Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Lfy" ta fada ba tareda ta dubeta bah,

"Naji kana baka nan ranar friday, babu wani business dake bukatar ka bar gda" takawa yayi zuwa gaban Mom,

"Yes ni da Husna zamuje Zaria taga gda sannan muga school din da zata fara zuwa"
Mom ta kalli Asma'u sannan ta maida kallonta kan shi

"Makaranta kuma, yaushe akayi haka ban sani bah" ta harde hannuwa a kirji,

Har ya bude baki ya rufe, ya zabi yayi shiru daya fadi abinda yazo mai a rai,

"Ina jin ka"da yayi shiru bece komai bah, saita maida dubanta ga Asma'u , take tsoro ya bayyana a fuskarta,

"Koh ansa bazan samu ba kenan" ta karasa bayan ta juya tana barin dakin,

"Yaushe zaka fadamata" data daga kai taga ita yake kallo,
"Meh yasa kike jin tsoron Mom" washe hakora tayi,

"Tsoron Mom kuma?, Mom ai mahaifiyata ce" ta fada da yar dariyar da bata kai ciki bah,

"Ni nasan abinda na gani a fuskar ki Husna" yayi maganar ba wasa,

"Kuma ke mallakina ce Husna,ni keda hakkin zaba maki abinda naga zefi dacewa dake,
Basai na gayama kowa decisions din da nake dauka a cikin rayuwar aure na bah"
Idanunta suka firfito waje, Girgixa mai kai takeyi a hankali,

"Mom baxata ji dadi bah in ka fada mata haka"
Ya jin jina kai,

"Na sani, amma gskyr lamarin kenan Husna, daba gdan nan muke zaune bah babu wanda ze san abinda mukeyi da inda zamuje"
Ya juya mata baya yana kokarin boye baccin ran shi,

"Amma ai gda daya muke dasu yanxu koh, ba matsala in sun san duka decisions dinmu"
Girgixa kai yayi ba tareda ya juyo bah,

"Dan Allah karka tado maganar data wuce, ni zan iya fasa zuwa makaranta kwata kwata in shine dalilun daya sa kakeso mu canza wurin zama"

A hankali ya juyo yana kallonta,

"Saboda kina tsoron kar Mom tace ra'ayin ki nake bi, ba decision din kaina bane bah" kaman zatayi kuka haka face dinta ya koma, takawa tayi sannu a hankali ta nufi gado ta zauna,

Zagayawa yayi ya kwanta saman gadon shima, da tunani iri iri a ranshi,

"Sai yanxu kayi lokaci na" kusa da ita ya samu wuri ya zauna,

"Zan fara da baki hakuri Mom, duk wannan babban decision da zan dauka saina sanar dake, amma wannan karon ban fadamaki bah,
Bawai bana so ki sani bane bah, Aa naga zabine daya shafi ni da iyali na, abinda zefi manah, naga mu zamufi sanin shi, shi yasa ban fada maki bah"
Shiru yayi yana jiran abinda zatace,

"Iyalin ka?" Ta fada kaman da takaici,

"Mom Asma'u nada hakuri sosai, har ya kai ga ko cutar da ita za'ayi she can't say anything,tana bukatar in shige mata gaba wurin yanke wasu shawarwari"
Idanu kawai Mom ta zuba mai,
"Kice wani abu manah" ta kyafta idanu tana hmmmm,

"Kana so kace kai da kanka ka nema mata makaranta a garin da iyayenta suke, ba ita tace tana so bah" ya daga mata kai a hankali,

"Dan Allah karka cemin kana so in yadda da abinda kace yanxu"
Ta bishi da kallon mamaki,

"Mom ni na zabi school din da kaina, makarantun da ta nuna tana so taje basuyi min ba shi yasa na canza mata, na zabi can ne kawai dan in faranta mata rai Mom,
Kuma ra'ayi na neh komawa gdanmu mu kadau"
Mom ta tashi tsaye, shima ya mike a hankali,

"Meh yarinyar nan tayi maka ne Ehsaas da kake son nisanta kanka damu, karka manta fah kaina meh fada a ji a gdanka, ba abinda takeso zaka dinga yi bah" ya katse ta da
"Mom abinda nakeso shi Husna keyi, komai da kikaga inayi abinda nakeso neh"
Harara ta watsa mai dataga yadda ya wani hakikance akan Matar tashi

"Mom dis is not fair, Dad na barinki kiyi duk abinda kikeso, in bakya son abu baze tursasaki bah, koh meh kika ce shi akeyi,
In nima haka neh meh yasa zaki dinga ganin laifinta toh, babu meh tsallake maganar ki" hannu tasa ta kwashe shi da mari,
kaman zeyi kuka haka yayi magana,
"Am sorry Mom"
Hannu tasa ta rufe bakinta, ranar farko data taba lafiyar jikin dan nata

"Bayan abinda nakeyi take kwaikwaya" ya girgixa kai,

"Am sorry Mom" kauda kai tayi tana kara jin haushin matar dan nata,

Sukuku ya koma dakinsu, kallo daya yayi mata ya kauda kai, ita batace komai bah dan ta karanci komai a fuskar shi, kuma dama tasa ran Mom baxata canza ra'ayi bah,

"Banda matsala in muka daga tafiyar zuwa wani lokaci, Ma'u ma bata shirya bah balle muje ganin makarantar tare"
Ta rungumeshi ta baya tana fada,

Kunyar abinda ya fada gameh da iyayenshi yakeji, shi yasa ya kasa kallonta,

"Ku wai bakwa jin kunya in kuka yini a daki ku kadai" kokarin tureshi tayi daga jikinta amma yaki tashi,

"Har kin dawo Granny Ma" Hajia tace Eh da murmushi,

"Dama nazo in ganku neh tunda ku kunki zuwa ku leka ni" Asma'u tace ba haka bane bah tana sadda kai kasa dan kunya,

"Zaki sake komawa can neh?" Yayi tambayar da kanshi saman cinyar matarshi,

"Eh, zan koma in cigaba da kula da danah" yayi murmushi da Hajia ta tafi,

"Husna" tace naam tana maida dubanta gareshi, shafa fuskarta yayi da bayan hannun shi, yana kallonta ido cikin ido, da hannun shi ya kai saman lips dinta saita dan bude su tana fidda raunanen numfashi, shima kuma ya fara shakan iska da sauri sauri,

Da sauri ya tashi daga jikinta yana gyaran murya, tunda bazan je ko ina ba karshen satin nan gwara in fadama Amyr tunda akwai inda yakeso in rakashi,

"Toh" tace tana kallon shi ta kasan ido hade da cije lips dinta na kasa,

Cike da kunya ta mike tana taku meh daukan hankali, shima kuma ya mike yana binta da kallo,

Lokaci daya ta juyo tana tunkaro shi,

"Muga in ka dauki waya da makullan ka" ta taka har gabanshi kaman zata shige jikinshi, boobs dinta na dan gogar kirjinshi,

Hannu tasa a hankali cikin aljihun jeans dinshi na duka gefe, tana jujuya hannunta a ciki,
"Baka dauki koh wallet dinka bah" kaman ba abinda ya faru, taje ta tattaro mai komai tasa mai cikin aljihu, yayi tsaye dan duk ta kashe mai jiki da sweet voice dinta, sannan ta tadomai da kwadayin kasancewa da ita da yakeji,

Yana fita tayi wani mugun murmushi,

"Badai kace kai good Samaritan bah, zanga iya juriyar taka" ta cigaba da murmushin samun nasara,

Be dade da fita bah sai ga Mom,

"Weekend dinnan, za muje wani wuri tare, dubo marayu da basu taimako da kungiyoyin da suke taimaka ma marasa hali" ba bata likaci ta aminta da taji abunda za'ayi,

"In shaa Allah mom" ta fada da ladabi,

"In ya dawo ki fadamai da kaina nazo nace ki rakani" tace toh


Yana dawowa ta fadamai yadda sukayi da Mom,koh in da yaje bata jira ya fada mata bah,

"Kina so ki je neh?" Ta daga mai kai da genuine fara'a,

"Kin san in da zakuje kenan" ta girgixa mai kai,
"Aiki neh ba karami bah Husna, kin tabbata kina so kije" a hankali ta daga kai dan taga kaman beso ta tafi,

Ranar friday suka fara ziyarta wurin, tara mutane akeyi iri iri manya da kanana, maza da mata ana basu taimako,
Saida suka jera kwana uku suna wannan aiki,kullum da babban bakon/bakuwar daze basu shawarwari kuma yayi alkawarin taimaka masu,

"Bazaki ce komai ba Asma'u" ta fiddo idanu waje,
"Aa Mom, ai duk kun fadi abinda ya dace,Allah ya saka maku da Alkhairi" Mom tace Amin da Murmushi a fuskarta,
Takawa tayi zuwa inda shugaban wata kungiya ke magana, wani abu ta rada mata a kunne kafin ta dawo inda suke zaune,

Kallonta tayi da murmushi itama saita maida mata, kaman daga sama taji an kira sunanta,
"Tashi manah, kema ki san kin bada wani gudunmuwa"

Heart na bugun ukku ukku haka ta mike, idanu a kanta, hannu na kyarma haka ta amshi 🎤, ko ita bata jin abinda take fada balle wasu, gyaran murya tayi ta kafin tayi sallama meh dan karfi, dataji an amsa sai tayi kokarin boye kyarman hannunta da murya ta hanyar murmushi,

A hankali ta fara jawabinta, mahimmanci taimaka ma juna tayi da kuma kyautata mah juna, sannan tayi mah bayin Allah dan suka hada taron godiya da fatan Alkhairi, karshe kuma ta tunatar dasu akan dagaro da kansu bada wasu ba, ta nuna masu yadda suke ja ma kansu kankanci ta hanyar karba ba tareda bayar wa bah, hakan nasa kullum suna ja baya, ta fada madu komin karancin kudin da kake samu yafi ka zauna jiran a baka,.

Kowa yaji dadi jawabinta amma bada Mom, da ke ganin so take ta nuna mata ba kowa ne ya damu da dukiyar su bah, wasu kwanciyar hankali da rufin asiri kawai suke su,
haushi ta kara ji da taga har manyan wurin na maraba da idea din nema masu abin yi fiye da basu kudi,

"Meh kikayi niyyan achieving?" Ta juya ta kalli Mom,

"Kina ganin ban gane abinda kikayi niyyan yi bane bah" dukar da kai tayi tana fidda numfashin dake nuna takaici,

"Mom honestly, taimakon bayin Allah nan kawai yake raina danayi magana, wata rana in bakwa na waze basu, ba gwara sun koyi dogaro da abin hannun su bah ko yaya yake, kila ki tafi koh rai yayi halin shi__" tayi shiru saboda kallon da Mom ta mata,

"Allahu Akbar har kin fara tunanin mutuwa ta, watau na zaman maki kashin baya koh na hanaki sakewa" dukar da kai ta sakeyi,

"Ba haka bane bah Mom" hmmmm inji Mom,
"Munafurci, shi yasa banson harka da talaka, saika ga komai ya karkace, ina taimakon ki kina ganin kaman cutar dake nakeyi"
A hankali ta dago da taji zancen Mom na karshe,

"Mom taimakon da zakiyi min shine ki rabani da Maganin nan , beh da wani amfani a gareni, sai illoli kala kala da yakeyi min"
Da Mom tayi shiru saita cigaba,
"Dan Allah"
Ajiyar zuciya Mom tayi,

"Shikenan tunda kin shirya rabuwa dashi, akwai wasu abubuwa da suka hana ni shigo da maganar Danyah but tunda da bakin ki kika ce tazo, no problem"

Ta fiddo wayarta tana texting,

Har zata ba Mom hakuri, sai wata zuciya ta hana tace bari taga abinda ze faru,

A falo suke zaune shida Dad suna dan tattaunawa, tsaye ya mike da suka shigo yana mata murmushi, maida mai tayi kafin tayi hanyar daki,
Wanka tayi ta shirya kafin ta sauka kasa dan cin abinci,

Baxata yaji ta runguemshi ta baya, sannan ta rada mai abu a kunne,

"Nayi kewar ka sosai My All" sannan ta matsa baya kaman ba ita bah, suma babu wanda ya lura dan duk sunyi gaba zasu nufi dining area,

Daya juya baya ya kalleta sai yaga ta shagala da kallon shi, a hankali idanunta suka sauka cikin nashi, cije lips dinta tayi cikin kunya tana kauda kai hade da rufe fuska da tafin hannunta,

Irin kallon da ya ga tanayi mai kaman babu kowa a gabanta sai shi,

Abincin shi kawai yake ci hankali kwance, koh magana bayayi saidai ya jin jina kai in aka sako magana dashi,
Tsayawa yayi da cin abinci data dora hannu saman cinyar shi ta kasan table, kallonta yayi yaga ita bata ma nuna alamun tasan inda hannunta yake bah,
Kokarin nunawa yayi kaman beh san tayi bah, ita kuma sai tayi upping game dinta,

Shafa shi ta fara daga sama zuwa tsakiyar cinyoyin shi, kware wa yayi yana zaro idanu waje,

"Sorry!"
"Saurin meh kakeyi, ci a hankali"
"Sorry ga ruwa ka sha" kowa yana kokarin agaza mai, amma shi ita yake kallo, sai kokarin bashi ruwa takeyi bayana itace silla,

"Sannu" ta marairace face tana samai cup din a baki,
Cin abincin yakeyi amma hankalin shi na kanta, jira yake yaji in zatayi wani abin kuma,

'Aha' yace a ranshi, sannan ya juya yana kallonta, harda dan tabota, data juyo wani innocent look ta bashi,
Sannan ta cigaba da shafa kafarshi da nata,
"Ya akayi hubby?" Ta tambaya murya kasa kasa,

'Oh baki mah san abinda akayi bah' ya fada a ranshi yana daga mata gira, daga kafadu tayi sannan ta shafa kafarshi one last time da nata kafan ta hada da kashe mai ido daya,

"Ahemmm" akayi gyaran murya, da sauri suka kalli gaban su suna tura abinci cikin baki,

Itace farkon tashi ta bar wurin, yana da niyyan binta Mom ta rikeshi da tambayoyi,

Ita kuma tana zuwa Daki ta kira Ma'u, taso ta bata tips din makeup, amma saboda yanayin yadda ta jita sai bata tambaya ba,

"Wai bazaku fadamin abinda ya faru bah, duk yadda muke da ya Abba amma yayi shiru kema kuma haka"
Hmmmm Ma'u tace

"Zan kiraki anjima namecy " toh tace tana kashe wayan,

Tana takure jikin gado, tunanin situation din Ma'u ya sha mata kai, tana jin sallamar shi ta sake hade da boye damuwarta, wani murmushi meh BOYAYYEN ma'ana tayi mai,

"My All granny ma ta wuce neh" ya daga mata kai,

"Uncle Yarima yaji dadi" ya daga mata kai
"Mom kuma kishi takeyi bah" tayi yar dariya daya fadi haka,

"Nima kuma kishi nakeyi" ta dago da kai sannan ta bude idanu tana kallon shi,

"Kishi kuma My All" ya rike hannunta,

"Mom tacemun a wurin charity event dinnan sai kallon mun ke akeyi, kema kuma harda yin surutu" hannu ta dora a saman kugu,

"Kaman kasani mazan nan duk suyi ta kallon mutum, harda notes suke aiko min wai ya sunana kuma in basu phone number,har mamaki nakeyi wai su meh suka gani da , Arghhhhh hubbby" ta fara kokarin kwace hannunta daya damke,

"Meh yasa baki fadamin bah tun ranar da abin ya faru, da ban bari kin cigaba da zuwa bah"
Shi da wasa ma yayi magana, amma ita ta xata da gaske neh Mom ta fadamai duk abubuwan da suka faru

"Ba ranar friday bane bah,kuma ai nace ni matar aurece,sune suka ki yadda, kuma sai Mom bata nan suke zuwa" ya daure fuska, kaman beh taba dariya bah,

"Tun ranar friday" ouchhh tayi tana makalewa a jikin shi,

"Hubby ni fah ba laifi na bane bah" ya kara matse mata hannu,har taji kwalla na son fitowa, sai lokacin taga ya kamata ta kwantar mai da hankali ba ta harzuka shi bah,

"Am sorry hubbby,kasan ur d only one for me, babu wanda ya isheni kallo sai kai, kuma duk lokacin nan missing dinka kawai nake tayi fah, kalli yadda na koma fah saboda kewar ka" ta turo baki tana fada da shagwaba,

"Duk ranar da wani yayi maki magana ki fadamin" tayi face din tausayi
"In kuma beh da ra'ayi akaina fah, tambaya zeyi" tayi magana tana turo baki,
" Husna! " ya fada da dan karfi, ita kuma ta daga hannu tana surrender, amma a boye dariya takeyi,
Fizgota yayi daya ga dariya takeyi, ba bata lokaci ya hada bakinsu yana mata wani hot burning kiss, a hankali ta rufe idanu tana Ajiyar zuciya,
'Duk abinda nayi maka beh sa kayi loosing control bah sai kishi, hmmmmm' ta fada a ranta,
Cire bakinshi yayi daga nata yana fidda numfashi sama sama,
"Dan Allah kar kiyi ciwon kai" 'Ayyah' tace a ranta duk matsuwar da yayi beh manta da ciwon kanta bah,

"Bayin kaina bane bah Ai" tana rufe baki yayi baya,

"Ya kamata musan abinyi Husna" ya cusa hannu cikin gashin kanshi yana kai da komowa,

"Karka damu da ciwon kan" ya tsaya amma beh kalleta bah,

"Taya ya zan iya yin haka" ita ta karasa kusa dashi,
"Yau kawai, in kaina yayi ciwo gobe sai musan abinyi"
He badly needs her, amma san kan nashi beh kai haka bah,

"No" ya girgixa kai yana kokarin tafiya,
Rungumeshi tayi ta baya da kanta kwance a tsakiyar bayanshi,

"What if ni nake bukatar ka hubby, sai ayi ya ya?" Ta fada da sanyin murya can kasa, yasan ba karamin kokarin tayi bah data iya bude baki ta furta mai haka,
Hannunta dake kirjinshi ya ja zuwa bakinshi yayi kissing, sannan ya dawo da ita gabanshi,
"Bana so in cutar dake Husna, yau kawai, after it saina tabbatar da ur okay" da kiss ta fadamai ta yadda da abinda yace,
Unlike dazu da komai hot hot, yanxu slowly amd leisurely suke yin komai.

Da safe data tashi baya nan sai tayi tunanin ya tafi wurin aiki, text ta tura mai sannan ta mike ta shiga bandaki,
Tsaye tayi da maganinta a hannu tana tunanin bari sai bayan kwana biyu, dan kar ciwon kai ya dameta, kuma tsoro take kar yazama useless in ta bari sai anjima,

"Wifey!" A tsorace ta amsa maganin na faduwa kasa, dukawa yayi ya dauki maganin,

"Oh God! Har kin fara ciwon kan" wani matsala tace a ranta, kar tace Eh ya jata zuwa asibiti,

"No wannan ahmmm maganin" ta tsaya tunani, shi kuma ya cigaba da karanta abinda aka rubuta a jiki,

"Wanda Mom ta bani neh, kasan irin maganin nan ana so ka sha har ya kare" ya daga kai yana ballan mata guda daya,

"Naji dadi sosai da kike kula da kanki, in ya ma kusan karewa" tace uhmmm tana karban wanda ya ballo da sachet din gabaki daya,
Beh tafi bah saida yaga tasha, bata taba jin zafin karyar da takeyi mai bah irin na ranar,

"Yau bazan je office bah zan tsaya in ga in kanki zeyi ciwo" kokarin sashi ya tafi tayi amma ya ki,

"Toh ni bari inje in dafa manah abinci" yace toh yana mikewa saman gado,

Panadol extra da green tea din ranan nan ta sha ovet dose, sannan ta fara dafa abincin,
Duk bayan minti 30 yake zuwa yaga if everything is okay,

Har dare yayi bataji koh alamun ciwon kai bah, dan haka yace su sake testing a ga koh zatayi ciwon kai gobe, ba wani dar dar tace toh dan tasa a ranta baxata sha maganin bama gobe,

"Kin tabatta ba ciwon kai har yanxu" tayi yar dariya,
"Akwai yanxu, zaka dawo neh?" Ta fada da wasa,

"Da gaske, bari inzo muje asibiti" dariya tayi sannan tace tana zuwa,
Picture ta dauka dan tasha kwalliya da smoky eyes sannan bold red lips sai ta turamai,
"Lfy ta lau,amma in ka dawo da wuri zan maka sabon kwalliya, ma idanun ka kadai"
Ya jingina da kujera yana jujuyata,

"In abinda yafi kwalliya nakeso fah" uhmmmm tace kafin tayi magana,

"Saika dawo da wuri, dan in ka barni ina jira zan iya canza ra'ayi" shima yace hmmmm
"Kodai ki kagu da son gani na" tayi yar dariya
"Na rigada na kagu in ganka mah, amma zan nemi abinyi dan kar tunaninka ya hanani sakat yau dinnan"
key din motar shi ya ja sannan ya mike tsaye yana dora coat dinshi saman kafada,

"My oh my oh my, anya da Cara Mia dina nake magana"
Kiss tayi mai ta cikin waya,
"Ki tausaya min ki bari in dawo manah, kar ki gama dani tun anan" kunya taji ta kashe wayan tana boye dariyarta,
Hotonshi dake wallpaper dinta ta kalla kafin tayi kissing screen din,
"Love is sweet" ta rungume wayar tana mirginawa side to side,

Office din ya bari ya nufi motar shi,
"Gda zamuje sir" yace Eh
"Alfie mu cigaba da aikin a cikin mota" Alfie ya cigaba da binshi a baya, suna cikin aiki a office ta kira daya ji call din ba meh karewa bane bah sai ya fita,

"Mu tsaya a pharmacy lukman" ya fada yana duba calender din wayar shi, sannan ya cigaba da irga kwanaki a ranshi,

"Sir" yace uhmm, dan hankalin shi kwata kwata baya wurin aikin da sukeyi,

"Ina kokarin tuno wani abu neh" a wani babban pharmacy suka tsaya, dama ya rubuta sunan maganin a paper sai ya bayar kawai a siyo mai,

"Sir meh ze hana mu siyo maganin wanda yafi karfi" ya kalli Alfie,
"No wannan aka ce ta sha" Alfie ya kalli sunan jikin paper din,

"Ba wani banbanci ai, duk aiki daya sukeyi kuma dayan yafi kyau mah, 89.9 guarantee din bazata dauki ciki bah, wannan beh kai haka bah kaman"
Saurin dukar da kai yayi da yaga yadda ogan nashi ke kallon shi,

"Je kayi abinda na saka Alfie"
Sai bayan ya tafi ya samu word din ya daina mai zagaye a cikin kai,
'Hana daukan ciki, kodai ban rike sunan bah da kyau'
Ya fada dan kar ya yanke hukunci da sauri,
Hankalinshi beh kwanta bah har Alfie ya dawo, dan paper din dake cikin kwalin Maganin ya zaro, beh san sadda ya cukwikwiye paper din

Please Login or Register in order to submit comment