Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

din Jameelah,

Babanshi kuma ta zaban mai, jallabiya brown color meh kwalliya milk, da half covers bakake,

"Yayi?" Ta tambaya,
yace perfect yana kallonta ba abinda take nuna mai bah,

"Mun gama koh" saura ke yace

"Bana bukatar komai" of course saida ya siya mata d same perfume data zaban mah Mom dinshi,

"Tnk u" don't mention Carrissimo,

Kaman ta tambayi ma'anan abinda ya kirata kuma ta share, tana cewa zata tambayi google anjima πŸ€“,

Shi kadai yayi ta surutu har suka dawo gda,
"Sir" ya juya yana kallon meh kiran

"Bari in shiga ciki ni" ta karbi πŸ›πŸ› din

"An kawo da baka nan, daga police station" yace Alhamdulillah

Yanxu ze iya facing mamanshi tunda ya gane kuren sakacin shi, kuma ya nemo abinda ya batar

Jera komai yayi a inda ya kamata cikin dan akwatin sarkan,

Ya dade yana kallan yan kunne, sarka, bracelet da zoben kafin ya fita dasu a hannu,


A bayan shi ya boye su yana kwan kwasawa,

"Kin yarda dani husna" tace na'am tana matsawa baya

"Pls ki fadamin in kin yarda dani" bayan dan lokaci ta daga kai

"Ki furta min" tace yes i trust you,

Ya shigo dakin yana cewa ta cire hijab dinta,

Baya ta karayi, 😳

"Dan Allah manah, yanxu kika gama cewa kin yarda dani"
A hankali ta cire hijab din bayan ta daura dankwalinta ta cikin hijab din,

"Yanxu rufe idanun ki" uhm uhuhmm tace tanayin baya,shima yana matsowa

"Pls Amore Mio, plsssss" badan yana boye abu a bayan shi bah da ya hada da hannu rokonπŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»,

Bayanta ya tsaya bayan ta kulle eyes gam, sannan ta kankame jikinta da hannayentaπŸ€—,
Kaman saman kaya take,

Dole ya bi a hankali wajen aiwatar da abinda yakeso, dan kar ya tsoratata dayawa,

"Yi taku hudu gaba, yauwa,,, yi dama kadan, toh bude eyes din MY CREME CARAMEL "☺☺☺☺

"Inna lillahi "

"wa inna ilaihi raji'un" ya tayata karasawa

Kaman ba ita bah data bude ido, kaman wata sarauniyar kyau koh wata princess daga Dubai,

Kwalli kawai da lip gloss ta shafa, sauran kyan datayi duk hasken da sarka da yan kunne, harda awarwaro da zoben daya samata ne keyi, shi ya haskata,

"Ya Ilahi" ta kara cewa,

Sarkan na farin gold ne, a tsakiyan sarkan shape din ganye neπŸƒ, meh kananan daimonds like a jiki, shape din ya kai tsawon babban yatsanta da fadin inchi 4koh 5,

Gefenshi kuma chain ne da akayi da kana nan leaf shape, meh daimond karami a tsakiya, steps guda biyar a ko wani side,

Sarkan kaman choker kuma ya kwanta a wuyanta at the same time,

"WOW" sai ranan taga jewelry din dayasa taji sha'awan sa sarka,

"Your beautiful, Mo Gra" ta rike sunan daya fada

Sannan ta fara cire zobe da yan hannun,

"Tsoron su mah nakeyi ni, ka tabbata bah 100Mil ne abinnan bah"

Dariya yayi sannan yace na tabbata beh kai bah,

"kuma Mom dina tayi designing dinshi" tana da baiwa, ta fada a hankali.


Tun da safe take ta shirye shiryen zuwan su hajia da mahaifiyar shi, abinci kala kala ta dafa sannan ta hada drinks masu rai da lfy,

Bata manta da condition din hajia bah, dan haka tayi wasu abincin dan ita kadai,

"Ya Mu'allima sannu da aiki" ta amsa da yauwwa


"Wai school dinki fah? " tace sai next year batare da ta kalleshi bah

"Meh zaki zama toh" kanta kasa amma ya gano murmushi takeyi

"Teacher"
Yace Teacher!?

"Babu kyau ne" yayi saurin cewa Aa,

"Zakiyi kyau da teacher kam, meh yasa kika zabi teaching " ta aje ipad din sannan tayi magana

"Lokacin dana fara secondary school babana yayi retire, amma dana je mutane sun mutun tani sosai,

Kuma na samu kulawa daga students staff teachers, duk saboda mutuncin babana,

Shi yasa nima nakeso na zama teacher, koda quarter din abinda yayi achieving zanyi,

Har yau students dinshi na kiranshi saboda suna sanshi sosai, i want that"
Yaga Alfahari a idanta gameh da babanta, tana Alfahari dashi a ko ina take,

'Kinyi dari bisa dari husna'

Ba ita bah har shi cikin damuwa yake,

"Wannan babban spoon din dashi zaki fara cin, appetizers , sai wannan" ya cigaba dayi mata bayani

"Na sani, dazu kayi min bayani, mamanka tana san mutum meh table manners" yace Eh da dan dariyar da beh kai ciki bah,

"In sunxo ai sai sun huta kafin mu kawo su wurin cin abinci koh"

Lura da tayi duk ya daburce

"Ya akayi ne wai? " ajiyar zuciya yayi

"Ina son komai ya tafi daidai ne Husna, komai"

Tace in sha Allah komai ze tafi daidai

'Allah yasa husna, dan in Mom ta yaba dake zan iya aurenki, shi yasa everything has to be perfect '

Ya kalleta yana ajiyar zuciya.





⚜B.W.AπŸ–Š
[3/22, 21:16] β€ͺ+234 706 870 0853‬: ⚜BRILLIANT WRITERS ASSOπŸ–Š




πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI.

πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’


Story & writing Noble judge.
Editing khaleesi.

Dedicated to Raheema & Meemah,

Allah ya baku sa'an exams din da zaku rubuta, da kuma wadan da zakuyi nan gaba,
Ku da yan uwa musulmai gabaki daya masu facing exams.
🍭🍭🍭🍭🍭🍭🍭🍭🍭

Marubuciyar quruciyar Jummai tazo maku da wani sabon littafi meh suna RIKICIN AURENA,
KADA KU BARI A BAKU LABARI,

SIS LEEMA, ja muje.

LAIFIN ABBA NA NEH,
Shin koh meh Abban Yayi?
Ku kasance da Marubuciyar Uwar Miji, wato Sis Rahama dan samun wannan Ansa.

πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘





4⃣1⃣.


IPad dinshi ya bata da hotunan irin abincin da Mamanshi ke so, bayan traditional data dafa,

Tsaf ta shirya komai, sannan ta gyara ma Mamanshi dakin da zata sauka,

Shiryawa tayi cikin wani lace marar nauyi, kuma marar tsada amma akwai daukan ido,
Purple color meh kwalliya silver, hijab ta sa batare da ta daura dankwali bah,

"No Husna banda Hijab din yau, pls" ta bata rai

"Dan Allah manah" ya biyota bayan ta wuce shi bata ce komai bah

"Mamanka ce zata zo fah, kuma kace min kai da ita are close"
Yayi ajiyar zuciya

"Baxaki gane bah husna"
Sannan yace ta bar hijab dinta,

Cikin suit yake meh laushi, jikinshi kaman na eskimo, maroon color ne sai yasa black T-shirt πŸ‘” da farin bow tie, wando shi mah fari da takalma bakake,

"Ina zuwa" tace tana komawa dakin ta,
Ita tafi sakewa in tana sanye da hijab, duk a takure zata zama in ta tafi haka,

Karan Doorbell taji, da kuma yar karamar kara,

"Surprise Husna harda Dad akazo"
Tace inna lillahi a ranta

Duk ya maida hankalin kowa kanta, gashi ta cire hijab din, babban dankwalin kayan kawai ta yafa

"And wannan kyakyawar fah? " ☺☺☺☺ Da kunya ta duka ta gaishe da iyayen shi,

Tana kallon mutumin data dago ta kasa dauke ido daga kanshi

"Nafi shi kyau koh"harda kanne mata ido daya

"Dad! " Ehsaas yace da yar shagwaba,

Banda kama harda tsokana da raha, duk wurin baban shi ya gadΓ², banbancin su kawai shekaru,

" husna yana ga kin rameh, koh duk kewata ne" ita sai lokacin taga hajia, wacce keta fara'a, itama tayi mata fara'a hade da gaisheta

"Na gaji fah" mamanshi ta fada hade dayin gaba,

"Ni ma haka Ehsaas" inji baban shi, sannan suka barsu su biyu


"Uhmhmmmm, ya kika ga iyayen nawa" harda sa kafadarshi ya tabata

"Kaman ka" yayi yar dariya,
Sannan ya wuce, itama tayi dakinta.


"Lokacin cin abinci yayi" ya leko yana fada mata

"Okay " ta mike tana binshi a baya,

Zazzaune ta gansu a dinning table, kara gaishe su tayi da yi musu ya gajiya,

Dan shiru sukayi, babu meh yin komai,

"Mom, Husna ta iya dafa abinci, exquisite i tell u, sai kin dan dana"

"Kayi gsky Ehsaas har missing girkinta nayi" inji Hajia, dake zaro 🍴daga cikin napkin dinsu,

"Bari in zuba maki" dama tasan warmers masu abincin hajia a ciki,

Tuwon alkama da egusi soup

"Oh My God, abinda nake tunani kenan" ya kara shakan kanshin

"Egusi soup, my God baxan manta da miyan nan bah"
Nan Baban Ehsaas yayi serving kanshi, shima tuwo da egusi din,

Bowl din ruwa ta kawo mai ya wanke hannu,

"Dad ka iya ci" ya daga kai kawai yana kai loma

"Uhmmm this is good, sannu da kokari Husna" kowa a wurin santin girkinta yakeyi amma banda Mom,
Da tayi kaman bata san da wata ajiya bah wai Husna,

"Mom dinka ta koya min cin African food, tun ina gudu har na daure na dan dana, and it was amazing, har san zuwa Nigeria nake ko dan Mom dinka tayi min girki"

Abinda babanshi beh fada bah shine yanxu ta daina, da wuya mah Mom dinshi tayi girki,

Mom dai ta tabe baki, shi ita kadai yake kallo yana son ya gano koh ta yaba da matar daya zaba,

"Asma'u koh" kowa yayi tsit da Mamanshi ta bude baki

"Meh kikeyi anan kuma meh ya kawo ki?" tana bude baki zata ansa ya rigata

"Karatu tazo yi, wasu abubuwa suka sa muka hadu da ita"

Babanshi yace good, meh kike karantawa

"Ahmmmm, Maths, teacher take son zama" ya sake amsawa

"Naxata mutane sai basu da yadda zasuyi suke yin teaching " kafin yayi magana Babanshi ya riga

"Nooo, honey, teaching good profession ne, da bama nan ai da bah teachers" yaji dadi da babanshi ya taimaka mai wajen bada ansa

"Kina da siblings ne? " tace Eh a hankali

"Baban yayanta nada aure kuma dan kasuwa ne, sai meh aiki a nan abuja financial Assistant ne, sannan meh studying sai Husna, itace last born"
Suna hada ido da ita yaga, idanunta sunyi jaa

"Wow! Yada sanin komai akanta kodai kodai" babanshi ya tsokana

Mamanshi kuma tayi guntun tsaki,


"Meh babanki keyi? " koda ya fara magana bata barshi ya karasa bah

"Wai kai ne Asma'u , koh bata da baki ne"
Tun anan yace akwai matsala,

Babu wani abu daya burgeta gameh da Husna da family dinta, da yanxu ta fara janta da hira kuma ta fara mata fara'a, saidai har yanxu tambayoyi kawai takeyi mata,


"Mom, Husna ta siyo maku gifts da taji zaku zo" mamanshi tace yayi shiru Asma'u ta gama

"Tana da register da asibiti amma, bata zuwa karban haihuwa can, a cikin unguwar mu takeyi" ta gama bayani akan Mamanta

"Haka nada kyau, Allah ya bata lada, dan tana taimakon Al'umma" ta amsa mah babanshi da Amin.

Gab da maghrib suka gama cin abinci, ita ta taya masu aiki tattara komai,

"Gashi Asma'u " mamanshi ta mika ta cup din data sha ruwa, bayan sun gama kwashe komai,

Tana jiyo hirar su sama sama daga kitchen inda take wanke wanke,

Bata sake fitowa bah sai can cikin dare, azatonta kowa yayi bacci
Shima kuma fitowarshi kenan da niyyan zarcewa dakinta, sai ya bita waje


"Sweet caramel" ajiyar zuciya tayi

"Kabar kirana da sunayen nan banaso" tayi gaba abinta,

"Ya akayi cara mia" ta juya dan tasan cigaba da bin ta zeyi,

😊😊😊😊
Murmushi taga yanayi

"Har kayi wani abun da zakayi farin ciki ne, bakin ciki ya kamata kayi" ya daure fuska yana harde hannu a kirji,

"Da raina, ina zaune kusa da kai amma ka dinga yimin karya" sai ya dan tausasa fuskar sa

"Husna___"
"Karya na daya daga cikin manyan zunubai, bakaji ance ka fadi alkhairi bah koh kayi shiru,

Kasan irin bala'in da yar karamar karya ze iya janyowa,
Kuma iyayenka kayi ma wa"

"Meh na fada aciki da yaje karya Husna, komai dana fada gsky ne, Akan babanki yan uwanki, duk gsky ne,

Kilan basu fadamaki bah, amma saida na tabbar komai nasu na tafiya normal kafin na fadi wani abu akansu"

Harde hannuwa tayi a kirji

"Naji labarin abinda kayi, tnk u but ina so in na bar nan, in bar duk abinda ya faru anan, in fara fresh taya zanyi haka in kullum iyayena da yan uwana zasu kasance cikin alfarmar ka"

Yayi saurin katse ta da No, yana girgixa kai

"No Husna, akwai abinda nakeso, kuma harga Allah in ban samu bah, bazanyi amfani da abinda nayi musu bah dan cinma burina, KUDIRI na akanki Husna"

Ta jin jina kai

"Abin kenan ai, duniya mutane basa yin wani abu sai sun san zasuci riba,

Fadamin abinda kakeso toh, ka fada da kanka ai, danyaya akwai abinda kakeso shi yasa ka tallafa ma yan uwana da iyaye"

Girgixa kai yayi yana shafa face

"Bamu da time din yin jayayya Husna, duk abinda na fadama ma Mom akanki in shaa Allah ze faru,


Kuma" πŸ˜”
Ya dan kara matsawa kusa da ita,

Akwai abinda nakeso" tace naji wannan ai, fadamin abinda kakeso


"Inata kokarin ganin Mom tayi maraba dake, bayan ban san matsayina a wurinki bah"

Ta bishi da idanu

"Dan Allah ki aureni Husna" sun kusan seconds 40 kafin ta daga hannu ta mareshi,

Yar kara tayi, bayan shine yasha mari

"R u OK " ya duka kasa yana duba hannun,
Kuka ta fashe dashi, sannan ta fara bashi hakuri

"Dan Allah kayi hakuri na mareka, Dan Allah, ban san Abinda yasa ni yin haka bah"
Yace hmmmmm da wani irin murya da bata taba jinshi dashi bah

"Kayi hakuri dan Allah" ta mike tsaye zata wuce, sai ya kirata


"Husna, ba bacin rai, fushi koh haushi a tare dani, sai tausayi,

Ina matukar tausayawa kaina,

Banzo kasar nan da niyyan aure bah, although ina son inyi auren,

Allah ya doramin sanki Husna bayin kaina bane bah,
Na fadama kaina in Mom tace bata amince in aureki bah zan hakura,

Amma yanxu naga kaman basai tace min Aa bah,

Ke zakiyi breaking heart dina,πŸ’”"
Ya dafe kirjinshi yana ajiyar zuciya

"Zan iya cewa its brokenπŸ’”, daga radadin da nakeji yanxu"

Tafiya yayi ya barta tsaye tana sharban kuka,

Mom kam tana kebewa da ummanta ta fadi abinda yasa take nisanta kanta da Asma'u

"Tunda nake da Ehsaas beh tabayi min karya bah, amma yau yayi, sannan yaje bada sanina bah yana inganta rayuwar wasu duk dan ya auri yarinyar can"

Hajia tayi shiru bata da bakin magana, dan duk halin nan daga wurinta ta koya

"Karki yanke mah danki hukuncin daze kwareshi, ke da bakinki kika ce kin san danki sosai,

Ina fadamaki ke zaki cutu idan kika rabashi da yarinyar nan, dan ya kwallafa rai already,

Kuma Asma'u batada wani aibu Safiya"

Mom ta katse ta

"A yanxu bah, ni ban manta bah in kin manta Umma, ba'a yaban dan kuturu sai ya shekara goma da yatsa"
Ta mike tsaye tana zagaye dakin

"Zan san abinyi gameh da wannan batun,

Akan Hanna kuma" hajia ta dafe fuskarta

"Ki share zancen nan safiya"

"Tattaki nayi fah dan in gane mah ido nah, bazan koma bah saina bata assignment,
Meh taramin rahotanni kawai nake jira ya kammala,
Sai in san ta inda zan fara",
Tayi mah mahaifiyar ta saida safe,

Fitowa tayi daga daki tana tamabayan inda mijinta ya shiga

"Sun fita da danki bada dadewa bah" ta koma cikin gda,


Ehsaas da zazzafan hawaye ya nufi cikin gda,

Yana shiga yaji an jashi ana rungumeshi

"Daddy" ya jawoshi suka fito

"Muje mu danga gari, saika fadamin komai ba wanda ka fadama Mom dinka bah,

Sannan sai batun Creme Caramel dinka"
Dariya ya kufce mai,

Zagaye suka fita cikin unguwa, jefi jefi suna haduwa da mutane kuma motoci na kai da kawo,

Fayyace mah babanshi zare da abawa yayi, tun daga zuwanshi kasar har zuwa abinda ya faru dazun tsakanin shi da Husna,


"Dad pls ka taimakamin, Naga first hand yadda Mom ta tsani talaka, kuma naga yadda take kallon Asma'u, nasan batayi mata bah"

Babanshi ya tsaya da tafiya yana kallon shi

"Bin iyaye yana gaba da san ranka Ehsaas, Zefi zama maka Alkhairi in kayi abinda mamanka tace"
Ya shagwabe fuska

"But dadd" kaman zeyi kuka

"Ka bari Asma'u din tace NA'am ta yadda, kafin ka tuntubi mamanka da zancen kaji" yace toh yana tuno marin daya sha

"Abin nan baxe zo da sauki bah" babanshi yayi yar dariya

"Ai haka love yake my son, kafi daraja shi in ka sha wahala akanshi sosai"

Ya jawoshi gefenshi sannan ya dora hannu saman kafadar shi,


"Karka damu, ina nan harsai ka ci nasara" yace nagode dad.





⚜B.W.AπŸ–Š
[3/22, 21:16] β€ͺ+234 706 870 0853‬: ⚜BRILLIANT WRITERS ASSOπŸ–Š




πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI.

πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’


Story& Editing by NOBLE JUDGE.
Writing KHALEESI.







⚜BRILLIAN WRITERS ASSOπŸ–Š


πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’


Wannan page sadaukarwa ne na musamman ga
ADMIN OF ADMINS

ZUBAIRU BABA HAYAT
Da mukafi sani da

YAYA HAYAT,

Jin jina da ban girma gareka, A groups dinka

COOL NOVELS, MAKEUP AND KITCHEN,
Mun karu sosai ta fannin girki, kwalliya ,harda zamantakewa,
Zumunci da kuma fadakarwa da nishadi,

Allah ya baka ladan hada mutane dayawa wuri daya dan su amfana da juna.

Ina mai tayaka murnar zagayowar ranar haihuwarka a yau,
22ND MARCH,

Allah ya Amsa maka bukatunka na Alkhairi ya kara daukaka zuwa wurare da baka taba tsammani bah,
Ya karo maka shekaru masu Albarka.

Yau ranar kace ka wataya san ranka,


A madadin duka members din, ⚜B.W.AπŸ–Š
ni KHALEESI ke cewa ka huta lfy,

OnceπŸŽ‚πŸΎ.
Again πŸŽ‚πŸΎ
Happy πŸŽ‚πŸΎ
BirthdayπŸŽ‚πŸΎ.


4⃣2⃣.

Da duk karfinta take sauri dan ta cinmashi kafin ya shiga dakinshi,

"Ehsaas " ta kwala mai kira,

Kaman badashi take bah haka ya shiga dakin yasa key,

Nata dakin ta koma sukuku, saman akwatinta data shirya komai nata ta dora kai, tana shirin fashewa da kuka,


"Kin kirani ne" da hanxari ta mike tana goge hawayen da basu zubo bah

"Tun tuni naketa neman ka"

"Banxata kira na kikeyi bah, dan nasha jin muryar ki a cikin kai na"

Yanxu da suka hadu bayan ta dade tana neman shi, kuma ta rasa yadda zata fadi abinda takeso

Sai wasa da yan yatsunta ta tsaya.




Kwana uku kenan yana shareta, tun ranar data mareshi,

Ta kagu ta koma gda ne, bakaman da mahaifiyar shi ta fito fili ta nuna mata bata santa,

Washegarin ranar da suka zo ne, ta tashi da wuri dan hada masu breakfast, gamawarta keda wuya saiga Ehsaas da mahaifinshi, dan haka tayi serving dinsu,

Sannan tayi dakin hajia ta gaisheta da yi mata ya jiki, sannan tace mata ta gama abinci


"Asma'u so kike sai na fada da bakina kin sa naji kunya" tace ban fahimta bah hajia

"Aikin da kikeyi nake magana akai, mun warware ai, yanxu koh tsinke in bakyaso bazaki daga bah a gdan nan"

Dan numfasawa tayi sannan ta gyara tsugunnawarta

"Nagode hajia da kika janye batun ki, Allah ya saka maki da Alkhairi ya baki gdan Aljannah"

Da fara'a hajia ta amsa da Amin

"kuma batun aiki, sakai ne hajia, ina sonyi shiyasa nake yi har yanxu"

Hajia tace shikenan amma ta daina ba kanta wahala,


"Kin gaishe da Safiya" tace Aa


DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment