Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Aa

"Allah ba haka bane bah" ya tambayi dalilin kin dawowarta sai ta cigaba da bashi hakuri

"Ina girmama ka, ina girmama maganar ka, dan Allah kabar fushi dani"

Irin abinda mamanshi keyi mai yakeyi mata, yanata sata taji ba dadi kuma tanata neman afuwa bayan ya rigada ya hakura,
Yasan yanxu zatayi mai duk abinda yakeso,

"Fyn zan hakura" tayi shiru tana maida numfashi,

"Amma sai kin dawo gda sannan" ta fashe mai da sabon kuka,
Sai ya kashe wayar shi,

"Bana tunanin kinyi nadama, da zakiyi abinda nakeso,

Amma tunda ban kai matsayin saki abu bah, shikenan kiyi yadda kikeso,
Har yanxu kwana biyu beh kare bah"

Hakuri ta bashi na karya sake kashe wayan,

"Toh ina jinki, zaki bi maganata ne koh zaki cigaba da bata ma mijinki rai"

Ajiyar zuciya tayi hade da gyaran murya,

"Yaushe zan dawo toh?" Yayi yar dariya,

"Yaushe ya kamata ace kin dawo"
Ta danyi shiru kafin tace ya dade,

"Zansa lukman yazo ya dauke ki gobe" har zai kashe wayan tace yayi hakuri

"Sai na ganki goben"
Bata taba tunanin Ehsaas ze juya ya matsa mata lamba irin haka bah,

"Asma'u" ta dago kan data kife saman gado tana aikin kuka,

"Na'am Mama" harda tashi zaune bayan ta goge hawayenta,

"Ya akayi?" Ta girgixa mata kai,

"Ba tun yau bah na lura kin takura, ya akayi" wasu hawayen suka tsiyayo mata,

"Gobe zan tafi gda" murmushi Mama tayi,

"Shine dalilin naki nayi kuka haka" ta dukar da kai

"Takura ki akeyi acan dinne" ba wani jin kiri ta girgixa mata kai,

"Ni anan nakeso inyi sallah" yar dariya Mama ta sakeyi,

"Auren nan sangarta ki yayi Asma'u" kuma sai taji kunya harda boye fuska,

"Karki ji komai kinji, babu inda ya fiye maki face dakin mijin ki,
Ki bar nuna mai bakya son abinda yakeso kiyi, kina rage ma kanki kima a idanun shi,

Mu mata da dauriya, juriya kuma da hakuri aka sanmu,
Mu shanye duk wani bacin rai da zamu fuskanta a gdajen aurenmu,

Haka ne zesa gdan ya bunkasa cikin so da girmamawa" sheshekar kukanta neh yasa Mama ta dafota,

"Kinga da kin fadamin dana hada masu irin cimar mu ta hausawa,

Akwai wani abu da kikeso ki koma dashi"
Data tuno tayi laifi tana bukatar abinda ze tayata neman yafiya saita tashi zaune ta share hawayenta,

"Aya, gyada da kuma zobo" tada ta zaune Mama tayi,

"Muje ki duba abinda kikeso toh"
Hannunta Mama ta kalla,

"Gashi ke koh dan gayun bakiyi bah" ta duba kanta

"Zanyi kitso in naje can" Mama bata saurareta bah,

"Bari ni in hadamaki kayan, Allah yasa masu gyaran jikin dana sani su yadda kije"
Ba yadda batayi bah akan Mama ta barshi amma taki,
Gashi gobe sallah, da kyar aka samu wani wuri suka kutsa ta da daren akayi mata,

"Asma'u" uhmmm tace da bacci cike da idanunta,
"Tashi, kuma ki kira direban ki yazo"
Bata fuska tayi tana laluben wayarta,

"Karfe hudu fah Mama"
"Eh sai ku isa da wuri, tashi ki shirya da an idar da sallar asubah sai ku wuce"

Dadinta daya ba itace ke tuki bah, zata samu tayi bacci cikin mota,

Neman bacci tayi ta rasa data shiga mota, haka ta zuba idanu a kan hanya,

"Kana da matane" yace Aa a dan kunyace,

"Iyayenka fah" ta sake tambaya,
"Suna nan lfy"
"Tare dasu zakayi sallah koh" saida ya dan jinkirta kafin ya bata ansa,

"Zan je in gansu in na samu lokaci, yanayin aiki" ta jin jina kai

"Bari muyi masu tsaraba" tasa ya tsayar da motar suka siye veggies,

"Nagode sosai Hajia" dariya tayi kafin ta rokeshi kar ya kirata hajia,

"Angama" lokaci lokaci sukan danyi hira har Allah ya kaisu gda lfy,

Da addu'a iri iri ta shiga cikin gdan,
Bigewa tayi da kallon yadda kowa ke sama da kasa, ta zata saboda ranar sallah ne,

"Barka da sallah Sir" da hausa aka maida da barka da sallah, kuma ta gane muryar shi ce,

Dan lekawa tayi taga yanata bah ma'aikatan kudi wai barka da sallah, girgixa kai tayi tana fata yasan abinda hakan ke nufi,

"Sannu da zuwa" wani daga cikin wadan da ya amshi kudi ze wuce ya ganta, sai ya gaisheta,

Kallon mutum yayi sannan ya kalli inda take, hadiyar miyau tayi ta natsu sannan ta bar wurin saboda bugun zuciyarta daya karu, ga kallon da yake mata,

"Wifey" dan karamin gudu tasa ta fada cikin kitchen,

Masu aiki cikin kitchen din na ganin ya biyota sai sukayi waje,

"Guduna kikeyi har yanxu, watau ga dodo koh" tayi saurin girgixa mai kai,

"Ka yini lafiya" ita data duka shi sai ya zauna kasa yana kallonta,

"Barka da sallah" ta sake fada dan yaki amsa na farkon,

"Kinyi kyau" a kunyace tace ta gode,
Tare suka mike tsaye, tana kallon idanun shi zata kauda kai cikin yanayi na jin kunya,

"Ina barka da sallah ta?" Ta dukar da kai kasa,

"Rowa zakiyi min" bag dinta dake rataye a hannu ta bude, duka kudin ciki ta damka mai,

Kallon kudin yayi sannan ya kalleta,

"Kema kina so in baki wani abu" ta girgixa kai
"Bakya san komai daga wurina kenan" ta sake girgixa mai kai
"Meh kikeso toh?"
Saida ta kwantar da murya kafin tayi magana,

"Ina so kayi hakuri dan Allah" hmmm yace yana bude jakarta, kudin ya maida cikin kafin yayi zipping,

"Bana son kudin wani abu nakeso na daban" ya rike hannunta yana wasa da lallen da akayi mata,

"Zaki bani" da sauri ta daga mai kai,

"Toh bani" a kunyace tace bata san abinda yakeso bah

"Ni nasan abinda nakeso, in dauka" ta daga mai kai,

Da wani freakish grin ya bugata da bango, har saida ta tsorata,

"Ai keh kikece in dauka, koh kin fasa" dakewa tayi tace No,
"Good" yace yana mata wani irin kallo,

Da sannu kuma ya hade jikinsu wuri daya, kallon daya bi lips dinta dashi ya ganar da ita abinda yakeso,

Kokarin tureshi tayi sai ya rike duka hannayenta,

"Too late love" kulle idanu tayi gam yana farma lips dinta da nashi,
Ta cije hakoranta amma hakan beh hanashi watanda da lips dinta bah, a sannu kuma ya saki hands dinta ya dora hannu daya a kugunta dayan kuma yana gefen fuskarta,

"Meye hakan kukeyi, bakuji nace kuyi sauri bah"
Ji tayi anayi mah Mom bayani
tun lokacin ta hau tureshi, amma sai yayi wani sound daga makogaran shi meh kama a takura,

"Ehsaas!" Mom ta fada da katon murya,
Kafin ta shigo har ya saketa ya koma chan gefe,

"Raina a bace yake basai na fada bah, kuma kuna kokarin karamin bacin rai,
Ku fitan mun a kitchen" nufota yayi ze rike hannunta,

"Ban samo bah Madam, lokacin sallah ne, abubuwan duk an saye su"
Wanda yayi maganan a bakin kofa ya tsaya beh karaso cikin kitchen din bah,

"Yanxu daka dawo so kake ni in fita in nemo Veggies din koh meh"
A sannu ta kira sunanta,

"Yanxu da zamu taho mun siya veggies akan hanya"
Hannunta da beh samu ya rike bah kenan Mom ta fizgota,
"Lissafo man abubuwan da kika siyo"

"🥒🥕 cabbage, green beans,peas da pumpkin"
Riko hannuta tayi suka fito waje,

"Dama ina neman ki, na yadda da dafa abincin ki dan haka ke zaki dafa ma bakina abinci"
Da sauri ya biyosu yana Mom
"What!" tace a dan tsawace

"Mom" yayi fuska kallan tausayi,

"Yanxu take dawowa, akwai gajiyan hanya safiya"
Zata gaishe da Dad maganar Mom ta hanata,

"Koh a gajiye kike" ta girgixa kai da murmushi

"Aa, bacci nasha a kan hanya"
"Kun ji dai koh, muje Asma'u"
Kafin su tafi saida ta kalleshi taga ita yake kallo da fuska daure,

'Laifina ne toh' irin kallon da yayi mata kaman yana bata ansa

'Waya saki kiyi magana, ina neman kubutar dake'

kafin ya haura sama

"Kaji dashi" inji Mom,
Lokacin yin sallah kawai take samu, abinci kala kala suka dafa na gda dana waje,

Abinda Mom ta tayata dashi shine dandana wa da kuma nuna mata yadda zatayi,

"Masha Allah" Dad ya shigo dining area din yana shakar aroma din dake tashi,

"Uhm uhm, sai sunzo kafin muci tare" ta tada Dad daya zauna saman kujera
"Muje falo, nasan ka yanxu zaka batamin presentation"
Yace toh yana mikewa tsaye,

Gimtse dariyarta tayi dan saida ya bata kam, tun kafin mom ta lura saita gyara tsarin abinda daya dauka daga cikin wani tray,

"Ehsaas ka shirya koh" yace uhmm can kasan muryar shi, kallo daya yayi mata ya kauda kai,

Bacewa murmushin da takeyi yayi,

"Tunamin su wamah zasu zo" ta daure fuska,

"Sorry na tuno" inji Dad yana gyara necktie dinshi,
Hannunshi ta ture tana gyara mai,

"Dr Sayyid da iyalenshi, ka gane wanda nake nufi koh Ehsaas" tsoron ce mata Aa yayi,

"Diyarshi Danyah fah?, na taba hadaki da ita"
Uba da Da suka kalli juna,

"Meh suka zo yi" kallon datayi mai yasa yayi kasa da kai,

"In nine kai zanyi fixing face dina in dora murmushi, daga uwa duniya suka zo ganin ka,
Gwara ka tarbeta da mutunci"

Ji tayi kaman an soka mata wani kaho a zuciya,

A daidai lokacin aka latsa door bell, zuciyarta ta fara harbawa,

"Asma'u jeki ce umma ta sauko"
Tace toh, tana jan kafa,

Ji tayi numfashinta na daukewa dataji wata siririyar murya na kiran sunan mijinta

Bata iya jurewa bah saida ta kalli baya taga ko wacece,

"Danyah" shima yace a dan sanyaye,

"Naji dadin kara ganin ka" yace nima haka, harda hannu ta mika mai wai su gaisa,

Bata iya karasa kallo bah ta nufi dakin hajia, bayan ta isar da sakon Mom sai ta nufi nasu dakin,

Tana rufe kofar dakinsu ta silale kasa tana danne zuciyarta,

Duk yadda taso ta hana kanta zubda hawayen kishi amma abin ya faskara,

'Ai dama tace zamanki na dan lokaci ne kuma kema kina da KUDIRIn zama na dan lokaci,

Dan ki biyasu Alkhairin da sukayi maku har suke tauye maku hakki dashi,

Kiyi farin ciki manah Asma'u, karshen BOYAYYEN KUDIRIn ki ne yake zuwa,

Da zaman auren ki ya kare dashi zaki koma ga iyayenki, ki cika burin ki nayin karatu, sannan ki dauki nauyin iyayenki,

Ki kare hakkinsu ta yadda babu wanda ze kara wulakanta ku'

Kokawa takeyi da hawayenta, tana sharesu suna zubowa,
Gado ta hau ta kwanta taci kukanta ta koshi har bacci yayi awon gaba da ita,


Knocking akeyi a hankali har aka fara da karfi, ji tayi ana kara lullubeta,

"Yi baccin ki bari in duba" ya rada mata a kunne,

Yaye bargon tayi tana tashi zaune,

"Asma'u karki shagala, da wuri zaki hada breakfast dan fita zamuyi, kinji koh"
Tace Eh tana mata sai da safe,

"Wai Mom yaushe zasu tafi" harara ta watsa mai,

"Sati zasuyi, hobe Kano zamu suga hawan sallah, suna nan har a gama"
Tana jin haka ta mike ta shiga bandaki,


Ranar sai gata ta fito daure da towel dinta iya cinya, abinda bata taba bah tunda sukayi aure, kullum da rigar wankan data wuce guiwwa take fitowa,


Yana zaune saman gado koh kayan jikin shi beh cire bah,

"Kin rufemin kofa, bayan kinsan nima wankan zanyi"

Wani yatsina fuska tayi da yayi shagwaba yau,
Bata bashi ansa bah ta karasa shiga cikin dakin sa kaya abinta,

Kanshi yasa cikin hannu yana tunanin yadda ze bullo ma matsalar dake kunno kai, dama yasan baxata ji dadin abinda sukayi mata,

Suyi baki amma ace baze nunata a matsayin matarshi bah,
A ranshi yana son sanin dalilin Mom na cewa ya barta karta zauna dasu suci abinci tare da bakinta,

Mikewa yayi ya nufi closet din, dan baxe iya shareta bah bayan yasan dalilin bacin ranta,

"Wifey" ta amsa mai da na'am sannan ta fara abinda ya kaita dakin, dan ta tsaya tunani,
Bacin ranta ta boye sannan ta hadiye duk wani gunguni dake san barin bakinta,

"Ya dinner din, sun yaba da girkina" da ta juyo taga yadda yake kallonta sai taji duk jikinta ya hau kyarma,
Kwarin guiwwar data fito dashi daga bandaki ya tafi ya barta da aikin kunya,

"Cutie pie matso nan" a hankali ta tako zuwa gabanshi, ta dade nan tsaye bece da ita komai bah,

Duk ta tsargu,sai kokarin kare jikinta takeyi,

"Angel eyes" tace uhmm kafin ta dago suka hada ido,
A kunyace ta saukar da kanta kasa,

"Kin tuna bases dinmu" muryar shi kaman ya tashi daga bacci,

Buttons din jikin suit dinshi ta kai hannu tana tabawa, shafawa takeyi tana zagaye button din, ji yake kaman a saman jikinshi take wannan wasan numfashin shi nata yin sama sama,

"Wanne muke yanxu?" Ya cire hannunta daga jikinshi sannan ya cire coat din ya hada da necktie,

"Tunamin Amore"
Daya cire shirt din da singlet sai ya tsaya dan kar ta kasa kallon shi,

"Nunamin toh in bazaki iya fada bah"
Tana jin kunyar fadamai abubuwan da sukeyi, amma sai taji gwara ta fada data nunamai,

Dazu kishi yasa taji zata iya yin koma menene, yanxu kuma daya kashe mata jiki da kusancin shi sai kunyarta ta dawo,

"Come on show me, kin san kunyarki na matukar burgeni, kuma tana sani inji yanayi daban daban a jikina,
Ba kaman in kika hada da wannan murmushin naki"

Kallonshi tayi ta kasan ido kafin tayi sauri kauda kai da murmushin meh dauke da kunya,

"Husna" ya fada da shagwaba harda dan bubbuga kafa,

Dariya ta fashe dashi sannan ta make kafada,

"Kinsan san zan iya karban abuna koh" yana mike hannu ze riketa ta matsa baya,

Yana kara yunkurin tabata, sai ta matsa baya da sauri, hada ido sukayi, sun dan jima suna kallon juna kowa na jiran dayan ya fara motsi,

Murmushinta na kara fadada ya yunkura ze Cafkota, da yar kara ta kauce hade da tafiyar sauri,shima kuma ya daga kafa ya bita, closet din beh ishesu wasan bah saida suka dangana da daki,


Tsayawa tayi tana maida numfashi shi kuma ya kafeta da idanu bayan ya iso gareta,

"Bari in nuna maki inda muka tsaya" sai haki takeyi tana mamakin shi meh yasa fitar numfashin shi yake normal bayan tare sukayi guje gujen,


"Breathtaking" ya fada a hankali, bakinta a dan bude tana kokarin daidaita fitar numfashin ta,

Hannu ya dora a saitin inda zuciyarta ke harbawa, ya kawo fuskarshi daf da tata,

"In cigaba" ta bashi ansa ta hanyar daga mai kai a hankali,

Bayan hannun shi yasa yana shafa nata hannun har zuwa kafadarta, da wuyanta sannan ya tunkari tsakiyar kirjinta da yaketa kallo tun sadda ta fito dga wanka,


"Karki damu, shima wannan din yana da nashi lokacin" yana sa hannu a tsakiyar kirjinta tayi saurin rike mai yatsa ba tare da ta sani bah,

Murmushi yayi ya bata wannan ansar datasa tayi kasa da kai,

"Kafin lokacin, mu koma bases dinmu koh"

Babban yatsan shi ya dora saman bakinta yana zagayewa kafin ya sakashi ciki,
Ba tareda ta bada umarni bah harshenta ya dan lashi yatsan, kafin ta tsuke lips dinta,


Dan cije lip dinshi na kasa yayi, hade da dan tsss kaman abinda tayimai har cikin zuciyar shi yaji,


"Love" ya fada da takura kafin ya zare yatsanshi daga bakinta, hannunta damke da towel dinta,
Kokarin sadda kai kasa tayi sai ya dago habarta sannan ya hada bakinsu wuri daya,


Sun dauki lokaci a haka yana aika ma duk ilahirin jikinta sakonni, yanayin data shiga ya karo data fara maida mai martani,
Tana bukatar ta shaki iska a makoshinta, amma ji take abinda sukeyi yafi iskan mahimmanci,


Wani annamimin knocking akayi a hankali, kafin aka hada da sunan shi,

Tana jin voice din dake magana taji, komai ya fita ranta, take ta raba jikinta dana shi,

"Nemanka takeyi" idanun shi canza kala gashi sun kankance,

"Lokacin mune yanxu Husna, babu wanda ya isa ya takura manah"
Ana sake knocking a hankali ta nufi inda suka baro dan canza kaya,


Wata rigar bacci fara marar nauyi ga tsantsi kuma shara shara, ta zabo tasa, kh madubi bata kalla bah ta feshe jikinta da turare sannan ta fito,

Harta kwanta ta tuno Mom tace sati zasuyi a kano, tashi tayi taje ta hada mai kayan tafiya,


"Amore mio da kin barshi, yau baki hutu bah fah"
Fuskarta daure tana niyyan share shi, kuma ta tuno fadan datayi ma kanta na daina nuna mai bacin ranta,

"Wa ze hada kayan toh kai?" Ta karasa da yar dariya,

Ji yayi ba dadi, dan ya tabbata rashin zuwa da ita beyi mata dadi bah,

"Kin san meh nene love" ta girgixa mai kai,

"Bana so inje dake, kice bazaki dawo bah, tsoron kara fitar ki nakeyi"

Wata dariya tayi meh dauke da takaici, dakaji kasan tafi kuka ciwo,

"Tunda da kaine ai dole mu dawo tare, amma da ni kadaice da sai nayi watanni"

Hmmm yace yana gyaran murya,

"Kayan mu biyu kika hada neh?" Tayi saurin girgixa kai,

"Nayi yawo dayawa, kaje kai ka gano gari"

Beh san lokacin daya rungumota ta baya bah,

Sai yau ya gane mahaifiyar shi bata san mutane su san ita matar shi ce, kuma tanada KUDIRIn aura mashi wata matar,


Tabbas Husna ta sani, amma yadda take nuna mai kaman ba komai na kara sashi santa da yaba mata,

"Da mun dawo in shaa Allah honeymoon zamu tafi,
Na kagara inga daga ni sai ke, nothing and no one else"


Tun karfe 4 na safe ta farka sannan ta nufi kitchen ta hau hada masu abincin safe, sallah ya maidata dakin su inda taga har ya tafi masallaci,

Data gama komai saita tsaya wankewa, sannan ta koma daki tayi wanka,

"Ina kwana" yana amsawa ta mike zata wuce, saurin rikota yayi,

"Koh gaisawar kirki bazaki tsaya muyi bah"
Murmushi tayi sannan ta bashi peck a kumatu

Kafin ta gama jera abincin a dining table taji kaman duriyar yan gdan a falo,

Kitchen ta koma ta bar sauran yan aikin suka karasa jera kayan abincin,

Lokaci lokaci takan ji dariya daga dining area din, smiling takeyi dan ta hana kanta zubda hawaye,

"Husna" dama tana zaune saman counter, tana jin an kira sunanta sai ta koma karkashi,

Tana ji ana kai da komowo, tasan tafiya zasuyi, kaman taje tayi masu Allah ya kiyaye kuma tana tsoron abinda Mom zatace,

Bayan duk motsin ya lafa sai ta fito tana lekawa ta window,

"Baki ji inata neman ki bah" a dan firgice ta juyo dataji muryar shi,

"Sorry" tace tana

Please Login or Register in order to submit comment