Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zama" yadda yayi tambayar yasata dariya

Shima kuma yayi,

"Naji gdan naku mah shiru" dan bin dakin yayi da kallo,

"Sun san ban ciki fitowa bah ai kullum aiki nakeyi,

Amyr mah ba nan yake zama bah,
Hannah kuma sai in na ganta"

Dago da fuskarshi tayi

"Ya jikinka? Kana fama da wani ciwo ne har yanxu?"
Kai ya girgixa mata yana daga wandon shi sama, kafar da aka samai ya nuna mata,

"Ana ta improving dinsu, kuma ana canza min lokaci lokaci,

Ba karya bana sanshi, but yafi zama a wheelchair"

In yana tafiya babu meh ciwo ba kafar shi ta asali bace bah, sai lokaci lokaci kuma akan ji dan creaking sound in yana tafiya,

"Meh ya hana ka kara aure Yarima"

Tashi tsaye yayi, yana dafe kanshi,

"Aafiya ta riga mu gdan gaskiya,
Haka AAYAN ,
dan Allah ka tausayawa halin da kake ciki, kana bukatar wanda ze kula da kai"

Jikinta yazo ya kwanta ya fashe da kuka, beh sakaya komai bah koh ya hana wani sauti fita,

Kuka yayi meh isarshi, yaci ya koshi kafin ya bari dan kanshi,

"Kayi hakuri Yarima" ta shafa kanshi, shi kuma sai huci yake yi,


"Ina kewar matata da danah umma, ina ji a raina suna raye, somewhere"
Yadda ya tsaya saika rantse hango su yakeyi

"Da nan ne farkon inda Aafiya zata nufo, da Allah yasa ta rayu a wannan hatsarin"

Zaune ya tashi yana karasa share hawayen shi

"Zanji saukin komai yanxu, tunda kina tare dani umma"

Murmushi tayi tana shafa kanshi

"Dan Albarka, sai ka dinga zuwa kana ganina koh,

Har Safiya ta huce"

Dariya yayi yana girgixa kai

"Zanzo in ganku in shaa Allah"

Har bayan isha da aka zo daukan ta bataga Hannah bah,
Bata tambaya bah kuma babu wanda yace mata gata,


"Sannu da zuwa" ta duka ta kwashe takalman daya cire, sannan ta dawo ta tayashi cire rigar sama watau coat din,

"Tnk u my cutie pie"
Ya manna mata kiss a kumatu,

"Kinyi missing dina yau?".
A kunyace ta ansa mai da eh

"Da gaske" ya tunkareta har ya mannata da bango

Ta sake daga mai kai
"Irin sosai dinnan koh kadan"
Ta dan kauda kai da kunya cike a fuskarta,

"Nasan sosai ne mah" wani nauyin shi takeji in sun hada ido

Kokarinta ta kwace kafin ya kafeta da idanun shi dake sa taji kaman tana nitsewa cikin teku,

"Bari in kawo maka abinci" ya girgixa kai

"Na rigada naci" ya make murya kaman yasan yanayin da yake jefata ciki,

"Husna, meh yasa kike wani dar dar dani,

Kina ganin wani abu ze faru tsakanin mu ne,

Kina so ya faru ne?"

Tayi saurin girgixa kai

"Meh nake nufi dana ce wani abu ya faru tsakanin mu"

Harga Allah shi kiss ne a ranshi, amma ita yasan tunaninta ya zarce hakan,

Kuma tunda hakan ta kawo a ranta, beh ga abinda ze hanashi zarcewa bah,

"Uhm hmmmm?" Harshen shi yasa yana wasa da kunnenta,

Data kasa hanashi sai tayi ta kame kame

"Kuma ina son inje gda" wannan kadai ya saurara,

"Gda kuma?" Ya tambaya da mamaki,

"Na dade ban gansu bah"

Ya jin jina kai,
Shi kullum yana ganin nashi iyayen,

"Da sharadi smoochsy pooh,

Zan barki ki tafi amma sai kin cika min alkawarin da kika daukan min"

Suna hada ido taga murmushin shi kaman harda mugunta a ciki,

"Wani Alkawari nayi?" Ta tambaya a hankali

"This" ya dora hannuwanta biyu samman faffadan kirjin shi sannan ya fara sama da kasa dasu

"Kyan alkawari cikawa wifey, u promised me a shower, ni ban manta bah"

Uhmmm hmmmm, ya hada da rausaya kansa,

"Ni, uhm uhm" ta turo baki, take ya matsa baya

"Ba matsala" ya daga kafadun shi,

"Amma karki ga laifina in na hanaki zuwa,

Dama in kikayi min sai in samu abin debe min kewa harki dawo, amma tunda bakyaso kije _____"

Gabanshi tazo tana hura hanci

"Saina bada cin hanci kenan kafin in tafi"

Ya sake yar guntuwar dariya yana mamakin canzawar ta

"Ba cin hanci bah wifey, agaji zaki bayar,
Amma sai in kina so, komai sai da niyya ai"

Bandaki ya nufa yana yin yar waka,

Tsaye tayi tana bin bayan shi da kallo har ya shiga



"Karki jira sai mijinki ya saki abu, bakaman in kin san yana son abin,

Maza nasan a nuna musu sunfi kowa mahimmanci, abinda suke so shi za'ayi

Kar kiyi korafi in ya juya maki baya koh ya daina bi ta kanki ya auro wata, meh riritasu suke so, wacce ta damu dasu,

Ke kau sai ya nema koh ya tambaya, kafin kiyi mai,wani lokacin mah sai kin bata mai rai,

Gani zakiyi kin dage kin zake wajen nuna mashi shine na daya a wurinki, babu kowa a gabanki in yana nan"

Tsaki tayi tana cuno baki,
'Wai meh yasa nake tuno surutan Ma'u ne, bayan banyi tunanin na saurareta ba mah'

Ta kara yin wani tsaki,

Hanyar bandaki ta kalla, ajiyar zuciya tayi sannan ta bar kafafunta suka jata zuwa Bandakin,

A hankali ta kwankwasa kofar,
Sake knocking tayi a hankali,

"Come in wifey" zaune ta ganshi gefen kwamin wanka koh kayan shi beh cire bah,

"Ya akayi" ya mike tsaye yana bAlle botir din rigarshi,

Kokarin nuna mata yake kaman ba komai beh wani damu bah,

"Kayi hakuri dani pls, karka daukan a matsayin matar da batayi ma mijinta abinda yakeso,

Kayi min uxuri na karshe, bazan kara yi ma musu bah"

Kyaleta yayi yaga karfin data ba kalamanta,

Ba karamin mamaki yayi bah data rabashi da kayanshi, sannan ta kalleshi da murmushi a fuskarta,

"Wankan kwanciya bacci zakayi, koh wankan huta gajia"

Kai kawai ya daga mata, okay tace kafin ta kunna ruwan zafi dana sanyi yana zuba cikin kwamin wankan bayan ta toshe magujin,

Kokarin nuna mata yake kaman abinda takeyi mai beh wani dameshi bah

"Gashi kafin ya taru" ta mika mai towel
"An gama" da kanta ta jawoshi zuwa bakin kwamin,

"Towel pls" ya cire ya mika mata, shiga ciki yayi ya zauna,

Sai data tabbata yana cikin ruwan meh cike da kumfa sannan ta maida dubanta gareshi,

"Kaji gajiyan na ragewa" ya daga mata kai a hankali,

"Yayi kyau" shampoo ta dauko ta wanke mai gashin kanshi,

"Ruwan ya fara sanyi, mu tafi hakanan" ya girgixa mata kai,

Murmushi meh dauke da kunya tayi mai,

Tana nan zaune daga gefenshi, a hankali kuma tana zuba mai ruwan a jiki,

"Muje hakanan, ruwan yayi sanyi" ta juya mai baya dan dauko towel,

Sa'in data juyo ya fito daga kwamin wankan, idanunta ta kafe a fuskarshi, koh kyaftawa batayi,

Tnk u yace mata daya karbi dan babban towel din ya daura a kugunshi,

"Akwai dan zafi yau" ta ajemai dogon wando na bacci sai singlet,

Yana zaune gaban dressing mirror inda ta aje bayan fitowarsu daga bathroom,

"Ni bana son takura in ina bacci" boxers din kawai ya karba,

Tana so ta san wani abu amma ta kasa furtawa,

Maida sauran kayan tayi, data fito yasa boxers dinshi,

"Ahmm, ahem" ya daga kai ya kalleta

"Ya akayi husna" ya zauna bakin gado yana kallonta,

"Akan abinda kace neh?" Ta kalli kasa tana wasa da yatsunta,

Girgixa kanshi yayi gameh da ajiyar zuciya

"Karki damu Husna zan samu lokaci sai in kaiki gda kinji" ya gyara pillow dinshi,

"Okay nagode, amma ba tambaya na kenan bah"
Saman gadon ta zauna kusa dashi

"Meh yake hanaka bacci?" Ya daga kafada kawai alamun shima beh sani bah

"Kullum in na tashi sai inga kaima idanka biyu"
Yar dariya yayi

"Ke kike tashi na, da 😴"
Ta bata fuska

"Bana minshari" tayi kokarin tashi,

Jawota yayi sannan ya rungumeta a jikinshi,

"Abinda ke sani nishadi kenan in na farka da daddare,

Husna kin takura ne?"
Sai ta daina mutsu mutsu ta zauna da kyau,

"Bayan shower dinmu na yau har yanxu kunyata kikeji"

Ajiyar zuciya yayi da bata ansa bah sai kokarin mikewa tsaye da tayi,

"Am sorry kana son wani abu ne" kallonta ya cigaba dayi data mike tsaye, har saida ta dukar da kai ta fara neman abinyi sannan yayi ajiyar zuciya,

"Babu abinda nakeso kiyimin husna, ni ke nakeso crème caramel "

Kamewa tayi kaman soja, koh numfashi bata fitarwa,fargaban abinda ze fada na gaba ya kamata,

"Ba abinda nake nufi ba kenan Husna, bawai bana son kasancewa dake bane bah,

Of course ina so, am a man for God sakes, amma aure ba jin dadi bane bah kawai, pleasure ne da kuma problems"

Fitar da numfashin da ta rike tayi hade da daga kai ta kalleshi a sanyaye

"Ina sonki Husna, kullum kara fadawa tarkon sonki nake, gani nakeyi kaman ke din IPhone ce kullum upgrading dinki akeyi, na yau yafi na jiya kyau, amfani harda tsada"

Misalin shi ya sa fara'ata ya bayyana ba tareda sanin ta bah,

"Haka abin yake Husna ba karya a ciki,

amma wani lokacin sai inga kaman duk abinda kikeyi min saboda igiyoyin aurene dake tsakanin mu,

Bakya sona?, kina sona?, abinda ke cikin ranki kike fadamin koh abinda nakeson ji?"
Ya kalli tafin hannun shi kaman list din abinda ya lissafo yake karantawa,

"Ni mijin ki ne, kina gudun bacin raina akan ki, kina gudun tsinuwar mala'iku,

Kaman shine dalilin daya sa kike maida min murmushi in nayi maki,

Kaman shine dalilin da kike yimin wasu abubuwan da bakyaso"

Sun dade a haka kowa na inda yake, babu wanda yayi magana,

Karshe daya sake magana saida ta dan tsorata dan bataji zuwanshi kusa da ita bah

"Do you love me Husna?"ya dago habarta dan su hada ido,

Tana kallon kwayar idanun shi ta kauda kai hade da matsawa baya,

Wani nauyayyen numfashi ya ja sannan ya fitar a gajiye,

Gado ya hau yana mai juya mata baya,

Da tunani ya barta tsaye,

'Ina son shi kuwa' tayi ta tambayan kanta,

Inda yake kwance ta kalla, ta yanke shawarwari dayawa da taji sun dace ta fadamai,

"Kuka kakeyi" ta dafashi, bayan ta haye saman gadon,

'Kanada gsky wasu abubuwan inayi ne kawai da kai mijina ne' ta girgixa kai wannan shawarar batayi bah, ta fada a ranta

Wata ta sake kakalowa,

'Duk abinda kakeso ina ina so, koh kuma ince meh yasa kake ganin haka'
Tsaki tayi cikin ranta,

"Na taki sa'a babba da Allah ya bani kai a matsayin mijina Ehsaas" ta sanyaya murya,

"Kana saurare na?" Beh bude ido bah kuma beh amsata bah, amma tasan yana ji

"Ina son in shiga cikin sahun mata na gari,
Ban san bacin ranka,koh kayi fushi dani,

Shi yasa koh bana son inyi abu zanyi maka, koh badan matsayinka na mijina bah
Koh da kyautatawar da kakeyi min"

Cigaba tayi da yayi shiru bah motsi kuma ba uffan

"Ina da aibu dayawa, am not flawless,
Amma duk da aibu na dinnan kana tare dani,

Shi yasa nake dagewa wajen yi maka abinda kakeso, bana son in kara ma kaina wani abinda zesa kaga flaws dinah"

Ajiyar zuciya tayi kafin ta fadi abu na gaba

"Watan mu biyar da aure, a kullum ina rokon Allah yasa kada in gaza wajen faran ta maka rai,

Ni kaina nasan na gaza wajen baka hakkin ka, duk ranar da nayi tunani akan hakan, bugun zuciyata na daban ne kaman ze bude kirji na ya fito,

Nasan bazamu zauna a haka bah forever, kuma bana so ranar tazo, ya zama kuma nayi disappointing dinka"

Sai lokacin ya bude idanun shi da yaji muryarta ta sarke,

"Husna!" Ya juya yana dubanta,
Goge hawayenta tayi sannan ta karasa fadan abinda ke cikin zuciyarta,

"Do i love you?" Ta tambaya a fili

"Basai kin amsa min bah wifey" ya tashi zaune yana riko hannayenta,

Damke nashi tayi itama sannan ta dora saman kirjinta,


"Meh ze hana mutum ya fada tarkon sonka, kai din 1 in a 1,000,000 ne, ni din nan stupid ce kuma kafi karfina"
Jikinshi ya jawota yana shhhhh

"Tun ba yau bah nasan ke daban ce husna, yarinya ce ke but kina da wayau"
Ya sa hannu yana share mata hawayen da suka tsiyayo,

"Meh ya samu lips dinki?" Ya dan daure fuska,
Daga share mata hawaye kuma ya bige da kallon lips dinta har saida ya taba,

"Bakomai" tasa bayan hannu tana goge bakinta,

Sai sannan taji ya bushe sosai,kaman zasu tsage

"Husna, zaki gama dani wallahi" ya mike tsaye yana kokarin janta

"Bakya yin sahur lokacin shan ruwa mah bakya cin komai"

Ta tirje taki tafiya

"Ina ci manah, wannan lip gloss kawai ne da ban shafa bah, shi yasa"

Ya dawo inda ta tsaya,

"Allah ina cin abinci" ta kara kwantar mai da hankali

"Ya akayi?" Ta dan matsa baya saboda kallon da yake mata, da wani murmushi da bata gane wani iri bane bah,

"Abinda kika fada dazu nake tunowa" tace inna lillahi tana dan kallon gefe

'Meh ze hana ka manta na furta wani abu'
Sannan ta dan dago ta kalleshi,

Hannayenshi ya mika mata, saida ta matso sannan tasa nata cikin nashi,

Dan jawota yayi, ya bari ta karasa takowa zuwa gabanshi,

"Caramel " tace uhmmm

"Am so sorry akan abinda ya faru dake,

Am sorry akan yadda kokarin faranta min da kikeyi yake tada maki hankali"

Shigewa jikinshi tayi, shima kuma yasa hannu ya kara kankameta a jikinshi,

"Caramel ina da wani shawara guda daya" ta dago ta kalleshi

"Kin yarda dani koh" ta daga mai kai ba wani bata lokaci,

Daukanta yayi chak bej ajeta ko ina bah sai saman gado,

"Relax matsoraciya" yace da yar dariya,

"Am serious sai kin kwantar da hankalin ki sannan zan fada"

Manyan eyes dinta dake kashe mai jiki kuma su dauke mai hankali ya tsaya kallo,

"


Kin san bayan amarya da ango sun tare, beh zama dole suyi consummating auren a ranar bath koh"

Ta daga mai a hankali,

"Zasu iya daukan lokaci dan su saba kafin a kaiga babbar harka koh" ta kara daga mai kai a hankali,

"Yanxu ace watannin da suka wuce neman auren ki na keyi,
Kenan mun san likes da dislikes din juna,
Kuma mun yarda da juna koh"

Wannan karon sai ta kalleshi tana so ta gano inda ya dosa

"Dan Allah ki cigaba da kallo na, ina son in muna magana kina kallo na"

Saida ta dan dauki lokaci tana kyafta idanu kafin ta dorasu saman nashi,

"Zaki iya fadamin abinda yasa kike jin tsoron tarayya dani"

Daina kallonshi tayi, dan tasan baxata iya cewa komai bah in tana kallon shi,

"Nasan akwai dan tsoro a lokacin farko,

Amma ba sauri, kuma ba kokarin nuna gwaninta, dukkan mu lokacin muke koya ai,
We'll take it slow, we'll keep trying har sai mun zama experts, mun san abinda kowannen mu yakeso,

Ba wani pressure kinji Husna, ina son mu dauki komai step by step,

Amma sai nasan abinda ke tsorata ki sannan sai mu cigaba"

Ajiyar zuciya tayi kafin ta girgixa kai a hankali,

"Nasan akwai Husna kar kiyi kokarin boyemin"

Ta daga mai kai,

"Toh fadamin"
Murya can kasa tana sunna kai kasa tayi magana,

"Bana jin tsoro kuma" yar kara tayi hade da zaro eyes, kafin ta dora hannu saman baki da yayi wuf yazo daf da ita,

"Kika ce bakya jin tsoro kuma" pillow ta jawo ta wurga mai

"Ba kaine ka tsorata ni bah" dariya yayi ma yanayin shagwabar ta,

Bayan dariyar ta tsagaita kuma suka koma kallon juna,

"Ban mah san ina tsoron bah,

Usually bana da problem in naji ana magana akai,

But ranar da akace washe gari za'a daura manah aure dashi, ranar na fara mafarkin abin,

Dana farka kuma da tsoro na tashi, har muka zo"

Kanta duke saman guiwowinta data ja zuwa kirjinta tana wasa da yatsun kafarta,

"Ranar nan fah da daddare, shima mafarki kikayi?"

Yar dariya tayi sannan ta daga kai,

"Ina cikin mafarkin naji kaman zahiri ne ba mafarki bah, shi yasa na tsorata, sosai,

Ina tsoron abinda suke so a wurina kawai kenan, kaman basu damu da abinda nakeji bah,

Abinda yafi tsoratani shine bana iya kare kaina in zasu cutar dani"

Ta boye fuskarta data gama,

"Shi yasa na bari har sai kin saba dani Husna dan karki ga kaman cutar dake zanyi,

Har yanxu kina ganin kaman abinda nakeso a wurinki kenan?" Ta girgixa kai

"In ka tabani bana jin tsoro kuma, wani iri nake ji yanxu,

Dan nasan kaine kuma baxaka cutar dani bah"

Ji tayi yana shafa mata hannuwa zuwa wuyanta, yana dora yatsan shi daidai inda jijiya ke harba jini taji numfashinta na sama sama,

Beh tsaya nan bah, dankwalin kanta ya cire sannan ya jawota jikin shi, a hankali take jin saukan numfashi a kumatunta,

"Caramel" ya kirata da sleepy voice,

"Uhmmm" ita tata murya kaman ta sarke,

"Kina son yanayin da kika shiga koh bakya so"

Hadiye miyau tayi dan har makoshinta ya bushe,

"Ina so, tun ranar dakace na saki jiki da kai nake jin kaman tsuntsaye da butterflies na yawo a cikina, in kana tabani koh ka kalleni kaman am no1"

Yar dariya yayi ciki ciki, a ranshi yace

'Dan ni bakisan yadda nakeji bane bah in hannu koh wani bangare na jikin ki na taba'

"Mun wuce first base" tace menene wannan,

"Rike hannu da rungumar juna" ta daga kai a hankali ma'ana ta gane,

"Plan din naka kenan" yace yap

"Toh meye second" yar dariya yayi

"Kin kagara ne Amore mio" tayi saurin girgixa kai

"Zan fada maki ai duk da haka,

Pecks da kissing"
Tayi kasake tana hango wani abu,

"Kinga abinda nake nufi" ya hau yin sautin kisses

Dariya tayi tana dan tureshi daga jikinta,a sukwane ta rarrafo daga gadon daya bita da muaaahhhh😘,

"Ina zuwa love" tace wanka zanyi da dan dariya a muryarta,

"Muje in tayaki kenan" tace Aa da serious face,

"Karki damu base din wannan na nan zuwa, a yanxu zan barki kiyi da kanki"

Ya fada shima da seriou face,

"Kin mah tunamin, zanyi ma Da magana, ince mun shirya mah honeymoon dinmu"

Ta fiddo idanu waje,
"Meh kace?" Ta tambaya da een eena

"Ba'a dade da yin auren mu bah Dad yace ya shirya manah honeymoon muje mu hutu, but nace ya bari in mun shirya zan fadamai,

Yanxu kuma mun shirya , after fasting, fewwwwwww" ya daga hannu yana kwaikwayon tashin jirgi sama

"Kuma saika gaya mah Dad in za muje wancan wurin" ya daga mata gira daya,

"Kunya kike ji koh meh" ta dora hannu saman kai,

"Ya ilahi, Ehsaas ze kasheni ni Asma'u, so yake duk inda naje in dinga sunna kai kasa"

Tayi maganarta da hausa tana gangarawa bandaki,


"Allah zan sa tara in kina magana da hausa" ya fada da karfi dan taji,

"Koh kuma kazo

Please Login or Register in order to submit comment