Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mom tayi magana cikin fada,

"Wai meh ke damunki neh Safiya, keh baza'a taba gaya maki magana bah kiji, nace maki ki bar zancen daukan fansa akan Hannah"

Beh karasa bah ta fara tafi,

"Munaga rasulu mata sunki maza, koh ince kaki yan uwanka ka manne mah bare"
Rumtse idanun shi yayi kafin ya bude,

"Umma dan Allah kiyi magana da ita kila keh ta saurareki" Ashe Hajia na nan zaune, nata tunanin kawai takeyi,

"Itace sanadiyar mutuwar shi" Ajiyar zuciya yayi, kuma ya dade bece komai bah,

"Bana tunanin itace Umma"
Wani tafin tayi hade da cewa You see,

"Godiya mah ya kamata kayi min, a matsayin ka na Shugaban Malik family gabaki daya, ka kasa yin komai a kai sai ni dana zo daga baya"

"Safiya karki manta ya riga zuwa duniya,kar shiru yasa ki nemi wuce iyakar ki"
"No umma barta, gsky take fadi, abinda na kasa yi shi takeyi"
Juyawa yayi gareta
"Kin tabbata zaki iya rayuwa da abinda ze biyo baya in kika cigaba da bin didiki,
Bari in fadamaki wani abu,

File din da kikasa a baki meh dauke da yadda mahaifin mu ya rasu da irin halin da aka tsince shi a ciki na karya neh" tace what din da beh fito sosai bah,

"Yes na karya neh file din, Amyr ya rubuta shi, bazaki iya bacci bah in kika kalli pictures kuma kika karanta na gaskiyan"
Hajia ta mike tsaye,

"A ainihin file din mah duk shaidar da aka samu yana nuna Hannah ce ta kashe shi,
Amma ni na san da itace baxata bar abubuwan daze sa a zargeta bah,

Karki ce banyi komai bah, a sanadiyan gano gsky na rasa Matata, unborn child dinah,da AAYAN" ya fidda sunan a wahalce kaman a dora mai dutse a saman heart dinshi,

"Zan tambayeki kuma Safiya, zaki iya rayuwa a haka kaman yadda nakeyi , kullum kina waige waige dan ki tabbatar makiya basa binki,
Kin rasa diyar ki ai koh, kin san zafin mutuwa ai, kn shirya rasa Ehsaas___"
"Stop it" ta toshe kunnenta
" koh Mijinki" ya karasa abinda zece,

"Price din dana biya kenan dan gano gskyar al'amari,duk taurin kan Amyr mah yayi shiru balle ke safiya na tabbatar maki da baki kamo kafar shi bah in dai wurin yin abinda kika gadama neh"


Duk sukayi tsit, itama ta dafe kirji dataji ance rayuwar Ehsaas dinta ze iya salwanta garin gano gsky,

"A family neh" mom ta ratsa shirun da wannan zancen,

"Wanda yayi komai a cikin family yake, harda shi yasa kukayi shiru kuma kuka yi wannan silent yarjejeniyar,

Kuyi shiru baku binciki wanda ya kashe Babanmu bah,shi kuma sai ya daina kokarin rufa ma kanshi asiri"

Yarima ya jin jina kai,
"Kin gano daidai, da alamu tsufa beh toshe wannan kwakwalwar taki bah"
"Waye a cikin family dinmu yakeso yaga bayan mu Yarima" Hajia ta katse wasan,

"Wallahi ban sani bah umma, kuma koh na sani bazan fito da abin fili bah"
"Meh yasa?" Inji Mom,

"Kin san yawan Malik's neh, manya da kanana,

Kowa da dangin daya fiso, kowa da wanda yake ganin yafi dacewa ace shine shugaba,

Karamin yaki za'a tayar in maganar ta fito fili, hakan kuma ze iya kawo rabuwar mu"
Tayi tsaki,

"Duk su kama gaban su manah, wa ya damu dasu, wallahi san kai neh ya cika family dinnan, ba adalci duk da bah a ciki nake bah yanxu"

Gsky ta fadi shi yasa beyi kokarin gyara mata bah,

"Yarima ban san zaman ka a gdan nan, ba kaman yanxu da Safiya ta jogalo maka tsiya, kar magana ta fito fili kuma su bi sahun dare su rabani dakai har abada"
Murmushi yayi mah mahaifiyar shi,

"Na saba da kwana da ido daya bude Umma, kuma Amyr ya tabbatar da tsaro na, duk abinda ya faru kuma a rubuce yake umma, ku ma zance yazo yasa maku irin security system din"

Mom ta juya tana kallon shi,

"Kasan kusancin ka da wannan Amyr din shima wani cece kuce ne koh,
Bazasu yadda da abinda kake shirin yi bah"
Kallon juna sukayi dan basai ta fayyace bah shi yasan abinda take nufi,

"Uwarsu daya ubansu daya, koh su yarda koh karsu yarda,
Amyr kanin mune, Malik neh shi,
Kuma tunda bana da magaji, shi ze jagoranci family dinmu bayan ba ni,
Koh kuma Ehsaas"
"Allah ya kikeyi, Allah kada ka kawo ranar, over my dead body"
Dariya yayi sosai abinshi daya ga reaction dinta,

"Salihin dana in dauke shi in jefe mah zakuna, Aa wallahi, da alamu ka shirya mah abinda ze faru ai tunda har kake jan Amyr din a jiki"
Ya jin jina kai alamun ya shirya,

"Kuma kema ki aje wannan at d back of your mind, in ba Amyr bah Ehsaas"
Da wannan ya mike tsaye,

"Umma zanje in ga in abinda wannan yarinyar tayi ya bade gari,
Kema kuma kije ki cire wannan karar"
Ta yatsina fuska tana binshi da harara,

"Ki dinga fadamin kafin ki aiwatar da wasu abubuwan Safiya"

"Yi hakuri umma" Hajia ta mike itama ta nufi nata dakin,

Saida suka watse kafin ta sake fitowa daga dakin dan zuwa kitchen,

Hango Ehsaas takeyi, shiru shiru dashi, gashi da saurin yadda,beh da matsala da komai,
Amma a hankada shi cikin yan uwan shi marasa gsky,
But still, ai shima Ehsaas din ba gaba da baya yake Malik bah, kila sunyi missing wannan point dinneh,
Ta tabe baki,
'Keh meh kika sani gameh da yadda suke abinsu'.


Da yamma neh iska meh dadi na kadawa a cikin garden din,
Yan gdan na zane saman kujerun da aka jera na alfarma, sai hira da dariya akeyi,

Tashi tayi dan zuwa ta karo masu refreshments sai taji kanta ya juya mata, cikin kankanin lokaci kuma ya washe,

Zobo da kunun aya tayi dan kowa na gdan na so tayi, har Mom dai nace mata well done in tayi,

Ta bude fridge ta tsiyaya drinks din cikin jugs, sannan ta bude drawer dan dauko biscuits da cookies,
Kasa ta duka ta goge dan zoban data zubar, tana mikewa taji kanta na juyawa kuma,
Bata dauka wani abu bane bah, sai ta kwashi kayanta zata bar wurin,

Kasa tafiya tayi daidai, sai zigzag takeyi tana tangal tangal, bata ankara ba sai jinta tayi a kasa, sannan wani kara ya biyo baya,

Farfadowa tayi taji ana shafa mata fuska,

"Daughter?" Tana jin muryar Dad tayi kokarin mikewa,
"No Husna tsaya wuri daya" a hankali ta bude idanunta,

Kwance take kasa yayi mata pillow da hannun shi, Dad kuma na daga gefen shi,

"Suma Kikayi na dan lokaci" aka tadata zaune,

"Ciwon kan neh?" Ta girgixa mai kai,

Hannu ta dora saman bakinta da taji amai ya taso mata,

"Sannu Husna" ta daga kai tana takawa sannu a hankali zuwa saman gado,
Allah yaso bata kwara aman bah har suka iso bandaki,

"Ji nayi kawai kaina na juyamin" ta kara tabbatar mai da bah ciwon kai bane bah,.

"Maybe ciki gareta" duk sukayi shiru suna kallon Mom,

"Ba alamomin ciki kenan bah, kila morning sickness neh wannan" bata san lokacin data mike tsaye bah idanu waje tana kallon Mom,

"Ciki gareki Asma'u, ?" Mom ta tambaya da murmushin dole,

"Uhm uhm, Allah banda ciki" ta dafe cikin nata tana baya baya,

"Wifey ki tsaya karki fadi kuma"

"Ai ba abin gudu baneh bah, besides ai kun dade da yin aure i yanxu ya kamata ace kukan baby ya dameh mu a gdan nan,

In kuma ba ciki gareki bah toh akwai matsala, ni dai haka nake gani"

Duk wanda yaji ze zaci kulawa neh Mom ke nuna wa, amma ita tasan cusa masu tunanin take so tayi, yanxu kowa ze fara ganin ya kamata ace tana da ciki, in dai komai lfy,

'Lokacin yazo kenan, da wuri haka har zan fara bankwana da kai, yaushe yaushe na fara sanka ma wai toh'

Dukawa tayi ta fashe da kuka,
Dad sai yayi tsamanin maganganun Mom neh, wani kallo da yayi mata kafin ya jata suka bar dakin,

"Wifey ba abin farin ciki baneh bah ace kina da ciki" sai ta kara ma kukanta karfi,

"Husna ba abinda muke ta so muna fata bah kenan, mu samu namu yayan"
Da kyar ya samu ya dago da fuskarta,

"Ni bana da ciki" ta fada da kuka, tana mikewa, abin batamai rai yayi dayaga yadda take karyata cikinshi dake jikinta,

"Naji toh bakya da ciki, fadamin abinda ke damunki toh"
Juyowa tayi fuska sharkaf da hawaye,

"Period dinah neh manah" ta hada da yar shagwaba,

Bayaninta yayi ma'ana,saidai beji dadi bah, tunda hakan ya tabbatar mai da she's not pregnant,

Wani kukan ta fashe dashi tana dukewa kasa,

"You're disappointed koh, kila gskyar Mom neh ina da matsala"
Ya bata fuska,

"Wannan wani irin banzan zance neh Husna, manta kawai da maganar cikin nan da akayi, yanxu fadamin dama period dinki nayi maki haka"

Karya ta fada ta hanyar cewa Eh,

Bayan beh taba yi mata haka bah, zatayi ciwon ciki, har ta dan rasa appetite dinta, taji koh ruwa bata san sha, bayanta ze danyi ciwo, kuma zata dinga jin amai na taso mata,
Amma bata taba jin jiri na dibarta bah har ta suma,

"Magani na ya kare neh shi yasa ban sha bah tun dazu"

"Gwara azo a siyo toh" ta daga mai kai,


Da safe ya kama sunday, ba aiki dan haka duk basu fito bah kowa na daki abin shi,

"Wifey wayarki na ringing" ta aje sa kayan ta fito,


daure da towel dinta fari,

"Hello ya Abbah" ta zauna gefen gado suna magana,

"Yace yana gaishe da kai" yace ina amsawa, hankalin shi kan ipad dinshi yana research din alamomin shigar ciki, da kuma alamomin dake nuna mutum baze iya daukan ciki bah,

"Wai yau zeje ya kaima Ma'u admission letter dinta" sai lokacin ya juya ya kalleta,

"Meh yasa baki fadamata da kanki bah"
Ta dan dukar da kai,

"Naga fushi takeyi dashi, kila ta sauko in ya bata good news" yayi murmushi yana girgixa kanshi,

"Wannan matar tawa akwai wayau" da yar dariya ta mike tana boye face dinta cikin hannayenta,

"Husna" ta daina shirme ta amsa da na'am,
Inda yake nuna mata da yatsa ta kalla,

Tunda uwarta ta haifeta bata taba staining daga period bah sai rannan,

Tsoro ya shigeta lokaci daya, gabanta ya fadi,

"Husna kin tabbata komai lfy tattare dake" fiddo kanta tayi daga tunanin da takeyi,

"Silly me, na manta ban_" bata karasa bah tayi saurin bankawa bathroom,

Rufe kofa tayi ta jingina a jiki, fashewa tayi da kuka tana dafe kirjinta,

Period dinta yazo late, kuma sai rushing take kaman ba gobe, har daina kirga pads din da tayi amfani dashi jiya tayi,

Kimtsa jikinta tayi ta wanke towel din ta daura wani kafin ta fito, ba karamin dadi taji bah data fito baya dakin,

Kasa zama tayi, kuma taki barin dakin su,

"Kin shirya" ta daga mai kai
"Amma bana jin yunwa ni, ka tafi kawai"
Kaman yasan dalilinta sai yasa aka kawo musu daki,
A takure taci abincin, bayan nan kuma data zauna bata minti sha biyar cikakke zata mike ta nufi bandaki,

Yana lura da komai, saboda kar ya kara mata damuwa sai beyi magana bah,

"Sai yanxu take kira na" mikewa yayi ya shiga ban daki dan lokacin sallah ya kusa, ita kuma ta cigaba da waya da Ma'u,

Dadin hira yasa ta shafa'a, suka kwashi mintinu dayawa suna magana harda shirya yadda zasuyi komai a makaranta,

Ko daya fito wanka tana nan suna ta waya,
Goge ruwan jikin shi yakeyi yana cuno baki dan ita yaso tayi mai, shi yasa beh mayi a bandaki bah,

Ya shiga ya sanyo kaya kenan ya ga jini dis dis a kasa in da take tsaye daya,

Hanyar bathroom ya kalla yaga drops din jini,
Cije lips dinshi yayi yana girgixa kai,
'Dis is not normal, da haka ake period ai kowa daya san in mace na period dinta'

"Haka yakeyi maki dama" kasa ta kalla tana fitowa daga bandaki, amma sai taga an goge,

Girgixa kai tayi, wannan karon ta zabi ta fadamai gsky,

"Sa hijab dinki mu je asibiti"
Ya mike tsaye yana laluban key dinshi,

"Ba sai munje asibiti bah" ta fada murya kasa kasa,

"Ni ma kaina tsoron nakeji Hubby, amma hakannada alaka neh da cimar danayi ta yi"
Ya zaune saman gado a gajiye,

"Yanxu so kike in zauna ina kallon ki jinin jikin ki na tsiyayewa"
Ajiyar zuciya tayi tana dan takowa gaban shi,

"Zakin danayi ta sha neh a tafiyan da mukayi, beh taba yi mun haka bah amma naji yana yin haka"

Kafin ta karasa inda yake aka kwala mata kira,
"Na'am" ta nufi kofa dan ta bude

"Yau rowa dai kikeyi manah koh, kinki dafa manah breakfast, yanxu mah na leka kitchen ban ganki bah"
Da dan murmushi ta kalli Mom

"Yanxu zan zo"
"Bata jin dadi har yanxu" Mom ta kalleta da kyau,

"Lfy ta lau Mom"
"Karya, seriously a gaba kikeyin karya" tayi kasa da kanta
"Fada mata abinda keh damunki"
Tasan ba wasa yakeyi bah daga yadda muryar shi ya canza, amma ai Mom surukarta ce, duk da taga su hakan beh dameh su bah,

"Husna!" Ya fada da wannan murya da beh dauke da wasa,

"Uhmmm dama, dama" ta fara wasa da yan yatsunta,

"Dama meh? Na gaji da jira"
Fidda numfashi tayi,

"Period dina neh yake zuwa sosai"
Mom ta dan nuna kulawa a fuskarta,

"Ciye ciyen meh da meh kikayi" daya ji maganar Mom ya karkata ga abinda taci sai ya dan saki ranshi,

"Duk caffeinated foods dinnan da sugar, yana disrupting abubuwa" ita dai sai jin jina kai takeyi tana kallon kasa,

"Kwanta ki huta abinki, yau munci abinci marar dadi sosai" kafin ta fita ta barsu su kadai,

"Ya akayi" ta kauda kai daya zo ya tsaya gabanta,

"Kai bazaka ganeh bah ai, Mom surukata ce fah, naturally kunya ce tsakanin mu" ta fada rai bace idanu sunyi ja tana son zubda hawaye,

"In yazo ga maganar lafiyar ki Husna ba mahaifiyata bah, har Baba da Mama zan iya tambaya, ba wani kunya a maganar lfy"
Ita dai bata ji dadi bah, dan haka tayi abinda Mom tace, watau ta kwanta ta huta,

"Dan Allah ka kaini gda" idanu ya zaro waje, meh ya kawo zancen zuwa gda kuma,

"Ni mamana nakeson gani" rasa ansar daze bata yayi,

"Dan Allah ka barnu in je gda" ta tashi zaune da hawaye a fuskarta,

Saida ya daina kallonta ya iya tunanin abinda zece mata,

"Ban manta wahalar da kika bani bah da nace ki tafi gda kika ki dawowa"
Fashewa tayi da wani kukan,

"Allah ki bar kuka Husna dan baze sa in yarda kije bah" saita kara mah kukan sauti,

"Husna!" Ya fada da dan karfi,

Daina kukan tayi ta goge hawayenta, sannan ta gyara kwanciyarta ta cigaba da bacci,

Bata farka bah sai gab da Maghreb,
"Sannu Wifey, yau ba baccin dare kenan koh" mika ta karayi tana tabe fuska,

"Masallaci zaka je" daga mata kai yayi yana tunkarota, kiss ya manna mata a goshi sannan ya tafi,
Hamdala tayi data tashi bataga tayi staining gadon bah, data shiga bandaki yin wanka taga ta bata kayanta, beh kai ga gado bane bah dai,

Ranta na bata harda After pill din da takesha, ya hargitsa mata labari,

"Mom tacemin ta baki magani daze taimaka maki" ta saki baki tana kallon shi,

"Eh ta bani" ya jin jina kai yana gyara zaman pillow dinshi, a saman gado,

"Ahmmm ita ta fadama da bakinta ta bani magani in dinga sha" yace Eh,
"Na period dinki bah"
saurin daga mai kai,

"Kin gani ke ce kika damu da kunya, ita ba wani ruwan ta"
Da dan karamin murmushi ta daga mai kai,

Bayan ya kwanta ta kashe fitila yake tambayan in tasha maganin,
"Eh na sha" ta kwanta tana juya mai baya,

"Wifey nayi tunani akan abinda kika ce" ya karasa janta zuwa jikinshi bayan ya matsa inda take,

"In weekend yazo sai muje ki ga mama koh" da sauri ta juya tana kallon shi,

"Da gaske ka barni in tafi gda, My All" ta koma jikin shi tana makalkaleshi,

"Eh manah, kema kin san ban iya ce maki Aa koh" tayi wani murmushi meh fadi,

"Tnk u mijina" yace ba komai,

"Da naso mu dawo ranar da muka je" ta tashi zaune tana matsawa daga jikinshi,
"Amma ina so in ga makarantar da zakije, so Friday zamuje mu dawo Sunday"
Yana yunkurin jawota jikin shi ta kara matsawa tana gunguni,

"Ya akayi" saita fara kukan shagwaba
"Kwana daya fa kace ni bana son inyi kwana daya" abin mah ya bashi dariya, dayace zasu je, aka wani makalkaleshi, yanxu da ya ce kwana daya shine aka ture shi,

"Kin fara koh Wifey, ni dai Allah bazan bari ki tafi ke kadai bah, salon ki sa in dinga kwanan kadaici"
Shima ya fada yana kumbura baki, dole ta hakura duk kwakwarta ta kwanta.






⚜B.W.AπŸ–Š
[5/11, 19:27] β€ͺ+234 706 870 0853‬: ⚜BRILLIANT WRITERS ASSOπŸ–Š




πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI.
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

Story,writing by Noble Judge,
Editing by
Khaleesi.



6⃣1⃣.


Dedicated to Haleematu Sadiya Muhammad (Leema),
Ina tayaki murnar kammala littafin ki, RIKICIN AURENA,
Littafin na dauke da darussa da dama, ya fadakar kuma ya nishadantar at d same tym,

Allah ya baki ladan ilimantar, ya kara basira, Muna Alfahari dake.❀❀❀❀❀❀





"Barkan ku da safia" ya duba hannun shi yaga ba agogo,

"Safia? Kodai Asubah, meh kakeyi anan" Hmmm yace yana jan ladder dinshi,

"Wai meye wannan karan?" Ya gaishe da Mom da Dad dake saukowa daga stairs,

"Sa ni akayi in zo inyi wannan abubuwan, security systems ne da cctv, na tabbata ya fada maku ba hakanan ya turoni bah" sai lokacin Amyr yayi maganan serious,

"Toh meye na zuwa tun da asubah" ya daga kafadu sannan ya jingina ladder din jikin bango,

"Yanxu nake da tym, da rana ta fito zan bar nan, gobe da jibi mah zan cigaba da zuwa da asubah" ya fara hawa ladder din,



"Da asubah kake da tym?" Tabe baki yayi ze tafi,

"Hey! Ya zaka barni ni kadai anan, keep me company" yadda ya tsaya kaman bejin tsoron faduwa,
"Ni na kawo ka" ya cigaba da tafiyar shi,

"Kana da abinyi weekend dinnan neh, zanso ka rakani wani wuri" dan tunani yayi ba tareda ya juya bah,

"Zanyi tafiya ranar friday, za'a iya zuwa kafin weekend"

"Ina zaka je ranar Friday"
Ta juya ga Amyr, "kuma koda beh da wurin zuwa bazaku je ko ina tare bah, ban manta abinda na gani bah ranar da muka je gdan ka neh ko na waye , oho"
Shiru yayi na dan lokaci kafin ya fashe da dariya,

Shi dai yayi gaba abinshi,

Rufe Qur'an din da take karantawa tayi daya shigo,
"Kin san ina jin dadin sauraron muryar ki" ya zauna a kasa yana kallonta da murmushi a fuskar shi,

"Shi yasa na bari ai" yace oh! Yana daga gira daya,

"Ya ka kwana jiya" ya mike kafa yana Ajiyar zuciya,
"Naji kana ta juye juye jiya da dare" gefe ya dan kalla kafin ya juyo kuma,

"Friday dinnan zamu tafi gda koh" murmushi ya bayyana a fuskarta,
"In Allah yaso ya yadda"
Da sallama hade da knocking aka shigo dakin,

"Ina kwana Mom" duk suka mike tsaye,



Please Login or Register in order to submit comment