Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

Da gudu ya fada jikinta yana murna,
"I love you Mom so much" hankade shi gefe tayi,

"Kana neman karasa ni kana cemin i love you"
"Wasu dai basa taba girma" inji Haider da karamin murya,

"Ku taso mu tafi" Amyr yace Yanxu
"Gwara mu tafi yau kar tun kan gari ya waye yayi manah sammako"
Haider ya mike bayan ya gama magana,

Da katuwar sallama ya shiga gdan, kafin yayi knocking,
Amyr ya kalli Haider, shi kuma ya girgixa mai kai,

"Sorry kuna ta knocking, daga ni sai Asma'u kawai a gda, itama aikin bacci kawai take tayi"
Suka gaishe da Mama, bayan sun iso falo,

Barinsu tayi a falo ta shiga dakin Asma'u,
"Ki tashi kije kiyi wanka,sannan kizo ki kaima baki abinci in sun gama sallah" tace toh tana murza idanu,

Sallaya Mama ta kai masu kafin ta koma kitchen tana hada abinda za'a kai masu,

"Mama na shirya" daga sama har kasa Mama ta kalleta kafin tayi magana,

"Haka zakije koh yar hoda baki barbada bah, baki duk ya bushe kaman meh ciwon yunwa"

Lashe lebenta tayi tana kara murza man data shafa a fuska,

"Sallamu Alaikum" saida aka amsa mata kafin ta shiga falon, saida idanunta suka linka gurman su saboda mamaki,

"Ahmmmm Ahem" tayi gyaran murya
"ina kwanan ku"

"Kwana kuma" Amyr da tsokana
" Ahmmmm ina kwan ahmm, i mean ina wunin ku"
Haider ya kwaikwayeta kafin ya amsa gaisuwar,

Sai kakalo murmushi takeyi ga kunya ta isheta, bata taba zama da abokan nashi ta wuce minti daya bah,

"Ya hanya" ta tambaya tana aje tire din saman table,
"Hanya Alhamdulillah"
" yanxu in muka koma sai ki ga hanyar da kanki" bata san wayace Alhamdulillah bah, kuma wa yace zasu koma tare, dan ba kallon fuskar su takeyi bah,

Murmushi tayi tana jera masu kuloli saman table,
"Bakya da lafiya neh Husna" sai lokacin yayi magana bayan ya gama kallonta tsaf,
Ta kasan ido ta kalleshi kafin ta cigaba da abinda takeyi,

Sannu da kokari suka ce mata bayan ta gama komai ta mike zata tafi,

"Congrats bro, ka kusan zama Daddy" Ehsaas ya kalleshi yana cewa Meh kace,

"Ni kadai na gani kenan, komai na tattare da ita yana ihun am pregnant" beh gama rufe baki bah Ehsaas ya mike,

"Kai ina zaka je, yadai san nan gdan surukan shi neh koh" Haider ya jawo coolers yana son serving kanshi,

"Shi yama san meh hakan ke nufi"Amyr ya girgixa kai yana jawo side stool kafinnya dora kafa a sama,

Tana shiga daki ta dafe kirjinta saboda irin bugawar da yakeyi, a kasalance ta cire hijab tana zama saman gado,

"Husna" tana jun muryar shi ta mike tsaye, shigowa yayi yana kallon cikinta,

"Nasan kince ba kyason ki dauki ciki,plssa tunda wannan ya shiga kiyi hakuri zuwa lokacin da Allah ze sauke ki lfy sai mu san abinyi"

Hawaye ya cika mata idanu, sannan kuma tayi maths din taga da gaske ze iya yiyuwa tana da ciki,

"Dama asibiti nake shirin zuwa a cire min, amma tunda ka roka zan barshi"
Idanu waje, baki bude yake kallonta,

Kyaftawa tayi saboda hawayen dake barazanar tsiyayowa,

"Haba Ehsaas, kana ganin koh haihuwar abin ciki nah ze zama ajali na zan iya aborting dinshi" siririn hawaye yabi kumatun ta,

Hijab dinta ta figa zata wuce ta gefenshi,
"Ina zaki kuma" ya rikota,
"Ina ganin kaman baka shirya ganina bah har yanxu Ehsaas, zan tafi in baka wuri neh"
Da karfi ya jawota tana fuskantar shi,

"In ke ranki ya baci toh ni ince meh Husna,
Kin san irij yardar danayi da ke, koh a tunani ban taba kawowa a raina zaki oya fadamin abinda beh kai zuci bah balle kiyimin karya"
Ta dukar da kanta tana goge hawayen da suka ki tsayawa,

"Karki ga laifina in na kasa amincewa dake kaman da" wani irin radadi takeji a ranta, wanda bata taba jin irin sa bah,

Sai shakan iska takeyi dan kar sheshekar kukanta ya fito,

"Ina sonki Husna, ze dauki lokaci kafin in yi maki yardar danayi da,
Kin fahimci dalilina koh" ta daga mai kai gana dora hannu saman baki,

"Kada kiji shakar fada min komai matata, koma akan waye, ni zan san yadda zan bullo ma komai" ta sake cewa toh tana daga kai,

"Granny ma tace ki yafe mata" da sauri ta dago kai tana girgixawa,

"Ni batayi kin komai bah, Allah ya jikanta da rahama" yace Amin yana damke hannuwanta cikin nashi daya,

"Baki bani hakuri bah har yanxu" a hankali ta dago da fuskarta cike da hawaye tana mai wani kallo meh dauke numfashi,

"Yi Hakuri my king, my All, to err is human to forgive is divine, dan Allah ka manta da komai mijina, kaji koh".

Ya make kafada,

"Bakayi hakuri bah" ya daga kai,
"Mom cewa tayi in dawo dake gda" ta bude baki tana mai kallon mamaki,

"Banji kina cewa plss Ehsaas ka maida ni gda bah" rufe baki tayi tana dariya saboda yadda ya kwaikwayi muryarta,

"I miss that laugh, tare zamu koma gda koh" ta tsagaita dariyar tana dukar da kai,
"Husna" a sannu ta dago kai kafin ta kalleshi,
"Zamu koma tare" ta sake girgixa kai tana dukar da kai,

Yana nan tsaye yace ta matso, a hankali ta tako zuwa gaban shi, kafin ta karaso ya jawota yana hada bakinsu wuri daya,
Ajiyar zuciya sukayi su biyu, kafin suka zurfafa kiss din,
Silalewa yayi kasa yana daga mata riga,

"Meh kakeyi" tasa hannu tana maida rigarta, bige hannunta yayi sannan ya sake daga rigar ya bayyana cikin ta,

"San kai na gaisa dake sai ki hana in gaisa da Baby nah" hmmm tace tana shafa kanshi,

Yana dora lips dinshi saman cikinta aka bude kofa,
"Asma'u kin bar mutane____" washe hakora yayi bayan ya mike tsaye,

Saida Mama ta fita kafin ya bar dakin,

"Mu dama tafiya zamuyi in bamu ganka bah" shiru yayi bece masu komai bah, basu dauki lokaci bah suka ce zasu tafi,

"Har zaku tafi" yace ma Mama Eh yana kallon Asma'u dake bayanta,
"Gashi baban su beh dawo bah balle ku gaisa" yace bakomai,

"Asma'u tace bata jin dadi da mun koma tare da ita" Mama ta juya gareta,
"Bata da lfy?" Tayi tambayar kaman tana jiran amsar da bata gamsheta bah,
Da gudu Asma'u ta bar wurin bayan itama ta watsa mai hararar wasa,
"Gata nan zuwa" Mama tabi bayanta,

Nasiha tayi mata meh shiga jiki kafin ta tayata shirya kayanta,

Da suka koma gda ma Mom tayi farin cikin ganinta, tun tana kaffa kaffa da ita har ta saba da kulawar da Mom ke bata,

"Wifey ina zuwa?" Ya mike tsaye
"Zamuje asibiti neh A.n.c"
Yace oh!
"Muje toh" baya taja tana ware idanu,

"Ba tare dakai zanje bah" ya daga gira shima,

"Muje daughter" sakin baki yayi da suka wuce shi kaman ba'ayi mutum a wurin bah,
Har cikinta ya tsufa kulluk da Mom suke zuwa asibiti, Dad mah ya kan zo Nigeria in ya samu time, Da ta Haihu Mom tace zasu tafi su barsu anan,

"Kayan wanki kika cunkusa a cikin ki" ta turo baki dan ba karamin nauyi tayi bah, gani takeyi kaman kullum kara girma cikin yakeyi duk da yakai wata na tara,

"Yama sunan abinnan da kika hana ni bacci akai" tayi murmushi data tuno, sashi gaba tayi tana kuka sai ya samo mata tsamiyar biri,

"Ai ba ni bace rigimammen babyn ka neh ai" yace like father like son,

Kwana biyu da wannan zance ta fara labor, taci azaba sosai, dan har ji takeyi kaman bazata rayu bah,

Bayan ta haifi baby boy dinta saiga su Ma'u anzo barka,
"Ban taba tunanin zanga ranar nan bah" Asma'u ta rufe fuska,

"Kyayi ki gama, azo a bashi abinci in gani Mama ta aiko ni dan in tabbatar da kin iya kulan mata da jika"
Labari suka sha kafin Ya Abba yazo daukan ta,

"Wannan anacin, shi dole sai nayi sharing wedding anniversary dina da birthday dinshi"
Asma'u ta kalleta ta gefen ido,

"Ban manta da bikin ki bah, ba sai kin tuna min a kaikaice bah" Ma'u tayi dariya
"Gwara ma dai ki sani, ke babbar kawar amarya ce, kuma kanwar ango"

Ranar suna aka rada mai Mustafa, amma ana kiran shi da khalifa,

"Wifey" da dare neh taci kwalliya ta kashe dauri, haka khalifa mah tayi mai das das,

"Fushi kikeyi dani har yanxu" ta kara cuno baki
"Ba kaki bari in zauna a gda bah" yayi yar dariya,

"Mon ta tafi fah, haka kikeso mijin naki ya zauna a gda shi kadai" ta turo baki tana gunguni,

"Haba wifey kin san sanki neh yasa na kasa amincewa da zaman naki a gda" yasa kanshi wurin wuyanta yana shakan kamshinta,
Da wasa da wasa kuma ya fara neman wuce gona da iri,

"Hubby" yace uhmmm,
"Ba zamu iya yi yanxu bah" ta fada da kunya cikin muryarta,

"Uhmmm" beh tsaya da abinda yake yi bah sai gaba da yayi,
"Hubby" ya matsa baya data sake kiran shi,
"Sai mu canza daki ai in saboda khalifa neh"
Girgixa mai kai tayi,

"Kwana Arba'in ka manata" ya dan tsaya kaman mind dinshi na processing wani abu,
"What!" Ya fada da karfi, har khalifa yayi motsi,

"Ughhhhhhh wifey zan mutu kafin lokacin" dariya tayi tana janshi su bar dakin, wani dakin ta kaishi,

"Karka kara kiran min mutuwa" sannan ta hade lips dinsu wuri daya,

"Wace irin mace zan zama in na bari ka kwana a takure" ya daga gira daya da ya ga ta duka tana kwance mai belt,

"I like where this is going" wani siririn dariyar tayi kafin ta cigaba da gashi,

Basu san da meh gobe ze zo masu bah, saidai sun san in suna tare to ba matsala, one step at a time har komai ya zama normal,

Zance they lived happily ever after duk da after din beh zo bah tukunna,
Bissalam,



The End🍾🍾🍾🍾🍾🍾🍻🍻🍻🍻πŸ₯‚πŸ₯‚πŸ»πŸ₯‚πŸ»πŸ₯‚πŸŽ‰πŸŽŠπŸŽ‰πŸŽŠπŸŽ‰πŸŽŠπŸŽ‰πŸŽŠπŸŽ‰πŸŽŠπŸŽ‰πŸŽŠπŸŽ‰πŸŽŠ.

Anan wannan littafi yazo karshe, Allah yasa akwai abinda muka amfana dashi kuma akwai darasin da muka fadakar akai,
Kamar yadda kuka sani wannan kashi na uku neh cikin Series dinmu meh take LOVE UNEXPECTED, (SO BAXATA).

Na farko cikin series dinmu ATSAKANINMU,
2. NI DA BODYGUARD DINAH,
3. BOYAYYEN KUDIRI,

SAI KUN JIMU AFTER SALLAH IN SHA ALLAH DA SABON LABARI MEH SUNA
πŸ…°YπŸ…°πŸ…°N.


Muna ma duk daukacin musulmai Marhaba da watan Ramadana, Allah yasa ayi azumi lafiya a gama lafiya, ya bamu ikon yin ibada yadda ya kamata, ya sa kar mu shagala mu bar falalan watan Ramadan ya wuce Mu,
Amin.



YOURS,
KHALEESI and NOBLE JUDGE.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment