Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaimu, amma yau ni dake zamu yini tare"

ya bar dakin, ita kuma ta kalli hanyar daya bi da kallo.






⚜B.W.AπŸ–Š
[3/26, 06:12] β€ͺ+234 706 870 0853‬: ⚜BRILLIANT WRITERS ASSOπŸ–Š




πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI.

πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’


Story, Writing by
NOBLE JUDGE.
Editng KHALEESI.



ABINDA YA BAKA TAUSAYI
(wata rana ze baka tsoro)

Na Halima Yahya twenty,

Allah yasa an fara a sa'a,
Kar ku bari dimbin darasin dake ciki ya wuce ku,



4⃣3⃣.



"Saurin meh kakeyi haka, ina kuma zaka?"

Ya tsaya dan yi ma mamanshi bayani

"Mom fita zamuyi da Husna"

Ya karasa har inda take zaune ya gaishe da ita sannan ya zauna kusa da ita saman 2sitter

"Ina zakuje"
Asibiti zasu yaga Haider, amma yasan in tasan wanda zeje gani baxata bari bah


"Ahmmmm dama zamuje yawo ne da Husna, supermarket da sauran su"

Tace Oh! Sannan tajawo wayarta tana dubawa


"Da wannan ba gwara kaje office bah, tunda muka zo banga kaje bah"

Ya bata fuska

"But Mommmm?" Tana kallon shi ya daina turo baki

"Mom tafiya zatayi fah" girgixa kai tayi tana cewa yaje ya shirya mah office


"My wife"
'Lallai har na zama matar taka kenan'
Ta kalleshi kawai batace komai bah

"Ba matsala in na bari sai anjima kafin mu fita, zan dan leka office ne"

Da murmushi tace bah matsala manah

"Ina nan ai harka dawo" yayi murmushi

"Tnk u Love" tace bakomai

Da fara'a ya koma falo yanata murmushi shi kadai

"Yanxu fah ka gama bata rai dan nace kaje office, ya kuma naga kana murmushi"
Ba tareda ya tace maganar bah kawai ya furta abinda ke ranshi

"Yanxu danaga Husna tacemin ba matsala in je in dawo zata jirani, sai naji ina mah san zuwa office din, saboda nasan she'll wait for me, kowani irin dadewa zanyi zata jirani"

Sai fara'a yake yana jin kanshi kaman a lambun furanni yana watayawa

"Bana so kaje office din kuma"
Sai lokacin ya maida hankali kanta

"Tunda saboda ita zakaje badan nace bah" ta fada da hausa

"Mom ba matsala zanje office din kinji, am sorry"
Ya nufi hanyar fita

"Ka dawo nan nace, na manta gobe zata tafi shi yasa nasaka zuwa, amma ka barshi kaje kuyi yawon naku"

"Da gaske Mom" ta daga kanta,
Ba kunya ya ruga upstairs yana Jaaaannnuuuuuu

'Tun wuri zan shawo kan matsalar nan, kar ina ji ina gani dana ya koma mijin hajia,
Yana bin maganarta tun kafin aure kenan mah'

Ta zurfafa cikin tunani batama san sun zo yi mata sallama bah,

"Mom karki damu yanxu zan dawo fah"
Ya fada da wasa yana sumbatar kumatun ta
Tace uhmmm

"Sai mun dawo" Asma'u tace kafin suka fita,


"Meh zamuyi a asibiti"
Ta bude kofar motar zata fita,

"Ni gentleman ne Husna, ki dinga bari ina bude maki kofa kinji koh"
Tace Aa bataso
"Baki da yadda zakiyi Habibty"

Ta juya idanu
'An koma sunayen kuma'


Ita kadai ta shiga dakin da aka kwantar da matar babansu Haider,
Shi kuma yana waje,
Da yake tasan su dan ya kaita Bikin Haider din, ta dan sake sunyi hira,

"Ya akayi?" Taso ta share amma wata zuciyar ta tunxurata ta tambaya,

"Bakomai My dear" tace naga kayi shiru dayawa ne


"Kin san Amyr, lokacin da bakya da lafiya shi ya dubaki"
Ta danyi tunani akai amma bata gano fuskarshi bah

"Mun hadu dashi a asibiti yau, naso yimai godiya akan zuwa dubaki da yayi, amma koh gaisuwata beh ansa bah,

He was very rude, kuma ban mah san dalilin shi nayin haka ba"
Shiru ne ya dan biyo baya dan bata san abinda zatace mai bah,

"Banaso ki tafi Husna, zanyi kewar ki dayawa"
Ta danyi murmushi
"Babu inda zakije koh"

'Kaman ba shine yaketa bata rai ba'

"Abinda ya faru da likitan ya daina damun kaneh"

Ya girgixa kai
"Ina wani abu ze dameh ni bayan kece babban damuwata, inyi yaya in kika tafi"

Aranta ta roki Allah in Alkhairi ne auren ya nuna masu, in ba Khairi bane bah kuma ya musanya masu da Alkhairi,

"Kinyi shiru, nace babu in da zaki"
Ya maida duban shi gareta, ita dai ta jingina da marfin mota,

Supermarket ya kaita sukayi dan siyayya kafin ya maida su gda,


"Granny Ma?" Ya bude kofar a hankali, dan kar ya tasheta in bacci takeyi

"Ehsaas" ya karasa cikin , sannan ya zauna kusa da ita

"Ya akayi ne, naga face din yau babu annashuwa"
Ya kakalo murmushin da beh haska fuskar shi bah,

"Seriously Ehsaas, meh ke damunka" ta cire tabarun data sa

"Granny ma yau na gamu da dan uwana?"
Bata kawo wannan maganar aranta bah, koda tayi tunanin matsalar dake damun shi, ta zata tafiyan Asma'u ne

"Dan uwanka kuma Ehsaas, ai daka zo dashi na ganshi"

"Kin sanshi" ya fada tana rufe baki

"Wanda yazo nan ranar da bakyada lfy, Shahid, amma Amyr ake kiranshi"
Bta maida dubanta gareshi bah har ya gama,

"Kiyi hakuri Granny Ma, naga abinda ya faru bayan kin ganshi, beh kamata ace na tunkaroki da maganar nan bah,

Amma an barni a baya dayawa, ban san komai bah kuma banda damar tambaya___"

"Ranar ina ganin shi nasan koh shi waye" ta katse shi da maganarta

"Kusan kullum da bakin ciki nake kwana Ehsaas" ta maida kallonta gareshi

"Zuwanka ne ya dan ragemin radadin da zuciyata ke ciki Kullum"
Hawayen daya tsiyayo mata saida ya kai har kasan wuyanta ya bace cikin rigarta

"Ita meh yasa zata dinga ganin danta kullum, ni kuma koh Hanya daya muka bi da dana ya daina binta kenan,
Ina adalci anan"
Ta kalleshi idanunta duk sunyi ja, hawaye kawai ke tsiyaya, amma bakinta beh Fidda KoWani sauti

Daga gani kasan ta saba da kukan zuci,

"Bakomai Granny ma basai kin fadamin bah, nafi bukatar lafiyar ki da sannin dangi na"

Ta girgixa kai

"Kana da daman kace a fada maka Ehsaas, nasan bakama san kana da Kawu ba koh"

Yayi shiru bece komai bah

"Banyi mamaki bah da mamanka bata fadama bah, ta yanke saka dashi ai,

Ni kuma kullum da tunanin shi nake kwana nake tashi"

Ta kusan minti biyar batace komai bah,
Kaman ya tambayi dalilin kin zuwa taga dan nata, amma yayi shiru,

Handkerchief ya fiddo daga aljihun shi

"Granny ma" ya mika mata da murmushi

"Nagode, kanada wurin zuwa ne" ya girgixa kai

"Toh zauna da kyau, yau kakarka zata maka tatsuniya"


Kasa ya zauna ya dora kanshi saman kujerar da take zaune

"Lokacin da ina yarinya, kakana yana son taramu ya bamu wannan labarin,
Duk ranar da babu hadda koh islamiyya, labarin nan yake bamu,
Karka so kaga yadda nake bata rai, kullum sai nayi korafi nace ya barmu mu kalli cartoon network,

Ban taba zatan zan tuno labarin bah ballantana in fadama nawa jikokin"



"Shekaru da dama da suka wuce, tun kafin asan za'ayi mota, lokacin rakuma ne abin hawa,

Ga mutanen Algeria kenan, a cikin wani gari na Ain Salah, har yau babu cun kosan mutane a garin,

Ubaydullah Hamid, tsatson King/ Malik family,
Asalin shi dan tamanrassat ne dake cikin kasar Algeria,
Kaman Ain salah, tamanrassat sahara ne, in da mutane daga kasashe dayawa ke zuwa yin kaasuwanci, daga kano ne Agadas, lake chad,

Ubayd bawa ne daya siya yancin shi daga hannun uban gdan shi,

Daya tashi sai ya koma Ain Salah da zama, cikin kankanin lokaci ya zama shahararren dan kasuwa,
Saboda ya koya sosai daga wurin uban gdanshi,

Yana da taimako sosai,kuma mutane na sanshi, saboda girmamawa da kauna da yake samu sai ya maida sunan shi Malik, ma'ana sarki,

Kuma mutane basu bata lokaci bah suka bishi da wannan suna na Malik,

A kwana a tashi yayi fadar shi ta kasa, kuma ya zuba bayi da ma'aikata dayawa,

Wasa wasa ya ba kanshi sarautar karfi da yaji,

Abu daya kawai ya rasa a masarautar tashi, shine magaji,

Bawai baya da yayan bane bah,
Aa, duk mata Allah ya azurta shi dasu, har ya kaiga ya fara auri saki, da kin haifi yara biyu kuma duka mata ze sake ki ki kama gabanki,

Ya tara mata da Iyali ba laifi, da ya sakeki sai ya baki dukiya yace ki tafi da yayanki,

Haka Malik family suka yadu a nahiyar africa,saidai babu wani zumunci tsakani,

Ya taba auren sisters guda biyu daya bayan daya, wadanda bayan ya sake su, sai sukayo nigeria da yayan su duk mata har guda biyar,

Cikin ikon Allah yaran nan biyar sukayi aure suka hayayyafa, kuma suka cigaba da amfani da sunan malik,

Saboda tsaro yasa basu yadda da auren na waje bah saidai. Cikin dangi,

Wannan al-ada tasu tun wanan lokaci ya fara, babu wanda ya taba aure a waje, sai Kan Hannah"

Ya tashi zaune dan anzo wurin da yakeso

"Ni na daukota da hannuna, na bata kulawa fiyeda yadda zan bah safiya,
Data tashi saita auri Mijina ta koroni waje, ta raba zumunci na da yan uwana,
Har yanxu tana nan tana rayuwar da nakeso"

Hannu yasa yana goge mata hawayen da suka tsiyayo

"Karka so kaga kangin dana fiddo yarinyar nan daga ciki, na bata rayuwa da ilimi meh inganci"

Kwantawa tayi tana aikin zubda kwalla

"Am sorry Granny ma" ta girgixa kai tana cewa nice marubuciyar matsalolina Ehsaas babu laifin ka aciki

"A Algeria bazaka samu King family bah, dan har ya mutu mai sama beh bashi da namiji bah, matan shi kuma duk sunyi garuruwΓ n su"

Godiya yayi mata duk da beji duk abinda yaso bah,

Saidai yasan irin abinnan na ba wanda mutum ze warke da wuri bane bah,

'Hannah' da wannan tunanin ya yini,

Sai cikin dare ya nufi dakin Asma'u,

"Naxata kinyi bacci"
Kaman tasan ze zo dama ta zumbula hijab dinta ta makure can karshen gado

"Meh kakeyi har yanxu bakayi bacci bah"

Beh bata ansa bah ya zauna saman gadon

"Zanyi kewarki Husna"
Pillow ya jawo ya dora kanshi sannan ya gyara kwanciyar shi

"Ka tafi dakin ka manah in kana Jin bacci ne"

Uhm uhm yace yana jan bargo

"Ehsaas manah"
Ta mike tsaya da taga ya lumshe idanun shi

"Kin rigada kinyi min rowar ganin ki, zakiyi min rowar muryarki ne yanxu"
Sai a lokacin ta iya kare mai kallo,

"Wani abu na damun ka ne" yace meh yasa kika tambaya

"Stress ya nuna a face dinka"
Da murmushi ya bude idanun shi a hankali

"Maki goma Husna"
Maki kuma?
Ta tambayi kanta, kaman ya san tayi tambayar

"Na sanin mijin ki na cikin damuwa ba tareda ya furta bah"

Ta kalli gefe

"Kai ba mijina bane bah"
Yace hmmm
"Tukunna dai Ma cherie, tukunna dai"

Gajiya tayi da tsayuwa kuma baxata iya cewa ya tafi bah,

"Saida safe" yana bude ido yaga ta kusan kaiwa bakin kofa

"Zo nan Husna"
Ya tashi zaune yana mika

Wani wahalallan numfashi ya fitar, yana murza eyes,

"Kar kayi taurin kai ka kwanta abinka"

"Tunda kin ki dawowa ai dole ni in biki,
Wai koda munyi aure haka zaki dinga bijere ma magana ta"


Tsaye ya mike yana tunkararta

"Ai kai ba miji na bane bah" ya katse da a yanxu bah

"Sai lokacin sannan kake da damar sani inyi abu koh in bari, kuma babu kyau mu kebe wuri daya"

"Kina nufin in munyi aure, ki fada da ihu manah, meye na boyewa"

Yana gaf da isowa in da take ta fita daga dakin


"Muje waje, nan bada dadewa bah in Allah ya yarda babu abinda ze hana mu kebe,


By the way, fadamin hakko kina dake kanki"
Ta turo baki
"Ba hakko kina da ke kanka bah"

'San kai kawai'

"Ki fadamin nawa sai in fada maki naki, 50/50 za'ayi"

Cigaba da tafiya tayi dan bata san in da zasu bah

"Husna Manah, shirun yayi yawa"
'Wai bazaka aje wannan shagwabar bah'
Ta fada a ranta,

"Sadakin ki right dinki ne, kiyi yadda kika so dashi, Haka sama mana wurin zama,

Ciyar da ita, tufafinta, da kuma kudin da zata kashe, duk yana cikin hakkinta akan mijinta,

In kina da abokan zama yayi adalci tsakanin ku,

Kina da abokan zama Husna?"
Tace hmmmm tana boye murmushin daya zo mata

"Ya zama meh kula da ita, kada ya muzguna mata, kuma kada cutar da ita, na gama

Cigaba toh Husna"

Suka iso wurin garden, sai ta tsaya bata shiga bah

"Cigaba manah" ya fada yana yin jagora,

"Kuji tsoron Allah gameh da matan ku, dan Amana ne su a wurinku

Yin biyayya a gareshi".

Yace uhm hmmm

" kada ta bar wanda baya so ya shiga cikin gdan shi ba tareda izinin shi bah,

Kada ta fita daga gdan ba tareda izinin shi bah,
Matar data bar gdan mijinta ba tareda izinin shi bah, tana daya daga cikin mutane uku da ba'a amsar sallar su, har sai ta koma gareshi kuma ta nemi yafiya"

Gani tayi ya tsaya sannan ya juyo

"Ina son in dinga kallon face dinki, ya za'ayi?"
Ta kalli kasa, tana dan bubbuga kafar ta

"A gani na, ya kamata ace ni dake mun san abinda ze faru bayan munyi aure shi yasa na tattago ki da daren nan"

'Ba bacci ya kawo ka dakin nawa ba kenan' ta kalli gefe tana fadama kanta

"Muje, kuma ki cigaba"
Yana juyawa ta turo baki

"Miji ze iya hora matar sa in taki yi mai biyayya akan abinda beh saba mah Allah bah"

Tayi yar karamar hamma

"Taya ze iya hukun tata?" Ta kalli bayan shi kafin ta cigaba

"Ta kaurace mata,koh dukanta, amma bah wani duka can bah, dan saisa saisa kaman mah baka duketa bah,
Dan kai meh kareta ne"

Ya juyo da murmushi
"Basai kin ja abin bah, bazan taba mafarkin taba lafiyar jikin ki bah,
Kila in kaurace maki, that is in zan iya"
Da ma'ana biyu yayi maganar, ita kuma kid brain dinta beh kaita ghana bah

Sai abin ya bashi dariya

"Ta zama meh ladabi ga mijinta, tasan irin maganar da zata dinga fadamai, da kuma yin kwalliya mah mijinta,
Ta zama meh kyakyawan mu'amula da Yan uwan shi,

Sannan ta amsa kiran shi a duk lokacin daya kirata"

Tana kaiwa nan ta juya zata tafi, dama tun kafin ya gama dariya ta cigaba, dan ta samu ta gudu

"Husna" ta daga kafa dan kar ya cinmata

"Husna, yanxu kika gama cewa fah ta amsa kiran sa"

Da bacin rai ta juyo

"Ba irin wannan kiran nake nufi bah"

Yayi wani shu'umin murmushi, hade dacewa anzo wurin

"Ni ban gane bah Amore Mio, pls explain" tana bude baki ya katse ta

"In details kuma, filla filla nakeso, kin san mun tsufa, sai ana maimaitawa kafin mu dauka da kyau da kyau"

Kaman ta fasa ihu,
'Daga amincewa zan aureka kuma sai ka zama dan east na gaba da west'

"Mi Amor????" Ya fada kaman tana bata mai lokaci

"Ai kasan abinda nake nufi" murya kaman meh kuka

"Oh ni Ma petite, ba'a san malamai da boye ilimi bafa saboda suna jin kunya"
. data gano so kawai yake ta fada sai tayi niyyan gudu


Yar kara ta saki tana kokarin kwace hannunta

"Na sanki sosai Husna, toh fadamin meh zanyi expecting a daren auren mu"

Bude bakinta tace Mama na, tana shirin yin kuka

"Okay fine zan kyale ki, amma bamu gama magana bah"
"Ni bacci nakeji" tana cewa bacci yayi hamma

"Ka gani koh, mu bari sai da safe"

Kyale ta yayi, sannan ya nufi wurin fountain ya zauna,

Janta akayi ita ta kai kanta, Allahu Aa -lam, ita dai taga yana Murmushi data zauna a wurin itama,

"Nagode Husna" tace Na meh fah

"Loving Me, a yadda nake"
Ta dan bude eyes

"Ni yaushe nace ina sanka" yayi dariya yana nunata da yatsa

"Yan xunnan kika ce INA SANKA, kuma bakin ki ne kawai ke kokarin karyatawa,

Amma idanun ki sun yaudareki, dan sun fayyace min komai"

Ya karasa da small voice.





⚜B.W.AπŸ–Š
[3/26, 06:12] β€ͺ+234 706 870 0853‬: ⚜BRILLIANT WRITERS ASSOπŸ–Š




πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI.

πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

Story Editing NOBLE JUDGE,
Writing KHALEESI.

Dedications.

πŸ‘±πŸ»β€β™€πŸ‘±πŸ»β€β™€πŸ‘±πŸ»β€β™€πŸ‘±πŸ»β€β™€πŸ‘±πŸ»β€β™€πŸ‘±πŸ»β€β™€πŸ‘±πŸ»β€β™€πŸ‘±πŸ»β€β™€πŸ‘±πŸ»β€β™€πŸ‘±πŸ»β€β™€

YAR HIJIRA
NA
UMMU FARHANA

Ina meh tayaki murnar kammala wannan littafi nake, dake dauke da darrussa masu amfani,
Meh kuma wayar da kan Al-umma, hade da koya Mahimmancin juriya da Hakuri,

Allah ya amsa maki Addu'arki ya kuma baki ladan abinda kika fada daidai a littafin , akasin haka kuma ya yafe maki,
Meh maki fatan Alkhairi.



🌈BπŸ…°DAQALA
NA SIS ASMEENAT BESTY'N SURRAYHAMS,πŸ’•

Munji dadin NπŸ…°miji sosai, Allah ya kara fasaha da basira, na tabbata Badaqala sai yafi shi dadi da illimantarwa, Muna biye dake dan jin yadda zata kasance.β€πŸ‘ŒπŸΌπŸ˜‰πŸ€­



4⃣4⃣.


Hannu ta cusa karkashin pillow tana jawo wayar tata, idanu rufe ta ansa kiran

"Assalamu Alaikum"

"Sorry na tashe ki love"
Cire wayar tayi daga kunne taga ashe video call ne

"Na kagara in dinga farkawa kusa dake, in ganin ka messed up haka"
Saurin katse kiran tayi hade da mikewa tsaye

Tana gama daure gashin kanta kiran shi ya shigo wayarta

"Hello, ina kike" amsa wayan tayi ta aje saman gado ita kuma taje ta suturta kanta

"Meye na wani boyewa wai" saida tasa hijab kafin ta dauki wayan

"Ina kwana" ya amsa da lfy lau

"Har yanxu gajiyan tafiya ne" ta girgixa kai tana kallon agogo,

"Past 11" yace yap, kinji dadin bacci kenan koh

'Gani ga iyayena da yayye, ai dole inji dadin bacci'

"Listen Sweet caramel, Granny Ma na kan hanya, tun dazu ta taho, na kira inji in ta iso ne"

Gyara zama tayi tana san tantance abinda yake fada

"Meh zata zoyi" ya yi yar dariya

"Apparently akwai wasu steps da ake bi in za'ayi aure, kuma tunda baki da idda" ta kara sunnar da kai

"Mun yadda kar a bata lokaci ayi auren da wuri". Ya karasa da tsantsan Murna a muryar shi

'Cewa yayi kakar shi na kan hanya' zumbur ta mike tana gama wannan tunanin

Tana fitowa daga dakin da take kwana tunda tazo ta dan tsaya,kafin ta yanki wata kwana

"Uhmmmm dama ina son inyi magana da kai" yace ina jin ki


"Dan Allah in zakayi manah irin abinnan ka fara fadamin" ta kalli fuskar shi taga kaman beh gane abinda take magana akai bah

"Wannan gdan nake cewa, wannan yafi karfin school ta bayar"
Da hannun shi yayi mata alaman ta share

"Mungode, amma dan Allah ka fadamin in zaka dinga yi manah irin abubuwan nan,
Dan in san___"
"Dan ki hanani"
Ya katse ta

" niyya ne Husna koh kince Aa kar inyi, babu abinda ze hana inyi"

Tayi ajiyar zuciya tana kauda wayar daga fuskarta

"Banyi mamaki bah, abin a jinin ku ne ai, abinda kuke so shi kukeyi"

Taji yayi gyaran murya

"Ina nan har yanxu fah, kike magana da hausa, fadamin abinda kika ce"

Ta ce bakomai

"Na bata maki rai kenan, Am sorry"
Ta sake cewa

Please Login or Register in order to submit comment