Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Dan gyara zamanta tayi

Abin dariya ya bashi,

Kaman tana shirya mah wani gaggarumin abu,

"Wifey dina tawa ni kadai"
Ya maida mata towel din sannan, ya fara wanke mata kai,

Kaman tafiyar tsutsa haka hannayenshi ke yawo cikin gashinta,

Komai a natse yakeyi mata,

"Tnk u" tace daya gama wankewa yana goge ruwan da towel,

Juyata yayi ta kalli madubi, fuskarshi ya kawo daf da tata, ya cigaba da kallonta ta madubi,

Kanta kasa tana wasa da yatsun hannunta,

Ajiyar zuciya yayi sannan ya hade hannun shi da nata,

"Husna, fadamin wani abinda bakyaso"

Bakomai ya bar bakinta kaman tana shirin yin kuka,

"Koh bazaki iya fadamin bah" wannan karon ta girgixa kanta,

Kaman tasan kallonta yakeyi, tana kallon madubi suka hada ido,
Murmushi ya sakan mata meh alamun it's okay,


"Kullum da haushi na kake kwana"
Kallon tambaya yayi mata,

"Mun dade da yin aure__" bata karasa bah sai kasa data sadda kanta,

Juyo da ita yayi sannan ya tsugunna kasa, suna kallon juna sosai,

"Ban taba kwana da bacin rai akan ki bah Husna,

True bacci na rabi da rabi ne,
Abinda nafi damu dashi shine ki gujeni,

Amma ni ban taba ganin laifin ki akan kowani abu bah,


Mun magance kashi 7 kicin 10 na matsalar nan,
Nasan kina da karancin shekaru, amma wayau da basirar ki yafi na wani meh shekarun,

koh ke baki lura bah,

Ina maki uxuri saboda karancin shekarun ki,

Yadda kike kallona mah kanshi ya canza"

Yasa hannayenshi a gefen fuskarta,

"Kin daina firgita in na tabaki, kina sakewa in muna tare,

Kin rage jin kunyata kuma"

Yayi kasa da idanunshi suka sauka a lips dinta,

"Nasan ranar da zanyi kissing lips dinki senselessly na zuwa"

Dan pink harshenta ne ya fito ya lashe lips din, shi kuma ya cije lips dinshi na kasa,

"Yi hakuri Ehsaas aski yazo gaban goshi"
Yar dariya tayi

"A fili ka fada" ya dago suka hada ido

"Na sani, daga yau abinda nakeji gameh dake shi zan dinga fada maki"

Ta dan kauda kai gefe, kunya takeji kuma a lokaci daya tana jin dadi

'Yaushe hakan ya faru da bata lura bah'.


Page na gaba ta bude meh ❌ a jiki,

Ranar bata rubuta abinda taji dadinsa bah kenan,


"Ya maganar mu daughter" tace lfy lau Mom

In uwar miji bata sanka akwai matsala babba,

Gashi koh Ehsaas ta kasa fadamawa, dan abinda Mom kesan tayi ze jawo mata fitina neh koh ta fada koh bata fada bah,

"Lfy lau" ta watsoY mata magun guna dayawa,

"Wasa nakeyi dake" tana ganin su tsoro ya shigeta,

Bayan kwana biyu da bata maganin, duk sadda ta tambayeta tasha sai tace Eh,


"I promise you kika sake kika dauki cikin dana ki kuka da kanki,

Ina binki ta lalama amma hakan baze dore bah in kina min wasa da hankali,

Ina da idanu da kunnuwa a ko ina,
Nxt tym kika so fadamin karya ki tuna haka,

Understand?"

Tayi saurin jijjiga kai

"Good, fadamin abinda ke faruwa tsakanin ki da dana"

Tace bakomai
"Toh meh yasa bakya sha"

Ta dukar da kai kasa,

"Meh hakan ke nufi, wulakanta dana kikeyi"

Tayi saurin girgixa kai, kwalla na san zubo mata

"Karya kike kice haka nan dana ya zauna ya zuba maki ido"

Ta daga mata kai,

"Meye dalilin da baya kusantar ki,
Kin san kina kara bata lokaci ne koh,

Koh bakida BOYAYYEN KUDIRI kuma"
Gabanta ya fadi

' ya akayi ta sani, diary dina ta karanta'

Ranta yayi matukar baci amma ta danne bata nuna bah,

"Ina dashi har yanxu" ta rasa inda muryar da tayi magana dashi ya fito, wani kakkausa


"Da kyau ina son mutane masu buri,

Ki cigaba da yin abinda nace, KUDIRIn ki ze cika"

Sukuku ta koma dakin su,

A diary dinta ta rubuta tana da BOYAYYEN KUDIRI na zama matar Ehsaas na dan lokaci,

Jiya kakar shi ce ta tsane ta, yau mamanshi, wa ya sani koh gobe shi ze tsane ta,

Zata bi kowace rana a yadda tazo, baxatayi kokarin barin su bah,

Dan tasan hakan ne ze faru, tunda har an shirya komai.

Tayi kuka kaman ranta ze fita, data lura Ehsaas na cikin ko wani bangare na rayuwarta,

Koh gida ta tafi Albarkacin sa zata cigaba daci, haka makaranta tunda da kudinsu babanta da yayyanta ke daukan salary,


Ba'a dade da yin wannan episode din bah, ciwon hajia ya tashi,

Babu abinda take ambata sai danta, Yarima,

Batayi mamaki bah da kowa ya yadda a hadasu, amma banda Mamanshi,

Ranar fadan iyayen nashi mah yafi na kullum, har shi saida ya tanka da suka shiga dakin Hajia dan dubata,


'Wai meke samun iyayenshi ne yanxu, da wuya babanshi yazo weekend basuyi fada bah, gashi yanxu yana nan har a gama azumin Ramadan'

"Karki damu Granny MA in shaa Allah zan samu hanyar hadaki da uncle Yarima"

Da idanunta rufe tace na gode Ehsaas,

Duk yinin ranar beh hadu da iyayenshi bah, kuma yaji dadin hakan,

Sai da gari yayi duhu, motsi ya rage sannan ya saci jiki ya fito daga gdan,

"Ina zuwa Ehsaas? Da daren nan?"

Saida ya dora hannun saman kirjinshi yana dukar da kai,

"Dad ka tsora tani" ya fada da babban murya,

"Maganin ka kenan, naga kana sando ina zuwa?"

Ajiyar zuciya yayi

"Zanje wurin Amyr ne, nayi mah Granny Ma Alkawarin hada ta da Danta"

Jin jina kai babanshi yayi,

"Haka ni mah, shi yasa zamu tafi tare,
Yanxu mamanka ta shiga kiran ka dan ka nuna manah gdan"

Ya dauke kai

"Har kun shirya kenan?" Ya zata a ranshi yayi magana,
Dariyar babanshi ya sanar dashi a fili yayi,

"Sorry Dad"
"Bakomai Ehsaas, na tabbata hakan ze dame ka ai"

"Gata nan zuwa"
Gaba yayi ya barsu suka taho tare


Juyawa yayi ga iyayenshi

"Nan ne gdan" beh gama rufe baki bah aka banko gate din,

Karar naushi da muryar gardawa na ihu kawai ke tashi daga cikin gda,

"Ehsaas ka tabbata nan ne gdan" babanshi ya tambaya

"Yeah" yana jin wata karar ya tukari gate din

"Ehsaas get back here" mamanshi ta fada da ihu,

"In yana bukatar taimako fah" ya cigaba da tafiya,

Yana fara bubbuga kofar gate din aka bude,
Da bindiga yayi karo

"Sorry kai saidai in aika ka lahira na gaji da jibgan mutane, jikina duk ciwo yakeyi"

Idanu ya fiddo waje duk da beji abinda yace bah da hausa, amma kan bindigar da kallonshi,

"Ehsaas!" Mamanshi ta fada da ihu tana ruguwo gareshi,

"Ehsaas?" Amyr yace da karamar murya

"Oh dude ashe kaine"

Karasa fitowa yayi daga cikin gdan dake dun dum saboda duhu,


"Inna lillahi kai haka akeyi, sai kace da manyan baki kazo"

Ya karasa zancen da karamin murya,

Da fara'a ya gaishe da iyayen nashi, dan dukawa yayi ya gaishe da Mom,

Har ze mika mah Dad hannu yaga yadda yake kallon shi,

"Dan Allah kuyi hakuri, amma ba haka nake bah, ranar yauce kawai ta baci"

Hannun shi duk jini,

Duk abinnan da sukeyi mutanen daya jibga na kukan azaba daga cikin gda,

"Dan Allah ku bani minti daya"

Gate yaje ya bude baki daya, sannan ya sabo mutane biyu ya jawo daya waje, ya wurgar kaman shara,


"Ku shigo toh"

"Kana hauka in kana tunanin zamu shiga,

Magana zamuyi daga nan ya isa"

Fara'ar fuskar shi ta dauke gaba daya

"Naji dadin ganin ki kema" ya fada da sassanyar murya,

"Ni dama nasan saidai wani abu ya kawo ku, badai zumunci bah,

Koh zan iya tambayan menene"

Gyaran murya babanshi yayi saboda da hausa suke magana,


"Am Mas'ud, my son Ehsaas, nasan kun hadu"

Amyr ya daga mai kai,

"Yes naji abubuwa dayawa akanku, nama fi jin dadi dana ganku face to face"

Uhmmm babanshi yace

"Abinda ya kawomu nada mahimmanci, bayan abinda muka gani, bana tunanin it's safe mu shiga gdan ka"

Mutanen daya aje a gefen titi ya kalla,

"Dan Allah kuyi hakuri, yanayin aiki nane haka,

Kullum masu kokarin kamani koh kashe ni karuwa sukeyi,

In abin meh mahimmanci ne kaman yadda kukace
Saidai muyi magana akai yanxu,

Dan yau zan bar gdan nan,

Makiya sun san inda nake zama"

Ya karasa yana kallon Mom data dauke kai,


"But pls ku shigo ciki"

"Beh dace in barku nan tsaye bah"

Ciki suka shiga,ya basu mazauni sannan ya wanke hannu da canza kaya,

"In kawo ruwa koh"

Barshi Mom tace

"Waya san abinda aka sa aciki"

Dan murmushin takaici yayi kafin ya zauna,

Yaso ace shi koh babanshi yayi magana, amma Amyr na zama mamanshi ta fadi abinda ya kawosu,

Beh san abi da takecewa bah, amma yasan beyi mah Amyr dadi bah,

"Baze zo bah"
Ya fada a takaice

"Wow! Har yanxu asirin munafukar uwarka na aiki"

Lokaci daya fuskar shi ta canza, duk yadda yaso ya boye amma saida bacin ran ya nuna,

"Safiya!" Babanshi ya katse ta,

"Abin haka ne har yanxu yana aiki"
Amyr ya fada kafin Iyayenshi suce wani abu,

"Shima kuma yuyuyu din beh da zuciyar tashi tsaye ya yi abinda ya kamata,

Allah wadaran naka ya lalace"

"Na kasa yadda da abinda nakeji daga bakin ki"

Beh bari ta cigaba bah ya daga mata hannu, sannan yayi magana da turanci

"Zanji kowani zagi da zakiyi min , kila in saurareki in kika aibata mahaifiyata,

Amma bazan saurari kowani zakin da zakiyi mah bawan Allah nan bah,

While kuna can bakwa nan bakisan yadda lfy dinshi ya juya bah,

Baki damu enough daki san halin da yake ciki bah, but kullum fatan Alkhairi yake maku, ke da yayanki everything,

Koh daurin auren Ehsaas ya sani tun kafin ku aika da invitation,

Kuma da babu abinda ze hana suyi celebrating a gda,

Basu taba mantawa daku bah,
Bakwa nan ne kawai a ido, amma a ransu kullum kune a ciki,

Baku dade da barin garin nan ba komai nashi ya juya upside down,

Ya rasa matar shi, danshi,
Gaku bakwa nan,
Ba'a dade bah mahaifin shi ya bar duniya,

Kinsan duka ragamar kula da dynasty dinmu ya koma kanshi,

And we were losing everything,

Dole ya tashi ya dauki nauyin kula da Maliks, dan kar kowa ya rasa farin ciki da iyalin shi,

Da kuma kusan inda suke in kun dawo,

Haka kullum yake kula da farin cikin kowa, bayan shi a raye yake amma bah rayuwa yake yi bah,

So dan in ga asalin farin ciki a fuskar shi zanyi wannan abin,

Na tabbata ganin Mahaifiyar shi ze kawo mai, hope din farin ciki,

Amma da sharadi daya,
Ke bazaki hadu dashi bah,
Har sai kin cire wannan kiyayyar ta ranki,

In zakiyi kiyi mah wadan da sukayi miki bah masu binki da Alkhairi bah"

Gdan shine amma shi ya tashi ya basu wuri,bah

"At least mun samu abinda muke so"
. babansu yayi baban kuskure daya fadi haka, Dan har shibari bata

Dan har suka koma gda mamanshi bata bar dura mah Amyr ashar bah,

Sunfi sati kowa na taka tsan tsan da ita,
. daka kalli fuskarta mah,
Alamomin danja zaka gani a rubuce,

In ka tabata zaka ji shocK,


Granny Ma ce kawai bata san wannan sharadin bah,



Bayan kwana biyu, anata shirye shiryen azumi, shi yasa bata samu ta sake rubutu a diary dinta bah,

Kuma tana da abin rubutawa meh βœ”, ta fara tunowa



"Badai waka kake ji bah" beh bude idanun shi dake lumshe bah,

Amma ya sakan mata murmushi meh kara bugun zuciya,


"An dai kusan fara azumi"
Ta haye saman gadon,

Yana jin ta hau ya jata jikinshi, suka makale can karshen gado,

"Kiss me under the light of a thousand stars"
'Ki sumbace ni a karkashin hasken dubunnen taurari'


"Place your head on my beating heart"
'Ki daura kanki saitin inda zuciyata ke halbawa'

"Am thinking out loud"
'A fili nake tunani'

Ya goga habar shi saman kanta,

"Abinda nake ji a cikin raina, zuciyata ta kasa boyewa
Tunani na ya fara fitowa fili"

Headphones din dake kunnen shi ya cire yana sa mata a kunne,

Da wuya yaji sabon wakar soyayya beh bata taji bah,

Bakaman in sun fita lambu, iska na kadawa kalaman so na tashi da kida meh sanyin dadi,

"Kinji dadin wannan?" Ta daga mai kai, bayan ta cire headphones din,

Daga kai tayi ta kalleshi da ya dade bece komai bah,

Har yanxu idanun shi a lumshe suke,
Gashin kanshi da girarshi taga sun hargitse,

Ba bata time tasa hannu ta kwantar mai da gashin kanshi, sannan ta kwantar mai da gashin girar shi,

"Yayi yanxu?" Ya tambaya da yar dariya a muryar shi,

"Saura kadan" tace,

Idanun shi lumshe,da murmushi a fuskar shi ya kyaleta,

Koh kwakwaran motsi bayayi saida tasa babban yatsanta tabi karan hancin shi,
Tana dora yatsanta saman lebenshi na sama, sai lumfashin shi yayi sama,

"Husna" murya na rawa ya kira sunanta

"Yanxu nasan abinda yasa shagwaba keyi maka kyau"
Ta cigaba da shafa lip dinshi na kasa, sannan ta tsaya a tsakiyan leben

Tsakiya kaman yar tsaga ce a wurin, ga lips din cike, naturally mah kaman turo leben yakeyi,

Harshen shi ya fiddo ya dan lashe leben hade da yatsanta,
"Ewwww" tace tana saurin cire yatsan ta daga bakin shi,

Damke hannu ta yayi sannan ya bude ido,

Kokarin nokewa takeyi saboda yadda yake kallonta,

"Ehsaas" tace a hankali, sai yaji kaman gayyata ce da izini sunan shi data kira,

Saida lokaci ya kure sannan taga matsowar shi daf da fuskarta, kiss yaso kaima bakinta, ta samu ta kauce, beyi kasa a guiwwa bah ya hau sumbatar kumatunta,

Gam ta rufe idanunta,tun tana kan kame jikinta tana kokarin tureshi, harta saki jiki, tana jin dadin abinda yakeyi mata,

Da zafi zafi yake kissing daga kumatun ta har zuwa wuyanta,

Bude idanu tayi da taji yana kokarin sabule mata hannun riga,,

"Ehsaas" ya kara shigewa jikinta data kira sunan shi,

Ringing din wayar shi ta katse su,
Yana sakinta ta gangara can gefe nesa dashi, sai ajiyar zuciya suke saukewa,

Ana sake kira ya dauki waya,

"Ahemm, uhmmm, yeah Amyr yes" yace yana sauka daga saman gadon,

Bandaki ta shiga tana mamakin abinda ya faru,
A madubi ta kalli kanta, dan kwalin kanta ya cire, saman rigarta bude, ga wani ja da wuyanta yayi inda yayita kissing dinta,

Murmushi tayi ma kanta, sannan ta dukar da kanta,wai taba kanta kunya,


Ita kadai taji kunyarta, shi daya dawo beh nuna yasan wani abu ya faru tsakanin su bah,

Sai labarin daya bata na cewa Hajia taje duk sadda ta shirya ta hadu da danta,

Friday din farko cikin watan azumi ta zaba, dan ganin dangin ta.






⚜B.W.AπŸ–Š
⚜BRILLIANT WRITERS ASSOπŸ–Š




πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI.

πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’


Story, editing by NOBLE JUDGE,
Writing KHALEESI.



5⃣2⃣.


"Ke wuri kawai kika samu kikayi ta rafka kiba abinki"

Matar da Hajia ke magana da ita ta rafka tafi hade da buga cinya

"Ai ni na tausaya ma kaina a haka, in kika ga Hikima"
Ta dora hannu saman baki tana girgixa kai,

Sa'ointa ne da suka taso tare, wasu daga ciki mah rana daya aka daura masu aure,

Gidan data raini yayanta ya canza sosai,

Da babban gda ne, amma yanxu unguwa guda ce, babu mah katanga yanxu, sai wani dan gutun daji daya kewaye wurin


Gidaje iri daya guda biyar masu bene ga kuma girma, sun zagaye wani katon mansion dake tsakiya, koh ba'a fada bah tasan nan ne zataga muradin ranta,


"Ina safiya? Naga danta daxu da Amyr"

Hajia ta dan hade gira

"Zata zo in ta shirya, ga azumi kuma fita tana dan wuya"
Tana shiru da baki, Mahaifiyar Nafi, wacce suke magana tare ta fito,

Kasa ta duka ta gaishe da ita, kaman uwa haka ta dauketa


"Bakomai mama, ya wuce ai"
Aka sata zubda wasu hawayen, dan tsananin farin ciki ji take kaman zuciyarta zata buga,

"Yanxu zaki shiga ki ga Yarima din koh"
Tace eh tana mikewa,

Dan duk ta leka dangin nata, saura wadanda take so kuma take tsoron gani,


Da ta shiga nasu gdan sai taji shi daban, ba kaman na sauran bah, nasu tsit babu guje gujen yara, koh alaman mutum bata gani bah,

Sallama ta kwada tana bin mattatakala zuwa sama,

"Umma" taji zuciyarta ta tsaya,
Bata iya juyawa bah sai shi ya iso inda take,

Hawaye suka tsiyayo mata,
"Sorry ina office dina ne"
Ya tsaya gabanta,

"Umma" ya fada a hankali, fashewa tayi da kuka, sai ya dafota su haura sama


"Umma zubar da hawaye kuma?, naxata haduwar mu ze kauda hakan"
Saman gado ya zaunar da ita shi kuma ya samu wuri kasa a gabanta,

Irin kallon da yakeyi mata meh dauke da tsantsar so da kauna shi ya kara narkar mata da zuciya,

Fuskar shi ta shafa tana murmushi,

"Dan Allah ki yafemin umma" girgixa kai tayi alamun ya bari kar ya cigaba,

"Wallahi ban sani bah, dana sani babu abinda ze hanani tsallake kowani teku ne, in rarrafa inzo in da kike"

Muryar shi tayi rauni, kanaji kasan akwai radadi a zuciyar shi,

"Ban taba kawowa a raina cewa asiri ne yasa yayi abinda yayi bah,

Duk da nasan ba haka yake bah"

Ya kalleta da idanun da suka rine zuwa jaa

"Ya wuce dana, Allah yayi maka albarka, ya yafe manah gabaki daya" kanshi ya dora saman cinyarta yana ajiyar zuciya

"Nayi kewarku sosai umma, harda meh kai kaman na kwakwa din nan,
Wai tana ina mah?"

Ajiyar zuciya tayi hade da hmmm

"Tana nan, kasan yadda take, nasan zata zo"
Shima hmmm din yace

"Nasan ta fah umma, tunda dai bata biyoki bah nasan wani abu ne nayi mata,

Laifin meh nayi mata yanxu?"

Yayi tambayar

"Gani take ka juya manah baya ne,

Kuma" ta kasa karasawa

Saida ya daga kai ya kalleta

"Ka gasgata mata daka ki koran Hannah bayan babanku ya rasu"

Ya tashi zaune yana kallon mahaifiyar shi

"Nima kuma ina son sanin abinda yasa take zaune har yanxu"

Kasa ya kalla kaman yana jin nauyin abinda ze fada,

"Umma irin tsanar danayi mah Hannah bayan tafiyar ku baxe misaltu bah,

Amma da abba ya kamu da rashin lfy, ta tsaya tare dashi, ciwon hunhu, Kinsan abba yakan sha taba in abubuwa sukayi mai yawa, ga ciwon siga, hawan jini, daga karshen rabin jikin shi ya daina aiki,

Duk ita ta kula dashi umma, karshe i had to accept matar shi ce, hakan ba yana nufin na yafe mata bane bah, amma ta dan shiryu"

Ta dan rufe idanta na yan sakans

"Kafin nan mah danayi accident, ta bani mamaki sosai yadda ta kula kaman ita abin ya shafa,

Wadan nan nasan ba dalilai ne na barinta anan bah,

Amma Amyr kanina ne, baxan kori mahaifiyar shi, shi kuma in ajeshi bah,

Dana rasa dana, umma shi ya debe min kewarshi,

Yana kyautata min sosai"


"Zefi zama mata Alkhairi ai in ta shiryu"
Ya jin jina kai,

"Umma zaki dawo nan da

Please Login or Register in order to submit comment