya kyauta Domin Lamarin Imran Sai dai Allah ya kyauta kawai.
Haka Itama Inteesar ta Shiga Gida a Tsorace,Sagir da Mama suna Falo Sagir ke Cin Abinci suna Hira SAma sama da Mama ganinta yadda ta Shigo Duk a tsorace Yasa Sagir da Mama suka Hada bakin Wajen Tambayanta Ko Lafiya..!
Sai da Ta Zauna ta Sauke Tagwayen Numfashi kafin tace"Ya Sagir Ashe Abokin naka mai Shan Sigari Yayan Munari ne..? Tab ayau Allah ne ya Kwaceni ba Domin Abbansu da ya Sumar dani nima Domin na Lura Shaye Shayensa ya Fara Tabamai Kwakwalwa..!
Sagir ya Zaro ido Kafin ya ijiye Spoon din Hannunsa yana Fadin"Kai badai Imran ba..!
Tabe Baki Inteesar Tayi Tana Fadin"Oho ni ina nama nasan Sunansa Inga shi..!
Nan ta Fara basu Labarin Abunda ya Faru ta karishr da Fadin"Ina zan je Ina jin Besty Muna tana Labarin in ya Fara Duka sai ya Sumar da Mutum aiko na Gudo chan na barsa da Munari Allah Sarki Allah ya kareta Kada ya Huce akanta gashi su Abba sun Fita..!
Sagir Da Mama suka Kalli juna Cikin Mamaki kafin Sagir ya kada kai yana Fadin"Imran baya Shan komai sai Taba Inteesar..Kuma Lafiyarsa Kalau haka Hallitarsa yake yana da Zuciya ce sosai wanda Wani Lokaci Baya iya Contolling din Fushinsa..!
Mama ta Jinjina Kai tace"Koda ga Alamunsa..Yata ki Daina cemai yana Shaye Shaye kin ji ko..?
Inteesar ta Gyada kai alamun Taji Sagir ya Mike yana Fadin"Ita kanta Taban da kika ga yana Shanta abaya bai ma Santa ba..Kawai yanzu din waniYanayi ne na Rayuwa ya kawosa Haka..Zaman da kikaga nayi kiransa nake jira ya Kirani yau zamu je kwallon Ball Daganan na gane Ransa yana bace ne zai Shiga Mutane in Ransa ya baci baya Kadaice kansa Saboda Kada Zuciyarsa ta Buga ya Gwammace ya Shiga Cikin Hayaniyar Daya Tsana Daya Zauna Takaichin Abun ya illatashi..!
Inteesar ta Jinjina kai kafin Tace"Kai Shi dai Matarsa ta Shiga uku..Allah yasa ma ya Samu mai auransa Mama..!
Daga mama Har Sagir sai da sukayi Dariya Mama Tace"In bai samu mai Auransa ba sai na bashi ke..!
Inteesar ta Kwalolo ido kamar Taga Wani abun Tsoro Lokaci Daya Ta Dafe Kirji Tace"Ni kuma Mama..?wlh ko Narasa mai sona Sai dai na Mutu ba aure bazan Taba auran wannan ba Tabdijam. Allah na Tuba Mama bari wannan mganar kada yan Ameen su Amsa..!
Ta karishe Fada Tana wani Dakuna Fuska Mama Dariya ta sakamata Shima Sagir din Dariyan yake ya Fice yana Fadin sai ya Dawo Mama ta Bisa da adawo Lafiya.
Wannan mganar da Mama Tayi duk sai ta Damu Inteesar Bini Bini ta Tuna ta yanka tsaki afili Tana Fadin Allah ya Tsareni da auran wannan Mara Mutumcin..!
Har tayi wanka Tayi Sallar mganriba ta Dibo Abinci tazo Tana ci Tana Tsaki Mama na lura da ita batace mata komai ba sai Dariyan Wauta irin ta Inteesar take Daga wasa sai ta Dauki abun da Gaske kadan taci Abinci sai ta Sha Tea kawai Saboda Zata kwanta ne.
Washagari da Daddy ya kirata da Safe Abun na Ranta sai da ta bashi Labari Komai Daya Faru Harda mganar Mama ta Karishe da Fadin"Daddy wai kaji fa Mama..Dan iskan zan aura mai Shan Sigari gashi Daddy Mahaukaci ne Wlh Duka fa wai yake har sai ya Sumar ni Wlh yanzu ma Tsoron Zuwa Gidansu Munari nake Daddy..!
Daddy na Dariya yace"Intee Daddynta..Ki daina Cemai Dan iska kin ji ko..?ko bakomai Ai Yayan Kawarki ce kinga ai yayanki ne kuma ba kyau Raina na gaba dakai ki Daina Saboda in ita Munarin taji kina cewa haka bazata ji Dadi kina Zagin Yayanta kamar yadda kema Bazaki ji Dadin azagar miki Yaya Basheer din ki ba..!
Inteesar ta Tura baki Kamar Yana ganinta Tace"Allah ya Tsare Ya Basheer dina ba D'an isk..!
Umma Dake Tsaye gefen Daddy Tana Hadamai Tea a Saman Dining yake Zaune Tashin su kenan zasu yi Breakfasat ya Kira Yar Lelen tasa Wayar Tana Handfree ne Umma Tana jin komai ita ta Katse Inteesar bata karisa ba Tace"Inteesar meyasa bakya jin mgana ne..? Ana miki Fada kina kara Sakarci..Ki kiyayi kanki fa Kina cemai D'An iska Tsaranki ne..Kince Yayan kawarki ce..Kuma kince Abokin Sagir ne Shine zaki Zauna kina Kiransan Dan iska mara Mutumci..? Haka muka Koya miki kiyi ma na gaba Dake..?
Ta Karishe Fada Cikin Bacin rai Daddy bai ce komai ba Sanin gaskiya ne gwara arika Gyarama Inteesar din in Tayi wani abu.
Sai dai kallonta yayi yana Fadin"Salaha ki mata a Hankali don Allah..!
Ko kallonsa Batayi ba ta Cigaba da Fadin"Ki Daina wannan Sakarcin ke ba yarinya bace yanzu..Ina so ki Sani kada mu rika Zargin mutane in bamu san komai akansu ba kada mu yanke musu Hukunci..!
Inteesar da Jikinta yayi sanyi Karo na Farko tace"Bazan Kara ba Umma..Kiyi Hakuri..!
Jin haka yasa Umma ta Sasaauta Tana Fadin"Yauwa ko kefa Yar Umma da Mamanta..Daga yau in kika gansa ki Rika gaishesa kin ji ko..? Duk wanda ya Girmeka yayanka ne Balle ma Yayan Kawarkice munari kikace..!
Inteesar ta Tura baki Tana Fadin"ni fa Umma tsoro nake ji kada ya Dakeni..kin jifa Munari tace yana Duka Har yana fa Sumar da Mutum..!
Ba Umma ba Harda Daddy sai da yayi Dariya Cikin Dariyan ne Daddy ke Fadin"Bazai miki komai ba..Daga gaisheshi sai duka..? Kada ki Damu kin ji Intee Daddy kedai ki Zama mai Ladabi da Natsuwa a Duk inda kika je..!
Inteesar tace"Insha Allahu Umma..!
Umma Tayi mirmishi Tana kallon Daddy tace"Allah yayi miki albarka ya Karatun..? Ina maman taki..!?
Inteesar tace"Alhamdulillah Umma..Mama kuma Tana Lafiya Tana Tsakar gida..!
Umma tace"Badai aiki take yi ba kina kwance.?
Da Sauri tace"A"a Wlh Nagama Duka ayyukan tana dai Zaune ne Tana Shan Hantsi suna Hira da Ya Sagir..!
Umma ta kadai kai Tana Fadin"Naji Dadin haka Allah ya bada Sa"an karatu Sai a kula Sosai kin ji ko..?
Inteesar tace"To Umma..Bama Daddyna Wayar..!
Daddy Dake gefe yace"Gani nan Inteen Daddynta..!
Inteesar Tayi Dariya kafin Tace"Daddy ina ya Basheer ya manta Dani kwana Biyu ko..?
Daddy tace"Injiwa..? Aiki ne yayi masa yawa ammh Zaki jisa da kuma Rashin Lafiyar Matarsa...Su Abiden ma Jiya suka koma suna nan Tare Damu.."
Inteesar tace"Wayyo Har yanzu Jikin nata..? Allah ya bata Lafiya Daddy wai Ciki ne da ita..!?
Umma Dake Turama Daddy Mug Din Tea gabansa ta Rike baki Daddy na Rike Dariyansa yace"Eh haka akace waya gayamiki..!?
Inteesar tace"Ya Basheer ya gayamin..!
Umma tayi karaf tace"bana son Shiga mganar manya Intee..!
Daddy shima ya karbe yana Fadin"To itadin me kika maida ita..? My Intee is Not a Small Bby kamar yadda kike Tunani..!
Umma tace"Yau kuma..? Ka manta kai ke Fadamin Kullum Intee yarinya ce..!
Daddy yace"Eh ina nan akan bakana Sai dai ba yarinyar da kike Tunani ba..She know wht she is Doing..!
Baki Umma ta tabe tace"Allah ya kyauta..!
Lokaci Daya jan Daya Daga Cikin kujerun Dinng din Dake kusa da Daddy ta zauna ,Inteesar Dake Jinsu a Waya aranta ta Murmusa tana Fadin Daddy bazai Saki ba ita kuma Umma bazata Daina Jayayyaba.
Cigaba da mgana sukayi da Daddy gabda Zasu yanke kiran Take Taambaysaa Daada ya jikinta..?
Daddy yace"Ta samu Sauki Sosai Last Week naje na Kara Dubata..!
Inteesar Tace"Allah ya kara Lafiya..Ka gaisheta Daddy..!
Yace"Zataji ki kirata Da kanki mana..Tana Tambayanki indai naje Dukku..!
Inteesar tace"bani da lambarta a wannan Wayar ka Turomin Daddy..!
Cikin jin Dadi yace"Ok zan Turo miki..Bye zamu Breakfast ne sai Zuwa anjuma zan kiraki..!
Inteesar ta Shagwabe Tana Fadin"Wait Daddy..Yaushe zaka zo..! ? Tunda kuka kawoni Almost 4 to 5 weeka ba wanda ya kara Zuwa ya Dubani..?
Daddy yace"Sorry My Angle..Rashin Lafiyan Daada yasa baki ganni ba..Ammh ki saka Ganina Next week in ban samu Zuwa ba Basheer zai zo in kuma Munzo Tare shikenan..Akwai wasu Karafan da Zamu zo mu siya anan kanon..!
Tsalle Intee ta Daka Kafin tace"Plz Come Daddy Don Allah..!
Cikin Farinciki yace"Insha Allahu.."
Daga haka suka yanke kiran Bayan sunyi Sallama Umma na Jinsu Tana ta Kurban Tea dinta Lokaci Daya tana Hadawa da Soyayyan Dankali da Kwai Kala batace ba Shima suna gama Wayar ya Fara karyawa Cikinsu ba wanda ya kara mgana Har sai da suka Kamallah.
Inteesar na gama Wayar ta Fita Tsakar Gida Tana Gayama Mama Mganar zuwan su Daddy Mama na kan kujera yar Tsugunno ta Fadada Fara"arta Tana Fadin"Kai masha Allah..Allah ya kaimu Allah ya kawosu Lafiya..!
Intee ta amsa da Ameen Tana Fadin"Mama ya Sagir ya Fita ne..?
Mama tace"Eh yanzu ya Fita Kamar an Kirasa a waya ne..!
Kai ta kada mata Kafin ta Koma Cikin Dakin.
Ba Dadewa sai ga Munari Tazo Dauke da Tarin littafai nan Waje ta Fara Tsaayawa suka Fara gaisawa da Mama kafin ta karisa Ciki,Rumgume juna sukayi da Inteesar suna Murna kafin su Zube kan gado suna Dariya Abun na Ran Inteeaar Cikin Zolaya tace"Besty ya kika kare da wannan yayan naki..?yama sunansa..?
Munari tace"Au yau kuma Sunansa kike Tambaya..? Ai da D"aniska mara Mutumci kike kiransa..!
Inteesar sai taji kunya Cikin Sanyin Murya tace"am sorry Besty..Nasan ban kyauta ban kara kiransa da wadanan sunayen Gayamin sunansa Allah dashi zan Rika kiransa..!
Munari tace"Imran muna kiransa Ya Imu..!
Da Sauri Inteesar tace"Yauwa Ya IMRANN..ya kuka yi Dashi..?na dawo gida ina ta Tunanin ko Kila jiyan ya Sumar Dake da duka..!ta Karishe Faada Tana Dariya Duka Munari ta Dakamata Abaya Tana Fadin"Muguwa ba Mutuwa bace kin manta ne ba Suma da kika gudu kika barni SAi yanzu ne zaki Tuna dani..!
Inteesar na Dariya tace"To sai na Tsaya..? Wlh ban tsayawa Gudu ya Zama Dole Besty nidai gayamin Allah yasa bai Dake ki ba..?
Munari Tace"Baimin komai ba Wlh..Sai yace na Wuce Cikin gida kafin yayi Kwallo Dani..!
Atare suka saka Dariya Har da Tafawa nan suka Cigaba da Hiransu Munari na kara bata Wasu Labaran Halin Imran Inteesar taji ai yama Wuce yadda Take Tunaninsa A Tsegaranci Shi lamba Dayane.
Ba su Fara karatun ba sai da Inteesar ta Zubo musi Dambun Nama ta Dauko musu Lemo suna Ci suna Korawa da Lemu suna Karatu ganin haka yasa Mama tace suyi Karatunta ita Zat Dafa abincin Ranar.
Haka kuwa akayi mama Tayi musu Danwake da mai da yaji da salad,Sukaci sosai Harda Santi Munari tace"Ya Imu nasan Danwake sosai ammh in nayi agida sai yace ban iya ba..Mama tafi ni iyawa..!
Mama na gefe tace"Ai yanzu ma Sagir yazo ya Daukan musu suna Shago zasu ci..Ni kaina Saboda shi nake yawnn yin Danwaken..Kuna Cikin Daki Dazu ya Shigo muka gaisa yake Cemin Mama ina Danwake kwana Biyu..? Shine nace yasha Kuruminsa yau Saboda shi Zan yi Danwaken..!
Munari ta Zaro ido Tana Fadin"Ammh baisan muna nan ba ko mama..?
Mama tace'A"a ina ma ya wani Damu da ku..Bai ma san kuna nan ba inaga..!
Ajiyar zuciya Munari ta Sauke Inteesar na mata Dariya Sanda ta Fito Gida Bata gansa ba Abba Kadai Tayi ma Sallama Anty Safiya ma da Ya yusuf suna Shashensu basu Fito ba.
Munari na Tare da Inteesar har yammah,Kana Tayi Shirin Tafiya Inteesar ta Sako Dogon Hijabinta Maroon wanda Anty Hauwa ta Dinkamata Mai Hannu sai Fuskarta Tayi kyau sosai.
Munari tayi Sallama Da Mama Suka Fito Tare da Inteesar Bayan ta Diban mata Dambun Nama dasu Cake da Donot,Dambun naman ya kare Cake din na Sauran kadan Dayake ba ita Kadai take ci ba,Mama bata cika ci ba ita da Sagir ne sai Munari Da takan Diba su tafi Dashi makaranta.
Koda suka Fito basu ga kowa akofar Gidan ba,Suna Daga Chan Cikin Shago su kuma suka yi gaba zuwa Hanyar Gidansu Munarin Har gida Inteesar ta Raka Munari ta Shiga suka gaisa da Abba munari ta Nunamai Abunda Intee ta bata yana ta Godiya da Saka albarka Wanda Inteesar ke jin Dadin hakam Har ga Allah in ta gansa sai Taji kamar Tana Tare da Daddynta ne Tana ganin a mgana da wasu abubuwan suna mata kamanceceniya da Juna sai dai shi Abba yafi kama da Alkali Hamisu ne su kuma su Daddy sun Dauko Fuskar Daada ne.
shashen Anty Safiya suka Shiga intee ta gaisheta tadan Zauna a Shashen Antyn Safiya suna Hira kafin ta Fito Munari ta Rakota Har Bakin get Taci Sa'a Imran baya Gida.




*Ina godiya Masoyana na Nesa dana kusa Masoyan Imu da Intee Suma sunce suna Godiya sosai Allah ya saka da alheri..*




*Shakira...*
3/22/22, 23:05 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️*



           *🅿?20*

Inteesar da Munari na wucewa Imran ya Fito daga cikin Shagon Sagir ya Tsaya a kofar Shagon ya Fito da Sigari Guda Daya ya kunnata ya Cigaba da Zuka yana Fesar da Hayaki.
Sagir ne ya Fito Daga Cikin Shagon Nashi Ya isa kusa da Imran yana Kallonsa Cikin Wani yanayi kafin ya Rausayar da kansa yana Fadin"Yau Kuma a waje ake son Busa Hayakin..?
Imran bai ma nuna yasan da Wanzuwar Sagir a wajen ba Ya cigaba da Busa Hayakinsa,Sagir ya kara Kallonsa yana Gyada kai kawai.
Har ya Fidda rai da zai bashi amsa sai yaji yace"Kawai yau naji ina son na Busata a waje ne..!
Sagir yace"Dahaka kake yi da baka Takurama yaran Shago na ba..kasan dai Tun Fara zuwanka Shagon nan Kake Takura musu ko..?
Imran ya wani Mele baki Lokaci Daya yana Sauyama Sigarin nasa Hannun Zama kafin yace"I know..!
Sagir ya kallesa Cikin mamaki kafin yace"Ka sani kace..?
Imran sai da ya Fesar da Hayakin Daya Busa kana ya Bude baki yace"To ni zan Hana Zuciyarsu yin Abunda Tagama Da Gangaar jikinsu ne..Ban isa na sa su soni ba..Ban isa na Saka musu Ra"ayina ba sai dai na Isa na Hana su yin Abunda ni zai zama Takura gareni..!
Sagir na Shirin mgana Imran ya Katseshi da Fadin"Har da kaima ai na Lura kamar na Takura maka ko..?
Sagir yace"Ai ni ba tun yanzu ba ka Dade kana Takura ma Rayuwata..!
Imran ya tsaki karamin Tsaki yana Fadin"Halin Dan adam kenan yanzu da ban rika zuwa ba sai kace naki Karban mganarka yanzu kuma ina Zuwa kana neman gayamin mgana..!
Yafada Cikin nuna jin Haushinsa Da Sauri Sagir yace"To daka karbi mganata Ka fara koyan Sana"an ne. ? Tunda ka Fara zuwa baka komai sai dai ka Zauna kana bin kowa da kallo in ka gaji ka Busa Hayaki gayamin me ka Koya..? Imran ya saki kayattacen Mirmishin da yakan Dade bai yisa ba
Kafin ya bude baki yace"Waya Fadamaka ban fara koya ba..? Tun yaushe ai ma nayi nisa da Fara koyon Dinki!
Sagir ya wani kalleshi a karkace kafin yace"Bangane ba..? Ta ina ka Fara Koyon..?me kuma ka Fara Koyan..?
Imran yace"Abunda Kake koyama Mutane mana Inace ba yanka Dinki bane da Hawa keke da Dinkawa bane..?
Sagir yayi Dariya yana Fadin"Sannu Mallam Riga maasllaci To ai ba Haka kaga kowa na Koyon Dinkim ba balle kace..!
Imran yace"Ai ni sunana Imran..Kuma Dabam nake da kowa..Kaganni nan da Kwakwalwata nake Koyon Abu bana da Bukatar Rubutawa ko Gwaji..!
Sagir ya kallesa kafin yace"Uhm..wai me ma ka karanta ne a makaranta..?
Imran na kallon Sagir Cikin ido kafin yace"Daman na taba Fada maka nayi Karatu ne..? Sagir yace"Ko baka Fadamin ba yanayinka da Tsarinka na Masu Ilimi ne sai dai in baka son Fadamin..Dama nine na Daukeka Abokina kuma Dan"uwana kai baka Daukeni ba Imran..!
Sagir ya Fada Cikin Wani yanayi Da Imran yaji wani iri,Baki ya Mele kafin ya Saki karan Sigarin Dake hannunsa Data kare,Ya saka Rufaffan Takalminsa ya Take ta Kafin ya Laluba Aljihun wandonsa ya Dauko Wata ya saka Lether ya kunnata Sagir Duk yana kallonsa Kai ya Girgiza kafin yace"Don Allah ka Rika Dagama Shan Sigarin nan kafa..Ba Saboda Komai ba sai Saboda Lafiyarka Imu.!
Imran yayi kamar bai jisa ba sai da ya Busa Hayakin yaji sa ya ji Daidai kana ya Fesar da Hayakin har zuwa Fuskar  Sagir wanda ya kauda kai yana Fadin"Bana son Wulakanci fa..kan Fuskatane wajen Fesa Hayakin Sigarin naka..?
Imran ya karkace kai yana Fadin"Kila..!
Daga haka ya Tsuke Bakinsa Sagir ya Bata Fuska yana Fadin"Au kila ko...?Nagode ai ba sai ka ganni ba ballatana kamin Wulakanci..!
Ya juya zai koma Shagonsa yaji Muryan Imran din yana Fadin"Ka Tambayeni Mena karanta a makaranta ko..?
To Accounting na Karanta Nayi Degree na Farko Har zuwa Master..!
Sagir Daya Dawo da Sauri lokaci Daya yana Zaro Ido Cikin Mamaki yace"Are u Serious..!?
Imran bai bama Tambayarsa Muhimmanci ba yace"A University of Ibadan IU,nayi duka Karatuna..!
Sagir da mamaki bai gama Sakinsa ba yace"To meyasa kake Zaune baka Nemi aiki ba..? Ko baka samu bane..?
Imran ya wani kallo Sagir a Dakune kafin yace"Nayi aiki da Gt Bank Reshen Jahar Lagos a baya..!
Sagir ya kara Sandarewa da mamaki Baki ya Bude Kafin yace"Kai din nan Ashe ma"aikacin banki ne Ban taba Sani ba Imran..!
Imran yace"Bagashi ka sani ba yanzu..Sai me..?
Sagir ya Dafasa yana Fadin"To meyasa ka bar aikin ka..?kenan in Hasashena ya Zama gaskiya ku a Lagos kuke kuka Dawo nan da Zama..!
Imran ya kalli Cikin Idanuwan Sagir kafin yace"Eh..!
Daganan bai kara cewa komai ba ya Cigaba da Shan Sigarinsa yana Fesar da Hayaki Sagir da ke Tsaye yana  kallonsa Cike da mamakinsa Sosai akan Fuskarsa Kafin ya kara Gyara Tsayuwa yana Fadin"Ammh Tambayar Data Dade tana DAmuna ban samu amsarta ba..Shin Meya Baro ku Dachan Lagos din kuka Dawo nan..? Kuma meyasa kabar aikin kazo nan ka Zauna baka da aiki sai Shan Sigari..!
Imran kamar bazai ce komai ba sai chan yace"Is a long Story..!Kila zaka san Dalilin Watarana Ammh Not Now..!
Sagir ya Bude baki zai yi mgana kenan ya hango Inteesar Tana Tahowa Cikin Natsuwarta Kura mata ido Yayi yana Tunanin kila Daga gidansu Imran Take ganin inda Sagir ya Shagala da Kallo ne yasa Imran Shima ya Waiga yana kallon inda yake kallo,Daidai Lokacin da Inteesar din ta Iso kofar gidan Tana Dago kanta sai Cikin na Imran kamar ko yaushe alokaci Daya Zuciyoyinsu suka Buga alokaci Daya gaban Inteesar ya Fadi Ras Data ganshi,Abun kuma Daya kara Bata mamaki ganinsa Dauke da Sigari yana kallon Cikin Idanuwanta yana Zukan Hayakin yana Fitar da Hayakin ta Hanci ta baki sai ta kara Jinjina al"amarin Tana Shirin Saka Hijabintata Toshe hancinta Ta Tuna da Abunda ya Faru sai tayi Saurin Maida Hannunta da Gudu gudu ta Shige Cikin Zauren Gidansu Sagir Tana maida Numfashi.
Imran ya Bita da kallo Cikin mamaki kafin ya Saki karan Sigarin Hannunsa Zuwa kasa ya saka Takalminsa ya Take ya murjeta Lokaci Daya yake Fadin"kalli yarinyar chan saboda Ta Rainani..In ta ganni tana guduna...Kamar Taga wani Dodo. ?
Sagir Dayake Lura da abunda ya Faru yace"Ba Dole ta rika Gudunka ba..Taji Labarin kana Sumar da Mutun indai ya Shiga Hannunka..!.
Imran yayi Tsai da idanuwansa da suka Kamkance suka Sauya Launi Saboda Busa Hayaki yace"Ina sumar wa..? Uban wa na taba Duka Har na Sumar dashi..?
Sagir yace"To ni ina zan sani..?Nima ita ke Fadamim..!
Imran da Ransa ya Fara Baci yace"Mganar banza..!
Daga haka kawai ya juya cikin Takunsa na Sassarfa da Jarumta ya Fara Tafiya Haka kurum yaji Zuciyarsa na tafasa Sagir ya Bisa da Kallon Haka kurum yake Tunanin Hanyar da Zai Taimakama abokinsa wajen Dawo da Rayuwarsa ta Baya ta Inganta yabar wannan Rayuwar Dayake Ciki.
Shikuwa Imran koda ya karisa Gida ko Gani Dakyau bayayi saboda Tsabar Bacin rai,Yana Shigowa Falon ya Fara Kwalama Munari kira Cikin Tsawa da Hargowa.
Abba na Tsaye a Falon yana gyara Zaman Hulan kansa da Casbaha a Hannunsa,Fitowarsa Daga Dakinsa kenan ya Dauro alwala yana Jiran Yusuf zasu tafi masallaci Imran ya Shigo Cikin Fushi shiyasa bai ma lura da Wanzuwar Abba a falon ba.
Yusuf ya Fito Daga Shashensu Safiya na Bayansa Cikin mamakin wannan Gigitattaciyar Tsawan da Imran ke amfani da ita Wajen Kiran Sunan Munari Daman shima yana Shirin Fitowa ne su tafi masallaci da Abba.
Ya yusuf ne Da suka Bayyana a Falon ya Kalli Imran yana Fadin"Lafiyanka..? Me Munarin Tayi maka kake mata wannan kiran..?
Ko Kallonsa bai yi ba illah Daga Murya Da yayi yana Kallon Safiya yace"Where is She..?
Cikin Launin Bacin Ransa da Tuni Muryansa ta Sauya Cikin Sanyinta Tace Tana Kallon Yusuf"Tana Dakinta..!
Bai Tsaya ma Mgana ba ya Fara Taku Zuwa Kofar Dakin Munarin yana Fadin"Wlh kinjin Rantsuwa Daya ko..Kika bari na Taka kafata Daga Inda Nake baki Fito ba.. sai na Tabbata da na Miki Dukan da Ba suma zaki yi ba sai kin ji Kamshin Lahira yadda Zaki ji Dadin ba wata Labarin ina Sumar da Mutane..!
Yafada Cikin Fushi Lokaci Daya Jijiyoyin Kansa suna Tashi Radau Kirjinsa na wani Tashi yana komawa Yusuf ya Kallesa ya koma yana kallon Abba Da yayi Tsaye kawai yana kallon Ikon Allah.
Munari Da Tun Fitowarta Daga Tiolet Taji kiran da Imran yake mata Tasan Yau Kashin taya Bushe Tsoro ne ya Hanata Fitowa,Tana Tsaye Tana Rawan Jiki dana Zuciya Jin abunda yace ne yasa ta Ta Sadakar ta Fito Domin ta Tabbata Zai aikata Abunda yace Ba wanda ya Isa ya Hanashi Mganar sa kamar Kaifi Tokobi ne in yasara sai tayi yanka..
Cikin karkarwan Jiki ta Fito Daman Kofar tana Bude ne tun Shigar ta bata Rufe ba Haka ta Hade Hannayenta Saman Cikinta Tana Fiki Fiki da ido Har sun Fara kawo Ruwa Saboda Tsoro Tana Hango Kanta Bayan ta Shiga Hannu Ya Imu yana Kwallo da ita kamar Yadda yake Fadi.
Bata gama Karisowa gabansa ba ya Daka mata tsawa Cikin Kakkausan Murya yana Fadin"Kina jina ina kiranki Kina banza Dani Don Ubanki..?kin Raina ni ko..?Ko ni Sa"an Wasan ki ne.?
Ya Karishe Fada yana Nuna ta da yatsa Lokaci Daya yana jin kamar yasaka Kafa ya bata wani Bugun da sai ta Suma nan take..
Munari Data Rude ai sai ta Zube gabansa ta Fashe da kuka tana yi tana Kamkame jikinta Waje Daya.
Abba Dake Tsaye ya Daga Baki yace"Imran kada ka Daketa Nace..!.
Ammh Imran bai ma san Abba na Mgana ba Bacin rai ya Rufemai ganinsa da Jinsa.
Cikin Kufuluwa ya Kalleta yana Fadin"Wannan kukan naki bazai Hanani Sauya miki kammani yau acikin Gidan nan ba..Wane ne ya Baki Izinin kawo wannan yarinyar Gidan nan..? Kuma Waya baki Izinin da Zaki Kulla kawance da ita Da Har Zaki Rika bata Labarai akan Gidanmu..? Iskancin naki ma bazai tsaya kan Wanda kika Raina ba sai kin Tsallako kaina ko..? Saboda ban taba Yima Fuskarki Dameji ba Shiyasa Har kike da Bakin Fada ma Wata Mara Kunyar yarinyar Chan ina Duka Har sai na Sumar da Mutum ko..?
Ya Karishe Fada da Tsawar data Gigita Munari Ta Fara mgana Cikin kuka."Ni..Ni...Wlh..Ban..Fada..mata ko..!
Ai bata kai karshen mganarta ba ya Daga Hannu ya Wanketa da wani Lafiyayyan marin da sai da ta Kife ya kuma saka Kafa yayi kwallo da ita ta Fadi chan

Please Login or Register in order to submit comment