Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kowa bane bah, kuma baya san zalinci,

Manzon Allah yace babu fakiri a ranar tashin alkiyama sai wanda zaizo cike da aikin lada amma a kwashe a raba ma wasu dan wani laifi da yayi masu ba tareda neman yafiya bah, inma cin zali ne gulma ne, fin karfi ne"

mikewa tsaye tayi tana goge hawayen ta
"Bukhari da Muslim sun rawaito cewa babu komai tsakanin addu'ar bawan da aka zalinta da Ubangiji sarki,

Kin dauki Alhakin mu, bazan saka maki da sharri bah, amma zan daga hannuwa sama in roka maki sauki a al amurran ki, Allah Gafurur Rahim ne"

"Tafi bana bukatar ki" ๐Ÿ˜“๐Ÿ˜“Hajia tace tana kokarin nuna mata kofa amma numfashinta na ja baya, ba bacin rai a fuskarta sai wani yanayi da Asma'u bata fahimta bah

Dafe kirjinta tayi tana bata fuska alamun zafi takeji,๐Ÿ˜ฃ๐Ÿ˜ฃ๐Ÿ˜ฃ๐Ÿ˜ฃ

Ga zufa duk ya keto mata,

"Ki kira Nurse dinta " tace mah secretary din dake kallonsu

Fita tayi ta fara knocking akan kofar Ehsaas

Da sweatpants iya guiwwa meh igiyar daure wa a kasa, ya bude kofa yana goge kanshi da towel,


"Kakar ka,she's" wuceta yayi ba tareda ta karasa bah,

"Nurse dinta tayi nisa da nan, amma tace akwai wani Doctor a nan unguwar zata turoma na number dinshi"

"Well tayi sauri meh take jira" ya rude yana kokarin agaza mah kakar tashi,

Kuka yaci karfinta dan tasan laifinta ne wannan, fata take jininta beh hau bah

"Sannu Granny Ma, sha wannan" suka fito da maganinta ana kokarin bata

"Na kira likitan na bashi address dinnan, yana zuwa"

Juyowa yayi gareta

"Meh ya faru" zata bude baki hajia ta rigata

"Ba tun yau bah nakejin wani iri"
"Kira mamana Husna"

"Ehsaas" kaka ta fada tana neman numfashi

"Wai ina Dr din, mu kai ki asibiti kawai"

"Akwai โ™ฟ wheelchair, bari in dauko"
"Ke za'a sa a ciki" hajia ta fada fuska daure๐Ÿ˜ 

"Ni bana son wannan kujerar". Ta fada kuma da kalan tausayi๐Ÿ˜”๐Ÿ˜”๐Ÿ˜”


Suna cikin haka, aka kwan kwasa kofar

"Dr din ya iso" wata ta fada tana bude kofa,

Da sallama ya shigo yana aje ๐Ÿ’ผ dinshi,

"Sunana Dr Shahid,___" yana kallon hajia ya fiddo idanu waje๐Ÿ˜ณ itama hajia haka take kallon shi,๐Ÿ˜ณ
Matashi ne Dr din, dan koh ze bah Ehsaas shekaru toh kadan ne

"Get out of my house get out" iya karfinta take ihu tana ra rumo abubuwa tana wurga mai

"Allah ya isa tsakani na da kai da shegiyar uwarka, Allah ya tsine maku ku duka, ka futan min daga gdana, koh gadon ka ne,ubanka ya bar maka"
"Gett ooouuttt" saida kowa ya tsorata da tayi ihu


Daukan ๐Ÿ’ผ dinshi yayi ya fita,
Ehsaas ya tsaya kwantar mata da hankali amma firrr taki daina bori,

"Sai Allah zai rabani da ke Hannah, cin fuska harda turo shi gdana naga danki, "

Lokaci daya kuma ta silale saman gadon bata motsi, da kanshi ya daukota ya sa cikin mota suka tafi asibiti aka bar Asma'u a gda.


Garin Allah na wayewa ta fata neman inda ake saida kati, bayan dan dogon tafiya ta samu wani babban shop ta siya,

Taso kiran Ehsaas taji yadda akeci, missed calls din iyayenta da yan uwa ya hanata yin haka, ta kira gda,


Bayan sun gaisa shiru ya biyo baya,

"Kinji komai koh, Ma'u ke fadamin Jiya da daddare"
Koda ta gama bata baki dan ta hakura karta dora mah kanta damuwa, fuskarta wanke da Hawaye,

'Abin damuwa ne wannan ai, bayan alkawarin data daukan min,
Meh mutane suka dauki duniya ne da suke mantawa da gdan gsky,suke mantawa da kwanciyar kabari'

Kaman da wani take fada haka ayi magana a ranta,


"AllAh ya kara maku juriya da hakuri Mama, yasa mu kasance kullum cikin faranta maku"

Amin
aka amsa mata dashi hade da shi mata Albarka,

"Ki bar kuka kinji Mama, Nima na daina"
Kafin a amsa mata taji ana kwala mata kira hade da zagi,

Da sauri tabi hanyar daze kaita cikin gda ta main entrance, kafin ta shiga aka fincikota,

"Munafuka koh meh ya samu Hajia ai kece sila"

Tace 'Inna lillahi wa Inna ilahi raji'un' aranta

'Allah yasa Hajia bata barmu bah' ta cigaba da aikin zubda hawaye kaman spongebob na kuka.
๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ





โšœB.W.Aโœ๐Ÿป
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’
BOYAYYEN KUDIRI.

๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’



$T0Rรฝ รƒรฑd รŠdรŽTรŽรฑG bรฝ รฑ0blรŠ jรบdGรช,
wRรŽTรŽรฑG KhรƒlรŠรŠ$รŽ .


Dedicated to

Members din khaleesi's Forum, Allah ya bar kauna.


Da farin ciki nake murnar sanar daku, fara littafin nan na Meh suna KISHIYATA, na Maryam Muh'd Hassan,

RUBUTACCIYAR KADDARA, Maja tsakanin shaharrarun Marubuta Biyu,
Meelat Musa da Ummu Affan,


In anyi ba ki/kai a Kishiyata Jihadina, toh kar ki/ka bari a tsare maka a NI DA YA MOHA,
Na Real Mai Dambu,

Mai sama ya bar kauna ya kara maku Basira da hazaka. AMIN.

โคโคโคโคโคโคโคโคโคโค




3โƒฃ7โƒฃ

Tun tana daukan dungurin har tayi karfin halin bige hannun su,

"Wallahi haushi take bani yarinyar nan, tunda tazo take daga ma mutane kai koh magana batayi masu, kaman ta fi mu take gani"

Shiru tayi kawai tana matsawa baya

"Dan taga jikan Hajia na kulata ne shiyasa, wai ita shalele"

"Shalele koh yar iska, aini naga abubuwa da koro koro eyes dinah"

Wannan karon harda turata ta fadi kasa

"Hajia na can kwance rai hannun Allah saboda bakin cikin da yarinyar nan ta dura mata"


Bakinta sai rawa yakeyi, tana so ta fadi wani abu koh ta samu ta fidda kanta, ko tana da gsky bata iya kare kanta saboda tsoro, gasu sun taru dayawa,


'Wayyo Allah Ma' u, da kina nan da kin saba fadan nan a kafada kaman naki, fada ba dake bah kin. shiga balle na namecy dinki'

Bata an kara bah taji an fizgota, kafin su illatata ta kwala ihu tana neman hanyar guduwa

"Ai ban gama dake bah kike niyyan guduwa, zuwa zakiyi ki tattara ya naki ya naki,ki bar manah gda"

Kokarin kwace hijabinta data makure mata wuya dashi takeyi,

"Ki koma can cikin matsiyatan da basu baki tarbiyya bah, daga masu sata sai karuwa, kai Allah wadaran iyaye irin___"

Daga inda karfi yazo mata har ta kwace kanta ta wanka mah Secretary din hajia mari bata sani,

Ita dai taga yatsunta na connecting da fuskarta,



Abinka da ana jira, kantace kiris ta rama marin, wasu kuma na cakumota ana dura mata ashar

Dukewa kasa tayi tana rokon su bari, kaman daukewan ruwan sama wurin yayi tsit,

Bata jira bayani bah ta ruga cikin gdan, bata sauka a ko ina bah sai dakinshi, tasa makulli ta rufe,


Rakubewa tayi a gefe tana kuka,harda kakkafewa,

Bayan kukanta ya lafa taji knocking,

Dama falo ta tsaya saita dangana da daki,

"Asma'u"
Muryar da taji ne ya sata komawa ta bude kofa

"Gashi ya dade yana kira, in baki amsa bah nasan ze zo da kanshi"
Karban wayan tayi tace ta gode

38 missed calls ta gani duk nashi, wani kiran ya shigo,
Maimakon ta dauka sai ta fashe da sabon kuka, ta sulale kasa tana tura wayar gefe,

"Ina wannan incompetent fool dinnan, tun dazu na turota bata dawo bah, And Husna mah ina ta kiranta bata dauka bah"

Lukman nata binshi a baya har suka je bangaren yan aiki, yana knocking kofar ta bude


"Meh kikeyi anan,aiken da nayi maki kenan,
And what the hell, meh kukeyi a dakin Husna, wadan nan abubuwan fah?"

Ya turo wasu ledoji da shopping bags da kafanshi๐Ÿ›๐Ÿ›๐Ÿ›๐Ÿ›

"Nima abinda nake tambaya kenan, Sir a ina ta samo kaya masu tsada haka"

Lukman dake bayan shi ya girgixa kai, bayan abinda sukayi mata dazu harda sharri suke so su ja mata,

"Sir, kai ka siya mata dukkan abubuwan nan, ranar da kukaje shopping"

Ya jin jina kai yana dafa goshin shi

"Yes hakane, na tuna yanxu" duk da beji dadi bah daya ga kayan cikin ledojin su ba'a taba su bah,


"Kuma akwai wani abu Sir" ya juya ga Lukman dake kallon secretariar hajia da wani mugun kallo


"Ehn, ina jinka"

Ya fada mai komai
"Na tabbata da ban zo bah zasuyi mata abinda yafi haka"

Jinin jikinshi tafar fasa yake amma fuskar shi babu alamun bacin rai, haka mah muryar shi da yayi magana

"Abinda na aiko kiyi kenan" yayi shiru bece komai bah,
Itama haka dan tasan bah ansa yake nemah bah


"Ina Husna"
"Tana dakin ka Sir" inji Lukman,

"Ku kwaso komai๐Ÿ›๐Ÿ›๐Ÿ›๐Ÿ›๐Ÿ› ku biyo ni" ya fadama yan aikin dake taya secretariar Hajia barna,


Yana juya baya Murmushin yaci karfin shi ya bayyana a fuskar shi,

'Dakuna dayawa a gdan nan,amma ta zabi nawa, am happy Husna da kika san cewa komin rintsi bazan barki bah, duk halin da kika shiga zan kasance dake In shaa Allah'

A hankali yayi knocking kofar,

"Husna, Ni ne, Ehsaas" ya fada kaman bata gane muryar shi bane ๐Ÿ™„

"Sorry dama yanxu zan bar dakin" janta yayi suka koma dakin ta hanyar rike hijab dinta

"Ba zama zanyi bah, ke zaki dinga zama anan"
Ta dan tafa hannun shi dan sauran su shigo,

"Husna kalleni, ku jera kayan cikin Closet" ya fada yana kallon ta

"Ya jikin Hajia?" Tayi tambayar tana kara dukar da kai

"Ba baki damu ba mah" daga jin muryar shi tasan har fuska saida ya shagwabe

"Yi hakuri, yanxu nake niyyan kira dama"

Yasa hannu kaman ze shafa face dinta sai tayi baya,

"So nake kawai ki dago in kalli face dinki, Kinga gda zan tafi harsai Granny Ma taji sauki zan dawo"

Ba tareda tasan tayi bah ta dago suka hada ido

"Jikinta is serious kenan, Ni Asma'u Meh ya kaini bude baki"

Harta dukar da kai beh kyafta bah, fuskarta tayi Jaa, duk da haka saida yaga sawun hannu a fuskarta,

Sau biyu yana ganin sawun mari a fuskarta, na farko beh iya rama mata bah,
Amma wannan beh ga abinda ze hana bah,


"Youuu!! Ya fada da karfi

Kaman tasan da ita yake sai gata ta fito, tana zuwa ya wanketa da mari


" ku bata Hakuri, sannan ku bar gdan na"
Da sauri ta fara tafiya tun kafin su fara bada Hakuri,

'Ni na shiga uku Asma'u, Mutumin nan ze jamin matsala, beh san duk abinda yayi masu zeje ya dawo kaina bah'

Karar wayarta taji, abinka da chaina tun kafin ta kai kitchen take jin ringin din


"Hello"
"Sis, ki kunna radio yanxun nan pls" ya fada mata station din sannan ya kashe wayan,

Ta danyi mamaki na lokaci kadan kafin ta kunna radio da wayarta,

"Okay wa kake son kayi mah murnar ranar zagayowan haihuwa" Meh gabatarwa ya fada da turanci

Ita kuma ta kasa rufe baki da taji muryar shi yana kiran sunanta hade da wishing dinta happy Birthday๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜

"Itace best sister a duk duniyan nan, and am very proud of her"

Meh gabatar da shirin yace ya zabi wakan da za'a samata


"Your the Reason why" taji an fada daga bayanta

"Well kanwar tawa bah meh jin waka bace bah sosai, but ina so a sa mata If your Happy and You know it clap your hands"๐Ÿ‘๐Ÿป

Da wanda baiyi dariya bah,har shi daya fada, ita kanta tayi nishadi,


"Nagode yaya Abbah" ta fada bayan ya sake kiranta

"No P, ga wannan miskilin yayan naki, idea dinshi ne amma kinsan shi bazeyi magana bah"

Shima tayi magana dashi sannan ta kashe wayan,

"Happy Birthday Husna,yi hakuri ban sani bah da nine first din yi maki fatan Alkhairi, kuma da rashin lafiyar Granny Ma da munyi party"

Tace bakomai

"Zan wuce Husna,kila in dawo anjima koh gobe da safe kafin Mu daga zuwa Australia"

Tana nan tsaye har ya shirya ya dawo yayi mata sai anjima,

"Alfie, zan baka aiki and i swear, kaji dai na rantse koh in bakayi shi daidai bah koh ka gayama Mom dina, toh ka nemi wani aiki"

Alfie ya fara bashi hakuri, amma beh saurareshi bah ya fadamai abubuwan da yake so

"Pls ka bani zuwa gobe, wasu abubuwan ban tabbata zan same su a nan Nigeria bah"

"Kai ka sani" ya kashe wayan shi,

Yana shiga mota ya fara duba kyautar daze siya Mah Asma'u.


"Wai meh yasa bakya san jin maganata ne Husna"

A firgice ta tashi daga kwance,

'Meye time' ta tambayi kanta tana laluben wayarta

"Meh kakeyi anan, dare yayi fah, kuma na kulle kofa"

Wani irin dariya yayi kafin ya zauna kasa ya mike kafafu


"Meh kakeyi, dare yayi sosai fah"
Yace na sani

Yana murza idanu

"Kuma na gaji sosai, kaman tun da garin Allah ya waye nake kokawa haka nakeji"๐Ÿ˜ช๐Ÿ˜ช๐Ÿ˜ช๐Ÿ˜ช


Shiru tayi da eyes waje batace mai komai bah,sai kara shigewa jikin bango da takeyi

"Sorry na lura kaman na takura ki" ya fada da wasa a muryar shi

'Sai yanxu ka lura'. Ta kafeshi da eyes din da yake kallo kawai yana murmushi


"Dare yayi fah" yayi dariya kafin yace tashi muje,gobe zamu wuce, koh kuma ince yau tunda 3 na dare ne yanxu koh"

Ya mike sannan ya mika mata hannu, wai ta rike ya tadata tsaye

"Oh! Sorry" ya hade hannuwan shi wuri daya,


"Happy belated birthday" suna zuwa gda har dakin shi yayi mata jagora,

"Yayi kyau?"

WOW ๐Ÿ˜ฑ๐Ÿ˜ฑkawai take furtawa a ranta

"Naso ace da rana ne, zakiga color din dutsen ya koma blue green, in kuma fitilan dim ne ze koma reddish purple"

Sai juya zoben take a hannunta,diamond din shape din๐Ÿฅš kwai, kalar shi meh dan duhu,ga wasu diamonds kanana da suka zagaye gefen azurfan da kuma dutsen,


"Rare diamond ne, Alexandrite sunan shi"
'Kaman ki, Allurar cikin ruwa' ya karasa zancen a ranshi

" Wannan kawai na samu saboda ban basu notice bah da sunyi min shape din da nakeso, A bangaren Engagement rings aka dauko min shi"

Ya karasa da karamar murya meh dauke da kunya, kaman yanada wani BOYAYYEN KUDIRI gameh da bata wannan zoben,

"And chocolates, saboda ina san chocolate kuma ni dake yawanci abu iri daya muke so a ganina kenan, shi yasa nasa Alfie ya nemo min su"

Ya zazzage wani bakin jaka๐ŸŽ’

"Kinga wanda nafi so nan, lindt & sprungli duk da Amedie, su debauve and Gallia's, Republica del cacoa sune best ni nafi san shi, try them

Harda magnum, uhmmmm๐Ÿ˜‹๐Ÿ˜‹๐Ÿ˜‹๐Ÿ˜‹๐Ÿ˜‹, ina son shan Ice cream dinnan in ina kallo, abinda zamuyi kenan in na dawo lfy"

Ya dauko yana miko mata, cikin leda suke but strong kanshin su saida ya fito,har miyanta saida ya tsinke


"Bana so tnk u" ta dora mai ๐Ÿ’ a hannun daya miko mata ๐Ÿซ ,

"Husna!!!!". Ya fada da karfi yana biyota

"Ka kyaleni, nace bana so, wai meh yasa bazaka taba ganewa bah" ta fada da hausa

Biyota yayi yana kokarin riketa

"Karka taba ni, in ka matsu daka taimaka ma wani akwai mutane dayawa dake bukatar taimako, na tabbata kana ganinsu in ka fita, why Me?"

"Saboda ke daban ce Husna, abinda zan fada maki kawai kenan"
Yana gamawa ta fadi nata

"Bana so, kuma bana so ka kula dani, ka tsaya a layin ka nima in tsaya a nawa"
Hannunta ya kama ya damke cikin nashi


"Saurara da kyau kiji Husna____"

"Bana so inji,kuma sunana Asma'u,

kai baka san lokaci yayi da zaka girma bah, ka bude idonka kalleni da kyau, babu wanda yafi karfin a taimaka mai, amma ni taimakonka ne bana so, saboda matsala ne a wuri na"

Ido cikin ido take kallonshi tana magana,

"Oh Really!"๐Ÿ˜’๐Ÿ˜’๐Ÿ˜’๐Ÿ˜’ harda daga gira daya

"Am afraid taimakona kawai zaki samu, saboda in ina nan bazaki bukaci kowa bah,

And i notice,yap na lura da wani abu, ni kadai na dauke ki da mahimmanci, ke kallon shirman meh kikeyi min, spoilt brat dake soka hanci cikin al- amurran ki,

But ban damu bah, nasan a karshe zan cinmma BOYAYYEN KUDIRI na akan ki Asma'u,"

Bayan su duka sun numfasa, har ta kauda kanta sai ya sake magana

"Nayi amfani da dan lokacin nan ne dan inxo in ganki, anyi mah Granny Ma alluran bacci zan koma kafin ta farka,

Jirgi kawai muke jira,da yazo zamu wuce"

"Allah ya sauke ku lafia ya dawo daku lfy, Allah ya kara mata sauki"

Yace Amin yana shafa fuskarta da bayan hannu

"Ka bari, kaga abinda yasa nake cewa ka girma, Ya Ilahi" ta juya zata tafi ya jawo mata hijab

"Arghhh" ta danyi kara dan janta ya cigaba dayi

"Nasa an shirya maki komai anan dakin, saura mu dawo in ga bakya nan"

"Good bye 'Cara Mia', Agapi mou, Mon Amor, Amour Meu, Mo gra, Xiao tian tian, Cariad, Yeo bo,Carissimo, Jaanu, Ma Cherie, Rakkani, Il Mio Amore"

Binshi kawai take da ido, shi kuma yana tafiya da baya baya, ga wani gooo gooo, lovey dovey๐Ÿ˜๐Ÿ˜ kallo da yakeyi mata,

"Kuma zan dinga kiran ki, karki shareni, Mi Amor, kinji Ma Cherie, Ma Petite"

'Allah meh iko, koh meh kake fada' ta bishi da eyes

' My love, sweet heart, Darling' abinda yake tacewa kenan da yaran da bata gane bah.




A yan kwana kin da baya nan sai waya kawai da sukeyi ta karance shi da kyau, abinda mutum biyu suka fadamata, dayasa ta fara lura, har kuma tagano gadar zaren,


Batayi maraba da hakan bah sai tsoro,wai santa yake,

Ta girgixa kai,tana kokarin karyata gaskiyar da ke fayyace kanta,


'Yan mata dayawa ya rasa wacce ze so sai ke'
'Ba kiga kallon da yakeyi maki bah, ga kulawa, he Love's you'

Zancen Hajia da Khadija suka fado mata arai.

'Ina da BOYAYYEN KUDIRI akanki Husna' shima ya sha fadamata haka






โšœB.W.A๐Ÿ–Š
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’
BOYAYYEN KUDIRI.

๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’


$ลฆร˜๏ฝ’ยฅ , Eรล‚ลฆล‚โ‚ฆG โ‚ฆร˜BลE ไบ…UรGE,
๏ผท๏ฝ’ล‚ลฆล‚โ‚ฆG ฮบาคฮปล‚EE$ล‚.


DใƒขDๅทฅCไธนTๅทฅOๅ‡  Tโ—ฏ,

Mothers a ko ina, Allah ya Amsa maku addu'oin ku, Ya shirya manah yara manyan gobe, ya kare manah su daga dukkan wani sharri ya dora manah su kan hanya ta gari, ya kara shirya manah su,

AMIN.


Ina jin jina maku uwaye mata, harda Maza. ๐Ÿ˜โคโค๐Ÿ˜โคโค๐Ÿ˜โคโค๐Ÿ˜โคโค๐Ÿ˜โคโค๐Ÿ˜


3โƒฃ8โƒฃ.

"Stubborn girl, kece daidai dani"
Ya sake kira yaji a kashe,

"Sir pls" yace naji yana kashe wayan, sannan ya kalli matar

"Belt dinka Sir" ya juya kai yana sawa

"Shikenan koh" tace Eh,

Jirgin na dira kasa๐Ÿ›ฌ bayan sun fito ya sake kiran wayarta,


"Lukman, Husna fah? komai lfy dai ko?"

"Eh Sir, bata cika fitowa daga daki bane bah"

Farin ciki ya mamaye shi, bayan kwanaki dayawa, yau ze hada eyes da ita,

Ba wannan kadai ne dalilin farin cikin shi bah, labari meh kyau daya samu daga Raees๐Ÿ•ด,
Na cewa ya san inda Mijin Asma'u yake kuma lokaci kawai yake jira ya tafi neman shi,

Straight dakinta ya nufa, beji dadi bah dya ga dakin wayam, bangaren yan aiki ya nufa,

Gaban shi ne ya fadi bayan kwankwa sawa da yayi ba'a bude bah,

"Ga spare keys din daka ce a kawo" da kyarma ya bude dakin


"Husna" dunkule take cikin bargo bata koh motsi,

"Husna" ya mika hannu da alaman tsoro yana dan taba bargon


Da kyar ya samu ya yaye bargon data kudundune cikin,

"Ya Mukhtar" ta kyafta idanu da sukayi wani fari,

"Meh ke damunki?" Ya taba goshinta,
Wani zafi yaji kaman garwashi,

"Inna lillahi, Husna meh yasa baki fadamin bah"
Surutu takeyi a hankali tana kara dunkulewa,

Mikewa yayi daga tsugunniyar yana fiddo wayar shi daga cikin Aljihu, take kiran abokin shi ya shigo

"Haider ina bukatan likita yanxun nan pls" ya fada bah koh sallama


"Lfy dai koh Ehsaas, naji damuwa a muryar ka"

"Dr zaka kawo min pls Haider" ya kashe wayan yana komawa gareta,

Daburcewa ya karayi daya

Please Login or Register in order to submit comment