Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Na kagara in ganki dauke da little angel dinah ni mah"
Tayi shiru, dan fara'ar da takeyi mah ya dauke,

"Koh bakya son Baby dinne wifey" ya tsare bayanta da kallo,

Murmushi ta dora saman fuskarta kafin ta juya ta kalleshi,

"Ni ina da baby ai" ta fada tana jan hancin shi

"Kina da baby?A ina yake, cikin ina kika boye shi" harda jujuyata, da daga mata riga yana neman baby din nata,
"Muga baby din" da yar dariya ta lakaci hancin shi,

"Ga ka nan" sannan ta wuce tana murmushi da kallon shi ta gefen ido,

"Watau ni neh baby din koh!" Ya daga ta sama yana jujjuya wa, da dariya take cewa ya sauketa,

"Ba ka cika rigima bah. Ai haka babies suke"

Dariya yafashe dashi kafin ya dorata saman gado , yana fidda numfashi sama sama,

"Kina son yara dayawa My wife" radadi takeji a cikin zuciyarta, amma a fili Fara'a kawai takeyi,

"Yara dayawa kakeso neh?" Ya daga kai yana dora hannu saman cikinta,
Tsikar jikinta duk ta tashi tsaye,numfashin ta yayi sama daya dan danna mata cikin,

"Naga cikin ya tsomare kaman ba'a zuba mai abincin" ya dan kara matsawa,

"Ana zubawa manah, baka ga yadda yayi kato bah"

Ta fada da yar dariya amma shi he's serious ,

"Ze iya daukan baby nah Husna" tana jin sunanta ya fito daga bakin shi tasan maganar gaske yakeyi bah wasa bah,

Hannu biyu tasa ta rungume cikinta,
"Baze iya dauka bah kenan" tayi saurin girgixa mai kai sannan ta tashi zaune, shima kuma ya zauna suna kallon juna,

"Ni bazan iya daukan baby a ciki nah bah da karan kai nah" ya mata wannan kallon nashi na yimin karin bayani,

"Sai Allah ya bani iko, in har ya bani ni kuma in shaa Allah zan kula da wannan kyautar har ya bar cikina"

Yana jin dadin yadda takeyi mai magana kaman tanayi da wani His Excellency, cikin sanyin murya da kwanciyar hankali, kowace kalma sai ta tauna kafin ta furta mai,

Dan dukar da kai yayi yana cije lebe saboda dadi da farin cikin daya mamaye shi, duk dan yaga irin mahimmancin data bashi,

"Ya kamata a baki babban kyauta" itama ta nuna nata farin cikin,

Matsowa ya fara yi amma bataji wani dar dar bah, dan sun saba da makale juna suna labari har bacci ya dauke su,

"Bari inyi tunanin irin kyautar da nakeso" girgixa mata kai yayi,

"Uhmm hmmm, ni zan baki abinda na ga ya dace da ke" ta dan turo baki harda harde hannuwa a kirji,

"Da abinda kike so kenan?" Ta daga mai kai da sauri da yayi tambayar,

"Shikenan toh, amma in kika fadi abinda kikeso ba zan baki abinda naso baki bah"

Ta daga kai tana dan tunani

"Mota, kaya koh takalmi, jaka, purse, in sabon phone ne dama nayi niyyan canza maki in munje gda, koh turare, meh da meh mata mah ke so?"

Alama tayi mai da yatsan ta mai nuni daya matso ta fadamai,

"Ni ga abinda nakeso" kiss din daya mantar dashi duniyar da yake ta yi mai, har yatsun kafar shi ya lankwasa saboda fita hayyacin shi da yayi,

Tana matsawa baya ya jawota ya matse a jikin shi, mataki na gaba ya daga su daga kissing zuwa make out,

Wuyanta da dukiyar fulaninta ya shiga sarrafawa, bata gane inda bakin shi ne koh hannun shi ne ke tabata, su duka sun birkice dan sun dade suna tado mah kansu da sha'awa sannan suki yin komai akai,

"Yau daran faranta ranmu ne koh" koda taso amsawa da baki baxata iya bah dan shakan numfashi yayi mata wuya, kai ta daga mai a amatsayin EH,

Tashi zaune yayi ya cire rigar shi, idanunta ne ya kai ga windows din dakin manya manya da su,

"Haske" ta fada murya shake,

Tsaye ya mike ya latsa wani button daya ja wasu labulaye masu duhu suka rufe dakin, sannan ya kunna night light, green color ne night light din ta four corners din dakin,

Matsa mai tayi ya komo saman gado, idanu suka tsura mah juna, numfashi suke fiddawa a hankali, gajiya yayi da tsumayar abinda ze faru ya hau yin aikin daya san nashi ne,

A sannu suke bin komai kaman duka tym din duniya nasu neh, abubuwan daya saba yi mata yayi, amma sai taji kaman ranar suka fara irin haka,
Ga tsimin datayi ta sha tun kafin ayi maganan honeymoon din nasu, sanin abinda ze faru beh hanata fargaba bah, yanayin data shiga na mata dadi sai kara preparing dinta yake mah babban harkar, matsalar ta kar duk jiran nan da yayi yazo batayi mai armashi bah,
Kaman kwai haka yake tarairayarta, yasan ta da hakuri ga zurfin ciki, yasan takai iya kurewa ne shi yasa ta rirrike shi tana kuka ciki ciki har ya fito waje,
Sunan shi take kira a hankali tana hadawa da kukan da beh fitowa sosai, maimakon ya sassauta sai ya kara kaimi, dan kaman kaimi take kara mai, in tana kiran sunan shi, Sau daya yasa a ranshi ze kusance ta a daren, amma beh san lokacin da ya wuce round two ya shiga na three bah,
Gefe ya koma ya kwanta yana maida numfashi da hamdala a cikin ranshi, yasha wahalan zuma, ya kwaidaitu ta dalleshi finally kuma ya dandani dadinta, bega abinda zesa ya hori kanshi da yunwa bah bayan yana da abincin da yafi kowanne kosarwa, wanda babu kamar shi a wurin shi,

"Yar Albarka" dan sautin datayi na takura kuma ta kara takurewa gefe daya yasa ya lalubi bedside lamp ya kunna,
Wani sautin tayi meh kama da na kuka, tana kara dunkulewa
Bargo yaja ya lullubeta, yana dora hannu saman kafadarta ta nuna rashin amincewar ta da hakan ta yin wani karamin kukan,

"Sorry wifey" ya dauke hannun shi, ya dade a dan kishingide yana kallonta, hartai bacci tana fidda numfashin wahala,
Sauka yayi daga saman gado ya nufi bandaki, wanka yakeyi yanata murmushi da fara'a shi kadai,

A dan firgice ta farka tana ji kaman ana jefota daga wani wuri, hannunta da yayi mata nauyi ta samu ta daga ta kunna fitila, gefenta ta kalla sannan ta shafa wurin, ji tayi wurin mah yayi sanyi alamun ya dade da barin gadon,

A cije ta mike tsaye tana daura zanin gadon a jikinta, fitila ta fara kunnawa tana kallon time, A'uzubillahi tace tana nufan labulayen da suka rufe window, tana yayewa taga rana kar tana kallonta,
Dauke idanunta tayi saboda sarawa da kanta yayi, tana kallon kasa tagan shi tsaye da wacce koh ba'a fada tasan Danyah ce,

Sai lokacin ta bar kukan da takeson yi data farka bata ganshi bah ya subuce daga bakinta, tana nan tana fama da jikinta shi kuma yana can yana tadi,

Saida tayi dana sani data taka da hanzari da zata bar wurin, jin gina tayi da bango radadin ya rage kafin ta taka a hankali zuwa bandaki,
Gasa kanta tayi yadda ya kamata, sannan tayi wanka hade da alwalla kafin ta gabatar da sallarta,

Bata tsaya nan bah saida ta dauki bed sheet din da suka bata ta wanke a bandaki, ta sako shi cikin basket zata kai laundry room tana tafiya sannu a hankali sai gashi ya shigo dakin,
Ganin shi mah sai ya fama mata ciwon dake cikin zuciyarta,

"Husna meh kikeyi" ya karbi basket din yana son ya aje a kasa,
"Bani in shanya" ya matsar da shi da kafar shi, ita kuma ta duka daidai lokacin,
Dafe bayanta tayi tana mikewa a hankali dataji ya kage, bata ida mikewa bah sai gashi a gefenta yana taimaka mata,

"Wa ya saki duk wannan aikin? " saman gado ya kwantar da ita,
"Wifey yi hakuri bana nan kika farka" kaman jira take ta fashe da kuka, gadon ya hau yana kokarin juyo da ita ta fuskance shi,

"Am sorry wifey dan Allah kiyi hakuri, ya kike ji yanxu, kina bukatar inyi maki wani abu, tausa, koh in kawo maki ruwa" yadda yake magana kaman yana lallashin dan karamin yaro,

Make kafada tayi tana tashi zaune dan kar ya mah cigaba,

"Meh takeso" dan bata fuska yayi yana daga gira
"Ita manah, meh tazo yi tun da safe"

Kasa yayi da kanshi ya dade beh dago bah, yana tunanin yadda ze fada mata abinda ya kawo Danyah, kishin daya gani karara a idanunta ya karasa shi jin nauyin fada mata,

"Babu boye boye tsakanin mu wifey zan fada maki abinda ya kawota,
But first, ina so kisan da ke kadai nake ra'ayin karasa rayuwata, ke kadai kawai nake so" hannunta ya rike yana mata wani lallausan murmushi,

"I love you wifey, thank you for the best night ever" kunya ta hanata cigaba da kallon shi,

"Ba fushi nakeyi dake bah Danyah, na dade ban gana da iyali na bane bah, kuma bana son wani abu ya hana mu hutun da muka zo yi shi yasa na raba kai na da wayoyi na aiki"

Yasan he owes her no explanation, saidai tausayinta yake yi shi yasa yake dan bata lokaci in tazo wurin shi,

"Bakaji wani sanyi daya ratsa ni bah, naxata fushi kakeyi da ni shi yasa ka shareni, pls ka bani digits dinka wanda bana office bah"
Ta bi zancen nata da wani katon murmushi,

"Danyah business relationship ne kawai ATSAKANIN MU"
Murmushin ya dauke amma bata nuna rashin jin dadin zancen nashi bah,

"Okay, da alamu baka sani bah?" Ya dan karkata kai

"Bayan haduwar mu ta farko Mom dinka ta tambaye ni if i like you, a lokacin ban san abinda zance bah sai tace bakomai ta bani tym,

Kasan na rasa mahaifiya ta tun ina yar karama, kuma ban san dadin mahaifiya bah sai akan taka,
Yadda take kula dani kaman ni diyarta ce, kuma na saba da ita sosai,

A wurinta naji abubuwa da dama gameh da kai, and i like you, abinda nakeji gameh da kai yafi like amma zan barshi a haka, duk sarda muka hadu sai nake ganin kaman kana da jan aji, nima kuma zan ja aji kafin in fada maka wannan kalma ukun"


Ajiyar zuciya tayi sannan ta dan saki fuskarta daya gama fadamata abinda ya wakana tsakanin su,

"Ai kin san ke kadai nakeso koh, ba bukatar mah ki damu kanki akan Danyah kinji" ta daga mai kai,

Tashi yayi ya bar dakin dan samo mata abinda zata ci,
Ita kam keda tunani, tunanin yadda zata tsara rayuwarta, rashin san Danyah baze hana ya aureta bah saidai in mahaifiyar shi batace bah, in koh har tace toh koh Dad baze hana ayi auren bah,

Mikewa tayi ta lalubu jakar data rataya da zasu bar Nigeria,
Kwalin maganin da Mom ke bata ta fiddo sannan ta zari sachet daya,

Bandaki ta shiga dan shan maganin, hawaye ne zazzafa ke tsiyayo mata a fuska,
Zata iya kin shan maganin nan, ta samu ciki, ta haifeshi sannan ta raine shi ita kadai, in tayi haka BOYAYYEN KUDIRIn ta beh cika bah, dan koh ta bar gdan shi sai ya dinga zuwa ganin abinda ta haifa, kuma ita so take ta raba jaha dasu gabaki daya,
Mirror take kallo amma fuskarshi take gani dauke da murmushi maimakon taga tata fuskar,

Bude tap tayi ta sharuwa bayan ta jefa maganin a baki,
Kuka ta hau yi kaman danneta akayi aka dura mata maganin ba ita ta sha a karan kanta bah,

Daya dawo ya iske tana kuka sai tunanin shi ya rabu biyu,na daya ya ji mata ciwo na biyu maganar daya fada mata akan Danyah,

Da kyar ya tursasata taci abinci, haka ta yini ranar tana kuka ga wani azababben ciwon kai daya addabeta,

Kasa hakura yayi ya kira mutumin daya ji ze iya fadama sirrin shi,

"Hey!" Yace, gardin muryar tashi duk ta washe saboda damuwar da yake ciki,,

Haider daya tsinci yanayin shi sai ya jero mai tambayoyi dake nuna kula da damuwa,

"Wai meh yasa mata suke da wuyar fahimta ne" harda jan hanci kaman kuka yakeyi,
Kaman a kashe wayan da yaji Haider nayi mai dariya,

"Barka da shigowa cikin layin mu My Friend" bata rai yayi kaman face to face suke magana,

"Wannan ba abin wasa baneh bah Haider" tsagaita dariyar tashi yayi kafin yayi magana,


"Kun samu wani sabani neh" girgixa kai yayi kafin ya furta,

"Ni a gani nah lami lafiya komai yake, saidai gata nan tana ta kuka tun da safe" abokin nashi yace hmmmm,

"Na san halin da kake ciki Bro, abin na daure min kai, sai kaga sun daure koh sun canza lokaci daya,
In ka tambayi dalili kuma ace maka bakomai, toh ta yaya za'ayi ka sani in bah aljannu gareka bah"

Ehsaas ya jin jina kai,
"Exact abinda nake magana akai kenan"
Haider yayi yar dariya

"Karka damu zata natsu ta dawo kaman da, kawai ka bata tym" Yace toh yana janyo wata hirar ta daban,

Jikinta duk yayi mata tsami ga ciwon kanta kaman ana karowa neh, saukin data ji wurin tafiya mah ya ragu sosai, dan haka tana idar da sallar isha ta shiga wanka,

Data fito saita iskeshi kwance saman gado,

"Kina jin zafi ne har yanxu?" Ya tambaya bayan ya gama lura da yadda take tafiya,

"Ba sosai bah" mikewa yayi ya daukota ya aje saman gado, bayan nan ya shiga bandaki inda ya dan jima kafin ya fito, dauke da towel,

"Meh za'ayi" ta fada tana ture hannun shi dake kokarin kware mata towel,

"Dan Allah ki bari wifey, ki barni in baki kulawa yadda ya kamata" ya kara dora hannu saman cinyarta ze daga towel din,

"Ka bari manah, ni am fyn" tsareta yayi da idanun shi data kasa kallo ta sauke nata kasa,

Saida ta cire hannu daga inda ta rike towel din gam kafin ya cigaba da abinda yakeyi,
Bargo yaja ya lullubeta kafin ya cire towel din data daura kafin ya dora mata towel din daya jika da ruwan zafi saman mararta, from time to time kuma yana zuwab ya kara tsoma towel din cikin ruwan zafi kafin ya dawo ya sake sa mata,

Godiya tayi mai daya fiddo mata kayan bacci, yar singlet da boy short, sannan ya tayata sawa,

"Good night" itama tace mai good night,


Haka suka cigaba da yi kullum, ko ta fadamai ta shiga ruwan zafi sai ya dan gasata da towel, haka yake cewa wa ya sa ta tayi aikin shi,

Zaune take saman gado tasa diary dinta a gaba amma ta kasa rubuta komai, ba abin rubutawa ta rasa bah, abinda ke ranta ne take tsoron fayyace a fili, ta karanta,

Flowers din da suka fara yaushi, dake gefenta cikin vase saman bedside drawer ta zaro tana cire petals din roses din🌹🌷🌺saman gado take ta watsa su ba tare da lura da abinda takeyi bah,
Data gama cire furen saita kwanta rigingine tana kallon juyawar fanka,

"Someone is feeling romantic today" da hanzari ta tashi zaune tana mai sannu da zuwa,

Gadon yake bi da kallo sannan rumfar da akayi mah gadon da wani peach sheer lace labule,

"Aikin ki yayi kyau" ta dan saki fuska tana cewa ta gode,

Saukan da tayi daga saman gadon ne yasa iska watsa flowers din saman gado,

"Yau mah cikin dakin kika yini" murmushi tayi tana girgixa kai,
Dan jawota yayi zuwa jikin shi data zo zata wuce ta gefenshi,

"Lafiyar ki lau koh?" Ta daga mai kai tana mashi proper sannu da zuwa ta hanyar bashi pecks a kumata da dan hug,

"Ya aikin?" Ta tambaya murya kasa kasa

"Alhamdulillah" yace yana lura da yadda duk tayi wani sukuku,

"Tun dazu nake missing dinki, yanxu kuma dana dawo peck kawai na samu" yar siririyar dariya tayi daya sa shi jin dadi, ita kuma ta dan dade bata ji yayi shagwaba bah,

"Nayi kewar shagwabar ka ni kuma"
Abin nema ya samu, sai ya narke mata a jiki, sai gasu a kasa da rabin jikin shi a samanta,

"Wifey!"
"Bakai ne ka cika nauyi bah" itama ta fada da shagwaba,
Kallonta yayi kafin ya babbake da dariya,

"Kema with time ai nauyin zakiyi, kuma in tsokane ki bah, harda nan ze kara cikowa koh" ya matsa dukiyar fulaninta,

Abinda ya fiddo ta daga tunanin magana biyun da yayi na in ta samu ciki zatayi nauyi,

"My All bari manah" yadda tayi maganan kaman baso take ya bari bah,
Ta cikin rigarta ya zura hannu yana sarrafata,

"Wifey hannun ki baya komai" kulle idanunta tayi gam sannan ta sakalo hannayenta a wuyanshi, yana cigaba da shafata ta sauke hannayenta,

"Kunyarki na galabaitar da ni Husna"
Duk da tasan yana san kunyarta,sai take ganin kaman ba in a good way yake nufi bah daya ce kunyarta na wahalar dashi,

Bata gama tunaninta bah taji ya raba jikinshi da nata, koh seconds biyu bata dauka bah wurin yanke shawaran bin shi,

Tana bude ido taga kayanshi yake cirewa, saita ture hannun shi tana maye gurbin su da nata, shi kuma sai ya koma aikin kissing dinta da rabata da kayan jikinta,
Daukanta yayi ya dire saman gado bayan ya kashe fitila, daren kaman na farkon su, it was satisfying duk da har yanxu akwai kunya tattare da ita, kuma yayi planning canza hakan,

"Ya akayi neh Husna" ya kira sunan meh dafa masu abinci
"Tace min duk yau baki fito bah"

A hankali ta dago fuskarta data kumbura ga idanu sunyi ja,

Tun jiya tasha maganinta dake hana daukan ciki bata bari sai da safe bah,

Bayan sallar asubah kuma bata san sadda bacci ya kwasheta saman sallaya bah, saidai ta farka ta ganta saman gado, text din barka da safiya da kuma fatan Alkhairi da sa'a a wurin aiki tayi mai, tana yunkurin barin gado kanta ya sara kaman an rabashi biyu,
Tun lokacin take fama da ciwan kai, tasha maganin tayi bacci, har abincin tasa ma cikinta koh yunwa neh, amma ciwon kan beh tafi bah, karshe kwanciya tayi tana aikin kuka,

"Husna ya akayi" ya zauna gefen gadon yana taba goshin ta,

"Kaina ke ciwo tun dazu" ta dafe kan tana kokarin shigewa jikinshi,

Tun kafin ta dora kai saman kirjin shi ya mike ya bar dakin gabaki daya,

Da ruwa da magani ya dawo dakin, zamzam neh sai pain reliever meh dan karfi sosai,

Tana gama sha kuma saiga meh dafa abinci ta shigo da tray,

"Na hado da wanda ba'a jika bah, in kun bukata anjima" godiya yayi mata kafin ya karbi tray din,

Wani Chinese green tea neh na ganyen da suka bushe,

Ruwan zafi ya zuba masu bayan sunyi kasa, sai ya tace ya bata tasha,
Kanta ta dora saman cinyarta har bacci ya dauketa, cikin dare ta farka taga ya rage wutan daki, sannan ya cire suit dinshi,

"Ya yah Wifey? Ciwon kan neh?" Ta girgixa kai tana kara shigewa jikinshi,
Sai lokacin ya iya Ajiyar zuciya ya bari bacci ya daukeshi,

"Ina kwana My All" ya amsa murya ciki ciki, sannan ya sauka daga saman gadon, wanka yayi yazo ya shirya,

"Na hada maka breakfast din daka fi so, chocolate pancakes, eggs da french toast, harda tea meh mint da vanilla flavor" kallon abincin yayi, ranshi ya kara biyawa,kuma sai ya kauda kai,

"Na makara Husna, sai na dawo daga office" ta bude baki kafin ta samu magana ya fito,

"Amma ka ce wai baka bukatar zuwa office kullum, kuma naxata yau a gda zaka yini"
Cigaba da shirin shi yayi, badan taso bah sai ta sa hannu tana taya shi shiri,

"Dan Allah ka tsaya koh breakfast kayi" kaman zatayi kuka haka tayi maganan,

"Ki kwanta ki huta Husna, baki da lfy" ya fada murya cunkushe,

"Kuma zaka tafi ka barni, kuma ranka bace yake, meh nayi pls Hubby"
Ba shagwaba a muryarta sai sautin kuka da yake fita a cikin maganar ta,

"Raina bace yake Husna, kin batamin rai sosai" sai ta fashe da kuka tana toshe baki da bayan hannunta,

"Daidai lokacin da kika ji bakya jin dadi, lokacin ya kamata ace na sani Husna" ya harde hannu a kirji, ita kuma ta fara share hawayenta data ji laifin nata,

"Dan Allah

Please Login or Register in order to submit comment