Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yasa kuke neman shi, our grandmother wants to know" datace our grandmother sai ya tsaya yi mata kallon mamaki

"Your grandmother?" ta daga kai
"Eh, he's my cousin"
Dan matsawa baya yayi sai driver din ya matso kusa dashi

"Kar ka bari securities din su karaso nan" ya rada
"But sun kusan isowa sir" ya kalli driver din

"Okay bazan bari su karaso bah"

Dan gyara suit din jikin shi yayi sannan ya koma inda take tsaye

"Ba karamin journey mukayi bah,koh zan samu ruwa in sha"
Hannu ta daga mai

"Give me a minute" ta juya ta koma cikin gda bayan dan lokaci kuma sai gata ta dawo

"Tace ka shigo ciki" yabi bayanta

Hannu ya mika mata sannan ya fadi sunnan shi
"Suna na Ehsaas Mas'ud"
"Oh! Sorry" yace dayaga ta kalleshi sannan hannun.
"Dan Allah ko zan samu ruwa in sha, tun da safe muke kan hanya" ta nuna mai kujera tacw ya zauna
"Kaka ruwa yakeso yasha" kaka daibaikin kallonshi kawai takeyi

"Toh je ki siyomai pure water manah"
Kallon shi ta karayi sannan ta dubi ka
"Shine yazo da motar can fah, ni bana ganin ze sha pure water"
Kaka ta dago tana dubanta
'Dama na tafi bace komai bah' ta dukar da kai

"Ai bani na gayyato shi bah, karshe mah in bashi ruwan randa" tana dan kallan gefen da yake zaune taga yayi murmushi

"Ruwan gora za'a siya mai kenan, toh je ki dauki kudi ki siyo mai, kodan inji dadin shawo kansu in mutuci suka zo ci wa jikana"


Cikin gda ta shiga ta barshi da baba, beh san abinda zece mata bah kuma koda yana da abin fada bah jin abinda yake cewa takeyi bah.

"Excuse me, I'll just go buy you the water"
Ya mike tsaye

"No lets go together" ya fada mata
"Zanje siyo maka ruwa ne, ka jira ni ina zuwa"
"Zan iya binki, ina jin kishir ruwa sosai"

Yama rigata fita waje

"Baba wai ze bini"
"Toh amma, ki kula sosai dan bamu san da wacce ya zo bah, kiyi kokarin bugun cikin shi kiji abinda ya kawosu"

"Toh, yan xun nan mah zamu dawo"

Saiti da juna suke tafiya duk yadda taso ta wuce gaba ya kasance yana binta a baya sai taga ya cimmata.

"Am sorry, i made you come out. I have water but it's in the car"
Ta girgixa mai kai alamun bakomai


"Ya sunan ki" ya tamabaya kan han yarsu na komawa gda.

"Kasan salisu ne" ta tambayeshi, murmushi taga yayi.

"So you won't tell me your name" ya fada da murmushi

bayan sun dawo an bashi wurin zama kaka ta tambayi abinda ke ci mata tuwo a kwarya


"Meh yakeso Asma'u, inji dai bah saleh na yake nema bah"
Tayi ajiyar zuciya

"Eh baba shi yake nema"
"Nan ne gdan su, meh ya faru?" kallonsu yayi su biyu zaune kasa shi ke zaune saman kujera kwaya daya dake cikin parlor din
"Ku yan uwanshi ne?"

"Eh, ita kakar muce, ni dashi cousins ne"


Ajiyar zuciya yayi, sannan ya kallesu da yanayin lyf dinsu,
Kara jadda da shawarar shi na kin sawa a kama su yayi,

Kama su a kulle zefi sauki wajen sawa thief din ya dawo gda,
I can't destroy the happiness of such innocent family bcos of his mistake, I'll find another to capture him


"A gidanmu yake aiki, naji ance kaduna yake zama shine dana zo nake son ya dan cigaba da yimin aiki duk da hutu aka bashi"

Kakarta yaga tayi ma magana wacce ta washe baki sannan tayi magana.
"Baya nan ya tafi yin wani aikin Lagos mah yace mon zeje, kuma tana so tasan in yana aikin shi yadda ya kamata".
Ya murmushi yana gyada kai


"Sosai kam, ya san aikin shi, that's the reason why am seeking him out"
Ta fadama kaka sannan ya sake magana

"When is he coming back"

"Kakata tace ze dawo nan bada dadewa bah saboda wani abu da zasuyi" bata fadamai cewa abin auren su bane.

"Auren zumunci za'ayi musu, tun daya sata a ido ya ke cewa Asma'u matarshi ce".

Kaka ta fada da farin ciki shi kuma Asma'u ya kalla dan ta fadamai abinda tace

"Ahhmmm, cewa tayi zaka dade anan garin ne"
"Tare zamu tafi dashi in ya dawo" ta kalli kaka

"Yace Allah yasa Alkhairi, kuma tare zeso su koma in ya dawo daga tafiyar da yayi"

"Ba matsala, kinga in zasu tafi saki bisu babu wani gayya"


"Tace ba matsala, zaku iya tafiya tare"
"Toh nagode, ni zan wuce"

Har bakin kofa ta rakoshi inda driver dinshi ke tsaye

"Tnk u" tace bakomai

Tana komawa cikin gda taji kaka na fadan irin kudin da zasu samu daga wurin bakon daya fita

Girgixa kai kawai tayi sannan ta fito, suna bakin kofa har yanxu amma a cikin mota,

Yana ganin fitowarta da bag yace su tafi a hankali, tafiyar da takeyi kaman saman ruwa, hijab dinta har kasa koh takalminta baka gani, kadan daga cikin fuskarta ya gani, ko wani lokaci kasa take kallo, taki bari yaga kwayar idanta

Juyawa yayi yana kokarin ganin idanunta da suka zo wuce wa saitin ta, kaman yace driver ya kara rage sauri , amma yasan koh anyi haka baze samu damar ganin kwayar idan ta bah.


Lot's of love 😍😍😍 for taking your time to read, tnx
[3/9, 10:57] β€ͺ+234 706 870 0853‬: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI
KHALEESI,
NOBLE JUDGE.
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’


1⃣0⃣.


Gdansu Ma'u babban gda ne meh jama'a cike,babansu mata hudu gareshi da yara dayawa

Ba'a tashinta sallar subhi dan da lokaci yayi take farkawa, amma a gdansu Ma'u tun kafin ta farka kacaniyar yara ya tada ta

"Meh zakiyi?" Ta tambayi Ma'u bayan sun yi sallah

"Meh hawa saman gado yayi miki kama da" ta fada ta murmushi

"Yayi min kama da zaki koma bacci"
πŸ‘πŸ»

"Kin canka daidai" ta ja bargo ta lullube

"Aikin gdan fah? Sai yaushe" ta bude ido tana kallonta,sannan ta kunna fitilar wayarta tana nuna mata agogo

"Kin daiga tym koh,gwara mah ki koma baccin ki"

Fitilar dakin ta kunna wanda Ma'u ta kashe bayan sun gama karatun Qur'ani,

Tasan bata kyauta bah in ta tsallake gdan nan ta nufi gdansu taya mamanta aiki, shi yasa takeso suyi na nan da wuri kafin ta tafi can

"Ni dai zuwa zanyi in fara aikin,kuma kema bazakiyi baccin asaran bah" tayi kaman bataga irin kallon da Ma'u keyi mata bah

"In gari ya fara wayewa ba baccin asara bane bah" ma'u ta fada da karfi bayan Asma'u ta fita

Ta dade tsaye a tsakar gda tana jiran taji alamun mutum,amma duk yan gdan sun koma bacci, sai ta nufi kitchen ta fiddo kayan wanke wanke sannan taja ruwa daga rijiya tazo ta fara,

Tana gamawa kuma ta hau sharan tsakar gdansu wanda babba ne sosai, yayi biyun na gdan su

"Asma'u kece ke shara" ta duka a inda take tana gaishe da maman Ma'u

"Lfy lau Asma'u, ni dama nasan badai Ma'u bah, tana can tana bacci koh"

Kaman tasan abinda maman Ma'u ke shirin yi tayi sauri ta bita dakin

"Mama, ki barta kawai ni nasa kaina ai" amma sai da ta tafka mata bugu

"Kin bar bakuwa tana aikin gda ke kina nan kina minshari, koh kunya bakiji bah"

"Mama ai ni ba bakuwa bace bah, nan ma ai gdan mu ne" Mama ta juyo kanta

"Duk da haka ai beh kamata ace ta bar maki aikin gda bah" ta harari Ma'u

Ma'u mah ta harareta bayan Mama ta fita

"Kinji dadi koh" ta hada da murguda baki

"Haba namecy kema kin san banyi dan aga laifin ki bah koh"
Batace mata uffan bah sai faman hade rai da takeyi

"Ina so inje gda in taya mama aiki ne, kuma ba dade in bar nan inje can yin aiki, shi yasa na fara anan"

Mau ta sauko kafafu daga saman gado

"Nasan yanxu ai mama tama gama aiki,tunda 8:30 ake nema" ta kalli agogon jikin bango

"Amma zamuje, bari in ga meh za'a karya dashi" ta fita daga dakin sai lokacin ta duba wayarta tunda ta tashi

"Su yaya Abba anyi kewata kenan" taga missed call din da yayi mata wuraren 11 na dare

"Meye wannan kuma Ma'u, mu dake sauri"
Ma'u ta aje wani roba meh dankalin turawa a ciki

"Kema dai kinsan mama ta gama aiki yanxu koh, shi yasa naga gwara mu soya wannan sai mu kai mata" dan murmushi tayi kafin ta fara tayata ferewa

Basu suka gama komai bah sai wuraren karfe goma,shi yasa suka hada da wanka kafin sukayi shirin fita

"Karfa ku dade Ma'u, kin san yau zaku shiga kasuwa koh"

"Koh kuma mu wuce daga can" ta fada tana kallon Asma'u da tayi kaman bataji meh suke fada bah

"Zamu wuce daga can Mama, ki fada manah abubuwan da za'a siyo" matsawa tayi daga gurin tayi kaman tana wani important abu da wayarta

"Kinji da wannan shirmen naki, wai ke kunya,zanga ta karshen kunya in muka ajeki a gefen gado"

Gabanta beh bar bugawa bah akan abinda Ma'u tace har saida suka je gda

Nan mah gabanta kara faduwa yayi da suka ga gdn a kulle da πŸ”’

"Calm down Asma'u, nasan bakomai mah in shaa Allah"

Suna nan tsaye a bakin kofa Ma'u na kira da wayarta dan garin sauri ta yarda tata kuma taki kawowa

"Yaya Abba zaki kira,wayan yay Mukhtar kullm silent" ta hada kai da Ma'u tana kokarin jin abinda ake cewa

"Ba'a dauka bah" ta cire wayan daga kunne tana kallon ta

"Ki kwantar da hankalin ki, bari in shiga gdan makotan ku"
Kafin Ma'u ta karasa maganar ta nufi hanyar gdan

Kwan kwasawa ta hauyi tana sallama

"Ina wuni, dan Allah koh mamana ta fada maki inda zataje"

Ma'u na bayanta tana trying numbers din yan gdansu amma duk shiru

"Tun da safe gdan ku yake kulle,kuma babu wanda yazo tun dazu"

Ma'u ta dafata dan ta kasa mikewa tsaye sosai, har ta fara kuka

"Bari in cigaba da kira, kin san meh muje wurin kaka kila ta sani" ta mike jiki ba kwari suka taka zuwa gdan kaka

"Daga asibiti nake nima, ciwon ciki ya turnuke mamanki da daddare, yanxu an turasu wani asibitin kudi ne, shine babanku yazo neman aran kudi"

"Yi hakuri Asma'u, nasan taji sauki" suna fitowa daga gdan ta fara kuka

"Bari in fadama Mama mun tafi asibitin" ta aje warmer din a kusa da inda take tsugunne

"Mama tace muzo mu daukan masu abubuwΓ n da zasu iya bukata"

"Ni dai asibitin nakeso in je" Ma'u ta dafata

"Ki bari mu tafi tare" ta girgixa kai

"Toh bari in karbo ruwan zafi da abinci, kafin ki samu adaidai ta" ta ruga da gudu tayi gdansu

Ita kuma tana tsaye tama kasa daga hannu ta tsayar, har saida Ma'u ta dawo sannan suka tafi tare


"Oww" ya dafe hannun data dukeshi

"Bamu fito da waya bah" ya mata bayani data ki dauke ido daga kanshi

"Mama fah?" Ma'u ta tambaya,sai ta bi bayansu ta kyale Abba

"Baba" suka gaishe shi da karamun murya dan Mama bacci takeyi

"Kar gadon da aka bata ya tsorata ki Asma'u, zataji sauki in shaa Allah" tayi kokarin share hawayenta da suka ki tsayawa

"Meh suka ce ke damunta" Ma'u ta tambaya

"Ciwon ciki,ashe ya dade yana damunta na jiya ne dai ta kasa jurewa"

Sabbin hawaye masu zafi suka sake ziyartar kuncinta

"Anjima za'ayi scanning da tests"

Da kyar suka shawo kan Asma'u ta daina kuka

"Baba tunda muna nan,kuje gda ku dan huta manah kuci abinci" Asma'u mah ta daga masu kai Alamun Eh

"Kar a bukaci wani abu" Ma'u ta dage har saida tasa suka tafi

Ba'a jima bah mama ta tashi daga bacci, wani kuka marar sauti ta far

"Ni dama nasan kina nan kina sana'ar taki" mama tayi karfin halin tashi zaune

"Sannu Mama,bari in kira nurse" mama ta girgixa mah Ma'u kai

"Barshi kawai Ma'u, bana bukatar nurse yanxu" Asma'u tayi karasa kusa da ita

"Da gaske babu inda keyi maki ciwo" mama ta ansa da murmushi

"Dan ciwan ciki ne, ba wani babban abu bah" Asma'u bata gamsu bah saidai tayi shiru

Saida aka basu go ahead din bata abinci sannan suka zuba mata taci, bayan tayi sallah kuma ta kishin gida saman gado

"Kaman kece meh ciwon,hala koh abincin safe baki ci bah"
Ma'u ta amshe

"Allah yaso taci na safe, badan haka bah nikam nasan da bazataci abinci duk yau bah"
Asma'u tayi kasa da kai

"Amma zansa taci abinci in muka koma gda" Ma'u ta fada

"Mama ni anan zan kwana" Mama ta girgixa kai dan dama tasan sai anyi haka

"Toh Asma'u, amma sai kinci abinci tukunna" babu wani musu taci abincin sama sama

Kafin ta gama mah har maganin da aka ba mama ya fara aiki tana bacci

"Ciwon ciki kawai ke damunta sukace koh,toh me yasa suka bata gado" ta tambayi Ma'u bayan suma sunyi sallah

"Shi yasa suka bata gado kuma zasuyi mata test, dan su san meye matsalarta"

Tayi mata bayani a hankali kaman yadda zatayi mah dan shekara uku,

"Kin gane abinda nake nufi"
Ta kara magana irin na da

"Na gane" ta dan tureta


"Asma'u kuzo ku tafi gda manah dare nayi fah" Bata motsa daga inda take zaune bah har abin yaba Ma'u dariya

"Ke ni dai in zaki tafi ki taso dare yayi,kuma bana san yawan daren nan"

Kaka ta fada, dazu da Baba ya dawo tare suka zu

"Mama tace wai in kwana anan"
Ta fada kai kasa, dariya mahaifinta yayi yana tasowa

"Ba yau bah toh ki bari sai likitocin sun gama dubata" ta dan bata fuska kaman zatayi kuka

"Dama bada ku nazo bah" kaka ta mike
"Sai na dawo gobe Allah ya kara sauki" kaka ta fita

"Tashi manah yar albarka, kin san tana bukatar kulawa"
"Ai nima zan iya kulawa da ita"

"Sis mutafi koh" Mukhtar ya shigo daidai lokacin

"Kaka tana waje kar ku barta tana jira, tashi yar Albarka"

Tana mikewa Ma'u mah ta tashi tana tattara abubuwan da suka zo dashi


Suna isa kofar gdan kaka suka iske yaran makota zaune kusa da gdan suna wasa, da yake akwai wuta kuma da hasken farin wata,

"Kaka dazu wasu suka zo neman ki"
Basu tsaya baya ya juya dan kai su gda


"Yanxu haka ya sanar dasu ne suka gudu"

Ehsaas ya nutsa cikin tunani

"Twice fah muka je gdan kulle, something is not right"

"I agree something is not right, but i don't agree that the ran away"

Simplicity din life dinsu yake hangowa, da calmness hade da shyness din yarinyar, shi ya tabbata baze hada baki dasu bah

"We'll go back tomorrow, am sure there's an explanation"

Duk yadda driver dinshi yaso convincing dinshi akan guduwa sukayi ya kasa yadda

"Kuma kace har yanxu wayarshi a kashe yake" ya tambayi driver din

"Eh,kuma babu wani news daga police din, duk inda yake zuwa baya can"

Lokacin ya tuno cewa kakar tace zeje lagos yin wani abu

"Alert the police force in Lagos"

Yana san ayi komai ba tareda ya tada mah bayin Allah nan hankali bah,

Komawa yayi ya zauna saman gado, hannu ya daga alamun yana son abu sai ya girgixa kai

Ya saba ana attending to his needs 24/7, gashi yanxu komai ya subuce mai dan beh saba bah.
[3/9, 10:57] β€ͺ+234 706 870 0853‬: [1/30, 2:55 PM] KHALEESI🎭: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI
KHALEESI,
NOBLE JUDGE.
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’


1⃣1⃣.


Bada san ranta bah suka jira har sai past 10 kafin suka fito daga gda,
Dan mahaifiyar Ma'u ta dage da abinci zasu tafi, taso gari ya waye tana tare da mamanta

"Allah mun gode maka,yau ga namecy tana wuce ni a tafiya"
Asma'u ta bata fuska

"Naga ke ba sauri kikeyi bah ai, gashi kuma sai mun jira ya Abba, ni dama ya bari munzo da kanmu"

Ma'u batayi kokarin cin mata bah dan tasan jira zasu tsaya yi

"Sai kiyi sauri ai gashi nan ya karaso" Ta fada tana barin inda suke tsaye tana cigaba da tafiya


"Ta yaya zanyi sauri kin ki tayani daukan basket dinnan"

Komawa baya tayi ta karbi basket din gaba daya, daidai lokacin motar su Ehsaas ta shigo layin

"Stop d car" ya nuna ma driver wata tana tafiya

"Ga yarinyar can" driver din ya sauke glass dan ya ganta da kyau amma tasa kai cikin napep sannan ta shiga

"Ze iya zama watace sir" Ehsaas ya girgixa kai

"Follow them " yace dan baze manta yadda take tafiya bah duk da yau kaman cikin hanxari take


"Yaya ya jikin Mama?" Abinda ta fara tambaya kenan suna shiga cikin napep din

"Da sauki sosai, Ma'u?" Itama din bata gaishe shi bah,amma da yake sun saba tsiya shida Ma'u ita yayi ma alama data gaishe shi

"Nikam tun jiya nakeso in tambaya,wai baka share napep dinnan ne koh yan aikin jan kasa kake daukowa"

Girgixa kai tayi dan yanxu zasu fara, duk da kaman yadda take girmama duka yayyanta haka Ma'u take girmama su

"Aa yan kauye nake daukowa masu noma" Ma'u ta daga kai

"Au koda nace" kafin ta karasa ya cigaba

"Yan kauye irin ki bah, yanxu wake yayin wani jagira a fuska" gani tayi Ma'u na hura hanci

"Kowa ya kalleni yasan ina da gashin gira na isashe kawai dai tsautsayi ne".
Dariya ya Abba ya hauyi mata, itama Asma'u badan akwai abinda ya dameta bah data tayashi

"Kina nufin garin neman kiba kika kwaso rama"
Taba girar tayi inda taje a daidaita mata su sai aka samu matsala aka kwashe karshen girarta daya


Suna shiga dakin da aka kwantar da mamanta ta karasa ta rungumeta tanayi mata ya jiki

"Jiki yayi sauki Asma'u, koh baki lura bah" murmushi tayi dan tana shiga ta lura da da sauki a tattare da mamanta

"An kusan sallamar mu kenan koh" Maman ta daga mata kai

"Anjima in shaa Allah" Muryar Babansu ta jiyo daga waje yana magana

"Bari inje kila da likitan suke magana" ta fita dan tana san taji hanyayoyin da za'a bi wajen kula da mamanta

"Bari in tafi Baba" tana fitowa ya Abba ya juya ze tafi,tana gaishe da Baban su ta bi shi

"Yaya Abbah ina zakaje,bazaka shiga kaga mama bah" dan dafota yayi


Ehsaas da shigowarsu kenan da driver ya gansu tsaye tare da hannun wani bisa kafadunta

"Waye wancan kuma?" Ya tambayi driver dinshi

"1 minute sir" driver din ya bar wurin yayi taking style ya tsaya kusa dasu Asma'u,

Saida ya Abba ya tafi kafin nan ya koma wurin Ehsaas

"Ina ganin brother dinta ne,naji tana cemai yaya" Ehsaas ya daga kai alamun ya cigaba

"An kwantar da mamanta a asibitin ne, yayanta kuma zeje wurin aiki ne"

Ehsaas ya kalli wurin,ko ba'a fadamai ba yasan asibiti ne nan,

"But meh yasa basu kaita asibiti meh Amenities standard bah, nan koh sanitation dinsu is questionable" ya bata face yana dan kare hanci

"Sir kudin da aka chaje su anan mah yafi karfinsu,balle suje wanda yafi wannan"

"How did you know?" Ya tambayi driver din

"Yanxu naji yayanta ya fada cewa kudin biyan bills dinsu zeje nema,dan anjima za'ayi discharging mamansu"

Wayar shi ya fiddo kuma ya maida aljihu dan koh yaje wurin biyan bill din beh san abubuwan daze yi bah,

A rayuwarshi beh taba biyan kudin wani abu da kanshi bah,dukka da da kudinshi ake biya,
Amma wannan hakin ya rataya akan wuyan masu yimai aiki

"Lets go and take of there bill" yayi gaba driver din biye dashi

Suna zuwa wurin cashier sai yaba driver dinshi wuri

"Tell her What we want to do"

"Daki da kuma sunan patient din?" Aka tambaya sai suka kalli juna

"You know what, why don't i leave the money with you,if the person whose bill i want to pay comes here, he'll tell". Ya nuna driver dinshi

" then you tell them it's been taken care of " matar ta daga kai alamun toh

Shi kuma yayi murmushi sannan yasa hannu cikin aljihu

"Oh no" yace dan yasan yana da wallet

Please Login or Register in order to submit comment