Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Muje kici abinci, Allah kaman bakya da lafiya" yunwa kam hartaci ta cinye ta


"Okay" yayi dan clap guda daya

"Good girl"
Basu karasa sauka daga saman stairs din bah aka kawomai wayar shi


"Hello" matsawa tayi dan ta bashi wuri yaji dadin magana sai ya bi inda tayi


"What do you mean Alfie? ta yaya za'ayi ta sani in ba wani ya fada mata bah" ya dan nuna damu a fuskar shi


"Tun jiya ta taho?"
"Ya kamata ace tana gda tun jiyan ai"

Kashe wayar yayi yana sauke numfashi

"Komai lfy" ta tambaya

"Yes Husna komai perfect, Granny ma dina zata iya shigowa a kowani lokaci, ina fata kin shirya haduwa da ita"

Ta danyi murmushi, shima kuma yayi dan yana son kakar tashi taga Asma'u


Saidai hankalinshi ya dan tashi daya ji cewa tasan sarkar da mamanshi tasa ayi mata an sace


Ya fadama PA dinshi Alfie ya nemo mai sarka irin wannan,saidai har yanxu ba'a dace bah,gashi kuma tana kan hanyar dawowa.









⚜B.W.AπŸ–Š
⚜BRILLIANT WRITERS ASSOπŸ–Š


πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI,
BY KHALEESI,
& NOBLE JUDGE.
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’



1⃣9⃣.


"Hajiya mun iso gdan" glass din motar ta sauke tana kare ma gdan kallo


"Banyi mamaki bah ai" tayi tsaki sannan ta maida glass din


Bude mata kofa akayi,yayin da ita kuma ta sauko kafa daya kafin daya, ta rufe idanu da manyan shades πŸ•Ά,


Sai da aka yi sallama sau biyu kafin kaka ta fito daga cikin gda


"Ince dai lfy koh?" Ta fada idanu waje😳,

Tana jingine jikin daya daga cikin motocin guda biyu SUV bakake da suka zo dasu


"Ke kadai ce acikin gdan koh barawon na ciki"
Kaka na jin haka tasan wannan ba bakuwar arziki bace bah


"Malama kin tabbata ni kike nema,kodai batan hanya kikayi"

Hajia turai tayi dan murmushin mugunta


"Babu wani babanci koda ba keh nazo nema bah, tunda fakiriya ce ke nasan baki da wani mutumci balle daraja"

Kaka ta bar bakin kofa tana kare ma matar kallo

Kayan jikinta kawai abin kallo ne,balle azo ga yankune da agogon dake hannunta


"Ka kira min yan sandan" ta fada ba tareda ta kalli wanda take mah magana bah


Nan kaka ta rude, mamaki ya kau firgici ya maye gurbin shi


"Yan sanda kuma baiwar Allah meh namiki, ina ga rasulu" ta dora hannu saman kai tana daga murya


"Aikin banza aikin wofi,har bakauyiya, talaka irin ki zata sani gaba tana ma kallon raini, kin isa koh an fada maki anyi ki ne"

Hajia ta cire glasses din tana nunata dashi


"Ke yau a cell zaki kwana"

"shi kuma koh waye naki da yazo har gdana yasa hannu ya dauki abu na, ze san Hajia Laila Turai abar tsoroce"


Ta juya zata shiga mota,Kaka ta duka tana rike mata kafafu, dan yanxu ta daina pretending bata san akanwa take magana bah


"Kiyi wa Allah kiyi wa annabin sa, ki saurareni" hajia ta hambareta


"Kar ki kuskura koh a mafarki ki tabani"

Hajia Turai na shirin shiga mota mlm Musa Wada, mahaifin Asma'u ya karaso wurin


Ganin abokiyar zaman mahaifiyar shi da guiwwa kasa tana roko ga hawaye a idanunta,sai yayi kanta yana son ya tadata tsaye


"Wannan ne wanda muke nema?" Ta fada tana nuna shi up and down

Daya daga cikin masu tsaronta yace Aa


"Da shine sai ince yaushe aka fara daukan marasa galihu suna mun aiki a gda"

Tayi tsaki tana gyara zamanta a cikin mota

"Salamu Alaikum baiwar Allah"

A daidai lokacin kuma suka fara jiyo jiniyar motar police



"Koh dan girman sunnan sarkin sammai da kassai dake cikin sallama,yaci ace kin ansa"
😠, ta bishi da kallon up & down,wannan da kanshi yasa sunan shi cikin blacklist dinta,dan haka ta sauko daga motar


"Kaima dangin tsiyan ne koh"
Kafin yace wani abu ta cigaba


"In ba haka bah meh zesa ka a cikin harkar da ba taka bah, makarantar allon basu koya maka haka bane bah"


Ajiyar zuciya yayi dan yau ya hadu da ikon Allah,

"Wannan mahaifiya ce a wurina" ya duka yana kokarin dago da Kaka

"Good kaima sai a hada da kai, kuje can ku karata,dama babu inda yafi dacewa da talaka sai kurkuku"

Zata shiga mota ya mike tsaye

"Ina fata bada kudi kawai kike takama bah harda gsky da kuma hujja, dan babu wannan babu wanda ya isa yayi maka koh kallon banxa"


A karo na biyu da taji bata san mutumin nan koh kadan,


"Ba uba** daya isa yasa Turai furta abinda batayi niyya bah"

"A'uzubillah"ya dan girgixa kai alamun tayi ba daidai bah


"Kila ke basai kin fada bah,amma su sai sun fada kafin suyi yun kurin wani abu"

Yan sanda ne mota guda suka karaso wurin,

Ran hajia turai in yayi dubu ya baci, dan haka tace polisawan suyi aikin da aka kirasu suyi


"Ni citizen din Nigeria ne, haifaffen dan kasa, indigene din Kaduna state, constitution kuma ya bani right"

😑😑😑😑,haka take kallonshi, tana maida numfashi dai daya

"Ya bani daman sanin laifin da ake tuhuma ta dashi, kuma yace ina da damar da zan bi hakkina in akaci zarafi"

Ya kalleta da kyau

"Toh ki tabbata hajia baki tada hankalin Family dina akan false accusations bah, dan nima ina da damar da zanyi karaki"

Kaka sai kokarin hanashi magana takeyi, amma yaki yin shiru, sai dora hannu take saman kai tana rawa a inda take tsaye


Yan sandan basuyi yunkurin taba Mlm Musa da Kaka bah,dan sunji maganganun shi da kyau da kyau,


Koda kuwa zasuyi fin karfi,bazasuyi ga wanda yasan hakkin shi bah


"Inspector Gaddafi ke magana dakai"
Ya matso kusa da shi,


"Ana tuhumar ku da boye barawon da yaje gdan Hajia Laila Turai ya saci set din sarka da yan kunne,meh yan hannu da zobuna"

Ya tsagaita kafin ya cigaba

"Kudin wannan abu dana lissafo yakai dala millyan 9 da dubu dari bakwai, dallar amurka nake magana akai"


Jama'ar da suka taru a wurin suka hau salati kowa na fadan Albarkacin bakin sa


"Sunan Barawo Salisu Auwal Wada" ya mika ma Baban Asma'u takardar data bada daman a cafko shi


Warrant din ya rike beh karanta bah,dan jikin shi bah karamin sanyi yayi bah, haka zalika Asma'un shi ta fado mai a rai

Gsky yau yayi nadamar boyewa kansa gskyr al-amarin,gashi yanxu yaja wa yarshi


"Ku shiga ku duba,in kun ganshi, sai ku tafi dashi, in baku ganshi ba kuma kunyi manah kazafi"

Inspector ya juya ga Hajia Turai data sandare wuri daya,dan mutumin yana san nuna mata iyakar kudinta,ya tozartata a bainar jama'a


"Basai kun duba bah" ta fada da wani BOYAYYEN KUDIRI aranta


Takowa tayi ta fizgi paper din hannun shi

"Kumin afuwa akan bata muku lokaci da nayi, securities dina dasu zaku zanta"

Saida ta police din hade da wasu daga cikin masu tsaronta sun tafi kafin tayi magana


"Ni talaka irinka yasa a gaba yana ci ma mutunci, wai kai nan meh gsky, a haka kuke farawa ku kare da sata da bara akan hanya"
πŸ‘πŸ» ya hada wuri daya

"Ban sanki bah Hajia, haka kuma ban san da wacce kika zo, saidai ina rokon ki da ki kyale min iyali na"

Tayi yar dariya


"Abinda ya kamace ka kenan, roko" ta karasa bayan ta dan lokaci


"Na dogara da Allah ne Hajia, duk abinda ya sameni koh iyalina ni a wurina kaddarace kuma jarabawa ce daga Allah, saduwar Alkhairi"


Ya ja Kaka sukayi gda,beh jira bah ya fito dan yin gda, a tsaye inda ya bar Hajia tana nan har yanxu


Yana zuwa gda ya karasa dakin matarshi, sai ya fara hawaye


Tashin hankali ya bayyana a fuskar Mama, da Abba da Mukhtar


Tambayan shi abinda ya faru sukeyi,shirun da yayi yana hawaye yasa duk suka jera layi suna taya shi 😭😭😭😭😭😭


"Ban kasance cikin jerin uban daya zaba ma diyarshi miji na gari bah"

Duk sun san halin salisu amma sukayi shiru dan mahaifin su mah bece komai bah


"Alkawari na daukan mah iyayena dana suna da rai, nayi musu alkawarin bazan sabama umarnin kaka bah tunda itama mahaifiya ce a gareni, amma hakan beh haifamin da meh ido bah, tunda diyata bata tsira bah"


Duk sukayi shiru suna jin shi, duk sun bar zubar da hawaye, tuno Asma'u kuma yasa duk suka fa da wani yanayin na san zubda hawaye

"Allah baya bacci Baba, kuma shi yace muyi biyayya ga mahaifan mu, yadda baka musanta mah kaka bah haka Asma'u bata musanta bah tayi abinda akeso"

Ya dan ja majina kafin ya cigaba


"Mai sama baze barta ta wulakanta bah, in mijinta bana gari bane bah, ita din ta garice,baiwar Allah ce kuma meh kai kukanta ga mahalicci ce, shi kadai ze iya bata mafita a rayuwar nan"


Mukhtar na idarwa ya tashi ya fita.




Hajia Turai fah????


Hajiya Laila Turai uwa ga Safiya, kaka ga Ehsaas, macece da a rayuwarta taki jinin talaka,

Dan acewarta sune sanadiyar rabata da duk wani farin ciki nata.


Giza gizai take kallo,sunyi duhu alamun hadari, kafin su hawo jirgi mah saida pilot din yace ba'a basu damar dagawa bah


Bacin rai yasa bata bi ta kanshi bah, da yake yasan ita ke biyanshi sai ya shiga jirgi suka haura sama


😑 har yanxu haka fuskarta take, sake saken hanyoyin da zata banbanta mah wannan mutumin tsakanin aya da tsakuwa kawai takeyi


Murmushi ne ya ziyarci fuskarta lokacin da ta fiddo wayarta taga video call ne daga Ehsaas


Fuskar nan tashi cike da annashuwa ya gaisheta



"Granny Ma cikin jirgi kike" ya fada yana sunno kai


"Eh jikana, yanxu kaga na iso" taga ya bata fuska


"Amma yanayin garin fah da hadari,anan har tsawa a keyi, meh yasa kika hawo jirgi"

Ya fada da damuwa a fuskar shi


"Ehsaas na gaji,ga jikin tsufa, kasan sai na nemi saukin doguwar tafiyar nan"

Ya jin jina kai alamun haka ne.

"Granny ma ina da wani surprise daze sa ki manta da laifin danayi"

Tayi murmushi dan tasan akan set din yan kunnen da aka bashi ne ya batar


"Ba laifin ka bane bah Ehsaas, low lives dinnan ne masu hannun bera fuskar biri"

Dariya zancen nata ya bashi da har itama saida ta dara


"Fadamin meye surprise din" koh mantawa yayi ne da surprise ze bata sai taga yana gudu wani ze nuna mata


"Asma'u, zo kiyi magana da Granny Ma dina" mamaki ya kamata


"I love her so so so so so so much" ta kara sakin baki saboda mamaki

"Mazarin meh kakeyi Ehsaas, naxata surprise zaka bani" sa yaja kuma ya tsaya yana shafa face dinshi


"Na kagara ki ganta , love at first sight ne, ina ganinta naji ya zaman min dole in kasance tare da ita"


Ya fara dariya kuma shi kadai


"In na fada maki bazaki yadda da abubuwan danayi bah dan kullum in dinga ganinta"

Washe hakori Hajia keyi,amma aranta tayi kicin kicin da fuska, so take kawai ta hada ido da wannan yarinyar


"Dad ze gane inda na dosa, dan shima haka yace min yaji daya hadu da Mom"

Yayi mata sallama da Allah ya kawo su lafiya kafin ya kashe wayar.



⚜B.W.AπŸ–Š
⚜BRILLIANT WRITERS ASSOπŸ–Š



πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI
NA KHALEESI,
& NOBLE JUDGE.
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’


2⃣0⃣.


"Mama"
taji ana cewa 'sa hands free' daga dayan bangaren

"Kin gama kukan ne Asma'u" tayi kaman zata fara hade da cewa uhm uhm

Dariya yayan nata yayi yana sako baki

"Sis yanxu nine da shagwaba, gwara ma ki daina dan baya yi miki kyau kuma"

Kukan da takeson yi beh hanata murmusawa bah

"Mama yaushe zaku zo"

"Ah ah hah, Asma'u kuka zaki fara kuma" fashewa tayi da kukan mah dan suji yadda take kewar su


"Little sis kin yadda ni inzo in maye gurbin ki a babban birnin tarayyan"
Tace eh hadda wallahi ta yadda

"Yi hakuri Asma'u, kuka babu abinda zeyi maki" Mama ta katse wasan da Ya Abba keyi mata

"Komai na dan lokaci ne, yanxu da kin saba zaki manta da mu ki daina kewar mu"

Ta girgixa kai tana cewa Aa

"Aa meh?" In ji Mama

"Ni nafi san can" ta fada da shagwaban da yazo mata a ranan

"Ina fata dai ana kula dake" ajiyar zuciya tayi tana kallon dakin da takeci, dan kula anayi,amma ita hankalinta ya kasa kwanciya


"Kinga shi mijin naki" ya Abba yayi karfin halin tambaya

Dan so suke suji in abinda akace salisu yayi gsky ne


"Ni banga kowa bah" ta fada tana tura baki, inna lillahi taji mamanta na fada


"Mama ya akayi?" Ta tambaya da damuwa

"Basai wani abu ya faru bah sannan zaka nemi agaji da ga Allah"

Ta kwantar da hankalinta dan,itama kullum cikin neman agaji take dga ubangiji


"Yanxu kina ina ne little sis" ya tambaya ba wasa a muryar shi


"Gdan wanda muka taho tare dashi"

Hankalin Mama ya kara tashi

"Gsky zamu dawo dake nan, bazan barki acan bah hannun wanda bamu sani bah, hakan beh dace bah kwata kwata"


Tayi hamdala acikin ranta,har wani sanyi taji ya ratsa ta


"Zanyi mai magana toh, si in dawo abuna" ta fada da farin ciki

Suma hankalin yan gdan nasu ya dan kwanta.

Hira suka dan taba kafin kwan kwasa kofar da akayi yasa tayi musu sallama


" Husna " ya fada yana so ta dago ta kalleshi,amma kanta kasa ta amsa mai

"Akwai alfarmar da nakeso kiyimin guda daya"
Ya tambaya da karamar murya

Daga mai kai kawai tayi tana cukwi kwiyar hannun hijab dinta


Shima kuma ya rasa yadda zeyi mata bayanin abinda yakeso

"Husna" ya sake kiran sunanta

Bayan tace na'am sai yayi magana


"Pls in Granny Ma dina tazo karki fada mata kina da aure" ta dan dago sannan tayi magana


"Meh zance mata dalilin zamana anan" kafin ya ansa kuma ta cigaba

"Kuma ni bazanyi karya bah Allah na gani" ta dukar da kai tana kallon yan yatsunta


Shima dukar da kai yayi sannan ya jingina da bango,

"Nima bazan saki kiyi karya bah Husna" ya biye mata shima yana wasa da nashi πŸ–


"Ni ina son zan koma gda, tunda baya nan kuma" ta fada kaman bata so yaji abinda tace

'In kika tafi ni inyi yaya toh?' Ya fada a ranshi


" Husna? An takura ki ne koh an mata maki ne?"
Shima kaman beh so maganar ta fito


"Nidai gdan mu zanje" ta fada kaman zata fara kuka,sannan ta juya ta koma cikin dakin

Dan riko hijab dinta yayi,wanda hakan yasata tsayawa


"Husna,ki yadda dani,bazan cutar ____"

Wata meh aiki data rugo ta hanashi karasawa


"Hajia Turai ta dawo Sir" ta fada da haki

Yana nan tsaye yana kallon Asma'u har saida ta dago ta kalleshi,kafin yayi mata murmushi


"Muje kiga kakata" girgixa kai tayi


"Ka bari ta huta sannan" ya ce toh kafin ya fara tafiya da sauri yana kiran

Granny Ma!!!!

Beh sake bi takanta bah,itama kuma bata nemeshi bah,


Sai can cikin dare bayan tayi shimfida kasa da bargo ta kwanta abinta bacci meh dadi yana daukanta sai taji knocking,


Tashi tayi da dan sauran baccin a idanta ta bude kofa

"Ina ta knocking baki budemin bah"
Ta dan mutsuka idanunta

"Kayi hakuri,na fara bacci ne"
Takowa gaba yayi alamun ze shiga dakin


"Da wannan kayan zakiyi bacci" ta harde hannuwa a cikin hijab dinta


Kayan daya kawo mata ya gani linke saman gado ta wurin pillows

" Husna kiyi hakuri na manta da batun siyo maki kaya" daukan kayan ya nufo ta

"In kuma kina so sai in sa aje a siyo maki, nafi son ne kawai muje tare sai ki zaba da kanki"

Ya mika mata kayan bacci,amma taki karba

Kaman yasan abinda take tunani,kuma ya hanata sa kayan


"Allah ban taba sasu bah, kuma daga yau sun zama naki"

Karba tayi tana mai godiya

"Toh jeki canza kayan" ta dan matsa daga kusa dashi

"In na tafi zaki iya ajiyewa baki sa bah, kuma kayan jikin ki sun gaji Husna"
Tace nima nasan haka a ranta

"Tun jiya fah kike sanye dasu" ya sake tuna mata

"Zansa" ta fada tana fata ze fita

Zama yayi saman gado,yana nuna bathroom

"Ina jiranki" ya fada

A wurinshi tsantsar kauna da kulawa kawai yake nuna mata,

Ita kuma takurata kawai takr ganin yana yi, kuma dan ya saba sa mutane suyi mai abinda ya keso


Tana cikin bandaki tana canza kayan,

Tana zura wandon taji wani irin kunya, dan ita in banda wandon makaranta toh bata mallaki wani bah


Gashi wannan dogo ne amma beh da wani fadi sosai, Allah yaso rigar ta danyi mata tsawo har zuwa saman cinyarta,
Tunani tayi na dan lokaci kafin ta cire bra dinta ta aje tare da sauran kayan


Hijab dinta ta maida kafin ta fito, tsaye ta ganshi ta dayan gefen gadon in da tayi shimfida


Ta zabi wurin ne dama dan in mutum ya shigo baze ga shimfidar bah


"Anan zaki kwanta?" Ya tambaya yana kallon wurin


"Saida nace maki in kina son wani abu ki fadamin" ya juyo gareta


"Meh yasa yau baki fadamin cewa bakiji dadin bacci saman gadon nan bah, kinga da an canza maki"

Girgixa mai kai tayi alamun ba haka bane bah


"Ina saura ranki" ya kafeta da idanu, ita kuma kanta kasa


"Ban tashi sallar asuba bah jiya,shi yasa nace a kasa zan kwanta yau"
Abin dariya ma ya bashi


"Zanzo in dinga tashin ki daga yau toh"

Dago kai tayi dataga yayi hanyar ban dakin


Da sauri ta tsayar dashi da tambaya


"Meh kake nema" ta taka zuwa gabanshi


"Kayan da kika cire zan dauko, kinga gobe zakiga Granny Ma dina, shi yasa nakeso kije tsaf tsaf"

Ze bi ta gefenta ya wuce ta hanashi


"Bari in dauko sai inje in wanke da kai na"

Girgixa kai yayi yana cewa Aa

"Ke bakuwa ce,mu yan gda ya kamata muyi wannan aiki"
Sannan ya nuna hijab dinta

"Harda hijab din zaki bani" dagowa tayi suka hada ido kafin, ta saukar da kai kasa


"Ka barshi zan wanke" daure fuska yayi

"Bana son gardama Husna, dauko min duka kayan ki bani"

Bandakin ta shiga ta cire hijab din sannan ta linke ta dora saman kayan, bayan ta dauke bra da undie dinta daga ciki


"Gashi,nagode" ta fada daga cikin makewa yin, bayan ta mikamai kayan


Wanke underwears dinta tayi kafin ta, fito ta zauna jiran ya kawo mata kayan


Shi kuma wata meh aiki yasa ta wanke kayan da washing mashin,tayi drying ta goge,duk yana kallon abinda takeyi

Bayan ta gama ya karba ya nufi dakin Husna da murmushi, dan yasan zataji dadin wannan gwanintar da yayi mata


Yana kwankwasawa ta amsa, lullube da bargo ta bude kofar ta karbi kayan, tana yi mai
godiya.




⚜B.W.AπŸ–Š
⚜BRILLIANT WRITERS ASSOπŸ–Š






πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI.
NA KHALEESI
& NOBLE JUDGE.
πŸ’πŸ’πŸ’


Please Login or Register in order to submit comment