Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka dawo daki,

Abaki ta bata abincin, shima baci take sosai bah


"Hehehe, Hajia labari da dumi duminta, na aiwatar da KUDIRIn da kika dauka"
Tun kafin ta karaso dakin take wannan zuban, tana zuwa ta iske Asma'u sai tayi shiru

"Jeki saina bukace ki" ta kalli hajia da fuskan tausayi

"Hajia baki ci abincin sosai bah, gashi bakya da lafiya"
Hajia ta bude baki

"Ki fita idona in rufe, ban san wannan shishigin da kikeyi min, ki tsaya a aikin da kikeyi, in kin manta in tuna maki, kina cemin sannu a baki a ranki kina tsine min, munafurcin talaka ne ban sani bah"

Dan karta kara bata mata rai saita tattaro kayan abincin

"Har a waya na dauko maki dan kar kallo ya wuce ki hajia"

Ta fita ta barta tareda secretary dinta,


"Granny Ma" ya soka kai cikin dakin

"Harka dawo Ehsaas " ya karasa cikin dakin

"Eh, ina ta tunanin ki ne shi yasa" yayi mata ya jiki, duk da yaga sauki a tare da ita

"Gsky Husna ta iya bada kulawa" ya fada yana πŸ˜€

"Tayi kokari"
Tashi yayi yana cewa zeje ya ganta,

Saura kadan ya banga jeta

"Sorry " yasa hannu yana tallabota duk da ba faduwa zatayi bah

"Bakomai" ta ture hannayenshi

"Na dawo" ya jira tace wani abu, har washe hakora yakeyiπŸ˜ƒ

"Sannu da dawowa ya aiki kuma" yace Alhamdulillah
Sai idanun shi ya kaiga abinda takeyi

"Ooooh i love that" yasa yatsa ya lakuto custard din da da madara aka dama shi kuma yasha milo,

Harda lumshe ido

"Oh! My! " ya kara sa yatsa ta bige

"Ouuuuchhh" ya rungume hannun kaman zeyi kuka 😫

"Am sorry dan Allah kayi hakuri, naxata wani ne" sai ya bata fuska

"Wani kuma!, da wa kike wasa har kina bige mai hannu?"

Hakuri ta kara bashi kafin tayi mai bayani

"Zanso inga wannan yayan naki, dake shanye maki kunu"
Wani cup ta dauko

"Ka sha wannan sai in hada ma hajia wani ka kaimata, bata wani ci abinci sosai bah, kila in ka bata tasha"

Da taga beh ansa bah sai ta kalleshi, taga ya sa cup din a baki yana sha

Beci abinci bah ya fita, itama dake gdan har yanxu bata ci bah, azumi mah kawai takeyi

Ta fada ma kanta,

"In kara maka!!" ta tambaya ido waje dan da itace baxata iya shanye na cikin cup din bama

Murmushi yayi yana daga kai😊

Saita hada mai da biscuits a saman plate,πŸͺ

"Uhm" ya debo a spoon yana cewa ta sha

Kauda kai tayi ta kama wani aikin

"In kana so muyi karatu yau sai kayi sauri dan la'asar ake nema"
Daga kai yayi sannan ya maida hankali ya gama,

"4:00, karki bata lokaci"
"Zuwa karfe 5 zamu tashi" ya bata faceπŸ˜–

"Ai fah sai kayi tayi" ta fada da hausa can kasar muryarta


Karfe hudu daidai ta shigo falo ta ganshi zaune yana jiranta

"Muje sama zefi" daga kai tayi sannan tabi bayan shi

Zama sukayi a kasa saman carpet babu meh cewa komai, ga Qur'ani a hannun su

"Toh fara" ya make kafada
"Ke zaki fara"
'Ina son jin muryar ki' ya fada a ranshi

"Ai ni bansan in da zan karanta bah"
πŸ€¦πŸ½β€β™€Tasan rabin karatun nan shirme ze zama

"Bana so in fara kice ban iya bah" πŸ˜• cikin ranta tace kana kokari da wannan shagwaba taka

"Toh fada min inda zan biya maka, kaima sai kayi"

Bude Qur'an dinshi yayi sannan ya bata ya karbi na hannunta,

Gyaran murya tayi sannan ta dago ta kalleshi, fara'a taga yanayi kaman anyi mai wani albishir daya dade yana jira

"Zan fara, in nayi kaima sai kayi" ya daga kai

" Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ψ© Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…"

Ta fara karan tawa yana biyawa, tayi mamaki dataga ya maida hankali, kuma ba laifi voice dinshi dadin saurare,

"Mu tashi da wuri koh" ta fada bayan sun idar

"Saura minti sha biyar" ta mika mai Qur'anin

Hannunta ya rike
"Kince in in tuna maki akan wannan " ta kwace hannunta

"Zaka so wani na taba maka mata"
Lokaci daya ya daure fuska

'Na sani Husna ke matar wani ce, basai kin tuna min bah' har wani hura hanci😀 yakeyi

"Koda ba matar wani bah, beh kamata muslimi ya taba matar da bah muharramar sa bah"
Ya maida kallonshi gareta

"Kasan wannan already, but tunatarwa nada kyau"
Ta cigaba

"Babu kyau mace da namiji su kebe tare, koh ba komai tsakanin su, akwai shaidan a inda suke"

Bin wurin yayi da kallo kaman yana neman shaidan din

"Tabbas daya daga cikin abinda ke jawo fitina shine taba macen da beh halasta ka taba bah"

πŸ˜”
"Kin fadi gsky Husna, tun ina mah mutane bayani har na daina abin ya zo ya zama jiki, bana jin komai dan mun gaisa koh wata ta yi hugging dinah"

Girgixa kai tayi tana A'uzu billah cikin ranta

"Karka gaji da fadan cewa koyarwar addinin ka kake bi, hakan ze iya jawo maka kima kuma ya zama hanya ta da'awah" 😊 yaji dadin wannan bayanin nata

"Zamanin nan wadanda basu girma cikin yahudawan bama sun dauki halinsu sun rike hannu bibiyu, dan sun rike hannu ba komai bane bah a wurinsu"πŸ‘«



"Akwai wani hadith da manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace: da dayan ku ya taba matar da bah muharram a gareshi bah, gwara a buga mai kusa da guduma a kai"

Rufe kunne yayi da hannu yana rumtse idanu, πŸ™‰πŸ™ˆ

Duk da yayi haka beh bar hango abinda tace bah

"Kayi istigifari, dan Allah gafurur Rahim ne" ya daga kai yana ajiyar zuciya

"Tnk u very much Husna, naji dadi sosai da kika kasance malama ta, gobe in shaa Allah a waje zamuyi karatu"
"Allah ya kaimu"




⚜B.W.AπŸ–Š
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’

BOYAYYEN KUDIRI.


πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

Story and Writing
Noble Judge,
Editing Khaleesi.




3⃣3⃣.


"Husna!!! " tana ji yana kwala mata kira, masu aiki yan gulma sai kallon su sukeyi

Sauri kawai take zubawa, tana so ta isa cikin gda kafin ya cinma ta

"Cara Mia, ina ta kwala maki kira"
Ta kalli gefe, tana bata rai

"Baki karbi sakon ki bah" ya mika mata ledan yana cewa ta duba in wanda takeso ne

'Inna lillahi, mutumin nan yayi hannun riga da kunya'
Ina ma kasa zata hadiye ta a yanxu

Kaman ta saki ledan kasa, hakan wani surutu ze ja mata, kawai ta juya kaman walkiya yaga bata wurin

Bar stool din kitchen ya samu ya zauna,
Tana fitowa bayan tayi wanka ta kimtsa kanta, taci karo dashi zaune a kitchen yana latsa waya,

"Komai lfy lau"😏

ta kara daure fuska, duk dashi ba abinda take tunani yake nufi bah

Kayan dafa abinci ta fara fiddowa,

"Meh zaki dafa master chef"
Kayan da zatayi amfani dasu ta fiddo

"Yau harda ni za'ayi girkin tunda babu islamiya gwara na koyi girki"
Bata san lokacin data watsa mai harara bah

"Ni ban san rashin kunya wallahi" πŸ˜’
Beji abinda tace bah amma yasan haushi takeji

"Sorry, nace wani abin daya bata maki rai ne"

Ya cire hular girkin daya dora saman kai yana kwance apron

"In tafi tunda ba kyaso in tayaki aiki"
'Kai ka sani ' tace a ranta

"Husna ya za'ayi in tafi kina fushi dani"

"Nayi missing chicken mignon da lasagna" ya fada bayan dan lokaci

sai lokacin ita kuma ta kalleshi

"Ina zuwa"
Da wayarta ta dawo ta how YouTube dan ganin yadda akeyi

"Ahmmmmm" yaki dagowa ya kalleta

"Lokaci ya kure yanxu, kila zuwa gobe sai inyi maka, lokacin na kara koyan yadda akeyi"
Kaman bada shi takeyi bah sai wasa yakeyi da tumatirπŸ… da attarugu🌢 da albasan dake cikin kwano yakeyi


"Ka ji" yayi shiru yana kallon kayan miyan kaman akwai wani sirri a ciki da yake nema

"Ehsaas " tace a hankali sai ya dago da murmushi

"Ashe kin san sunana, naxata sai na sake koya maki" πŸ˜‰
Ta juya idanu tana tabe baki

"Nasan yadda yan America kesan pizza, abinda nayi niyyan yi maka kenan, dan ina ta kallon videos din____"
Ta matsa dataga yazo daf da ita

"Badai bakisan kasar da aka haife ni bah"🀨
Tace na sani ba tareda ta kalleshi bah
"Kuma kika ce ni dan can ne"

Tayi shiru

"Akwai banbamci"
"A turancin ku bah"
Yayi dan dariya

Ta dauko blender zata markada kayan miyan

Yar kara taji yayi, saita juya idanu

'Ai fah!!!!'

,saida ya sake yi sannan ta kalleshi

Yaji! ranta ya bata lokaci daya,
ya dage kuma sai murza idanun yake da hannu biyu

"Bari" ta sa towel tana bige mai hannu

"Uhm uhmmmm, ina ga na makance" muryar shi sarke

Kaman ya zauce, janshi tayi zuwa wurin famfo ya wanke fuskar shi

"Meye wannan? " ta sake dungura mai

"Lasa zakayi"
"UghhπŸ˜‘, gishiri ne"
"Nima haka naga anayi"

Ya dade nan zaune da jan fuska, idanu rufe

"Ina tsoron in bude idona in ga na makance"

Ta girgixa kai mah shirman shi,



"Wannan mutumi, babba da kai harda kuka dan yaji ya shigan maka ido"
Ta fada da hausa

"Ina kike naji kina magana" ya hau lalube

"Malam ka bude idon ka" ta sake fada da hausa


"Zan fara karban tara in kina magana da yaran da bana ji"
Aranta tace akwai aiki gaban ka

Kanshin abinda ta gama ne yasa ya dan kanne idanu yana kallo

"Saika bude ido sannan yajin ze tafi gaba daya"
😭😭😭😭

'Asma'u da gaske fah kuka yakeyi' ta zaro eyes😳

" Mommy, granny ma, help me!!!!!!" πŸ—£πŸ—£πŸ—£πŸ—£πŸ—£bayan ya gama fada da karfi,

mikewa yayi ze tafi,
kuma yayi tuntube da kujerA

"Husna help me" ya bude hannuwa😭😭😭

"Ka bude idanun ka babu abinda ze faru"

Saida ya dora hannuwa sama kafin ya bude πŸ‘€

Saida taga yadda idanun sukayi jaa kafin ta tausaya mai, dan tasan yau ya fara dandana irin wannan azabar

"Am sorry, laifi nane"πŸ˜“πŸ˜“
"No Husna ba laifin ki bane bah, kin gama"
Ta daga kai tana zuba maiπŸ•a 🍽,

"Har naji sauki sosai"
Tayi ☺ sannan ta dauki wasu a tray ta hada da ruwa juice ta kaima Hajia,


Gabanta ne ya fadi ta fara inna lillahi a cikin ranta
😠

"Barka da yini Hajia" 🀬 zagi shine amsar gaisuwarta


"Yi hakuri hajia"
Wurgo mata wani abu tayi da bata san koh menene bah saida ya tabata sannan,☎

"Yi hakuri" ta sake fada tana tattara telephone din

"Har cikin gdana kika kawo min yan uwan ki marasa galihu, sannan kika sa Ehsaas yin dawai niya dasu harda maidasu cikin motar gda na,

Ban fada maki bansankina hulda da jikana bah,

Banda wannan gaba kika sashi ya siyo maki abu, harda sashi kuka, uba* meh kika bashi a ruwa yasha da yake duk abinda kikeso"

Ta fasheda kukaa
"Allah duk shi yayi ko meh yayi, ni ban mah fadamai zasu zo bah"

Hanata karasawa tayi ta hanyar watsa mata ruwan dake aje kusa da ita


"Bana son wani talaka ya kusanci zuri'ata har ya samu daman sani nadama,
Tun wuri ki yanke wannan shirmen dake tsakanin ku"

Ta wurgo mata wani littafi meh jikin fata harda zaren daurewa

"In kin manta dalilin zaman ki a gdan nan bari in tuna maki, ki dinga rubutawa kullum har sai kin haddace"

"Kuma ki tabbatar kin wanke min kalar tsiyar da kuka shafa min a mota, saura inji yazo yana man korafi akan ki"


Tana fitowa taga yan gulman dake kaiwa hajia rahoto, tunda ta dade bata fita, kullum tana daki kwance,

Koh karatu sukeyi ta dinga ganinsu sune leke, basa mata magana sai aikin nunata da tsaki in zata wuce,


Tana kaiwa step na karshe ta ganshi yana nufo stairs din da plate a hannu

"Husna yi sauri kafin ya huce, best pizza din dana taba dandanawa kenan"

Saurin juya mai baya tayi tana goge hawayen da yaki tsayawa

"Husna" ya fada a hankali yana jira ta juyo

"Kukan meh kikeyi" koh kadan beh kawo a ranshi cewa kakarshi zatayi mata wani abu bah

"Akan ya Mukhtar ne, karki damu zeji sauki" ta juyo tana kallonshi da fuska jike da hawaye

"Na tabbata ya kusan jin sauki tunda har yana amfani da hannun"

Bata san abinda yake magana akai bah, kuma tana tsoron yan gulma, karsu kaima Hajia rahoto

Da gudu ta nufi bangaren yan aiki tana shiga ta kulle kofar ta jin gina akai tana kuka meh cin rai


" Husna open d door"
"Husna!pls!!!! " ya kara fada da karfi yana dukan kofan,

Bata san in tafiya yayi bah, ita dai taji shiru, bude littafin tayi taga abinda ta rubuta,


* Ni Asma'u Musa Wada, diya ga Musa wada Kanwa ga, ta zayyano sunayen yan gdansu,
Na dauki Alkawarin biyan bashin da Mijina
Salisu yaci mah Hajia Laila Turai, ta hanyar yi mata aikatau, nI da zu'ri'ata har sai mun biyata,

Kudin sarkan $9.6 milliyan, daya sata aka gani a hannu na

A kasa tasa hannu, _____ *

a inda Hajia ya kamata tasa hannu kuma babu komai *


Biron dake jikin littafinπŸ““ ta zaro ta rubuta date sannan ta fara rubuta alkawarin data dauka,


Tana tsakiyar yi ta canza zuwa rubuta duk wani abu daya faru da ita tun daga zuwanta wannan gdan,
Duk ta jika rabin pages din da hawaye,

A babban kitchen taje ta dafa masu abinci, sannan ta kai ma hajia nata, nashi kuma ta aje a dining table,


Gyangyadi takeyi amma taki kwanciya so take ta daina jin motsin kowa kafin taje ta wanke motar da hajia tasa ta,

Tana cikin wanke motar ta tuno lokacin da babansu nada mota, tana tayashi wankewa koh kuma yayyanta in suna wankewa,

Tana cikin murmushi taje muryar shi

"Meh kikeyi" tun fitowarta ta bayan gdan yake kallonta dan yau mah yana waje yana aikin tunanin shi da kallon taurari⭐⭐⭐

"Husna magana nakeyi" ta debo ruwa tana watsa mah motan

"Wai yau din nan meh ke damun ki ne? " yana shiga gabanta tana watsa ruwa, wanda ya jika shi sharkaf

"Dan Allah ka kyaleni, kayi kaman bakaga mutum anan bah"

Duk inda tayi sai yabi wurin yana mata magana

"Husna i said stop! " haushi ya kamashi ya shiga gda

"Gwara ka tafi ai" ta fara goge motan, tana cikin goge wa taga motan ta kawo haske,

Gefe ta matsa dataga ya fizgi motan kaman ze tashi sama,

Tiyon dake jikin 🚰 ta kashe sannan ta dauki bucket dinta tayi gaba,

Hakanan ta tsinci kanta da yin sauri, tana kulle kofa koh second 5 ba'ayi bah taji ana kwankwa sawa,

Kayanta kawai ta canza ta kwanta πŸ›ŒπŸ»,

Gari beh karasa wayewa bah ta shigo cikin gdan, zaune ta ganshi saman kujera,

"Ina kwana" yace da fara'a bata tankashi bah,

Kuma kaman yasan baxa tace komai bah, sai ya tafi kawai πŸ˜”,



'Safiya wannan raino naki akwai alamar ❓'

"Komai lafia jiya, amma kafin dare ta canza bata kula ni, bata san hakan na kona min rai bah, it's breaking my heart πŸ’”"
Ya dukar da kai kaman zeyi kuka

"Yi hakuri Ehsaas zanyi mata magana kaji"

Ya dago da sauri

"In kirata Toh"
Ta girgixa kai aranta tana mamakin halin da ya shiga

"Granny Ma ke kadai na fadama ina Son Husna, koh Mom na kasa fadama wa har yanxu, ina da KUDIRIn aurenta a raina"

"Matar aurece fah Ehsaas " ta katse shi tana fada da karfin Murya

Tashi yayi tsaye yana tura hannuwa cikin gashin kanshi


"Na sani Granny Ma, abinda yasa ban aureta bah kenan har yanxu"
Sallamarta ta katse shi

"Breakfast dinki Hajia, kin tashi lfy"
Ta amsa tana binta da kallo

"Sannu da aiki Husna" tayi kaman bata ji bah,

"Kin gani koh" ya fada bayan ta tafi

"Koh kallona bata sanyi"
Ya fada saman gado 😫😫😫😫😫😫😫😫.





⚜B.W.AπŸ–Š
⚜BRILLIANT WRITERS ASSOπŸ–Š





πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI.


πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

Story, editing by Noble Judge,
Writing Khaleesi.

Albishir na kwaso maku da dumi dumi,

Shaharrarun Marubutan nan su bude sabon fahe da wasu kayatattun littatafai

Grab 'em while their hot
πŸ”₯🌢πŸ”₯🌢πŸ”₯🌢πŸ”₯🌢πŸ”₯🌢πŸ”₯🌢πŸ”₯🌢




RUBUTACCIYAR KADDARA na UMMU AFFAN da MEELAT MUSA

NI DA YA MOHA na REAL MEH DAMBU
πŸ’•

Karku bari a baku lbr😘😘😘😘😘



3⃣4⃣.



Iska meh sanyi ke kadawa acikin garden din, garin yayi lup lup ba rana, ga dan duhu duhu alamun hadari ya hadu,

Zaune Yake cikin garden din da suke karatu yana duba abubuwan daya kamata yayi acikin wayarshi,

Yana gamawa ya kira mamanshi,

"My son, ya kake"
Ya amsa mata da lfy lau

"Ya aikin ka, kagama korafin ka hakura" yayi murmushi

"Ai da baki ragemin aikin bah korafin zan cigaba dayi" ya fada da wasa a muryar shi

"Ya kike mom ya Dad kuma"
Ta dan bashi takaitaccen lbri akan abubuwan da sukayi da baya nan

"Hakan yayi kyau, Ahmmm dama maganan meeting din yau ne"

Tace ina jin ka

"Koh zaki sa wani ya wakilce ni ne Mom, wallahi bana jin fita yau, ballantana har zuwa wata kasa"

Yaji tayi ajiyar zuciya

"Na dora maka aiki dayawa koh"
Yace Aa can kasan muryar shi,

"Karka damu wani zeje a madadin ka"

Yayi mata godiya sannan suka katse kiran,

Beh jima bah yaji wayar shi na ringing,

"Lfy dai koh Alfie" ya fada direct

"Lfy lau sir, dama na kira in ji in komai lfy ne, koh akwai abinda kakeso inyi maka"

Ya hade girar sama da kasa

"Kaman ya kana so kaji in lfy"
P. A dinshi nata bada uxurin da basu bulla bah

Kashe kiran yayi yana mai jin haushi,

"Dama can shi ke kai ma Mom rahotannin abinda nakeyi, kenan tasan batun Asma'u, bayanai akan Asma'u din ne kawai bata dashi, shima dan ban gaya mai bah"

Ya karasa tunanin da tsaki

Tsaki yayi yana jin haushin sakan mah Alfie ragamar kula da komai na rayuwarshi da yayi.



Sallama akayi mai, ya ansa ba tareda ya kalli ko waye bah

"Lokacin dana dawo jiya ancemin kana aiki"
sai lokacin ya kalli wanda ke magana

"Hey,ya tafiyan jiya"
ya danyi murmushi

"Alhamdulillah"
ya jin jina kai

"sunce sun gode kuma Allah ya saka da Alkhairi"
yace amin da farin ciki

"Ya suke,ka tadda kowa lfy"

"Sir, tunda kazo aka dauke ni aiki a matsayin driver dinka, kuma nasan matsayina, saidai ban san koh in fadamaka gsky abinda naji bah"

Ehsaas ya kalleshi da kyau, maganar gsky beh kyauta bah,tunda koh sunan mutumin beh sani bah


"Ya sunan ka" ya fada yana nuna mai kujerar dake gefenshi wai ya zauna


"Sunana lukman Sir, ina kokarin tsayawa akan aiki na kuma inyi abinda aka sani"

Ya kalli mutumin da kyau, aranshi yana fata baya kaima wani rahoton abinda yakeyi




Please Login or Register in order to submit comment