Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

manah da ki bashi tuwo in ya dawo"
Mama ta girgixa kai ta shiga daki

"Babanku ai yafi son tuwa,gashi kice ina gaisheta"

Kulan ta karba ta rungume ta cikin hijab dinta har kasa kafin ta fita ta tafi

Tun cikin zaure ta fara kwada sallama, da yake ba meh kwaramniya bace bah, muryata bata fita sosai

"Allah kuwa kaka, ni ina ganin zan bar aikin direban nan tunda wannan harka tayi dadi"

Kaka ta duba rafar yan dubu 1 guda uku daya zube mata a gaba

"Saleh na, jikalle nah, wannan duk gudummuwar da ogan naka ya baka ne" ya washe hakora

"Ji dani yakeyi ai sosai, da badan haka bah da tuni na aje aikin direban shi"
"Karka sake ka yanke manah hannun arziki, dama saida na sha wuya kafin aka kaika gdan dan daukan ka aiki"

Da dauki rafar kudin tana dubawa
"Dasu nakeso kiyi mah Asama'u lefe"

"Kund** ub** can" Asma'u ta toshe kunne

"Da duka wannan kudin za'ayi mata lefe, yar gwal ce ita koh meh, Allah sitiri bukwi, Allah ka kareni"
Ta tura kudin karkashin pillow dinta

"Karki damu kaka, da munyi aure itama kaita can zanyi su dauketa aiki, kinga sai in dinga turo maki kudi masu dan tsoka"

Farin ciki bayyane a fuskar kaka

"Ita ta dage maganar karatu, toh taje can tayi ta bauta ina cin kudin aikinta"

"Amma karki fadamata kaka, kinga lallabata nakeyi a samu ayi auren nan"

Asma'u ta jingina da bangon falon tana sauraron abinda suke cewa
'Abinda suka kudurta yi min kenan, banyi mamaki bah ai tunda ba tun yau bah na zama yar aiki a gurinku, Allah ka fidda daga hannun makiya da basa san kwanciyar hankali da farin cikin mu'

"Salamu Alaikum" saida akayi yan kus kus kasa kasa kafin aka amsa sallamarta

Hakimce yake saman lotsatsiyar 3str din dake falon kaka, wanda sai ka zama mai mahimmaci a gunta kafin ta bari ka zauna sama,

ciki da falo ne dan
haka bata ga kaka bah data shigo

'Ba shakka taje boye kudin ta ne'

"Kaka gani nazo" koh ba'a fada bah tasan ita yake kallo

"Baki ganni bane bah"
"Sannu da zuwa" ta fada ba tare da ta kalleshi bah sannan tayi waje

"Ja'ira, kin fara munafurcin koh, gaisuwar mah saida ya roka"

"Ina yini kaka, gashi in ji mama tana gaishe dake kuma" ta mika kullan daga inda take tsugunne

"Aje acan" ta nuna fridge din dake waje
Zuwa tayi ta dora a sama

"Damu nakeso kiyi mah , jikalle nah na bashi tuwo ya kasa ci, ke naga kin dan iya abincin meh dadi"

Kaka ta shige cikin falo, kafin ta fito sai ya biyota waje

"Ba yar tarban nan, koh ya hanya bakiyi min bah, balle in sa ran yar sumbata da runguma irin ta masoya"
'Meh hali dai baya barin halin shi' sai tayi mai murmushi a fili

"Gashi kije ki siyo kayan miya da couscous din, ki biya ki siyo nama dan kar ayi mai abincin sa lam"

'Inna lillahi yau sai na kai dare kenan, zan biya gda in fadama Mama toh'
Hannu ta mika zata karbi kudin sai ya cafke

"Wa na kama" sai ta zaro idanu tana kokarin kwacewa

"Aa kaka, ki bari mu danyi hira manah, ki aiki almajiri ya siyo" data kasa fizge hannu nata saita sa dayan hannun tana kokarin bambare nashi daya riketa

"Gata kuma sai na yi aikin nemo almajiri"

"Aa, kaka ki kawo in siyo, kuma kinga ban nuna maki wayata bah sai in biya in dauko maki ki gani, dan Allah"

Ta roka, duk da tasan yanxu dole kaka ta barta ta tafi tunda dama tayi tsegumi akan wayan

"Sai na dawo toh" gda ta nufa ta fadama Mama cewa zata tsaya yi ma kaka girki

Bata fadamata salisu yazo bah, dan kar suyi tsammanin zatayi wani abu dan shi

"Wannan tafiyar taki kika tsaya yi koh" gani tayi an zuba mai dafa duka na shinkafa da waken data kawo wanda yaji mai yayi warawara

"Kaka koh in bar abincin sai gobe tunda" ta nuna shi bata karasa bah

"Aa, kaka ina so in kara cin wani girkinta, kinji yadda wannan yayi dadi"

"Ai dama ba tafiya zatayi bah"



Allah gamu gareka.👏🏻😘
[3/9, 10:57] ‪+234 706 870 0853‬: 💐💐💐💐💐
💐💐💐💐
💐💐💐
BOYAYYEN KUDIRI
KHALEESI,
NOBLE JUDGE.
💐💐💐
💐💐💐💐
💐💐💐💐💐


Ji daga gareku is always nice, nagode sosai Allah ya amsa manah du'ain mu.😘


0⃣8⃣


"A duk duniya nafi kowa sa'an mata,koh ya kika ce" ya daga mata gira

'Kalolin iskanci babu wanda baka iya bah'

"Matso in baki abincin a baki"
Koh kallon shi batayi bah ta bashi ansa dan tasan yanxu kaka ta fito ta fara tsine mata albarka

"Kaci kawai, bana marmarin wannan" ta kagara ya gama ta mike ta tafi gda

Banda dafa abinci, har zobo kaka tasa tayi mai sannan ta kimtsa mah kaka gdanta ta wanke kwanu kan da aka bata,
Bata barta ta tafi bah tace ta tsaya suyi hira tunda gobe ze koma wurin aiki

"Ni kam ina san jan ajinki Asama'u, harda shi yasa ina ganin ki naji in ba ke bah sai rijiya meh kwalabeh"

'For the gazillion time sunana Asma'u, ba Asama'u bah' ta girgixa kai kawai

"Na gama toh" kaman tana jira ta mike at attention zata kwashe kwanu ka ta gudu

"Zauna akwai abinda nakeson in baki" kaman ta harba a guje dan hankalinta beh kwanta bah

"Dare fah ya rigada yayi ka bari sai da safe"

"Shin baki san hirar masoya tafi dadi da dan duhu duhu bah"
"Zauna " ya kama hannuta, wannan karon tayi sa'ar fizgewa sai ta zauna dan nesa dashi

"Wannan naki ne, shi nakeso kisa ranar darin auren mu, dan kowa yasan ke tawace ni kadai" karban dan akwatin tayi wanda yayi kama dana sarka

"Yayi koh" kasa dagowa tayi daga kallon design din yan kunnen, ba sarka a ciki duk da ga wurin shi nan

"Gwada ki gani" bata san lokacin da ya matso bah sai jin shi tayi a gefenta kaman ze shige mata

"Gashi banaso" wurga mai tayi dan ta samu ta bar wajen, koh ta kan kwanuka bata bi bah ta fita daga falo

"Bazan sa kayan sata bah ni Asma'u, dan koh makaho ya laluba yasa yan kunnen nan yafi karfin ka"
A hankali take magana kaman yadda take tafiya, duk da sauri takeyi a haka

"Wa kike cema barawo" ashe biyota kawai yakeyi saida ya bari ta isa zaure in da keda duhu sannan ya jata ya manna da bango

"Allah ka sakeni koh in tara maka jama'a" rufe mata baki yayi da tafin hannunshi yana huci

"Bari in baki shawara matata, baki san abinda zan iya yi miki bah, saboda haka kiyi taka tsan tsan dani"

Saboda tsabar tsoro har hawaye ya fara tsiyaya, haka mararta a shirye take data saki fitsari

"Allah ya isa" ta fada daya cire hannu daga bakinta

"Wa ke daure maki gindi wai, nasan dai yan gdan ku bazasu iya tabuka komai bah"
Ya manna jikinshi a nata, hawaye tsiyaya yake kaman a kunna fanfo, ga wani tsoro da takeji wanda yasa ta shike

"Muje ciki ki fadama kaka" ya fara janta cikin gda

"Allah zan fadama Raees ya sake ci maka mutunci" saukan mari taji wanda har idonta saida ya samu nashi kason

"Ya akayi ne?" Kaka ta fito ta isketa duke kasa tana rufe fuska


"Wai Raees" beh karasa zancen bah kaka ta harzuka itama ta kai mata duka

"Dan uwa*** ki kira wanda yafi basamuden, gantalalla"

Mikewa tayi zata tsere ya rikota gam gam
"Bani wayar ki" girgixa kai tayi, kaka zata duketa sai tayi saurin magan

"Allah bata nan" wayarshi ya fiddo,

"Samun number dinki" da kyarma tada number dinta, dan shine ze zame mata mafi a'ala,

Tunda ta isa gda da fuska cikin hijab bata sake fitowa bah

"Yau kuma kaka yan dukan nata sun motsa ne" batace ma mamanta uffan bah ta cigaba da kukant

"Kaka ce koh" ta daga ma mamanta kai

"Yi hakuri kinji,mai sama ze saka maki". Tasan abin yayi mah Mama zafi dan bata taba cewa Allah ya saka mata bah.


"Banga Asma'u na ayyukanta bah" Baba ya tambaya yana karyawa

"Jiya har kaka taje tayi ma aiki, in gajiya beh gama sakinta bah"

"Jiya ban fadamaki abinda ya faru bah da na dawo"
"Ai naga dare yayi ne lokacin dak dawo"

Har tashi tayi zaune dan taji abinda suke fada
'Da karfi da yaji na koma meh labe ina sauraran mutane'

Komawa tayi ta kwanta amma bata bar jin abinda suke cewa bah

"Duk sun goyi bayan auren nan"
Babu wanda ya sake cewa komai na dan lokaci

"Kin san Mai bagaruwa dinnan?" Baba ya tambayi Mama
"Ya za'ayi in manta dashi" ta fada da murmushi
"Harda gudummuwa yace ze aiko dashi,bayan ya bada abu a kawo min"

"Dama can akwai sji da kyauta, Allah ya biya shi"
Tunda taji Baba beh fadi abinda yan uwa suka bada a matsayin gudummuwa bah tasan haka yaje ya dawo hannu biyu

Mirgina tayi tayi a saman gado har saida Baba ya tashi ya fita kafin ta dauko kudin wayarta data saida ta fito

"Kin dai samu bacci koh?" Ta ce sannan ta karasa kusa da mamanta ta zauna
"Mama gashi wannan" ta mika mata kudin wanda mama ta kalla da mamaki

"Na saida wayata" mama ta zaro ido

"Waya saki Asma'u, wa kika tambaya, in kika saba da saida abinki saboda kudi toh sai kin tashi baki da wata kadara"

"Mama wannan ne na farko kuma na karshe in shaa Allah, na gaji da ganin ku cikin damuwar nan ta rashin kudi"

"Ni mama da zaki bi ta tawa kuyi amfani da kudin nan dan biyan bukatar ku, kada ku kashe su akan wadan da baza suyi appreciating efforts dinku bah, dan Allah mama"
"Asma'u bukatar mu a yanxu shine mu rufa ma kanmu asiri, mu aurar dake cikin rufin asiri, koda kuwa zamu karar da dukka abinda muka mallaka, wannan hakin ki ne a kanmu basai n damu da yadda zakiyi ki taimaka bah"

Bata gamsu bah amma ta yi shiru kawai ta fara aikinta, yunwa bata dameta bah dan hankalinta ba kwance yake bah balle taji ta damu


"Sis ana neman ki a waje" Mukhtar ya koma daki fuska daure kaman yadda ya shigo a daure

"Surprise test akayi muku a makaranta ne koh meh kake cunno baki yaya"
Da sauri ta koma cikin gda tasa hijab kafin ta fita zuwa soro inda yake tsaye, tasan ba karamin aikin shi bane bah ya kunno kai cikin gdan

"Jiya kinyi mantuwa" ya miko mata akwatin sarka da yan kunnen data ce bata so
"Nace ka bar" matsowa yayi daf da ita sannan ya manna mata saman jiki

"Kar ki bani kunya,kuma ki kiyaye karki bari sanarin nan a zuwa wurinki" yasa kai ya fita

Cikin hijabi ta shiga da yan kunnen gda sannan ta boye a dakinta.


"Na sa an hada maki appointment da wani likitan kashi, in kin je ssai ki fara ganin shi koh"
Har airport ya rako Granny ma,dan ranar zata nufi kasa meh tsarki dan yin umarah

"Akwai ka da kulawa Ehsaas, gashi ni zan tafi in barka kai kadai"

"No ba matsala Granny,dama zan dinga ziyartar office dinki tunda ke bakya nan"
Ta jin jina kai

"Daka kyauta toh. Amma ai hutu kazo ba aiki bah"

"Bakomai Granny MA, zan so in zagaya duk inda kuke da office in dan ga abinda ake ciki"

"Allah ya shi maka Albarka Ehsaas, kaman kasan ya dade rabon da in fita zuwa branches dinmu dake wajen abuja har na manta wallahi"

Yayi murmushi sannan suka rungume juna

"Sai kin fadamin yadda kukayi da Dr din" suka dagama juna hannu saida jirginsu ya daga kafin ya koma cikin mota

"Sir an kira ka" aka mika mai wayar ya duba ko waye

"Meh yace?" Suka cigaba da tafiya zuwa inda sukayi parking mota

"Wai yazo da wanda sukayi hiring masu yi maka aiki"

"Good, were getting somewhere"

Suna shiga akayi parking ya fito daga motar, a jere ya gansu masu aikin gdan da wanda ke nemo masu yan aiki a gefe

"Kaine wah?" Ya tambayi mutumin

"Shine meh kawo manah masu aiki"
Ya rigada ya san haka, kawai dai ya saba da anayi mai abubuwa ne

"Sai kayi mistake din kawo manah barawo, he stole something precious"

"Am sorry sir"
"In dai ba so kake ka kwana a hannun police bah, you'll tell me more than sorry"

Mutumin ya duka kasa kan guiwwowin shi

"Kayi min afuwa sir, alfarma nayi ma wani family friend dake neman aiki, banyi bincike bah saboda ban zata its necessary bah, kayimin afuwa"

"Family friend?" Ya juya ga sabon driver dinshi

"Waye?" Driver din ya tambaya

"A zaria suke zama"
"Karbi address din gdan,gobe zamu tafi ka shiry"


P.S, people Ehsaas half British half Nigerian ne, baya jin native language dinshi watau hausa, muna sa maganarshi da hausa ne kawai da littafin hausa ne wannan, but frm now on yawancin maganar shi ze zama da turanci ne,

Later everyone.
[3/9, 10:57] ‪+234 706 870 0853‬: 💐💐💐💐💐
💐💐💐💐
💐💐💐
BOYAYYEN KUDIRI.
KHALEESI,
NOBLE JUDGE.
💐💐💐
💐💐💐💐
💐💐💐💐💐

Akwai lots of typing errors acikin book dina,dana gama page kawai so nake in aje shi a side in fara tunanin wani shi yasa bana editing, but ina fata mistakes din ba irin wanda za'a rasa gane meh nake nufi bane bah.

09033325153 whatsapp your comments to the 👆🏿 number. Tnk u😘


0⃣9⃣.


Zaune take ta tattara zaninta tana cuda kaya
"Ki tabbatar kin kama bakin zanin kin wanke shi shima, tana nan ake gane ka iya wanki"

"Toh kaka" ta fara kama kasan zanin tana tattarewa

"Jikalle na ya kira ki kuwa" tana jijjiga kai

"Dake nake magana fah" tayi saurin bude baki ta bada ansa

'Wannan meh makon Allah na tuba ai koh ke baze iya kira bah'
Tuno yan kunnen da ya kakaba mata tayi

Makon shi ya kara tabbatar mata da abinda zuciyarta ke raya mata, shi yasa hankalinta ya kasa kwanciya da su

"Yanxu haka aiki ne yayi mai yawa, ina fata dai yana nan lfy, in kin kai gama na hannun ki zaki je siyo min kati"

"Toh kaka" tana gama wanke zanin kuma ta mike ta zura hijab dinta sannan ta nufi inda kaka take zaune ta karbi kudin katin

Data dawo daga siyo katin bayan tasa mah kaka a waya, sai ta dauraye wadan da ta gama wanke tasa cikin bokiti kafin ta fita kai shanya makota

"Salamu Alaikum" tana nan waje har saida aka amsa kafin ta shiga
Gaishe da matar tayi dake kwance saman tabarma a tsakar gda

"Asma'u shine koh a dan leko ace an daga biki" tayi murmushi dan matar babbace ba yarinya bah

"Allah yasa Albarka toh ya sa ayi a gama lfy" a cikin ranta ta amsa da amin
"Zan wuce toh kaka" ta fada daga bakin kofar daki

"Shigo ciki" ta bude labule ta shiga da sallamar da kaka bata ansa bah

"Wani iya shege ne yasa baki fiddo anko ba har yanxu, badan haka kukasa aka kara sati biyu bah"
Gabanta faduwa yayi, dan da ba'a kara sati biyun nan bah da yau ita matar aurece

'Allahumma Ajir ni fee musibhati wa klif ni khairan min ha' abinda tayi ta maimaitawa kenan bata bah kaka ansa bah

"Ki koma gda kice mah uwa*** nace ta aje iya shege ta dage mah shirin aure dan yin shi za'ayi ba fashi"
Ita ta gaji da tsugunni tayi ma kaka sai anjima

"Kuma kada ki manta ki dawo ki kwashe shanya, dan bazan dinga bi makota ina kwasowa bah"
Toh tace kafin tasa kai ta fita daga gdan, bata bar neman tsari da mika kukanta ga mahalicci bah saida ta shiga cikin gda

"Sannu da aiki Mama" ta fada bayan ta gaisheta

"Ke zance mah sannu Asma'u" dan waken da maman ke jefa tasa cokali ciki zata juya

"So kike ki wargaza min abu koh" cire matsamin tayi daga cikin tukunya

"Wanki kawai nayi mah kaka, sai markade dana kaimata" Mama ta jin jina kai tana harkar gabanta

"Bari in tsame wannan kici ki tafi" ta katse hamma da takeyi

"Zaki aike ni ne mama" taji mama tayi ajiyar zuciya

"Yanxu na fara yadda cewa kin kusan barina" ta bata fuska zatayi kuka

"Ke karkiyi min kuka anan, abin murna ne ai" batayi kukan bah amma dai yana makale a makoshinta

"Ma'u tazo,dama nayi ma mamanta magana akan zaman ki acan har lokacin biki yayi" girgixa kai ta farayi, da mamanta ta bude baki zatace wani abu saita kara girgixawa

"Kije ki shirya Asma'u, na rigada na bada kudin duk abubuwan da za'a bukata, kuma mun makara mah" ta cigaba da girgixa kai

"Bari sai kinci abinci kafin nan ki je ki shirya" ita dai aikin turo baki kawai takeyi, duk santa da dan wake bataji dadin wannan bah

"Toh in na tafi waze dinga tayaki yin aikin gda" ta tsaya da hada kayan ta

"Kaman aikin gdan wani meh yawa ne, ni zanyi abuna" har yanxu dai hankalinta beh kwanta bah

"Kuma ki je ki siyo anko Asma'u sai tambaya ta akeyi"
"Toh mama in na samu lokaci zamuje" fada kawai tayi bata da niyyan zuwa

"Gwara mah da zakije gdan su Asma'u nasan ita zata sa kuje ku siyo" bata lokaci kawai take wurin shirya kayan, dan haka Mama tayi taking over

"Zan zo gobe da safe in tayaki aiki" mama ta shafa kanta
"Ki barshi kawai, ki taya kaka tafi bukata" ta gyara mata hijab dinta

Gdansu Ma'u dan gaba ne da gdansu kaka dan haka ta fara shiga can tana kwashe mata shanya

Bayan ta fito daga wani gda dauke da kayan data linke taga wata mota GMC baka anyi parking dan kusa da gdan kaka, wani mutum ta gani jingine da motar ta wurin driver, kara sauri kawai tayi ta fada gdan kaka

"Kinga wasu mutane a waje koh" ta daga mata kai

"Yanxu aka hadosu da wani almajiri ya kawosu nan gdan, wai salisu suke nema"
Aje kayan tayi saman kujera tana kokarin fiddo wayarta

"Bari in kira yaya Abba tunda yana gda sai yazo yayi magana dasu" fizge wayan hannunta akayi

"Gwara ke kije, in kika je kice musu jika nah maraya ne su dubi Allah kada su lakaba mai sharri"

Banyi mamaki bah da kikayi tunanin magana ya jawo maki harki gda bah, tunda dai kin san halin nasa

"Bari dai in kira yaya abba din"
"Kije ke, tunda ke macece zaki fi canza masu ra'ayi"
Allah ya saukake mata alamarin nan tace

"Salamu Alaikum" ta makale bakin kofa tana fada cikin karamar muryarta,

Tun data shiga cikin gda dazu yake jira ya sake ganinta, dan beh ga face dinta sosai bah

Manna face dinshi yayi jikin window yana kokarin ganin face dinta, gani yayi ta kallo inda motar yake dan haka ya bude ya fito

"Salamu Alaikum" ya fada yana karasawa kofar gdan

"Wa'alaikumus Salam" ta ansa da karamin murya
"Ina wuni" sai yayi murmushi kawai, driver dinshi ne ya matso kusa dashi

"She's greeting you sir" taga ya daga kai once sannan ya kalleta

"Yana ansawa" kallon shi tayi da kyau

"Am sorry to ask but why are you here" ya ciro hannu daga aljihu

"No need to be sorry, muna neman wani salisu na bukari" ta daga kai

"Eh nasan shi"
"Is he home?" Ya tambaya

Kai ta girgixa mai
"Ku fadamin abinda yasa kuke nemanshi,koh ku su waye sai in fadamai in ya zo" ta fada da turanci

"Just tell us when he'll be back"
"Sai nan da sati biyu,yana wurin aiki" taga ya kalli driver din sannan ya juyo gareta

"But this is he's permanent address right?" Ta daga mai kai

"Meh

Please Login or Register in order to submit comment