Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

in bar duk abinda ya faru anan, in fara fresh taya zanyi haka in kullum iyayena da yan uwana zasu kasance cikin alfarmar ka"

Yayi saurin katse ta da No, yana girgixa kai

"No Husna, akwai abinda nakeso, kuma harga Allah in ban samu bah, bazanyi amfani da abinda nayi musu bah dan cinma burina, KUDIRI na akanki Husna"

Ta jin jina kai

"Abin kenan ai, duniya mutane basa yin wani abu sai sun san zasuci riba,

Fadamin abinda kakeso toh, ka fada da kanka ai, danyaya akwai abinda kakeso shi yasa ka tallafa ma yan uwana da iyaye"

Girgixa kai yayi yana shafa face

"Bamu da time din yin jayayya Husna, duk abinda na fadama ma Mom akanki in shaa Allah ze faru,


Kuma" πŸ˜”
Ya dan kara matsawa kusa da ita,

Akwai abinda nakeso" tace naji wannan ai, fadamin abinda kakeso


"Inata kokarin ganin Mom tayi maraba dake, bayan ban san matsayina a wurinki bah"

Ta bishi da idanu

"Dan Allah ki aureni Husna" sun kusan seconds 40 kafin ta daga hannu ta mareshi,

Yar kara tayi, bayan shine yasha mari

"R u OK " ya duka kasa yana duba hannun,
Kuka ta fashe dashi, sannan ta fara bashi hakuri

"Dan Allah kayi hakuri na mareka, Dan Allah, ban san Abinda yasa ni yin haka bah"
Yace hmmmmm da wani irin murya da bata taba jinshi dashi bah

"Kayi hakuri dan Allah" ta mike tsaye zata wuce, sai ya kirata


"Husna, ba bacin rai, fushi koh haushi a tare dani, sai tausayi,

Ina matukar tausayawa kaina,

Banzo kasar nan da niyyan aure bah, although ina son inyi auren,

Allah ya doramin sanki Husna bayin kaina bane bah,
Na fadama kaina in Mom tace bata amince in aureki bah zan hakura,

Amma yanxu naga kaman basai tace min Aa bah,

Ke zakiyi breaking heart dina,πŸ’”"
Ya dafe kirjinshi yana ajiyar zuciya

"Zan iya cewa its brokenπŸ’”, daga radadin da nakeji yanxu"

Tafiya yayi ya barta tsaye tana sharban kuka,

Mom kam tana kebewa da ummanta ta fadi abinda yasa take nisanta kanta da Asma'u

"Tunda nake da Ehsaas beh tabayi min karya bah, amma yau yayi, sannan yaje bada sanina bah yana inganta rayuwar wasu duk dan ya auri yarinyar can"

Hajia tayi shiru bata da bakin magana, dan duk halin nan daga wurinta ta koya

"Karki yanke mah danki hukuncin daze kwareshi, ke da bakinki kika ce kin san danki sosai,

Ina fadamaki ke zaki cutu idan kika rabashi da yarinyar nan, dan ya kwallafa rai already,

Kuma Asma'u batada wani aibu Safiya"

Mom ta katse ta

"A yanxu bah, ni ban manta bah in kin manta Umma, ba'a yaban dan kuturu sai ya shekara goma da yatsa"
Ta mike tsaye tana zagaye dakin

"Zan san abinyi gameh da wannan batun,

Akan Hanna kuma" hajia ta dafe fuskarta

"Ki share zancen nan safiya"

"Tattaki nayi fah dan in gane mah ido nah, bazan koma bah saina bata assignment,
Meh taramin rahotanni kawai nake jira ya kammala,
Sai in san ta inda zan fara",
Tayi mah mahaifiyar ta saida safe,

Fitowa tayi daga daki tana tamabayan inda mijinta ya shiga

"Sun fita da danki bada dadewa bah" ta koma cikin gda,


Ehsaas da zazzafan hawaye ya nufi cikin gda,

Yana shiga yaji an jashi ana rungumeshi

"Daddy" ya jawoshi suka fito

"Muje mu danga gari, saika fadamin komai ba wanda ka fadama Mom dinka bah,

Sannan sai batun Creme Caramel dinka"
Dariya ya kufce mai,

Zagaye suka fita cikin unguwa, jefi jefi suna haduwa da mutane kuma motoci na kai da kawo,

Fayyace mah babanshi zare da abawa yayi, tun daga zuwanshi kasar har zuwa abinda ya faru dazun tsakanin shi da Husna,


"Dad pls ka taimakamin, Naga first hand yadda Mom ta tsani talaka, kuma naga yadda take kallon Asma'u, nasan batayi mata bah"

Babanshi ya tsaya da tafiya yana kallon shi

"Bin iyaye yana gaba da san ranka Ehsaas, Zefi zama maka Alkhairi in kayi abinda mamanka tace"
Ya shagwabe fuska

"But dadd" kaman zeyi kuka

"Ka bari Asma'u din tace NA'am ta yadda, kafin ka tuntubi mamanka da zancen kaji" yace toh yana tuno marin daya sha

"Abin nan baxe zo da sauki bah" babanshi yayi yar dariya

"Ai haka love yake my son, kafi daraja shi in ka sha wahala akanshi sosai"

Ya jawoshi gefenshi sannan ya dora hannu saman kafadar shi,


"Karka damu, ina nan harsai ka ci nasara" yace nagode dad.





⚜B.W.AπŸ–Š
[3/26, 06:12] β€ͺ+234 706 870 0853‬: ⚜BRILLIANT WRITERS ASSOπŸ–Š




πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI.

πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’


Story& Editing by NOBLE JUDGE.
Writing KHALEESI.







⚜BRILLIAN WRITERS ASSOπŸ–Š


πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’


Wannan page sadaukarwa ne na musamman ga
ADMIN OF ADMINS

ZUBAIRU BABA HAYAT
Da mukafi sani da

YAYA HAYAT,

Jin jina da ban girma gareka, A groups dinka

COOL NOVELS, MAKEUP AND KITCHEN,
Mun karu sosai ta fannin girki, kwalliya ,harda zamantakewa,
Zumunci da kuma fadakarwa da nishadi,

Allah ya baka ladan hada mutane dayawa wuri daya dan su amfana da juna.

Ina mai tayaka murnar zagayowar ranar haihuwarka a yau,
22ND MARCH,

Allah ya Amsa maka bukatunka na Alkhairi ya kara daukaka zuwa wurare da baka taba tsammani bah,
Ya karo maka shekaru masu Albarka.

Yau ranar kace ka wataya san ranka,


A madadin duka members din, ⚜B.W.AπŸ–Š
ni KHALEESI ke cewa ka huta lfy,

OnceπŸŽ‚πŸΎ.
Again πŸŽ‚πŸΎ
Happy πŸŽ‚πŸΎ
BirthdayπŸŽ‚πŸΎ.


4⃣2⃣.

Da duk karfinta take sauri dan ta cinmashi kafin ya shiga dakinshi,

"Ehsaas " ta kwala mai kira,

Kaman badashi take bah haka ya shiga dakin yasa key,

Nata dakin ta koma sukuku, saman akwatinta data shirya komai nata ta dora kai, tana shirin fashewa da kuka,


"Kin kirani ne" da hanxari ta mike tana goge hawayen da basu zubo bah

"Tun tuni naketa neman ka"

"Banxata kira na kikeyi bah, dan nasha jin muryar ki a cikin kai na"

Yanxu da suka hadu bayan ta dade tana neman shi, kuma ta rasa yadda zata fadi abinda takeso

Sai wasa da yan yatsunta ta tsaya.




Kwana uku kenan yana shareta, tun ranar data mareshi,

Ta kagu ta koma gda ne, bakaman da mahaifiyar shi ta fito fili ta nuna mata bata santa,

Washegarin ranar da suka zo ne, ta tashi da wuri dan hada masu breakfast, gamawarta keda wuya saiga Ehsaas da mahaifinshi, dan haka tayi serving dinsu,

Sannan tayi dakin hajia ta gaisheta da yi mata ya jiki, sannan tace mata ta gama abinci


"Asma'u so kike sai na fada da bakina kin sa naji kunya" tace ban fahimta bah hajia

"Aikin da kikeyi nake magana akai, mun warware ai, yanxu koh tsinke in bakyaso bazaki daga bah a gdan nan"

Dan numfasawa tayi sannan ta gyara tsugunnawarta

"Nagode hajia da kika janye batun ki, Allah ya saka maki da Alkhairi ya baki gdan Aljannah"

Da fara'a hajia ta amsa da Amin

"kuma batun aiki, sakai ne hajia, ina sonyi shiyasa nake yi har yanxu"

Hajia tace shikenan amma ta daina ba kanta wahala,


"Kin gaishe da Safiya" tace Aa

"Amma yanxu zanje bayan na gama hada maki ruwan wanka" tana gamawa ta nufi dakin da dan fargaba,


Da sallama ta shiga dakin, sannan ta sakeyi dataji shiru ba'a ansa bah,

Har zata fita kuma taga wasu abubuwan na bukatar a kimtsa su, saita fara tattarawa ,

Zata zuba wasu abu cikin kwandon shara taga kwalin turaren data siyo, ta zata kwalin ne kawai sai da taga spray din mah a ciki,

Fiddo su tayi tana dorawa saman side table,

"Ni na yarda su, basuyi min bah"
Da en eena ta duka ta gaishe da mahaifiyar shi

"Lfy lau, ya mah sunanki" ta tambaya bayan tayi kaman tana naxari

"Asma'u " Mom ta maimaita bayan ta fada,

"Kanshin su beyi min bah, shi Ehsaas din ai yasan irin abinda nakeso, da har ya amshi wannan a matsayin wani tsaraba"

Ta dukar da kai tana neman abin fada

"Zoki ga" ta mata alama data biyota

"Kin gani" tace Eh,
Turaruka ne designer ko wanne da irin nashi kanshin

"Baki taba ganin irin su ba koh" tace Eh

"Banyi mamaki bah, ai bana common people bane bah, ballantana talaka"
Ita kuma sai aikin maimaita sunayen su cikin kanta takeyi,
'Black opium, j'adore, coco Chanel, hypnotic poison, black orchid, Allah mai iko ni Asma'u'

"Muje muci abinci, dama ina ta son magana dake ba tareda My Dearest Son a wurin bah"

Suna kaiwa bakin kofa sai gashi a tsaye a wurin

"Mom, yanxun nazo kiran ku dama" tana ganin wannan daman ta tsere dakinta,

"Har yanxu baka fadamin abinda nasan kana so ka fada bah"
Maimakon ya jata zuwa dining area sai ya maidata daki,


"Mom, nasan bazan iya boye maki komai bah"
"Kasan da haka jiya ka zauna kana min karya" kasa yayi da kanshi yana dan jan hanci kaman zeyi mums

"Mom kiyi hakuri dan Allah, duk abinda nayi dan tayi maki ne"

Ta sake katse shi
"Karka lakamin ni ban saka kayi karya bah, kuma baka daukeni bakin komai bah,

Da kana girmama ni da bakayi komai gameh da rayuwar su bah, sai ka sanar dani,

Yanxu ne mah na fara jin bacin ran"

Ta juya zata tafi, da sauri ya duka kasa ya rike kafafunta yana kuka

Bataji dadin kukan shi bah, amma taji dadin cin nasarar da tayi na sashi nadama,
Yanxu zata iya sashi yayi duk abinda takeso,


"Ni ka barni kaje wurinta, tunda tafiye maka ni" wani kukan ya fashe dashi

I
"Pls Mom ina sonta, amma sai kin yarda zan iya yin wani abu akai"

Tasan horon yayi haka amma, saita cigaba da nuna fushinta, shi kuma sai sharba kuka yakeyi yana bata hakuri,

"Safiya" ta shagala tana dariya ciki ciki, bataji shigowan babanshi bah,

Daga yadda yake kallonta tasan beh aminta da abinda takeyi bah,

"Okay Ehsaas yayi haka nan" ta dagoshi tana janshi jikinta harda dan bubugamai baya, kaman karamin yaro shima kuma ya shige jikinta,


"Tnk u mommy, am sorry" babanshi ya girgixa kai yana karsawa cikin dakin

"Kin gama koh, yanxu zaki barshi ya auri matar da yakeso koh" tayi kaman bataji abinda babanshi yace bah,

Saida ya tsareta da idanu sannan ta dan, janye shi daga jikinta

"Da alamu babanka ya yaba da Matar daka zaba" ya danyi kasa da kai yana goge hawayen shi,

"Na zabe ta, amma ita bata zabeni bah"
Mamanshi tayi wani stylish tsaki

"Ta kam ganka, san kowa kin wanda ya rasa" yayi dariya yana zama saman gado

"Barni da ita, zanji dalilin ta na kin Fine Boy dinah, In shaa Allah labari meh dadi zan fada maka bayan mun zanta da ita"

Yace ya gode sannan, yayi niyyan barin dakin

"Kaje ka huta kaji Son, kafin lokacin tafiya ta yayi"
Ya ce Toh,


Tana kwance dakinta tana buga subway surfers a wayarta, akayi mata sallama,

"Gani Hajia ance kina kirana"
Ta fada bayan tayi sallama ta ansa

"Shigo manah in-law dita"
Bata san dalili bah, amma tunda tazo gdan da ta ganta sai taji faduwar gaba,

"Ina wuni" ta durkusa ta gaisheta,

"Daga abinda na gani, akwai ki da diri" ta kankame jikinta ta cikin hijab

"Umma tacemin dama kullum cikin hijab kike, koh ta yaya yaga jikin ki harya kwadaitu"

Ta fara neman tsari cikin ranta,


"Koh kullum in yaje dakin ki da dare wani abu na shiga tsakanin ku"
Fashewa tayi da kuka

"Safiya nace maki karki saurari zancen yan aikin nan,
Ni nayi sakaci dana bari suna kawo min gulma ban kwabe su bah"

Safiya ta juya ga mahaifiyar ta

"Da ban gani bah bazan tambaya bah Umma, na gaya maki ranar da muka zo da ido na na ganshi ya nufi dakinta,

Bashi ya fito bah sai gab da Asubah,

Jiya mah dana je dakinshi da tsakar dare baya ciki,
Da babanshi na nan ne sai ince sun je yawon daren su da suka saba, amma baya nan,

Tambayan ni meh na iske shi yana yi da asubah danaa shiga dakinshi, daga wanka ya fito"

Kara fashewa tayi da kuka,

"Karki damu nasan dana ba dan iska bane bah, amma duniyan nan koh zanin jikin ka baka shaida dan baze fada maka bah in ze yage"

Sa hijab din tayi ta rufe bakinta kar kukanta ya fito,


"Fadamin tsakani da Allah, meh kukeyi? "
Kasa magana tayi sai aikin girgixa kai da takeyi

"Shikenan na yadda, gwara azo ayi auren nan koh ze kashe kishin ruwan dake damun shi,

Dan nason infatuation ke damun shi yake ganin kaman sanki yakeyi"


Dukawa kasa tayi bakinta na rawa

"Dan Allah ku barni in tafi gda, ni bana son in aureshi"

"Privilege ne dana ya kula, karki cika min kunne tashi ki tafi"
Batayi motsi bah tana nan tsugunne

"Bakiji meh nace bah"

"Allah ni bana sonshi kuma bana so in aureshi, bashi kadai bah ni bana son inyi aure, dan Allah ku barni in tafi, bazan sake koh ambaton sunan ku bah"

Matsowa tayi daf da ita sannan ta mikar da ita tsaye

"Dana nason aurenki kuma abinda ze faru kenan, kinji ni koh,

Kuma in kika ce bah haka bah, toh zaki ga wani bangare na da bazaki so bah,

Gwara ki rufa ma kanki asiri ki aureshi, kafin in kai ga taba na kusa dake,

Dan abinda dana keso shi yake samu"

Kallon Mom tayi sannan hajia

"Ban taba shiga hakkin wani bah, ban taba zaluntar kowa bah a rayuwata

Meh yasa kuke yimin haka nida yan uwana, meh yasa kuke amfani da dukiyar ku akan abinda baze amfane ku a lahira bah"

Da kuka take wannan maganar tana kallon kasa

"Asma'u jeki abinki"Mom tace mah hajia Aa

"Kinji na rantse maki koh kiyi abinda nace koh kiyi dana sani,

Bana sassauta wa kaman mahaifiyata, ni in zanyi da karfi nakeyi yadda zaka dade da raunin"

Da gudu ta juya tayi dakinta tana kuka, kayanta dama a hade suke, kadan kawai ta karasa shiryawa,

Ta dade nan zaune tana tausayawa kanta har dare yayi sosai,

Karar bude kofar falon dakin taji,
Da sauri ta mikar da akwatin sannan ta hau saman gado tayi lamo,


'Da gaske ne' haka tayi ta fada a ranta,

Bata iya bacci bah daren, data rufe idonta sai taga kaman ze cutar da ita,

Shi kuma baccin shi kawai yakeyi hankali kwance,

Gab da Asubah ya farka, bayan yayi mika da addu'a kuma ya zagaya gefenta,

Shafa fuskarta yayi sannan ya manna mata kiss a gashi, ya rada mata i love you a kunne,


Yana fita ta kara karfafa zancen ta na barin gdan, tun kafin abubuwa suyi nisa.


Karfe 7:00 daidai na safe ta fita nemanshi, ta rasa wani abu zata fara fada,


"Ina son kunyar nan taki, abin na biyu dana gani a tare dake dayasa na kudirci wani abu a raina"
A hankali ya takowa izuwa gareta

"Na farko jikin ki da kika rufe, na lura kuma haka kike, kunya da Hijab dinki basu sa na kamu da sanki bah saida naga eyes dinki,

i was hooked dana ga eyes dinki, kal kal gasu so expressive, ina iya ayyana abinda kike son fada in dai ina kallin idanun ki yayin da muke magana"


"Na rasa ta yadda akayi na kamu da sanki,

BOYAYYEN KUDIRI na shine in rabaki da mijinki in aureki Husna, wannan kadai ne niyyan babu wani kuma"


Saidai taga sun hada ido, bata ma san ta dago kanta bah

"Kar in cika ki da surutu, meh yasa kike nema nah? "

Ya matsa baya dan da ya shagala da fada mata abinda ke ranshi ya kureta har jikin bango,


"Tsoro nakeji Ehsaas " ya nuna damuwa ta hanyar bata fuskarshi,

"Kar komai ya baki tsoro My love, ina tare dake, zan kareki daga duk abinda zeso cutar dake"

Ya fada ba wasa a muryarshi, alamun da gaske yake

'Meye abin gudu a tare dashi Asma'u ' ta kara kallon shi da kyau

Ya hadu iya kar haduwa, yana da tsawo daidai shi, haka jikinshi mah kaman na dan kwallo, komai fit,

Ga shi ba girman kai, hakuri, tausayi, rikon amana da fadin gsky, meh kuma zata nema a wurin da namiji,

Kila shagwaban ne kadai ya kamata ya bar yi, amma tanayi mai kyau

Ta tsinci kanta da yin murmushi,

"Will you marry me" sai bayan yan seconds kafin kwanyar shi ta gama tantance abinda tace


"Bama irin wasan nan Husna, ina son ki amma bazan jure bah in zaki dinga jamin rai"

Ya bata fuska


"Da gaske nake, in da gaske zaka aureni, kuma kana sona, ni ma zan aure ka"

Taga lokacin daya nufota, bata san lokacin daya karaso inda take bah har ya dagata sama yana juyi da ita,


"Ka saukeni" duk abinda take fada baya ji, murna da farin ciki sun toshe kunnen nashi,

Dan kanshi ya gaji ya sauketa kasa sannan ta juya zata tafi, jawota yayi ya rungumeta ta baya,

Kyarma jikinta ya hauyi, bari kawai take kaman kankara ne jikinshi,
Kokawan sha kan iska takeyi, ji take kaman ana fizgo iskan daga cikin makoshinta,

Tana jin yasa fuskarshi jikin nata yana bata pecks a kumatu ta sike, ta kasa ko wani motsi,
Ihu kawai takeji bata san daga ina yake fitowa bah,
sai da taji makoshinta na zafi kafin ta gane itace ke wannan ihun,

"I swear Mom babu abinda nayi mata, granny Ma? " duk ya tsure daya ga Masoyiyar tashi kwance kasa tana fidda numfashin wahala,


"Asma'u kina jina" ta daga masu kai tana kokarin tashi zaune

Yana kai hannu ze tayata tashi tayi saurin matsawa baya,

"Ehsaas " mamanshi ta fada da babban murya

"Allah babu abinda nayi Mom,

May be i got over excited and hugged her,

But shikenan mom, Allah banyi komai bah"

Tayi ma Mamanshi murmushi da hajia


"Lfy ta lau hajia karku damu, ji nayi numfashi na na neman daukewa"

Mamanshi ta bata fuska, sannan ta daure fuska

"Kai Allah ya sauwake, daga tabaki shine kika wani hargitse haka,

Dama ance masu shiru shiru dasa dogon hijab dinnan duk sune basa iya controlling kansu, mtsewwwwww"

Ta fada da hausa sannan ta bar wurin

"Cewa tayi ka kara yimin laifi in fada mata, zatayi maganin ka da kanta"
Yayi dariya yana cewa ,zata iya

Tunda suka fita ya zauna kasa yana naxari, tasan abinda Mamanshi ta fada yakeson sani,

"Dan Allah ka maida ni gda"
Ya jin jina kai bayan dan guntun tunani da yayi,

"Gobe toh in Allah ya

Please Login or Register in order to submit comment