Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Girgixa kai tayi


"An kusan kawomin kayana" tasa hijab dinta zata goge tears dinta,

Hannunta ya kara rikewa

"Dan Allah mu tafi Husna,in son inyi maki wani abu daze faranta maki rai"

Bayan ta kwace hannunta sai ta nufi motar dan tasan naci irin nashi,in dai yana son abu toh abinnan za'ayi

"Sha wannan" ya bude ruwa ya bata,
Karba tayi amma ta kasa sha,sai kallon ruwan da takeyi


"Na manta dazu nace ki kira sunana Γ—20"

Ruwan ta fara sha a hankali kaman ta samu wan juice meh sanyi 🍷🍷🍷🍷


Sparkle's spa and store taga an rubuta da pink paint meh kyalkyali


Sun shiga sukaci karo da provisions,

"Ci wannan " ya dauko mata inibi cikin wani farin leda da dabino

"Tnk u" ta fada kafin ta cigaba da binshi a baya


Sunje wurin biya,yana laluben aljihun shi sukaji ance ya barshi


"Khadija, an sanar maki da zuwana ne" ta amsa masu da murmushi


"Ka barta a hannuna kawai,zan kula da ita" jin jina kai yayi sannan ya fara bin boutique din da kallo


"Meh da meh kike bukata" kafin ta amsa ya rigata


"Everything, komai da komai,daga dinner gowns,casual wears, office wear, shoe's bag's accessories"

Dan jan matar daya kira da khadija tayi


"Black and White, simple abubuwa nakeso kaman guda biyu haka" ta ga bayanta take kallo


Da gira daya sama yayi mata tambaya

"Meh kike cewa" ajiyar zuciya tayi saboda irin karyar da akesata yi


"Abune irin namu na mata,bazaka gane bah" Khadija ta fada


"Okay zanyi nawa shopping din,karkiyi hanxari ki dauki lokacin ki kinji" saida ta maidamai murmushi sannan ya tafi


Skirt baki da fari guda biyu ta dauka,sai riga baki da fari,

"Zan so hijab mah baki da fari" kallonta Khadija tayi kafin ta girgixa kai


"Zo muje kiga, ba baki da fari ba kawai akwai colors da kuma irin kayan daya kamata ace kowace mace nada su a wardrobe dinta"

Bada san ranta bah ta biye mata taa zaban mata kaya


Flat shoes da kuma masu dan tudu, sannan ta zabi wanduna pencils guda uku, bags ne taki yadda ta hada dashi


"Shopping is fu,ashe shiyasa Alfie ke son lokacin canza kayan wardrobe dina yayi"


Daya bayan daya masu tsaron shi ke shigowa da kaya niki niki, duk wanda ya shigo sai gabanta ya fadi,


Duk ansa kayan cikin shopping bags,bata san meh da meh ya siya bah, kayan data zaba ta fara mayarwa


"No muje tunda da kanki kika zabi wannan" ya karaso yana kwashe kayan harda wanda Khadija ta zaba


"Muje ki zabi hijabs toh" rumtse ido tayi tana neman abinda zesa ya maida kayayyakin


"Bana bukatar dukan kayan nan plspls" beh saurareta bah ya wuce abinshi.


Hanata daukan kayan yayi sai shi da masu aiki suka kai har dakin da aka sauketa,


A takaice kayan zasuyi akwati uku,banda bags da takalma,


"Ina wuni hajiahajia" ta duka har kasa tana gaisheta


"Ban san iyayi, ki rike gaisuwar ki nasan badan Allah da annabi kikayi bah"

Wurgo mata wani book tayi


"Rubuta Alkawarin da kikayi na zama baiwata,kuma in kika saba alkawarin koh kuma na ga mishkila cikin aikin ki, yan uwanki zasu dandani kudar su"

Sannan ta juya mata baya,

Kafin kasani hawaye ya fara diga yana jika book din

'Ni kam a rayuwa banda sa'a'

Astagfirullah ta fara yi

"Ka gafarta min ya ubangiji"

'Na kasance acikin
tsoro ba wanda ze iya fiddani sai kai "HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKEEL", ta karanta

Bakin ciki nake kujewa ka agazamin,"LA ILAHA ILLA ANTA SUB'HANAKA INNEE KUNTU MINAZ ZALIMEENA"


Na shiga babban matsala "LA HAULA WALA ƘQUWWATA ILLA BILLAHIL 'ALIYYIL 'AZEEM"


Abinda ta cigaba da cewa kenan tana rubuta abinda ya zaman mata dole


Hajia kam har tayi bacci, dan haka ta mike dan sannin kan aikin nata,


Bata sake koma mah hajia bah saida tasan duk routine din Hajia da Ehsaas, sannan ta bukaci a kaita servant quarters.






⚜B.W.AπŸ–Š
⚜BRILLIANT WRITERS ASSOπŸ–Š




πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI
NA KHALEESI,
& NOBLE JUDGE


Babban RASHIN RABO na tare da wanda yabi kyautar Allah da πŸ‘ŠπŸ»πŸ‘ŠπŸ»πŸ‘ŠπŸ»,
Allah ya bar mana ke Jameela Musa (meelat), ya kuma biyaki dan kin fadakar hade da tunatarwa acikin littafinki,


SO MUGUN WASA,
na nan tafe
By
Meelat musa
Ku kasance da BRILLIANT WRITERS, danjin wannan kayattacen lbrin,basai na zuba surutu bah, sunnan novel din kanshi da takenshi ya faso,kada ku bari ya wuce ku.πŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌ



2⃣4⃣.



"Daki na goma sha bakwai" ya rufe sannan ya cigaba da bude dakuna yana kiran sunanta

"Husna!"
Gashi ya nemi ma'aikatan gdan ya rasa,
'Hutu suka dauka ko meh?' Ya tambayi kansa


Kaman tasan hakan ze faru ta shigo cikin gdan a lokacin

"Waye nan" da sauri ya koma dayan bangaren dayaji motsi

"Nice, zanje in kwanta ne" ya bita a baya

"Duk yau ina kika shiga,dazu nayi ta neman ki yanxu mah kuma naga dakin ki ba kowa"

Akwai wani dagan in yasan inda ta koma, dan kallonshi tayi a ranta tana cewa wai meye hadin ka dani ne


"Na fita waje nayi waya da mama na ne"
Yace. "Awwww,hw cute, har kin sa na kara missing Mom dina"

Harda rungume jikinshi yayi


"Mom dina bata yadda da zamana anan bah tunda na fada mata mu uku ne kawai a cikin gdan, tace beh dace ni matar aure in zauna anan bah"


Ya bata face yana kallon gefe

Ajiyar zuciya tayi tace. Wannan mutumin sangarta tayi maka yawa


"Zaka iya tsallake maganan mahaifiyar ka" ya juyo da sauri yana kallonta


"Dan Allah kice mata na dauki alkawarin kula dake,kuma bazan bari komai ya sameki bah, pls ki bata hakuri kice mata kema kina son zama anan tare dani"


A karshen maganar shi saida ya hada da shagwaba


"Ta yadda in zauna anan amma nace mata ba cikin gda nake zama bah,shi yasa na koma servants quarters dan kar ya zama nayi mata karya"

Zece wani abu ta katse shi


"Kana so inyi karya ne" ta dauke kanta da suka hada ido


"No!" Ya fada yana turo baki,

"Fynnnnnnnn, muje in rakaki" ya fada kaman an sashi dole


"Tnk u" tace bayan sun tsaya a cikin kitchen wanda ta nan zata wuce bangaren yan aiki


Yaune ranar shi na farko da ya taba shiga kitchen din tunda yazo,sai ya tsaya kallon yadda wurin yake,

Koda ya gama ta dade da barin wurin,


Kiran sallar farko a kunnenta,tashi tayi ta gyara katifar data kwanta sannan tayi shirin yin sallah,

Gari beh gama wayewa bah ta mike dan shiga babban gda


"Barka da safia" ya fada da murmushi

Da een eena ta amsa mai dan batayi tsammanin ganinshi bah a lokacin

"Jiya baki bari nayi maki sai da safe bah, zanje inyi bacci" ya fada yana daga mata hannu


Dakin hajia shine na karshe a bangaren hagu kuma gefen hagu,

Da sallama ta shiga jikinta na mata dar dar,

Babban parlor taci karo dashi wanda zeyi gdansu gabaki daya,an kawata shi da abubuwan more rayuwa iri iri,


Wasu abubuwan mah bata san sunan su bah,cikin tsoro da hanzari ta janye kafarta daga inda taji ya lume

Carpet ne kallar green,in ka gani zaka rantse real grasses ne suka girma a wurin,sai kasa kafa sannan kaji ya lume ciki


"Wai zaki shigo ne koh sai kin gama saka abubuwa cikin wannan katon munafikin hijabin naki"
Kaman an tunku data sai ganinta tayi ta iso dakin

"Hanaki sa hijab dinnan zanyi,dan karki dinga yimin yan dauke dauke"

Dukawa tayi har kasa ta gaishe da Hajia da kanta kasa


Tsaki hajia tayi bata ansa bah,duk da ladabin ya tabata


"Munafurci, a zuci kina zagina a fili kina mun ladabin karya,ni zo nan"

Har tuntube takeyi da zanin jikinta saboda sauri,


"Gani" ta fada murya kasa kasa cike da ladabi


"Sauko dani,ki kaini bathroom, ko kuma yi setting mun shawa din tukunnan, ina san ruwan da dumi sosai yana fidda surace"


Tashi tayi ta shiga bandakin, da tana da lokaci data tsaya kaallon wurin,


Akwai bathub,sannan jacuzzi, ga wani wurin zama meh labule,ta wani gefen mah kuma ga wani wuri shima meh labule saidai bah wurin zama kaman dayan,


"Ni dama nasan incompetence dinki sai ya samin ciwon kai, daga saita min shower ki fito shine har yanxu"

'Na shiga uku' ta fada tana rufe baki da hannunta,

Wani abu kaman iPad ta gani like jikin bango dan haka ta nufi wurin,

Duk da tana ji da kokari saida tayi shirme irir kafin ta samu ta daidaita ruwan shower zuwa medium da steam,


Sharkaf ta fito tana tsiyaya, har lokacin hajia na kwance saman gado


Da sauri ta taimaka mata ta tashi zaune sannan ta mikar da ita tsaye, Hajia sai yi take kaman tabatan da Asma'u keyi na satq kyama 🀒🀒🀒


Ciwon jikinta ne ya tashi,ba kaman kafafunta sunfi addabarta da ciwo,


Shower meh wurin zama ta ajeta sannan ta fito ta bata wuri,cikin kan kanin lokaci ta fara attishawa saboda ruwan sanyi daya jikata ga kuma a.c har biyu na hurata yadda ya kamata.


Gyaran gado tayi sannan ta jira fitowar ta daga wanka,


Cikin kaya na alfarma ta fito da hijab a hannunta,

"Zauna inyi sallah sai ki min tausa" ta wullo mata wani magani


"Sannu" ta fada da sauri dataji hajia tace wassshh daga fara danna mata kafafu,


Bata bar aikin da takeyi bah har hajiya tayi bacci,


"Allaahumma lakal-hamdu ' anta kasawtanee, ' as'aluka min khayrihi wa khayri maa suni'a lahu, wa'a'oothu bika min sharrihi wa sharri ma suni'a lahu."

Tofe kayan tayi da saka sanon kaya kafin ta iya zirawa,

Bakin skirt da wata tshirt baki meh tsawo,wanda da'alamu da wando akeso ta sashi, wani farin gyale ta daura a kanta dan kar bakin yayi yawa, kafin tasa bakin hijab,


"Asma'u ina breakfast dina" Zaro idanu tayi dan cin abinci ba damunta yayi ba haka zalika ta manta da hadawa hajia karin kumallon ta


"Bari in kawo maki yanxu, anan koh a dinning table zaki ci?" Ta tambaya kai kasa


"Zan sauko kasa,ki tabbata komai is ready".
Tana rufo kofar ta fantama a guje ta nufi kitchen

Tana inna lillahi a ranta,

"Meh zanyi, wani irin abincin yan gayu na iya"

Gashi babu wanda zata tambaya, masu aikin gdan duk sun gyara ko ina sun tafi.




⚜B.W.AπŸ–Š
⚜BRILLIANT WRITERS ASSOπŸ–Š




πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI.

NA KHALEESI.
DA NOBLE J
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’



2⃣5⃣



Gdan yan gayun data taba shiga shine gdan su Ma'u, kuma bata cika kallon iyayin da Ma'u ke kwabawa a kitchen bah,

"Irish potatoes mah zeyi, koh"

Sashen masu aiki taje,inda ta samesu suna dafa nasu abincin,

"A can babu kayan abinci,sai kinje dayan babban kitchen din sannan"

Tambayar inda babban kitchen din yake tayi,akayi mata kwatance


"Nagode" da hanzari ta koma makeken gdan sannan ta nufi kitchen din dake da store,


Manayan dankali guda 6 ta dauko sai kwai hade da veggies din da zata bukata, tana bude freezer taga abubuwa iri iri ko wanne da sunan shi a jiki, bacon da sausages ta dauko dan ta taba ganin an kawo ma Ehsaas lokacin da take P.A dinshi


"Where have you been?" πŸ‘€ ta zuba mai

"Husna,its past 8" ya nuna hannunshi kaman akwai agogo a jiki

"Ina nan,aiki nakeyi" ya bata fuska

"Kin manta P.A dina nace zaki koma,basai kinyi duk wannan abubuwan bah"

"Cikin ayyukan da zan dinga yi dai" ta fada da hausa

Hannu ya dora saman kugu

"Meh kika ce" saida ta rumtse idanunta kafin ta dago kai

"Ina son inyi maku brkfst ne kai da Granny MA dinka, saboda in nuna godiyata akan Alkhairin da kukeyi min"

Jingina yayi da wurin hada abincin,sannan ya dora hannayenshi sama

"Duk sunan da kika kira sai inji kaman babu wanda ya kaiki iya kiran sunan, pls say my name"

Ding din oven din ne ya ceceta, alaman abinda tasa yayi,

"Yi hakuri grandma dinka na jirana"

Ta fiddo plates ta jera saman tray sannan ta hau serving abinda ta dafa


"Tana son Green tea kuma" ya fada yana tayata jera komai


"Tnx" tace zata tafi

"Wait! Ni fah". Ya turo baki πŸ™Žβ€β™‚πŸ˜”

" yanxu zan dawo sai in kawo maka"

Zuwa gabanta yayi yana hada hannuwa wuri daya


"Don't be late,dan zan jiraki" ya kashe mata ido dayaπŸ˜‰


Bayan tayi addu'a a zuciyarta sai ta yi sallama sannan ta bude kofa, wata mata tagani tsaye daga gefen hajia

"Gashi"
Da yatsa hajiya ta nuna ta

"Na fahimta da kyau madam" kafin ta fita daga dakin


Attishawa ta jero har guda biyu, tana daga ido taga ita take kallo


"Sorry" ta juya zata tafi


"Kina da wani contagious disease ne, dan karki goga min"
Girgixa mata kai tayi

"What is this" dago kai tayi taga hajia na kallon yatsanta


"Banga komaibbah hajia" bayan ta kura ma finger din ido bataga komai bah


"Its dust,kura a dakina, no wonder kke ta attishawa, keda kika ci tuwo kika rika kenan inaga ni"

Dukawa kasa tayi tana bata hakuri


"Ki bacemin da gani,kije kiyi abinda ya kata"
Da gudu ta fito,tana zuwa kitchen ta hada mai brkfst dan ta kaimai


"Shigo" ya fada daga cikin dakin bayan tayi knocking


"Gashi, kana bukatar wani abune kuma"

Kanta a kasa yake shi yasa ya bita da kallo


"Black nayi maki kyau" dan dago ido tayi ta kalleshi saboda yadda voice dinshi yayi kasa kasa


"Zan tafi" da sauri ya tsaidata da wait


"Baki fiddo min kayan da zansa bah, koh daga towel sai bathrobe kikeson gani na"


"Na shiga uku ni Asma'u, ban san meh ke ranka bah dan haka bazan ce komai akan ka bah tukunna"

Kafin ta matsa ya sha gabanta

"Meh kikace" ta ware idanu dan kallon tuhuma yayi mata


"Sake fada in ji" ya fada da turanci


"Ya ilahi, u hav d sexiest eyes" πŸ‘πŸ‘

saurin dukar da kai tayi
"Ba bataun baka lokaci, wannan iskanci haka"

Taji kaman ta bangaje shi ta wuce


"Am sorry plss pls pls pls pls pls". Haka yayi tacewa pls yana tare mata hanya har saida ta ce bakomai sannan

"Phewww, a raina sai naji kaman kin yanke hukunci a kaina wanda kuma ba haka bane"

Suit ta fiddo mai dan su kadai gareshi a jere cikin dakin kayan nashi


"Excuse me" kaman ya rikota sai ya ja baya kuma


"Am sorry, dan Allah ki koya koyamin yaren nima" dan goge face dinta tayo da hannu


"Ina kwana, good morning kenan"
Da farin ciki ya fara maimaitawa


"Zan fita tareda Ehsaas ki tabbatr kin gyara ko ina hade da dafa mana abinci"

Kanta duke ta hada da toh, tana rike da tsintsiya da parker sai ledar zuba shara,


Da daki ta fara, tana cikin yi taji muryar shi alamun yana shigowa



"Husna!" Aje kayan aikinta tayi sannan ta tare shi kafin ya shigo



"Wai zamuje wani wuri yau" bayan shi ta kalla inda hajia ke tsaye ta hade rai


"Eh am sorry ban fada maka bah, pls forgive me" kaman yasa hannu ya dago habarta

"Meye abin neman yafiya" clapping yayi wanda ya ja hankalinta gareshi


"Muje mu shirya toh, ya kamata muyi color co-ordination"

Har yayi gaba ya dawo baya

"Banda pink color, ina da reputation da zanyi maintaining"
Ya kara kashe mata ido daya


"Sai ki san yadda zakiyi dashi dan babu inda zani dake, nima ina da reputation dinah"
Tayi tsaki kafin ta taka cikin takalminta meh dan tsawo


Bakin kofar dakinshi taje ta tsaya,tana jira ya fito tace mai baxata iya zuwa bah


"Yauwwa dama wurinki zanje" taji maganar shi ta bayanta

"Ina wayar ki?" Ya fada da nashi wayan a hannu


"Yana daki?" Tayi mai karya dan wayar na jikinta,bataso yaga ta fiddo da shine

"Okay muje ki zaban min kayan, sannan ki kirani dan inga wanda ke zaki sa"

Tsaye tayi tana kallon ikon Allah,da baki bude


"Husna" ya hada yatsun shi a gefen fuskarta

"Muje manah"
Hajia ta gani tareda matar dazu suna nufo inda suke


"Bana son wannan wasan kwaikwayon ya wuceni"

Ta fada da annashuwa

Lokaci daya ta duke kasa tana dafe cikinta hade da dan kara Ah Ah Ah.




Pls manage wannan, am busy yau dinnan.😘



⚜B.W.AπŸ–Š
⚜BRILLIANT WRITERS ASSOπŸ–Š




πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI.

NA KHALEESI,
DA NOBLE J.
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’


2⃣6⃣.



"Are you okay" ya duka shima yana zaro idanu

"Husna, talk to me" ya fada da damuwa

Dan marairaice fuska tayi, tana dan tabe baki

"Cikina, ya fara ciwo kuma" ta fada tana rufe baki da hannu dan kar maganar ta ya bada ita


"Sorry, yanxu ya fara" ta girgixa kai

"No yana danyi kadan kadan Arghhh"

Ta kara dafe cikin tana dukar da kai hade da rumtse idanu


"Kuje kawai ni bazan iya zuwa bah"

Hajia na daga gafe tana kallon drama,fuskarta cike da mamakin yarinyar


"No tashi muje asibiti" Turancin nashi ya fara fitowa da kalmasa irin na yan Australia


"Bazan iya tafiya bah kawai ku tafi" ta yi kaman zata kai goshi kasa

"Inna lillahi this is serious "

Batayi aune bah taji ya dauketa chak yana mata sannu yana nufan stairs


"Ka saukeni, Arghhhhhh" ta fara ihu dan ta tsorata, shi kuma ya zata duk zafin ciwon ne


"Ku fiddo min mota, granny ma she's in pain" πŸ˜–πŸ˜–πŸ˜–πŸ˜–πŸ˜–πŸ˜–


"Ehsaas ka sauketa koh, ina zakaje da ita"
Hajia ta fada tana bin steps daya bayan daya shi kuma bibiyu yake tsallakewa



"Arghhhhh"😱😱😱😱😱😱😱 ita kuma sai aikin cika gdan takeyi da ihu tana kokarin sauka


Ta rude hade da daburcewa kawai so take taga tayi nisa dashi


Garin saurin shine da tsallen da takeyi a hannunshi sukayi tumbling daga matattakalar.

Hajia da sauri ta karaso inda sukayi crash landing


Shi kadaine duke a kasa,ita kuma ta mike tana waige waige koh ciwon da jikinta ya fara bataji bah kawai so take ta ganta ita kadai


"Husna calm down asibiti zan kaiki yanxu"

Yayi kokarin mikewa dan ya kwantar mata da hankali, kafin ya isa gareta Hajia ta rigashi


Wani lafiyayyen mari ta wanka mata πŸ‘‹πŸ»

Lokaci daya ta dawo h@yyacinta ta dafe kuncinta


"Grandma!!!" Ya shiga tsakaninsu,
Saura kadan marin datayi niyyar sake kaimata yayi landing a face

Please Login or Register in order to submit comment