Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kafa, kafin suka koma daki


"A shago mana, amma bana unguwar mu bah, kar babana yaji labari,

Shiga makewayi in wanke maki kan"

Gulder kwalba daya Ma'u ta hada da kwai sannan ta shafa mata a kai, maganin dan druff,
Sai jiya da za'ayi mata sabon gyaran kai, suka lura da tana da dandruff,

"In ya bushe sai a sa relaxer din koh" ta bata fuska

"Ni kam bana so, kar kaina yazo ya gwigwiye"
Tsaki Ma'u tayi

"Ai gashi bakya sa relaxer din amma gashin ki sai kakkabewa yakeyi"

Tana sa hannu cikin gashin ta zaro,suka biyo hannun

"Ni meh sa relaxer din mah kaina yafi naki kyan gani"

Bayan ta cuda mata kan da shampoo tasa towel tana dan tare ruwan,

"An fasa sawa ne" Ma'u tace uhmm
"Zan rufa ma kaina asirine, a haka mah baki kula da gashin bah ina ga nasa maki relaxer,kwakwido zaki koma ai"

Ta cigaba
"Gashi ke basan kitso bah, in da relaxer din ai zakifi jin saukin kan naki, daya bushe kika sharce shi kenan, amma cunkus haka, sai kin dage kina ba gashin ki lokaci sosai"

Shiru babu wanda yace komai har suka gama ta daure mata gashin,

"Gashi" karban Vaseline din tayi ta shafa mah lips dinta, da kuma girar ido,

Bakinta beh rabuwa da Vaseline koda kuwa bacci zatayi, Ma'u tace mata yana rehydrating lips,
Kuma taga zahiri, bakinta yanxu babu bushewa koh tsagewa, gashi yayi tsantsi kalar shi ta deep pink ya kara fitowa,

"Koh mascara zaki shafa, ki fara goga Vaseline da wani Mascara brush zakiga sun mike tsaye"
Ita bata shafa mascara shi yasa ta bige da shafawa haka nan,

"Likacin darasin make up" bata tunanin zata taba yin makeup din, amma tunda Ma'u na daukan lokaci wajen koya mata,saita maida hankali,

"Kinga 24hours lipstick dinnan, yana da kyan sha'ani amma sai lips dinki is smooth, shiyasa ki fara shafa Vaseline kafin shi, sannan in kin zo cirewa ki shafa Vaseline kuma, in ya danyi minti biyu, sai ki goge cikin sauki,

Kuma ordinary jan baki irin wannan"
Ta dauko tana nuna mata

"In ya karye zaki iya sashi saman cokali, ki kanga ga wuta in ya narke, sai ki zuba cikin gwangwanin eye shadow wanda ya kare"

Kallonta takeyi tana magana tana kwalliya,

"Heavy Makeup ne wannan" ta jin jina kai

"Kin kam canza sosai"
Ma'u tayi murmushi

"Imagine in kullum bakya make up, mijinki ya dawo ya ganki haka, koh be yaba bah nasan sai kin dauki hankalin shi, kin sa ya dinga kallon ki,

Karkiyi mamakin yadda kananun chanji ke tasiri a aure"

Mamaki ya kamata, wai Ma'u ke bata lecture akan aure,

"Ke a ina kika koya"
Ta bushe da dariya

"Zauna nan namecy jaba ta fiki kwalliya ranar sallah"
Ta juya idanu tana zana Highlights ,

3 kawai ta rubuta a kowani gefe na fuskarta, daga saman girarta, saita lankwaso zuwa cheek bone dinta,sannan ta karasa ja a habarta,

"Kin tunamun mah, na bude maki WhatsApp, nasan bakya so, amma ai mutanen da kika sani kawai zakiyi chats dasu,

Babu meh zama haka nan yanxu namecy, kowa kokari yake yaga kanshi ya waye ya iya abubuwa,

Koh ke ba matar aure bace bah, ai kina sa ran yi koh,

Ki dage Asma'u, karki bari kunyar nan ta kaiki ta baroki, tana da nata amfani, saidai ki fara gano a ina da ina tukunna,

Duk abinda na ga ze amfane ki zan turo maki ta whatsapp sai ki duba kinji koh"

Tace toh aunty Ma'u da wasa.




⚜B.W.AπŸ–Š
[3/26, 06:19] β€ͺ+227 99 95 15 93‬: [3/25, 8:27 PM] 🎭KHALEESI.🎭: ⚜BRILLIANT WRITERS ASSOπŸ–Š




πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI.

πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

Story, Writing by NOBLE JUDGE,
Editing by KHALEESI.



4⃣6⃣.
[3/25, 8:30 PM] 🎭KHALEESI.🎭: "Su Ma'u ansha kuka ashe, ki dage kiyi new catch a abuja, kinga sai ku dinga ganin juna" itama ta kauda kai

"Ku shiga ciki ku kimtsa kafin anjima koh, a je kaita " Ma'u ta kama hannunta sukayi dakin Aunty karima wacce yaya ce ga Ma'u,

Koda suka shiga babu wanda yace komai, sai corner da kowa ya kama ya zauna,

"Kiyi hakuri kinji Ma'u" kaman ta kara tunxurata saita fashe da sabon kuka

Kowa ya zata saboda shakuwar da sukayi ne yasa Ma'u kuka kaman ranta ze fita,

Amma zahiri babanta ne ya rabata da Ya Abba,

Abin beh dameta bah saida tazo gdansu, taga ya Abban mah ya daina kulata,

"Ze dawo ku shirya, kema kin san yadda yake, ki bari ya dan samu lokacin tunani"

Bata taba ganin Ma'u haka bah, wai abu ya dameta har da zubda hawaye

"Sorry kinji namecy" suna shiga motoci taji nata kukan ya tafi, amma saboda Ma'u saita kasa bari

Daga waje aka kwala mah Ma'u kira,
Data fita ita kuma ta tashi tana shirin yin wanka, dan duk zufa ya dameta

"Karki sa wannan" ta zata kayan data fiddo take nufi sai taga ta kwashe undies din data aje

"Wai baki saurareni ranar da ina maki bayani ba koh"
Ta fara kokarin tunowa koh ta mata lecture kan underwear

"Nace maki wannan na period dinki ne" ta aje abincin data karbo sannan ta dawo gareta

"Bari in sake kuma Allah ki saurareni wannan karon" tace toh tunda ta samu ta daina kukan

"Kinga yadda yake, koh kinyi heavy flow indai wannan pant din kika sa toh bazakiyi staining bah"

Harda ruwa ta zuba, saida tasa da dan dama kafin ya nuna daga kasa

"Kiyi organizing komai in kinje can kinji,

Zakiga na siyo maki fararen panties cotton, ya kamata ace kin san irin abubuwa dake fitowa daga jikin ki yanxu,

Da irin warin da suke zuwa dashi, na bayan kin gama period da kowanne sai kin gane,

Wani ze iya zama na infection ne, be careful, wani infection din beh nunawa sai ya dade a jikin ki, in kika ga wani ruwa da baki gane mai bah, ki je asibiti, banda kunya"
Harda nuna da yatsa, irin ita yarinyar nan ce

"Good hygiene Asma'u, ban sanki da kazanta bah amma akwai abubuwan da zan sake fada maki,

Shaving akai akai, ki dinga amfani da towel koh tissue bayan kinyi tsarki, dan jikakken pant bah abokin ki bane bah, ze iya yanayin da infection keso ya girma,

Canza panties 2 koh sau 3 a rana, ki san irin sabulan da zaki wanke undies dinki dashi, banda meh karfi sosai, banda amfani da medicated soap kowani lokaci, dan akwai wasu kwayoyin bacteria da bana cutarwa bane bah, kuma su dettol koh delta dinnan zasu iya kashe su"
Zata katse da tambaya kuma ta mata alama datayi shiru

"Sai na gama sannan kiyi tambaya"
Abin mah ya bta dariya

"Ba jikin ki kawai ke bukatar yayi kanshi bah, harda can kasa"
Tayi tagumi tana sauraron ikon Allah

"Shi yasa ki dage da siyan cotton saboda ze bar iska yana zagaye a jikin ki,

Abubuwan da kike ci mah ze iya jawo maki wari na daban

Kaman Albasa, Garlic, yawan cin jan nama, curry mah, haka caffeine, irin su nescafe, lipton, kisha su saisa saisa, haka chocolate, saidai dark one zaki rage sha, compound koh milk, zakiga basu kai dark🍫 caffeine bah,
Sugar mah ba friend dinki bane bah sister tah,

Infection na son siga sosai, kuma yana kara sa ciwon ciki yayin da zakiyi period,

Ki dage da shan ruwa sosai, shan lemu, cin banana da πŸ₯‘πŸ,
Vanilla ice cream mah da watermelon,

ba abin kunya bane bah in kika ce gaban ki na wari kina neman magani, amma ze iya zama cuta gareki in kikayi shiru,

Madamar ba infection bane bah,toh in shaa Allah zakiga ya daina,

Sai farin miski, once in a while, kaman lokacin da kika gama period dinki, kuma ki samu meh kyau in wannan ya kare kinji"
Ta jawo wani bag, kafin tace toh

"Kinga wadan nan,soap ne na tsarki, ba kowani sabulu ake amfani dashi bah, sai wanda dama na tsarkin ne,banda cusa abubuwa a gabaki, kiyi consulting dina first kafin kiyi amfani da wani abu da bani na koya maki amfani dashi bah


Kafin in manta, na kara koyan wani abu, shi wannan nasan ban fada maki bah,

Na hammata ne, yadda zaki dade bakiji kina tsami bah,

Kwanaki naji anata magana akan antiperspirants, ance suna kawo cancer toh meh ze hana mu koma home made,

Kinga Irish potato, cucumber, koh lemon tsamiπŸ‹
Zaki iya shafa slice a hammatan ki, bayan minti biyu ki wanke,

Lemon tsamin ze iya sawa kiga hammatan na saba, toh fatar wurin ne ta bushe dama, wurin zeyi saba ya fita,
Wannan abin mah kuma ze iya sawa hammatan ki yayi haske daidai da jikin ki, in dama yayi baki sakama kon amfani da shaving cream koh powder,


Na baking soda dinnan kar kiyi amfani dashi likacin da kika gama shaving dan zeyi maki zafi sosai, baking soda da ruwa zaki shafa na minti goma zuwa sha biyar kafin ki wanke,

Akwai lemun zaki mah, amma wannan zaki busar da bawan in ya bushe ki daka, sannan ki kwaba da ruwa ki shafa,

Alum mah, kidan jika shi ki goga zakiji kin dade tsamin zufa beh dame ki bah"

"Har yanxu girma kikeyi, Bra's dinki da sun fara matse ki ki canza kinji koh"

Zata bude baki, a ka budo kofa

"Zaman jiran ku zasuyi, ku shirya manah,

Koh abincin baku ci bah, kai yaran nan"

"Yanxu zamu shirya"Ma'u ta bata abincin ta ci, ita kuma ta shiga wanka,

Hankalinta beh tashi sosai bah, dan yace mata sai sunzo ze dawo,

Dan haka ana gama yi mata nasihohi, ta sharbi kukanta ta gama, saita kwanta tana tunani,

Gyaran da duk akayi mata, da abubuwan da aka dirka mata tasha, harda abubuwan da Ma'u ta fada mata, duk dan ta gamsar da mijinta ne,

Data tuno wani abu kuma sai gabanta yayi ta faduwa, dan haka batayi mamaki bah data tsinci kanta da yin mafarkin abin daya faru,

Kokawan kwace hannunta shine farkon abinda ke zo mata, daga nan sai ya murde mata hannuwa ya matseta da bango,

Ga duhu babu abinda take iya gani, akin lalubarta kawai yakeyi, sai kokarin cusa mata hannu cikin riga da kuma skirt dinta yakeyi,

Gashi sai goga kugunshi yake a nata, yana faman lashe mata wuya, hade da rada mata wasu yan iskan kalamai, da karamar kwakwal warta ta kasa dauka,

Abinda ke dan sanyaya mata zuciya shine karshen mafarkin, inda ake kwatarta kafin ya samu ya zubda mata mutunci a zauren mutane,

Sai ce ma kanta takeyi mafarkine, baze cutar dake bah,
Cikin bacci taji kaman ana bin fuskarta da kisses, sannan a hankali kuma ana dan shafata,

Sake cema kanta tayi mafar kine, saida taji baki saman nata sannan ta bude ido da sauri tana addu'ar tashi daga mummunan mafarki,

Jitayi ta kasa kwace hannunta,

Bude baki tayi zata kwala ihu aka toshe mata,

"Relax wifey ni ne"jin shine beh kwantar mata da hankali bah,

Sai sabon tsoro daya darsu a zuciyarta, beh taimaka wajen kwantar mata da hankali bah daya fara shin shina wuyanta yana wasa da harshen shi a wuyanta,

"Mafar kine Asma'u" haka ta dinga fada

"Babu abinda ze sameki mafarki kikeyi"

Yana dan sassauta rikon da yayi mata ta mirgina daga saman gafon ta fadi kasa,

Bin bayanta yayi, yana kokarin taimaka mata

"Wai meye haka Asma'u, sai kin ji mah kanko ciwo kenan, Meye hakan"
Cikin duhun ya rikota, sai ta saki kara tana rokon shi daya kyaleta,

Ba shiri ya saketa ya nufi switch din fitila,

"Asma'u" ya fada a hankali, ita kuma duk ta hargitse, idanu sun fito waje, sai girgixa kai takeyi

"Mafarkine, mafarkine kawai" kanta kaman yayi mah wuyanta nauyi sai gaba da baya yake,

Yana tunkarota tayi baya tana hardewa zanin jikinta, sai gata a kasa,

Da gudu ya karasa inda take yana kokarin bata dauki,

"Dan Allah ka kyaleni, kaimin rai Dan Allah, Mutuwa zanyi in ka tabani"
Da tsoron kalamanta yayi baya,
Yana dan bada tazara tsakanin su
Ta ruga cikin bandaki,

Yayi magiyar duniya amma bata fito bah, har sallar asubah ya kusan rasawa,

Beh dawo bah saida gari ya waye sosai,
Dakinta ya shiga straight,

Tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga light blue color, sannan ta nannade kanta da gyale light pink,

"Ina kwana" har kasa ta duka ta gaishe dashi, amma beh ansa bah

"Ka tashi lfy" yace hmmmm
"Seeing as bamuyi bacci bah kwata kwata jiya, amma kike tambaya na yana kwana"

Ta dukar da kai kasa

"Kayi hakuri na bata maka rai jiya, kuma na hanaka samun kwanciyar hankali, hakan baze kara faruwa bah in shaa Allah"

Da karfi ya kama hannunta yana fizgota tsaye, har yar kara tayi saboda yadda ya damki guiwwar hannunta,

"Kin tabbata lafiyar ki lau, babu wani matsala da 🧠 ki"
Ya fada rai bace

"In ba haka bah, taya zaki kalleni kaman babu abinda ya faru jiya,
In a wurinki ba komai bane bah, ni a wurina wani abune,

Kin san yadda kikasa zuciyata cikin damuwa, kika tsorata ni gaba daya,

And now smile greet me, meh ke damunki"
Suna kallon kwayar idanun juna tunda ya fara magana har ya kai karshe

"Abinda ya faru jiya yana da dalili, fadamin menene"
Sai lokacin tayi kasa da kanta

"Asma'u" ya fada kaman duk hakurin shi ya kare, yanxu a kage yake

"Bakomai, ka man__"
"Na tsani makaryata Asma'u in bazaki fadamin bah karki bude bakin ki"

Babu abinda yafi ci mata rai kaman sunanta da yake kira, Ba husna bah koh sauran lakani da yayi mata
"Bazaki fadamin ba kenan"
Ta girgixa kai wasu sabbin hawaye na fita

Saurin saketa yayi yana, zagaye dakin da wargaza gashin kanshi,

"Ba kuka na tambayeki bah, ki fadamin abinda nakeson ji"
Komawa gefe tayi tana rufe fuska da tafukan hannunta

"Am hurt Husna, abin nan da kikeyi min yana min zafi, ina ga ya kamata kisan haka"kana kallonshi kasan yana cikin damuwa,

Yana gamawa ya nufi kofa, da sauri ta tareshi tana dukawa kasa

"Dan Allah kayi hakuri, ban taba fadama kowa bah saboda haka ban san ta inda zan fara bah"

Dukawa yayi yana so ya tabata, amma ya bada tazara tsakanin su, sannin yadda take tsorata in ya tabata

"Kin yadda dani kuwa Husna, babu abinda nayi face sanki tunda muka hadu, dan Allah ki agazamin ki saukake mah zuciyata wannan radadin,

Koh bazan iya sama maki sauki bah in tayaki daukan sirrikan dake cikin zuciyarki"

Da kanta ta matso cikin jikinshi, ta cusa kanta cikin kirjinshi, sannan ta bashi labarin komai,

Bari jikinshi yakeyi saboda bacin rai, amma saboda ita ya tausasa zuciyar shi, sannan ya shiga lallashinta, har ta daina kuka, tana maida numfashi.
⚜BRILLIANT WRITERS ASSOπŸ–Š




πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI.

πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’


β“’β“£β“žβ“‘β“¨, β“”β““β“˜β“£β“˜β“β“– ⓑⓨ,
NOBLE JUDGE

β“¦β“‘β“˜β“£β“˜β“β“–
KHALEESI.


β““β“”β““β“˜β“’β“β“£β“”β““ β“£β“ž,
❀ BRILLIANT WRITERS, Ina maku fatan Alkhairi a duk endeavors dinku,
Allah ya kara basira da hazaka.❀


πŸ’‹zuwa ga masoyan book dinnan nan, jiya bamu samu yin update bah, saboda typing da nayi kuma by mistake nayi deleting dinshi,

Haushi naji sosai shi yasa na kasa typing,

Na samu nayi rewriting, Allah yasa yafi na farkon dadiπŸ’‹

Tnx and lots of love to u all,
Allah ya barmu tare ya hada faces dinmu a Aljannah.



4⃣7⃣.



Tana kokarin barin jikin shi ya kyaleta,

Gefe tayi ta zauna,

"R u okay?" Kai ta daga mai kafin ta tashi tayi bandaki,

Ajiyar zuciya yayi data fito, dan ya zata kulle kanta zata sakeyi

"Muje mu gaishe dasu Mom koh"
Saman gado ya zauna sannan ya dan buga gefen shi alamun ta zauna,

"Muna da Matsala Asma'u, ya kamata mu tattauna akai koh"

Dukar da kai tayi tana wasa da yan yatsun ta,

"Pls seat" saida ta zauna kafin ya cigaba da magana

"Am sorry,akan abinda ya faru jiya,
Niyyata ta jiya badan in cutar dake koh in tsoratar dake bane bah,

Kawai farin cikin ganin ki ne ya ruda,
Kalli mah time din dana dawo,so late, but nasan zan ganki in na dawo"

Ya dan numfasa

"But ya zama dole in san"
Ya tsaya beh cigaba bah,

Dago kanta tayi ta kalleshi kafin ta ayuana abinda zece. A gaba

'Ya zama dole kasan in haka rayuwar mu zata kasance'

"Ina bukatar in san in ina baki tsoro"
Hawaye ne ya tsiyayo mata a fuska

"Shit! Am sorry,
Kin san meh, manta kawai,
Mu bari sai hankalin ki ya kwanta sannan,
Komai ze iya jira"

Mika yayi da hamma bayan wani dan lokaci

"Ya kanata inyi wanka, but nagaji dayawa" ya karasa da mika yana mikewa saman gado

"Bari inje in hada ma breakfast" yace tnk you yana lumshe idanu,


"Allah yayi aure da marar kwabo, naxata yau bazaku fito bah ai,

Ina yake, shi dadi Mata tunda ya dawo beh neme ni bah"

Har kasa ta duka ta gaishe da Mom da Granny ma

"Lfy lau Asma'u, ya gajiya" tana cewa Alhamdulillah, mamanshi ta mike

"Muje, da zan barki na dan two days, amma naga maxarin kadin can sai rawar kai yakeyi,

Muje" ta rike mata hannu har suka isa daki

"Sha" ta dora mata wani magani saman hannu,

Bata fuska tayi, dan taki jinin magani, gwara ayi ta mata allura,

"Mom ? Bana rashin lfy"
Mamanshi tayi dariya

"Tabbas nasan lafiyarki lau, daga hayaniyar ku na jiya da daddare mah ai mutum ya isa yasani"

Ta girgixa kai sannan ta cigaba da cewa

"Ke koh dan jan ajin nan bakya yi,
Mtsewwwww,
Gwara ma kar kiyi,

Ayi a gama wannan episode din koh mun samu kan shi a gdan nan"

Magazines ta kwaso ta zuba a kasa, sun kusan 7-9

Hotonshi ne a saman kowanne,
Daga wanda aka rubuta, Most eligible bachelor,
Sai Young Brilliant Minds,
Most stylish,
Most Handsome, new face of business,

"Ehsaas yafi karfin ki, kema kin sani koh?" Ta daga mata kai a hankali,

"Good, kuma nasan kin san bana son hada jini koh iri da Talaka"
A ranta tace kaman mahaifiyar ki

"I mean meh sukeyi banda buttom feeding,
Daga can zuwa can suna kwakulan mutane, da labaran su na karya,

Duk abinda kika ganni dashi a yau dinnan, i worked my ass off to earn,

Lokacin kina ina?"
Ta zo har gabanta ta tsaya,

"Bama wannan bah Asma'u, ni ke kwatakwata bakiyi min bah,
Kuma baki dace da dana bah,

Kuma ina da yakinin sha'awa ce ta rufe mai idanu yake ganin kaman sanki yakeyi,
Koh ba haka bane?"
Da bata ansa bah sai tace

"Koh kin asirce min shine" dago kai tayi da sauri

"Kar kiyi mamaki, ba yau kuka fara bah"

Wata leda ta bata
Tana dubawa ciki taga magani, a receipt kuma an rubuta pack din Ella

"Na hana daukan ciki ne" bata san ta saki komai bah

Wani murmushi mamanshi tayi

"Yap ni din haka nake, bana wani boye boye, straight to the point nake,

In ina son ka kaci sa'a, in bakayi min bah kumaaaa"
Tsk tsk tsk

"I make sure ba zaka tsayamin a hanya bah,

Kuma in a way, ke nake taimaka mawa
Saboda Ehsaas wani aure zeyi, da matar dana zabamai, wacce take da duk abubuwan da dana yake bukata a rayuwar shi, ba ke bah"

Dago fuskarta tayi
"Am classy, sophisticated, Eloquent,

Abin kunya ne aga dana da mata kaman ki"


Dukawa tayi ta dauko mata ledan maganin

"Zaki godemin in kuka rabu, kika kama hanyar ki salin alin, yafi daki tafi da yaro a hannu,
Koh ya kika ce"
Yadda tayi maganan kaman tausayinta take ji,

"Good Girl" harda dan taba mata kai

"Mun kulla yarjejeniya kenan koh, to yi maza ki sha"

Tana

Please Login or Register in order to submit comment