Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

karfin naki na wanda ya lauji tuwo ne"
Dariya tayi mah Ma'u data rada mata maganar,


"Mama!" Ta fada da karfi ta kankame mamanta dake kitchen tana hada kayan iftar,

"Ke meye hakan, shirmen da bakiyi bah da kina yarinya sai yanxu da kika grima zaki yi"
Ta kara cewa Mama da shagwaba,

"Bari inje inyi sallah" ta nufi dakinta, bayan ta idar ta koma kitchen,

Ba yadda basuyi da ita bah akan ta bar aikin suyi amma taki tafiya,

Saboda tsananin farin ciki bata bi takan wayarta bah, shi kuma bawan Allah yayi ta kiranta, sai a wurin lukman ya samu labarin sun isa lfy,

"Ke baki gane nufinta bah" tace hmmm tana shiga dakin nasu,

"Na gane manah, manta dasu suyi ta surutun su"

Ta yada zango saman gado tana aje sallaya hade da cire hijab dinta,

"Nima dai nabi sahunsu Namecy,

Allah kin rameh amma kinyi haske, kodai kodai" ta hada da daga mata gira,

"Kya ji dashi koh mah menene kike tunani"

Ta wurga mata pillow, sannan ta zube kasa

"Kedai zaki ji dashi, tunda a jikin ki yake, zanga su namecy da baby, arghhhhh"

Tayi yar kara harda tsalle

Asma'u tayi tsaki tana girgixa kai,

Jakar data shigo dashi ta jawo, tana fiddo abubuwan ciki,

"O.M.G Ya akayi kika san ina neman irin agogon nan,

I've been dying to see one"

"Sai ki daina mutuwa haka nan ai"

Ma'u ta manta da ita ta koma duba agogonta meh hade da awarwaro,

"Wannan mah naki ne, amma tunda wancan kadai ya ishe ki"

Fizge ledan tayi tana duba abin ciki,

Wani ihu ta karayi,

"Ki rufamin asiri karki taramin mutane" ta kara wani guntun ihun data fiddo dayan takalmin,

"Jimmy choo ne Namecy"

Kwankwasa kofa akayi kafin aka shigo,

"Ina fata dai komai lfy" kaman ta sani ta kalli Ma'u taga ta daure fuska koh inda yake bata kallo,

"Komai lfy ya Abbah, ya aiki"
Yace Alhamdulillah sannan ya dubi Ma'u

"Karki kware manah rufi da ihun ki" bata kalleshi bah amma ta murguda mai baki,

"Mun daina ya Abba" yace toh amma idanun shi kan Ma'u data hanashi ganin fuskarta,

"Yanxu kuma wani kalan wasan kukeyi?" Ma'u tayi tsaki hade da turo baki,

"Ai sai anga fuska ake wasa dakai, wannan fah?" Ma'u ta jawo lace da sauran kayan da Mom ta bata,ita batayi niyyan bah iyayenta su bah,

Shi yasa ta siyo masu wasu da sunan Mom ta bada a kawo masu, duk da basu kai na wadancan tsada bah,


"Ahmmm, nawa ne"
Ma'u tace shegiyar nan tana mikewa tsaye hade da gwadasu a jikinta,

"Wanne ne nawa" ta kwato su,

"Wallahi ba ayi ki bah, ki zabi daya in zabi daya, raba dai dai zamuyi kuma ni zan fara zaba tunda nice karama"
Tana daukan wani ta kara fizgewa,,


Suna cikin haka sai taji vibration sau daya, bayan dan lokaci kuma sai ta sake ji,
"Wayar ki ce?" Ta tambayi Ma'u,

"Nope tawa ba silent take bah"
Tana jawo handbag dinta taga missed calls, akwai na Hajia sai nashi dayawa,

"Ehsaas" ta fada a hankali,

"Ehsaas fah kika ce" Ma'u ta fada idanu waje
Ita kuma ta daga mata kai,

"Tabdijam, Haka kike kiran shi" ta fiddo idanun mamaki,

"Ba sunan shi bane bah" Ma'u ta tafka mata bugu,

"Allah ki bari, koh in rama ni mah" ta sake dukanta,
"Idiot" tace tana mikewa da sauri,


"Nayi fushi cutie pie" hakuri ta bashi kafin ta fadamai dalilinta na kin daga wayar shi,

"An ga yan gdan an manta da wannan bawan Allah koh"

Tace uhm uhmm
"Ya Mama da Baba, kowa da kowa"
Ta zauna saman gado,

"Duk suna nan lfy" yayi mata ya gajiya kuma da fadan cin abinci,

"Ahmm, Kace ma Mom, iyayena na godiya da abin arziki"
Ya tambayi na meh

"ATSAKANIN MU, ne ni da ita"

Yar dariya
"Oh! Keda ita, ni basai na sani bah kenan"
Tace exactly,

Bata bari sun cigaba da hira bah, dan kar ta koma tunanin matsalolin data baro a can,

Badan yaso bah yayi mata saida safe,


"Meye kike bina da ido" Ma'u tayi tagumi,

"Allah namecy kina bani mamaki wani lokacin,

Nasan ke din wayayya ce, amma sai kiyi tayin abubuwa kaman wata bagidajiya"

Tayi ajiyar zuciya sanna ta kalleta,

"Toh Ma'u yanxu kuma meh nayi"
Tana kauda kai ta maida ga kayan gabanta tasan bataji dadi bah,

"Wani abu nayi maki neh?" Hmmm Ma'u tace, sannan ta kalli kofa,

"Ina jin dama nice a inda kike yanxu,
No lie ina son inyi aure, in auri wanda nakeso,

Amma ke naga kin samu wannan chance din kuma kina sakaci dashi"
Dafata tayi sannan tayi mata murmushi

"Kiyi fata kada Allah yasa kiyi irin rayuwar da nakeyi,

Bazan mah makiyi na fatan haka bah,

Ki cigaba da addu'a my friend, in RABOn ki ne Ya Abba,
Toh zaki aureshi"

Ta dan saki fuska, kafin tace tnk u,

"Mu koma kan abin da nakeson yin magana akai,

Allah da nice mijina ya kirani sai abinda ya ture mah buzu nadi"
Ta mike tsaye tana wani taku dai dai

"Ai yau ba bacci, sai mun soye minyi kurmus koda zamu sarara"

Dariyarta takeyi tana mamakin abinda Ma'u ke cewa,

"Wallahi namecy ki dage, mazan da dana yanxu ba daya bane bah,

Mata ke bin maza yanxu, kiyi sakaci wata ta kwace maki shi, tun a waje mah basai ta shigo ba tukun"
Ji tayi ranta ya baci daga hango zancen Ma'u

"Kadan mah kenan, hango wata makale jikin Ehsaas" saida ta cije leben ta na kasa saboda wani bari da jikinta yayi,

"Ashe kin damu dashi, shine kike kiranshi da sunan shi gatse gatse,

Ni Namecy din dana sani koh wanda bata sani bah bazata kira sunan shi kai tsaye bah balle mijinta"

Turo baki tayi tana daga kafadu,

"Shi yake so in kira shi da sunan shi ai"

Ta zauna gabanta,

"Toh meh ze hana ki kirashi da abinda yafi sunan shi dadi,

Koh shagwaba zakiyi koh wani abu kikeso daga wurin shi, in kika bishi da swt name Allah zefi saurin yi maki abinda kikeso,

Koh a wani wuri yaga koh yaji koda irin sunan da kike kiran shi dashi ne, sai ya tuno ki, sai yayi murmushi, koh be yini yana tunanin ki bah"

Aranta tace duk wannan kika shirya yima mijin ki, ni kuma meh na iya?

"Zan gwada Ma'u, tnk u"

Ma'u ta e bakomai, sisters 4 lyf,

Abin ya bata dariya, dan ya tuno mata da lokacin da suke secondary school,

Suka rubuta sunayen su jikin desk da permanent marker sannan suka sa sisters 4 lfy,

"Kema abinda kika tuno kenan koh" ta girgixa mata kai

"Ni bulala da kuma punishment din na tuno"
Suka fashe da dariya a tare,

"Mene neh?" Ta jawo wayarta data katse su da kara, text ne daga Ehsaas

"Meh ya kunsa" da Ma'u ta zunguro kai bata hanata karantawa bah,

^Yau na yini ba tare dake bah,
zan kwanta bacci ba tare dake a kusa dani bah,
Haka in na farka bazan yi ajiyar zuciya in jawoki jikina bah,

Yau ne kawai kikayi nisa dani, amma ina jin kaman in na ganki gobe na rike ki bazan kara bari kiyi nisa dani bah,

Ina jin dama na fadamaki duk abinda ke raina, na rungume ki kaman bah gobe,

Bamu da tabbacin gobe, shi yasa na fadamaki yadda nakeji a raina yanxu,

I miss you, and i love you, so dream of me pls^

Wani ihu Ma'u ta kwada daidai saitin kunnenta,

"Love is sweet" ta tashi tsaye tana jujuyawa da hannuwa bude,


"Pls love of my life ka bayyano hakanan, ina kewar ka tun ban ganka bah"

Knocking akayi a kofar dakin,abinda ya hanata karasa dariyarta,

"Wai lafiyarku"
Wannan karon Ya Mukhtar ne,
Hakuri ta bashi, beh tsaya saurare bah mah yayi gaba abinshi,

"Wallahi namecy kina bayar dani, ki turo mai daddadan kalamai manah"
Harda jijjigata saboda excitement din da takeji,

"Naji karki nakasa ni" ta ture hannayenta,

"Ki kirashi da wani swt name anan kinji namecy,
Bari in barku ku ba tsuntsun soyayya wahala,
Bacci zanyi dan gobe da safe zan tafi gda"

Zancen Ma'u ya fiddo ta daga tunanin da takeyi

"Tun da safe" Ma'u ta rike haba

"Da kyar aka barni na fito, gobe saidai kizo gdan mu, kila in an ganki a kara barina in fito"
Tace toh, ita kuma Ma'u ta kakkabe masu gadon,

"Tunanin meh kikeyi?" Kaman tasan so take ta tambayeta abu amma ta kasa furtawa,

"Ni bansan da sunan da zan kirashi bah" Ma'u tace hehehe

"Kinzo gdan sister,

Bari in baki hint,karki kirashi da abinda ake yayi,
Kar sunan ya cika tsawo koh wuyar fada,
Zaki iya amfani da su Darling Honey, amma ni ina ganin sun tsufa,

In zaki sama mijin ki nickname ya zamana yana da wani ma'ana a wurinki, wani abu da yake saki kiji a jikin ki koh a ranki,

Irin yanayin da kike shiga in kika ganshi koh in aka kira sunanshi,

Kin ganeh ai"

Ita kara rikitata tayi dan abubuwa dayawa takeji gameh da Ehsaas

Ajiyar zuciya tayi kafin tace tnx, ita kuma Ma'u ta shiga wanka abinta,

Bayan ta tuna sunayen da yake kiranta dasu, depending da irin yanayin da ake ciki,

Saving number dinshi tayi da My All,

A text dinta kuma ta kirashi da my cuddly brat,
Cuddly saboda yana son jinta a jikinshi,
Brat kuma saboda shagwabar shi,

Koh minti daya batayi da tura mai text bah taga video call,

Ta mika hannu zata dauki dankwali ta rufe kanta kuma ta fasa, lashe lips dinta tayi hade da dan ciza su dan suyi deep pink,

"Ina so in tabbatar neh, kece kika turomin text yanxu"
Da kunya ta dukar da kanta,

"Haba sweet bunny dinah, kasa naji bah dadi, am sorry bana texting dinka"
Dariya ta fashe dashi saboda yadda ya fiddo idanu waje,

Lips dinshi ya cije saboda yadda take sashi ji ajikinshi ba tareda tasan tanayi bah,

Hakan kuma na kara rudashi,

"Kin san meh nake tunani" ta girgixa mai kai,

"Sugar" tace sugar!
"Ina kokarin hana kaina kwatanta zakin lips dinki dana sugar"

hade lips dinta tayi tana dan kauda fuska kuma saita koma kallon shi,

"Kullum in kikayi bacci sai nabi face dinki da kisses, ban taba kissing lips dinki bah dan ina so in zamuyi ya zamana ina amsar irin sakon da nake aika mah duk illahirin jikin ki"

Ba shiri ta kashe call din tana fiddo idanu waje,

Suna magana akan intimate abubuwa, amma ba a fayyace haka bah,

Call dinshi ne ya shigo wayarta, da kyarman hannu ta amsa,


Dariya ya karasa kafin yayi magana,

"Am sorry Caramel, ganin ki da kuma jin dariyar ki ya rudani har na fadi abinda ke cikin raina"

Taji dadi da bah video call suka cigaba bah,

"Meh zaki min daze karama mafarkina na yau armashi"

Kaman ruwa ya cinyeta koh numfashi ta daina yi,

"Angel eyes kirani da wani suna pls" ta tabbata yadda take ji a yanxu shima haka yakeji, koh fiye da haka ma, daga jin canzawar muryarshi,


"Amore mio" tace uhmmm,

"Pls" ya fada kaman bacci yakeyi,

"Ehsaas" sauti ya fito a cikin murmushin da yayi,

"Kinsan ina so ki kira sunana, but yau wani na daban nakeson ji"

A hankali ta jika makoshinta daya bushe,

"Your my heart beat, without you my whole body is paralyzed"
Hangoshi tayi yana sauke numfashi hade da lumshe idanu,

Dan motsi taji Kaman yana jan pillow zuwa kirjinshi,

"Wani kuma my wife"
Itama gado ta hau taji dadin dunkulewa a can karshen bango,

"Love ne kai a wurina, da kai kadai nasan so, haka cikin littafin so nah ka kai kadaine"

"Nasan farin ciki iri iri soul mate, farin cikin dana sani da kai duk shi yafi tasiri da kyal kyali a rayuwata"

Yanayin yadda yake fidda numfashi ke sanar da ita yana jinta,

"A zuciyata hoton ka ne gaba da baya,
A ruhi na tunanin ka ne kadai ke yawo,
Kwarjinin ka ke linka min bugun zuciyata,
Kallon ka ke sa in manta da iska ke jagoran rayuwa bah idanun ka bah,
Kasan cewa cikin jikin ka wani magani ne da illahirin jikina ke bukata,

You are MY ALL Hubby, hasken ranata in na farka,
Tsalelen watana in zan kwanta bacci__Arghhhhhhhh"

Ta kwala wani ihu daya sauko dashi daga saman giza gizan daya kwanta, ya naka shi a kasa,


"Wifey, meh ya faru, komai lfy"
Dariya yaji daga dayan bangaren kuma yasan ba nata bane bah,

"Ni naxata bacci kikeyi shi yasa na kwara maki ruwa"

Asma'u ta daure kaman bata taba bude hakoranta bah

"Namecy kiyi hakuri pls" Dariyar da Ma'u keyi kara sata daurewa yakeyi,

"Wani hauka ya shige ku yau" Ma'u tayi nata yar kara tana kare jikinta kafin ta duka kasa

"Allah ya isa" ta fada bayan ya Abba ya fita daga dakin

Meh Asma'u zatayi banda dariya, bata taba irin wannan dariyar bah harda share kwalla

"Allah namecy ki bari, ya ganni fah"
Kaman lokacin abin ya faru, sai tsalle take tana kare jikinta da towel ne kawai ta daura,

"Tun kafin ki shiga gdan shi bah" ta kara iza wutan,

Da yaji dariya kawai sukeyi nothing serious sai ya kashe wayan ya kwanta.





⚜B.W.A🖊
💐💐💐💐💐
💐💐💐💐
💐💐💐
BOYAYYEN KUDIRI.

💐💐💐
💐💐💐💐
💐💐💐💐💐


Story,Writing by
NOBLE JUDGE
Editing by
KHALEESI.




Dedicated to Ummi mi, mungode sosai da kulawar ki, Allah ya bar zumunci da kauna,

Ina maki fatan sa'a a karatun ki, Allah yasa ki gama da First class my dear,
Amin.


5⃣5⃣.



Kwanan ta biyu a gda ta shirya taje gdansu Ma'u,
Kayan data zo dasu Mama ta fidda lace da atamfa sai wani shadda coffee color tace a kaima Iyayen Ma'u, tunda mahaifiyar ta tayi dawainiya sosai a duka auren ta da akayi,

"Namecy ni na zabi wancan fah" harara mamanta ta galla mata kafin ta cigaba da magana da Asma'u

"Sai kije ki nace har a baki" ta fada daya rage su biyu a dakin,

"Koh kuma inzo in dauki naki bah" yar dariya tayi dan itama a tutar babu ta tashi,

"Saidai ki dauki na jikina" ta mike tana rataya bag dinta,

"Lallai mah, yanxu zaki wuce"
Ta daga mata kai,

"Ina zuwa toh" dakinsu taje ta dawo da wasu abubuwa a leda,

" Mama tasa aka hada ma aunty karima, sai ta diban maki"
Tana duba ledan ta yatsina fuska

"Da azumi mah sai mutum yayi ta shan wadan nan abubuwan"
Karba tayi tasa mata a jaka
"Kin yi ki gama korafin naki kuma ki sha"
Godiya tayi mata,

Waje ta fito dan ta nuna mata da gaske tafiya zatayi,

"Muje in gaishe da Baba in yana nan"
Fitowa Ma'u tayi ta mata jagora zuwa bangaren mahaifinta,

"Nagode Baba, asha ruwa lfy"
Ta mike bayan yayi mata fatan Alkhairi,

"Bashi ya kawoni bah kike wani daure fuska"
Ma'u ta harare ta,
"Ni wani abu nace" ta girgixa kai, tunda Ma'u tayi tsit bata fadamata dalilin rabuwar tasu bah itama tayi shiru bata tambaya bah,
Dan tasan ba fada zatayi bah,

Sallama sukayi kafin ta shiga mota,

"Ahmm ya kira yana tambayar in mun kusa isa gda"
Ajiyar zuciya tayi sannan tace mah lukman su tafi,

Yana ajeta a gda ya juya ya koma masaukin sa, ita koh wayar bata fita da ita bah dan kar ya kira tace mai bata taho bah,


Bayan sati da zuwanta, tana zaune dakin Mamanta suna hira saiga ya Abba ya shigo,

"Ina kika aje wayar ki, tun dazu da rana mijin ki ke kirana"
Gabanta ne ya fadi, kana kallonta zaka san bata da gsky,

"Na barshi a daki ne" ta mike sumi sumi zata fita,

'Yau koh ya akayi ya nemi ya Abbah'

"Bari in gayamai ya kira ki toh" tace toh,
Ya bi bayanta shima ya fita
Tun zuwanta da kwana biyu rabon da suyi waya dashi, tunda lokacin daya ce tayi a gda ya kare, kuma bata san ya takurata shi yasa ta kashe wayan,

Tana kunnawa texts rututu suka antayo cikin wayan,

Bata samu damar duba koh daya bah call dinshi ya shigo,


"Karamin abinda zaki iya yimin shine ki ansa call dina in na kiraki,
Abinda kawai na bukata kenan Asma'u,

Banso yin haka bah amma kin sa zan fara kafa maki takun kumi"
Ta katse shi kafin ya cigaba

"No pls, dan Allah kayi hakuri, pls"
Rai bace yake magana

"Kin wulakantar da daman ki Asma'u, banson in takuraki shi yasa na baki free reign kiyi abinda kikeso,

Tunda haka ze jawo ki daina ganin girma na sai mu canza tsari koh ya kikace"
Ta kara cewa she's sorry

"Am the Alpha abinda nace shi za'ayi, yes or no"
Tace mai yes da karamar murya,

"Good" ya kashe wayan,

Baki bude take kallon wayan, ta kasa ganeh meh ya faru yanxun nan, kuma meh yake so tayi,


Maganganun mah da muryar kwata kwata kaman ba nashi bah, kaman samai su akayi a baki,

Kodai ta matukar batamai rai ne, kaman ta kirashi ta bashi hakuri kuma tace sai an sha ruwa in yaci ya koshi kuma hankalin shi ya dawo jikin shi,
Kasa sukuni tayi, sai juya wayar take a hannunta,

Bata san ranshi ya baci sosai bah saida ta lalubi layinshi taji a kashe,

Nan take hawaye suka fara tsiyayo mata, bata nufi gogesu bah ta barsu sukayi ta wanke mata fuska,

Sukunin ta ya canza tun daga ranar, duk second koh minute din da zata samu sai ta nemi layin shi taji a kashe,

Sai ta yanke shawarar komawa gda kuma sai ta tuno iyayenta zata bari, ta koma inda take kaffa kaffa da kowa, inda ba'a san ganinta,

Shima hana kanshi jin muryarta ba karamin damun shi yayi bah,

Amma so yake taji yadda yaji in ya kira yaji a kashe,
Abinda ke kara karfa shi yayi haka shine kin dawowa da tayi,


Sun kai azumi na ashirin da tara akaga wata, farkon eid dun dazeyi celebrating da aure,

Ba tare da wani tunani bah ya tashi ya dauko wayarshi,

Ji yayi kaman karya kirata daya kunna wayan, ya nemi text koh guda daya daga wurinta ya rasa


"Kukan meh kikeyi kuma yanxu" bugu biyu ta dauki call din,
Yana cewa hello kuma ta fashe mai da kuka,

"Am sorry, ban kyauta bah na sani, dan Allah ka yafemin"

Zuciyar shi ta karaya, yaji baze iya jure jin kukanta bah,


"Meh yasa baki dawo gda bah toh, saboda kin raina ni" ta katse shi da

Please Login or Register in order to submit comment